ya kalle taya ya ce.
"Ammi yanzu kina nufin wannan mutumin ɗan uwanku ne?"
",Eh da shi da mahaifin Ajmal uwa ɗaya uba daya ne.Matsalar ta samo asali ne shekaru talatin da biyu da suka wuce. Abubakar shine babban ɗan Marka sai na biyu shi ne Ibrahim da autarsu Laila. Laila ta yi fama da babban ɗanta ya fitar da matar aure bai fitar ba lokacin da ya tashi fito da mata sai ya fito da Fatima, bayan Marka ta yi bincike ta gano yarinyar ba su da tarbiyya a gidansu kowa ya san halin uwarta da bin bokaye ya sanya ta hana shi aurenta amma ya ƙi rabuwa da ita. Dalilin da ya sa bai yi aure ba har ƙaninsa Ibrahim ya yi aure inda ya auro Ni daga ƙasar Qatar. Bayan dawowarmu 9ja Abubakar ya bijirewa Marka ganin ni ƙaninsa na yi aure shi bai yi ba, ada muna zaune a garin Adamawa a gida ɗaya ne da dangin mijina duk da kowa part ɗinsa daban. Lokaci ɗaya Abubakar ya canza halaye baya jin maganar kowa sai na Fatima da iyayenta. Wata rana ya dawo gidan tare da Fatima suka tare a ɗakinsa ba aure wanda ta tare a ɗakinsa, hankalin Marka ya tashi ta sanarwa Baffa ya bada shawarar s ɗaura masu aure gudun abin kunya, hakan ya saka aka daura auren ba tare da son ran Marka ba, dama sun yi haka ne don daura masu auren, lokacin ina da tsohon cikin Ajmal. Kuma a lokacin ne Muka bar garin Adamawa muka dawo garin Kaduna da zama.
Ban sake komawa garin ba sai bayan na haihu yaro na da watanni hudu. Nan na tarar da zaman da ake yi tsakanin Marka da matar Yaya Abubakar. Kwata-kwata ba ta ganin girman Marka ta raina ta wai saboda ba ta son ta wanda duk abinda Fatima ke yi wa Abubakar na ganin cin kashin da matarsa ke yi wa mahaifiyarsa amma baya iya magana. Wata rana sai Marka ta saka Abubakar a gaba akan sai ya saki Fatima amma ya ce rabuwa da ita tamkar rabuwa da rayuwarsa ne. Ana cikin wannan halin aka yi auren autar Marka wato Laila.
Ranar da Marka ta kasa hakuri da kanta ta shiga ɗakin Fatima ta ce ta fito ta nufi gidan ubanta, ta ce ba inda za ta je saboda mijinta bai sake ta ba, Marka ta bashi umarnin ya sake ta ya ce ba zai iya rabuwa da matarsa ba, ta ce to Ni za ka iya rabuwa da ni ko, to ka ɗauki matarka ku yi nisa da mu ba na son sake ganinku a rayuwata. Na cire ka daga cikin 'ya'yana ko mutuwa na yi kada ka zo kan gawata. Ya ce ya amince tunda ya ɗauki matarsa suka bar gidan ba wanda ya san inda suke kuma basu nemi kowa ba, don Marka ta ce bata yarda sauran yaran su neme su ba, duk da Dadyn Ajmal ya sa a masa bincike a ɓoye ba wani labari, sai yau da na hadu da su."
Wannan shine labarin a takaice.
Kai Ahmad ya jinjina tare da cewa.
"Allah ya daidaita tsakanin su."
Da Amin Ammi ta amsa.
Dad ɗin Munnir ya nufi ɗakin Mummy ya sanar da ita tafiyar da zai yi kuma daga nan zai nemi tafiyar mahaifiyarsa, ita ma dole ta bishi ta nemi afuwar Marka idan har tana son cigaba da zama da shi.
Yana fadar haka ya fice don yanzu haushin Mummy yake ji a zuciyarsa
*Maman Ihsan ce*✍️
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
🤦♀️ *'YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page1️⃣0️⃣3️⃣
Yana gama faɗar haka ya fice don yanzu haushin Mummy yake ji a zuciyarsa.
