ta yi wa Amatullah ta ce,
"Ba ku haɗu a islamiyya ba ne?"
"Umma dama abinda ya kawo ni kenan, na ga sati ɗaya kenan ba ta zuwa school haka ma islamiyya ba ta zuwa shine na zo na duba ta ko lafi..."
Umma ba kalmar da take furtawa sai inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un. Abba ne ya fito daga ɗakinsa ne ya fito Ana jin Ummu na ta sallallami
"Lafiya kuwa na ji sai sallama koke"
Mallam ina cikin damuwar abinda na gani a jakkar yarinyar nan, yanzu kuma ga ƙawarta ta biyo hanyarta wai tsawon sati ɗaya kenan ba ta zuwa islamiyya."
Ji yayi kamar an watsa masa ruwan dalma a zuciya, cikin tashin hankali ya ce,
"Ke Fadila kin tabbata kuwa?"
"Jikinta ne ya yi sanyi dan ita a tunaninta wata matsala ce ta saka ba ta zuwa, amma da ta san cewa ana turo ta daga gida ita ce ba ta zuwa ai da ta zo ta sanar da iyayenta wannan zancen ba, sai dai ta neme ta daga gefe ta ji ba'asi."
Murmushi ta ƙaƙalo tare da yin yaƙe ta ce,
"Abba ban tabbatar ba gaskiya, saboda nima bani da lafiya tsawon kwanaki goma ban je ba, wata ce nake tambayarta cewa ko ta ga Amatullah ta ce, a'a, sai na yi tunanin ba ta je ba ne, ashe tana zuwa. Ku yi haƙuri na tayar maku da hankali ko?"
Cikin rashin gamsuwa da zancenta Umma ta ce,
"Ke Fadila ki faɗa mana gaskiya dan nima na lura da ɗabi'un Amatullah sun sauya."
Murmushi ta yi tare da cewa
"Ba komai Umma ka da ki damu."
Abba ne ya kalle ta ya ce,
"To idan haka ne me ya saka yau ba ki ganta a islamiyya ba?"
"Abba ai ban san tana zuwa ba nima yau na fara zuwa dake yanzu an taba mu kashi biyu a ajinmu ita tana ɗayan aji ban duba ta ba na zo."
Girgiza kai Abba ya yi tare da cewa
"Na fahimci kamar kina kare ta ne, amma ko ma mene ne zan gano shi. Dan 'ya mace rauni ne da ita, tarbiyyar 'ya mace akwai wahala."
Kallon Umma ya yi tare da cewa
"Bari na tafi makarantar islamiyyar ta su na tabbatar, insha Allah ranar Monday ma sai na bita school ɗin na tabbatar."
Yana gama faɗar haka bai tsaya ɓata lokaci ba ya fice daga gidan.
Fadila hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba, dan ta zauna a gidan dan tana buƙatar jin ta bakin Amatullah.
Abba na fita daga gidan ya yi kiciɓis da Munnir a ƙofar gidan, cikin girmamawa Munnir ya gaishe shi tare da tambayar Ko Amatullah na ciki.
Abba ne ya yi shiru yana nazarin yadda zai fada masa zancen, sai ya yi tunanin cewa Munnir auren Amatullah yake so kuma ya lura Amatullah tana saurarensa, dan sau uku yana zuwa zance kuma ta aminta da shi, dan haka yayi ajiyar zuciya ya ce,
"Makarantar su Amatullah zan je na duba, dan ga ƙawarta nan ta shigo ta ce ba ta gan ta ba."
Cikin tashin hankali Munnir ya ce,
"Subhanahi Baba mu tafi tare."
Girgiza kai Abba ya yi tare da cewa
"Ka yi zamanka ka tafi gida idan ta dawo sai ka zo."
Munnir ya ce
" Ba zan iya tafiya ba Abba, dan ko ka tafi zan bi bayanka ne sai na san halin da take ciki kafin na na koma gida."
Ya so Abba ya shiga motarsa su tafi amma Abba sam ya ƙi tsohuwar babur ɗinsa ya nemi tayarwa amma ta ƙi tashi, dole ya bi maganarsa ya shiga motar suka tafi.
