cewa
"Ina Dad ɗin ka ya ke ne?"
"Ya tafi masallaci."
Tunawa ya yi dama idan an idar da sallah daga masallaci sai ya zuba yayi ta azkar karfe biyar yake shigowa gida.
Ƙarfe biyar Dad ya kalli Affan dake kwance a jikinsa yana kallon cartoon a tv.
"Affan ka ɗauki IPad ɗinka ka yi kallo da shi,ƙarfe biyar bari mu kalli labarai
Daga nan Dad ya canza channel idan ya kunna news.
Inda canzawarsa kenan ya ga an nuna fuskar Ajmal a tv.
Inda Affan ya fara tsalle sanya ga Dad ɗinsa a tv.
Hakan ya janyo gaba ɗaya hankalin kowa ga tv. Ida suka ji ana cewa.
A yau ne aka dakatar da ɗan takarar Gwamna Ajmal Ibrahim Tafida daga tsayawa takarar Gwamnan jihar nan. Sakamakon cewa yana amfani da damarsa ta hanyar lalata da 'yan mata da suke neman taimako a wajensa. Hakan ya faru ne tun ranar da ya kai wata mace asibitinsa ta haihu bayan likitoci sun yi bincike sun tabbatar da cewa ɗansa ne. Kuma yarinyar ya mata barazanar kada ta tona masa asiri hakan ya sa ta kasa faɗa. Amma bincike ya tabbatar da cewa ɗansa ne.
Wata aka nuna tana cewa tabbas ta yarinyar tana bin layi a kofar gidansa da ake rabon kuɗi.
Wata kuma ke cewa take
Gaskiya bai kamata irin wannan mutumin ya zama shugaba ba.
Wani ya ce Gaskiya idan ana fakewa da sunan taimako ana zaluntar ƙannimu da 'ya'yanmu ba.
Ganin Ajmal tsaye yana kallon tv wanda ba su san lokacin da ta shigo ba ne ya sa Ammi ɗaukar remote control ta kashe tv.
Jamal ya nufi upstairs da sauri har yana tsallake step ya nufi ɗakinsa. Zama ya yi kan gadon tare da fashewa da matsanancin kuka.
Baƙin cikinsa ba dakatar da shi ba ne, a'a yadda sunansa ta ɓaci a idanun mutane, suke masa kallon fasiƙi .
Kuke yake sosai kamar ƙaramin yaro.
A can falo kuwa bin shi suka yi da kallo.Nasreen na shirin binsa sai Ammi ta ce ta dakata yanzu ba zai saurari kowa ba.
Wayar Dad ne ke ruri, dubawa ya yi ya ga Dr Fu'ad ne ke kiransa.
Bayan ya ɗaga ne ta ce,
"Assalamu alaikum"
Daga can ɓangaren Dr Fu'ad ne zaune a falo yana kallon news idanunsa sun yi ja hankalinsa ya tashi jin abinda ake ta faɗa game da abokinsa wanda ba haka ba ne.
"Wa'alaikumus salam Dad Barka da yammaci"
"Yauwa Fu'ad barka dai ya kake?"
"Dad zan shigo bayan sallar isha'i magana mai mahimmanci zan zo da ita na yi ƙoƙari Ajmal ya saurare ni ya ƙi . Sannan idan na zo ina son a kira Ajmal da Yarinyar da aka ce ta haifa masa yaro."
Jinjina kai Dad ya yi tare da cewa
"Ba komai Allah ya kai mu."
Daga nan ya kashe wayar.
Da misalin ƙarfe takwas da rabi na dare Dr Fu'ad ya iso gidan. Kai tsaye part ɗin Dady ya nufa, knocking ya yi aka bashi izinin shiga.
Dad da Ammi ne zaune a falon, ya shiga bakinsa ɗauke da sallama.
Suka amsa masa ya shigo ya durƙusa cikin girmamawa ya gaishe da su. Suka amsa masa cikin sakin fuska da walwala.
Zama ya yi tare da cewa
"Dama akwai abinda ba ku sani bane na ke son sanar da ku, duk da cewar Ajmal bai sauraren ba."
Nisawa ya yi tare da cewa
"A kira su dukkansu."
Ammi ce ta kalle shi tare da cewa
"Me ya saka har da yarinyar?"
