yi cikin mamaki rana kallon photon na tsawon mintuna biyu kafin ta kira Ammi .
Ammi dake zaune a saman sofa Dad na gefenta, sai Ajamal da ke zaune saman carpet yana jiran ne Kakarsa za ta faɗa.
Handsfree Ammi ta saka wayar ta yadda kowa zai iya ji, sannan ta amsa sallamar Umminta.
Can cikin wayar ta ji muryar Umminta na cewa.
"Wannan photo da kika turo mani da ba don na ga yanayin photon da kalar irin na zamani bane da na ce jikana ne da yake yaro, duk da cewar ina ta photunan shi da yawa na jarintaka amma wannan ɗaukar na yanzu ne, ko dai wannan sha sha shar matarsa ce ta haifi mai kama da shi?"
Gaban Ajamal ne ya faɗi jin abinda Kakarsa ke cewa.
"Ai dole na ce matarsa sha sha sha dan ba ta san darajar aure da kimar mijinta ba, ta ya mace da aure ta tare a gaban iyayenta a wata ƙasa, tsawon watanni ba za ta zo inda mijinta yake ba wai ita aka dole 'yar gata, dake suma iyayenta basu da..."
Ammi ce ta katse ta da cewa
"Ya isa Ummin ai yanzu ta dawo da ta ji cewa na yi alƙawarin matukar bar dawo ba sai na aura masa wata mace."
"Yanzu ita ta haifi wannan jarirai?"
"Ba ita ba ce."
"To ta yake tsakanin kama da jikana."
"Abinda ke bani mamaki kenan, dan uwar yaron ma jikanki ya ce bai sanya ba, kuma baya da alaƙa da ita kama ce kawai."
"Wannan ya wuce ace kama ne kawai ba wata dangantaka..."
Katse ta yayi bayan ya karɓi wayar hannu. Amminsa.
"Ke tsohuwa me kike nufi ? Kema biye masu za ki ko mene? Ke da ba ganin kirki kike ba ta ina za ki iya banbance kamanni?"
Ammy ce ta kira sunansa tare da masa kallon gargaɗi, wanda hakan ya sa ya miƙa mata wayarta.
Bara wayar ta yi sannan ya fice, daga part ɗin su, lambu ya nufa kai tsaye.
Ammi ta bawa Umminta labarin komai da ke faruwa a yanzu, jiminta ne ya yi sanyi ta ce za ta kira Ajmal dan ta yi magana da shi, kasancewar baya taɓa iya ɓoye mata komai, duk sirrinsa da ko iyayensa bai faɗawa ba ita ta sani, ba ya ɓoye mata komai, sanin hakan ya sa Ammi ta riƙe ta akan ta lallɓa shi ko akwai abinda ke faruwa da basu sani ba.
*Daga alƙalamin*
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
Comments & share
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
🤦♀️ *YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
Ban yarda a karanta mani shi a youtube ko a maida shi audio ba tare da izinina ba.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Page4️⃣0️⃣&4️⃣1️⃣
Ammi ta roƙe ta akan ta lallaɓashi ko akwai abinda ke faruwa da basu sani ba. Nan Ummu ta yi alƙawarin za ta saka ya faɗa mata komai, nan suka yi sallama ya kashe wayar.
Ɓangaren Umman Amatullah kuwa jikinta ne ya tsananta sosai, dan jininta ya hau ga ulser da ya saka ta gaba, kasancewar ba ta cin abinci yanzu.
Kamar kullun dai haka Mallam Abdullahi ya ke ta rarrashinnta da bata baki. Abu kamar wasa sai ya ga ai ma bata cikin hayyacinta ne gaba ɗaya. cikin tashin hankali ya fita waje dan zuwa nemo mai napep ya kai su asibiti.
Yana tafiya kamar zai tashi sama sai ga wata mota na horn, bai juya ba sai da motar ta ɗan dawo baya tare da sauke gilashin motar ya kira sunansa.
"Baba lafiya kuwa?"
Munnir ne da ke ƙoƙarin zuwa gidansu kamar yadda ya kanyi duk sati sai ya je gaida su, da kuma tunanin ko zuwa lokacin Allah zai saka Amatullah ta dawo.
