Share this page
kowa a tsakar gidan, don haka ta nufi d'akinta ta kwantar da Khalifa Wanda har lokacin barci yake yi hankalinsa kwance. Muryar Umma ta ji tana cew ta kawo Khalifa ta masa wanka, Hakan ya saka ta d'auke shi ta fita da shi ta kaiwa Umma. Ledojin kazar ta duba kasancewar guda uku ne sai ta d'auki d'aya ta fita da biyu don kaiwa Umma na ta da na Abba, duk da ta ji tsaro a zuciyarta don Abba ya taba yi mata gargadi akan karbar abinci daga hannun saurayi irin haka. Bayan ya gama hada kayansa a jaka ne ya kira lambar wayar Amminsa, bugu niyu ta daga cike da fara'a ta fara magana. "Assalamu alaikum rabin raina ya jikin naka?" ",Da sauki Ammina." "Ma Sha Allah." "Ammi wai me zan yi wa wancan tsohuwar ne take nema na?" Ita a tunaunta Umminta dake k'asar Qatar yake magana, don haka ta ce. "Mai yiwuwa ta yi kaewarka ne ka San ba ta ki a ce kullun kana tare da ita ba." Jin ba ta gane wacce yake magana ba ya sa shi cewa. "Ni da ba wani zuwa Adamawa nake yi ba ko kin manata ne?" Sai a lokacin ta ce. "Okay Marka kake nufi?" Duk maganar da suke yi cikin harshen larabci suke yin ta, don shi dama idan ya ce zai yi doguwar magana da hausa to sai an ji kwab'a, don har yanzu ba wani iya ta ya yi ba duk da yana junta Kuma yana mayarwa sai dai wani maganar tana masa tsauri wajen Maidawa. "To gaskiya ban San dalilin son ganinka da take yi ba, Dan ina kyautata zaton Dad d'inka ma bai sani ba, don yanzu daga part d'insa nake ya dai sanar dani sakon kakar taka amma ban San dalilin Kiran ka ba." "Ba komai gobe in Sha Allah zan bi jirgin k'arfe bakwai na safe." Fira suka d'an taba daga bisani suka yi sallama ya katse Kiran wayar, Jin ana kirayr kirayen sallar magrib ne ya saka shi tashi ya nufi bathroom dake cikin bedroom na d'akin hotel din da yake ciki. Bayan sallar isha'i ne bayan sun gama cin abinci dare daga Abba sai Umma a tsakar gidan. Dubanta ya yi tare da cewa. "Umman Amatullah dama wata shawara nake so muyi da ke." Jin haka ya saka ta tattara duk nutsuwarta zuwa gare shi, inda ya cigaba da cewa. "Yaron nan ne ya zo da zancen turo magabatansa wajena, akan maganar auren Amatullah." Umma ta jinjina kai tare da cewa. "Waye kenan Munnir ko Ajmal?" Kallonta ya yi tare da cewa. "Wani Ajmal Kuma?" "Ajmal mana uban d'anta." Hade rai ya yi tare da cewa. "Mata Kuma da karancin tunani wa ke maganar Ajmal, Munnir shi ne Wanda ya fara ganin ta ya zo ya yi sallama da ni ya nemi izinin zuwa zance wajenta na bashi dama, tun tana da mutunci ba yanzu ba, duk da halin da ta shiga na shaye-shaye da abunda ya faru ta yi ciki na kore yaron nan bai yanke kauna ba, da shi akan dinga Fadi tashin neman ta da wani ne ya ji labarin abunda ta aikata ya fasa aurenta kenan, amma bai hakura ba ya zauna zaman jiranta shekara d'aya, duk da ya ganata da yaro bai fasa aurenta ba to idan ba mu aura masa ita ba mun kyauata masa kenan?" "Gaskiya ba mu kyauata masa ba, sai dai ina tsoron abunda zai iya zuwa ya dawo ne, ka da su yi ta samun matsala akan abunda ya faru da ita