ma'ikatan gidan.
Knocking ya yi a ƙofar ɗakin, har sau uku ba'a buɗe ba kuma ba'ayi magana ba. Hakan ya sa ya kutsa kai a cikin ɗakin, inda ya ga babyn na barci akan gado. Sai ƙarar ruwa da ya ji daga bathroom da alama wa tonka ta ke yi.
Zan ka she ki ke da ai ki
Zubawa yaron Idanu ya yi cike da son yaron, yana na tsaye yana kallon yaron ne sai Amatullah ta fito daga wanka.
Ganinsa ne ya sa ta juya da sauri tana ƙoƙarin shigewa bathroom ne ya lallei ta ganin yadda jikinta ke rawa wajen shiga bathroom ɗin ne ya bashi dariya.
Zama ya yi a gefen gadon tare da kallon babyn cike da so da kauna.
Fitowa ta yi daga bathroom ɗin sai dai wannan karon ta lulluɓe jikinta da wani babban towel ne, kallinsa ta yi tare da cewa.
"Zan saka kaya ne?"
"Ba tare da ya lalle ta ba ya ce,
"To ki saka mana."
Tsuke fuska ta yi tare da cewa.
"To ka fita daga ɗakin nan."
"Ba zan fita ba sai na yi abinda ya kawo ni."
Ya yi maganar idanunsa a kanta.
Tsayawa ta yi ko zai fita amma sai taga bai da niyyar tashi,hakan ya sa ta nufi wajen wardrobe ɗin kayanta ta ciro wani riga da siket na atmafa sannan dauki pant. Gaban dressing mirror ta tsaya ta dauki man shafawarta da powder sai turare ta nufi bathroom ɗin da su a hannunta. Turo ƙafar ta yi a ciki ta shafa mai ta saka pant, dama ba kowane lokaci take saka rigar mama ba.
Ajmal na riƙe da Abdallah yana ta ɗaukarsa photo, bayan ya ɗauke shi ne sannan ya masu selfie a tare.
Suna tsaka da yin selfie ne ya ji ƙamshin turaren ta, ɗaga kai ya yi ya kalle ta tana sanye da riga da siket na atmafa. Ɗinki ya zauna mata ɗagwas a jiki, shape ɗin jikinta ya fito a kayan dan hips ɗinta da ƙirjinta duk sun bayyana.
Ba ta wani yi kwalliya ba powder ne ta shafa a fusakrta amma duk da haka ta yi kyau sosai.
Tashi ya yi ya ƙarasa wajenta kusa da ita ya tsaya ya fara yi masu selfie, ganin haka ne ya saka ta ƙoƙarin matsawa nesa da shi, hakan ya sa ya janyo hannunta ta tsaya dab da shi kallonsa take tana tura baki. Hakan ya saka shi murmushi yana kallonta ya dinga masu selfie.
Sai da ya gama ne ya saki hannunta.
"Magana nake so mu yi da ke ki zauna mana."
Zama ta yi dan nesa da shi,har lokacin ba ta saki fuskarta ba.
"Kina cigaba da shayar da yaron mama ko kin dina? Ki sani duk wani madarar da zava dinga bashi bai kai nonon uwa tasiri a gare shi ba."
"Ni fa ba zan shayar da shi ba."
"Na ce ki faɗa mani ko nawa kike so zan biya ki kuɗin shayar da shi, dan ba wani abu ba ne ma idan kin ce sai na biya ki, ana haka ai."
Mamaki yake yi jin yana magana akan cewa zai biya ta kudin shayarwa ko an faɗa masa cewa ita dukiya na a gabanta ne ko me? Sannan ya dinga maganar kuɗi ta ce ba za ta shayar da shi ba shin dukiyar da yake da shi ne zai sa ta shayar da shi. Wato shi a tunaninsa tunda yana da dukiya komai ta nema zai samu? To lallai sai ta nuna masa cewa ba komai ba ne dukiya zai baka, wato don ya taso cikin gata da jin daɗi da komai na more rayuwa, ya tara ma'aikata da masu tsaron lafiyarsu yana basu kuɗi yana ganin kamai yake so kuɗi zai masa, to yanzu zai gane cewa wata rana dulaiya ba za ta iya amfana masa komai ba.
