mata tsawa wanda hakan ya saka ta saurin buɗe baki cikin Muryar kuka ta fara magana.
"Amatullah ki duba girman Allah da Manzonsa ki yafe mani, na san cewa na cutar da rayuwarki, kin yarda da ni yayin da na ci amanar ki, sharrin shaiɗan ne da son zuciya, na saka kin faɗa harkar shaye-shaye sannan daga baya na sa an lalata rayuwarki saboda son zuciya, a halin yanzu na yi nadama na yi da na sanin abinda na maki dan Allah ki yafe mani dan Allah ba don halina ba. Wallahi na yi nadama tun tuni, ga shi alhakin ki ya dade yana bibiyata. Masu yaƙi da shaye-shaye sun Kama ni na sha wahala a hannun su sosai. Sannan kwana ɗaya da na yi a ofinshin 'yan sandan nan daga juya zuwa yau na sha wuya sosai dan Allah ki tafe Mani na bi Allah na bi ki Amatullah."
Ta ƙarasa maganar tana sakin sabon kuka. Amatullah ma kukan take yi kamar ranta zai fita,wanda hakan ya saka Ajmal karɓar wayar ya katse kiran wayar.
Nan ta kwantar da kai a kafar Anni tana cigaba da kuka, Anni n shafar kanta hadi da rarrashin ta.
DPO ya karbi wayar daga hannun Hafsat tare da cewa.
"Idan ita ta yafe maki kina tunanin kin tsira kenan? To ba ki tsira ba dan wanda kika saka ya aikata abun fa shi ma yana da hakki akai. Dan ko kin nemi yafiyar ta ba zai saka kunsallams ki ba har sai dai idan shi ne da kansa ya bamu izinin mu sake ki, ki yi addu'a idan ta yafe maki Allah ya sa shi ma ya yafe maki."
Goge hawayen fuskarta ta yi tare da cewa.
"Idan ta yafe mani ai ba wata matsala saboda ita na cuta ba shi ba, dan shi kam namiji ne ba abinda ya ragu a tare da shi, sai ma dai taimakon da da na yi ya samu nutsuwa a..."
Kallon da DPO ya mata ne sa ta yi shiru ba tare da ta ƙarasa maganar da take son yi ba,daga nan ya saka aka maida sel aka rufe, kuka ta ke yi sosai dan a cikin sell ɗin ana kawo wasu tantirai jiya daddare wanda suka dinga dukanta tare da hana ta yin kuka dan kar wani ya jiyo kukan nata.
Ɓangaren iyayen Amatullah kuwa har yanzu har jikin Ummanta, yau lafiya gobe ciwo, yau lafiya gobe ciwo haka suke fama. Abba kuwa ganin halin da matarsa yake ciki duk ya dame shi, hakan ya saka shi yake nadamar korar Amatullah daga gidan, dan ya san da bai Kore ta ba ai da yanzu lafiyar matarsa ba ta illata ba. Ga shi duk inda yake saka ran cewa ta tafi ba inda ta tafi, korar Amatullah daga gidan da ya yi yana ganin shi ne kuskure mafi girma da ya tafka a rayuwarsa.
Zaune suke a akan ta tabarma a tsakar gidan, yayin da Abba ke shan koko da ƙosai, ita dai Umma ta tasa ƙosai da koko a gabanta sai tunanin Amatullah take yi, ta kasa kai komai a baki.
Duk wanda ya san Umma lokacin da Amatullah ke tare da ita idan ya kalle ta yanzu ba zai yi tunanin ba ita ba ce.
Kallonta Abba ya yi tare da cewa
"Umman Amatullah dan Allah ki daure ki ci abinci ko kadan ne, dan Allah rashin cin abinci ma karin wani ciwon ne ai."
"Mallam ba za ka gane halin da nake ciki ne, Ni nadan ciwon da zuciyata ke yi ba ne, ta ya ya ya zan iya cin abinci cikin kwanciyar hankali alhalin ban san halin da yarinyata take ciki ba, ta ci ko ba ta ci ba, tana raye ko ba ta raye, tana hannu mau kyau ko mugun hannu ta faɗa?"