don na ga alamar haka, ka ga idan uban yaron ne ya aure ta shikenan asiri ya rifu ke..." Abba ya d'aga mata hannu alamar dakatarwa kafin ya Dora da cewa. "Kul na ji kin kawo wannan maganar a cikin gidan nan, sanin kanki ne na Riga na yi alkawarin bawa aurenta ga Munnir, idan kin ga ba'a d'aura da shi ba sai dai idan shine y ce ya fasa, Kuma wallahi na ji matsala daga wajen yarinyar nan to ke zan bawa laifi, shi ya saka nake so ta yi baya-baya da shi ta rabu da shi." "Shikenan Mallam duk yadda ka ce haka za'ayi, Allah ya sa Hakan shine mafi alkhairi, sannan zancen ta rabu da Ajmal ka ga ba zai yiwu ba, saboda ga yaro a tsakaninsu, dole zai dinga waiwayar dansa ko kiranta a waya don Jin lafiyarsu." Jinjina kai ya yi alamar gamsuwa, kafin ya dora da cewa. "Yanzu shi so yake yi a saka masu ranar biki. Na ce zan yi shawara dake don Jin yadda zamu yi." "A gaskiya Mallama da an bari idan Amatullah ta yaye yaronta sannan ayi maganar aure, amma yanzu ga karamin goyo ta yaya zata je gidan aure da goyo alhalin ba shine uban yaron ba?" "To yanzu ya zamu yi?" "A bari ta yaye yaron kawai tunda yanzu watanninsa hudu da haihuwa, ka ga auren zai kai shekara d'aya nan gaba." Ta yi maganar tana jiran amsar da zai bayar. Ji ta yi yana cewa. "Gaskiya Amatullah ba za ta kai shekara d'aya a gidan nan ba." Shiru ya yi yana tunani kafin ya dora da cewa. "Nan da watanni goma ne zan saka na bikin auren ta da Munnir, kin ga zuwa lokacin yaron ya kai shekara d'aya da watanni biyu sai ta yaye shi." Umma ba ta so Hakan ba sai dai ba yadda ta iya dole ta bi umarnin Abba. K'walawa Amatullah kira Abba ya yi, ta amsa inda ta fito sanye da Riga da wando ba barci, a gabansu ta durkusa. "Ki kira Munnir a waya ki sanar da shi cewa zai iya turo magabatansa gobe." Gabanta ne ya yi muguwar fad'uwa, Wanda har sai da ta rintse idanunta, Jin ba ta yi magana ba Abba ya ce . "Ko baki ji me na ce maki ba ne?" Kai ta jinjina tare da cewa. "To Abba." Daga nan ta mike ta nufi d'akinta jiki a Sanya ye. Har za ta shiga sai ta ji muryar Abba ya sake kiranta, komawa ta yi ta durkusa a gabansu. "Yauwa Kuma ki sanar da shi cewa ka da ya boyewa iyayensa komai game da ke har yaron da kika haifa ya sanar da su. Idan sun amince shikenan idan ba su amince ba sai ya hakura." Da to ta amsa masa sannan ta tashi ta nufi d'akinta cikin wani irin yanayin da ta kasa gane kansa. *ADAMAWA* A airport ne ya ga Sudais yayan Nihal ya zo daukarsa, dama kafin ya taso sun yi waya, trolley d'insa Sudais ya saka a bayan motar, sannan ya zagayo ya zauna mazaunin direba yayin da Ajmal ke gefensa. Hanyar gida suka nufa inda Ajmal dai shiru ya yi duk fira da Sudais ke masa daga uhm sai a'a, shima Sudais din bai damu ba kasancewar ya san wayar Ajmal ba mutum ne Mai yawan magana ko sakin jiki da mutane ba. Kuma kusan sa'anni suke Dan watanni bakwai Sudais ya girmi Ajmal da shi, sai dai har yanzu bai sake wani aure ba tun bayan rasuwar matarsa da ta rasu wajen haihuwar farko, ita da d'an duka ba Wanda ya rayu. Sudais da