Mallam Abdullahi ne ya dakata da tafiyar da yake yi tare da cewa
"Manniru kai ne ke tafe?"
"Eh ni ne Baba, fatan lafiya naga kamar hankalinka a tashe."
"Wallahi jikinta ne ya yi tsanani shine na fito neman mai napep dan mu kai ta asibiti.
"Shigo mana mu koma gidan dama gidan naka zan je, kafin na ƙarasa ne sai na hangi tahowarka."
Mallam Abdullahi ya shiga gaban motar suka ƙarasa gidan. Shi ya shiga ciki yayin da Munnir ya tsaya a waje yana jingina da motar.
Bayan kamar mintuna goma sai ga su sun fito, Abba da riƙe da ita, da sauri Munnir ya buɗe masu bayan motar Abba ya shigar da ita sannan shima ya shiga.
Munnir ma ya shiga cikin motar ya juya yana gaida Umma ta kasa magana a amsa masa ta yi da kai.
Jan motar ya yi tare da barin wajen.
Kai tsaye wani asibitin kuɗi ya nufa da su, mai suna *TOP MEDICAL HOSPITAL.* Acan ne aka kwantar da Umma. Dan jikinta ya yi tsanani dole aka kwantar da ita aka bata gado. Munnir ne ya ɗauki nauyin komai.
Zaune suke a falon Nafeesat, kowace da kwalbar Benelin tana sha a bakinta, yayin da Nafeesat ke busar hayaƙin shisha, daga gefenta kuma Hafsat ce riƙe da kwalbar giya tana zubawa cikin glass cup.
Bayan ta cika kofin ta shanye ne Nafeesat ta kalle ta tare da cewa
"Wato ke dai har yanzu baki yi sanyi ba ko? Bayan kwana biyun da kika shafe a hannun hukumar yaƙi da shaye-shaye bai sa kin ladabtu ba ko?"
Ƙara tsiyaya giyar take a cikin kofi sannan ta kalli Nafeesat ta na cewa
"Me za'a fasa to? Mutuwa ko hisabi? Ai ba abinda zan daina, sai dai idan mutuwa na yi."
"Baki tunanin cewa wannan ɗabi'ar ita ce tushen faruwar matsalar ki da wanda za ki aura?"
"Ai aurena da Munnir talas ne, duk rintsi ba fashi, sai dai idan ɗaya daga cikinmu ne ya mutu."
"Amma ya ce maki ya fasa aurenki."
"Idan ya isa ya ce a a dawo masa da kayan baikonsa mana, kar ki manta cousin brother na ne shi, bai isa ya ce wa iyayenmu ya fasa aure na ba."
"Amma baki tunanin ko kunyi auren za ki iya fuskantar wulaƙanci daga gare shi?"
"Nafi karfin wulaƙanci wallahi, babu yadda ya iya dani na zame masa ƙadangaren bakin tulu"
Tana magana ta na kurɓar giya tana ta zuba surutu.
Tashi ta yi tare da ɗaukar makulli motarta, hanyar fita ta nufa. Nafeesat ce ta ce
" kada ki fita a cikin wannan halin da kike ciki."
"Kada ki damu zan iya."
Bata jira cewar Nafeesat ba ta nufi motarta tana tafiya irin ta masu maye. Key tayi wa motar sannan ta fara driving.
Ko tafiyar mintuna biyar bata yi ba sai ga shi motar ta kufce mata ta sauka daga kan titin ta daki wata babban motar, sai sauti ga motarta ta bayar tare da fashewar gilashin motar.
Jama'a dake wajen hankalinsu ya dawo wajen da aka yi accident ɗin, cikin tashin hankali wasu sukayi kansu. Yayin da hafsat ke zaune amma kanta na kwance jikin sitiyarin motar, rufe sai jini da ke kan fuskarta.
Zaune yake a cikin lambun bisa wani kujera idanunsa a lumshe, ba abinda ke tashi wajen sai kukan tsuntsaye, ga duk wani nau'in kayan marmari a cikin lambun.
Zaune yake sai sanyi dake kaɗawa yana jin daɗin yanayin.
Tsawon awa ɗaya ya ɗauka a wajen sannan ta tashi. Kai tsaye part ɗinsu ya nufa.
