Share this page
Ahmad ke shaida masa cewa an ce Samuel ne ya fita daga gidan. Ya tambayar ko tare da waye suka fita ba Wanda ya gani kasancewar motar mai bak'in gilashi ne. Gaba d'aya sai ya ji hankalinsa ya kasa keanciy, dan haka sai ya nufi d'akinsa. Nasreen dama ko da Ajmal ya ce ta je ta yi breakfast d'akinta ta nufa, wayar ta ta d'auka ta kira lambar wayar Fareeda. Bayan Fareeda ta d'auka ne ta ce. "Hello k'awata." Daga can bangaren Fareeda ta masa da . "Ma'am ya kike?" "Ina lafiya." "Fatan kin yi amfanin da shawara ta?" "Nayi kuwa har na k'ara da tawa basirar." Murmushi mai sauti Fareeda ta yi tare da cewa "Dakyau, wata basirar kika k'ara da ita?" Nan Nasreen ta bata labarin abunda ta yi tun da shigarta dakin Ajmal har tura message da ta yi da Kiran Samuel duk ta bata labarin komai. Dafe goshi Fareeda ta yi tare da cewa. "Wai ke me yasa ba Kya tunani kafin ki aiwatar da abu ne? Ta ya ya za ki aikata wannan d'anyen aikin? To wallahi tun wuri ki dakatar da shi ki janye kudirin ki akan abunda kike kokarin aikata wa, Dan na san CCTV camera ta d'auki komai idan wani abu ya faru mijinki zai binciko komai." Daga nan ta katse Kiran wayar, sai a lokacin Nasreen ta yi tunanin maganar kawarta gaskiya ne. Dan haka da sauri ta kira lambar wayar Samuel. Daidai lokacin da Samuel ya yi parking a gefen hanya, Dan zuwa lokacin Amatullah har ta fara kuka, Dan tun da ta ga ga sunbar cikin gari tana ta masa magana cewa ina zai kai ta ya yi kamar ba ya Jin ta sai ta fara kuka ganin irin gudun da yake yi, ta d'auki waya da niyyar Kiran Ajmal ya fisge wayar. Daga nan ta fara kuka ta sadakar yau sai yadda Allah ya yi da ita. Suna zaune a cikin motar ne ta ji wayarsa na ruri, da sauri ya d'aga wayar, bai yi magana ba zuwa can ta ji ya ce. "Okay." Daga nan ta ga ya mik'o mata wayar ta. Ya juya akalar motar ya koma hanyar da suka baro. CCTV camera Ajmal ya duba yana kallonta tun fitowarta har zuwa lokacin da Samuel ya k'araso ya bude mata mota har fitarsu. Wayarsa ya lalubo, ya dannawa Samuel kira, bugu d'aya ya d'aga sannan ya yi parking. "Tambayarsa ya yi inda ya kai Amatullah ya sanar da shi cewa yanzu zai kai ta saloon, dama ya tsaya ne kai wani sako da Nasreen ta aike shi Hakan ya saka ba su isa saloon ba. Katse Kiran wayar ya yi ganin Kiran Amatullah na shigowa wayarsa Bayan ya d'aga kira wayar kafin ya yi magana ne ya ji muryarta ta ce . "Yaya." Jin muryarta kamar t yi kuka ne ya saka hankalinsa ya tashi, da sauri ya ce. "Me ya same ki ne ina ta kira baki dagawa?" Kallon Samuel ta yi cikin tsoronsa ta kasa cewa ya amshe mata waya, Dan haka sai ta ce. "Zan maka message." Daga nan ta katse Kiran wayar ta fara tura masa message kamar haka. _Yaya ban yarda da shi ba please ka zo ko ka turo Ahmad ya kai ni_ Tana turawa ba jimawa sai ga reply ya mata da cewa. _Okay ina zuwa_ Wayar Samuel ce ta yi ringing inda Ajmal ya bashi umarnin ya tsaya inda yake. Nan Samuel ke sanar da shi cewa sun k'araso saloon d'in ya bashi address na wajen sai Ajmal ya bashi umarinin ya wuce ya barta gashin nan zai zo da