Sallama suka jiyo daga ƙofar gidan, daga jin Muryar sun shaida waye ke sallamar.
Amsawa suka yi tare da ba shi izinin shigowa, nan ya shigo cikin gidan.
Umma ce ta kalle shi tare da cewa.
"Mummir kai ne ke tafe."
Fuskarsa ɗauke da murmushi ya ƙarasa tare da durƙusawa ta gaishe su , suka amsa masa cikin farin ciki da walwala.
Tabarma da ke gefensu ya bude ya shimfida ya zauna , Umma ta yi masa tayin koko ya ce ba zai sha ba ya gode, dama kwana biyu bai zo ba ne ya sa shi zuwa ya dan ya duba lafiyarsu.
Fira suke ɗan taɓawa zuwa can ya ɗaya kai ya kalli Abba ya ce.
"Abba ko an ji labarin ta a wani waje?"
Girgiza kai ya yi tare da kallon Munnir sannan ya ce
"Har yanzu ba wanda ya ce ya ganta ko ya ji labarin ta. kullun dai muna ta addu'a Allah ya bayyanar mana da ita, ya juyo da hankalinta ta dawo gidan."
Nisawa ya yi tare da cewa.
"Mummir har yanzu kana nan akan bakanka na auren Amatullah?"
"Abba in sha Allah ba gudu ba ja da baya."
"Amma kar ka dawo daga baya ka janye, na faɗa maka cewa Amatullah tana shaye-shaye, sannan kuma na faɗa maka cikin shege ta ta yi na Kore ta daga gidan nan ka da ka ɗauke an Munafurce ka za ka iya aurenta a haka?"
Murmushi ya yi tare da cewa.
"Zan iya Abba na sani ai, canza Amatullah ba abu ba ne mai wahala,dan da alama ta samu tarbiyya daga gida,shawarar mugayen kawaye ne ya kai ta wannan halin, dan haka canza ta ba zai zama wani abu mai wahala ba, ballantana ma ina tunanin korar nan da aka mata ma kaɗai ya isa ya saka ta gane abinda ta aikata kuskure ne kuma ta yi nadama."
Jinjina kai Abba ya yi tare da cewa.
"Lallai ka cikaasiyin ƙwarai na hakika, tabbas son gaksiya kake yi wa Amatullah tunda har ba k guje ta ba, dan haka duk ranar da Amatullah ta dawo ba ta da wani miji sai kai in sha Allah, na maka alƙawarin baka auren Hafsat."
Murmushi ya yi cikin jin daɗi ya yi wa Abba godiya, wayarsa ce ta yi ringing ya ciro daga cikin aljihunsa ya duba, baƙuwar lamaba ce ke kiransa.
Ɗagawa ya yi tare da kara wayar a kunnensa.
A can kuwa Hafsat ce ta sri wayar ɗaya daga cikin 'yan sanadar tana tsaye bakin sel ɗin, sai wani ɗansanda yana tsaye yana azalzalarta ta yi sauri ta bashi wayarsa.
Jin Munnir ya ɗaga wayar ne ya saka shi ta ce.
"Hello Ya Munnir dan Allah ka zo ina ofishin 'yansanda sun kama ni."
"Tsuki ya yi tare da cewa.
"Wannan kuma matsalarki ce, tunda kin ce ke ba za ki ladabtu a rayuwa ba kaɗan kika gani."
"Haba Ya Munnir duk matsalolin da nake ta shiga ka ce kadan na gani, dan Allah ka zo."
"Ba inda zan zo Berlin ki."
"Ba za ka zo ba?"
"Eh ba zan zo ba ki yi ta zama a hannunsu."
Murmushi ta yi tare da cewa.
"Idan har kana son na sanar da kai inda Amatullah take to ka zo ka same ni, idan kuka ba ka son sanin labarin inda Amatullah masoyiyarka take ka zo,idan kuma ba ka so to ka yi ta zama a can."