ke driving ne ya d'an Kalli Ajmal tare da cewa. "Yau mun yi babban bak'o a garin, don rabonka da garin nan har na manta ba ka da kirki wallahi, ba ziyara sai dai sako, duk da haka muna godiya Allah ya Kara budi." Murmushin gefen baki ya yi tare da cewa. "Ba na samun lokaci ne shi ya saka ka San yanayin harkonina yau ina can gobe ina nan, wani lokacin ma ba na sanin inda zan kasance a gobe sai don lokaci d'aya za ka ga tafiyar gaggawar ta kama ni." "Haka ne mu dake likitoci ne kullun muna asibiti." Haka dai suke d'an taba fita har suka iso k'ofar gidan Hajiya Marka, horn ya yi Mai gadin ya bude masa gate, suka fito daga cikin motar, Sudais ya ciro trolley bag din Ajmal suka nufi cikin gidan. "Nihal dake jikin window tana hangesu ta yi saurin ta fesa turare, dama ta gama shiryawa tana jiran isowarsu ne. Da sallama suka shigo cikin falon inda Sudais ke gaba Ajmal na biye da shi a baya, Nihal da fitowarta kenan cike da farin ciki ta k'arasa tana cewa. "Oyoyo Ya Ajmal." "Rungume shi ta yi Wanda hakan ya saka Sudais jefa mata wani mugun Kallo, Ajmal bai ce komai ba sai zame ta da ya yi daga jikinsa ba tare da ya kalle ta ba. Bata rai ta yi cikin shagwaba ta ce. "Haba Ya Ajmal." Kallonta ya yi tare da mata alamar tambaya. "Ba kai ne ka share ni ba ina maka oyoyo ko kallona ballanata ka yi magana." "Ki yi hak'uri a gajiye nake." Daidai lokacin da Marka ta fito fuskarta d'auke da murmushi ta ce. "Oyoyo da mijina na kai na." Tana magana tana tafa hannaye, zama ya yi yayin da Nihal ta zauna gefensa, kan kujera Mai zaman mutum biyu. "Ina wuni na same ku lafiya?." Ya gaishe ta yana kallonta. "Lafiya lau Ajmal ya hanya ya mutanen gida ya iyali ya aiki?" Da lafiya ya amsa mata, Sudais ne ya kalle shi tare da cewa. "Muje na kai maka kayanka sai ka yi wanka ka fito mu ci abinci ko?" Ba tare da ya amsa ba ya tashi ya bi bayan Sudais zuwa d'akin da aka gyara masa sai kamshi d'akin yake yi. A falo kuwa Nihal sai farin ciki take yi tana cewa "Marka dan Allah kafin ya bar garin nan ki saka a tsayar da ranar aure na da shi." Murmushi Marka ta yi tare da cewa "Kada ki damu ai komai zai zo da sauki." "Marka dole na damu wallahi kina ganinsa nan yana da wiyar sha'ani ga shariya da mishkilancin tsiya, zaman da na yi a gidansu wallahi ba hanyar da ban bi ba wajen ganin na janyo hankalinsa, har aka kawo shegiyar da aka ce ya mata ciki a gidan ya fara kula ta ita da yaron ta amma ban ishe sa Kallo ba karshe ma sai suka shirya tafiya kasar Qaatar har da Amminsa Kuma ta San ina son sa sai ta yi kamar ba ta gani ba, da na ga zasu barni ni kadai ne sai na dawo nan na ce zan koma tunda ba shegiya nake ba." "Ki yi shiru ki zuba idanu ki ga yadda zamu Karke da shi, dole ya aure ki ko yana so ko baya so indai na isa da ubansa Kuma ni na haife shi." Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z 🤦‍♀️ *YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) Page8️⃣4️⃣ "Kiyi shiru ki zuba idanu ki ga yadda zamu Karke da shi, dole ya aure ki ko yana so ko baya so indai na isa da ubansa Kuma ni na haife shi. Murmushin Jin dad'i ta yi tare da kwanciya ta dora Kanta a Saman cinyar kakar. Shiga cikin d'akin suka yi yayin da Sudais ya fito ya bashi waje don ya yi wanka ya fito. Zama ya yi akan gadon sannan ya lalubo lambar wayar Ammi ya danna mata kira, bugu biyu ta daga ya sanar da ita ya iso yanzu, farin ciki ta yi tare da Sanya masa albarka, sannan ta mika wa Dad wayar suka gaisa shima albarka ya saka masa sannan suka yi sallama ya kashe Kiran wayar. Wayoyinsa ya ajiye Saman bedside drawer tare da cire tsadadden agogon hannunsa, kayan jikinsa ya fara ragewa sannan ya nufi k'ofar bathroom don yin wanka. Har ya nufi k'ofar bathroom din ya ji wayarsa na ringing, da kamar ba zai dawo ba sai Kuma ya dawo ya duba, ganin Amatullah cs Mai Kiran wayar ya saka ya zauna bisa gadon, kallon wayar yake yi yana tunani don ya San ba dabi'arta ba ce ta kira shi haka Nan kawai, sai dai idan shi ne ya kira ta, don haka sai ya yi tunanin akwai dalilin Kiran nasa. Har ta katse bai daga ba kafin daga bisani ya maida mata Kiran wayar. Bugu d'aya ta daga tare da yin sallama, amsa mata sallamar ya yi cikin sanyin muryarta ta gaishe shi. Madadin ya amsa mata gaisuwar sai Jin muryarsa ta yi yana cewa. "Me yake faruwa?" "Ba komai" Ta bashi amsa a takaice,sake tamabyarta ya sake yi a karo na biyu. "Meye matsalar?" "Ba komai na kira ka ne don na ji ya jikinka?" Murmushin gefen baki ya yi yana cewa "Ai tunda kika zo na ganki na ga yaro na sai na ji ciwon ma na neme shi na rasa, sai ya kasance kamar kune maganin cutar dake damuna. Shiru ta yi ba ta sake yin magana ba, ga ranta a cunkushe ta rasa abunda ke mata dad'i, tunda Abba ya yi maganar cewa ta kira Munnir ta sanar da shi ya turo magabatansa ta ji ranta a cunkushe, madadin ta kira Munnir sai ta kira Ajmal." "Naji yanayi na rashin jin dad'i a cikin muryarki, idan da abunda ke damunki ki sanar da ni." "Ba komai." Ta bashi amsa a takaice. "Ina yarona?" "Yana barci." "In Sha Allah gobe zan kira ku video call na sake ganinsa." "Ba za ka sake dawowa bane?" ",Na bar garin Ku." Da sauri ta Kalli wayar kamar shi ne take Kallo, tunani ta fara yi, a zuciyarta tana cewa. 'Dama tafiya za ka yi shi ne ko sanarwa ballantana mu yi sallama.' Kamar ya San abunda ke ranta ya ce "Tafiyar ce ba ta shiri ba shi ya sa na tafi." Dafe kansa ya yi don shi mutum ne da bai cika son yawan magana ba, dama ya gama waya da su Dad da Ammi, yanzu ga Amatullah sai ya ji kansa na neman masa ciwo, don haka ya ce mata zai kira ta anijima. Daga nan ya katse Kiran wayar ya tashi ya shiga bathroom don yin wanka. Yana shiga sai ga Nihal ta shigo d'akin bakinta d'auke da sallama, ganin bayan ciki ne ya saka ta gane cewa wanka ya shiga, madadin ta fita daga d'akin sai ta zauna Saman bedside drawer gefen wayoyinsa, d'auka ta yi ta ga da password a jiki, ta sake d'aukar dayar, itama haka, sai ta d'auki cikin ta ukun nan ma haka cikin takaici ta ajiye wayoyin. Tana nan zaune ya fito daga wanka yana d'aure ta towel a