gashin kaina."
"Nan kam ba handryer kai mai yawan suma ya kamata kana yawo da shi ɗan balarabe."
Bai kula shi
ba ya dinga goge kansa.
Sai a lokacin ya lura bai ga agogonsa a saman side dorower ba.
"Ina agogonsa yake? Kai Ni sai na ga kamar ba nan ɗakin na kwana ba."
"Ya kake magana wani iri ne? Idan ba nan ka kwana ba ya za'ayi ka tsinci kanka anan?"
Shiru ya yi ba tare da ya ce komai ba, inda Fu'ad ya cigaba da cewa
"Ni na ɗauki agogon bari na ɗauko maka."
Daga nan ya fice daga dakin ya nufi ɗayan ɗaukin, cike da tinani iri-iri a zuciyarsa, wai ya hakan ta faru ne? Da a ce yarinyar na cikin hayyacinta da dole sai ya tuhume ta akan abinda ta yiwa abokinsa, amma ita ma ba abinda ta sani amma bari ya je ya same ta.
Ko da ya shiga ɗakin ba kowa a ciki, sai dai duk jini ya ɓata sanin gadon.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un. Kenan Ajmala cikakkiyar budurwa ya yi amfani da ita ba tare da sanisu ba, ta ya ya idan yarinyar nan tuggu adan haɗa mata ba ba za ta ji ciwon rasa budurcnta ba."
Gaba ɗaya ya rasa me ke masa dad'i, haka ya fita bayan ta dauki agogon Ajmal.
Komawa ya yi ta kai masa agogon nan da nan suka shirya suka bar hotel ɗin kasancewar jirgin ƙarfe tara Ajmal zai shiga.
Sai da ta taka Ajmal har airport sannan ya juya ya koma hotel ɗin, ya shirya kayansa, duk da baiyi niyyar komawa Kaduna yau ba haka kawai ya ji hotel ɗin baya son sake kwananta.
A ranar ya bar garin Minna ya koma garin Kaduna.
*Cigaban labarin*
Bayan Fu'ad ya gama basu labari ne Ajmal ya mike a fusace tare da janyo Dr Fu'ad ya shaƙe masa wuyan riga yana cewa
"Da kyau ka iya tsara labari sosai, amma ka sani wannan ƙirƙirerren labari ne, amma labarin zahiri ya fara."
Dad ne ya kalli Ajmal tare da cewa
"Sake shi Ajmal."
Kamar ba da shi yake ba, jikinsa har ya fara rawa.
"Za ka faɗi gaskiya ko sai na kashe ka?"
Ita kuwa Amatullah tana zaune a wajen sai kuka take yi. Jamal ransa ya kai ƙololuwar tashi idanunsa sun yi jajir kamar garwashin huta sai huci yake fitarwa, kamar wani mayunwacin zaki.
Ammi ce ta saka masa tsawar bai sake shi ba, a fusace ta ɗaga hannu ta gaura masa mari. Sai a lokacin ya sake Dr Fu'ad wanda idanunsa sun yi ja ya fara tari a galabaice ya zube a wajen.
Ajmal ke kallon Amminsa cike da mamaki, tunda yake yau ne karo na farko da ta mare shi kuma akan Fu'ad.
"Ammi ki faɗa masa ya fadi gaskiya, wannan zancen nasa ban yarda da shi ba, domin ban ga hujjar da zan yarda da ita ba."
Daƙyar Dr Fu'ad ya iya cewa
"Za ka ga hujja yanzu kuwa."
Wayarsa ya ciro daga cikin aljihunsa yana daddannawa.
*Kuyi haƙuri da wannan ba yawa, saboda bana da lokaci ne, ganin kuna ta tambaya na ɗan maku*
*Da alƙalamim*✍️
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
09065327995
🤦♀️ *YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
Ban yarda a karanta mani shi a youtube ko a maida shi audio ba tare da izinina ba.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Page4️⃣6️⃣
Wayarsa ya ciro daga cikin aljihunsa yana daddannawa. Bayan ya lalubo lambar da zai kira ne ya danna kira.