kansa. Bayan ta shiga shagon Samuel ya bar wajen. Amatullah ta shiga ciki ta gaida wadanda ta samu ciki ta zauna tana jira. Wayarta ce ta yi ruri ta duba ta ga Ajmal ne ke kiran wayar. Bayan ta d'auka ne ta saka masa kuka. Cikin tashin hankali ya fara tambayar ta yana cewa. "Meke faruwa ne kina ina kika ke da waye?" Cikin kuka ta fara magana tana cewa. "Ina wajen saloon d'in da ya sanar da kai." "Ki shiga ciki ina zuwa yanzu." Bai jira cewarta ba ya katse Kiran wayar tare da fitowa falon. Ammi da ke zaune a falo ganin yanayainsa ya sa ta mike tsaye tare da cewa. "Lafiya kuwa?" Bai tsaya ba yana tafiya yana cewa. "Ba komai Ammi ina zuwa yanzu." Yana fita bodyguards d'insa suka taso zuwa inda yake, da hannu ya dakatar da su ya nufi d'aya daga cikin mitocin da ke gidan. Shiga ya yi ya yiwa motar key horn yake dannawa ba kakkautawa, nan da nan aka wangale masa gate ya nufi unguwar da Amatullah take, kasancewar ya san wajen saloon d'in nan matarsa Nasreen ke zuwa. Munnir yana zaune a mota wajen mai zaman banza yayin da Sadik ke driving. Kallonsa Sadik ya yi sannan ya kau da kansa tare da cewa. "Amma abokina yanayin yadda ka yi wa iyayen Amatullah magana fa ka san ba zai masu dad'i ba, bisa la'akari da cewa suna tunanin ta tuba ta yi nadama zuwanka ya saka masu shakku akan ta.." Ajiyar zuciya Munnir ya sauke tare da cewa. "Ai nima daga baya na yi tunanin haka, wallahi rai na ne ya baci da abunda gayen nan ya yi mani, sannan itama ai bai kamata ta zauna gidansa ba bayan ya lalata mata rayuwa zaman me take yi a gidansa, karatu yake koya mata?" "Koma mene ne dai ka kyautata masu zato, sannan idan Allah ya kai mu gobe muka tafi zamu ji komai idan ya so daga baya zaka yanke mata hukunci." Jinjina kai Munnir ya yi sannan ya Kalli Sadik ya ce. "Haka ne, wannan ba halina bane amma in Sha Allah Hakan ba zata sake faruwa kawai kishi ne ya sa na Fadi haka. Suna tsaka da tafiya kamar an ce ta wai ga ya Kalli gefensa, sai ya hango Hafsat tsaye akan titi, da kayan da yake jikinta lokacin da take hannun yansanda. "Tsaya! Tsaya! Tsaya!" Munnir ya fad'a Wanda hakan ya sa Sadik sauka gefen titi ya tsaida motar, kallonsa ya yi kafin ya yi magana har Munnir ya bude murfin motar ya fita, kallonta yake da mamaki a fusakarsa yayin ita ma shi take Kallo tana murmushi Wanda ita kadai ta San ma'anarsa. K'arasa wa y yi tare da cewa "Gudowa kika yi daga offishin yansanda ko?" Wani dariya ta k'yalk'yace da ita tare cewa . "Guduwa, ai ni ba mai guduwa ba ce kai ma ka San ba zan taba guduwa ba." "K'arya kike yi ba yadda za'ayi a sake ki, dan badinki a cikin al'umma ba karamar hatsari ba ne." Ya yi maganar yana rike hannunta. Kasancewar ta san ba guduwa ta yi ba Hakan ya sa bata damu ba, wayarsa ya lalubo ya nemo lambar wayar inspector ya danna masa kira. Bayan inspector ya d'auki waya ne Munnir ke tambayarsa akan Hafsat, nan ya shaida masa cewa eh Ajmal ne ya bada umarnin a sake ta. Murmushin takaici ya yi tare da sakin hannunta, nan Kuma Hafsat ta saki murmushi tare da cewa. "Da alamar ba ka yi farin cikin fitowa ta