ba ta gani ba, dan haka da rarrafe ta ƙarasa a bakin ƙofar, ta saka hannu ta murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin.
Tana kuka ta buɗe ƙofar amma ta kasa fita sai kuka take. Nafeesat da ta fito daga ɗakin da ke kallon inda Amatullah take ne ta ji sautin kuka, da firgici ta juya dan ganin wace ce ke kuka.
A firgice ta zaro idanu tare da furta kalmar
"Subhanahi! Amatullah wa ya maki wannan aikin?"
Sautin kukanta ta ƙara tare da cewa
"Nima ban sani ba."
Ganin Amatullah na ƙoƙarin tashi ne ya sa Nafeesat ta ƙaraso wajenta da sauri ta taimaka mata ta miƙe tsaye.
Wani namiji ne ya fito daga ɗakin da Nafeesat ta fito, Kallonta ya yi tare da cewa
"Baby ina kuma za ki shiga wajen?"
"Ina zuwa ka fita inda za ka tafi sai ka dawo."
Jinjina kai ya yi tare da cewa
"Okay."
Ya bar wajen yayin da Nafeesat ta taimakawa Amatullah suka shiga shiga toilet din da ke cikin ɗakin.
Ruwan zafi ta haɗa mata tare da Kallonta cikinn tausayawa ta ce
"Amatullah sai kin daure fa amma idan kika daure za ki ji sauƙin raɗaɗin da kike ji.
Jinjina kai kawai Amatullah ta yi sai hawaye dake fita daga cikin idanunta.
Bayan Nafeesat ta gama hada ruwan ta tabbatar da zai yi dai-dai sannan ta bawa Amatullah umarnin ta shige.
A hankali ta zauna cikin ruwan zafin, ƙara ta saki na azaba,ta yunƙura za ta tashi sai Nafeesat ta yi saurin riƙe ta ba ta bari ta tashi ba.
Sai da ta canza mata ruwa sau biyu, sannan a na uku ne ta barta ta ce,
Tayi wanka tana jiranta a ɗakin.gaba ɗaya ranta ya gama ɓaci dan ta san cewa mawuyacin abu ne Amatullah ta yarda a mata wannan aikin.
Fita ta yi daga ɗakin zuciyarta cike da saƙe-saƙe. Ba komawa ta fito hannunta dauke da doguwar riga na material da ƙaramin mayafi.
Dai-dai lokacin da Amatullah ta fito tana tafiya a hankali, ba laifi ta rage jin zafin da take ji .
Nafeesat ta miƙa mata kayan da ke hannunta ta karɓa ta saka, har lokacin hawaye bai daina kwaranya daga idanunta ba.
Hannunta kawai ta ja tare da cewa
"Wa ya kawo ki wannan ɗakin?"
Kuka ta fashe da shi tare da cewa
"Wallahi ban sani ba ban san komai ba."
A firgice Nafeesat ta kalle ta tare da zare idanu ta ce,
"Kina nufin ba ki san lokacin da kika zo ɗakin nan ba? Kuma ba ki san wanda ya maki wannan aikin ba?"
"Wallahi bansan komai ba farkawar na yi na ganini awannan ɗakin."
"To daga ina kike kafin kika tsinci kanki a nan?"
Nan ta bawa Nafeesat labarin komai da yadda suka yi da iyayenta har kiran wayar da Hafsat ta mata da kawo mata waya har izuwa alluran da ta ji an soka mata ta sulale za ta faɗi ta ji an riko ta, daga nan ba abinda ta tuna.
Ajiyar zuciya Nafeesat ta sake tare da ɗaukar wayarta ta dannawa Hafsat kira?
Ya na ta ringing ba ta ɗaga ba, daga nan ta ja hannun Amatullah suka fice daga ɗakin.
Kai tsaye ta nufi gidanta da ita dake kusa da club, Amatullah ne ta coge a ƙofar gidan alamar ba za ta tafi ba. Kallonta ta yi da murmushi a fuskarta ta ce,
"Ka da ki damu Amatullah ba cutar da ke zan yi ba, ina son Hafsata ta zo ne inji dalilin da ya sa Hafsata ta aka aka maki wannan ɗanyen aikin?"