Murmushi ta yi tare da cewa
"Akwai wasu tambayoyi da zan mata ne."
"Hajiya Bilkisu ta dauki waya ta kira Ajmal ta sanar da shi cewa ya zo falon Dad ɗinsa. Bayan ta kashe wayar ta sanar da shi ne ta kira wayar Iya mai kula da Amatullah ta sanar da ita cewa ta kawo Amatullah da jaririnta ɓangaren Dad.
Bayan kamar mintuna biyar sai ga Ajmala ya zo, bakinsa ɗauke da sallama ya shigo, idanunsa jajir na kuka da ya yi ya koma kamar ba shi ba.
Ganin Dr Fu'ad ya sa ya tsuke fuska tare da cewa
"Me ya kawo ka nan?"
Bai tanka masa ba haka. Ya sa Ajmal cewa
"Tashi ka fita kafin na nuna maka ainihin kalata."
Kallon gargadi da Amminsa ta masa ne ya sa ya samu wuri ya zauna.
Ba wanda ya sake cewa komai zuwa can suka ji knocking, hakan ya sa Ammi tashi ta isa ga kofar ta buɗe.
Iya ce riƙe da jariri sai Amatullah da ke bayanta tana sanye da da hijabi har ƙasa. Ammi ce ta karɓi jaririn sannan ta ce wa iya ta tafi ta bar su a nan.
Sallama ta masu ta tafi.yayin da Ammi ta shiga falon ɗauke da jariri Amatullah na bayanta.
Ammi ra zauna gefen Dad yayin da Amatullah ta rakuɓe can gefe, Ajmal da Fu'ad ne zaune saman Centre carpet.
Ammi ce ta kalli Amatullah tare da cewa
"Ƴata tashi a nan wajen akwai sanyin tile ga shi kina jego, tashi ta yi zata zauna gefen Ajmal wani mugun kallon da ya mata ne ya sa ta ja baya ta koma gefen Fu'ad ta zauna.
Ammi ta miƙa mata fili tare da cewa
"Ki zauna anan."
Amatullah ta zauna kan kujera tare da cewa
"Na gode."
Tunawa ta yi bata gaishe su ba haka ya sa ta gaida Dad sai Ammi sannan ta gaida Ajmal ko kallon banza ba ta ishe shi ba ballantana ya amsa, ta gaida Dr Fu'ad ya amsa cikin sakin fuksa.
Dr Fu'ad ya yi ajiyar zuciya tare da cewa
"Ya sunanki?"
"Sunana Amatullah."
"Daga wane gari kike zo nan?"
"Garin Minna Niger state."
"Kin Sanni?"
"Na dai taɓa ganinka sau ɗaya."
"A ina kika taɓa gani na."
"A mazanya Hotel."
" Me kika je yi hotel ko dama can kike zaune?"
"A'a wata ƙawata ce ta na je kaiwa waya bayan na kai mata ne na fito na haɗu da kai kana fitowa daga wani ɗauki da ke a cikin hotel ɗin."
"Za ki ita tuna kwanan watan ranar?"
Shiru ta yi tare da dogon tunani. Kafin ta ce,
"25 ga watan October."
Murmushi ya yo tare da cewa.
"Yau nawa ha wata muke?"
Ba tare da ta kalle shi ba ta ce,
"18 ga watan August."
"Yau kwanaki nawa da haihuwa?"
"Yau kwana uku."
"Daga ranar 25 ga watan October zuwa ranar sha biyar ga watan August da kika haihu tsawon watanni tara da kwana goma kenan ko?"
Jinjina kai ta yi alamar eh.
Jinjina kai ya yi tare da kallonsu ɗaya bayan ɗaya kafin ya maida kallonsu zuwa ga Ajmal.
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
09065327995
*Idan kun yi comments ku ga posting kullum, idan kun yi shiru ku ga shiru*
🤦♀️ *YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
Ban yarda a karanta mani shi a youtube ko a maida shi audio ba tare da izinina ba.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Page4️⃣4️⃣
Jinjina kai ya yi tare da kallonsu ɗaya bayan ɗaya kafin ya mai da kallonsa ga Ajmal.
"Idan ba ka mance ba ranar ashirin da uku ga watan October na kira ka lokacin kana ƙasar Qatar."
