shi karfi nesa ba kusa ba. Ganin haka ya sa ta rab'a ta gefen shi ta wuce dan dama ta yi mamaki ganin yadda ya kai hannu yana kokarin rike mata hijabi.
Ganin ta wuce ne ya sa Ajmal ya saki hannun Munnir tare da masa wani Kallo mai cike da gargadi. Wajen motarsa ya nufa inda Amatullah da Ahmad da ke tsaye suna kallonsa ya k'arasa.
Kallonta ya yi tare da cewa
"Ki shiga mota."
Kallon Munnir ta yi wanda shima su yake kallo sannan ta sunkuyar da kanta kasa ta kasa shiga motar, Jin muryar Ajmal ta yi yana cewa.
"Kina jiran sai ya baki izini ne?"
Yana fadar haka ya shiga gaban motar ita ma ta shiga ganin haka ya sa Munnir yin sallama ya shiga gidan nasu, dan dama baya da shamaki da gidan.
Umma da ke zaune a tabarma ce ta amsa masa sallamar tare da masa sannu da zuwa. Durkusawa ya yi ya gaida Umma ta nuna masa tabarma dake shimfide a gefe ya zauna .
"Umma ya karfin jikin naki ne?"
"Da sauki Munnir ya kokari?"
"Alhamdulillah."
Abba ne ya k'araso wajen tare da yi wa Munnir barka da zuwa, suka gaisa tare da tambayarsa aiki da mutanen gidan, ya amsa da Alhamdulillah.
Nan ya masu murna da dawowar Amatullah, Abba ya Kalli Umma ya ce
"Ina Amatullah take?"
"Ta fita suyi sallama ne da yaron."
A cikin motar kuwa Ajmal kasa cewa komai ya yi, sai dai ta lura yanayinsa da fara'a da annurin dake kan fuskarta sun gushe.
Jin ya kasa cewa komai ne kuka ga Munnir da ya zo yana jiran su gaisa ne ya sa ta ce.
"Ya Ajmal lafiya kake kuwa?"
Kyawawan idanunsa masu d'auke da nasaba ya zuba mata, har lokacin ya saka cewa komai, ganin irin kallon da yake mata ne ya sa ta yi saurin cire idanunta daga nashi, dan tsabar kwarjinin da yake mata. Cikin disashshiyar murya Mai kama da Wanda mura ya kama ya ce.
"Me kika gani kike tambaya ta?"
"Na ga ba yadda muka zo kake ba, ka sauya kamar Abu na damunka."
Ta yi maganar tana wasa da yatsun hannunta da suka ji Jan lalle, zara-zaran yasun hannunta yake Kallo sannan ya ce.
"Waye shi?"
Cikin rashin gane me yake nufi ta ce.
"Wa ke nan?"
"Waye ya kai hannu ya rike ki?"
Turo baki gaba ta yi tare da cewa.
"Ni ba rike ni ya yi ba hijabina zai rike Kuma ai ka rike hannunsa, Munnir ne sunansa Wanda na taba fad'a maka Abbana ya bashi izinin zuwa wajena zance.
Cije leb'e ya yi sannan ya ce.
"Dan an bashi izinin zuwa zance shine zai rike hijabin ki, to ki ja masa kunne kada ya sake yunkurin kai hannunsa zuwa jikinki, dan yau hannunsa na rike idan kuwa na sake gani hannun zan karya."
Ransa ya gama baci sosai dan ba iya rike hijabin ne ya bata masa rai ba har da kishi Musamman yadda ya ga suna yi wa junansu murmushi.
Ba tare da ya kalle ta ba ya ce.
"Jibi zamu tafi amma gobe zan dawo idan kawai abubuwan da kike bukata naki da na baby ki sanar da ni."
"Ba mu bukatar komai yanzu."
Shiru ya yi kafin ya kalle ta ya ce.
