Share this page
ya amsa sallamar tare da cewa. "Barka da warhaka yallaɓai." Ajmal ya ce "Yauwa barka dai ya aiki?" "Alhamdulillahi" "Ma sha Allah an kama yarinyar ne?" "A'a bamu kama ta ba amma in sha Allah mun..." Bai jira me zai ce ba ya katse kiran wayar, dan ya gaji da sauraren uzurirrika da suke kawo masa. Dubansa ya maida ga Amatullah sannan ya ce. "Ka da ki sake yin ganganicin raba uba da ɗansa." Dubansa ya maida ga Abdallah da ke kwance yana barci murmushi ya yi tare da ƙarasawa wajen gadon ya sunkuya, sunbatarta ya yi a goshi sannan ya miƙe ya ƙarasa gaban Amatullah. "Ki shirya da karfe biyar na yamma za mu je ki zaɓi wayar da kike so, kin ga idan kina da waya za ki rage zaman kadaici da kewa, dan na san wayar za ta ɗebe maki kewa ne. Kai ta gyaɗa ba tare da ta ce komai ba, daga nan ya fita daga ɗakin. Shiru ta yi tana tunani dan gaskiya ita ma a yanzu ba ta jin za ta iya rabuwa da ɗan ta, da a baya ne lokacin da ta ƙi shayar da shi nono za ta iya rabuwa da shi, amam a yanzu da take shayar da shi sai take jin sa kamar wani sashe daga jikinta, dan gaskiya ba za ta iya nesa da shi ba. Ajmal na fita daga ɗakin daidai lokacin da Nasreen ke dawowa gidan, tana shigowa falo duka haɗa Idanu tana riƙe da Makulkin motarta da wayarta. Gyalenta na rataye a gefen kafaɗarta. Mamaki yake yi dan shi kam bai ma san cewa ba ta gudan ba dan a tunaninsa tana cikin ɗakinta. Ɗauke idanunsa ya yi ya nufi ɓangaren Amminsa. Bin bayansa ta yi da kallo sannan ta kalli ɗakin da ya fito, mamaki take to me ya kai shi ɗakin baƙi. Tunawa da ta yi da Amatullah ya sa ta nufi ɗakin kai tsaye. Banka ƙofar ta yi da karfi sannan ta bar ƙofar a buɗe. Da sauri Amatullah ta tashi tsaye ganin yadda ta bango ƙoafar ya sa ta tsorata. Cikin takun isa da gadara ta ƙarasa kusa da Amatullah. Kallonta ta yi sama da kasa sannan ta yamutse fusakrta ta ce. "Ke!" Ko kallonta Amatullah ba ta yi ba ballantana ta amsa mata. "Uban me ke tsakanin ki da mijina me ya zo yi nan ɗakin?" Ba tare da ta kalle ta ba ta fara magana. "Ai mijinki shi ya fi dacewa ki tambaya ba ni ba, dan ni ma ganinsa ne yi ban gayyace shi ba." Mamaki ya kama Nasreen dan ba ta taɓa tunanin haka yarinyar take ba. "Ke ni sa'ar ki ce da za ki faɗa mani maganar da ta zo bakinki?" "Idan ke ba Sa'a ta ba ce to ya kamata ki ja girmanki, dan idan babba baya son raini riƙe girmansa yake, dan mutunci madara ce idan ta zube ba'a kwashe ta duka." Amatullah ta yi maganar tana kallon Nasreen. Nasreen da ranta ya gama ɓaci ne ta ce. "Ke wallahi idan har ba ki iya bakinki ba zan gaggaura maki mari a wajen nan, na yi maganin rashin kunyar ki." Dariya ta yi tare da cewa "Aunty Nasreen ka da ki gwada dan wallahi ba zai maki daɗi ba, dan idan har Mallam bai ji kunyar hawa jaki ba shi kuma jaki ba zai ji kunyar kayar da shi ba duk farin gemunsa." Mamaki ya gama kama Nasreen ta ce. "Ƴar gidan uban waye ke, wace ce ke, me kike da shi, me kike taƙama da shi?" Amatullah ta buɗe baki da niyyar yin magana kenan sai ta hangi Ajmal na ƙarasowa ɗakin, ya