"Mun yi magana akan cewa ka zo washe gari ranar ashirin da huɗu ga wata, saboda ranar ashirin da biyar ga wata za'a ɗaura auren abokin Kamal."
Nisawa ya yi sannan ya daura da cewa.
"Sai ka nuna mani cewa baka so ka zo ƙasar Nigeria a wannan lokaci, saboda Amminka za ta riƙe ka ne sai ka kwana biyu wanda a lokacin kuma akwai aikin da kake yi, kuma kana buƙatar komawa cikin gaggawa. Bayan haka ma Amminka tana ganin kamar babu wata kyakkyawar mu'amala ko zamantakewa mai dad'i tsakanika da Nasreen. Ita kullun magana take akan baka samu kwanciyar hankali da nutsuwa kamar kowane cikikakken magidanci ba, hakan ya sa ta ce ka ƙara aure. Wanda kai kuma baka da ra'ayin ƙarin aure. Na ce to tunda haka ne ka zo kawai tunda a garin Minna za'ayi bikin idan an gama sai ka koma ba sai ka je Kaduna ba."
*WATANNI TARA DA SUKA WUCE*
Dr Fu'ad yana driving kan hanyarsa ta zuwa ɗaukar Ajmal a airport. Wayarsa ce ta yi ruri, ganin Ajmal ke kira ya sa shi cewa.
"Afuwan na kusa ƙarasowa."
Daga nan ya katse kiran wayar ya na murmushi.
Bayan ya isa airport ne ya hangi Ajmal na saukowa daga jirgi. Yana rataye da jakkarta. Bayan ya sauko daga matattakalar jirgin ne ya ƙarasa wajen Dr Fu'ad.
Cikin farin ciki Dr Fu'ad ya rungume shi tare da masa sannu da zuwa.
Bayan sun shiga mota ne Ajmal ya kalle shi tare da cewa.
"Hankalinka ya kwanta na zo bikin auren Kamal ko?"
Murmushi Fu'ad ya yi tare da kallon Ajmal kafin ya mai da kallonsa ga riƙon da yake yi.
"Ai gani na yi ya kamata a ce ka zo ne, dan dukkan abokan mu da kowa na nan kai kaɗai ne ba ka nan. Ta ya ya bikin zai yi armashi?"
"Yanzu dai ba wannan ba, ka san cewa ba wai na san garin nan sosai ba ne, ina zan samu masauki?"
"Wane irin masauki?"
"Hotel mana."
"Ba sai ka je hotel ba, ai a gidan Jamal akwai ɗakuna sannan nima a nan nake."
"Gaskiya ba na son takura wallahi, na fi son na kama ɗaki ni kaɗai."
"To ba damuwa yanzu bari mu ƙarasa wajen sauran abokan ku gaisa ka huta ko?"
Ajmal ba sake wata magana ba har suka isa gidan Kamal.
Kai tsaye ɓangaren Kamal suka nufa, a nan suka tarar da Kamal da sauran abokan ango. Nam suka rungume juna.
Nan dai aka kawo wa aka kawo masa abinda zai ci da na sha.
Fira suka yi sosai na yaushe gamo da juna, ganin lokacin sallar magrib ya yi ne ya sa Ajmal shiga ban ɗaki ya yi wanka ya sauya kayan jikinsa.
Masallaci suka nufa suka yi sallar magrib, wanda sai da aka yi sallar isha'i sannan suka dawo gidan.
Nan ma suka cigaba da fira sosai kamar ba za su sake haduwa ba, kafin su ankare har ƙarfe sha ɗaya na dare ya yi.
Nan dai Najeeb da Yaseer suka miƙa tare da kallon Kamal suka ce .
"Mu za mu ƙarasa gida."
Kallonsu Fu'ad ya yi tare da cewa
"Gara kam ku tafi dan wannan bikin lami ne, ba wani shagali ba ko zuwa reception daga ɗaurin aure sai walima."
Murmushi Ajmal ya yi tare da cewa
"Ya hutawa kansa ai."
Najeeb ya ce,
"Wani hutu kuma? Ai ya kamata a ce akwai wani ɗan dinner ko lunching da aka shirya, amma da an yi walima an d'aura aure shikenan? Kamar ba wani wayayye ba."
