yi ringing, dubawa ta yi ta ɗaga tare da cewa.
"Hello...okay gani nan fitowa... Okay.
Kallon Nafeesat ta yi ta ce .
"Na yi sabon kamu ga shi can waje."
"To sai kin dawo."
Ta faɗa tana kwanciya akan gadon yayin da Hafsat ta fita waje don haɗuwa da sabon saurayin da ta yi.
Tana fita daga gidan ba ta ga maza guda biyu a saman babur, fuskarsu sanye da facemask. A hankali ta ƙarasa wajen su tana kallon su kafin ta yi magana ɗaya daga cikinsu ya bude wata kwalba ya watsa mata abinda ke ciki a fuska. Wani gigitaccen ƙara ta saki tare da kwanciya a Wajen, daidai lokacin da suka gudu akan babur ɗin a guje.
Kasancewar unguwar ba mai yawan mutane ba ke kowa na cikin gida. Nafeesat da ta jiyo ihunta ta fito a guje sai wasu maza da ke cikin gidan.
Ɗaya daga cikinsu ne ya ce.
"Wa ya watsa maki acid?"
Ihu kawai Hafsat ke yi wanda har maƙota sai da suka fito, da sauri aka ɗauke ta zuwa asibiti.
Washegari ana gobe ɗaurin aure ba yadda Dad bai yi da Munnir ba akan ya zo ayi shagalin biki da shi amma sam ya ƙi amincewa, sai uzuri da ya kawo masa wai aiki ya rike shi.
Ɓangaren su Munnira da masoyinta Sudais kam sai shagalinsu suke ba kama hannun yaro an shirya lunching anyi shagali reception yayi kyau sosai.
Nihal dai ta saki jiki tana ɗan walwala amma ta san akwai damuwa a cikin zuciyarta, sosai take ƙoƙarin ɓoye damuwarta musamman ganin yadda dangin mahaifiyarta da mahaifiyarta ke murna da wannan rana, hakan ya saka ita ma ta yi ƙoƙarin ɓoye damuwarta don gudun sanyaya masu guiwa.
Amatullah kuwa dama duk yadda Ajmal ya so suyi wani abun sam ta nuna ba ta so sai dai walima da za ta sa a shirya mata ranar ɗaurin auren nasu. Sai dai ya sanar da ita cewa ranar da za kawo ta abokansa sun shirya masu dinner kuma dole taje.
Kasancewar wurare daban-daban ne za'a ɗaura auren ya sa aka tsara lokuta daban-daban. Na Munnir da Nihal a Adamawa ne za'a ɗaura, na Sudais da Munnira ma a Adamawa ne za'a ɗaura. Yayin da na Ajmal da Amatullah kuma a Minna za'a ɗaura auren.
Dan haka na Adamawa aka fara ɗaurawa da misalin ƙarfe goma na safiya jama'a suka shaida ɗaurin auren Munnir da Nihal, sannan kuma aka ɗaura auren Saidais da Munnira.
Duk da Munnir bai zo ba amma abokansa sun zo Sadik da Sulaiman. Don bai sanar da jama'a auren nasa ba.
Bayan an ɗaura na Adamawa ne kuma dangi suka bi jirgi don halartar ɗaurin auren Ajmal da Amatullah.
Dama shi Ajmal ya kwana biyu a garin inda ya tare a gidansa da ya siya a garin, shi da abokansa suka tare, har da abokan kasuwancinsa daga ƙasashe daban-daban.
Da misalin ƙarfe biyu na rana dubban jama'a suka shaida ɗaurin auren Ajmal da Amatullah akan sadaki Naira dubu ɗari biyu.
Farin ciki a wajen Ajmal ba'a magana,take ya yi sujudu Shakur.
Dr Fu'ad da Dr Khalil sai dariya suke masa wai yanzu hankali ya kwanta.
A wannan ranar angwaye biyu zuciyarsu cike da farin ciki wato Ajmal da Sudais yayin da zuciyar Munnir kuwa baƙin ciki ne fal a cikinsa.