Kamar da fitowarsa kenan daga bathroom ya ga wayarsa na ringing. Ɗagawa ya yi tare da cewa.
"Fu'ad ya kake?"
Ba tare da ya bashi amsa ba ya ce,
"Kana ina ne?"
"Ina zan je a daidai wannan lokaci?"
"Dan Allah taimako za ka mani."
"Wane irin taimako zan maka?"
"Ina son ka je mazanya hotel akwai wani ma'aikacinsu mai suna Murtala wanda na ji ana masa laƙabi da IN DA KUƊINKA, to ina son ka bashi waya zan masa magana ne."
"Okay ba damuwa amma ba a wannan daren ba ko?"
"Yanzu nake buƙata."
"Dan Allah ka bari sai da safe."
"Ba zai yiwu ba ne, kawai matsala dan Allah ka taimaka."
"Shikenan."
Daga nan ya katse kiran wayar nan da nan ya saka jallabiya ya fito.
Bayan sa sanarwa matarsa ne ya yi sauri ya fita dan zuwa hotel ɗin .
Ajamal ya kalli Fu'ad tare da cewa
"Ka gama duk shirin da za ka yi ina da hanyoyin da zan gano gaskiya. Ko da ma ace hakan ta faru kai ka shirya komai."
Sai yanzu ya fara tunani abubuwa suka dawo masa, bayan fitar Fu'ad daga dakin wani ya shigo ɗauke da cup ya ce abokansa ne ya ce ya kawo masa coffe. Sannan tunda ya sha coffee gaba ɗaya yanayinsa ya sauya sai wani mugun sha'awa da bukatar mace ke taso masa. Daga nan sai barci ya fara ci dan haka ya shige cikin bargo.
Zuwa can kuma sai yake jin kamar mace a tare da shi daga nan hankalinsa ya ƙara tashi feelings ɗinsa ya karu mararsa na masa ciwo kamar zata fashe.
Da duk da baya gane komai ji yake kamar a mafarki ne, amma tabbas ya san ya kasance tare da mace a daren ranar amma sau yake gani kamar mafarki ne ba gaskiya ba.
Tunawa ya yi da lokacin da ya farka daidai lokacin da Fu'ad ke shigowa ɗakin, lallai da hadin bakin Fu'ad a cikin wannan lamari shi ya shirya Komai, dan akan me ba zai faɗa masa ba, sannan shi da ya kwanta daga shi boxer da singileti ya farka ya ga kaya a jikinsa, bai ga agogo ba inda ya ajiye sai daga baya Fu'ad ya kawo masa, tabbas Fu'ad ya san komai.
A fusace ya tashi yana huci ya nufa Fu'ad da niyyar sake rarumarsa sai Ammi ta daka masa tsawa, wanda ya shi shi dakatawa ba tare da ya yi motsi ba.
Dawowa ya yi tare da zama yana ta faman huci.
Ammi ce ta kalli Dr Fu'ad tare da cewa.
"Wannan ce yarinyar da gansu kwance a gadon tare a wancan ranar?"
Girgiza kai ya yi tare da cewa
Ban da tabbacin ko ita ce, domin ko da na shiga na same su kwance ita macen gashin kanta yana da tsawo sosai dan a hargitse gashin yake duk ya rufe mata fuska kuma..."
A fusace Ajmal ya ce,
"To dama baka da tabbas akan cewa ita cewa ita ce shi ne ka ce wai mine uban ɗan da ta haifa?"
"Eh bana da tabbas akan wacce na ganka kwance da ita amma ina da tabbas cewa kai ne uban wannan jaririn."
Ransa ne ya ƙara ɓaci ya buɗe baki da niyyar zai yi magana sai Dad ɗin sa ya ce.
"Ka yi mani shiru Ajmal ka bari mu bi komai a hankali, hakan zai sa mu fahimci gaskiyar al'amari."
Shiru ya yi tare da komawa gefe.
Ammi ce ta kalli Amatullah da ke ta kuka ƙasa-ƙasa sai hawaye da ke wanke mata fuska ta ce,
"Amatullah cire ɗankwalinki na ga gashin kanki."
