biyu da fita."
Wayarsa ya ciro daga cikin aljihunsa ya dannawa lambar Ajmal kira.
Dama shi Fu'ad sau tari idan yana waya sai ya saka waya handsfree yadda duk wanda ke kusa sai ya ji maganar cikin wayar.
Ajmal na can riƙe da Amatullah tana masa raki dan ya lura har da raki ne abu nata wayarsa ta soma ruri.
Bai duba ba balle ya daga. Daidai lokacin da ya canzawa babyn mama daga na dama zuwa na hagu, dan ya tsotsi kowanne, dan tunda ta ce ba za ta shayar da shi babyn ba shi kuma ya dauki niyyar ko ta halin yaya sai ta shayar da shi ita ko kan nipple ɗinta sai zugi take mata kamar dai yadda ake ji wajen fara shayar da yaro.
Lokacin da ya canzawa yaron kan nipple ɗinta sabon zafi ta ji. Wayarsa aka sake kira ya ga Dr Fu'ad ne sai ya ɗaga kafin ya yi magana ne ta cikin wayar suka ji muryar Amatullah tana cewa.
"Washh da zafi dan Allah sake ni haka nan, ka barni na huta wallahi da zafi na gaji."
"Kuyi hakuri nan da mintuna biyu zan ƙyale ki amma a yanzu sai..."
Daga Ammi har Nasreen da Nihal sun ji me Amatullah da Ajmal ke faɗa.
Lura da hakan ya saka Fu'ad ya yi saurin katse kiran wayar, su a tunaninsu Sex Ajmal ke yi da Amatullah.
"Nasreen ƙwalla ne ya cika mata idanu, yayin da Nihal ma ta ji haushi amma dole Nasreen matarsa ta fi jin haushi.
Ammi kama shiru ta yi ta kasa cewa komai ta kasa gasgata wannan lamarin da kunnenta suka jiyo mata.
Nasreen ta tashi ta haura upstairs da sauri tare da shiga bedroom ɗin ta.
Ajmal kuwa tun da ya ga an kira a katse shima ya ajiye wayar, har lokacin yana riƙe da Amatullah tana ta zuba raki ga kunya duk ya ishe ta, tana ƙoƙarin sa hannu ta kare ƙirjinta ganin irin mayataccen kallon da yake yi wa ƙirjinta baya ko ƙyafta idanu.
*Daga alƙawarin*✍️
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
09065327995
Love you oll😍😘
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
🤦♀️ *YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
Ban yarda a karanta mani shi a youtube ko a maida shi audio ba tare da izinina ba.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Page5️⃣4️⃣
Ajmal kuwa tun da ya ga an kashe kiran wayar shi ne ya ajiye wayar, har lokacin yana riƙe da Amatullah tana ta zuba raki ga kunya duk ya ishe ta, tana ƙoƙarin sa hannu ta kare ƙirjinta ganin irin mayataccen kallon da yake yiwa ƙirjinta baya ko ƙyafta idanu.
Amma ina ta kasa saboda ya riƙe hannayenta. Abdallah kuwa sai zuƙar mamanta yake yi har ya fara lumshe idanu alamar barci zai koma.
Takaici duk ya ishe ta dan ba ta yi niyyar shayar da shi ba yaron kwanta-kwata ga shi yau Ajmal ya karya alkadarinta. Tsabar takaici ya ishe ta, dan ba ta son ta saka shi a ranta sosai saboda duk daran daɗewa tana so ta koma gaban iyayenta. Kuma komawarta tare da wannan babyn akwai matsala dan ta san iyayenta ba zasu huce da baƙin ciki ba. Ga Kunyar mutanen unguwa gulmarta ma kaɗai ya ishe su. Ta dan tasirin da ke cikin nonon uwa, matukar ta fara shayar da shi zai shiga ranta ne sosai ta yadda ba za ta iya rabuwa da shi ba, hakan ya sa ba ta ɗora masa so ba ballantana zuwa gaba idan ta barshi ta shiga damuwa.