fito daga ɓangaren Ammi sai ya hangi ƙofar a buɗe da kuma Nasreen ta juya masa baya. Jin Amatullah ta yi shiru ne ya sa ta cewa. "Ina tanabayrki kin yi shiru ƙaramar mara kunya kawai 'yar iska karuwa." Idanun Amatullah suka Kada suka yi ja, dan a rayuwata ta tsani a kira ta da kalmar karuwa, lura da yanyinta ya sa Nasreen Murmushi tare da cewa. "Ko a cikin ƙaruwai ma ke kina da lasisi dan ga ribar nan kin samu ɗan da kika..." Jin yadda aka finciko hannunta ne ya sa sauran maganar maƙalewa a bakinta. Ajmal ne ta janyo ta suka fita ya rufe kofar, bai sake hannunta ba har suka haura upstairs. Bedroom ɗin ta ta buɗe suka shiga ya hankaɗa ta a kan gado, ɗora ƙafarsa ya yi akan gadon tare da nuna ta da yatsarsa manuniya, alamar kashedi yake mata. "Na farko kuma na ƙarshe zan maki gargaɗi ki fita daga harkar yarinyar nan, ba ruwanki da ita, ba zamanki take ba kuma ba tare maki komai ba. Akan me za ki bi ta har ɗaki da cin zarafi? Ka da ki sake kiranta da karuwa idan ba haka ba wallahi sai kin yi mamakin abinda zan maki." "Yanzu akan ta ne kake Mani ihu haka? Ko da ke ban yi mamaki ba saboda tana baka kanta yadda kake so ko? Hakan ya saka ka dawo da ita kusa da kai yadda za ku cigaba da harkokinku ko? To asirinku na dab da tonuwa." "Ke ba ki ji kunyar fadar haka ba? Idan ma hakan ne da gaske ke ce kika bani lasisin da na nake bin wata. Dan haka ya na maki gargadi a kan yarinyar nan kin gane ko?" Afusce ta mike tsaye tare da cewa. "Ba zan taɓa ganewa ba, akan waccan karuwa da kake fasiƙan..." Lafiyayyun tagwayen maruka guda biyu ya sauke mata, wanda sai ta ta ji jinta da ganinta sun kauce na dan daƙiƙu kafin ta dawo daidai. Kuka ta saka tare da cewa "ka mare ni?" "Matuƙar za ki cigaba da kira na fasiƙi to kaɗan na maki shashasha kawai." Daga nan ya fice daga ɗakin ransa a ɓace. Da misalin ƙarfe huɗu da rabi na yamma, bayan Ammi ta idar da sallar la'asar ta fito zuwa babban falon gidan. Amatullah ce ta fito sanye da doguwar riga ta atamfa, ta yi kyau sosai, duk da ba kwalliya ta yi ba man shafawa ne kawai sai powder. Tana riƙe da Abdallah hannunta, Ammi ta miƙa mata hannu alamar ta ba ta babyn. Durƙusawa ta yi ta mikawa Ammi shi sannan ta zauna a gabanta. "Amma tana kallon Abdallah tana Murmushi ta ce. "Mijin da na cefene sai bacci, kai wani irin ragon miji ne ba ka iya komai ba sai barci." Dubanta ta maida zuwa ga Amatullah ta ce "Ajmal ya ce za ku tafi ki zaɓi wayar da kike so ko?" Kai ta jinjina tare da cewa. "Eh Ammi." "Okay to ba damuwa daga nan dai ban yarda ku tafi wani waje ba ku dawo gida, yamma ta yi ka da magrib ya maku a wajen." "To Ammi." Daga nan ba ta sake magana shiru ne ya biyo baya. Nihal ce ta fito daga dakinta ta nufo babban falon, kallo ɗaya ta yi wa Amatullah ta ɗauke kai. "Barka da hutawa Ammi." "Hauwa Barka dai Nihal, kin fito?" "Eh Ammi." Ta faɗa tare da zama a daya daga cikin kujerun da ke falon. Ammi ta cigaba da wasa da Abdallah tana tsokarnarsa kamar wani babba. Biyar da mintinan biyar suka jiyo ƙamshin turaren Ajmal tare da takun