Daga nan ta katse kiran wayar tare da tabbacin cewa sai ya zo ba saboda kowa ba sai saboda Amatullah.
Tana katse kiran wayar Munnir ya kalli Abban Amatullah ya ce.
"Baba bari na je ana jira na."
"Na ji kana maganar beli ina fatan ba wata matsala ba ce?"
"Ba wata matsala Abba, ƙanwata ce take hannun jami'an tsaro zan je na same ta."
Addu'a suka masa ya tafi yana masu sallama ya tafi.
Kai tsaye police station ya nufa kamar ya yi tashi sama yake ji ya matsu ya ji labarin inda Amatullah take dan ya je ya same ta.
Yana zuwa police station ɗin sai ya yi Sa'a ya inda ya haɗu da inspector dake wajen abokinsa ne, nan shi gaisa ne yaushe rabo. Inspector Kabir Umar abokin Munnir ne tare suka yi karatu.
Munnir ne ya sanar da shi dalilin zuwansa yana son ne a bashi belin Hafsat, nan inspector yake sanar da shi cewa ba zai taɓa yiwuwa ba saboda DPO ya bada Umarnin ka da wanda ya bada belin Hafsat.
Jinjina kai ta yi tare da cewa.
"To ina son zan yi magana da ita ko za ka taimaka mani?"
"Ba damuwa ga wuri can ka je ka zauna bari na sa a fito maka da ita."
Ya yi maganar yana nunawa Munnir wani hanci dake can gefe.
Sannan ya bada umurnin a fito da Hafsat.
Bayan an fito da ita ne ta je ta zauna a gefensa.
Ba wanda ya yi wa wani magana a cikinsu, zuwa can ta ce.
"Ya Munnir saboda Amatullah ka zo nan ko?"
"Ki faɗa mani inda take."
Ya yi maganar yana tsuke fuska, marmushi ta yi tare da cewa.
"Kafin sanin inda take ya kamata ka san komai da ya faru da ita."
Nan ta kwashe komai tun ranar da ya ragewa Hafsat hanya daga islamiyya ta dauko Hafsat a buge ta maganganun da suka yi da yadda ta lura yana son Amaty ita kuma ya juya mata baya saboda shaye-shaye ya sa ta koyawa Amatullah shaye-shaye, da gorin budurci da ya mata ta saka wani ma'aikacin hotel ya san yadda ya yi wani ya yi mata fyaɗe bayan ta kira ta hotel ta bada hotonta aka mata fyaɗe.
Tana kawowa wajen fyaɗen Munnir bai jira abinda za ta sake cewa ba ya shaƙe wuyarta sannan ya dinga gaura mata mari ta kowane gefe na fuskarta.
Kakari take yi irin wacce ke gaɓar mutuwa ta fito da Idanunta waje, miyau na dalala daga bakinta.
Hankalin inspector Kabir ne ya zo wajan a guje ya ƙarasa domin ceto rayuwar Hafsat, shi ne ya ƙwace ta daga hannun Munnir.
"Da ka barni na kashe ta
"Idan ka kashe ta ai ba ƙyale ka hukuma za ta yi ba."
"Yarinyar nan ita ce saboda kishin banza ta saka aka lalata rayuwar yarinyar da ba ruwanta, bayan ta koya mata shaye-shaye, wai saboda ina son yarinyar ne ta yi haka, anya mace ce ke kuwa?"
Ya yi maganar yana kallon Hafsat dake riƙe da wuya tana maida numfashi.
Na sani amma ai bai kamata ka ɗauki doka a hannunka ba, ka zuba ido ka gani mana.
Wani matsiyacin kallo mata tare da cewa.
"Kin ce kin san inda take to ki sanar da ni yanzun nan."
"Sai ka yi mani alkawarin fita daga wajen nan."
Ta yi maganar daƙyar saboda maganar ke fita daga bakinta. Har lokacin tana riƙe da wuyanta.