"Duk abunda kike bukata na ki ko na Kika San baby na bukatar ki sanar da ni, ba sai kin tamabayi kowa ba sannan Kuma kada wani saurayin ya baki abu ki karba ko ma mene ne, matukar ba Abba ko Umma ne suka baki ba to ban yarda ki karbi abu daga hannun wani ba, ko me kike so zan maki shi ba zan rage Ku da komai ba, sannan ban yarda ki dinga fita zuwa ko ina ba sai dai idan da izinin Abba da Umma Wanda fitar sai ta kama dole dan bana son yawo kema kin sani."
Kallonsa take yi ta kasa cewa komai tana mamakin Iko da karfin hali irin nasa, duk da yanzu a gaban iyayenta take amma sai ya saka mata doka kamar a gabansa take.
"Idan ka gama ni zan shiga ciki ko gaisawa da Umma sosai ban yi ba, kace na fito muyi sallama sai kuma kana ta kafa mani dokoki ko ka mance yanzu a gidanmu nake?"
"Na sani a gidanku kike Kuma ki kiyaye abunda na fad'a maki duk da bana garin ki d'auka duk abunda kike yi akan idona kike yi."
Ba ta ce komai ba ta fita tana mamakin karfin hali irin nasa.
Fitowa ya yi daga motar yana kallonta har ta shige ciki, sanan ya shiga bayan motar Ahmad ya ja suka bar wajen.
Tana shiga ciki da sallama a bakinta, suka amsa mata inda ta zauna a tabarma ta gaida Munnir cikin fara'a sai ta ji ya amsa mata a takaice ba walwala a fusakarsa.
Umma ce ta kalle ta ta ce
"Karbi yaronki na tashi na shiga na kwanta na huta."
Sai a lokacin Munnir ya gane yaron Amatullah ne, dan ya d'auka ko makota ko bakuwa suka yi, kallon yaron ya yi ya ga tsantsar kamanninsa da ubansa Ajmal, take ya ji wani malolon bakin ciki a zuciyarsa, tana karbar yaron Umma ta basu waje dan su yi zance a tsakaninsu.
Matsawa ta yi a tabarmar da yake zaune ta ce.
"Ya Munnir."
Kallonta ya yi ba tare da ya amsa ba yana jiran me za ta ce.
Shima gani ta yi fusakarsa ba walwala amma sai ta daure ta ce.
"Wannan shine kaddarar da Allah ya kaddaro mani, ka gan shi nan, sunansa Abdallah watanninsa uku yanzu."
A tuanininta zai karbi yaron daga hannunta amma sai ta ga ya kau da kai ko kallonsa bai yi ba, Hakan ya sa ta ji jikinta ya yi sanyi. Sai Jin muryarsa ta yi yana cewa
"Allah ya raya shi."
Ta amsa da Ameen.
Tunda na ganki lafiya zan tafi gobe in Sha Allah zan dawo dan akwai magana Mai mahimmanci da ya kamata mu tattauna."
"Allah ya kai mu."
Ta fad'a cikin sanyin jiki."
Sallama ya masu ya tafi.
Kasancewar yamma ta yi Hakan ya saka ta shiga kitchen bayan ta goya Abdallah, dubawa ta yi akwai abubuwan bukata Wanda za ta yi amfani da su, Hakan ya saka ta debi garin danwake ta hada ta kwaba, dama akwai garin dakakkiyar barkono da Mai Hakan ya saka ta yi danwake cikin kankanin lokaci ta kammmala, wanka ta yi wa Abdallah ta shirya shi sannan ta kwantar da shi ganin yana Jin barci.
Bangaren Nasreen kuwa farkawarta ya yi daidai da komawar Ajmal hotel din, inda nan ma ya tarar da sabon tashin hankali sosai ba kadan ba, Dan yadda kasan mahaukaciya haka ta koma, ga haushinsa take ji yadda ya bari Amatullah ta tafi bayan ta kuntata mata, nannya dinga rarrahin ta tare da mata dad'in baki har ta tsagaita kukan da take yi, ba ta tambaye shi akan soyayya da yake yi wa Amatullah ya nuna mata ba wannan zancen sannan ta hakura amma can k'asan zuciyarsa ya San dai ya biye mata ne kawai Dan a samu masalaha. Affan dam yana tare da kakarsa wato Ammi.