"Eh na ji ban waye ba, ba komai, ba ruwana bidi'a nikam, aje ayi ta raye-raye da kaɗe-kaɗe an gayyato shaiɗanu su zo wajen bikin ba da ni ba."
Yaseer ya ce
"To ai shikenan"
"A tara malamai su yi mata wa'azi akan zaman aure da yadda za ta kula da ni, ta san duk wasu hakkoki da ke kanta ayi mana addu'a na zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba."
Fu'ad ya yi dariya tare da cewa
"Daga nan kuma fa sai me?"
"Sai a tara jama'a a ɗauka mana aure a shafa fatiha kowa ya watse. Daga nan sai a kai mani matata gidana."
Dariya suka yi gaba ɗaya tare da masa fatan alkhairi.
Daga nan Najeeb da Yaseer suka yi masu sallama suka tafi.
Daga Kamal ango sai Ajmal da Fu'ad suka rage, yayin da Kamal ya gyara kwanciyarsa akan kujerar mai zaman mutum uku.
Ajmal ya kalle su tare da cewa ni fa hotel nake son kwana.
"Wane irin hotel ana zaune lafiya."
Jamal ya ƙarasa maganar yana tashi zaune. Fu'ad ya ɗora da cewa
Rabu da wannan balaraben ba hotel ɗin da zai kwana, tun muna bayanta yake ta magana a kan kama masauki na ce ba inda zai tafi."
"Gaskiya kam, ai bai kamata ba."
"Kwantar da hankalinka ango, ba sai ka ɓata bakinka ba akan masa magana, domin kana ganinshi nan duk yawace-yawacensa a faɗin duniyar nan wai bai taɓa zuwa jahar nan ba."
Dr Fu'ad ya yi maganar yana 'yar dariya.
"Haba kalli kuwa na ji dadi tunda a dalilina ka bar wata ƙasa ka zo jahar da baka taɓa zuwa ba."
"Rabu da shi kawai ai koasaukin yake nema a matsayinsa na baƙo a garin nan bai san ta ina zai fara neman masauki a wannan daren da na san ƙafa sun fara ɗauke wa."
"Ka da ku damu tunda kun hana ni yau ai gobe in sha Allah ba za ku hana ni ba, dan tun da wuri zan nema da zaran an gama ɗaurin aure zan nema ne, idan na kwana washegari zan koma ƙasar Qatar."
"Ba za ka tafi Kaduna ba kenan?"
Murmushi ya yi tare da cewa
"Bana son Ammina ta san na zo ne, ba wanda ya san da zuwa na sai kai da Fu'ad sabis tafiyar sirri ce."
Dariya suka yi dukkansu inda Kamal ya ɗora da cewa.
"Yadda kake da Amminka ta ke ji da kai ne za ka iya zuwa ƙasar nan ba tare da ka je wajenta ba?"
"Bari kawai idan na tafi to kila sai dai ku ji labarin ɗaurin aure na."
Dariya suka masa tare da cewa
"To me ye a ciki?"
"Ba za ku gane ba ne guys."
Dr Fu'ad ne ya yi saurin cewa sai dai idan ba ka ganar da mu ba.kai gara ma a ce ta sake maka wani auren, dan kai wai kana da aure kenan kake zama kamar wani gwauro."
"Kai wai kana nufin har yanzu Nasreen tana can US ne?"
Taɓe baki Fu'ad ya yi tare da cewa
"Na rasa wace iriyar mace ce Allah ya ba shi, wai kin yi aure amma ba ki rabu da gidan iyayenki b? Tunda ka yi aurenta da Ajmal aka kawo ta Nigeria ya zo da ita ko cikakken wata ɗaya ba ta yi ba ta koma gaban iyayenta, ko ta zo inda yake sati biyu ya yi yawa za ta koma gidan iyayenta, can california. Da Ajmal ya ga kamar tafi son ƙasar hakan ya sa shin ya koma ƙasar ya nemi gida dan dai kawai su kasance tare, amma dake ba rayuwar auren na a gabanta ba taƙi zaman gidan nasa, sai ta tafi gidan iyayenta ta wuni wata tana har ta kwana ta barshi shi kaɗai."