Shiga suka yi Amatullah sai tafiya take yi a hankali, wanda bai sani ba zai ɗauka yanga ne.
"Shamsiya ce a falo tare da wata ƙawarta suna fira.
Suna ganin shugabar ta su suka fara gaishe ta, ta amsa tare da tambayar ko Hafsat ta zo, suka sanar da ita cewa ba ta zo ba.
Shiga kitchen Nafeesat ta yi yayin da ta ke cewa Amatullah ta ba ta mintuna biyu, ita dai Amatullah hankalinta na wurin Abbanta da Ummanta,ba ta san ya za ta ce masu idan ta koma gida ba.
Nafeesat ce ta fito daga kitchen rike da kofin tea da ledar bread a hannunta. Miƙawa Amatullah ta yi tare da cewa
"Karɓi ki sha."
Kuka ta saka mai cin rai tana cewa
"Aunty Nafeesat ba zan iya shan komai ba, wallahi ban san inda zan saka raina ba. Me zan cew..."
Kafin ta kai ƙarshen zancenta sai ga Hafsata ta shigo, kallon juna suka yi kafin Hafsat ta ɗauke kanta tare da taɓe baki.
Nafeesat ce ta kalle ta tare da cewa
"Hafsat anya ke bil'adama ce kuwa? Anya kina da imani kuwa? Kina kishin 'yar uwarki mace Kuwa? Wane irin rashin imani ne wannan? Kin saka ta shaye-shaye sannan kuma yanzu kuma saka akayi repe ɗin ta me ye ribarki akan wannan abun?"
"Ban gane me kike nufi ba?"
"Ai dama kin faɗa sai kin yi sanadiyar da za ta rasa budurcinta ko kin mata ne? To burinki ya cika komai ya faru. Wane ne kika sanya shi ya mata wannan ɗanyen aiki?"
"Oh abinda ya faru kenan?"
"Ka da ki raina wa mutane hankali mana? "
"Bari ki ji Nafeesat, bani da masaniyar abinda ya faru, tabbas maganarki haka ne na faɗi wannan zancen kuma ko da ta zo kawo mani waya na so na idasa nufinna akanta amma sai ba ta sha lemun da ke da wannan magani ba, ta fita ni na ɗauka tana gidansu ashe akwai abinda ya faru, to ta ya ya zan san..."
"Ka da ki raina mana hankali mu ba jahilai bane da za mu yarda da abinda kike faɗa?"
"To tunda ba ku yarda ba shikenan ba abinda zan ce maku, tun farko ku je ku nemi wanda ya mata wannan aikin amma ni bansan shi ba."
Tana gama faɗar haka ta juya ta fice daga gidan gaba ɗaya.
Amatullah ce ta durƙushe a wajen tana kuka , hatta Nafeesat sai da ta zubar da hawaye
na tausayin Amatullah. Ta rasa yadda za ta yi da ita ba, ga Hafsat ta bijire mana ga shi bamu da wata hujja duk da har yanzu ina zarginta.
Kuka sosai Amatullah ke yi tare da cewa kiran sunan Abbanta da Ummanta. Na feesat ta ce,
" Bari na ce wajen masu kula da wajen na sa abinciko muna sauna wanda ya kama ɗakin."
Daga nan ta fita nan Amatullah ta cigaba da kuka, bayan kamar mintuna ashirin sai ga ta ta dawo cikin sanyin jiki, kallo ɗaya za ka mata ka gane cewa ba nasara.
Daga kafaɗar Amatullah ta yi tare da cewa
"Yanzu na dawo an bincika ba wanda ya kama wannan ɗakin, tsawon kwanaki uku ɗakin ba kowa, kuma na sa abinciko jiya ko sunga wani alamu na rashin yarda daga wani? Nan ma ba nasara."
Nan Amatullah ta miƙe bayan ta yiwa mai Nafeesat sallama , Nafeesat ta raka ta har wajen abin hawa.
Nafeesat ce ta biya shi kuma mai.adaidata .