takalminsa. Nihal ce ta juya tana kallonsa. Sanye yake cikin ƙananan kaya ya yi kyau sosai. Da sallama ya ƙaraso wajen inda suka amsa masa dukkansu. "Barkanku da hutawa." Ammi ce ta amsa da "Yauwa ka fito?" "Eh Ammi." Kallon Amatullah ya yi tare da cewa. "Madam za mu iya zuwa yanzu?" Ba tare da ta kalle shi ba ta tashi ta bar wajen ta nufi ɗakinta. Mamaki ya kama Nihal 'Wai Madam ko zasu iya tafiya to gidan uwar waye za su tafi oho.' Amatullah ce ta fito sanye da hijabi ta kalli Ammi ta ce. "Amma sai mun dawo." "To shi Abdallah ba da shi za ki tafi ba ne?" "Eh Ammi yana daɗewa yana barci, har mu dawo na san ba zai farka ba." Ajmal ne ya ce. "Ka da da ya farka ya fara kuka, dan ba ki san lokacin da zai farka ba." Kafin ta yi magana ya karɓi Abdallah daga hannun Ammi ya sannan ya cewa Ammi. "Sai mun dawo." Saka kai ya yi ya nufi hanyar fita. Sallama ba yi wa Ammi sannan ta nufi kofar fita. Ahmad na hangensu ya taso da hannu Ajmal ya dakatar da shi ta hanyar ɗaga masa hannu. Hakan ya saka sauran bodyguards ɗinsa da suka yi niyyar zuwa suka koma, dan hakan alama ce da ke nuna masu shi kaɗai yake son fita. Sai da suka ƙarasa gaban wata danƙareriyar mota sannan ya tsaya tare da buɗe mata gaban motar. Shiga ta yi ta zauna wajen mai zaman banza. Miƙa mata babyn ya yi sannan ya zagaya ya zauna mazaunin direba, key ya yi wa motar ya bar gidan bayan mai security sun bude masa gate . Daidai kwanar da zai fita daga layin sai ga motar Nasreen ta danno kai,ganin Ajmal ya fita tare da Amatullah ne ya saka ta juya akalar motar ta ta bi bayansa. Hakan ya daka Ajmal rage gudun motarsa dan ya tabbatar da binsu take. Hakan ya saka ita ma ta rage gudun motarta, hakan ya tabbatar masa da bin bayansa take, dan ya na lura da ita ta madubin motar. Murmushin gefen baki ya yi tare da jinjina kansa. Wajen siyar da waya suka nufa inda ya ce ta zabi wacce take so, ita dai ta ce ba ta da zaɓi kowacce ta samu tana so. Hakan ya saka ya siya mata iphone 16 pro max, ya siye mata sim. Fitowa suka yi suka nufi wajen motar inda ya hango motar Nasreen daga nesa, yana rike da babyn da kuma leda wayar. Bayan ta shiga ne ya miƙa mata, sannan ya zagaya mazauninsa ya shiga. Tada motar ya yi suka bar wajen. Ganin Nasreen na biye da shi ne ya saka shi tabbatar da lallai zarginsa take, jinjina kai ya yi yana mai magana a zuciyarsa. 'Lallai sai na tabbatar maki da zargin da kike Maniw gaskiya ne.' Guest house din sa ya nufa da ita, ita Amatullah ba ta kula sosai ba dan ba ta gama sanin garin ba, sai da ta hangi kwanar da za ta sada ta da guest house din. Kallonsa ta yi kafin ta yi magana ne sai ta ga har sun ƙaraso, security sun bude masa gate ya shiga. Gefe daga can nesa Nasreen ta juya motarta tana driving tana kuka. Amatullah ta kalli Ajmal tare da cewa. "Me ya saka ka kawo ni nan? Ammi ta ce mu koma gida da wuri." "Abu zan ɗauka a gidan shi ya sa." "To ka tafi kai kaɗai ba inda zan shiga." "Ashe ko za ki kwana a nan, dan sai kin shigo ne zan iya fitowa." Daga nan ta saka kai a wuce bayan ya