A babban falon gidan ya ji motsi a dinning area, juyawa ya yi ya ga Rufaida da Mufida ne masu masu girki ke jera abinci a dinning table. Durƙusawa suka yi suka gaishe shi, da kai kawai ya amsa masu ba tare da ya ya magana ba.
Yana ƙoƙarin haurawa upstairs ne sai ga Nihal ta sha gabansa, hannu ta ware alamar ba hanyar da zai wuce, murmushi ne ɗauke a fusakrta ta kalle shi tare da cewa.
"Gud morning lovely bro"
Kau ka kansa ya yi tare da cewa
"Morning"
Ƙoƙarin bi gefenta ya haura upstairs ɗin yake ta kara tarar gabansa ta ce,
"Tun juya bana da lafiya ban iya fitowa ba amma shine ko ka tambaya ina nake ko.?"
"Sorry Allah ya baki lafiya."
Rausayar da idanunta ta yi tare da cewa.
"Ameen"
"Bari na wuce mana Nihal sauri nake."
"Za ka fita ne sai na raka ka, dama tunda na zo garin nan ban yi yawo ba."
Dafe goshinsa ya yi cike da takaici.
Ƙoƙarin cire masa hannun take sai ta ji Nasreen ta saka mata tsawa.
"Ke!"
Ɗaga kai ta yi tana kallon Nasreen da ke saukowa yayin da Ajmal ya samu ya haura upstairs ɗin.
Bayan Nasreen ta ƙaraso wajenta ne ta kalle ta sama da ƙasa tana cewa.
"Ki tsaya iya matsayinki Nihal."
Taɓe baki ta yi tare da cewa
"Idan kuma ba haka ba fa?"
"Ai dole gyaɗa ta yi mai idan ta ƙi ta sha matsa."
Wani irin dariya Nihal ta yi sannan ta kalli Nasreen ta ce,
"Da sannu Akuya take shiga gidan Kura ta ci ta da yaƙi, ta tarwatsa 'ya'yanta sannan ta mallaki karagar mulkin da take taƙama da shi."
"Ƙarya kike wallahi domin na maki nisan da ba za ki iya taro ni ba, idan har kina mafarkin cewa za ki mallaki Ajamal ne ma gara ki farka ki yi sadaka. Domin babu wata mace da ta isa Ajmal ya kalle ta a matsayin mace sai ni, domin kuwa ni kaɗai ce ke mulki a birnin zuciyarsa."
"Haba da gaske? To ita kuma waccan da ta haifa masa ɗa fa? Kenan na ke kaɗai yake kallo a matsayin mace ba, yadda kika haifa masa ɗa haka ita ma ta haifa masa, yadda kike zaune a cikin gidan nan haka ita ma ya ɗauko ta ya kawo ta kenan matsayinki da nata ɗaya ne a wajen mu'amala sai dai zuwa yanzu ban san wace ce mowa ba ban san wace ce bora ba, amma da sannu lokaci zai yi halinsa."
Daga nan ta juya zuwa falo ta bar Nasreen wajen cikin tsananin baƙin ciki da takaici. Ji ta yi kamar ta kurma ihu.
Juyawa ta koma inda ta fito.
Tura ƙofar ɗakin Ajmal ta yi ta same shi zaune saman gado, yana riƙe da waya a hannunsa ya kara a kunne yana magana. Da alama waya yake da Kakarsa.Dan ta ji yana cewa.
"Kin Sanni kin san abinda zan iya aikatawa da wanda ba zan iya aikatawa ba, ke za ki iya yarda cewa zan aikata zina? Na tsani fasƙan mutane, ba yarda za'ayi na aikata haka."
Ita dai Nasreen zuba masa idanu ta yi tana kallon sa, take yi duk da bata jin me yake cewa kasancewar da larabci yake maganar ita kuma ba ta jin larabci. Dan ko da ta je ƙasar Qatar ɗin da turanci take magana da su.
Numfasawa ya yi sannan ya ɗora da cewa
"Ki yarda da ni ba abinda na aikata, kawai wannan sharrin 'yan adawar siyasa ne. Kuma zan gano gaskiya.