Ba musu ta cire ɗankwalin kamata sai dai ta tufke suman da ribbon. Sai Ammi ta sake cewa.
"Ki warware shi na gani."
Cire ribbon ɗin da ta tufke kai ta yi nan da nan suman kanta suka zubo har gadon bayanta.
Jinjina kai ta yi tare da kallon Fu'ad wanda shima Amatulla ya ke kallo.
"Ammi za ta iya kasancewa ita ce fa amma bari Kamal ya..."
Dakatawa yayi da maganar jin wayarsa na ruri, ganin Kamal ne ya saka shi cewa ɗagawa tare da cewa.
"Assalamu alaikum."
Kamal da ke tsaye a hotel ɗin ne ya amsa tare da cewa.
"Na zo da shi wanda kake nema fa wanda ake wa laƙabi da IN DA KUƊINKA ance ya tafi ƙauyensu juya sai bayan sati ɗaya zai dawo."
Jikin Fu'ad ne ya yi sanyi jin cewa baya nan, dan haka ya yi wa Kamal godiya ya kashe wayar.
Kasancewar a handsfree ya saka wayar duk sun ji.
Cikin ɓaci rai Ajmal ya ce ba ƙauye ya tafi ba ko rami ya gina ya binne kansa a ciki sai na saka an nemo shi sai ya gane kurensa.
Wayarsa ya ɗaga ya kira wata lamba, bugu biyu aka daga tare da cewa.
"Yallaɓai kai ne ka kira ni yanzu? Fatan dai lafiya?"
"Ba lafiya ba D.P.O wani yaro nake so ka saka yaranka su binciko mani shi a duk inda yake."
D.P.O ya ce baka da matsala waye ya taɓo ka?"
"A mazanya hotel akwai wani ma'aikacinsu mai suna Murtala ana masa laƙabi da IN DA KUƊINKA, ina son ku kama shi idan ya shigo hannu ku sanar da ni."
"Amma yallaɓai me ya haɗa ka da shi?"
Murmishin takaici ya ya tare da cewa.
"Na sauka a hotel ɗin ne ya zuba mani abu a cikin coffee wanda ba a cikin hayyacina ba har na kusanci wata mace?"
Da mamaki D.P.O ya ce,
"What!, Lallai ya ɗebo ruwan dafa kansa, ka da ka damu da shi da wanda ya sake shi, dan akwai lauje cikin naɗi saka shi aka yi."
Sallama suka yi da niyyar cewa da safe zai saka a nemo shi a duk inda ya shiga.
Dad ne ya lalli Fu'ad ya ce ya tafi gida dare ya yi.
Nan ya masu sallama ya tafi, inda ya kalli Amatullah da har yanzu kuka take tare da cewa.
"Ƴata ki daina kuka haka kin ji ki yi hakuri da yadda kaddararki ta zo maki, kuma ki karɓe ta hannu bibbiyu Allah zai kawo maki mafita.
Ammi ta miƙa mata jaririyar ta karɓa tayi masu sallama ta fita. Da kallo suka bita har ta fice, ajiyar zuciya Ammi ta sauke tare da cewa.
"Ni yarinyar nan ma wallahi tausayinta nake."
Jinjina kai Dad ya yi tare da cewa
"Allah ya warware mana wannan matsala."
Bayan ta fita ne sai Dad ya yi wa Ajmal maganar cewa shi ma ya je ya kwanta.
"Dad ai wallahi ba zan iya barci ba cewa cikin wannan tashin hankali da nake ciki."
"Ai ba wai ina nufin ka yi barci ba ne, ka tafi ka kwanta ka huta."
"Ba zan taɓa iya hutawa ba har sai na ga an Kama wannan tsinannen yaron."
Haka ya fita tana ta huci shi kaɗai.
Ɓangaren Amatullah kuwa tunda ta shiga ɗakinta kuka take. Iya da ta ji shigowar ta ne ta shigo ɗakin, ganin yadda take kuka ne ya saka ta tambayarta abinda ke faruwa, ba ta faɗa mata ba sai kuka, rarrashinnta take yi akan ta yi shiru.