Ganin Babyn ya yi barci ne ya kuma saki nonon ya daina tsotso ta sa Ajmal zare shi tare da kwantar da shi gefe kan kujerar da ke kusa da shi ya miƙa hannu ya ajiye shi.
Ganin haka ne ya sa ta fara ƙoƙarin jan rigarta dan ta rufe ƙirjinta sai ya yi saurin riƙe hannayen nata suka biyu, har lokacin idanunsa na kan ƙirjinta, dan bai taɓa ganin nono mai kyau da ɗaukar hankali irin nata ba, ga gasu a tsayayyu kamar zasu tsokane idanun mai kallonsu, cikakku kamar an hura balon-balon ba su rankwafa ba ballantana su zube.
Idanunsa ne suka fara canza launi zuwa ja jikinsa ya fara mutuwa, take yanayin jikinsa ya sauya. A sukwane ya fara magana.
"Nawa za ki siyar mani da nonon?"
Kallonsa ta yi cikin rashin fahimta dan ba ta fahimci me yake nufi ba.
"Dama ana siyar da su ne?"
Rukitattun idanunsa da suka canza launi zuwa ja ya zuba mata, sannan ya ce.
"Na ji kin faɗa cewa ba za ki shayar da shi ba ko? Saboda me ya sa kika ce haka bayan ke kika haife shi? Saboda mahaifinsa bai kashe ko sisi ba ya same ki a arha? Haka kike nufi tunda kin ce sai ɗan halak za ki shayar, saboda shi ɗan halak mahaifinsa sai ya biya kudin aure sadaki lefe da sauransu ko? Wannan kuma ban biya ko sisi ba. To yanzu ki faɗa mani bawa kike so daga Naira miliyan ɗaya zuwa miliyan ashirin zan baki dan ki shayar da shi."
Murmishin takaici ta yi dan ta ga kamar yana mata kallon mai son kuɗi wanda kuma kuɗi baya gabanta. Shiru kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba. Wanda take ta ga idanunsa sun koma ja, ita ta ɗauka tausayin babyn ne ba ta san jarabarsa ta motsa sakamakon arangama da ya yi da kyakkyawan ƙirjinta.
"Ka sake mani hannuna zan mai da rigata ne."
"Okay ba kin ce kina jin zafi ba?"
Shagwaɓe fuskar ta yi tare da gyaɗa kai alamar eh.
"Okay bari na shafa maki magani a wajen da ya cije ki ko?"
Hannu ya miƙa a saman Centre table dake gabansu ya ɗauki wata 'yar ƙaramar roba mai murfi ya buɗe, Idanunta ya kalla da ta rintse, sannan ya kai hannu a saman ƙirjinta da niyyar shafa wa sai wayarsa ta soma ringing.
Amminsa ce ke kira ya san dalilin kiran dan haka ya ce wa Amatullah.
"Ki maida rigarki mu tafi."
"Ba musu ta yi saurin mai da rigar yayin da ya daga wayar ya yi magana a cikin kasala da sarƙewar murya."
"Assalamu alaikum"
Ammi dake tsaye a falo ita da Fu'ad da Nihal, Nasreen dama tun da ta ji mauryar Amatullah ta tafi ta bar wajen tana kuka.
"Wa'alaikumus salam."
"Kuna ina ne?"
Ba zai iya mata ƙarya ba a karo na biyu, dan haka ya ce.
"Muna nan dawowa."
"Ya naji muryarka ta canza?"
"Ba komai."
"Na ce ina ka kai Amatullah? Na san ba ka yi mani ƙarya idan kuma ka fara ne to"
"Guest house ɗina."
"Ina jiranka yanzun nan."
Daga nan ta katse kiran. Wayar Fu'ad ya mata sallama ta tafi."
Wayarsa ya ciro ya dannawa Ajmal kira.
Lokacin da Ajmal ya tashi bayan ya rungume babyn da ke barci. Ɗaya wayar ya yi tare da cewa
"Hello Fu'ad ya kake?"
"Ajmal wai yaushe ka lalace haka ne?"
"Kai bana son iskanci , ka kira ni ne dan ka tambaye ni yaushe na lalace?"