Ɗayar wayarwa ce ta soma ruri ya yi sallama da Kakarsa sannan ya katse kiran wayar.
Ɗaukar wayar da aka kira shi ya yi ba kowa bane illa shugaban jam'iyarsu.
Amsa kiran ya yi inda shugaban jam'iyar ya gayyace shi zuwa zaman da za su yi.
Idanu Nasreen ta zuba masa ta kasa cewa komai, zuciyarta ta shiga wasi-wasi shekara shin ta yarda da shi ne ko kuma kada ta yarda da shi? Gaba ɗaya kanta ya kulle.
Shi kuma gaba ɗaya ya shiga damuwa a kwana biyu har ya rame, saboda baƙin ciki da tunani ga rashin cin abinci da baya ci.
Nasreen kuwa fita ta yi daga ɗakin kai tsaye downstairs ta nufa, kai tsaye ta fita daga part ɗin ta nufi part ɗin ma'aikatan gidan.
Tura ƙofar shiga ta yi yayin da ma'aikata dake a harabar wajen suka dinga durƙusawa suna gaishe ta.
suka
Ko amsawa bata yi ba ta kalle su tare da cewa
"Ina ne yarinyar nan take?"
Wata ce ta ce
"Wace yarinyar?"
"Ke! Kina dawo Mani da tamabaya akan tambaya?"
"Kiyi haƙuri ban san wa kike nufi ba?"
"Ina yarinyar da aka kawo tare da jaririnta?"
"Okay Amatullah?"
"Ban sani ba!"
"Muje na nuna maki ɗakinta"
Gaba ta shiga Nasreen na binta a baya suka shiga cikin falon har bedroom da aka warewa Amatullah.
Bakin Kofar ta tasya tare da cewa
"Wannan shine ɗakin."
Daga nan ta juya ta tafi yayin da Nasreen ta ta banka ƙofar da ƙafarta ta shiga.
Jin yadda aka banko ƙofar ne ya sa Amatullah tashi tsaye da sauri tare da zubawa mai shigowa idanu.
Ganin irin mugun kallon da Nasreen ke mata ne ya sa ta sunkuyar da kanta ƙasa.
Ba abinda ake ji da ɗakin sai sautin takun takalmin Nasreen, sai ƙwas ƙwas ƙwas ake ji.
Bayan ta iso gabanta ne ta ce,
"Ba'a koya maki tarbiyya bane daga gida? Ko baki san ki gaida mutane ba ne? Ko da yake tarbiyya ya yi ƙaranci tunda har aka shiga yawon duniya karuwanci daɗi ko? Sai ga shi har da riba kin samu."
Ta ƙarasa maganar tana kallon jaririn da ke kwance a gadon, an shirya shi cikin kayan sanyi masu kyau da sha'awa.
Ita kanta Amatulla ta yi kyau sosai dan ta shirya cikin doguwar riga ta material baƙi mai ratsin pink, cikin cikin kayan da Ammi ta bada Kuɗi ayi mata siyayya ita da Baby ne, ɗinkin ya mata kyau ya kuma fito da kyawun dirinta sosai, fuksarta Nasreen ta zuba mata idanu tana kallo, don Amatullah kyakkyawar gaske ce ko mace 'yar uwarta ta kalle ta sai ta sake kallonta ballantana namiji. Dan idan ba ta yi magana ba ka ji harshenta sai ka ɗauka wata ba'indiya ce daga ƙasar Indiya. Dan ma ba ta kwalliya ga kwayar idanunta mai matukar ɗaukar hankali da burgewa.
"Na ce baki iya gaisuwa ba ne?"
"Ina kwana?"
Kau da ta yi tare yin tsuki.
"Kin sanni?"
"A'a ban san ki ba."
"Ni ce Nasreen matar Ajmal, wanda kike ikirarin cewa shine uban ɗan ki, wanda kuma ba haka bane, kawai an yi amfani da ke ne dan a ɓata masa suna, ke kuma da ke matsiyaciya ce ke tunda za su biya ki shine kika yarda kika ɓatawa mijina suna ko? To yanzu ina son ki faɗa mani gaskiyar lamari idan ba haka ba wallahi rayuwar ki tana cikin hatsari."
Da sauri Amatullah ta kalle ta gabanta na faɗuwa.