ba, gudun na zame maka matsala nan gaba ko? To ka da ka damu indai matsala kullun a cikinta kake, ba za ka taba fita daga matsala ba har sai ranar da ka aure ni." "Wannan karon idan har kika yi yunkurin shiga sabga ta to wallahi zan manta cewa 'yar uwata ce ke, zan maki abunda baki taba tunani ba." Yana gama fadar haka ya shiga cikin motar Sadik ma ya shiga suka bar wajen, bin motar ta yi da harara. Ajmal na parking a wajen gaban saloon d'in ya fito daga cikin motar, daidai lokacin da za'a fara wa Amatullah. Wayarta ce ta yi ruri ba ta daga ba kasancewar ita ake yi wa, d'aya daga cikin matan da ke wajen ne ta rike mata Abdallah. Jin wayar ta katse ne ya sa ya karasa Jikin shagon Saloon d'in, k'ofar gilashi ne daga ciki ana ganin mutumin da ke wajen. Wasu 'yan mata da ke ciki ne suka hangi Ajmal ta waje d'aya ta ce. "Wannan ba Ajmal Ibrahim Tafida ba ne?" Gaban Amatullah ya Fadi Jin an ambaci sunan Ajmal, lokacin wayarta na cikin jaka Kuma wayar a silent take, so ba ta ma San yana kira ba. Dayar budurwar ce tace. "Shi ne mana ke baki gane shi ba ne, ai ni gayen ya yi mani ne wallahi, ya hadu ba k'arya." Wata ta ce, "Wai na ji an ce ya janye takarar da yake yi ko?" "Eh ya janye tunda an ce an gano gaskiya ba ya da laifi akan abunda ya faru aka bukaci ya dawo bayan an dakatar da shi." Wacce aka gamawa kitso yanzu ne ta tashi ta kalle shi ta cikin gilashin tare da cewa. "Ko ba laifinsa ba ne dai ya aikata yana da d'an shege lallai haka abun yake ba wanda zai karyata ta, kuka fa an ce yarknyar da babyn suna zaune fa a gidansa sannan a ce ba laifinsa ba ne?" Wacce ke rike da Abdallah ne ta ce. "Amma Kuma bani mamaki wallahi, to ina ruwanku ne , mutane nawa suke aikata abunda ya fi na shi ba Wanda ya yi magana saboda baku San su ba, saboda yana babban mutum dan takarar da ya yi suna yasa kike ta wannan maganar, Kuma ko Ku yarda ko kar Ku yarda an ce mutumin kirki ne kaddara tana kan kowa abunda mahifina ya fad'a kenan." Kasancewar saloon d'in matan manya da yaran manyan mutane ke zuwa, nan wata ta ce to mahifina naki ai kowa ya sani barawon gwamnati ne har aka kore shi." Nan Abu ya so zama fad'a tsakaninsu Amatullah ba ta ce komai ba sai ma kunyar kada su gane ita ce yarknyar da suke maganar ya mata ciki. Mai saloon ta raba wannan fad'a inda ta nufi waje wajen Ajmal ta bar d'aya daga cikin ma'ikatan ta ta k'arasa wa Amatullah. Tana fita ta gaishe shi cikin gairmamawa tare da tambayarsa ko akwai abunda yake so ne, nan ya ce ta tambayar masa ko akwai Amatullah cikin wadanda suke wajen. Dawowa ta yi tare da cewa "A cikinki wace ce Amatullah?" Cikin sanyin murya ta ce. "Ni ce." Kowa ya kalle ta sannan suka Mai da kallonsu ga Mai saloon d'in, dan Jin me zata fad'a, sai suka ki ta ce . "Sir Ajmal ne ya zo wajenki." Kallon jakkarta ta yi tare da cewa. "Bari na kira shi." Wayarta ta ciro taga missed calls d'insa, kiransa ta yi bugu d'aya ya d'aga, matayen da ke ciki su kalle ta su Kalli Ajmal dake waje Dan su tabbatar da ita yake waya. Jin ya d'aga kiran wayar ne ya sa ta cewa "Assalamu alaikum." Ya