dauki Abdallah. Ba ta da wani zabi ta bi bayansa ba don tana so ba. Suna shiga ya samu waje ya zauna akan kujerar mai zaman mutum uku. Nafeesat ce ta nufi hotel ɗin. Tana fita jami'an dake saka ido suna kula da shiga da ficen mutane, suna ganin Nafeesat suka gane ta. Dan haka suka nufa ta kai tsaye nun mata ID card dinsu suka yi, cikin tashin hankali ta ce . "To lafiya me na yi?" Kwantar da hankalinki, akwai wata tambayar da zan maki, da zaran kin amsa mana wasu tambayoyi za ki yi sai mu sallame ki." A mota suka saka ta suka nufi ofishinsu da ita. Bayan sun isa ne suka kai ta Ofishin DP0, nan ya nuna mata wani photo da suke tafe za su shiga hotel ita da Hafsat. "Wace ce wannan da kike tare da ita?" "Ƙawata ce." "Ina za mu same ta yanzu?" "Lafiya yallaɓai ni ban gane ba me muka aikata?" "Ba abinda kuka yi ki bamu adireshin gidansu." B tare da wani tunani ba ta basu adireshin gidansu Hafsat. Nan ya tura jami'ai gidansu Hafsat dan a taho da ita. Sannan ya bada umurnin a ɗauko masa INDAKUƊINKA. *Daga alƙalamin*✍️ Zainab Abdullahi KNT (Maman Ihsan) 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z 🤦‍♀️ *'YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) *NA* Zainab Abdullahi KNT (Maman Ihsan) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. Ban yarda a karanta mani shi a youtube ko a maida shi audio ba tare da izinina ba. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHIM* Page6️⃣3️⃣ Nan ya tura jami'ai gidansu Hafsat dan a taho da ita. Sannan ya bada umurnin a ɗauko masa INDAKUƊINKA. Hafsat komawa gida ta yi inda ta tarar Mamanta ba ta nan a falo, kai tsaye ta nufi bedroom ɗin Maman nan ma ta tarar ba ta ciki kuma ba alamar mutum a toilet. Fitowa ta yi harabar gidan tana tambayar mai gadin gidan ko Mamanta ta fita ne. Nan ya ke sanar da ita cewa ta fita amma da alama ba ta yi nisa ba dan ba ta fita da Direba ba. Ƙarar bubbuga gate suka ji inda mai gadin gidan ya nufi gate ɗin da sauri ya buɗe. Ɗaya daga cikin jami'an ne ya kalli maigadin tare da mika masa hannu suka gaisa. "Hafsat muke tambaya ko tana ciki?" "Eh yallaɓai Allah dai ya sa lafiya?" "Lafiya lau tambaya zamu yi mata." "To bari na sanar da ita." Yanda ya barta tsaye nan ya same ta, Kallonta ya yi tare da cewa. "Hajiya kina da baƙi a waje." Da mamaki ta kalle shi tare da cewa. "Su waye?" 'Yan sanda ne fa wai tambaya suka zo maki." Take sai gabanta ya faɗi ta lalle shi tare da cewa. "Ka ce ba Hacsat a gidan nan." "Ai Hajiya na ce masu kina nan cik..." Mari ta sauke masa a fuska tare da cewa. "Ba ka da hankali ne da za ka ga 'yan sanda ka ce ina nan?" "To Hajiya sun ce tambaya za su maki kuma idan kina da gaskiya ai ba za ki damu ..." Ƙarar buga kofar ne ya saka ta ƙarasawa wajen kofar da ba ta da wani zabi idan ba haka ba za su iya shigowa. "Ke ce Hafsat?" "Eh lafiya?" "Muna gayyatar ki ofishinmu dan ki amsa mana wasu tambayoyi." "Yanzu Maman ba ta nan ku sanar da ni..." "Ka da ki damu mu tafi kawai." "Ba yadda ta iya dole ta bisu a motar su suka tafi da ita. Ajmal na shiga