Tana tsaka da tunani ne ya ji muryarsa yana cewa.
"Ki faɗi daga Naira miliyan daya zuwa ashirin ko nawa kike so zan baki, sai ki shayar mani da shi. Bayan haka kuma ina son kuyi tunani akan goben yaron mu duk da cewar ba ta hanyar da ta dace muka same shi ba amma ba yadda za mu yi ƙaddararmu ce haka. Gara ya tashi ya ga kansa a gaban mahaifinsa da mahaifiyarsa ya fi a ce ya tashi a wani wajen yana tambayar ina mahaifiyarsa take ko ina mahaifinsa yake, me za ki faɗa masa game da Asalinsa?"
"Sai na faɗa masa gaskiya ba ta hanyar halak aka same shi ba, cikin shege na yi na haife shi."
Rintse idanu ya yi da ƙarfi tare da cije baki, sannan ta cigaba da cewa.
"Da kake Magana akan za ka biya ni dan na shayar da shi kai ka ɗauka komai kuɗinka zai iya yi maka? To ka yi kuskure domin ba komai dulaiyarku zai maku ba. Kuma zancen aure a zahirin gaskiya ba zan aure ka ba saboda wasu dalilai."
Daga nan ta fita daga dakin ta barshi riƙe da yaron, jikinsa ya yi ba ƙaramin sanyi ya yi ba.
Tana fita ta haɗu da Iya a bakin ƙofar dama tana ƙoƙarin shiga ne ta ji maganar da Amatullah ke yi dan haka ta canzawa Amatullah fuska, dan ranta ya ɓaci da maganganun da ta fadawa Ajmal kallon da ta mata ma ya sa ta gane ran iya ya ɓaci, kwaɓe fuska ta yi kamar za ta yi kuka, dan kallon uwa take wa iya.
Iya ta nufi ɗakinta Amatullah ta bi bayanta.
Cikin sanyin jiki Ajmal ya fito daga ɗakin ya nufi part ɗinsu. Ma'aikatan gidan na ta gaishe su bai kula ba balle ya amsa masu.
Ammi na zaune a falo ta ga shigowar sa da alamar damuwa a tattare da shi, upstairs ya nufa sai ya ji muryar Amminsa.
"Lafiya kuwa?"
Dakatawa ya yi tare da cewa.
"Ba komai Ammina."
"Na ga ka fita cikin farin ciki ka dawo tanayinka ya sauya."
"Ba komai Amminta bari na shirya an gayyace ni ne wani zama da gidan TV suka shirya, ina sauri zan tafi lokaci ya kusa."
Daga nan ya haura upstairs da sauri Ammi ta zauna zuciyarta cike da tarin tambayoyi.
Da misalin ƙarfe biyar na yamma aka fara tattaunawa da Ajmal a gidan TV.
Kuma kai tsaye suka haska shirin.
Inda suka yi masa tambayoyi akan halin da ya shiga lokacin da wannan jarabawar ta same shi.
Ammi ta kunna tv daidai lokacin da ake masa tambaya ake cewa.
"To yallaɓai yanzu me ye makomar siyasarka, bisa la'akari da cewa a baya lokacin faruwar wannan al'amari aka dakatar da siyasarka, to yanzu an tabbatar da cewa ba ka da laifi. Shin za ka koma takarar kujerar Gwamna kamar yadda ka fito?"
Murmushi ya yi tare da cewa.
"Dama ni ba na da alaƙa da siyasa, ni ba ɗan siyasa ba ne lokaci ɗaya na fito takara a bisa wasu dalilai da kuma goyon bayan wasu daga gwamnati da na samu, wanda suke ganin cancanta ta ce ta saka suka mara mani baya. Wanda hakan ya bani ƙwarin guiwar tsayawa takara. Amma a yanzu gaskiya bana jin zan iya cigaba da takarar Gwamnan jihar nan."