Kallon banza ya mata yana da niyyar bude baki ya yi magana, sai ya ji muryar inspector Kabir yana cewa.
"Inda yarinyar take kake nema?"
"Eh ka sani ne?"
"Me ye dangantaka da ita?"
"Ada ita wannan Hafsat nake so, sai na lura da ba ta da tarbiyya kuma tana da wasu halayyar da na tsana, kuma ciki har da shaye-shaye, sai na rabu da ita,na koma ina son Amatullah, kasancewar ta yarinya mai nutsuwa tarbiyya da kamun kai. Shi ne Hafsat ta shiga rayuwarta har ta yi nasarar saka ta cikn harkar shaye-shaye,daga karshe ta yi sanadiyar da aka lalata rayuwarta har ta samu ciki a lokacin, daga ƙarshe iyayenta suka kore ta daga gida."
Jinjina kai Inspector ya yi tare da cewa.
"Gaskiya ba ki kyauta ba kin cutar da rayuwar baiwar Allah saboda kawai saurayinki na son ta, me ye laifinta a ciki, Allah ya kyauta."
Munnir ne ya kalli Inspector tare da cewa.
"Ka ji labarin inda take?"
"Na ji an ce tana jahar Kaduna."
"Zan iya samun adireshin gidan da take?'
"Gaskiya ba zan sani ba, sai dai idan ka je Kaduna samun adireshin ba abu mai wahala ba ne, kasancewar nace shi wanda ya mata cikin a gidansa take zaune, mahaifin kuma sanannen mutum ne a garin, ko shi wanda ya mata cikin ba ɓoyayyen mutum ba ne ya yi suna a jihar kowa ya san shi, dan har ta fito Neman takarar Gwamnan jihar saboda bayyanar cikin ita yarinyar bayan an tabbatar da cikin nasa ne aka soke takardar sa tatsayawa takara, a yanzu bayan gaskiya ta yi halinta kowa ya gane ba laifinsa ba ne aka nemi ya cigaba da takararsa shi kuma ya ce ya janye ba zai cigaba da siyasa ba. Ba na da adireshin gidan, sai dai ina da yaƙinin cewa idan ka je garin ka tambayi gidan Alhaji Ibrahim Tafida kowa ya san shi, ko cewa ka yi a nuna maka gidan Ajmal Ibrahim Tafida an ce kowa ya sani yaro da babba saboda halinsa na taimako da jin ƙan talakawa."
Shiru Munnir ya yi ko da ya ji an ambaci Ajmal Ibrahim Tafida ya san akwai inda ya taɓa jin sunan kuma yana jin labarinsa a jarida ne ko a social media, amma tabbas ya san sunan."
Godiya ya yi wa inspector sannan ya fita ya nufi wajen motarsa, inda aka mai da Hafsat a sel.
Munnir na shiga mota ya kira abokinsa Sadik ya ce ya shirya gobe zai raka shi Kaduna.
Daga nan ya ja motarsa ya tafi.
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
09065327995
Love you masu like da comments🥰🥰🥰
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
🤦♀️ *'YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
Ban yarda a karanta mani shi a youtube ko a maida shi audio ba tare da izinina ba.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Page6️⃣6️⃣
Daga nan ya ja motarsa ya tafi, zuciyarsa fara ƙal yana tunanin zai ga Amatullah ɗinsa
Ɓangaren Amatullah kuwa tunda ta ji Ammi ta yi maganar mai da ita gidan iyayenta ta fara farin ciki tare da addu'a Allah ya sa Abbanta ya sauko zai karɓe ta a matsayin 'yarsa, kuma ya karɓi Abdallah a matsayin jika a wurin su, kamar yadda Dad da Ammi suka karɓe shi a matsayin jika a wajensu.
Tana zaune a falo ita kaɗai tana buga game da wayarta, fuksarta ɗauke da fara'a tana murmushi. Shigowarsa kenan ya ga tana Murmushi ya lura tun lokacin da Ammi ta yi maganar mai da ta gida gaban iyayenta take cikin farin ciki.