amsa da "wa'alaiki Salam." "Dan Allah ka yi hak'uri an fara mani ne ba zan iya fitowa ba." Murmushi ya yi tare da cewa. "Hak'uri na me kuma gimbiya, zan jira ko nan da gobe ne." "To na gode." Ta fad'a cikin sanyin murya, sai ta ji ya ce. "Ina babyna?" Kallon Abdallah dake rungume wajen wata mta ta yi tare da cewa. "Yana barci wata ce ta karbe shi." "Okay" Ya fad'a lokacin da ya juya yake sauka daga steps d'in, a tunanin ta tafiya zai yi kamar za ta yi kuka ta ce. "Kada ka tafi ka bar mu" "Kar ki damu ina nan ina juranku." Bayan ta kashe wayar ne ta ga kowa na kallonta wata na nuna ta da hannu tana Jin maganar da wasu ke fad'a, suna cewa wai ita ce wacce ya yi wa cikin ashe dama, wasu na cewa ba wani kaddara tunda ga shi yana tare da ita ana nuna Abdallah ana cewa shine jaririn da suka haifa wata cewa ta hi ga shi kamar an tsaga kara shi da Abdallah. Haka dai suke ta magana ba ta kula su ba, zuwa can sai kiransa ya sake shigowa Inda yake mata maganar kudin saloon zai bata, ta nuna masa ai Ammi ta bata har ta biya. Ko da aka gama mata har da gyaran kafa duk anyi mata sannan ta karbi Abdallah ta masu sallama ta ta fito. Nan ta same shi jama'a sun zagaye shi yana ta raba masu kudi, tana gefe tana kallonsa sai da kudin hannunsa suka kare, ya d'aga masu hannu alamar sun kare sannan suka waste, ya bude mata gaban mota ta shiga suka bar wajen. A hanya yana ta tambayar abunda ya d'aga mata hankali ta ce b koamai amma kada ya sake hada ta da Samuel ya kai ta wani wajen bata yarda da shi ba, shi duk bai gane ba saboda ba shi ya turo Samuel ba Nasreen ce amma sai dai ya bata hak'uri akan ta kwantar da hankalinta. A ranar bayan su Saliha sun zo aka yi mata lalle na zanen fulawa da kitso ta yi kyau Sosa. Nan aka dinga shirin tafiya Ammi, Ajmal Nasreen, Amatullah sai Affan da Abdallah. Dan Nasreen ta matsala ita ma sai an je da ita har gidansu Amatullah, duk da sun nuna mata cewa Qatar zasu fara zuwa amm ta ce sai ta bi su. K'arfe goma na safe jiriginsu ya tashi, ya yin da Kuma a can bangaren Munnir ya taho tare da Abban Amatullah zuwa nan garin Kaduna Dan komawa da ita gida. zuwa nan garin Kaduna Dan komawa da ita gida. 🤦‍♀️ *'YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) Page7️⃣1️⃣ K'arfe goma na safe jiriginsu ya tashi, yayin da Kuma can bangaren Munnir ya taho tare Abban Amatullah, zuwa nan garin Kaduna. Suna shigowa garin ko masauki ba su tafi ba kai tsaye suka nufi gidan Alhaji Ibrahim Tafida. Munnir ne ke driving sai Sadik da ke bayan mota tare da Abba. A k'ofar gidan suka yi parking motar, fitowa suka yi inda suka nufi gate din gidan, duk da security na kallonsu ba Wanda ya masu magana. Sai dai Munnir ya lura da cewa wadancan security da suka kore su ba su ba ne a gate din yau. Da sallama suka karasa wajen yayin da security din suka amsa masu, kasancewar sun ga futfura ya da suka gaida Abba cikin gairmamawa. D'aya daga cikin su ne ya Kalli Abba tare da cewa "Baba ko akwai abunda kake bukata ne, duk da na ga a mota kuka zo shi ya sa ban yi tunanin Kun zo neman taimako ba ne