Jinjina kai Kamal ya yi tare da cewa
"Lallai Amminka na da gaskiya sosai kuwa, dole ta ce sai ka kara aure."
Tashi ya yi ya barsu dan shi baya m sha'awar sake yin wani auren.
Nan dai suka cigaba da tattaunawar su kafin Fu'ad ya tashi ya nufi bedroom.
Nan ya tarar da Ajmal baya dakin sai dai ya ji saukar ruwa a banɗaki, da alama wanka yake yi.
Idanunsa ne suka sauka akan wasu ƙwayoyin Magani da robar ruwa a gefe. Ajmal ne ya sha maganin Sannan ya shiga toilet."
Kallon maganin yake da mamaki sannan ya samu wuri ya zauna yana jiran fitowarsa.
Bayan ya fito daga wanka ne Dr Fu'ad ya lalle shi tare da cewa.
"Me ya haɗa ka da wadannan ƙwayoyin ne?"
Kallon maganin ya yi tare da cewa
"Da matsala ne?"
"Amma ai kai kana da aure bai dace ace kana amfani da shi ba."
"Hmm ai bana da banbanci da wanda ba ya da aure ba."
"Lallai akwai matsala tunda har ba ka iya jurewa sai ka haɗa da wannan magunguna akwai matsala."
Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa
"Tun yaushe ka fara shan wadannan magunguna?"
"Tun kafin na yi aure."
"Kuma ko da ka yi aure ba wani canji?"
"Ba wani canji hasalima matsalar ta fi yawa bayan na yi aure."
"Amma gaskiya na tausaya maka, irin haka idan ba tsananin tsoron Allah da kau da kai ba sai ka fara bin matan banza."
" Shi ya sa nake yawan azumin Litinin da Alhamis."
"Gaskiya da sake wannan rayuwar ba zata yiwu a haka ba, dole ka nemi mafita ta hanyar neman wata mace.
"Kaga mu bar wannan zancen haka nan."
Jinjina kai ya yi tare da cewa
"Shikenan tunda haka ka faɗa."
Washegari da misalin ƙarfe biyu na rana aka shaida ɗaurin auren Kamal Idris da Kamila Sa'id akan sadaki naira dubu ɗari biyu da saitin akwatuna.
Ajamal ya bawa Kamal gudunmawa na bikin naira dubu ɗari biyar. Dr Fu'ad ya ba shi naira dubu ɗari biyu.
Bayan an kammala ɗaurin aure aka yi walima na mata a gida. Da yammacin ranar aka kai amarya gidan mijinta.
Bayan sun raka ango ɗakin amaryarsa ne aka yi siyen baki suka watse. Har wata daga cikin ƙawayen amarya ta nuna tana son Ajmal . Ganin bai sakar mata fuska ba ne ta kama kanta. Duk da cewar ba ita kadai ta kamu da sonsa ba, amma ita ce ta bayyana, sauran matan kuwa gani suka yi yafi ƙarfin ajinsu.
Kasancewar dama Fu'ad ya kama masu hotel ne ya sa daga rakiryar ango suka wuce hotel ɗin.
Fu'ad ne ke driving motar yayin da Ajmal ke zaune a gefensa.
Sai da suka tsaya a hanya suka siye abinda za su ci kafin suka tafi.
A harabar hotel ɗin ya yi parking suka fito, Ajmal ne ya tsaya yana kallon hotel ɗin tare da yamutse fuska ya ce,
"Ni fa wannan hotel bai mani ba."
"Ya kake so ayi yanzu?"
"Gaskiya wannan wajen sai a hankali, ba zan iya..."
"Kaga Mallam duk wannan yanzu ka ajiye kwana ɗaya kacal zaka yi a nan ba kwanaki ba, dan haka ka daure kawai mu shiga daga ciki."
"Ya tsaftar ɗakin?"
Ka da ka damu za ka so ɗakin?"
"Gaskiya suna da tsafta sosai."
"Mun shiga daka ciki na gani."
Fita suka yi suka nufi cikin.
Ɗakuna biyu da ke jere suka kama Ajmal ɗaya Fua'ad daya.
Bayan sun shiga ɗaya daga cikin ɗakin ne Fu'ad ya kalli Ajmal tare da cewa
"Wannan ne ɗakinka kenan. Wanda ke gaban naka shi ne nawa ɗakin.