A hankali ya ƙaraso wajenta hannayensa duka biyu a cikin aljihun wandonsa, Idanu ya zuba mata yana kallonta ko ƙyafta Idanu ba ya yi.
Ji ta yi kamar ana Kallonta dan haka ta daga kai ta kalle shi suka haɗa Idanu.
Sunkuyar da kanta ƙasa ta yi ganin irin kallon da yake mata, can kuma sai ta sake ɗago kai ta kalle shi nan ma suka sake haɗa Idanu, tura baki ta yi tare da sunkuyar da kai ta rasa wani irin kallo yake mata ga shi ita ba ta iya haɗa Idanu da shi. Zuwa can sai ta ji muryarsa yana cewa.
"Na lura kina cikin farin ciki ko?"
Murmushi ta yi tare da cewa.
"Eh ina cikin farin ciki, na matsu ba ga kaina a gida, ban ƙi yau mu tafi ba dan ji nake kamar na yi tsutsuwa na ga kai na a gida, ina son komawa wajen Ammina cikin gaggawa."
Kallonta ya yi tare da cewa
"Jinkiri yakan zamo alkhairi, gaggawa ya zamo akasin haka.
Ki tuna cewa ALLAH (SWT) shi ke juya al'amurra, ya tabbatar dasu lokaci mafi dacewa. Kada kiyi shakka idan kika ga jinkiri, da sannu rahama zata riske ki."
Yana gama faɗar haka ya juya ya haura upstairs, bin bayansa ta yi da kallo duk ta ga jikinsa ya yi sanyi, ba ta daina kallonsa ba sai da ya b'acewa ganinta, taɓe baki ta yi tare da maida hankali kan wayarta ta cigaba da danna wayarta.
Tunawa ta yi ranar da aka yi sunan Abdallah kasancewar ba ta da kowa a gari, sai ita kadai saboda rage zaman ƙaɗaici ya sa Ammi ta kira Nurses da suka kula da ita a asibiti Saliha da Madina suka taya ta zama suka ɗebe mata kewa. Dama ranar sun rubuta mata lambar wayarsu hakan ya sa da sauri ta nufi ɗakinta ta lalubo lambar a jakarta.
Sai ga shi ko ta ga lambar da sunan kowacce,nan ta saka a wayarta ta yi seved da sunan kowace.
Saliha ta fara kira a waya, bugu ɗaya ta daga tare da sallama. Amatullah ta amsa mata sallamar, sai ta ji Saliha na tambayar me magana, sai da ta yi murmishi tare da cewa.
"Patient ɗin ki ce Amatullah"
Saliha da ke riƙe da waya ne a ya yin da take bin Doctor duba patient, jin Amatullah ce ta daka wani tsalle da ihu tana jin daɗi. Kallonta Doctor ya yi tare da cewa.
"Kin mance a asibiti kike ne?"
"Sorry sir."
Daga nan ta rage murya ta cewa Amatullah.
"Ranar mun zo ni da Madina gidanku dan mu sake ganin baby security suka hana mu shiga, wallahi ƙurar mu suka yi. Amma yanzu wayar waye hannuki."
"Wayata ce."
"Okay to idan mun tashi zamu zo ni da Madina tunda kina da waya sai mu kira ki sai ki shiga da mu ko da security sun hana mu shiga."
"Okay ba damuwa na ji dadi kuwa jin za ku zo, bari na kira Madina na sanar da ita ga lambata."
Sallama suka yi sannan ta kira Madina ta sanar da ita cewa ga lambar ta , ita ma ta ji dadin jin muryarta.
Ɓangaren Maman Hafsat kuwa jin shiru ba dan Hafsat ba ta kwana gida ba wani abu bane a wajen ta,dan ta saba da hakan, abinda daga hankalinta shi ne ganin wayar a gida, ta dan ba lafiya ba ne fitar.
Maigadi ta fita take tamabayarsa ya sanar da ita police ne suka tafi da ita, hakan ya sa hankalinta ya tashi ta lalubo lambar wayar Munnir ta danna masa kira.