Ganin Babyn ma na kuka ne ya saka iya ta haɗa masa madararsa ta bashi ya fara sha. Dan har lokacin Amatullah ba ta yarda ta bashi nono ba,dan ta ce ba za ta shayar da shi ba, sai dai madara kawai ake ba shi.
Sai da ta ƙoshi ya yi barci ne sannan ta kwantar da shi a gadonsa ta sauke masa net.
Daga nan ta fice Amatullah kuwa ta nufi bathroom ta sake watsa ruwan zafi a jikinta sannan ta dawo ta kwanta ranta babu daɗi.
Ta saba da a cikin yanayin bakin ciki ta kwana tana sallah amma a yanzu ba hali kasancewar jego take yi."
Ɓangaren Hafsat kuwa tunda ta yi tuƙi a cikin maye ta yi accident kwananta daya asibitin ta wuce ba tare da likita ya sallame ta ba.
Umman Amatullah kuwa tana samun duk kulawar da ta dace daga likitoci, Munnir ne ya tsaya tsayin daka akan komai, shi ya ɗauki nauyin na ta da komai dukan kudin da aka kashe. Har yanzu tana ƙarƙashin kulawar likitoci ne.
Washe gari da sassafe ne motar police ta yi dirar mikiya a mazanya hotel.
Gaba ɗaya hankalin jama'a na kan su ana mamakin abinda ya kawo su.
Shiga ciki suka yi suka nemi ganawa da manajan Hotel ɗin.
Suka sanar da shi abinda ke tafe da su, hankalinsa ya tashi sosai kuma ransa ya ɓaci da abinda IN DA KUƊINKA ya aikata.
Ya kuma sanar da su cewa ya yi tafiya ba ya garin ya tafi ƙauyensu sai nan da kwanaki shida zai dawo.
Nan suka ce ba zancen a tsaya jiransa dole ne duk inda yake a a kamo shi.
Nan aka tara sauran ma'aikatan hotel ɗin ake tamabayarsu wanda ya san ƙauyen na su, nan kowa ya ce bai sani ba.
Inspector ne ya kalle su tare da cewa.
"Yanzu dukkanku nan kuma tare da shi kuma aiki amma ba wanda ya san garin da yake?"
Manajan Hotel ɗin ya kalli ɗaya daga cikin ma'aikatan hotel ɗin ya ce,
"Aminu ba kai ne ka kawo shi ba?"
Sai da gabansa ya fadi dan yana tsoron ya afka ciki.
"Eh yallaɓai shi ya same yake cewa yana neman aiki ko zan masa hanya ko gadi ne, shi ne na masa hanya har ka ɗauke shi aiki."
Inspector ne ya lalle shi tare da cewa
"A ina kuka haɗu da shi?"
"Yallaɓai unguwar mu ɗaya, yana haya ne a kusa da gidan mahaifina."
"Ko a cikin fira bai taɓa fada maka sunan ƙauyensu ba?"
"Bai taɓa sanar da ni ba sai dai idan zai tafi sai na ji yana cewa zai je ƙauye."
Shiru ya yi tare da yin nazari kafin ya ce,
"Ya taɓa fadin sunan amma wallahi na mance sunan ƙauye na su, yallaɓai dan Allah ka yarda da magana ta wallahi zaman unguwa daya ne kawai ya haɗa mu amma sam ba na da wata alaƙa da shi."
Jinjina kai inspector ya yi tare da cewa
"Shikenan zamu tafi idan da buƙatar dawowarmu za mu dawo."
Manajan ya masu godiya tare da cewa.
"In sha Allah yallaɓai da zarar ya dawo garin nan ni da kaina zan kirawo ku na sanar da ku."
Inspector ya masu gargadi cewa ka da sanar da shi ko ya dawo, saboda hakan zai iya sakawa ya gudu.
Nan suka amince da bukatar shi.
Daga nan suka wuce suka nufi motarsu tare da barin wajen.
Lokacin da D.P.O ke sanar wa Ajmal zancen cewa abokan sana'arsa ba wanda ya san garin, ya bari nan kwanaki shida zai dawo za su kama shi.