Amare kuwa su ma dai Amatullah da Munnira zuciyarsu cike take da farin ciki, Nihal kuwa tausayin kanta ne kawai a cikin zuciyarta.
Mummy ma ta koma wata kala daban don ba ƙaramin takura take yi ba, don mahaifiyarta ce kawai a raye dama ba kula da ita take yi ba, abincin da suke ci ma Munnir ke taimaka masu da shi. Mummy duk ta rame ta yi baƙi kamar ba ita ba.
Kasancewar dama an siyewa Nihal kayan ɗaki a nan garin saboda nisa, duk an jera mata komai sai abinda ba'a rasa ba wanda idan za su kawo Amarya za su zo da su.
Ana gama ɗaurin aure karfe goma na safe aka kama shirin tafiya kai Amarya, kasancewar garin da nisa. An kai ta ta yi sallama da iyayenta inda aka mata nasiha mai ratsa zuciya. Baffa ma ya mata nasiha sosai ba abinda take yi sai kuka.
Motoci biyu na abokan Munnir Sadik da Sulaiman su suka ɗauko amarya da jama'arta.
Mota ɗaya Nihal ce da ƙawayenta su uku, a cikin motar Sadik suka shiga. Ɗayar motar kuma iyayen amarya ne ƙanwar Abbanta da yar Abbanta, sai kuma ɗiyar Baffa da ƙawar Mama ɗaya.
Tun a hanyar zuwa Nihal ke aikin kuka ƙawsyents na ta aikin rarrashi, Sadik ma da ke driving tausayinta ya cika shi, musamman da ya san Munnir ba son auren yake yi ba.
Ajmal kuwa yana can gidansa da ke garin Minna, don ya ce nan za'a fara kawo masa amaryarsa, sai sun yi shagali da abokansa kafin su wuce Kaduna. Gidan ya cika da jama'arsa kowa na abincin da ransa ke so, wanda ya sa aka yi order lafiyayyun abinci da naman kaji da sauran abinsha kala-kala.
Burinsa ya ga an kawo masa Amatullah a matsayin matarsa.
Munnira kuwa da misalin ƙarfe biyar na yammaci motocin ɗaukar amarya suka ji parking a ƙofar gidan Marka.
Ita ma nasiha aka mata mai ratsa zuciya, ta rungume Dad tana kuka, daƙyar aka ɓanɓare ta daga jikinta aka wuce da ita gidan mijinta.
Nasreen kuwa tunda ta tabbatar an ɗaura auren Ajmal Amatullah ta rufe kanta a ɗaki Affan ma korar sa ta yi ya tafi wajen mai kula da shi. Goge hawayenta ta yi sai kuma ta fashe da kuka, tana cikin kukan ne kuka sai ta fashe da wata irin dariya mai cike da manufofi, kamar wacce aka tsikara ta ɗauki handbag ɗinta da wayarta, takalmi ta saka ta ɗauki gyalenta a hannu ta rike ta fito daga cikin ɗakin.
Gudu-gudu sauri-sauri take saukowa daga stairs ɗin, falon dake downstairs akwai mutane da suke zaune wanda ko kallon su ba ta yi ba ta fice suka bi ta da kallo.
Parking space ta nufa Wada ɗuya daga cikin direbobin gidan ya nufo ta, don ya ga alamar fita za ta yi, da hannu ta dakatar da shi ta nufi ɗaya daga cikin motocin da ke parking space. Shiga ta yi tare da yi wa motar key, ta fige ta da gudu ta bar wajen tana danna horn ba kakkutawa.
Da sauri security da ke kula da ƙofa ya wangale mata gate ta fice, tun kafin ta kai ɗayan gate da zai sada ta da waje take danna masa horn, shima jiki na rawa ya wangale mata don ya san ba ƙaramin aikinta ba ne ta fara surfa masa zagi, don ya lura a fusace take tun jiya da ta zo fita, sai dai ya san kishi ne wanda duk macen da aka yi wa kishiya sai ta ji zafin kishin nan.