"To wallahi Ajmal ka sani kana cikin matsala, dan asirinka ya tono."
Mamaki ne ya kama shi
"Ban gane asirina ta tonu ba me na aikata ne?
"Ina ka kai 'yar mutane kake tumurmusa tana ihu tana roƙonka?"
Shiru ya yi sai a lokacin ya tuna cewa Fu'ad ya kira shi lokacin da Amatullah ke rakin tsotson da baby ke yi.
Dariya ya yi yana kallon Amatullah dake tsaye ita ma shi take kallo.
"Kai kar ka damu ba wani abu ba ne fa, wai ita ba za ta shayar da babyn ba, ga babyn na ta kuka yana jin yunwa shi ne fa na cire mata rigar na baya babyn mama ya sha, akan wannan ne fa take ta raki kamar wacce nake..."
Shiru ya yi bai ƙarasa ba, ka tabbatar haka ne?"
"Kai ma ka san baka isa na yi maka ƙarya ba."
"Shikenan tunda haka ka faɗa sai ka shirya yadda za ka kare kanka. Dan dai abinda na ji shi Amminka da matarka suka ji. Dan ina tare da su, kuma i dan wayata a handsfree nake yi."
Dafe kai Ajmal ya yi tare da cewa.
"Fu'ad ka ɓata komai."
"Ac ba abinda na ɓata kai ne ka ɓata da kanka, da ka san za ka yi ƙarya da ni me ya saka ba ka sanar da ni ba? Da na sani ai ba zan tafi gidan nemanka ba?"
"To me ya sa kafin ka tafi baka kira ni ba? Dama na saba kiranka ne na nemi izinin ka idan zan zo? Ai ko kana kasashen waje ina zuwa gaida Ammi."
"Sai an jima."
Ajmal ya faɗa tare da katse kiran wayar.
Tunanin yadda zai ɓullowa lamarin yake. Gashi har yanzu jikinsa a kasalance yake, wani yanayi ke taso masa tunda yayi arba da ƙirjin Amatullah hankalinsa ya tashi.
Kallonta ya yi tare cewa.
"Mu tafi."
Fita ta yi ya bi ta a baya a susuce.
Ahmad na ganin fitowarsa ya ƙarasa ya rufe ƙofar.
A bayan mota suka shiga yayin da Ahmad ya shiga ya ja motar.
Kallon yadda jikinsa ya yi sanyi ta yi ga idanunsa sun yi ja, ksllonsa ta yi tare da cewa.
"Baka da lafiya ne?"
Lumshe idanu ta yi tare da cewa
"Am Okay."
Taɓe bak tayi tare da cewa.
Kau da kai gefe ta yi yayin da ya lumshe Idanu yana da ya sanin abinda ya aikata, dan da ace bai cire mata riga ba ai da bai kalli abinda zai tayar masa da hankali ba. Ga shi yanzu ya shiga wani hali. Ko ya koma gida ya tafi wajen Nasreen dan ya biya buƙatarsa a wajenta ba yarda za ta yi ba tunda tana fushi da shi. Ya ma rasa yadda zai yi. Ga ƙwayoyin magani da yake sha sun daina masa aiki yanzu.
Kallonta ya yi Idanunta na kan titi tana kallon ababen hawa.
"Dan Allah ki dinga shayar da yaron nan mama, domin ba karamin tasiri yake da shi ba a wajen yaro. Zan biya ki ko nawa kike so Indai za ki shayar da shi."
"Idan za ka bani duniya da abinda ke cikinta ba zan shayar da yaron nan ba, dukiya ko wani ƙyale-ƙyale na duniya basa gabana ballantana ka ruɗe ni da su."
Wani marmushi ya yi wanda shi kaɗai ya san ma'anarta. Ba wanda ya sake magana a cikinsu shi dama ba komai bane illa yanayin da ya tsinci kansa a ciki, dan haka sai ya kumshe idanunsa kawai va tare da ya sake cewa komai ba gefe ɗaya kuka tunanin yadda zai cewa Amminsa yake yi.