Ajmal da kansa ya kai ta toile ya hada mata ruwan wanka ya taiamka mata ta yi wanka suka fito, da taimakonsa ta shirya tsaf Dan ya kwantar mata da hankali.
Bayan sallar isha'i suna zaune a tsakar gidan suna cin danwake da Amatullah ta yi masu, Abba sai tsokanar Umma yake yi wai daga dawowar Amatullah ta warke, kamar ba ita ke ciwo ba, dariya ta yi tana cewa.
"Dama ita ce magaanin cutar tawa kuka ta dawo na warke."
Amatullah farin ciki ne ya lullub'e ta mara misaltuwa, sai murmushi take yi na farin ciki, Abdallah na d'akin Amatullah kwance akan gadonsa yana barci, an lullub'e sa da net dake jikin gadon babyn.
Washe gari da misalin k'arfe goma Sha d'aya na safe motoci guda biyi suka yi parking k'ofar gidan Mallam Abdullahi.
Ajmal ne da Ahmad a cikin motar sai wata motar da suka zo da ita Wanda d'aya daga cikin direbobinsa ya tuko.
Wayarsa ya ciro ya kira lambar Amatullah Dan ya sanar da ita cewa ta fito yana waje, sau uku yana ringing ba'a daga ba, Hakan ya faru ne Sakamakon Amatullah ta ajiye wayar a d'aki ta shiga wanka, kasancewar band'akin gidan a waje yake, Abdallah na d'akin Umma yana barci.
Sam bata San ya kira ba tana fitowa man shafawarta ta shafa Mai kamshi, ta shafa turaren jiki ta saka wata doguwar rigar abaya.
Tana tsaka gyara gashin kanta ne wajen tufke shi da ribbon ta ji sallamar yara, ta amsa ba tare da ta San ko waye ba.
Yara ne Ajmal ya samu daga waje ya ce su shigo da kayan da ya kawo, nan yaran suka fara shigo da kayan abinci.
Buhun shinkaga biyu katon sun taliya biyi na macaroni ma biyi buhun farin shinkafa na tuwo ma biyiy, su kwalayen indomie da su jarakunan Manja da man gyada, su kwalin magi katon din madarar ruwa, Dan kayan tea manyan gwangwanayen Madara da Milo da kwalayen suga da su kwai haka ya jido su.
Sai kuka kayan gwangwanayen kunun Abdallah da madararsa da wasu takarce da pampers duk ya siyo su.
Umma ta fito ganin yawan kayan ta rude take tambayarsu daga ina, yaran suka ce wani ne daga waje ya aiko mu, sannan ya ce wai mu ce wa Amatullah ta zo inji Ajmal.
Umman ba ta San waye Ajmal ba daidai lokacin da Amatullah ta fito tana yafa mayafin abayar dake jikinta Umma ta kalle ta tare da cewa.
"Waye Kuma Ajmal?"
Amatullah ta nuna Abdallah dake rungume a hannun Ammi ta ce.
"Babansa ne ya zo."
Sai a alokacin Umma ta San sunan Ajmal, mamakin yawan kayan take tana cewa
" kayan nan ai sun yi yawa."
Amatullah flat shoe ta saka ta nufi hanyar waje dan itama kayan sun bata mamakin yawan su.
Ahmad da wani bodyguard nasa suna waje shi Kuma yana bayan motar yana danne-danne a wayarsa.
Da sallama ta k'arasa wajen motar ta gaishe da Ahmad da dayan bodyguard din sannan ta bud'e murfin motar ta shiga da Sallama.
Ya amsa mata can k'asan makoshinsa, cikin sanyin murya ta gaishe shi, ya amsa mata ba yabo ba fallasa, duk da ba wani kwalliya ta yi ba amma ta yi kyau Sosai ta fito kamar wata balarabiya.
"Ya su Umma da Abba.?"