k'ugunsa, hannunsa rike da wani karamin towel yana goge gashin kansa, sakin baki ta yi tana kallonsa, faffaden k'irjinsa Wanda ke d'auke da kwantaccen gashin da suka kwanta luf luf a k'irjinsa har shainin suke yi kamar yadda suman kansa ke shainin, Sam bai kula da ita ba sai da ya k'arasa gaban mirror ne ya hango ta zaune sai kallonsa take yi. Tsuke fuskar ya yi tare da cewa. "Ke lafiya?" Sai a lokacin ta ji kunya ta d'auke idanunta daga kallonsa ta fara magana. "Am na ga ba ka fito be ne." "Akwai abunda zan maki ne?" Girgiza kai ta yi ba tare da ta yi magana ba. "To me ye na biyo ni." "To Ya Ajmal laifi ne don na biyo ka? Ga abinci can na shirya maka ko na kawo maka nan ne?" "No zan fito." Madadin ta fita sai ta zuba masa idanu kamar za ya cinye shi. " Ki fita zan saka kaya." Sai a lokacin ta daina kallonsa ta fita tare da rufe masa k'ofar .Tsuki ya ja yana bin bayanta da harara. Bangaren Amatullah kuwa tunda Suka gama waya da Ajmal ne ta zubawa wayar idanu, tana tunanin yadda za ta kira Munnir ta sanar da shi zancen da Abbanta ya sanar da ita. Ganin ba ta da yadda za ta yi ne ya saka ta Kiran wayarsa. Suna zaune a dinning table suna shirin fara cin abinci yayin da Mai aikinsu take service d'insa wayarsa ta yi ruri, yayin da Munnirat ke gefensa tana cin abinci ta Kalli wayar, ganin Sunan da ke kan wayar ne ya saka ta kalle shi tana sakin murmushi. Dagawa ya yi ya Kara a kunnensa yana cewa. "Hellow babyna ya kike?" Daga Dadinsa har Mummynsa kallonsa suke yi. Daga can bangaren cikin sanyin murya Amatullah ta gaishe shi, sannan ta dora da cewa. "Abbana ne ya ce na sanar maka wai ka turo magabatanka." Ihun farin ciki ya yi tare da cewa. "Kai gaskiya yau ina cikin farin ciki da ba zai misaltu ba masoyiya, yanzu zan sanarwa Dad d'ina." Ya yi maganar fuskarsa d'auke da murmushi,sai ya ji muryarsa tana cewa. "Ya ce kada ka boye masu komai game da ni ." "Kamar ya ya kenan?" "Ka fad'a masu gaskiya a baya na kasance ina shaye-shaye kuma ina da yaron da na haifa ba ta hanyar aure ba, ka da suji daga baya a samu matsala." "Kada ki damu wannan ba wata matsala ba ce ai ni zan aure ki Kuma na San da wannan zancen, amma duk da haka zan sanar da su kamar yadda kika ce. Sallama ta masa yana murmushi ya katse Kiran wayar. Yana ajiye wayar ya ji muryar Mum d'insa tana cewa. "Kai da wace ce kake waya?" Cikin nuna Jin dad'i ya fara magana. ",Mum wallahi yarinyar da nake son aure ne iyayenta suka ce na turo magaba ayi maganar saka ranar aure na da ita." Murmushi Dad ya saki tare da cewa. "Ma Sha Allah wannan abun farin ciki ne ai." Kallonsa ya maida zuwa ga Mum wacce tunda ya Munnir ya fara magana yanayinta ya sauya, ranta a b'ace ta fara masifa. "Wato kai Munnir ban isa da kai ba ko? Na fad'a maka cewa ka janye zancen neman wata mace ka je ga 'yar uwarka can tana mutuwar son kamar za ta yi hauka shi ne ka bijirewa magana ta ko? To ka sani Hafsat na zaba maka ba kowa ba da ita nake son ka yi rayuwar aure. Dad ne ya kalle ta yana cewa. "Wai meye matsalarki