"Ƙwarai kuwa rayuwarki na cikin hatsari domin ba abinda ba zan iya aikatawa akan mijina ba."
Nuna yaron ta yi tare da cewa
"Waye ubansa?"
"Wallahi ban sani ba?"
"Karda ki sake bamu wannan amsar rainin hankalin naki. Tun yaushe kika san mijina?"
"Ranar da na haihu na fara ganinsa."
"Ya aka yi aka ce shine ya maki ciki? Nawa aka biya ki na ninka maki abu da suka biya ki don ki je ki faɗi gaskiya ki wanke shi?"
Kuka ta saka tare da cewa
"Wallahi ba wanda ya bani kuɗi?"
"Kenan barazana suka maki?"
"Ba abinda wani ya ce nima haka kawai na ji Doctor ya faɗa ɗansa ne."
"Wato kin kafe akan zance guda kenan ko? Yadda suka siye likitoci haka suka siye ki ko?"
Cikin kuka ta ce,
"Me ye ribata dan na masa ƙazafi wallahi Ni ba halina ba ne ba tare ba tarbiyyar da iyayena suka bani ba ne.."
"Shut up wace tarbiya ce ga wacce ta yi cikin shege ta gudu ta bar iyayenta? Ai tarbiya ya yi gardama a wajen."
Goge hawayen da ke idanunta ta yi tare da cewa
"Duk abinda Allah ya ƙaddara wa bawa bai isa ya tsallake shi ba, na san cewa jarabawa ce daga Allah, kuma ni musulma ce na yarda da ƙaddara mai kyau da mara kyau mai daɗi ko mara daɗi, kuma ina addu'ar Allah ya bani ikon cinye jarabawa ta da..."
"Ba wannan nake so ji ba ki faɗa mani nawa zan baki ki fita daga rayuwarmu.?Miliyan goma ko ashirin talatin ko arba'in?"
Murmishin takaici Amatullah ta yi tare da cewa
"Ni dukiya bata gabana."
"Ƙarya kike 'yar matsiyata gara ma tun kafin..."
Turo ƙafar aka yi tare da sallama. Ammi ce sanye da baƙar jallabiya. Ganin Amatullah na kuka ga Nasreen a gabanta ya sa ta cewa.
"Me ke faruwa a nan?"
Nasreen ta ce,
"Ba komai Ammi."
"Akawai komai"
Ammi ta faɗa tana kallon Amatullah.
"Me ya faru kike kuka?"
"Ba komai."
Ta faɗa kanta a sunkuye, nan da nan kuma sai ga hawaye na zirya daga idanuwanta. Wanda hakan ya tabbatar wa Ammi cewa ita da Nasreen ce, dan haka ta ce,
"Nasreen me ya kawo ki nan?"
"Na zo ne dan na mata gargaɗi na ƙarshe..."
Cikin kakkausar murya Ammi ta fara mata magana.
"Nasreen mun riga mun wuce wannan wajen yanzu, saboda haka ba ruwanki da ita. Dan haka ba buƙatar ki sake zuwa nan ɓangaren da sunan wajenta kika zo."
Mamaki ne ya cika Nasreen dan haka ta ce,
"Ammi kina giyaon bayan wannan munafukar ne? Kenan kema kin yarda da ita?"
"Ba haka nake nufi ba, illa iyakar na ga tana buƙatar taimako ne ya sa na taimaka mata, zuwa nan da ɗan lokaci za ta tafi."
Cikin ɓacin rai Nasreen ta bar part ɗin kamar za ta tashi sama.
Da misalin ƙarfe goma na safe Dr Fu'ad ya shirya dan zuwa gidan Ajmal.
Sallama ya yi wa matarsa Zahrah, wacce ta zuba masa idanu ganin kwana biyu yanayinsa ya sauya, kuma kwana biyu baya fita. Kallonsa tayi tare da cewa
"Yau za ka leƙa asibitin kenan?"
Girgiza kai ya yi tare da cewa
"Ba aibiti zan tafi ba, zan je ne na sauke wani nauyi dake kaina."
"Nauyi fa ka ce."