Cikin ɓacin rai ya fara magana yana cewa.
"Ba zan iya jira ba D.P.O."
"Ka yi hakuri yallaɓai tsawon watanni tara da kwanaki aka dauka ba tare da sanin haka ba, tsawon kwanaki biyar ne kawai ba za ka iya jira ba."
Shiru ya yi tare da cewa
"Shikenan Allah ya kai mu."
"Ameen yallaɓai."
Sallama ya masa tare da kashe wayar.
A ranar ne aka sallami Umman Amatullah daga asibiti, inda ya Munnir ya dauke su ya kai su gida.
Mutane da yawa ne suka haɗu a club ana cashewa ciki har da Hafsat, da misalin ƙarfe goma sha biyu na dare ne. Hafsat ta tashi daga cikin club ɗin ta nufi ɗakin da sauran ƙawayenta suke. Wasu na kwance suna barci wasu na shan kwalbar Benelin. Kwalbar giya ta dauko daga cikin fridge ɗin ta buɗe ta zuba a kofi za ta fara sha kenan sai ta ga kamar mutun na kallonta, juyawa ta yi da sauri dan ganin wane ne.
Ba kawo ba ne illa Munnir yana tsaye ya rungume hannayensa biyu yana kallonta. Miƙewa ta yi da sauri tare da sakin kwalbar giyar da ke hannunta ya fadi ya fashe.
Juyawa ya yi ya bar wajen ya yin da ta bi bayansa tana kiran sunansa, ko juyawa bai yi ba ya ja motarsa ya bar wajen.
Mamaki take me ya kawo shi nan? Kuma ta yaya ya san cewa ba ta gida? Shin ya fara yawon club ne ko kuma yana bibiyar lamuranta ne? Ga shi yanzu zai san tana shan giya, da iyaka dai ya san tana shaye-shaye na maganin maran yara bai san tana shan giya da shisha ba. Ga shi yau ya kama ta da kwalbar giya tana budewa.
Wa ya san ya zasu kare tana kananan shaye-shayen bai kula ta ba ya tsane ta ina ga yanzu da ya san cewa tana shan giya.
Hannu ta ɗora akai kamar za ta yi ihu.
A safiyar ranar ne aka wayi gari jaririn Amatullah ya tashi da zafin jiki, tunda iya ta zo masa wanka ta ke cewa.
"Amatullah ya na ji jikin babyn da zafi?"
Ita dai Amatullah ba ta ma sani ba, dan haka ta ce,
"Iya zafi kuma?"
"Amatullah kenan? Yanzu baki san cewa jikin shi da zafi ba? Ko da yake ba ki damu da yaron ba ne ko?"
Sunkuyar da kai kasa ta yi ba tare da ta yi magana ba.
Bayan tayi ta masa wanka ta shirya shi ne ta haɗawa Amatullah ruwan wanka ta taimaka mata ta yi sannan fita zuwa part ɗin su Ammi.
A babban falon ta yi sallama inda ta samu Ammi ta fito daga falonta za ta nufi falon Dad.
Iya ta gaishe ta ta amsa mata tare da tambayarta su Amatullah da Baby.
Nan iya ke sanar da ita cewar bayan ba lafiya jikinsa da zafi.
"Subhanahi! To gani nan zuwa yanzu bari na sanarwa Alhaji."
Cikin hanzarin ta nufi falon Dad, yadda ta shiga ne ya saka Dad da ke waya cire wayar a kunnensa tare da katse kiran wayar ya yana tamabayarta abunda ke faruwa.
Cikin yanayi na ɗan damuwa ta fara magana.
"Alhaji wannan babyn ne ba lafiya."
"Subhanahi me ya same shi?."
"Ban sani ba yanzu Iya da ke kula da su take sanar mani."
"Okay to ba damuwa su shirya sai Ahmad ya kai su asibiti."
Jinjina kai ta yi tare da cewa
"Okay hakan za'ayi bari kawai na shiga na duba su sai na saka Ahmad ɗin ya kai su, daga nan ma sai a masa alluran riga kafi dan na ga kamar ba'a masa ba."