Bayan Munnir ya yi parking a ƙofar makarantar ne suka fito, ofishin shugaban makarantar suka nufa bayan sun yi sallama sun shiga suka gaisa, nan Abba ke masa bayanin abinda ya kawo shi.
Ajiyar zuciya shugaban makarantar ya sauke tare da yin tunani, dan tabbas ya san cewa Amatullah ta daina zuwa kusan kwana goma kenan, kasancewar ta yarinya mai ƙwazo kowa ya san Amatullah. Shi ya sa ko da ba ta zuwa duk sun damu, suna da niyyar tura wasu ɗalibai gidansu a duba ko lafiya sai ga wannan zance.
"Mallam Abdullahi a zahirin gaskiya ɗazun nan muka gama zancen Amatullah ni da Mallaminta, ta fi sati ɗaya rabonta da makaranta, a tunaninmu ba ta da lafiya ne."
Mahaifin Amatullah kuwa ya shiga tashin hankali sosai ba kaɗan ba, ji yake abin wani iri, ga shi kullun za ta sallame su da niyyar zuwa islamiyya kenan ina take zuwa kenan.
*LONDON*
Kwance yake kan makeken gadonsa na alfarma, ya lulluɓe rabin jikinsa da wani haɗaɗɗen lallausan bargo, idanunsa a lumshe kamar mai barci, amma a zahiri ba barci yake ba. Lokaci-zuwa lokaci sai ya yi tsuki tare da motsa bakinsa.
Wayarsa ce ta fara ruri, har ta katse bai buɗe idanun ba ballantana ya ɗauki wayar, aka sake kira a karo na biyu, nan ma bai buɗe ba a karo na uku ne ya buɗe idanunsa da niyyar kashe wayar gaba ɗaya sai ya ga Amminsa ce ke kiransa a waya video call ne.
Amsawa ya yi bayan ya tashi ya jingina bayansa da jikin gadon. Zuba masa idanu ta yi tare da cewa,
"Ajmal lafiya kake kuwa me ke damu ka haka?"
Cikin harshen larabci take masa magana, shima ya amsa mata tare da cewa
"Ba Komai Ammina ka da ki damu?"
"Akwai komai saboda ga shi nan ina hango damuwa a kan fuskarsa? Ka da ka ɓoye mani komai ni fa uwa ce a gare ka, ko akwai wata matsala a tsakaninka da matarka ne, dan na lura babu wani kyakkyawan fahimta a tsakaninku kamar ba ma'aurata ba."
Shiru ya yi yana nazarin Ummansa kuma ya san tabbas maganarta gaskiya ne, sai dai ba ta ta fahimce shi ba ko ya faɗa mata, dan haka ya yi ƙoƙarin fahimtar da ita ta hanyar cewa
"Ammina ba yadda kike tunani ba ne fa babu wata matsala a tsakanina da mata ta, kinsan ni mutum ne mai yawan tafiye-tafiye yau ina wannan ƙasar jibi ina can kuma kinga ga jikanki na school ba zai yiwu na dinga yawo da su ko ina ba."
Shiru ta yi kafin ta ce,
"Shikenan mubar wannan zancen mu koma zancen, mu koma zancen da maihaifinka ya zo da shi na siyasa, to ni dai gaskiya ba na sonsa ya ka shiga siyasar nan, ba za ka iya ɗaukar nauyin al'ummar jahar nan ba, mulki ba abun wasa bane ba ƙaramin nauyi ba ne nauyin mulki ba za ka iya ɗaukarsa domin sai Allah ya tambaye ka ɗaya bayan ɗaya da mutane sun san nauyin da ke wuyansu da ba su amshi mulki ba..."
"Ka da ki damu Ammi tunda ba ki so ba zan yi ba."
"Amma ba za ka faɗa mani matsalarka ba na ga kamar fa kana cikin damuwa, ka faɗa mani ko akwai taimakon da zan iya maka."
Murmushi ya yi tare da cewa
"Ammina ke ce kike ganin kamar ina da damuwa amma ba abinda ke damu na, addu'a na ke buƙata daga gare ki."