falon ya samu wuri ya zauna kan kujerar mai zaman mutum uku, wayarsa ya ciro daga cikin aljihunsa ya fara danne-danne a wayar. Mamaki ne ya kama Amatullah dan haka ta ce, "Ka ce abu za ka ɗauka to ka ɗauka mu tafi mana ka ga yamma ne ba jimawa magrib za ta yi, sannan Ammi ta ce mu dawo da wuri." Wasa ya cigaba da yi wa Abdallah sannan ya ce. "Ni ma ban yi niyyar zuwa nan ba, kawai dai hakan ta kama, dan na tabbatar da zargin da ake mani ne." "Ban gane me kake nufi ba wani zargi?" Murmushi ya yi tare da cewa. "Ki manta kawai." "Dan Allah ka tashi mu tafi." "Dan Allah ki ƙara hakuri, wato ina da wata ɗabi'a ce idan aka ce na yi abu alhalin ban yi ba to kuwa ni kan ji ba daɗi har sai na aikata abin nan kafin na ji sanyi a raina." Ɓangaren Hafsat kuwa tunda aka kai ta Ofishin DP0 ta ga INDAKUƊINKA gabanta ya tsananta bugawa, tsuke fuska ta yi tare da kau da kanta ta maida dubanta ga Nafeesat tana mamakin zuwanta. DPO ya kalli INDAKUƊINKA sannan ya ce. "Ita ce ta baka aikin?" "Eh ita ce ranka ya daɗe." Ya yi maganar yana kallon Hafsat. Cikin burin kunya ta fara magana tana cewa. "Wa kake magana ka sanni ne, ka da ka yi mani sharri." "Wallahi yallaɓai ita ce, da kanta ta bani photon yarinyar wallahi karya take ita ce." "Wai wata yarinya kake magana ni ban san yarinyar ba." Wayarsa ya ciro ya nuno photon Amatullah ya nuna mata, ta dage sam bata san Amatullah ba. DPO ya nuna wa Nafeesat photon ya ce. "Kun san ta?" Kai ta gyaɗa tare da cewa "Eh mun san ta yallaɓai, amma yanzu ba mu san inda take ba." "Me ye alaƙar ku da ita?" Nuna Hafsat ta yi tare da cewa. "Ƙawar Hafsat ce a dalilin Hafsat na san ta, ita ta kawo ta cikinmu." Kallonsa ya maida zuwa ga Hafsat sannan ya ce. "An ce ke kika kawo ta sannan ki ce ba ki san ta ba?" Wayarsa ya ciro a aljihu ya kira wayar Ajmal. Ajmal da ke zauna Amatullah na tsaye a akansa ne ya ga wayarsa na ruri, ganin DPO ne ya sa shi dagawa da sauri tare da cewa. "Assalamu alaikum" Daga can bangaren DPO ya ce. "Wa'alaika salam." "An samu yarinyar ne`` "Eh ga ta nan amma tana musun cewa ba ita ba ce kuma ba ta san Yarinyar ba." "Bari na kira video call." Daga nan ya katse kiran wayar kafin ya kira shi video call. Janyo Amatullah ya yi ta zauna kusa da shi, tana shirin mik'ewa ya zaunar da ita tare da riƙe hannunta. Kallon DPO ya yi tare da cewa. "Mu ga yarinyar." DPO ya saita fuskar wayar zuwa ga Hafsat bayan ya tashi daga kujerarsa ya dawo kusa da ita. Kallonsa ta yi cike da mamaki, dan a tunaninta wani ne dai can aka samu wanda ba kowa ba, amma kallo ɗaya da ta yi wa Ajmal ta san cewa shi na daban ne ba irin gamagarin maza ba ne. Mugun kallon mai cike da tsana da ta ga yana mata ne ya sa ta sunkuyar da kai. Ajmal ne ya matso kusa da Amatullah har jikinsu na gugan na juna ya ce. "Kalla ki gani ko kin san ta?" Kallon wayar ta yi lokacin da ita ma Hafsat ta kalli wayar. A zabure Hafsat ta miƙe tare da cewa. "Ke!" Ta buɗe baki da niyyar yin wata magana sai Kuma ta fasa ta yi shiru, fuskarta ɗauke da zalllar mamaki take kallon