"Me ya saka ka ja da baya bayan kana da goyon bayan gwamnati da kuma talakawa suna son ka da saka ran cewa za ka kawo masu sauyi a cikin rayuwarsu.
Murmushi ya sake yi tare da cewa.
"Shawara da ban su shi ne su yi addu'a Allah ya kawo masu shugaba adali mai tausayin takawa wanda zai zame masu garkuwa a gare su."
"To yanzu kana nufin ka bar takarar ko na ce ka janye ke nan?"
"Gaskiya na hakura da neman wannan kujerar ya fita daga raina yanzu, amma dai ban riga na gama yanke hukunci ba."
Za ta sake masa wani tambayar ne ya ce
" Duk wani abinda zan faɗa na faɗa."
"To ga tarin daƙonni daga masoyanka sun turo ko guda biyu muna son ka daure ka amsa mana."
Fara karanto sakon ta yi inda take cewa.
"Yallaɓai ba wanda ya dace da kujerar wannan jahar sai kai, dan Allah ka da kada ka janye irinka muke buƙata."
Murmushi ya yi bayan an karanta tare da cewa.
"Godiya nake za ku ji daga gare ni."
"Sako na biyu kuma inda wata baiwar Allah ke cewa Yallaɓai Ajmal dan Allah ka taimaka mu ka dawo takarar Gwamnan jihar nan, ko da aka dakatar da kai mun shiga damuwa sosai saboda taimako da kake yi ga talakawa, wanda ba ka zama Gwamna ba ka taimake su ina ga ka zama jagoranmu."
Murmushi nan ma kawai ya yi tare da godiya ya masu sallama ya tafi.
Ko da ya fito ga motocin da ya zo da su a jere da kuma security nasa da suke kiran fitowarsa.
Motocin guda biyar ne suka zo da su, biyu a gabansa suna bin sa yayin da kuma biyu ke bayansa nasa motar. Suka fito a jere suka hau saman titi suka fara tafiya.
*Weekend ba lallai na samu yi maku update ba maybe dai ranar Monday in sha Allah*
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
09065327995
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
🤦♀️ *YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
Ban yarda a karanta mani shi a youtube ko a maida shi audio ba tare da izinina ba.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Page5️⃣8️⃣
Motoci guda biyar ne suka zo da su, biyu a gabansa biyu na binsa a baya. Suka fito a jere suka hau saman titi suka fara tafiya.
Ɓangaren Amatullah tunda ta faɗa wa Ajmal maganganu marasa daɗi ta fito ta ga Iya na jin ta. Ta nufi ɗakinta sai Amatullah ta bi bayanta.
Suna shiga Iya ta zuba mata Idanu tana Kallonta tare da cewa.
"Kin kyauta kenan ? Me ya maki da zafi da har za ki jefe shi da kalamai marasa daɗi? Ɗan da kika haifa ne ke da kanki kike sheganta shi ina ga wani ne ya sheganta maki yaro? Ashe za ki ji daɗi ko?"
Kanta a sunkuye ta durƙusa kamar mai roƙon gafara, girgiza kai ta yi alamar a'a.
"To me ya laifinsa da har za ki wulakanta shi? Kin san waye shi da kuma matakan da ya taka a rayuwarsa, idan ban da jarabawar rayuwa ke baki isa ki wulaƙanta shi ba. Mata nawa ne ake yi wa ciki amma kiga namijin baya ƙaunarsu baya so a danganta shi da ɗan shegen da yayi wa wata ciki, har ƙaryata mace suke amma ke kin samu yana ƙaunarki yana ƙaunar ɗan da kika haifa amma duk da haka kike wulaƙanta shi. Idan har kika bari ya guje ki ko ya juya maki baya ke ce za ki yi nadama ba kowa ba."