Jinjina kai ta yi tare da cewa
"Shikenan tunda haka ka ce, addu'a kullun ina maka shi."
Duk a cikin harshen larabci suke magana, daga ƙarshe suka yi salla ya kashe wayar.
Cikin tashin hankali Mallam Abdullahi ya fito daga office ɗin shugaban makarantar, Munnir na biye a bayansa inda yake daɗa kwantar masa da hankali.
"To Baba ga shi ka hana ta riƙe waya da za'a ji inda take, amma mu koma gida ko za mu tarar ta dawo."
Motar suka shiga inda a hanya ma Munnir ke sake kwantar masa da hankali, shi dai ko a bai ce masa ba.
Suna shigowa unguwar dai-dai layin gidan ne Munnir ya hangi motar Hafsat mamaki yake me ya kawo ta bakin layin gidansu Amatullah, sai kuma ya hangi Amatullah na fitowa daga motar Hafsat burki ya danna mamaki kwance a saman fuskarsa.
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
Love you oll😍😘
🤦♀️ *ƳAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Dedicated to
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubucirsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Page9️⃣&🔟
Birki ya danna mamaki kwance a saman fuskarsa, shin me ye alaƙar da ke tsakanin Hafsat da Amatullah? Kuma ya aka yi ta san Amatullah,duk da ranar da suke sake haɗawa a bige take baya tunanin za ta iya gane Amatullah.
Mahaifin Amatullah ne ya kalli Munnir ya ce,
"Lafiya?"
Girgiza kai yayi tare da cewa
" Ba komai."
Daga nan ya ja motar suka shiga layin gidan, daga Hafsat har Amatullah ba wanda ya lura da Munnir, domin magana suke wa junansu.
Bayan ta mata sallama ne ta tafi yayin da Hafsat ta ja motarta ta bar wajen.
Tana tafiya sanye da kayan makaranta riga da wando da hijabi, jakkarta na riƙe a hannunta duk wanda ya kalle ta zai ce daga islamiyya take.
A ƙofar gidansu ta ga motar Munnir, ƙarasawa ta yi wajen motar yayin da yana hangen ta ya sauke glass ɗin motar.
"Assalamu alaikum"
"Wa'alaiki salam"
"Ina wuni Yaya Munnir?"
"Lafiya lau, daga ina kike?"
Murmushi ta yi tare da cewa
"Duk wanda ya ganni ya san daga Islamiyya nake."
Girgiza kai yayi tare da cewa
"Ina son mu yi magana mai mahimmanci amma yanzu ki shiga gida anjima zan zo."
"To Allah ya kaimu."
Daga nan ne ta nufi ƙofar gida shi kuma ya ja motarsa ya bar wajen.
Tana sallama a tsakar gidan ta ga Abbanta da Ummanta da ƙawarta kowa ya yi jugum yana tunani. Gabanta ne ya faɗi dan ta san rashin ganin ta ne ya sa Fadila biyo sawunta.
Amsa mata sallamar suka yi ta ƙaraso ta gaida su cikin girmamawa. Suka amsa ba walwala a tare da su.
Murmushi ta sakarwa Fadila tare da mata alamar ta taso su shiga ɗaki.
Muryar Mahaifinta ne ta ji yana cewa
"Daga ina kike?"
Bakinta na rawa ta fara makyarkyata
"Daga islamiyya?"
Wasu zafafan tagwayen maruka ya sauke mata a fuska, a gigice ta ƙwalla ƙara tare da zubewa wajen tana kuka.
"Ka da ki bari na sake tambayar ki a karo na biyu."
Kuka ta saka masa tare da bashi haƙuri ta kasa sanar da shi ina ta tafi.
"Abba dan Allah ka yi haƙuri ka yafe mani ba zan sake ba."
Cikinta ya yi da niyyar kai mata duka Ummanta ta sake shiga tsakaninsu, dan ta san idan ya riƙe ta sai ta ji jiki a hannunsa.
Firgita ta yi da ganin yanayinsa ta ce
"Abba wallahi gidan ƙawa na tafi?"