wajen masu gidan." Abba ya kalle shi tare da cewa. "Yaro ko ka San wata Amatullah a cikin gidan nan?" Shiru ya yi ya tuna da cewa lallai wannan yarinyar da ke zaune a gidan tare da masu gidan sunan ta Amatullah. Dan haka ya Kalli Abba ya ce. "Lafiya Baba waye kai?" "Yaro 'yata ce ita na ji labarin cewa tana zaune a gidan nan, shi ne na zo da kai na, dan wadancan bayin Allah sun zo dan su dauke ta aka hana su shiga." Yayi maganar yana nuna masu Munnir da Sadik. Shiru security din ya yi yana kallon abokin aikinsa Dan Jin me zai ce. Sai shi wannan security da tun bayan da suka gaisa da Abba bai yi magana ba sai yanzu ya ce. "Baba ka bari mu kira maka wani daga cikin gidan da zai maka bayani." Tashi ya yi ya shiga daga cikin gidan, ba jimawa saj ga shi ya dawo tare da Ahmad, wato amintaccen bodyguard din Ajmal kenan. Cikin gairmamawa Ahmad ya gaishe da shi tare da tambayarsa dalilin zuwansa. Nan Abba ya sanar da Ahmad dalilin zuwansa. Murmushi Ahmad ya yi tare da cewa. "Bisimillah Baba dan Allah Ku shiga daga ciki." Bayansa suka bi zuwa cikin gidan, ba inda ya masu jagora zuwa b'angaren bak'i. Ya sa aka kawo masu abinci da abunsha. Ba abunda suka taba Abba ya kalle Ahmad tare da cewa "Ina 'yata take?" Kallonsa Ahmad ya yi tare da cewa. "Ka Sha ruwa sai mu yi magana." Gurgiza masa kai Abba ya yi tare da cewa. "Ka da ka damu ina son ganin ta ne yanzu kafin na sa komai a bakina " Ajiyar zuciya Ahmad ya sauke tare da cewa. "Baba ka yi hak'uri ka Sha ruwa ka ci abinci Amatullah in Sha Allah nan da kwanaki buyu zuwa uku za ka ganta an kawo maka ita har gida." Kallon mamaki Mallam Abdullahi ya yi masa tare da cewa. "Yaro ban gane me kake nufi ba ka mani bayani yadda zan fahimta, 'yata na ke so na gani yanzu-yanzu ka kira ta ina son ganin ta." "Baba ka yi hak'uri ba za ka samu ganin ta yanzu ba, saboda yanzu haka ma ba ta k'asar nan gaba d'aya." Ba iya Abba kadai ba hatta Munnir da Sadik sai da suka daga kai suna kallon Ahmad. Inda ya cigaba da cewa. "Dama sun yi wata 'yat tafiya ce ita da Yallabai da Kuma..." Kafin ya kai karshen zancen da zai yi ne Abba ya dakatar da shi ta hanyar cewa. "Me ka ce!? Sun yi tafiya ba sa ma k'asar baki d'aya, sun tafi wata k'asar kenan ko? 'Yata Amatullah ce haka?" Kallon Munnir da Sadik ya yi tare da cewa. "Ku zo mu tafi kawai." Ya yi magana yana tashi tsaye, fita ya yi suka bi bayansa,duk yadda Ahmad ya so ya fahimtar da Abba Sam bai saurare shi ba ya yi ficewarsa, Munnir fa Sadik Suna biye da shi a baya dukkansu jikinsu ya yi sanyi. Har waje Ahmad ya bi su yana basu hak'uri amma ba su saurare shi ba, kasancewar Abba ya d'auki abun da zafi, gani yake yi kamar ta watsar da tarbiyar da ya bata ne ta d'auki wata tarbiyar daban, ta canza daga Amatullah ta sa da ya sani. Bangaren Hafsat kuwa ko da ta koma gida ba ta fadawa Mamanta abunda ta aikata ba, ko da mama ta tambaye ta cewa da gaske ne Munnir ya ce an gayyacr ta ne police station ta amsa wasu tambayoyi ta cewa Mama eh haka ne, daga gefe Kuma ta dinga tufka da warwara abunda za ta aikata. D'akinta ta shiga