Da misalin ƙarfe shida na yamma mitaocin ɗaukar amarya suka yi parking a ƙofar gidan Mallam Abdullahi. Amatullah kuwa sai kuka take yi kamar ranta zai fita, tana zaune a gaban Ummanta tana mata nasiha akan zama aure.
"Amatullah yau Allah ya nuna mani ranar aurenki, ina godiya ga Allah da ya bani aron rai har na ga wannan ranar. Shi auren ibada ne bautar Allah kika je yi, kuma zaman auren zama ne na haƙuri, duk macen da kika gani a gidan mijinta haƙuri take yi irin rayuwar da kika yi a gidanku ba shi za ki je ki yi a gidan miji ba. Yi na yi bari na bari ki yi wa mijinki biyayya ki kyautata masa ki bi umarnin duk abinda ya umarce ki da shi matukar bai saɓawa mahaliccinki ba. Kada ki yi gardama ko jayayya da mijinki, idan ya ce wannan fari ne ko da kina ganin baƙi ne ki ce eh fari ne, da kansa zai gane abinda kike nufi ya san irin biyayyar da kike masa, ki kyautata masa ki nuna masa kulawa ki sauke duk wani haƙƙinsa dake kanki da kyautata masa hakan zai sa ya ƙara ƙaunarki, ki so iyayensa da 'yan uwansa ki kyautata masu ki ɗauke su iyaye ba surukai ko dangin miji ba. Ki zauna lafiya da kishiyarki, ki zama mai kau da kai akan al'amuran mijinki kishiyarki m, ke dai ki mayar da hankali wajen tarbiyyar ɗanki da cusa masa aƙida mai kyau a cikin zuciyarsa."
Sosai Umman ta mata nasiha mai shiga zuciya kafin ta ce su tafi wajen Abbanta ta masa sallama. Tana kuka ta rungume Umma suka tafi.
Abba ma ya mata nasiha sosai sannan ya masu sallama tare da fatan zaman lafiya a gare su.
Sai Magrib sannan motar ɗauko amarya daga Adamawa ta iso garin Minna, zuciyar Nihal sai bugawa take yi lokacin da ta ji an ce sun iso gidan Munnir, don daidai lokacin ta farka daga barci Bayan kukan da ta sha.
Ƙanwar mahaifinta ne ta zo ta fito da ita daga cikin motar, idanunta duk sun kumbura saboda tsabar kuka. Fuskarta lulluɓe da mayafi ta fito ƙanwar mahaifinta mai suna Aunty Uwani ta riko ta suka nufi ciki, da ƙafar dama ta ce ta shiga.
Sadik suka shigo da sauran kayan da suka zo da su. Sannan suka fice da motocinsu daga gidan.
Masha Allah madaidaicin gidan ya burge su m, sai addu'ar zaman lafiya suke masu.
Bayan fitar Sadik ya yi parking a gefen hanya ya ɗauki wayarsa ya dannawa Munnir kira.
Sai da ta kusa katsewa ya ɗaga ba tare da ya yi magana ba, cikin ɓacin rai Sadik ya ce
"Munnir wallahi ba ka da kirki, ka duba uban tafiyar da muka yi zuwa ɗaurin aurenka, mun dawo maka da mata tun safe muka tafiya sai yanzu muka iso, don wukaƙanci ko ka kira ka ji wani hali muke ciki ko?"
Munnir da ke zaune a motarsa ya kishingiɗa ne ya ce
"Na aike ku ɗaurin auren ne ko ni ne na ce ku ɗauko su ku kawo su gidana, da Amatullah kawai na tsara rayuwata don haka wannan matsalarku ce."
"Kar ka manta Amatullah yanzu matar wani ce, Nihal ce matarka ka rungumi ƙaddararka kuma..."
"Dalla Mallam ya isa!"
Cikin ɓacin rai Sadik ya ce.
"Ba laifinka ba ne, mun rabu da iyakinmu tun jiya muna ta maka hidamar har yanzu da dare y fara amma kake faɗa mani maganae banza ko?"
"Ai dama na ce kar ku je."
"Shikenan yanzu amaryarka da danginku suna can ka je ka yi masu order na abincin da za su ci."