Tsayawa ya yi yana Kallonta tare da cewa
"Gidan ƙawa? Irin tarbiyyar da na baki kenan? Yaushe kika canza? Tsawon kwanaki da kika ɗauka ba ki zuwa makaranta fa?"
"Duk gidan ƙawata na ke zuwa?"
"Wace ce ƙawar ta ki kuma ina kika haɗu da ita?"
Kasa faɗa masa ta yi sai kuka take yi ba kakkautawa.
Kallon Umma ya yi tare da cewa ta ɗauko masa abinda ta gani a cikin jakkarta.
Umma ta ɗauko kwalaben da ta gani ta kawo masa, fitowa ya yi da su tare da cewa
"Waɗan nan fa daga ina?"
Zare idanu ta yi ta kasa magana sai kuka kwai take yi, tsawa ya daka mata wanda ya sa ta sake firgita ta ce,
"Yaron ƙawar tawa ce ba lafiya shine ta bani saƙon cewa na siya mata maganin tari da mura."
Yadda ta yi maganar ma kadai zai tabbatar maka da cewa ba ta saba yin ƙarya ba.
Girgiza kai kawai Abba ya yi tare da cewa
"Amatullah ban san ya aka yi kika canza ba, ban san yaushe kika fara ƙarya ba, a da Amatullah ba ta mani ƙarya ba ta taɓa saɓa ma iyayenta, amma yanzu kin canza daga tarbiyyar da muka baki. Ki sani daga yau na dakatar da karatunki ba za ki sake zuwa makarantar boko ko na islamiyya ba, dama kin sauke al-ƙur'ani haddasa kike zuwa to ki yi a gida. Makarantar bokon ma na so ko da ba kiyi karatu mai zurfi ba ki gama secondary school, amma shima hakan bai samu ba. Duk ranar da na ga kin saka ƙafa kin fita a ƙofar gidan nan to sai na masifar ɓata maki rai."
Aguje ta nufi ɗaki ta faɗa kan katifarta tana kuka. Fadila ce ta bi bayanta tana rarrashinta.
Ture hannunta ta yi tare da cewa
"Ke ce kika haɗa ni da iyayena ko?"
Itama Fadila kukan take tana cewa
"Ban haɗa ki da su ba, dama ko da na zo suna maganar kwalaben dake cikin jakkarki, kuma dama na yi tunanin ba ki da lafiya tunda kika daina zuwa makaranta, hasali ma ni ƙoƙarin kare ki na yi ta hanyar ce masu an canza..."
Hannu ta daga mata alamar ba ta son jin zancenta.
"Fadila ki tashi ki tafi ba na son ganin ki a kusa dani."
Ɓangaren Munnir kuwa yana barin layin ya yi parking, wayarsa ya ɗauka ya dannawa Hafsat kira. Tun kafin ta yi magana yace,
"Kina ina ne?"
"Ina wani waje ne."
"Mu haɗu a gidanku."
Daɗi ne ya lalluɓe ta tare da yin tunani kila hankalinsa ya dawo gare ta.
Kai tsaye gidansu ya nufa, bayan ya yi horn maigadin gidan ya buɗe masa gate ne ya shiga,a harabar gidan yayi parking ya zauna a motarsa, dama ya tambayi mai gadin ta ce Mom ɗin Hafsat ba ta nan.
Bayan kamar mintuna ashirin sai ya ji horn ɗinta alamar ta dawo, bayan mai gadin gidan ya bude mata gate ne ta ƙarasa shiga ta yi parking.
Yana ganin ta fito shima ya fito daga motarsa fuskarsa a murtuƙe ya fara magana.
"Me ke tsakaninki da Amatullah?"
Yamutse fuska ta yi tare da cewa
"Wace ce kuma mai wannan sunan?"
"Raina mani hankali kike son yi?"
"Bansan Amatullah ba gaskiya."
"Munafuka maƙaryaciya ni da kaina na ganki sanda kika ajiye ta a mota."
Dariya ta dinga ƙyaƙyatawa kamar mahaukaciya, sannan ta ce,
"Ƙawata ce ita."