Shiru tayi tana jin iya dan ta dauki Iya tamkar uwa a gare ta. Inda iya ta cigaba da cewa.
"Sannan saboda wauta irin taki hatta ɗan da kika haifa kike nunawa ko ina kula, me ye laifinsa? Ajmal bai cancanci hakan da kika masa ba, yadda yake mutum mai kyautatawa ga kowa ko ya san mutum ko bai san shi ba yana kyautatawa mutane jama'a na alfahari da shi. To shi ne zai fusakanci rashin kyautata wa daga gare ki ba, ka da ki ga laifinsa ba shi ya kai zomon ba rataya aka ba shi."
"Iya ba zan iya aurensa ba ne"
"To na ji ban tilasta ki ba akan ki aure shi, amma ka da ki juya masa baya ta hanyar ƙin shayar da yaron nan, dan na lura yadda mazaje da yawa ke gudun ɗan da suka yi sanadiyar zuwansa duniya ba ta hanyar aure ba sai su juya masu baya basa ma ƙaunar ganinsa saboda rashin adalci, amma ke kin samu ma ya amsa ya ƙaunace shi har za ki wulakanta shi? Idan har na isa da ke na faɗa maki ki dauka to ki shayar da yaron nan mama."
A firgice ta ɗago kai tana kallon Iya da take maganar, inda iya ta cigaba da cewa.
"Ba ki san baiwar da Allah ya masa ba, ka da ki hukunta wanda bai da laifi bai san komai ba akan laifin da wani ya aikata hakan kuskure ne."
Kuka ne ya taso mata dan ba ta jin za ta iya tsallake maganar iya kallon uwa take mata, tana tsaka da kukan ne suka ji sallamar Ammi ta shigo.
Ganin yadda Amatullah ke kuka ne ya sa ta ƙarasa wajenta da sauri tare da dafa kafaɗarta ta fara magana .
"Subhanahi me ya same ki 'yata?" Ko dai Ajmal ne ya maki wani abun? Dan na ga ɗazu ya zo nan ya koma ransa a ɓace."
Shiru ta yi tare da dakatar da kukan da take yi dan abin da kunya ta iya nunawa Ammi ce wa ba ta san gudan jininta, matar da ta dauko ta a rana ta kawo ta inuwa ta canza mata rayuwa daga wahala zuwa huhu da jin daɗi bai cancanci ta mata haka ba. Dan haka ta yi shiru ta kasa magana.
"Faɗa mani gaskiya idan shi ya saka ki kuka zan ɗauki matakin da ya dace a kansa."
"Amma ba abinda ya mani."
Iya ce ta yi saurin cewa.
"Ba wani abu ba ne ranki ya dad'e wai akan zancen shayarwa ne ita ba za ta shayar da shi ba fa shi ne."
Murmushi Ammi ta yi tare da cewa.
"Wannan ba matsala ba ne ba wanda zai tilasta ki , shi ma zan masa magana ba zai sake maki maganar shayarwa ba."
"Ammi zan shayar da shi ɗin tunda na san kema za ki so hakan, Iya ma haka zan yi dan farin cikinku."
Rungume ta Ammi ta yi tare da sanya mata albarka, ita dai tana tausayin yarinyar har cikin zuciyarta.
"Kin tabbata ba tilasta maki ya yi ba?'
"Ammi ba wanda ya tilasta mani wallahi."
Murmushi ta yi tare da sanya mata albarka sannan ta masu sallama ta tafi.
Ajmal na kan hanyarsu ta zuwa gida ne sai ga kiran wayar mai girma Gwamna, ɗagawa ya yi tare da cewa.
"Assalamu alaikum."
"Wa'alaika salam, Ajmala ka koma gida ne?"
"Excellency ina kan hanyar komawa gidan kenan."
"Okay idan ba damuwa ka ka biyo ta ofishina ina son magna da kai."