"Af na mance bari na ɗauko abinda muka siya a hanya, na manta da shi a cikin mota."
Daga nan ya fita ya bar Ajmal yana ƙarewa ɗakin kallo.
Har ya dawo Ajmal na tsaye bai zauna ba. Ajiye masa leda ɗaya na kazar ya yi tare da lemun da ruwa sannan ya juya har zai bar ɗakin sai ya juyo ya kalli Ajmal, ganin kamar yana cikin damuwa ne ya lalle shi tare da cewa.
"Lafiya kuwa?"
"Ba komai."
"Na ga kamar kana cikin damuwa."
"Eh gaskiya kam ina cikin damuwa."
"Ko zan iya sanin me ke damu ka?"
"Ban san yadda zan maka bayani ba."
Ya ƙarasa maganar yana cije laɓɓansa na ƙasa.
Murmushi Fu'ad ya sake tare da cewa.
"Na fahimta, ka da ka damu kai zai yi daidai."
Har ya buɗe ƙofa zai fita ya ji muryar Ajmal na cewa
"Ko zan iya samun coffee?"
Murmishi ya yi tare da cewa .
"Bayan coffee ba ka bukatar komai, ko na haɗo maka da zazafar cika 'yar shila wacce za ka rage zafi da ita?"
Harara ya banka masa tare da kau da kansa.
Fu'ad ya fita yana dariya.
Dawowa ya yi tare da cewa.
"Idan na saka aka kawo maka coffee ba sai da safe za mu haɗu? Dan zan tsaya a club ɗin da ke cikin hotel ɗin nan na ga ana casu."
Daga nan ya fita daga ɗakin ya ja masa ƙofa.
Tunda daga nesa ya hangi Amatullah sanye da doguwar hijabi har ƙasa, fuskarta babu walwala sam, hannunta riƙe da waya tana kallon wayar tana tsuki.
Gaba ɗaya Dr. Fu'ad ya shagala da kallon Amatullah, murmushi ya sake tare da ƙarasawa wajenta.
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi e
(Maman Ihsan)
09065327995
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
🤦♀️ *YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
Ban yarda a karanta mani shi a youtube ko a maida shi audio ba tare da izinina ba.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Page4️⃣5️⃣
Gaba ɗaya Dr Fu'ad ya shagala da kallon Amatulla, murmushi ya sake tare da ƙarasawa wajanta
"Assalamu alaikum"
Ba tare da ta kalle shi ba ta amsa xa da
"Wa'alaika salam."
"Ga ki da alama kamilalliyar yarinya ce me ya kawo ki hotel?"
Sai a lokacin ta kalle shi tare da cewa.
"Dama mutanen ƙawarai ba sa zuwa nan ne?"
"Ba haka nake nufi ba, na ganki da kamala ce kuma wallahi tunda na kalle ki sai..."
Ba ta tsaya saurarensa ba ta wuce ta nufi ɗakin da Hafsata take da niyyar kai mata waya.
Ɗaya daga cikin ma'aikatan hotel ɗin ne ya gani yana waya, tsayawa ya yi yana jiran ya kammala, inda ya ji yana cewa.
"Ka da ki damu na shirya komai kamar yadda kika buƙata ba za'a samu akasi ba."
Kashe wayar ya yi tare da kallon Fu'ad ya ce,
"Akwai abinda kake so ne yallaɓai?"
"Akwai abokina yana ɗakin da muka kama."
Jinjina kai ya yi tare da cewa.
"Na sani akwai abinda yake bukata ne?"
"Yana bukatar coffe yanzu bayan haka ka tambaye shi bayan shi ko akwai wani abun, dan yana da ɗan damuwa pls ka hanzarta."
Daga nan ya wuce zuwa club. Yana zaune ana ta raye-raye da kaɗe-kaɗe, ma su shaye-shaye suna ta yi.
Nan ya raba dare sai ƙarfe biyun dare ya tashi ya nufi ɗakinsa, dan ya san a lokacin AJMAL ya yi barci, dan haka ya nufi ɗakinsa da ke kusa da na Ajmal.
Kasancewar bai yi barci da wuri ba ya saka ya makara sai da gari ya fara haske ya farka , mamaki ya ke yadda lokaci ya tafi ga shi ko sallah bai yi ba.