"Eh nauyi ne mai girman gaske zan sauke, sai dai dan Allah ko da kin ji ki yi mani uzuri kuma ki mani adalci bani da wani zaɓi."
Jinjina kai kawai ta yi ba tare da cewa komai ba.
Fita yayi ya nufi motarsa, tare da yiwa motar key, mai gadi ya wangale masa gate ya fice.
Jamal ne ya fito daga part ɗinsa, sanye yake da T-shirt fara mai dogon hannu da baƙin wando, ƙafarsa sanye da takalmi baƙi kafa ciki.
Dama security ɗinsa suna zaman jiran fotowarsa, mitoci biyar suka shirya biyu na gaban nasa biyu na bayan nasa.
Bayan an buɗe masa ƙofar motar ne yana ƙoƙarin shiga ciki sai ga motar Dr Fu'ad ta danno kai.
Nan da nan ta fito tare da nufar inda Ajmal ke tsaye, wani kallo na tsana Ajmal ke binsa da shi.
Miƙa masa hannu ya yi tare da cewa
"Assalamu alaikum"
Bai miƙa masa hannu ba sai dai ya amsa sallamar da ya masa.
"Wa'alaika salam."
Murmishi Fu'ad ya yi tare da cewa
"Idan ba damuwa mu shiga daga ciki dan maganar da zan maka tana da mahimmanci sosai."
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
09065327995
🤦♀️ *YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
Ban yarda a karanta mani shi a youtube ko a maida shi audio ba tare da izinina ba.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Page4️⃣2️⃣&4️⃣3️⃣
Idan ba damuwa mu shiga daga dan maganar da zan maka tana da haimmanci sosai."
Wani irin kallo ya wurga masa kafin ya ce,
"Ba abinda za ka fada mani mai mahimmanci na saurare ka, sai dai idan ka zo ne ka wanke ni ka canza maganarka na cewa binciken da ka yi ya tabbatar maka da cewa jaririn ɗana ne ka janye ta hanyar canza kalamanka."
"Mu dai shiga ciki."
"Maganar ka zo canzawa ko ba ita ba?"
"Ba ita ba ce, amma akan maganar ne zamu tattauna yadda za ka fahimce ni."
Yanke fuska ya yi tare da cewa
"Ja motarka ka fita daga gidan nan, kuma ba na son ganinka."
Fu'ad girgiza kai ya yi tare da cewa
"Ka tsaya ka saurare ni."
"Ba zan saurare ka ba."
"Za ka tafka kuskure babba."
"Abota da kai shine babban kuskuren da tafka a rayuwata."
Daga nan ya shige mota tare da security ɗinsa suka bar gidan.
Bayan fitarsu ne Dr ya ja motarsa ya bar gidan.
Kai tsaye ya nufi jam'iyyar su dan amsa kiran shugaban jam'iyyar.
Security ɗinsa ne suka tsaya daga waje inda ya dakatar da su, ya yi n da ya shiga ciki shi kaɗai.
Gaba ɗaya kowa na zaune a kujerarsa sai babban teburin da ke tsakiyarsu. Gaba ɗaya fuskarsa babu walwala a tattare da su.
Mamaki yake akan wani dalili 'yan majalisar jaha suka yi masa irin wannan kiran.
Sallama ya masu tare gaishe da kowannnsu, kafin ya samu waje ya zauna.
Gaba ɗaya kallon 'yan majalisun yake yi kafin ya ji muryar wani na karanto masa bayanai kamar haka.
"Ajmal Ibrahim Tafida, ana zarginka da aikata fasiƙanci, wanda har ɗaya daga cikinsu ta haifa maka yaro, kuma mun ji daga majiya mai ƙarfi cewa ɗaya daga cikin matayen da suke zuwa neman taimako gidanka ne, wanda kuma mun ji cewa dama kana tara su da sunan basu tallafi ne da biyu, idan har ka ga wacce ta maka ne a ciki sai ka ha ra'ayinsu ka yaudare su ta hanyar lalata da su. Wanda su kuma saboda matsi da halin da suke ciki ya sa suke saurin amincewa da kai, saboda ka riga ka yaudare su ka siye zuciyarsu da kyautatawar da kake masu."
Idanunsa ne suka rikiɗe suka koma jajir da su, saboda ɓacin rai. Sai ya kuma ji ana tambayarsa.