"Duk abinda ya dace sai a masa, sai ki fadawa Ahamd din ya samu Doct da kansa ya masa bayanin ni ne na turo su."
Daga nan ta fita zuwa ɓangaren da Amatullah take.
Da sallama ta shiga dakin da Amatullah take, lokacin Amatullah ta shirya cikin riga da zani ta atamfa.
Gaida Ammi ta yi cikin girmamawa ta amsa mata cikin fara'a da walwala.
Daidai lokacin Iya ta kawo mata kakkuaran shayi da biredi sai soyayyen ƙwai.
Matsa mata ta yi akan ta sha da zafinsa, haka ta zauna tana sha, Ammi ta lura da yadda ƙirjinta ya cika gan kamar an hura balon-balon. Kallon Iya Ammi tayi tare da tambayarta ko tana shayar da babyn nono ne dan ta ga sun cika.
Dariya Iya ta yi tare da cewa
"Har yanzu ba ta taɓa bashi ya sha ba sai dai madara, nima na lura da yadda suka cika har na mata magana ko za ta bashi amma ta nuna ba za ta bashi ba."
"Okay shikenan. Yanzu ki gama yin breakfast ki fito Ahmad zai kai ki hospital har office ɗin Doctor, ki sanar da shi cewa na ce ya duba bayan sosai."
Jinjina kai Amatullah ta yi tare da yin godiya.
Daga nan ne ta fita ta bar ɗakin.
Ammi ta kira Ahmad ta sanar da shi inda zai kai Amatullah, dan haka ya ya zauna zaman jiran fitowarta
Bayan kamar mintuna goma ta kammala shiryawa ne sai Iya ta faɗa mata cewa ta goya babyn sun tafi.
Nan ta dauka baby da niyyar goyawa ta kasa, tura baki ta yi tare da cewa.
"Iya ni fa ban iya goyo ba."
Dariya Iya ta yi tare da cewa
"Kamar ta ba ki iya goyo ba Amatullah."
"Ina ɗaukar yara a maƙotanmu amma bana son goyo, kuma kin ga babyn ya yi ƙarami bana ma iya riƙe shi da kyau."
Dariya Iya ta dinga mata ta ce,
"Ai ko dole ki so goyo kuma ki koyi yadda za ki dinga goyo."
Tashi ta yi ta goya mata babyn tana cewa.
"Akwai sanyi a garin shi ya sa na goya maki shi."
Bayan an goya mata babyn ne ta sanya hijabinta tare da flat shoe ra nufi hanyar fita tana yiwa Iya sallama.
Tana fita ta daga part ɗin ta hangi Ahmad yana jiranta. Tana ƙarsawa ta masa sallama.
"Assalamu alaikum."
"Wa'alaiki salam"
"Ina kwana Ya Ahmad."
Murmushi ya yi tare da cewa.
"Lafiya lau Amatulla, ya Baby."
"Tana lafiya."
"Ba fa lafiya ba tunda an ce na kai ku wajen likita."
Murmushi kawai ta yi.
"Ina babyn na ga ke kaɗai ce."
"Yana baya na goya shi."
"Okay amma da kin sauke shi tunda mota za mu shiga."
"Ka da ka damu zan iya zama da goyo."
"Ba za ki takura ba?"
Murmushi ta yi tare da girgiza masa kai.
Zuba mata idani ya yi yana kallonta, shi ne mutum na farko da ya fahimci ciwon da ke cikin zuciyarta, ba abinda yake hangowa a cikin ƙwayar idanunta sai tsananin damuwa. Murmushi kawai take a kan fuskarta yayin da baƙin ciki ne a cikin zuciyarta, tana kokarin ɓoye damuwarta ne kawai dan kada wadanda ke tare da ita su fahimci halin da take ciki.
Girgiza kai kawai ya yi tare da yi mata addu'a Allah ya kawo mata mafita, dan ya fahimci ƙunar da take ji a cikin ƙwayar idanunta.