"Okay"
Daga nan ya katse kiran wayar sannan ya ce a sanarwa motocin da ke gabansu inda za su nufa.
Tafiya take a cikin maye ta fito daga cikin wani gida, sai haɗa hanya take yi tana marisa. Tana riƙe da handbag ɗin ta a dayan hannu, dayan hannun kuma ta riƙe takalmominta da shi.
Wata mota na tafiya ta tare gaban motar ta bude hannayenta alamar ba hanyar da motar zai wuce, Allah ya so matuƙin motar a hankali yake tuƙi, hakan ya saka shi taka burki da sauri.
Mamaki yake yi ya tsaya yana kallonta daga sama har ƙasa, riga da wando ne a jikinta riga da jikinta wando duk ya matse ta sai yar rigar ta da kaɗan ta kadan ta wuce cibiyarta, karin gasshin attachment da ta yi kamar mahaukaciya ya rufe rashin fuskarta.
Gadan-gadan ta nufi wajen motar, ɗaga ƙafa ta yi tana ƙoƙarin haurawa can saman motar. Mamaki dattijon yake yi yadda ta ke ƙoƙarin haurawa can saman motar, ta gaban motar ne ta bi duk zafin rana da zafin da wajen ya ɗauka haka take haurwa, sau biyu tana faɗowa ta na sake yunƙurin hawa, a na uku na ta samu ta haura ta haye can saman tsakiyar motar ta zauna.
Sai bubbuga hannu take yi tana cewa.
"Ja mu tafi."
Ta yi maganar cikin maye,shi dai dattijon dai ɗaga kai ya yi yana kallon saman motar da ta ke ji tana duka kamar ta samu ganga.ƙarar ne ya ishe shi daga saman kansa, fitowa ya yi a fusace tare da daka mata tsawa, dariya ta yi tare da cewa.
"Ka kai ni gida mana."
Ta yi maganar cikin maye, gangarowa ta yi ta sauko tare da faɗuwa ƙasa.
Bude bayan motar ya yi tare da cewa
"Shiga."
Murfin motar ta taka tana ƙoƙarin sake haurawa can saman motar ne ya hankaɗa ta ta faɗa cikin motar ya rufe marfin motar.
Zagayawa ya yi ya shiga mazaunin direban ya ja motar ya bar wajen.
Bayan Ajmal ya isa ofishin mai girma Gwamna ne aka yi masa iso bayan Gwamna ya bada izinin shigowarsa.
Ko da Ajmal ya shiga ya tarar da Gwamna tare da shugaban jam'iyyar su.
Kasancewar su manya sun haife shi a haife, dan haka ya durƙusa ya gaida su cikin girmamawa.
Bayan sun gaisa ne suna zaune mai girma Gwamna ya yi wa Ajmal jaje na abinda ya faru a baya, kasancewar ba ya ƙasar lokacin yana kasar waje wajen jinyar lafiyarsa. Dawowarsa ne ya tarar da halin da ake ciki.
Nan dai suka gaisa sosai na yaushe rabo inda kuma Gwamna ya ke ƙara bashi yaƙirin abinda ta faru da kuma hukuncin da shuwagabannin zartarwa suka yanke ba tare da tabbatar da cewa yana da karfi ko akasin haka ba, sannan ya daura da masa zancen cewa ya dawo kan kujerarsa da yake neman takara.
A nan ne ya nuna masu ƙin amincewarsa na zancen takara, dan dama tun farko ba wai shi ne ya yi ra'ayin siyasa ba, Gwamna ne ya janyo shi da kuma Dad dinsa da ya bashi ƙarin guiwa, amma yanzu da hakan ta kasance ne siyasar fita fita daga kansa.
Nan dai suka dinga bashi shawara da jan hankali dan ya janye ƙudiransa, wanda daga ƙarshe sai ya nuna masu zai yi shawara da ahalinsa.
Sallama ya masu inda ya fita ya samu security dinsa na jiransa, suka shiga motocinsa suka bar wajen.