"Shin yarinyar bata ɗaya daga cikin masu zuwa neman taimako ƙofar gidanka?"
Shiru ya yi dan bai san me zai ce da su ba.
Wani ne ya ce,
"Wallahi ganau nake ba jiyau ba, naji sanda wasu ke cewa sun ganta a ƙofar gidansa da tsohon ciki tana bin layin rabon kudin da yake bayarwa ayi."
Wani kuma ya ɗora da cewa
"Sannan dun rashin imani da tausayi ka yi wa yarinya ciki amma ka yi biris da ita ka kasa ɗaukar nauyin ta har sai ta cigaba da zuwa layin kyautar da kake bada wa."
"Dubunka ne ya cika Allah kaɗai ya san yawan 'yan matar da ta ke yiwa haka da sunan rabon kuɗi,ana ta zaginmu a gari cewa bamu kyuta ba mu bayar da sadaka kai ne mai kyuta da tausayi suna ta yabonka yayin da basu san ɓarnar da kake aikatawa wadanda kake taimakawa ba, kana fakewa da sunan bada taimako ta wani ɓangaren kake zagayewa ka fanshe kyautar da keke masu ta hanyar lalata da..."
Fusata ya yi tare da cewa
"Ya isa!"
Tsawan da da ya daka masu ne ya sa suka yi shiru.
"Kun zo kuma karanto mani wasu zantuttuka ba tare da kun tambaye ni haka ne ko ba haka ba, wata hujja kuke da shi na cewa na aikata hakan?"
"Hujja kowa ya gani tunda a bainan nasi aka faɗa, duk asibitin da kuka je an tabbatar kai ne uban yaron, ciki kuwa har da abokinka da kuka tashi tare wanda ba zai maka karya ba ba wanda ya san sau nawa ka aikata hakan yanzu ne dai dubunka ya cika."
Wani ɗaci ne ya ji a cikin zuciyarsa,tare da rintse idanu.
"Saboda haka mun dakatar da kai daga tsayawa ɗan takarar Gwamnan jihar nan, saboda ba ka cancanci zama shugaba kuma wakilin al'umma ba."
Wani takarda suka aje masa wanda ko kallon meye bai yi ba ya tashi ya fita ransa a matukar ɓace.
Bodyguards ɗinsa na ganinsa sun san akwai matsala, sai dai ba wanda ke da zarrar tamabayarsa halin da yake ciki.
Buɗe masa murfin motar akayi ya shiga ya zauna suka bar wajen. Ahmad da ke shi yana cikin motar da Ajmal ke ciki na yana gefen Direba ya ce,
"Yallaɓai lafiya kuwa?"
Bai ce masa komai ba hakan ya sa ya yi shiru bai sake masa wata tambayar ba.
Har suka isa gida Ajmal ko jiran a buɗe masa murfin motar bai yi ba, ya buɗe tare da fitowa da kansa. A babban falon gidan ya samu Amminsa da Nihal, Nihal ta kwantar da kanta a cinyar Mom, sai Nasreen dake kwance kan doguwar kujera ta kwanta tana danna wayarta da alama chart.
Da sallama ya shigo falon, kallo ɗaya suka masa suka san hankalinsa a tashe yake, da sauri suka yi kansa tare da tambayarsa abinda ke faruwa.
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya sanar da su komai.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un.,
Shine kalmar da suke faɗa. Cikin takaici ya ce,
"Ni ba wai dakatar da ni da suka yi ne damuwata ba, a'a zargin da ake Mani aka ɓata mani suna shi ne damuwata."
Daga nan ta nufi upstairs da sauri ya wuce. Ammi ce ta kalli Nasreen ta ce,
"Ki je ki kwantar masa da hankali."
Daga nan Nasreen ta bi bayansa, yayin da su Ku suka zauna a falon.
Da misalin ƙarfe biyar na yamma ne sun zaune a falon gaba ɗaya, har da Daddy da shivowrsa kenan, ya gan su shi ma ya zauna suna fira da Ammi da Nihal da Nasreen. Sai Affan da ya haye ƙafar Daddy.
Kallon Affan Daddy yayi tare da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 51