ne yaron nan tun baya ya ce baya son Hafsat, nima kaina ban goyi bayan ya aure ta ba, duk da cewar da ke da uwar Hafsat ciki d'aya kuka fito Hakan ba shi baki damar da za ki tilasta masa auren yarinyar da baya so ba, ki barshi ya auri zabinsa." "Alhaji ba zan barshi ba dole ya bi umarnina." "Ke bari kiji ko da ace shi ya amince da auren Hafsat to ni ubansa ban goyi bayan wannan auren ba, domin duk yarinyar da ta rasa ilimi ta rasa tarbiya ba abunda ba zata iya aikatawa ba, ko kin manta da fadin manzon Allah (saw) ne idan yake cewa ku zabawa 'ya'yanku uwa ta gari wacce za ta bawa 'ya'yanku tarbiya ta k'wara? Ina Hafsat ina tarbiya da za ta bawa 'ya'yanta? Yarinyar da idan ba shaye-shaye da iskancin ba ba abunda ta sakawa gaba, yarinyar da za ta yi kwanaki ba ta kwana agidan iyayenta ne zan nemawa d'ana, da kaina na ga Hafsat a yanayin da take ciki Wanda ba zan taba yarda Munnir ya aure ta ba." Dubansa ya maida zuwa ga Munnir sannan ya ce. "Ya yanayin yarinyar tana da tarbiya da ilimin addini ko?" Jinjina kai ya yi tare da cewa. "Eh Dad tana da tarbiya Kuma har ta sauke alqur'ani Mai girma tana da sanin yakamata." Murmushi Dad ya saki tare da yin hamdala, lokaci d'aya kuka murmushin kan fuskarsa ta gushe Sakamakon jin maganar da Munnir din ke yi. "Dad amma k'addara ta fad'a mata a baya ta Dan fad'a harkar shaye-shaye na dan lokaci, Kuma sai tsautsayi ya fad'a mata har ta ta haihu yanzu tana da yaro..." Kallon Da Dad din ya masa ne ya saka shi kasa k'arasa maganar da ya yi niyyar k'arasawa, don bancin rai nr ya gani kan fuskarta Dad din nasa, yayin da Mum din kuwa ta saki wani murmushi Mai cike da ma'ana Wanda ita kadai ta San haka. Ajmal ne ya fito daga d'akin da aka sauke shi, yana sanye cikin kananun riga amles da wando 3quter, tun kafin ya k'araso k'amshin turarensa ne ya sanar da su fitowarsa. Suna zaune su uku a dinning area suna jiran fitowarsa, da sallama ya k'araso fuskarsa ba yabo ba fallasa. Zama ya yi akan d'aya daga cikin kujerun dinning din ya sake gaida Marka sannan Suka gaisa da Sudais Nihal ta gaishe shi . Marka sai fara'a take tana jansa da tsokana irin na kaka da jika, bai amsa mata ba sai danne-danne da yake yi a waya. "Nifa matsala ta da kai mishkilancin tsiya, mutim ace ba rahama a tattare da shi kullun fuska kamar hadari, gaskiya Nihal sai kin shirya zama da wannan mutum don za ki Sha wahala." Da sauri ya dago da kansa daga kan wayar ya dawo da shi kan Marka sannan ya Kalli Nihal fuskarsa a tsuke. *Kuyi hak'uri da wannan*🙏 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z 🤦‍♀️ *YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) Page 8️⃣5️⃣ Da sauri ya dago da kansa daga kan wayar ya dawo da shi kan Marka, sannan ya Kalli Nihal fuskarsa a tsuke. Bai ce masu komai ba ya share kamar bai ki me suka ce ba. Nihal ce ta kalle shi ta fara magana. "Ya Ajmal me zan zuba maka?" Ba tare da ya kalle ta ba ya ce. "Am okay." Ya fad'a ba tare da ya Kalli d'aya daga cikinsu ba, Nihal na shirin yin magana ta ji muryar