Amatullah. Ajmal ne ya kalli Amatullah tare da cewa. "Kin san ta ko?" Shiru ta yi ba ta ce komai ba, inda ya cigaba da cewa. "Ita ce ta bawa INDAKUƊINKA kudi akan ya samu wanda zai lalata rayuwarki, mene ya alaƙarki da ita da har ta yi maki wannnan aikin, dan gaskiya lamarin babba ne, ƙiyayyar ta yi yawa. Ita dai Amatullah banza kuka ba abinda take yi a sai kuka. Ita ko Hafsat mamaki duk ya bi ya dabaibaye ta a garin yaya Amatullah ta zama haka haka? Sannan ya ta yi ta hadu da wannan babban mutum da ko a mafarki ba ta taɓa tunanin cewa zai iya kallon Amatullah ba, yanzu ga su a tare ina suka haɗu Kum ya aka yi aka bankaɗo sierrin dake rufe, wanda bayan ita da INDAKUƊINKA to ya aka yi suka gano gaskiyar lamari? Ita a tunaninta Amatullah na can a wulaƙance take rayuwa na ƙasƙance tamkar mabaraciya sai ga shi ta ganta tamkar wata sarauniya. Sunkuyar da kanta ta yi cike da jin kunya, dan ba za ta iya haɗa Idanu da Amatullah ba,dan wani kwarjini ta mata da yawa yau. Amatullah ta kalle ta tare da cewa. "Me na yi maki haka da zafi Aunty Hafsat? Me na tare maki a iya sani na da ke ban taɓa maki wani abu da ba daidai ba, hasalima ni ce nake cutar kaina saboda ke amma ki rasa abinda za ki saka Mani da shi sai ki sa a yi..." Kuka ne ya ci ƙarfi ya ta kasa cigaba da magana, saboda kukan da ƙarfinta take yi har cikin zuciyarta na mata zafi. Ajmal ne ya janyo ta jikinsa yana rarrashinnta, ɗan bubbuga bayanta alamar rarrashi. Kwantar da kanta ta yi a jikinsa ta cigaba da kukanta, Hafsat da Nafeesat sake baki suka yi suna kallon ikon Allah. Ya aka yi suka haɗu bayan wancan abun ya faru? Kuma ai dukkansu ba sa cikin hayyacinsu ta ina suka gane cewa wani abu ya faru da su? Ballantana su kasance tare a haka. Nafeesat Murmushi ne ɗauke a saman fuskarta dan dama ita fisabilillah take kaunar Amatullah, ganin yadda Ajmal ya ke rarrashinnta yana ɗan bubbuga bayanta da daya hannunsa sayar hannun na riƙe da babyn. Dama wayar ajiye ta ya yi a gabansa, kukan Amatullah ne ya ke ƙara tsananta idan ta tuno da yadda ta zauna da Hacsat da zuciya daya, sam ba ta taɓa tunanin cewa da biyu ta shigo rayuwarta ba, kuma ba ta zaci cewa za ta iya cutar da ita har haka ba,. Yanzu ga yaron da ta haifa nan an ɓata masa asalinsa. Kukanta ne ya fara rikita Ajmal nan da nan ya rikice, katse wayar ya yi inda ya cigaba da rarrashinnta. Tsagaitawa ta yi da kukan da take yi ƙamshin turarensa kawai take shaƙa, sai a lokacin ma ta tana da cewa nanne take a jikinsa, da sauri ta ture shi tare da ja da baya ta zame jikinta. Kiran sallar magrib aka yi dan haka ta kalle shi da sauri tare da cewa. "Mu tafi gida." Kallonta ya yi tare da cewa. "Tunda an kira sallar ki bari mu yi sallar tukunnah idan muka yi sallar sai mu tafi. Kafin ta ta yi magana har ya Ajiye Abdallah akan kujerar ya tashi. "Ki shiga daya daga cikin bedrooms ɗin nan kiyi alwala da sallah, nima yanzun masallaci zan tafi in sha Allah." Ba ta sake cewa komai ba ganin ya saka kai ya wuce. Ɗaya daga cikin bedrooms ɗin ta shiga bakinta ɗauke da sallama