Har ƙofar gida ya kai Amatullah ta fito ta yi tsaye ta kasa shiga gidan ga kuma tunanin me za ta ce masu kuma ga wannan kayan na jikinta wanda basu san ta da shi ba fa?
A hankali take tafiya saboda ƙasa ta har yanzu tana jin raɗaɗi.
Da sallama ɗauke a bakinta ta shiga gidan, Ummanta da ke zaune kan kujerar tsakar gida ta mike d sauri tare da zuba mata idanu, ganin kayan jikinta ba wanda ta tafi da shi ba ne ya sa ta jin wani iri. Ƙarasawa ta yi gaban Ummanta tare da durƙusawa a kan guiwar ƙafarta ta ce,
"Umma ina kwana?"
"Ba ta amsa ba ta yi shiru tare da zuba mata idanu, kuka ya ƙwacewa Amatullah ta fara magana.
Na san cewa ba za ki sake yarda da zancena ba saboda bisa la'akari da alƙawarin da na yi jiya Yau kinga na saɓa ko? Za ki yi tunanin tubar ƙarya ce na yi..."
Dakatawa ta yi jin muryar Umma na cewa
"Ina kika kwana?"
Shiru ta yi tare da yin tunani ina za ta ce masu club ko hotel? Tana tsaka da tunani kenan sai ga Abba ya fito daga ɗakinsa.
Kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kansa, tashi ta yi zata ƙarasa gabansa ya daga mata hannu.
"Ba na buƙatar jin komai daga bakinki dan duk abinda zai fito yanzu ƙarya ce, ba na buƙatar ki zo inda nake ko ki gaishe ni, tunda kin fi ƙarfin mu kin zama ƴar kanta.
Kuka ne ya ƙwace mata Abban ya fice daga gidan.
Umma ce ta kalle ta tare da cewar
"Ina kika kwana?"
Shiru ta kasa magana sai kuka kawai take yi kamar ranta zai fita, sai da Umma ta tambaye ta a karo na biyu ne sannan ta amsa mata,
da cewa.
"Umma na san na maku laifi na roƙe ku akan na daina, sai ga shi yau na sake wani laifin da ya fi na baya. Amma na maki alƙawarin cewa daga yanzu idan har na sake makamancin wannan ko na sake fita ƙodar gida ba tare da ke ce kika Umarce ni ba to a ranar duk hukuncin da kika yanke akaina na amince, wallahi ba zan sake ba karo na ƙarshe kenan da zan nemi afuwarki kan bijire maki in sha Allah."
Shiru Umma ta yi ta zuba mata idanu tare jin tausayi ta da dukkan alamu ta sha kuka dan idaninta a kumbura suke.
"Ina kika kwana?"
"Umma fita da na yi daga gidan nan kuskure ne abinda ya faru da ni ƙaddarata ce kowane bawa bai isa ya kaucewa ƙaddara ba duk abinda ya samu bawa muƙaddari ne daga Allah, ki taya ni da addu'ar Allah ya bani ikon cinye wannan jarabawar . Dan Allah Umma ki bar maganar nan wallahi ba zan sake ba."
Shiri Umma ta yi tare da zuba mata idanu yadda take ta riskar kuka, ba ta iya fushi da Amatullah, dan haka ta ce,
Daga yau idan har kika sake kada ma ki sake riƙon afuwa daga gare ni.
Girgiza kai ta yi tare da yin murmushi ta ce
"Na amince."
"Abbana fa?"
"Abbanki yana da zafi kinsan haka amma idan ya ga kin canza kin koma yadda ya san ki a baya zai sauko."
"Ina sha Allah Umma."
Tuna abinda ya faru da ita ne ya sa ta yi saurin fashewa da kuka, Umma da mamaki ta kalle ta tare da cewa
"Lafiya kukan me ye kuma na ce na yafe maki ko."
Shiru ta yi tare da cewa
"To Amma na daina."
Daga nan ta ce,
"Umma bari na shiga ɗaki na kwanta. Barci na ke ji."
"Yanzu akwai abinda za ki iya ɓoye mani? Ina kika kwana? Bayan shaye-shaye kin fara bin..."