Ya tambaye ta idanunsa na kan wayarsa, ta amsa da lafiya lau.
"Ina Mai sunan Baba?"
Shiru ta yi kafin daga baya ta gane Abdallah yake nufi, har cikin ranta ta ji dad'in karar da ya mata, daga jiya da ta tabbatar sunan mahaifinta ne da shi ya daina Kiran sunansa,Hakan ya nun mata cewa ya San girman iyayenta.
"Yana wajen Umma, tunda ya masa wanka ta shirya shi to yana wajenta."
"Ki nemi wani lakani da Za ki dinga kiransa da shi saboda ki sakaya sunan ko?"
Jinjina kai ta yi tare da sakin murmushi, sai ta ji ya ce.
"Na zo ne na maki sallama yau zan koma Sakamakon wani uxuri da ya taso mani, ba zan iya jira har gobe ba."
"ATM card ya mika mata tare da sanar da ita pin number na cire kudin."
"Duk sanda kika bukaci kudi ki cire a ciki kiyi amfani da shi, ba sai kin tambaye Abba kudi ba."
Key din mota ta bata tare da cewa.
"Wannan motar da kike ciki taki ce."
Da sauri ta kalle shi tana kallon 🏧 card tana Kallon makulkin motar,cikin rawar murya ta ce.
"Ka karbi ATM card da key din motar nan ba zan iya karba ba, Abbana ba zai kasa mani duk abunda nake bukata ba Kuma..."
Kallon da ya mata ne ya sa ta yi shiru tare da cewa.
"To ba ke na bawa ba yaron na bawa saboda bukatarsa idan ta taso ban dorawa kowa ba, Kuma ga mota nan dan bana son rana ya dame shi ko da fita ya kama Ku, zan saka a Koya maki yadda za ki iya driving idan baki bukata sai na nemi direba Wanda shi aikinsa ya kai ki inda Zaki je Kuma ya dawo dake, duk lokacin da kike bukatar fita ki kira shi a waya. Dan ban yarda ki hau bayan wani Kato da sunan kin hau Babur/mashin ya goya ki a bayansa, ko napep ba na so."
Mamakin karfin hali da isa da yake nuna mata take yi.
"Ba zan karba ba Dan ban san yadda zan cewa iyayena ba idan na koma gida."
Kinga tafiya ta kama ni na gaggawar k'asar zan bari gaba d'aya lokacin tafiyata ta k'araso kada ki sa na yi missing jirgin da zan shiga, ki karba muje na gaishe da Abba da Umma na tafi sai na sake dawowa."
Bata ce komai ba Kuma ba ta karba ba ta fita daga sabuwar motar da aka ce mata nata ne.
Da sallama ta shiga gidan inda Abba daga d'akin ya fito Jin sallamarsa, dama yanzu ya shiga bayan ya gama da fadar kayan da ya siyo sun yi yawa
Umma ma ta fito daga d'akinta tana masa Barka da zuwa, Amatullah ta shinfida masa tabarma.
Cikin gairmamawa ya gaida Umma da Abba inda suka masa godiya tare da nuna masa kayan yayi yawa ya rage dawainiya haka, Umma ta mika masa Abdallah ya karbe shi yana Jin dad'in karamci irin na iyayenta.
Ruwa Amatullah ta kawo masa suka Dan taba fita ya sanar da su tafiya ce ta kama shi zai tafi, inda ya bawa Abba bandir din dubu d'aya guda d'aya wato duba d'ari kenan, Umma ma haka, kin karba suka yi ya ajiye masu ya tafi, fita ya yi da Abdallah inda Amatullah tabi bayansa Dan masa rakiya.
Duk yadda ya yi da ita akan ta karbi ATM card da key din motar Sam taki karba dole ya kyale ta ya mika mata Abdallah bayan ya sumbace shi a goshi, sannan ya masu sallama ya tafi.
Komawa gidan ta yi kai tsaye d'akinta ta nufa duk sai ta ji ba dad'i tafiyar Ajmal, ji tayi ta rasa me ke mata dad'i ta rasa dalilin damuwa da tafiyarsa.