bayan ta cewa Mama barci za ta yi kada ta tashe ta. Dan haka tana shiga ta dauko kwalaben kayan shaye-shayen ta ta fara Sha,anan zaune tana cikin Sha ne ta bingire tana barci. A can k'asar Qatar kuwa ko da jiriginsu ya sauka suka fito sun ga motar da Umma ta Aiko a d'auke su. Ajmal ne a gaban motar yana rungume da Affan da ya yi barci, yayin da driver ke tuki. A baya Kuma Ammi da Nasreen ce sai Amatullah. Nihal dama tun kafin su taho Qatar ne ta nufi Adamawa. Dan ko da Ammi ta yi mata maganar ta bi su cewa ta yi za ta je gida ta ga iyaye da sauran dangi. Ammi ce ke rike da Abdallah shima barci yake yi, ita dai Amatullah sai kalle kalle take yi tana kallon yanayin k'asar Qatar da jama'ar dake cikin k'asar. A zuciyarta tana cewa. ' Allah d'aya gari banban.' Nasreen ce take kallon yadda Amatullah ta ke ta kalle-,kalle sai ta tuna a cikin jirgi yadda Amatullah ke ta tsoro da Kuma lokacin da jirgin zai tashi yadda ta ta kame jiki be tana rintse idanu. Kallonta ta yi tare da cewa. "Da alama ba ki taba shiga jirgi ba sai yau ko?" Ba tare da ta Kalli Nasreen ba ta bata amsa da cewa. "Eh Anty." "Okay, shi ya sa kika nuna k'auyanci ko, Hakan bai zana maki alamin cewa kin shiga cikin mutanen da rayuwarsu ta banban da taki ba, dan haka sai ki yi gaggawar..." "Nasreen." Sunanta da Ammi ta kira ne ya sa ta yi shiru da zancen da take yi. Har direban ya k'arasa gidan Nasreen ba ta sake magana ba, Ammi da Ajmal ne kawai suke firar garin. Bayan direban ya fito ya bude masu bayan motar ne suka fito. Umma tana tsaye dama tana juran karasawarsu. Ammi ta k'arasa ta rungume mahaifiyarta cikin farin cikin ganin ta, sannan shi ma Ajmal duk da yana rike da Affan Hakan bai hana ya rungume kakar ta sa ba. Nasreen ma ta rungume tsohuwar yayin da tsohuwar ta k'arasa wajen da Amatullah ke tsaye kanta a sunkuye, ba za zato ba tsammani ta ji tsohuwar ta rungume ta har da sumbatar goshinta. Durkusawa Amatullah ta yi da niyyar gaishe ta sai ta yi saurin Jan hannunta ta tashi suka nufi cikin gidan. A tangamemen falon gidan suka zauna, Umma ta karbi Abdallah daga hannun Ammi. Tuno mata ya yi da jarintar Ajmal. Kawai sai gani suka yi hawaye na fitowa daga fuskar tshihuwar, zama ta yi Saman kujera sannan ta cire medical glass dake kan fuskarta. Kallon Amatullah ta yi tare da mata alama ta zo, cikin sanyin jiki Amatullah ta k'arasa wajen ta, zama tayi akan carpet tsohuwar ta riko habarta tana kallonta tare da sakar mata murmushi har lokacin hawaye ne akan idanunta. Sunkuyar da kai Amatullah ta yi ta kasa gane hawayen me tsohuwar take zubarwa na tausayin ta ne ko Kuma na ciwon takaicin hanyar da aka Samu jikan na ta ba ta hanayar da ta dace ba, Ammi ma jikinta ne ya yi sanyi ganin yadda mahaifiyar ta ke kallon babyn tana kuka, ita ma sai ta fara goge k'walla cikin hikima da dabara ba tare da kowa ya gani ba. Kallon babyn take yi tana Kuma kallon Ajmal da Amatullah, bayan ta maida medical glass dake kan fuskarta. Bayan ta goge hawayen ne ta Kalli Ammi tare da ce mata su je su ci abinci ga shi can a shirya masu a dinning