"Ba abinda zan yi Sadki ka kiyaye ni fa."
Daga nan ya katse kiran wayar, kallon wayar Sadik ya yi tare da cewa.
"Allah ya kyauta."
Da kansa ya je ya masu order na abinci ya kai masu sannan ya bar gidan.
Bayan sun kammala Aunty Uwani ta saka Nihal yin wanka ta shirya ta cikin wani farin kishi mai adon golding a jiki, ta feshe ta da turarurruka masu daɗin ƙamshi.
Waya ta ɗaga ta kira Dad din Munnir ta sanar da shi sun gama, ya ce zai turo direba ya dauke su ya kai su gidansa a can zasu kwana, da safe sai su kamo hanya.
Ɓangaren Amatullah kuwa bayan ta yi wa Abba sallama suka fita har lokacin tana kuka.
Motoci ne kusan guda goma suka zo ɗaukar amarya, ɗaya daga cikinsu ya fito ya nuna wata mota yana cewa.
"Waccan motar ce amarya za ta shiga, kuma ita kaɗai ba tare da kowa ba. Wata ƙawar Amarya Fadeela ce ta ce tare za su shiga, wata maƙociyarsu ce ta ce.
"Tunda mota ɗaya suka ce na amarya su bari ta shiga ita kaɗai, Allah ya kai su lafiya."
Motar ce a tsakiya aka saka ta ita kaɗai sauran jama'a kowa ya shiga. Aka tayar da motocin suka bar layin , kowa na binsu da idanu.
Daidai suna gab da hawa babban titi bayan sun baro titin da unguwar su Amatullah suka ga jama'a sun taru kamar ana faɗa, hayaniya ya cika wajen dole suka tsaya a tsakiyar titin don ba hanya.
Wani mutum ne yana sanye da facemask ya ƙaraso wajen motar da amarya ke ciki, Amatullah kanta na bisa cinyarta sai aikin kuka take yi. Direban ya sauke gilashin motar ganin an tsaya a gefen sa ana knocking glass. Yana saukewa aka fesa masa wani abu a fuska. Take jikinsa ya saki, wasu mutane biyu suka ƙaraso suka ɗauki direban suka kama suka shiga cikin jama'ar, wanann mai facemask ne ya shiga mazaunin direban.
Ɗaya daga cikin security na Ajmal ya ga abin ya yi yawa ya fito kenan ya ga suna watsawa, ya koma cikin motarsa.
Sai ya ga motar amarya ta wuce a guje ta riga su barin layin, ya bi motar da kallo yana mamakin saurin meye haka.
A hankali motocin suka bar wajen.
*Maman Ihsan ce*✍️
🤦♀️ *'YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*Na*
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*LAST FREE FAGE*
Page1️⃣0️⃣7️⃣
Sai ya ga motar amarya ta wuce a guje ta riga su barin layin, ya bi motar da kallo yana mamakin saurin meye haka. A hankali motocin suka bar wajen.
Sai sheƙi da ɗaukar ido tsadaddun motocin suke yi.
Koda suka isa ko da suka tsaya a bakin gate ɗin tangamemen gidan horn suka yi , maigadi na ganin motocin da sauri ya wangale masu gate yana washe baki.
Cinna hancin motocin suka yi a cikin gidan. Bayan duk sunyi parking n ne aka fito wasu na kallon gidan da tsaruwarsa yayin da wasu ke raba idanu suna neman motar da aka ɗauki amarya da ita.
Ganin ba motar ne y saka wata ƙawar Amarya Fadeela ta ce.
"Jama'a ba motar amarya fa ana."
Hankalin wasu ya dawo kanta jin me take cewa, ɗayan daga cikin direbobin ne ya ce .
"Maybe suna hanya yanzu za su ƙaraso."
Wannan bodyguard ɗin Ajmal ne da ya kalli motar da suka dauke amarya ya fito yana amsa waya yana cewa.
"Eh Ahmad mun ƙaraso yan..."