Kasa ƙarasa maganar ta yi dan nauyinsa bakinta. Gaban Hafsat ne ya faɗi duk da ta yi ƙoƙarin dai-daita tafiyarta ko Umma ta gane ne.
Kuka ta saka tare da cewa
"Na san me kike ƙoƙarin cewa Umma kina son cewa bayan shaye-shaye ina bin maza ko? Umma kina tunanin da hankalina da tunani na zan iya bawa namiji kaina yadda na tsani mazinata, tabbas ina ƴar maye ce amma ba mazinaciya ba."
Ta ƙarasa maganar ƙirjinta na dukan uku uku
"Ina kika kwana kuma kayan da ke jikinki fa?"
"Na ƙawata ce nawa sun lalace ne kwata ce ta ɓata mani shne ta ce na canza da nata."
Tana gama faɗar haka ta yi saurin shigewa ɗaki dan kuka ne ya zo mata.
*KADUNA*
Hajiya Bilkisu ce ta shigo cikin kitchen ɗin yayin da ma'aikatan gidan ke ta aikace-aikace, kallon ma'ikatan ta yi tare da cewa ku tabbatar kun kammala komai akan lokaci, dan Alhaji ya ce ƙarfe sha biyu na rana za su ƙaraso, manyan baƙi ne ku yi hanzarin gamawa ba tare da an samu matsala ba."
Cikin girmamawa suka amsa da to, daga nan ta fice zuwa falo inda Alhaji Ibrahim Tafida ke zaune yana kallon news.
"Alhaji wai wasu baƙi ne za su zo da ka ce na sa ma'ikatq su yi girki kala-kala?"
"Mai girma Gwamna ne zai zo da kansa na so ya bari na zo na same shi sai ya nuna mani tafiyar ba tawa ba ce ta ki ce?"
Nuna kanta ta yi da yatsarta manuniya tare da cewa
"Ni kuma?"
"Eh yana neman amincewarki ne dan ki amince da cewa an tsayar da ɗanki Ajmal takarar Gwamnan jihar nan."
Take fara'ar fuskarta ta ɗauke kallo ɗaya za ka mata ka ga ɓacin ran dake kan fuskarta.
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
🤦♀️ *ƳAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Dedicated to
*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION*
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubucirsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Page1️⃣5️⃣&1️⃣6️⃣
Take fara'ar fuskarta ta ɗauke kallo ɗaya za ka mata ka ga ɓacin ran da ke fuskantarta.
"Gaskiya ɗana baza'a ɗaurawa ɗana nauyin al'ummar jahar nan ba, me ya sa bai zaɓi kowa ba sai shi kaɗai?"
"Bari ya zo sai ku tattauna wannan maganar."
Tashi ta yi ta nufi upstairs ya bita da kallo.
Dama ya san hakan ka iya faruwa, sai an yi da gaske.
Da misalin karfe goma sha biyu ne Hajiya Bilkisu ce zaune a falo saman royal chair dake falon. Sanye take da wani tsadden leshi fari an yi masa fulawa da golding colour, kunnenta da wuyanta ɗankunnen gold ne da sarƙarsa.
Kimiya ta fara jiyowa tun daga nesa har ta ji ya doso gidan nan, hakan ya tabbatar mata da cewa Gwamna ya iso.
Mayafinta golding colour dake ajiye a gefenta ta ɗauka ta tare da yafawa ta lulluɓe jikinta da shi.
Bayan kimanin mintuna biyar sai ga mijinta ya shigo da sallama, bayansa wasu security ne da baƙin kaya idninsu da baƙin gilashi, sai mai girma Gwamna ya shigo bayansa kuma wasu 'yan sanda ne hannunsu riƙe da bindigogi.
Murmishi ta ƙaƙalo tare da cewa
"His Excellency kai ne da kanka."
Murmishi ya yi tare da zama akan kujera yayin da ya zauna akan kujera masu tsaronsa suna daga bayansa.
Hajiya Bilkisu ce ta kalle shi
"His Excellency ina wuni?"
"Hajiya Bilkisu fatan na same ku lafiya?"