Ɓangaren Amatullah kuwa bayan Ammi ta masu sallama ta fita ne sai ta koma ɗakin Amatullah, babyn na kwance yana barci ta ɗauke shi ta fito da shi, inda ta bawa daya daga cikin ma'aikatan gidan sakon cewa ta a sanarwa Iya ita ce ta ɗauki Abdallah.
Iya ta cewa Amatullah ta bi Ammi ta sake sanar da ita cewa ba fa Ajmal ne ya saka ta kuka ba, dan ta lura da Ammi kamar ranta ya ɓaci tana ganin kamar shi ne ya tirsasa ta.
Dan haka tashi ta nufi ɓangaren su Ammi. Da sallama ta tura ƙofar ta shiga inda ta sami Ammi da Nihal zaune a farko.
Amma ce kawai ta amsa mata sallama inda ya shiga cikin nutsuwa zata zauna a carpet Ammo ta ce ta hau kujerar ta zauna amma ta ƙi, dan haka Amminta barta nan ta zauna.
Babyn na hannun Ammi tana kallon sa tana murmushi, dan yana tuna mata da jarintakar Ajmal.
Kallon Amatullah ta yi tare da sakar mata murmushi ta ce,
"Ko akwai abinda kike buƙata ne Amatullah?"
Sunkuyar da kai ta yi tare da girgiza kai dan ta ma rasa abinda za ta ce.
Abdallah ne ya fara kuka, inda Ammi ta kalle Amatullah tare da cewa.
"A bashi madara ne ko za ki bashi mama ya sha."
Satar kallon Nihal ta yi inda ta ga sai mugun kallo take jifarta da shi.
Amma ta ga alamar kunya take ji dan haka sai ta tashi ta miƙa mata babyn tare da cewa.
"To ba shi ya sha."
Dai-dai ka lokacin da Motocin Ajmal ke shigowa cikin gidan.
Ba musu ta ɗan daga riganta ta saka masa nonon a baki, take kuwa ya kama ya fara tsotsa. Jije baki ta fara yi alamar yana mata zafi.
Turo ƙofar aka yi aka shigo tare da sallama, ƙamshin turaren da ta ji ne ya tabbatar mata da cewa Ajmal ne ya shigo, kanta a sunkuye taba cije laɓɓa.
Turus ya tsaya tare da aka hannayensa a aljihu ya zubawa Amatullah Idanu, fusakarsa ɗauke da annuri yake kallonta. Ita duk ba ta san yana yi ba, Ammi da Nihal ne suka lalle shi ganin wacce yake kallo ne ya sa Ammi kau da kai tare da mai da sunanta kan wayarta.
Nihal kan duk ranta ya gama ɓaci ne ya sa ta yi tsaki,wanda jin tsukin ne ya saka Amatullah ɗaga kai ta lalle ta, sannan ta kalli inda Nihal ke kallo, ganin yadda yake kallon babyn ne ta saka ta taɓe baki ta ɗauke Idanunta.
A hankali ya ƙaraso tare da sunkuyawa a gabanta ya fara magana fuskarsa ɗauke da murmushi.
"Na gode da kika yanke shawar da ta dace."
A hankali ya yi maganar yadda bayan Amatullah ba wanda zai ji, inda ya cigaba da cewa.
"Me kike son na baki, kin yanke shawara iya kudaden da kuke bukata ne? Miliyan nawa? Ta account zan tura maka ko cash kike so?"
Tsuke fuska ta yi ba tare da ta ce komai ba
"Ya kika yi shiru?"
"Ka ci darajan me daraja, dan haka akan shayar da yaron nan bana buƙatar ko kwabo daga gare ka."
Kallonta yake jin me take cewa dan a wanan zamani zai yi wuya mace ta ƙi karbar miliyoyin kudin da ya mata tayinsu.
Ya rasa me zai ce mata sai murmushi yake yi, tare da cewa
"Zan zo na maki godiya ta musamman."