Ita kuma kallon Babyn da ke hannun Abbansa take yi gefe ɗaya hankalinta na wajen Ummanta da Abbanta.
Horn ta ji anyi a gate na farkon shiga gidan, sannan hankalinta ya dawo jkiknta, sacurity ne suka buɗe masu gate ɗin suka shiga. Har suka isa gate na biyu nan ma security ya buɗe masu gate suka shiga.
Bayan Ahmad ya yi parking ne ya ne ɗaya daga cikin bodyguards ɗin Ajmal ya buɗe masa murfin motar ya fito rungume da babyn a hannunsa.
Sannan bodyguard ɗin ya ƙarasa ya buɗe wa Amatullah ta fito itama .
Daga ciki kuwa Nihal tunda ta ji shigowar motar ta yaye labulen window tana kallonsu. Ganin Ajmal ya fito riƙe da Baby ne ya sa gabanta faɗuwa, musamman da ta ga yanayin yanda rigarsa ta yamutse bata miƙe kamar yadda take ba.
Tsanar Amatullah ne kawai ke yawo a zuciyarta, dan yanzu ba ta jin haushin Nasreen matar Ajmal sai Amatullah. Dan ta lura Nasreen ba ta iya kula da miji ba, harkar gabanta kawai take yi, dan haka take ganin ƙwace shi daga wajen Nasreen abu ne mai sauki,sai dai yanzu Amatullah ce matsalarta.
Tsuki ta yi tare da maganar zuci tana cewa.
'Wato ni ce ba ka son haɗa jiki da ni ko? Sai wannan kucakar yarinyar? Ba zai yiwu ba ko da ba ka aure ni ba sai na ɗanɗani zumarka. Buri na na jini a jikinka kyakkyawar surarka kullun cikin ja mani hankali yake.'
Miƙa ma Amatullah babyn ya yi dan ta san part ɗin su za ta wuce, bayan ya miƙa mata ne ya ce ɗan tsaya mana.
Dakatawa ta yi da tafiyar da take yi, ta lalle shi inda ya ƙaraso gabanta.
"Dan Allah ki cigaba da shayar da shi, zan baki duk abinda kike so Please."
"Hmmm ni fa ba zan taɓa iyawa ba, na saka a raina haka zan yi ina Banda wannan da ka sata ka bashi ya sha."
Dariya ta yi tare da cewa
"Sata kuma?"
"Eh sata mana tunda ban ba shi ba."
"Shikenan anjima ma zan shigo na sake satar maki."
Ya yi maganar yana kashe mata idanu ɗaya, sannan ya tafi ya barta tana tura baki. Duk Nihal na kallonsu ganin yadda yake dariya da kashe mata idanu ɗaya.
Daga Ajmal har Amatullah ta kowa ya nufi part ɗin sa tana tunanin yadda za ta yi ta hana Ajmal zuwa ɗakinta.
Da sallama Ajmal ya shiga falon inda Ammi da Nihal suka amsa masa sallamar.
Ganin Nihal a falon Kum ya ga ran Amminsa a ɓace ne ya saka ya fara magana da harshen larabci dan gudun ka da Nihal ta san me suke tattauna akai.
"Ammina lafiya na ga kina cikin damuwa, za ku tayar mani da hankali ai."
"Ina kai yarinyar nan da sunan asibiti?"
Nihal ta ji haushi dan ganin Ammi ma haka ta juya zuwa larabci.
"Ammi guest house ɗina muka tafi."
"Saboda me?"
"Akwai maganar da nake so kuyi da ita ne?"
"Wace irin magana ne da ba za ku iya yinta a nan ba?"
Tuna cewa Amatullah ba ta amince da zancen auransa ba ne ya saka bai faɗa wa Ammi ba.
"Ya na ji ihun yarinyar a cikin waya me kake mata?"
Nan ya bawa Ammu labarin duk yadda suka yi akan ta ƙi bawa Babyn mama ya sha.
Shiru ta yi tare da cewa.