"Lafiya lau ranka ya daɗe."
Nan dai suka cigaba da gaisawa yayin da ta sanar da shi cewa ga abinci can an shirya masu a dinning, su fara ci.
Murmishi ya yi tare da godiya sannan ya kalle ta ya ce,
"Ammyn Ajmal ina fatan kinsan maƙasudin zuwana gidan nan ko?"
Shiri ta yi tare da jinjina kai yayin da ya ɗora da cewa
"Wa'adin sauka sauka ta daga kan mulki ya ƙarato, kuma akwai abubuwa Waɗan da na so na yi wasu kuma bann ƙarasa ba zan sauka, wannan dalilin ya sa na yi nazari wani mutum ne mai kirki da tausayin talakawa haɗin da kishin jihar shi da zan kawo dan ya yi takarar Governor? To a gaskiya ɗanki ne kawai na ga ya cancanci wannan kujera, bisa la'akari da kyawawan ayyukansa da taimakon talakawa ya yi abubuwa da yawa waɗanda kuka sani da waɗanda baku sani ba ya yi a ɓoye duk ina sane da haka. Da yawa al'ummar wannan gari da kuma karkara suna kallonsa a matsayin wani garkuwa a gare su. Na san cewa shi ba don siyasa yake abinsa ba yana yi dan Allah da manzonsa, yanzu ga misali duk ranar da yake garin nan aka ce ga shi ya dawo ƙofar gidan nan naku cike yake da jama'a talakawa masu neman taimako haka zai dinga raba masu kuɗaɗe musamman mata marasa shi, haka suke cika kamar kasuwa. Banda abincin da yake raba masu haka motocin shinkafa suke zuwa ƙofar gidan nan yake sakawa a raba masu. Ga ƙauyuka da ya inganta rayuwarsu ta hanyar yi masu hanya da ruwan sha ga wutan nepa duk a dalilinsa sun ga haske a rayuwarsu aikin da yakamata a ce gwamnati ne ta yi duk da gwamnatin ma na bakin iya ƙoƙarin ta. Bai shiga siyasa ba yake irin wannan aikin ina ga ace ya shiga siyasa? Yana da nagarta haƙiƙa zai kawo sauyi a cikin wannan jahar akwai ayyukan da na fara wanda ban samu damar ƙarasawa ba wanda ina da yaƙinin cewa zai ƙarasa abinda na fara kuma zai yi aiki tuƙuru fiye da tunani. Dan Allah ki amince masa jahar nan tamu irinsa take buƙata. Ki taimaka ki amince in sha Allah za ki yi alfahari da hakan zai share hawayen talakawa. Na yi shawara akan hakan tare da abokina kuma mijinki ya ce shi bai da matsala ya san idan ya yi wa Ajmal magana ba zai ƙi amincewa ba."
Shiru ta yi tare da sakin ajiyar zuciya tare da cewa
Ba wai na ƙi amincewa ba ne, ina duba irin nauyin mulki ne ba zai iya ɗauka ba, ba zai iya ɗaukar girman nauyin al'ummar jahar nan da kewayenta ba domin sai Allah ya tambaye shi ɗaya bayan ɗaya..."
Dady ne ya dakatar da ita ta hanyar cewa
"A halin yanzu addu'ar ki kawai yake buƙata ba wani abu ba."
"To shikenan sai dai idan har yana da ra'ayin mulki idan har ba ya da ita wannan ra'ayin ba za'a tirsasa masa ba."
Mai girma Gwamna ne ya yi murmishin jin daɗi, dan ya san cewa Indai har Dad ɗin Ajmal ya masa magana ba zai watsa masa ƙasa a ido ba."
Ɓangaren Amatullah kuwa haka ta cigaba da zama a cikin gidan Ummanta ce kawai ke kula ta Abbanta kuwa har yanzu bai sake mata ba, sai dai yanzu yana amsa gaisuwarta. Kullun aikin gida take yi ita ke gyaran gida shara wanke-wanke da girki. Idan kayan wanki Abbanta da na Ummanta sun taru ita ke wankewa.