Bayan ya tafi da mintuna ashirin ya kira ta a waya, bayan ta daga ne ta yi sarin ajiye wayar tare da zare towel da ke jikin Abdallah, zaro idanu ta yi cike da fargaba da kaduwa a cikin idanunta.
Bi tashar TASKAR MAMAN IHSAN a WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
🤦♀️ *'YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
7️⃣7️⃣
Bayan ya tafi da mintuna ashirin ya kira ta a waya, bayan ta daga ne ta yi saurin ajiye wayar tare da ke jikin Abdallah, zaro idanu ta yi cike da fargaba da kaduwa a cikin idanunta.
Key din motar ne sai ATM card ta gani ya saka mata, shiru ta yi tana tunanin yadda za ta iya nunawa su Abba, har lokacin bai katse Kiran wayar ba, sake d'aukar wayar ta yi tare da cewa.
"Wai me ya sa ba za ka fahimci abunda nake son fahimtar da kai ba, ta ya ya zan iya ce masu ka bani makulkin mota tare da damka mani ATM cc card d'inka Wanda na tabbatar da cewa zunzuutun kudi ne a ciki. Akan me za ka bani.?"
Ba tare da wani tunani ba ta ji muryarsa yana cewa.
"Ko abunda ya fi haka na baki ba zan iya biyanki abunda kika mani ba, na rasa me zan maki ne ya zama tukuici a gare ki na tambaye ki a kwanakin baya ba ki fad'a mani ba, shi ya sa na maki wannan karamar kyautar."
,mamaki take da Jin kalamansa, sannan ta bud'e baki ta jefa masa tambaya.
"To akan me za ka bani tukuici me na yi maka haka?"
"Duk da cewa abun ya zo a yanayin da ban so ba, amma dole na yi maki wata karamar kyautar saboda karbar budurcin ki da na yi sannan a karon farko Allah ya azurta mu da yaro Wanda sanadiyarsa kika shiga kunci da gararin rayuwa kika haife shi kike shayar mani da shi ai ban biya ki ba, dan ko da ace munyi aure ne a Daren farko na same ki cikakkiyar budurwa dole na maki kyaut..."
Katse Kiran wayar ta yi tare da rintse idanu wasu zafafan hawaye ne bin kuncinta, sake kira ya yi har ta katse bata d'auki wayar ba, zuwa can ta ji shigowar message, dubawa ta yi ta ga shine inda yake cewa.
'Kiyi hak'uri ba ina nufin fama maki dabon dake zuciyarki ba ne, ke ce kika tambaye ni dalilin baki wannan kyautar, ni Kuma na fad'a maki gaskiyar dalilin dan ba zan maki k'arya ba. Ni kaina idan na tuna nikan ji ba dad'i a cikin zuciyata amma ba yadda zan yi kaddararmu ce. Amatullah wallahi a ranar da na gane cewa ni ne na aikata abunda ya faru tsakaninmu wallahi na shiga matsanancin damuwa na yi kuka na shiga bakin ciki Wanda ban taba shiga makamancinsa ba, na kasa ci na kasa Sha kwana na yi ina kuka tare da tsanar kaina.
Kiyi hak'uri ki yafe mani.'
Bayan ta gama karantawa a zuciyarta kuka ta fashe da shi, tare da toshe bakinta Dan kada Umma ko Abba su jiyo kukan nata.
Bangaren su Ammi kuwa sun gama shirin tafiya don komawa Kaduna. Jin shiru Nasreen ba ta leko ba ya sa da suka gama shiri Ammi ta nufi d'akin da Nasreen take.
Knocking Ammi ke yi daga k'ofar d'akin Wanda dama suna jere ne daga d'akin Ammi sai na ta. Tana daga kwancen da take jan gado idanunta a lumshe kamar Mai barci amma ba barci take yi ba, tunanin yadda za be ta kuntatawa rayuwar Amatullah take yi, dan ba za ta kyale ta ba, Kuma shima Ajmal din tana tunanin ta wace hanya za ta rama abunda ya mata, hannu ta kai tana taba goshinta inda yake mata ciwo.