Ka da ya sake mata irin haka ya ƙyale ta tunda Babyn na shan madara, kuma madarar madadin nonon uwa ne. Sai ya nuna mata tasirin da nonon zai fi kyau fiye da madara,ta nuna masa ta sani amma ba ta yarda ta takura mata ba. Ta yarda da zancen Ajmal dan ta san halinsa dama.
Har lokacin dai bai koma daidai ba yanayin jikinsa ya sauya. Upstairs ya nufa da sauri kai tsaye ya shiga bedroom ɗin Nasreen.
Da sallama ya shiga inda ya samu tana zaune tana kuka. Ƙarasawa ya yi tare da zama gefenta, ta yinƙura da niyya tashi ya janyoya jikinsa ya rungume tare da ɗan bubbuga bayanta a hankali alamar rarrashi.
Ture hannunsa ta yi tare cewa.
"Ka fita ba na son ganinka, Abban Affan wai yaushe ka zama haka? Kai yanzu fasiƙanci ba ka ɗauke shi a bakin komai ba?."
"Kin ga kuskuren fahimta kuka yi ki tsaya na maki bayanin komai."
"Ba abunda zan saurara a gare ka, illa tambaya ɗaya zan maka."
Goge hawayen da ke fuskarta take sannan ta kalli Ajmal da kyau ta ce.
"Da sunan zuwa ina kuka fita daga gidan nan?"
"Asibiti."
"To ina kuka tafi?"
Shiru ya danyi kafin ya ce mata.
"Guest house ɗina."
"Muryar wace ce na ji a waya tana kuka?"
"Amatullah."
A fusace ta fara magana tana cewa.
"Wallahi ka fita a ɗakin nan kafin ka ga haukana."
"Shikenan zan fita kamar yadda kika ce. Sai dai dole ne na sanar da ke gaskiya, abinda kuke zargi ban aikata ba, ihun da take raki ne kawai irin nata, dan na tilasta mata akan ta bawa baby mama ya sha, shi ne take wannan ihun."
"To akan me za ka kaita guest house din ka?"
"Na so ne nayi amfani da wannan damar wajen ba ta haƙuri, kasancewar ni ne sanadin da ta samu ciki har iyayenta suka kore ta, ga shi ta sha wahalar rayuwa. Ina son na ba ta hakuri kuma na nemi yafiyarta ne."
"Akan me za ka bata hakuri? Da saninki ka aikata haka? Ko kai ne ka ce zuba maka magani cikin coffee, kuma a mata allura?"
"Ba ni ba ne."
"To akan me za ka bata haƙuri?"
Numfasawa ta yi sannan ta kalle shi ta ce,
"Zan haƙura ne kawai idan ka yi mani wani alƙawari."
"Wane alƙawarin ne zan maki?"
"Daga yau ba ita ba kai, ba ruwanka da lamuranta, ba ruwanka da yaronta ka ɗauki kuɗi masu yawa wanda zai ishe ta ta rayuwa ta raini ɗan ta, irin kuɗin da har su mutu ba zasu yi talauci ba, ta je ta ja jari ta kula da ɗanta. Idan ka Mani wannan alƙawarin shi kenan komai ya wuce."
Shiru ya yi tare da yin nazari, Kallonta ya yi tare da cewa.
"Idan na mata haka ban mata adalci ba, saboda ba kuɗi ne maganin matsalarta ba. Hakki ne da ya rataya a wuyana na kai ta har gaban iyayenta."
Gabanta ne ya yi mummunar faɗuwa, a fusace ta fara magana.
"Abunda ba zai taɓa yiwuwa ba kenan, akan me za ka damu da ita har haka? Har da mai da ta gaban iyayenta matsalarka ne? Dama can ita ba yarinyar arziki be ce, wace 'yar mutunci ce za ta tafi hotel? Har wanann tsautsayi ya riƙe ta a can? Har ka ke maganar mai da ta gaban iyayenta for what reason?"
"Wai ke mene ne matsalarki da ita ne, da kika damu akanta?"
"Saboda namiji bai da tabbas."
"Saboda ba ki yarda da kanki ba dai."
"Me zai sa ban yarda da kaina ba?"
"Saboda kin san kin gaza wajen kula da mijinki da ɗaukar ɗawainiyar bukatarsa ko?"