"A ina kuka haɗu da ita?"
" Motartarka."
Shiru ya yi yana nazarin yadda hakan ta faru dan shi dai kam iya saninsa ba ta cikin hayacinta ashe duk tana jinsa.
"Ina mai maki gargaɗi da babban murya, akan cewa ki yi gaggawar fita daga harkar Amatullah,idan kuwa ba haka ba..."
"Idan ba haka ba me za ka mani? Wai shin da me Amatullah ta fini ka ce wai tana da tarbiyya ba za ka iya auren na ba?"
Gyara tsayuwar sa ya yi tare da yin tsuki.
"To bari ka ji bani da banbanci da Amatullah domin kuwa kamar yadda nake cikakkiyar 'yar shaye-shaye haka itama take cikakkiyar 'yar shaye-shaye,ka ga kuwa tunda har ka ƙi ni itama dole ne ka ƙi ta?"
"Okay saboda haka ne kika sanya ta a harkar ta ku ta shaye-shaye?"
"Ni ban saka ta ba dama da abinda take."
"Ƙarya kike yi ƙarya ne wallahi Wallahi Amatullah ban yarda tana ma shaye-shaye ba."
"Ina zuwa yanzu zaka yarda da zancen da nake faɗa maka."
Wayarta ta ciro daga jakkarta tana dannawa ta miƙa masa, kamar ba zai amsa ba sai ya amsa yana dubawa.
Amatullah ce zaune kamata babu ɗankwali tana shan kayan maye tana surutai ita kaɗai, ba wanda ya kula ta daga ƙarshe sai ta faɗi tana barci a wajen."
Ji yayi wani abu ya tokaro masa daga cikin zuciyarsa, murmishin takaici ya yi tare da cewa
"Duk da haka na ji na gani kuma ba zan fasa aurenta ba, kuma abinda kika aikata mata bai dace ba, kin saka ta a mummunar ɗabi'a ta shaye-shaye, kin cutar da ita kin cutar da iyayenta..."
"Dakata Munnir ni ban saka ta a harkar shaye-shaye ba dama da abinda take."
Ƙarya ne wallahi ranar da na ɗauke ta na rage mata hanya a ranar kika ji zance na, daga nan kika shiga rayuwarta. Har makarantar da take mun tafi da Mahaifinta tsawon sati biyu ba ta zuwa, kenan dama ba ɗabi'arta bane a kwanakin nan ne suka canza kuma a dalilinki."
"Okay wato har maihaifinta ka gana da shi ko? Lallai da gaske kake aurenta za ka yi, to ya za ka yi da baiko da aka mana."
"Ƙwarai kuwa aurenta zan yi da gaske domin kuwa ina da tabbacin cewa ita ba lalatacciya ba ce."
"Kamar ya?"
"Kema kin sani da mutunci na ba zan auri karuwa ba."
Da sauri ta kalle shi cike da mamaki ta ce,
"Munnir?"
"Na'am"
"Ni kake kira da karuwa?"
"To da me ya sunanki? Kina da wani suna da za'a kira ki da shi ne da ya wuce ƴar maye kuma karuwa?"
"Oh saboda na baka jikina ka ci moriyar ganga shine za ka fara aibata ni bayan ka lalata mani rayuwa ko?"
"Waya ya lalata maki rayuwar ni? To tun wuri bai ƙure maki ba ki je ki nemi wanda ya lalata maki rayuwarki amma ba ni ba."
"Oh ka mance abinda ya faru a ɗakinka last month ko? Ka manta ko?"
Girgiza kai ya yi tare da cewa
"Ba abinda na manta na san komai ko da na yi mu'amala da ke ba a cikakkiyar budurwa na same ki ba, bayan kin je kin gama yawon banzarki ne za ki ce ni lalata maki rayuwa, kalle ni da kyau ni ba sakarai bane da zan auri ragowar wani saurayin."
Ƙwalla ne suka cika idanunta ga zuciyarta da ke mata zafi kamar an watsa mata harsashin wuta, inda ya cigaba da cewa.