Munnir ya kan zo lokaci lokaci sai dai Abba ya masa izinin shigowa cikin gida, daga zaune gidan suke zama su yi fira.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya komai na tafiya dai dai. Bayan watanni biyun ne Amatullah ta tashi da matsanancin zazzaɓi da kasala.
Haka dai ta yi ƙarfin halin tashi da asuba, sallah ta fara yi tare da yin azkar, ji ta yi ma gaba ɗaya ba za ta iya yin aikace-aikacen gidan kamar yadda ta saba ba.
Komawa ta yi ta kwanta nan da nan barci Mai nauyi ya ɗauke ta, a haka har ƙarfe tara na safiya ta yi ba ta farka ba. Kasancewar ita ke masu abin karya kumallo ko Umma ta fito ba ta bari ta yi, dan haka Umma ta daina fitowa.
Abba ya fito da niyyar fita daga gidan zuwa kasuwa, abin mamaki sai ya ga gidan kamar ba wanda ya fito musamman Amatullah da ya saba ganinta idan ya fito.
Ɗakin Umma ya shiga bakinsa ɗauke da sallama.
Umma da barci ya ɗauke ta a ne ta amsa a cikin barci.
"Lafiya na ga daga ke har Amatullah ba wanda ya fito?"
Tashi zaune ta yi tare da cewa
"Na ɗauka Amatullah ta fito kamar yadda ta saba, anya lafiya kuwa dan na san ita ba ma'abociyar barcin bayan sallar asuba ba ce."
Tashi ta yi ta nufi ɗakin Amatullah tare da yin sallama. Tana barci ba ta ma san ta shigo ɗakin ba.
Ganin ta na barci ya sa ba ta tashe ta ba ta fita.
Abba ta kalla ta ce,
"Barci take yi ta yiwu ba ta jin daɗi ko gajiya ne amma na san da wuya ta yi barci yanzu."
"To shikenan ni zan fita sai na dawo."
"Ko za ka bari na hura wuta na dama komo ka sha kafin ka fita kasuwar?"
"A'a kada ki damu idan na fita ba zan rasa abun siya ba, kinsan yau laraba mutanen ƙauye da wuri suke kawo muna kayan Gwari, idan ban samu da wuri ba sai da na siya wajen masu sari."
Addu'ar Adawo lafiya ta masa sannan ya fice daga gidan.
Umma ce ta yi aikin gidan sai karfe goma sha ɗaya na safe ta farka. Kasancewar ta ce wa Ummanta zazzaɓi na damun ta sai Umma ta fita zuwa Chemist ta shigo mata panadol d maganin malaria.
Washe garin ranar ma haka haka ta tashi da zazzaɓin, fiye da na baya. A ranar ma Munnir ya zo mata sallama akan zai yi tafiya zai iya kai wata ɗaya kafin ya dawo.
Ba ta yi niyyar fita ba sai da Umma ta ce ya ce wai ya zo su yi sallama ne ta fita.
Da hijabinta har ƙasa ta yi sallama ta gaishe shi, ya amsa ganin ba ta lafiya ya sa shi sanar da ita cewa zai yi tafiya nan da wata ɗaya zai dawo, kuma da zarar ya dawo ne zai turo magabata sa ayi maganar aure.
Kuɗi ya ba ta masu yawa sannan ya yi mata sallama, dan ya so su tafi asibiti amma ta ce ta samu sauƙin haka ya haƙura ya barta.
Ta nufi ɗakin Umma da niyyar ba ta kuɗin sai ta ga ba ta ciki dan haka ta nufi ɗakinta ta ajiye kuɗin ƙasan filo ta kwanta.
Abu kamar wasa tana kwanciya ta ji amai ya tunƙuro mata, a guje ta fita zuwa makwarari ta fara kwara amai.
Ko abinci ma ta daina ci idan ta ci sai amai.
A yammacin ranar bayan Mallam Abdullahi ya dawo daga kasuwa ne ya tarar da yadda take ta kwarara amai ta galabaita, a cikin kwana biyu duk ta rame ta yi fari sai idanu da dogon hancin.