Jin abinda ake faɗa ne ya sa ya katse kiran wayar ba tare da ya ƙarasa maganar da zai yi ba. Ƙaraswa ya yi da sauri yana tambayar me suke cewa. Nan suka maimaita maganar da suke yi .
Tunawa ya yi da lokacin da ya keƙo jama'ar suka watse da yadda motar ta ɗiba a guje. Ga shi bai san waye direban ba don Dr Khalil ne ya kawo sauran direbobin don shi ne ɗan gari kasancewar motocin da yawa bayan na Ajmal shi ya nemo wasu ya ce a ƙara da su.
Wannan bodyguard ɗin mai suna Abdulrazak ya kira wayar Ahmad ya ce ya bawa abokin ango Dr Khalil wayar.
Suna tare da Ajmal sai tsokanarsa suke ya yana dariya, Ahmad ne ya masa alama da ya zo, bayan ya taso ne ya ke samar da shi abinda ke faruwa.
Wayarsa ya ciro daga aljihu ya dannawa diraban kira kasancewar ya san shi direban Yayansa ne wani sanata.
Wayar na fara ringing kuka sai aka katse kiran wayar. Kallon Ahmad ya yi tare da cewa.
"Ta fara ringing aka katse maybe yana tuki ne."
Ahmad ya karbi lambar wayar sannan ya bar gidan ya nufi gidan da za'a kai amarya.
Ko horn bai tsaya yi ba ya yi parking a wajen gidan sannan ya shiga kai tsaye.
Abdulrazak ya ƙaraso wajen da ya ga Ahmed.
"Wallahi cunkoso mutane ne suka cika hanyar wanda hakan ya sa muka tsaya jiran su wuce, kasancewar ba wata hanyar da mota za ta iya wucewa. Da na ga jinkirin ya yi yawa ne sai na fito don na duba matsalar a daidai lokacin da suke watsawa na ga motar da ta ɗauki amarya ta bar wajen a guje. Ban kawo komai a raina ba na koma cikin motata na ja muka bar wajen. Koda muka ƙaraso nan sai na ji an ce ba motar da amarya ke ciki."
Sake gwada lambar Ahmad ya yi still wayar a kashe. Kallon Abdulrazak ya ji tare da cewa
"Ka koma ka bi hanyar da kuka bi ni kuma zan bi ɗaya hanyar ko za mu same su."
Daga nan Abdulrazak ya shiga motarsa yayin da Ahmad shima ya fita ya shiga tasa motar.
Sauran matan da suka rako amarya wasu suka shiga ciki wasu suka tsaya cirko-cirko, yayin da wasu suka fara ɗauro alwala dan gabatar da sallar magrib don lokacin sallar ta yi.
Ɓangaren Nihal kuwa tunda kowa ya watse ya barta ita kaɗai zama ta yi tare da yin tagumi tana tunani. Ganin lokacin sallah ta yi ne ya sa ta mike ta shiga bathroom dake cikin ɗakin.
Alwala ta ɗauro ta fito ta shimfida sallaya ta fara gabatar da sallah. Bayan ta idar ta zauna tana zuba addu'oi. Har ƙarfe tara na dare tana zaune akan sallaya ta haɗa kai da guiwa tare da faɗawa duniyar tunani.
Ahmad da Abdulrazak ba inda ba su zagaye ba inda dai suke tunanin za su iya ganin su amma shiru. Ba ko alamar motarsu.
Hankalin Ahmad idan ya yi dubu ya tashi, ga shi bai sanarwa Ajmal ba don yana tunanin zai iya gano su, haka Dr Khalil ma sai da ya zame jiki ya fita suka hade da su Ahmad.
An kira Umma an faɗa mata hankalinta ya tashi sosai, sai dai an kwantar mata da hankali ta hanyar cewa kila motarsu ce ta lalace a hanya. Ga shi Amatullah ma wayarta na hannun Fadeela ballantana a kira ta aji.
Bangaren amarya Munnira kuwa bayan ana kai ta gidan mijin ɓangaren Mama aka fara kai ta. Har bedroom ɗin Mama aka kai ta. A Gabanta aka zaunar da ita saman carpet, murmushi Mama ta yi tare da cewa.