A gaggauce ya tashi ya faɗa toilet ya yi wanka tare da alwala ya fito. Sallar asuba ya gabatar sannan ya fito.
Ɗakin Ajmal ya nufa, knocking ya yi ya ji shiru, hakan ya saka ya tura ƙofar ya shiga.
Turus ya tsaya tare da furta kalmar.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un."
Ajmal ya gani kwance ta mace akan gado, duk da bargo ya rufe jikinsu amma da dukkan alamu babu kaya a jikinsu, suna kwance dab da juna sai dai Dr Fu'ad bai ga fuskarta ba, saboda tana da tsawon gashi duk ya yamutse ya baje a saman fuskarta. Hakan ya saka bai ga fuskarta ba."
"Ajmal ne nake gani haka?"
Ganin dukkansu da alama basa cikin hayyacinsu ne ya saka shi ƙarasawa, cikin tashin hankali ya fuskarsa ya duba ya gane akwai matsala. Yarinyar ma da alama ba ta cikin hayyacinta. Ganin haka ya saka ya Sakawa Ajmal kayansa tare da ɗauko shi suka nufi dakin da Fu'ad ya kwana. Kwantar da shi ya yi a saman gadon sannan ya koma can ɗakin ya ɗauki jakar Ajmal da wayarsa.
Kasancewar ɗakin duka komai iri daya ne gado labulaye sofa da komai, idan ba ka duba lambar ɗauki ba ba za ka gane cewa ba ɗakin ba ne.
Fita Fu'ad ya yi ransa a ɓace ya nufi reception ɗin. Zuba idanu ta yi yana duba wanda ya aika ɗakin Ajmal bai gan shi ba. Tambaya ya yi dan bai ga sauran abokan aikinsa ba, wadanda ke wajen ya tambaya aka je ƙarfe bakwai suka tashi daga aikin. Sauran wadanda ke nan yanzu suka zo suka karɓi wad'ancan.
Haka ya kasa komai ya koma ɗakin daidai lokacin da ya ga Ajmal na bude idanu tare da yamutse fuska yana dafa kansa.
Bibbiyu yake ganin shigowar Fu'ad kafin ya koma gani daidai.
"Fu'ad ka shigo ko? Wai har gari ya waye ne baka tayar da ni na yi sallah ba?"
Shiru Fu'ad ya yi yana kallonsa.
"Kaina ke masifar ciwo sosai, ban taɓa jin irinsa ba."
"Ka tashi ka yi wanka sai ka yi alwala, idan ka idar da sallah sai a kawo maka breakfast ka sha magani."
Tsayawa ya yi yana tunani wane irin mafarki ya yi ne haka, sai kawai ya basar dan ya san cewa shi kaɗai ne kuma ya san yanayinsa.
Kqllonsa Fu'ad ke yi tare da cewa
"Akwai wani abu ne?"
Girgiza kai ya yi tare da cewa
"Nothing, kawai ka tashan ka yi wanka, sannan har da wankan tsarki ma ka yi."
Kqllonsa ya yi da mamaki tare da cewa.
"Wankan tsarki? Me ya sa ka ce na yi wankan tsarki?"
"Ba komai kawai na yi tunanin ka yi mafarki ne har ka yi..."
Shiru ya yi tare da cewa
"Tashi ba lokaci."
"Kamar ko ka sani wani mafarki na yi wai Nasreen ta biyo ni nan ɗakin."
Fu'ad kasa magana ya yi dan abin da mamaki, ya aka yi abokinsa ya faɗa farko haka? Ko dai yarinyar ce ta masa wani abu?
Haka ya dinga tambayar kansa har Ajmala ya tashi ya shiga banɗaki, ganin yadda jikinsa ya kenya a ya fara tsarkake jikinsa kafin ya yi wanka ya ɗauro alwala.
Har lokacin Fu'ad na inda ya barshi tsaye."
"Lafiya kai kuma har yanzu? Ka gama shirinka ne ka biyo mani? Ga shi na makara yau."
Sauri sauri ya goge ruwan jikinsa, tare da yin tsuki.
"Me ya faru kake tsuki?"
"Wallahi ba abun busar da kai da zan busar da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 51