area, idan Kuma sai sunyi wanka sun huta ne sannan zasu ci abincin to. Dubanta ta maida kan jikan nata tilo d'aya da Allah ya bata Kuma mafj soyuwa a zuciyarta ta sakar masa murmushi tare da goge hawaye Ganin yanayin tsohuwar ya sauya ne ya sa suka ji ba dad'i, Ajmal dai tashi ya yi rungume da Affan ya nufi b'angaren da dake cikin gidan. Nasreen ma tashi, Nasreen ma bin bayansa ta yi ganin ya nufi part din Wanda dama nasa ne anan yake komai nasa yake. Ganin yadda tsohuwar ke kallon Abdaytana hawaye ne ya sa Amatullah ita ma ta fara kuka, tsohuwar ta dago habarta tana share mata hawaye tare da gurgiza mata kai, alamar ta daina kukan da take yi. Bangaren Abban Amatullah kuwa ko da suka koma garin ba farin ciki a tattre da ko wannensu, a k'ofar gida suka ajiye shi ya ce su tafi zuwa gobe sai su dawo zai tatyauna da su. Haka Sadik ya ja motar suka tafi Munnir zuciyarsa zafi kawai take masa. Abba na shiga da Sallama Umma ta fito daga dakin da farin cikin ta, a tunaninta tare da Amatullah suke. Ganinsa shi kadai ya sa ta ce "Ina 'yar tawa take?" Bai iya ce mata komai ba sai dai kawai kallonta da ya yi ya gurgiza kai cikin tausayin matar. Ganin bai yi magana ba ne ya sa ta leka har k'ofar gida ko zata ga Amatullah amma ba Amatullah ba alamar ta. Dawowa ta yi tana kallon Abba ta ce. "Amatullah tana hanyar zuwa ne?" Kallon ta ya yi ta yi tare da cewa "Ki cire tuninin yarinyar nan a cikin zuciyar ki, domin mu ne muka damu ita amma ita ba ta damu da mu ba, ba ta damu da halin da za ki shiga ba. Ina son ki cire tunaninta, gudun saukakawa zuciya kada ki takura wa zuciyarki. Kuka ta fashe da shi tare da cewa "Mallam kada ka ce ba ta yarda ta biyo ka ba?" "Bari na takaice maki zancen yarinyar nan ba ta k'asar wai aka ce ta bi shi yaron da ya mata cikin sun bar k'asar sun tafi wata k'asar can kina nan kina damuwa da ita, ko sunanta ba na son sake ji daga bakin ki." Yana gama fadar haka sai ya ji Umma na tari tana rike sai saitin zuciyarta, take Kuma sai ta yanke jiki ta fad'i Cikin tashin hankali Abba ya yi kanta yana Kiran sunan ta, amma ina ko motsi ba ta yi. Bi tashar TASKAR MAMAN IHSAN a WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z 🤦‍♀️ *YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) 7️⃣2️⃣ Cikin tashin hankali Abba ya yi kanta yana Kiran sunanta, amma ina ko motsi ba ta yi. Randar ruwa ta kasa sake tsakar gidan k'asar bishiya ya nufa, ruwa ya debo ya zo ya yayyafa mata a jiki, amma ba ko alamar za ta farfado. Sau uku yana watsa mata ruwa Umma ba ta farfado ba. Fita ya yi a rude daga cikin gidan don neman abin hawa. Ganin yadda ya ke tafiya ba lafiya ya sa wani makocinsu Mai suna Mallam Danladi ya tare gabansa yana tambayar sa abunda ya faru. "Mallam Abdullahi lafiya kuwa ina zuwa haka?" "Mallam Danladi wallahi matata ce ba lafiya yanzu haka ma ta yanke jiki ta fad'i ko motsi ba ta yi." "Subahanalilahi, ka koma gida bari na yi wa kira yarona yanzu ya dawo daga tasha kasan direba ne bari ya zo ya kai Ku asibiti." Godiya Mallam Abdullahi ya yi masa sannan

Chapter 30 of 51