"Ba baƙatar ku bani amanar ƴata domin ba matsayin suruka take a wajena ba ƴata ce, Mahaifinta da ni uwa ɗaya uba ɗaya. Kar ku ji komai in Sha Allah za ta ji dadin zama da ni, za ta maye mani gurbin Nihal."
Tayi maganar idanunta na kawo ƙwalla saboda tausayin ƴarta Nihal, don ta lura ba ta cikin walwala kuma ta lura kamar ba kyakkyawar fahimta tsakaninta da Munnir, ta dai yi kawaici ne kawai saboda Marka da Dad ɗin Munnir da ke tsananin farin ciki.
Nasiha Mama ta yi mata bayan ta goge ƙwalla sannan ta saka mata albarka suka mata sallama. Kai tsaye part ɗin amarya suka nufa Mama har bakin part ɗinta ta rako su, tana tuna shekaru biyu da suka wuce yadda aka kawo matar da Sudais ya taɓa aure wacce ta rasu da ciki.
Mama komawa ta yi ciki tana neman maganin bawan hawan jininta, don ta ji yana son tashi mata musamman da ta fahimci yanayin da ƴarta ke ciki.
Da misalin ƙarfe goma na dare kuwa abokan ango ne suka zo gidan. Motoci biyu ne suka shigo cikin gidan ɗaya na Sudais sai na abokinsa. Saidai ne sai abokansa guda uku. A ƙofar part ɗin Sudais suka yi parking.
Fitowa suka yi ɗaya daga cikin abokan ango mai suna Nasir yana rike da ledoji guda biyu hannunsa.
Kai tsaye suka nufi ƙofar da za ta sada su da falon.
Da sallama suka shiga falon, ba kowa sai ƙamshin turaren wuta dake tashi. Bedroom ɗin suka shiga kai tsaye. Tana zaune ita da wata ƙawar da ta samu ƴar maƙociyar Marka. Kasancewar Munnira ba wasu ƙawaye ne da ita ba, ba ta ma sanar da kowa zancen auren na ta ba.
Da sallama ɗauke a bakinsu suka tur ƙofar bedroom ɗin. Ƙawar da mai sun Zulaihat ce ta amsa masu sallamar .
Munnira tana zaune tsakiyar gadon sai Zulaiha dake zaune a side drawer.
Tsayawa suka yi suka yi siyen baki kamar yadda ake yi a al'ada, daga karshe suka masu fatan alkhairi suka tafi da Zulaiha.
Bakin ƙofar falo ya tsaya bayan sun fita ya tura ƙofar ya murza key ya rufe.
Komawa ya yi cikin ɗakin tana zaune kamar yadda ya barta, mayafin Liyafa da ta rufe rabin fuskarta ta sunkuyar da kanta ƙasa ya janye mayafin. Zama ya yi gefenta tare da shafa gefen fuskarta, a hankali ya mikar da ita tsaye, sumbatar goshinta ya yi tare da warware lifayar da ta yafa.
Kunyarsa ce ta kama ta dan haka sai ta yi saurin riƙewa.
"Bari na rage maki kayan mana sun yi maki nauyi ko?"
Girgiza masa kai ta yi alama a'a.
"Okay na san ba ki ci abinci ba zo mu tafi."
Ya ja hannunta suka fita zuwa falo. Zama ta yi a Centre carpet shi kuma ya nufi kitchen, fuskarsa ɗauke da murmushi da ka kan shi ka san yana cikin shauki🤦♀️ *'YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*Na*
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*LAST FREE FAGE*
Page1️⃣0️⃣7️⃣
Sai ya ga motar amarya ta wuce a guje ta riga su barin layin, ya bi motar da kallo yana mamakin saurin meye haka. A hankali motocin suka bar wajen.
Sai sheƙi da ɗaukar ido tsadaddun motocin suke yi.
Koda suka isa ko da suka tsaya a bakin gate ɗin tangamemen gidan horn suka yi , maigadi na ganin motocin da sauri ya wangale masu gate yana washe baki.