Yana tsaka da driving ya ji wayarsa tana ruri, duba ba ballantana ya san ko waye mai kira, har sai da ta katse sannan ya san waye mai kiran wayar.
Sai da aka sake kira har sau uku sannan ya ɗaga wayar tare da cewa.
"Assalamu alaikum.
Ta amsa da wa'alaikumus salam sannan take sanar da shi cewa tana buƙatar ganinsa, na ya juya akalar motar ya nufi gidan su Hafsat.
Bayan ya yi parking ne a waje sannan ya yi knocking maigadin gidan ya bude masa ya shiga .
Da sallama ya shiga cikin falon, inda ya tarar da Mama zaune a falo ta haɗa ragumi, amsa masa sallamaf ta yi ya shiga ya durƙusa cikin girmamawa ya gaishe ta , cikin damuwa ta ce
"Munnir ko ka san inda Hafsat take?"
Shiru ya yi yana nazari, dan ua rasa me ze ce mata, dan gaskiya ya san idan ya sanar da ita gaskiya inda Hafsat take hankalinta zai yi matukar tashi. Ga shi tana da bawan jini ciwon ta zai iya tashi, kuma ko ta je police station ba zasu ba ta belin Hafsat ba, sai dai zai yi iya kokari da zai iya ganin ya kwantar mata da hankali. Yana cikin tunanin ne sai ta ji muryar Mama tana cewa.
"Munnir ka yi shiru ina tambayar ka."
Murmushi ya ƙaƙalo cikin son kwantar mata da hankali saboda uwa ce a wajensa, ko ba komai ƙanwar mahaifiyarsa ce yana mata kallon uwa ce a wajensa tunda ciki ɗaya suka fito da mahaifiyarsa, gyaran murya ya yi tare da cewa.
"Mama ba ki san ta tafi biki ba ne? Za ta kwana biyu ƙafin ta dawo gidan nan, na san da bikin amma..."
Dakatar dashi ta yi ta hanayar daga masa hannu.
"Munnir ka da ka mani ƙarya maigadi ya sanar da ni cewa police ne suka tafi da ita, duk da na san cewa Hafsat ba ta jin Magama tana fita ta kwana ba tare da sani na ba amma dai ba za ta tafi ta bar wayarta ba."
Shiru ya yi tare da takaicin wannan abu, wai uwa ce za ta bari 'yarta ta fita waje ta kwana ba tare da ta san inda take kwana ba kuma ta zuba mata idanu.
"Mama kema kan ki kina da laifi dan duk abinda Hafsat ke yi ba ki tsawatar mata,komai ta yi daidai ne a wajen ki..."
"Munnir ba tambayar da na maka kenan ba,kuma ba shi na kira ka dan na ji ba, kawai idan ka san inda take ka sanar da ni."
"Biki na san za ta je kuma ta faɗa mani, maybe dan ba ki gida ne ya sa ba ki sani ba."
Shiru ta yi tana nazari dan ba abun mamaki ba ne idan ta je biki ta kwana, amma an ce police ne suka tafi da ita. Ta mai da Kallonta ga Munnir ta ce.
"Police ne tabbas da ta ɗauki wayarta."
"Eh police sun ɗauke ta Mama, amma tambayeta suka yi akan wata ƙawarsu da ta ɓata,bayan sun nemi jin ta bakinta suka sallame ta. Amma ka da ki damu na san zuwa gobe za ta dawo, idan ba ta dawo ba zan bi bayanta, dan da alama bikin ba garin nan ba ne zan bincika na sanar da ke."
Haka ya cigaba da kwantar mata da hankali kafin ta mata sallama ya bar gidan.
Bayan ya isa gida ya samu Dad da Mom ɗin sa a falo, sallama ya yi tare da tura ƙofar .
Gaba daya suka amsa masa sallamar inda ya zaune ƙasan carpet tare da miƙa ƙafa ya kwanta da bayansa da jikin kujera.