Knocking ta ji ana yi duk da ta ji Ajmal ya sanar da ita cewa tafiya ta kama shi zai bar k'asar, wai tabi su Ammi su koma gida, ita Kuma ta yi alkawarin ba za ta koma gidansa ba, America za ta wuce wajen iyayenta.
Ta San ba Ajmal din je knocking ba amma tana kyautata zaton Ammi ce, kallon Affan dake barci ta yi ganin ya juya yana gyara kwanciyarsa kan gadon.
Jin shiru ya yi yawa ne ya sa Ammi ta d'auki wayarta ta lalubo lambar Nasreen ta dannan mata kira. Tana kallon wayar n ringing sai da ta kusa katsewa ta daga ba tare da ta ce komai ba.
Ammi ce tayi sallama tare da tambayarta lafiya take kuwa, ta nuna mata ba komai lafiya lau, sai Ammi ta sanar da ita ta shirya yanzu zasu tafi zasu biya suyi sallama da iyayen Amatullah sannan su kama hanyar Kaduna.
Yamutse fuska ta yi tare da cewa.
"Ammi Ku tafi kawai wallahi a gajiye nake ba zan iya iya tafiyar mota ba zan bi fly ne na koma."
Kasancewar Ammi ta San Nasreen da son jiki ya sa ta yi tuanininta wahalar tafiyar motar ne ba ta so, don haka ce ba komai Allah ya kai su lafiya.
Daga nan Ammi ta koma ta sanarwa Abba wai Nasreen ba za ta hau mota ba jirgi za ta bi, ya ce to ba damuwa su tafi kawai.
Shiru Ammi ta yi tare da cewa.
"Dad din Ajmal Anya ba matsala kuwa na ji muryarta wani iri Kuma ba ta bud'e mani k'ofar ba, Rabon mu da ita tun isowarmu jiya fa."
"Ka da ki damu ki San ta ba ta cika sakewa da mutane ba maybe gajiya ne kamar yadda ta ce maki."
Jinjina kai ta yi ta ce.
"Shikenan."
Fita suka yi inda suka samu direbansu na jiransu a harabar hotel din, suka shiga bayan sun sanar da shi ya fara kai su gidansu Amatullah.
Akan hanayarsu ta komawa ne Ammi ta Kalli Dad ta ce
"Me zai hana idan mun je ka nemawa Ajmal auren yarinyar nan Amatullah wajen mahaifinta. Ka ga ko ba komai zasu reni yaron da suka haifa cikin rufin asiri ba tare da kowa ya Dan cewa yaron bai da uba ba "
"Shi Ajmal din ne ya sanar da ke cewa yana son ya aure ta?"
"Bai fad'a mani ba amma na San ba zai ki ta ba Musamman yadda na ga yana son yaron da ta haifa masa, bai banzatar da su ba kamar yadda wasu mazan suke yi idan sun gama da mace shikenan bukatarsu ta biya shikenan sun gama da mace basu waiwayarta basa so a danganta su da yaron, amma shi naga yana matukar nuna soyayya ga yaron."
"Duk da haka Hakan ba shi zai tabbatar maki yana son uwar yaron ba."
"Amma Alhaji ai maso uwa yaso d'anta."
"Duk da haka ki bari a tsakaninsu su daidaita kansu idan ya ce yana son ta ita ma ta amince ai mu abun farin ne a wajen mu fan yarinyar kirki ce ta San darajar mautane, ki bari ya dawo mu zauna mu yi magana da shi."
Duk da Ammi ta so ayi magana amma ba yadda ta iya haka ta hakura har suka k'arasa gidan.
"Ammi ce ta shiga da Sallama Abba da Umma dake zaune a tsakar gidan suka amsa da tare da mata sannu da zuwa.