"Duk ƙoƙarin da nake ba ka gani ko sai dai jarabarka ne ba zan iya jurewa ba?"
"Idan kika kasa jurar jarabarka kamar yadda kika ce waye zai iya ɗauka? Ina da wata matar ce bayan ke? Ta ya ya ace ina da mata amma sai na dinga shan magani idan buƙatar mace ya taso mani? Me ye amfanin matata?"
Taɓe baki ta yi tare da cewa.
"Wannan ne kuka ba zan iya ba, saboda kai ba ka ƙi kullun kana naniƙata ba ko gajiya ba ka yi kamar wani injin, kafin ka ƙyale Ni ma sai na saka maka kuka kake saurara Mani, Ni kuka duk wannan bai dame ni ba bana son harkar. Wannan dalilin ne ya saka nake nesa da kai na cigaba da zama a gaban iyayena a America dan ba na son takura. Don haka bana zuwa turaka ake cewa ko me? Kuma na ke rufe ɗakunan dan kar ka shigo, dan wallahi idan na biyu maka sai ka tsufar da ni da wuri."
Ta ƙarasa maganar tana kau da kai gefe.
Murmushin takaici ya yi tare da cewa.
Murmushin takaici ya yi tare da juyawa zai fita, har ya kai ƙofa ya ji muryarta tana cewa.
"Kafin ka fita ina mai tunatar da kai cewa yarinyar nan ta bar gidan nan."
Ba tare da ta jiyo ya kalle ta ba ya ce,
"Ba ki isa ba tunda ba gidanki ba ne kuka ba ƙarƙashin ki take ba, duk abinda za ki iya kiyi sha sha sha kawai."
Duk maganar da suke a kunnen Nihal dake masu laɓe, jin takun ƙafar Ajmal ta yi saurin guduwa ta nufi downstairs.
"Wallahi idan baka sallami yarinyar nan ta bar gidan nan ba sai na illata ta."
Bai ce komo ba ta fita daga ɗakin tare da tunanin matakin da zai ɗauka akan Nasreen.
*MINNA NIGER STATE*
Motocin police guda baiyi suka yi dirar mikiya mazanya hotel. Hafsat tana shawo kwanar hotel ɗin ta hangi motocin police, ba ta damu ba ta ƙaraso wajen ta yi parking daga can gefen motarsu.
Police ne suka fara fitowa inda suka janyo INDAKUƊINKA cikin hotel ɗin dan ta nemi wacce ta bashi kwangilar wannan mugun aiki.
Bayan sun shiga ne ita dama Hafsat ba ta ga fuskar INDAKUƊINKA ba.
A hankali ta fito daga cikin motar ta ta tana rike da key ɗin motar tana karkaɗawa ta nufi cikin hotel ɗin.
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
09065327995
Comment & share pls
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
🤦♀️ *YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
Ban yarda a karanta mani shi a youtube ko a maida shi audio ba tare da izinina ba.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Page5️⃣5️⃣
A hankali ta fito daga cikin motarta tana riƙe da key ɗin motarta tana karkaɗawa ta nufi cikin hotel ɗin.
Ta nufi ɓangaren club ɗin kenan ta ji wasu samari na magana.
"Kai dai ka bari ba ya ce INDAKUƊINKA komai zai maka ba? Shi shugaban masu son kuɗi. An bashi Naira duba ɗari kacal da wata ta bashi watannin baya yanzu zai zame masa matsala."
Ɗayan ne ya ce,
"Zai zame masu matsala dai ita da shi."
Gabanta ne ya faɗi ta dakata da tafiyar da take yi ta kalle su.
"Me ke faruwa ne na ga motar police?"
"Hajiya ba lafiya da,wani ma'aikacin hotel ɗin nan ne wata ta bashi kuɗi ya yi wa wata allura, sannan ya kai ta d'akin wani da ya kama ɗaki a hotel bayan ya zuba masa magani a coffee wanda ya fita hayyacinka har ya yi lalata da yarinyar."
Kallonsa ta yi tare da cewa.