"Ina da matuƙar kishi ni a rayuwata ba zan iya zaman aure da matar da wani ya riga Ni saninta a 'ya mace ba, domin baƙin ciki ne zai kashe ni idan ina Kallonta, wannan abun da ya faru tsakanina da ke a wancan rana laifinki ne kece kika janyo da kika shigo har ɗakina bana ciki kila kwanta kina barci, wanda ba suturar kirki a jikin ki duk da ana biki a gidan ɗakunan gidan akwai jama'a ai bai kamata ki kwana ɗakina ba, mun kwanta a gado ɗaya ni waliyi ne da ba zanji komai ba, kuma kika biye mani kema. To a nan ne fahimci wani ya riga Ni saninki duk da baiko da aka mana na ji ba zan iya aurenki ba, domin ko na aure ki ba zan iya zaman jin daɗi da ke ba, ina da matuƙar kishi ba zan iya ba Amatullah zan aura?"
Wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokaro mata maƙoshi ta ce,
"Ita Amatullah ka na da tabbacin cewa cikakkiyar budurwa ce?"
"Na ga alamar haka, shi ya sa na shi ya sa na nace mata."
Shiru ta yi tana nazari zuwa can ta yi murmushi tare da cewa
"Na gode da abinda ka mani."
Ta buɗe baki da niyyar sake masa wata magana ta ga ya juya zai shiga motarsa, binsa take da kallo har ya bar gidan.
Itama motarta ta shiga ta bar gidan a guje, yana Kallonta ta wuce shi kamar za ta tashi sama.
Kai tsaye gidan Nafeesat ta nufa. Suna zaune a falo Nafeesat da Shamsiya da Mairo suka ga ta shigo kamar an jefa ta daga sama. Kallon mamaki suke mata inda Nafeesat ta tashi tsaye tare da tambayar ta lafiya, wasu mata biyu da suka yi barci gabansa da kwalabe ta kalla ta ɗaga kwalaben ta ga ba komai a ciki, ƙarasawa ta yi gaban Nafeesat ta ɗauki glass cup ɗin da ke cike da ke cike da haɗin da Nafeesat ta yi za ta sha, ba tare da ɓata lokaci ba Hafsat ta ɗauki kofin ta kafa baki ta fara sha, Kallonta kawai suke ba wanda ya ranka mata sai da ta shanye kofin tas sannan ta ajiye ta fara magana.
"Wai ni zai yiwa gorin budurci ko, har yana ce mani a wajen Amatullah ne kawai yake saka ran budurci idan ya aure ta."
Dariya ta sake yi tare da ɗaukar kwalban giyar ta zuba a kofi ta ƙara sha kamar rabin kofi sannan ta daura da cewa.
"Ya mani gorin cewa ni ina shaye-shaye baya son 'yar shaye-shaye sai ita, na mayar da ita 'yar shaye-shaye dan ya guje ta amma bai damu ba. Sai cewa yayi yana sonta haka wai ni ba budurwa ba ce ragowar wani ce, yana da kishi ba zai iya zama da macen da ba shi ya fara saninta ba. Ya fasa auren nawa saboda ni ba cikakkiyar budurwa ba ce ita zai aura yana sa ran samun budurci daga gare ta ko? To ni kuma na yi alƙawarin ba zai taɓa samun budurci daga gare ta ba."
Ta ƙarasa shanye kofin giyar sannan ta saki kofin ƙasa ya faɗi ya tarwatse ta ɓingire a kan kujerar sai barci.
Ɓangaren Amatullah kuwa ba abinda take sai kuka ita kaɗai a ɗauki, ganin halin da iyayen nata ke ciki ya tayar mata da hankali. Kuma ta ci alwashin cewa ba ita ba Hafsat har abada, dalilinta ne ta shiga wannan halin. Za ta cigaba da zama da bin Umarnin iyayenta sai yadda suka yi da ita.
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
Love you oll😍😘
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
🤦♀️ *ƳAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Dedicated to
*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION*
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubucirsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Page1️⃣1️⃣&1️⃣2️⃣
Za ta cigaba da zama da bin Umarnin iyayenta sai yadda suka yi da ita.