Tana sanye da bakar abaya ta fito sak balarabiyarta, murmushi ta saki tare da zama tabarmar da Umma ta shinfida mata.
Suka gaisa inda suke tambayarta Dad ta sanar da su yana waje, Abba ya fita ya shigo da su, suka gaisa Umma ta kwalawa Amatullah kira, suka amsa Ammi ta karbi Abdallah tana masa wasa.
Ruwa aka kawo masu suka Dan taba fira sannan suka masu sallama, inda Ammi ta sa aka shigo masu da tsarabar da suka zo da shi, turamen zannuwa da shaddodi da turarurruka, dai sabulai.
Abba na ta fadar dawainiya ta yi yawa ga Wanda Ajmal ya kawo, su Dad suka ce ba komai suna sauri yau zasu koma.
Har waje suka raka su inda Amatullah har da kuka tana rungume Ammi, Dan sai ta ji ba dad'i Musamman yadda Ammi ta d'auke ta kamar yarta.
Suka d'auki hanyar komawa Amatullah suka dawo gida. Da safiyar nan makota suka shigo suna wa Amatullah Barka da dawowa tare da gaida Umma, duk wacce ta shigo sai Umma ta bata sabulu da omo.
Da misalin k'arfe goma Sha d'aya na safe motar Munnir ta yi parking a k'ofar gidan su Amatullah. Wannan karon bai shiga ba sai ya tsaya daga waje ya kira ta a waya wai ta fito yana waje.
Kallon sabuwar falleliyar motar dake k'ofar gidan yake yi, kafin ya kau da kansa yana fitowa daga cikin motar ya nufi zauren gidan, inda suka Saba zama suna zance tun kafin barinta gida.
Nasreen ta kammmala shirinta dama tana dama ta saka d'aya daga cikin security na Ajmal ya mata bukin din jirgi tun jiya da yamma bayan Ajmal ya tafi gidansu Amatullah.
Ta shirya ta shirya Affan ta fito daga hotel din don neman abin hawa da zai kai ta airport.
*Kuyi hak'uri da ni, da Kuma typing error bana editing*
Bi tashar TASKAR MAMAN IHSAN a WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
🤦♀️ *YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
Page 7️⃣8️⃣
Ta shirya Affan ta fito daga hotel din don neman abin hawa da zai kai ta airport.
Ta dade tsaye a bakin titin ga ababen hawa tun daga kan motoci da babura da masu Keke napep nan suna ta kai kawo,amma Nasreen na tsaye tana kallonsu don ba ta San yadda zata tsaida su ba, don tun da take a rayuwarta ba ta taba tsayawa kan titi don neman abin hawa ba, infact ma ba ta taba shiga motar haya ba sai dai duk inda zata tafi direba ya kai ta ko Kuma ta yi driving da kanta.
Ganin lokaci na wucewa tana tsaye sai ta fara yamutse fuska cikin gajiyawa kamar wacce za ta yi kuka.
D'aya daga cikin ma'ikatan hotel din ne ya k'araso zai wuce, ganin yanayinta ya saka shi tambayarta inda za ta je, nan ta sanar da shi airport take son zuwa, nan ya tare mata mai napep tare da sanar da shi inda zai kai ta. Godiya ta yi masa ta dauki Affan suka shiga cikin napep din ne ya ja suka bar wajen.
Suna cikin napep din wayarta ya soms ruri, ciro wayar ta yi daga cikin handbag dinta ganin Ajmal ne ke kiran wayar ya saka ta katse Kiran wayar tare da kashe wayar gabad'aya.
Yana zaune a zauren gidan yana danne-danne da waya k'amshin turarenta ne da ya ji ya saka shi d'auke idanu dan daga kan wayar ya maida zuwa gare ta daidai lokacin da take karasowa wajen bakinta d'auke da sallama. Sanye take da hijabi har kasa, amsawa ya yi tare da sakar mata murmushi, ita ma martanin murmushin ta sakar masa tare da yi masa sallama.
Amsawa ya yi idanunsa na
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 33 Chapter of 51