"To akan wannan ne har za'a Turi jami'an tsaro su tayar da hankalin jama'a?"
"Kin san waye ya taɓa kuwa!? Daga shi har yarinyar da ta saka shi wannan aikin ina tausayinsu."
"Waye shi."
"Ajmal Ibrahim Tafida, babban mutum ne da ake ji da shi a jaharsu, kuma ya fito takarar Gwamnan jihar Kaduna har ya lashe zaben primary election. A yanzu haka an dakatar da shi saboda wannan da suka aikata masa."
Zufa ne ya fara tsatstsafowa daga duk wata kafar gashi dake jikinta. Gabanta ta tsananta faɗuwa. Ta juya da sauri ta fita inda ta nufi wajen motarta.
Shiga ta yi ta figi motar a guje ta bar wajen.
Sai da ta yi tafiya mai nisa kafin ta yi parking a gefen hanya, tunani ta shiga yi neman mafita.
Murmushi ta yi lokacin da ta tuna cewa bai santa ba kuma bai san sunanta ta ba. Daga nan ta ƙudiri niyyar ba za ta sake zuwa wannan wajen ba sai dai ta canza waje.
Motarta ta je ta nufi hanyar gida. Zuciyarta na wasi-wasi idan kuma suka binciko cctv camera kuka fa? Anya ma hakan zai faru abinda ya afku kusan 10 month ta ya ya zasu busu binciko shi.
Haka ta dinga tunani har ta isa gida.
Bayan ta fito daga motar ne ta jingina jikinta a jikin motar tana cewa
"To ina ma ita wannan Amatullah take ne? Ga shi abinda na aikata maki ne ke neman zame mani tashin hankali. Ko da yake ba yadda zasu iya nemo ni."
Murmushi ta saka tare da cewa.
"Ina kika shiga Amatullah? Allah sarki 'yar talakawa ko kina ina oho."
Kai tsaye ta nufi cikin gidan tana murmushi.
Motar Munnir ne yayi parking a ƙoafar gidansu Amatullah. Ba kowa a ƙofar gidan inda ya fito daga cikin motar ya nufi zauren gidan.
Sallama ya yi a ƙofar gidan inda ya Mallam Abdullahi ya amsa masa.
Shiga ya yi cikin gidan Umma na kwance a tabarma a tsakar gidan. Yayin da Abba ke tsaye hannunsa riƙe da buta da alama banɗaki ya fito.
Cike da fara'a Abba ya ce.
"Munnir kai ka tafe yanzu?"
"Eh ni ne Abba."
Ya durƙusa ya gaishe da Abba, ya amsa masa cikin sakin fuska da walwala.
Ƙara sawa ya yi a tabarmar da Umma ke kwance, wanda har yanzu ba ta warware ba, dan har yanzu ba ta cin abinci sai kuka ta yawan kiran sunan Amatullah.
Ba ta yi cin komai sai farau-farau kaɗai take iya sha. Bayan ya gaishe ta be ta amsa ya na tambayar jikinta ta amsa.
Abba ne ya ƙara masa godiya akan akan yadda ya damu da su, duk da cewar Amatullah ba ta nan amma bai yanke ƙauna ba, yakan zo Lokaci zuwa lokaci yana gaishe su.
Kallon Abba ya yi tare da cewa
"Abba har yanzu ba labarin Amatullah ko?"
Jinjina kai Abba ya yi tare da cewa.
"Har yanzu, na yi nadamar korar da na yi mata daga gidan nan, ga shi tun tsawon lokacin da ba ta bar gidan mahaifiyarta ba ta samu nutsuwa ba kullum cikin ciwo take yau lafiya gobe ciwo."
"Abba kuka ba wasu dangi da za'a iya tuntuɓa. Ko ta je wajensu?"
Ba mu da kowa a ƙasar nan, asalinmu mutane ƙasar Niger ne, mu ba 'yan Nigeria ba ne ,kuma rabon da nu tafi tun tana karamar yarinya."
Jinjina kai Munnir ya yi tare da cewa
"Allah ya bayyanar da ita."
Daga nan ne ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 51