Bude mata gaban motar ya yi ta shiga ta zauna ya ja motar tare da yin horn security dake bakin gate ya bude masa gate ya fice.
A ƙofar asibitin ya yi parking ya sanar da ita cewa zai je ya karɓo saƙo ya dawo yanzu.
Waya ya kira ya yi wa Doctor bayanin cewa sun iso, ya ce yana office yana jiransu.
Bayan sun isa office ɗin Doctor ne Ahmad ya gaida Doctor sannan ya ce zai je ya karɓo saƙo ya dawo. Nan ya barta yayin da Doctor Samuel ƙwararren likitan yara ya karbi babyn daga bayan Amatulla.
Yayi duk dube-dube da binciken da zai yi bai ga wata matsala a tattare da babyn ba, ya saka an masu alluran riga kafi ne ya basu magunguna.
Bayan ta kammala abinda zai masu ne ya hada mata magungan.
Fita ta yi waje ko Allah zai sa ta ga Ahmad ya dawo. Sama da mintuna talatin tana jiransa bai dawo ba. Hakan ya saka ta dana fara takowa ta fito daga cikin asibitin.
Ta gaji ga shi ba ta san unguwar ba ballantana gidan.
A hankali ta fara takawa tana rungume da babyn a hannunta.
Wata mota ce baƙa mai baƙin gilashi ta zo ya tsaya a gabanta, ba ta ganin mutanen da ke cikin motar.
Daga cikin motar kuwa maza uku ne a ciki, wanda ke zaune gefen Direba ne ya ciro wayarsa ya duba photon Amatullah ya tabbatar ita ce kafin ya kalli wanda ke baya ya ce,
"Mu je."
Buɗe murfin motar suka yi suka fito tare da nufar Amatulla.
Tana rungume da babyn ta zuba masu idani.
Wuƙa ɗaya daga cikinsu ya nuna mata tare da cewa
"Ke Amatullah ki kawo jaririn da ke hannunki mu tafi mu barki da ranki, idan kuma kika mana taurin kai yanzu zan huda cikinki da wukar nan na kashe ki kuma mu tafi da babyn zaɓi ya rage naki."
Idanunta ne suka cika da ƙwalla ta waiga gabanta da bayanta ba kowa a kan hanyar ta cije baki tare da rintse idanunta.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
🤦♀️ *YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
Ban yarda a karanta mani shi a youtube ko a maida shi audio ba tare da izinina ba.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Page4️⃣7️⃣
Idanuwan ne suka cika da ƙwalla ta waiga gabanta da bayanta ba kowa a kan hanyar ta cije baki tare da rintse idanunta.
Duk da cewar wannan babyn tana kallonsa shi ne matsalar ta, da har ta bar iyayenta. Amma ba ta jin za ta iya ba su yaron nan, domin daga ganinsu ba mutanen ƙwarai ba ne cutar da shi za su yi.
Hannu ya miƙa mata alamar ta ba shi babyn.
Ganin dukkansu sun saka ta gaba ne ya sa ta juya baya tare da ɗiba a guje, ganin haka ya sa suka bi bayanta suna binta a guje suma.
Gudun da take yi ita kanta ba ta san ta iya yinsa ba, ga shi ta gaji sosai dan tun fitowar yaron nan daga cikin cikinta jikinta har yau bai koma daidai ba.
Bayan dogon gudun da suka yi ne ta har ta gaji ta faɗi a wajen daidai lokacin da motar Ahmad ke ƙarasowa.
Dama ya hango sanda ta ke gudu wadannan suna binta a baya yayin da direba motarsu shi ma ya biyo bayanta.
Ganin yadda Ahmad ya fito ne yana kiran sunanta ya sa suka gudu ɗaya daga cikinsu ne cewa.
"Wannan fa jami'i ne mu gudu."
Da hanzari suka shiga cikin motar ta su, yayin da Ahmad ya ke ƙoƙarin taimakawa Amatulla ta tashi, bayan ya karbi jaririn da ke hannunta.
Bayan ta miƙe ne Ahmad ya ciro bindigarsa cikin rashin sa'a motarsu
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 51