"Dad Mom sannunku da zama."
Ya yi magana yana kallon Mom da tunda aka ce ya fasa auren Hafsat ta canza masa, gani take kamar shi ya zuga Dad ɗin aka janye zancan auren, tunda ya fara nuna ba ya son auren a baya can.
Dad ne ya sakar masa murmushi tare da cewa.
"Ka gaji ko?"
"Eh Wallahi Dad na gaji, ga kuma tafiya gobe a gabana."
"Tafiya kuma zuwa ina?"
"Dad zan raka abokina Sadik Kaduna ne."
"Lafiya me za ku je yi."
"Ɗaurin aure ne Dad wani ɗan uwansa ne ke aure."
"Okay Allah ya kai ku lafiya ya sanya alkhairi ."
"Ameen Dad."
Ya faɗa yana Murmushi idanunsa akan Mom ya ce.
"Mom ba ki ce komai ba."
"Allah ya kai ku lafiya."
Ameen ya amsa dan ya lura tana fushi ne amma da Dad ne fushin ya fi yawa, kasancewar shi ta hana zancen auren da Hafsat.
Tashi ya yi nufi ɗakunan kai tsaye zuciyarsa cike da farin ciki. Har ya tura ƙoafar zai shiga ya ji muryar Mom na kiransa, dawowa ya yi ta zauna yana jira me za ta ce.
"Munnir me kake shiryawa?"
Kallonta ya yi cikin rashin gane inda zancen ta ya dosa, dan haka ya ce.
"Ban gane ba Mom"
"Akwai abinda kake shiryawa a ɓoye, mene ne shi?"
"Mom me zan shirya kuma?"
Kallinsa ta yi tare da cewa
"Wannan kuma kai ka sani, amma tabbas akwai abinda kake shiryawa da ka ɓoye, Ni fa na haife ka na san ka ciki da waje, sai dai na fadawa wani halinka ba dai a faɗa mani ba."
"Mom me kika gani ya sa kika mani wannan tambaya?"
"Wannan farin ciki da kake yi na mene ne, me kake shiryawa, ba banza ba akwai dalili, kawai dan za ga tafi Kaduna kake farin ciki haka da zumuɗi?"
"Ai ko Saudiya da wata ƙasar da za ka tafi ba ka yi wannan zumuɗin da farin ciki da nake hangowa a cikin idanunka ba. Ballantana wani gari dan za ka je Kaduna, da walakin goro a miya."
"Mom ba wani abu kawai dai haka yanayin ya zo Mani."
Za ta yi wata magana kenan Dad ya ce
"Tashi ka tafi abinka."
Bayan ta tafi ne ya kalli Mom ya ce.
"Kuna ta masa ta tambayoyi ya ce ba komai ba sai ki ƙyale shi ba, na san ba zai aikata wani abun da ba daidai ba."
Shiru ta yi tare da tashi ta nufi ɗakinta.
Ƙawayen Amatullah Saliha da Madina kuwa kamar yadda suka ce hakan suka yi. Da misalin ƙarfe biyu na rana mai adaidaita sahu ya ya ajiye su a ƙofar gidan Alhaji Ibrahim Tafida.
Sun zo zasu shiga sai suka ga securitys suna ƙofar gidan. Gaishe su suka yi suka amsa inda suka ce wajen Amatullah suka zo.
Security ya kalle su da da kyau duk da sun saka after dress a saman kayansu na Nurses hakan ya sa sun gane ma'aikatan lafiya ne, sai dai duk da haka ba su basu izinin shiga ba, dan ba su da shaidar da za su nuna a basu izinin shiga. Ƙarshe ma korarsu suka yi.
Gefe suka koma suka kira Amatullah a waya dan su shaida mata zuwansu.
Suna zaune a dinning table suka cin abincin Ammi da Amatullah sai Nihal, su uku ne, dan Nasreen ba ta gidan Affan na school Ajmal kuma baya gidan.
Wayarta ce ta yi ringing inda
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 26 Chapter of 51