Sudais yana cewa. "Bros ba za ka ci abinci ba ne, why?" "Am okay." Ya fad'a yana d'aukar robar ruwa tare da balle murfin robar ya tsiyaya a glass cup ya Sha. Ganin yana shirin barin wajen Marka ta ce. "Ajmalu saboda me ye ba za ka ci komai ba?" "Ba na Jin yunwa." "Ka San wahalar da Nihal ta yi wajen girka maka abincin da za ka ci kuwa, nan ta zage ta dinga aiki duk da akwai Mai girki amma ta ce ita za ta maka don ta San irin abincin da ka fi so, shine za ka watsa mata kasa a idanu?" Shiru ya mata kamar bai ji me take cewa ba, ganin ya share ta ne ta fara masifa. "Yau na ga iya shege ni Marka wannan yaron kamar ba jinin Ibrahim ba? Dan shi Sam bai da wannan mugun halin naka, ace kai Sam ba za ka saki jiki da mutane ba , ni na haifi ubanka a cikina na rene shi ya tashi cikin fara'a da son mutane baya gudun 'yan uwansa da danginsa duk cikin 'ya'yana uku da Allah ya bani ya fi kowa saukin kai, amma kai na lura wiyar sha'ani ne da kai ko sakin jiki da mutane ba k yi ballanata ayi raha da kai halinka d'aya yake burge ni yadda aka ce kana da taimakon marasa shi, da yadda jama'a ke taruwa k'ofar gidanka a duk lokacin da kake gari kana basu tainako Musamman mata, bayan haka ba wani hali Mai kyau a tattare da kai, yanzu haka ka dauko halin masu jajayen kunnuwa don can k'asar ka tashi wajen dangin uwarka larabawa don na ji ance basa son bakaken fata kyamarsu suke yi, ko da ubanka ya tafi can ya auri uwarka ya kawo ta nan garin haka ta zauna ba ta sakin jiki da mutane sai dai ta yi shiru tana kallon mutane." Zuba mata idanu kawai ya yi yana kallonta don ransa ya fara baci da ita, ta ya ya daga cewa ba zai ci abinci ba ta fara masa masifa har da za gi, don shi a wirinsa zaginsa take yi tunda ba ta ce mahaifinsa ba sai dai ubansa sai Kuma uwarasa madadin ta ce mahaifya. A kifule ya ce. "Kiran me kika mani ne?" "Magana ce Mai mahimmanci zuwa anjima zamu tattauna ko zuwa gobe." "Ba na da lokacin batawa tafiya zan yi." Ya bata amsa yana barin wajen, da Kallo suka bi bayansa inda Marka ke kiransa bai ma tsaya ba ballanata ya San me zata ce masa. Yana shiga d'akin ya zauna Saman doguwar kujera dake falon ya lalubo lambar wayar Dad d'insa. Bugu biyu ya d'aga bayan sun gaisa ya ce. "Dad wai mene ne aka ce na zo garin nan?" "Ajmal nima ban sani ba umarni ta bani akan tana son ganinka " Jin Dad din ma bai San komai akan zuwan nasa ba ne ya sa ya masa sallama ya kashe wayar. Laptop d'insa ya dauko ya fara danne-danne a jiki, sallamar Marka ya ji tana kwadawa, amsa mata ya yi a cikin yanayinsa na rashin son hayaniya, shigowa ta yi ta zauna gefensa tana cewa. "Ba ka Jin sallama ne ko zama cikin nasaara ne ya saka ba ka iya amsa sallama?" Kamar bai ji ta ba bai Kuma sake amsawa ba don shi ya San dai ya amsa duk da ya tabbatar ba ta ji ba amma bai sake magana ba. Cigaba da danne-danne ya dinga yi a laptop d'insa kamar bai San da zuwan ta a wajen ba. Yau na ga tsiya ni Marka boni ta cimmani wai kai wane irin mutum ne haka, ba ka ji sallama ta ba

Chapter 37 of 51