Bayan ta ci kuka ta ƙoshi babu mai rarrashinta. Tashi ta yi ta nufi ɗakin Ummanta, da sallama ɗauke a bakinta,sai da ta ji Ummanta ta amsa tare da bata izinin shigowa ne ta shiga. Durƙusawa ta yi akan guiwarta ta cigaba da rusa Kuka.
"Ummata dan Allah ki yi haƙuri na tuba wallahi ba zan sake ba, ku daina fushi da ni domin fushinku a gare ni masifa ne, na canza daga yanzu zan koma yadda kuka Sanni, ita wannan ƙawar da ta saka ni cikin wannan halin na rabu da ita in sha Allah."
Nan ta cigaba da kuka kamar ranta zai fita, Umma ce ta rarrashe ta har ta haƙura ta bar kukan.
Daga nan ne ta tashi ta nufi ɗakin Abbanta, sallama ta yi amma ta ji shiru bai amsa ba, a lokacin yana zaune akan sallaya hannunsa riƙe da ƴar rediyo yana saurare.
Sam bai ji sallamar da take ba, jin haka ita ta ɗauka ko fushin da yake da ita ne yasa bai amsa mata ba, alhalin ƙarar rediyo ce ta hana shi jin Muryar ta, dama muryar ta disashe saboda tsabar kuka.
Durƙushewa ta yi a wajen tare da sakin marayan kuka, sheshsheƙar kukan nata ne ya sa shi kashe rediyon.
Da gaske kuwa kuka ne ya ke jiyowa kuma kukan na Amatullah, a fusace ya ɗaga murya tare da cewa
"Idan ba ki bar ƙofar ɗakin nan ba na fito na same ki sai na yi maki halakakken duka."
Ta san halin Abbanta yana da zafi har yanzu bai sauka ba, cikin sheshsheƙar kukan nata ta fara magana
"Abba ka yafe man..."
Tsawar da ya daka mata ne ya sa ta tashi ba shiri ta bar wajen, dan ta san idan har ya riƙe ta mai kwatar ta a hannunsa sai dai Allah kaɗai.
Ɗakin Ummanta ta nufa ta roƙe ta akan ta taya ta bawa Abbanta haƙuri. Nan Umman ta ce mata ta bari sai ya sauko ta same shi ta bashi haƙuri.
Cikin sanyin jiki ta tashi ta nufi ɗakinta, ta ƙudundune kanta a katifarta sai kuka take kamar ranta zai fita.
Ganin kuka ba zai amfane ta ba ta tashi ta fito ta ɗauki buta tare da shiga banɗaki, bayan ta fito ne ta ɗauro alwala ta zo ta fara salloli.
Waje gari ko da Umma ta fito ta samu Amatullah ta gama aikin komai, kamar yadda ta saba kafin haɗuwaeta da Hafsat. Gaida Umma ta yi ta amsa mata ba yabo ba fallasa har za ta nufi ɗakin Abba sai ta tuna da korar da ya mata, dawowa ta yi ta cigaba da aikinta
Har girkin rana da dare duk Amatullah ce ta yi kasancewar Abba ya ce ya cire ta daga kowace makarantar.
Bayan ta idar da sallar isha'i ne ta ji wayarta na ruri, gabanta ne ya faɗi ta tuna ake Hafsat ta siya mata waya, kasancewar lambar Hafsat ɗin ne kawai a ciki, dubawa ta yi tare da jifa da wayar.
Sau biyar Hafsat na kira a na shida ne ta ɗauka,tare da ɗaga murya tana cewa
"Mallama dan Allah ki fita daga harka ta!"
Daga can ɓangaren Hafsat dake zaune akan kujerar mai zaman mutum uku ta ɗora ƙafa kan ɗaya ne ta ce,
"Lafiyarki kuwa kin san da wa kike magana?"
"Ƙwarai kuwa!"
"To wace ce kike ɗaga wa murya haka?"
"Wace ce ke shashasaha ce ke fa, 'yar maye kuma ballagaza, ko kina da wani sunan da ya wuce wannan ne, na yi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 51