Ganin kamar rigar ya sauka ne akan hancin baby tunda baya ganin Maman da bakin Baby dan haka sai ta kai hannu zai janye rigar ne sai ya fasa ganin yadda take cije baki alamar zafi.
A ɗan rikice ys yi maganar yana cewa.
"Ammitana jin zafi fa kin ga yadda take yi da fuska wai wannan zafin da take ji ba ya da magani ne? Ammi ko na kai ta Asibinti ne?"
Kallonsa Ammi ta yi tare da cewa
"Sannu da dawowa yaushe ka shigo?"
Kunya ce ta kama shi ya sosai ƙeya tare ta mik'ewa tsaye.
Horn dattijo ya yi inda mai gadin ya leƙo ganinsa ne ya saka shi buɗe wa da sauri, inda ya yi parking tare da fitowa ya bude bayan motar ta finciko ta wanda har yanzu a cikin maye take, hanayar ya yi ta fito waje ya yi cilli da ita ƙasa.
*Ku yi hakuri da ji na shiru da rashin update bana da lokaci ne.*
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
🤦♀️ *YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
Ban yarda a karanta mani shi a youtube ko a maida shi audio ba tare da izinina ba.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Page5️⃣9️⃣
Horn Dattijon ya yi inda maigadin ya leƙo, ganinsa ne ya sa shi buɗe wa da sauri, inda ya yi parking tare da fitowa ya bude bayan motar ya finciko ta wanda har yanzu a cikin maye take, ya yi cilli da ita ƙasa.
Nan ya barta a ƙasa sai suratai take yi, inda ya nufi ce ƙofar da za ta sada shi da falo. Tun kafin ya shiga yake ƙwala mata kira.
"Hajiya Maryam! Hajiya Maryam!! Hajiya Maryam!!!"
A ruɗe ta fito jin yadda yake ƙwala mata kira ta san ba na lafiya ba ne. Munnir ne ya fito yana biye da Mamansa a baya. Kallon Hafsat suke cikin mamaki, Maman Munnir ba karamin al'ajabi take yi ba ganin halin da Hafsat ke ciki. Yayin da shi kuma Munnir farin ciki ne ya kama shi, dan ya san yanzu ya samu hanyar rabuwa da ita da hujja.
"Wa nake gani haka kamar Hafsat?"
Hajiya Maryam ta yi maganar tana kallon Hafsat, Munnir ne ya ɗora da cewa.
"Ba kama ba ce Mama ita ɗin ce dai kike gani, ai na faɗa maki cewa tana shaye-shaye ba zan iya aurenta ba, amma kike ganin kamar sharri nake mata, gara da kuka ga zahiri da kanku."
Nufar inda Munnir yake tsaye ta yi yayin da Yusuf ya shige ciki. Hafsat na ƙarasowa wajen Munnir ta fara magana tana cewa.
"Kwa..na biyu..shshine ba ka zuwa wu...wurina na ko? Meee.n.na yi maka ne?"
Bai saurare ta ba ya juya ya nufi ciki, ta bi bayansa har tana cin karo da ƙofa, Mama ma ta rufa masu baya.
Bedroom ɗinsa ya nufa inda Hafsat ke binsa, tana cewa.
"Yaya ya Munnir?"
Kafin ta ƙarasa har ya shige ya murzawa kofar key, ko da ta zo gaba ɗaya ta afkawa kofar, sai ta ji ƙofar a datse, bubbuga ƙofar take yi, tana kiransa.
Mama ce ta ja ta suka nufi ɗakinta. Suna shiga ta haye saman gadon Mama ta fara barci.
Cikin sanyin jiki ta fito dan ita fargabarta kada Alhaji Yusuf ya ce an fasa aurawa Munnir Hafsat, dan ta san rikicin da zasu kwasa ita da 'yar uwarta mahaifiyar Hafsat.
Kai tsaye ɗakin Alhaji Yusuf ta nufa, inda ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 51