Cinna hancin motocin suka yi a cikin gidan. Bayan duk sunyi parking n ne aka fito wasu na kallon gidan da tsaruwarsa yayin da wasu ke raba idanu suna neman motar da aka ɗauki amarya da ita.
Ganin ba motar ne y saka wata ƙawar Amarya Fadeela ta ce.
"Jama'a ba motar amarya fa ana."
Hankalin wasu ya dawo kanta jin me take cewa, ɗayan daga cikin direbobin ne ya ce .
"Maybe suna hanya yanzu za su ƙaraso."
Wannan bodyguard ɗin Ajmal ne da ya kalli motar da suka dauke amarya ya fito yana amsa waya yana cewa.
"Eh Ahmad mun ƙaraso yan..."
Jin abinda ake faɗa ne ya sa ya katse kiran wayar ba tare da ya ƙarasa maganar da zai yi ba. Ƙaraswa ya yi da sauri yana tambayar me suke cewa. Nan suka maimaita maganar da suke yi .
Tunawa ya yi da lokacin da ya keƙo jama'ar suka watse da yadda motar ta ɗiba a guje. Ga shi bai san waye direban ba don Dr Khalil ne ya kawo sauran direbobin don shi ne ɗan gari kasancewar motocin da yawa bayan na Ajmal shi ya nemo wasu ya ce a ƙara da su.
Wannan bodyguard ɗin mai suna Abdulrazak ya kira wayar Ahmad ya ce ya bawa abokin ango Dr Khalil wayar.
Suna tare da Ajmal sai tsokanarsa suke ya yana dariya, Ahmad ne ya masa alama da ya zo, bayan ya taso ne ya ke samar da shi abinda ke faruwa.
Wayarsa ya ciro daga aljihu ya dannawa diraban kira kasancewar ya san shi direban Yayansa ne wani sanata.
Wayar na fara ringing kuka sai aka katse kiran wayar. Kallon Ahmad ya yi tare da cewa.
"Ta fara ringing aka katse maybe yana tuki ne."
Ahmad ya karbi lambar wayar sannan ya bar gidan ya nufi gidan da za'a kai amarya.
Ko horn bai tsaya yi ba ya yi parking a wajen gidan sannan ya shiga kai tsaye.
Abdulrazak ya ƙaraso wajen da ya ga Ahmed.
"Wallahi cunkoso mutane ne suka cika hanyar wanda hakan ya sa muka tsaya jiran su wuce, kasancewar ba wata hanyar da mota za ta iya wucewa. Da na ga jinkirin ya yi yawa ne sai na fito don na duba matsalar a daidai lokacin da suke watsawa na ga motar da ta ɗauki amarya ta bar wajen a guje. Ban kawo komai a raina ba na koma cikin motata na ja muka bar wajen. Koda muka ƙaraso nan sai na ji an ce ba motar da amarya ke ciki."
Sake gwada lambar Ahmad ya yi still wayar a kashe. Kallon Abdulrazak ya ji tare da cewa
"Ka koma ka bi hanyar da kuka bi ni kuma zan bi ɗaya hanyar ko za mu same su."
Daga nan Abdulrazak ya shiga motarsa yayin da Ahmad shima ya fita ya shiga tasa motar.
Sauran matan da suka rako amarya wasu suka shiga ciki wasu suka tsaya cirko-cirko, yayin da wasu suka fara ɗauro alwala dan gabatar da sallar magrib don lokacin sallar ta yi.
Ɓangaren Nihal kuwa tunda kowa ya watse ya barta ita kaɗai zama ta yi tare da yin tagumi tana tunani. Ganin lokacin sallah ta yi ne ya sa ta mike ta shiga bathroom dake cikin ɗakin.
Alwala ta ɗauro ta fito ta shimfida sallaya ta fara gabatar da sallah. Bayan ta idar ta zauna tana zuba addu'oi. Har ƙarfe tara na dare tana zaune akan sallaya ta haɗa kai da guiwa tare da faɗawa duniyar tunani.
Ahmad da Abdulrazak ba inda ba su zagaye ba inda dai suke
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 50 Chapter of 51