Mallam Abdullahi ne ya ce su shirya a kaita asibiti,nan da nan suka shirya ya fita ya nemo mai keke napep ya zo har ƙofar gida.
Suka fita bayan sun kulle gidan ta waje ne shiga inda mai nape yake tambayar wane asibiti za su je, Abba ta ce na gwamnati zai kai su.
Nan kuwa mai napep ya ce bari ya kai su asibitin mata.
Bayan sun isa ne Abba ya biya mai napep suka ƙarasa ciki. Nan suka siye kati suka zauna zaman jiran layi ya zo kansu.
Sai da aka kira sallar magrib ne bayan Abba ya dawo masallacin dake cikin asibitin Umma ma ta yi a masallacin mata.
Wata nurse ne ta kira Umma ta ce ta shiga Doctor na son ganinta.
Ko da ta shiga Doctor na zaune a wajen zamansa yayin da Amatullah ke zaune a kujerar da masu ganin Doctor ke zama, ta haɗa kanta da teburin gabansa ta na rafsa kuka kamar ranta zai fara fita.
Da mamaki Umma ke kallon Amatullah tare da cewa
"Ke lafiya!"
Doctor ne ya kalli Ummanta tare da tambayarta
"Kece mahaifiyarta?"
"Eh ni ce likita."
"Tana da aure ne?"
"Aa ba ta da aure."
Ajiyar zuciya ya sauke tare da kallon Amatullah ya girgiza kai
"Tana ɗauke da juna biyu wata biyu da sati biyu."
Tashin hankali ba'a saka masa rana, gaba ɗaya Umma ji ta yi kamar ya watsa mata garwashin wuta a ƙoƙon zuciyarta, jiri ne ya fara neman ɗibarta, bangon office ɗin Doctor ta jingina bayanta da shi, dan idan ba haka ba faɗuwa za ta yi.
Tsawon mintuna goma suka ɗauka a haka, daga baya Doctor ne ya ce,
"Ga sakamakon gwajin da ka yi nan za ku iya fita ina da baƙi."
Amsa Ummanta ta yi tare da ficewa Hanyar ƙafa ta fice.
Doctor ne ya kalli Amatullah ya ce,
"Ki ɗan fita dan Allah wasu za su shigo."
Jiki a sanyaye ta mike ta fice ita kadai ta san irin ciwon da ta ke ji a zuciyarta
Abba na ganin fitowar Umma ta miƙe tsaye yana jiran ta ƙaraso, tana zuwa ne ya kalle ta tare da cewa
"Me ya same ta?"
"Mu tafi gida sai mu yi magana ."
Dai dai lokacin da Amatullah ta fito, cikin sanyin jiki ta ƙaraso,tafiya suka fara yi zuwa bakin gate a nan suka samu abun hawa dan komawa gida .
Bayan sun isa ƙofar gida. Mallam Abdullahi ya nufi masallaci yayin da su kuma suka shiga cikin gida.
Umma ɗakinta ta nufa yayin da ita kuma Amatullah ta yi alwala ta shiga ɗakinta.
Tana idar da sallar isha'i sai barci ya ɗauke ta mai daɗi.
*QATAR*
Zaune yake a cikin lambun tangamemen gidan, sanye mai daɗi ne yake ratsa shi. Ga kukan tsuntsaye masu daɗi idanunsa a lumshe kamar mai barci, a hankali ya buɗe idanunsa wanda cikin ƙwayar idanun nasa ba baƙi bane, ruwan tako ne. Suman kansa da ke nannaɗe irin na larabawa ne ya cusa hannunsa cikin suman kan nasa tare da yamutse gashin kan nasa tare da furta cewa
"Ni Ajmal ake ƙoƙarin ɗorawa nauyin kujerar Gwamna ta jahar ɗaya, kuma ga shi bana ra'ayin siyasar nan, ya ma aka yi suka yanke wannan shawara ne dole kawo masu shi aka yi dan na san daga Ammyna har Abbana ba mai ra'ayin siyasa, dole kawai abinda ke faruwa."
Tashi ya yi daga zaunen da yake ya nufi hanyar fita daga lambun, kai tsaye ya nufi ɓangaren Kakarsa dan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 51