ta shiga. Tsayawa ta yi tana kallon ɗakin komai na more rayuwa an zuba a ciki ba abinda mutum zai buƙata. Cire hijabinta ta yi ta ajiye a saman gadon, sannan ta nufi toilet. Alwala ta ɗauro sannan ta fito,darduma ta gani a cikin drawer ta shimfida sannan ta gabatar da sallah. Bayan ta idar ne ta tsaya ta zauna tana azkar. Hawaye ne kawai ke sintiri a fuskarta idan ta tuna lokacin da take tare da Hafsat da abinda ta yi mata, sai ta tsananta kukan da take yi. Tana cikin haka kuwa sai Ajmal ya turo ƙofar ɗakin ya shigo bakinsa ɗauke da sallama. Amsawa ta yi tana zaune a saman sallaya. Ganin tana kuka ne ya ce. Ki daina kuka ka da ki damu za ta girbi abunda ta aikata, tunda ta shiga hannu yanzu. A can ofinshinn DPO kuwa bayan ajmal ya katse kiran wayar, ne ya saka aka kai Hafsat da da INDAKUƊINKA aka garƙame su, a daban-daban aka ajiye su ita wajen mata shi kuma wajen maza. Ita kuma Nafeesat sai aka sallame ta bayan an tabbatar da cewa ba ta da laifin komai ita. Gida ta wuce kasancewar magrib ta yi sannan da safe dole ne ta je gidansu Hafsat ta sanarwa Mamanta abinda ke faruwa da 'yarta. Wayar Ajmal ce ta yi kara, dubawa ya yi ya ga Ammi ce ke kiransa, ya san dalilin kiran nata, ba zai wuce saboda ya fito da Amatullah ba ne. Bai daga wayar ba ya kalli Amatullah tare da cewa "Tashi mu ci abinci sai mu tafi." Hawaye ne kawai ke bin fuskarta dan sai yanzu take kara jin ciwon abinda ya faru da ita, bayan ta gane wace ce sanadin shigarta wannan halin, ƙawarta wacce ta ce tana ƙaunarta kenan, ashe dama da ake cewa ciwon 'ya mace na 'ya mace ne dama ba haka ba ne?' Kuka take da takaici dan sosai abun ya mata zafi, ta ji bakin ciki sosai. Ganin ba ra da niyyar ta shi ne kuma ko ya ce ta tsaya ta ci abincin ba ci xa ta yi ba ya sa ya ja hannunta suka nufi kofar fita. A falo ta dauki Abdallah da har lokacin yana barci, suka nufi ƙoafar fita, anan suka yi kiciɓis da Ahmad. Mamaki ne ya kama shi ganin Ahmad alhalin shi bai fadawa kowa inda zai tafi ba, dan haka ya ce masa. "Ahmad me ka zo yi a nan?" "Yallaɓai Ammi ce ta ce na zo na ɗauko Amatullah." Shiru ya yi da jin zancensa wato Nasreen ce ta faɗa wa Ammi yana guest house din sa kenan. Wato shi ne hakankalin Ammi ya ƙi kwanciya ta kira shi a waya bai ɗaga ba shi ne ta turo Ahmad. Kallon Ahmad ya yi tare da cewa ka tafi ga mu nan zuwa. "Am sorry sir, ta ce ƙafata ƙafar Amatullah." "Kai Ahmad wa kake yi wa aiki ne?" "Kai ne yallaɓai." "Shi ne har zan baka umarni ba za ka bi ba? Yaushe raini ya shiga tsakanin mu ne?" "Ba haka ba ne yallaɓai a ƙarƙashin ka nake ba ƙarƙashin kowa ba, amma ina taya ka yi wa Mahaifiya biyayya ne." Ba abinda zai iya ce masa kuma dan haka ya nufi motar da Ahmad ya kawo ya bar nasa motar anan. Ahmad na gaba su nuna baya har lokacin ba ta daina kuka ba, Ahmad dai bai dan dalilin yin kukan ba, amma ya ga dai kukan ya yi yawa, da ya ga Boss dinsa na aikin rarrashi ne ya sa bai yi magana ba. Ajmal ya ajiye Abdallah a gefe ya maida hankali wajen rarrashin uwar Abdallah. Rintse

Chapter 24 of 51