Bangaren 'yan Adamawa kuwa Sudais ne ya sanar da su halin da ake ciki, don haka gabaɗaya suka zo Kaduna, anan asibitin suka tare.
Washegari da safe kuwa Dad ɗin Munnir ya sanarwa Mummy ta shirya ita da Munnira da ita za su tafi amma ya hana a sanarwa Munnir har sai ya dawo. Ba yadda Mummy ta iya ba don ranta na so ba ta saka Munnira ta shirya ita ma ta shirya don Dad ya mata barazanar cewa idan har ba ta shirya sun tafi tare ba to ka da ya dawo ya tarar da ita a cikin gidansa.
Da misalin ƙarfe takwas na safiya motar su Ammi ta yi parking a ƙofar gidan Dad. A tare suka fito Dad na gaba Munnira na biye da biye da shi rike da trolley bag ɗinta tana ja, sai direban Dad na rike da wata trolley bag da alama na Mummy ce dai wata jaka na Dad da ke hannunsa ɗaya. A boot ɗin motar ya zuba jakunan sannan ya zagaya ya buɗewa Dad da Mom bayan motar suka shiga. Dad ne ya kalli Munnira ya ce
"Ko za ki bi Amminku a motarsu?"
Ya yi maganar yana nuna mata motar da Ammi ke ciki, dubanta ta kai bayan motar ta kalli Ammi zaune tana sakar mata murmushi, take ta ji hankalinta ya kwanta da matar ta shiga ranta, don haka ta ɗagawa Dad kai alamar eh.
Ƙarssawa ta yi wajen motar ta bude murfun bayan motar ta shiga bayan ta gaida Ammi. Cikin farin ciki ta amsa mata tare da rike hannunta.
Mum kam baƙin ciki ya ishe ta amma tuna gargadin da Dad ya mata ne ya sa ta yi shiru don ys fada mata idan ba ta ja zaren aurenta ba zai iya tsinkewa.
A haka Ahmad ya ja su Ammi yayin da direban Dad ya mara masu baya.
To Allah ya kiyaye hanya zan ce.
Amatullah ta ɓangaren ta duk ta wani canza kallo ɗaya za ka mata ka san tana cikin damuwa sosai, musamman ƴar ramar da ta yi don tun ranar da Umma take waya da Ammi take sanar da ita rashin lafiyar Ajmal da halin da yake ciki Amatullah ta shiga damuwa. Wani lokaci haka za ta zauna ta yi ta risgar kuka a cikin ɗaki, Umma ta yi rsrrashi har ta gaji ta zuba mata idanu. Kullun kuma ko wane lokaci ba ta da aikin da ya wuce kiran layinsa, ba ta shiga kuma ba za ta fasa kiran wayar ba. Ko kuma ta ɗauki waya tana kallon hutonsa a wayarta. Duk da Munnir ya ga sauyi a tare da ita duk sanda suke waya ya tambaye ta damuwarta sai ta ce masa ba komai, sai dai tana jure tsawon lokacin da suke ɗauka suna waya, duk da ba wani fira take masa ba daga eh sai a'a.
Da misalin ƙarfe ɗaya na rana suka iso garin Kaduna. Direct asibiti suka wuce. V.I.P inda aka kwantar da Ajmal suka nufa.
A cikin ɗakin kuwa har lokacin Ajmal na kwance idanunsa a rufe, Sudais na zaune a gefen gadon yayin da Marka da Ummi ke zaune saman sofa, sai Mama mahaifiyar Nihal. Daga can gefe kuwa Nihal ce ke waya da wata ƙawarta.
Da sallama Ahmad ya tura ƙofar falon ya shiga, bakinsa ɗauke da sallama.Ammi ce a bayansa, ita ma sallamar ta yi gabaɗaya suka amsa tare da masu sannu da dawowa. Ammi ce ta ce.
" Yaya bisimillah ku shigo mana."
Kowa ya zubawa ƙofar ido ana jiran ganin mai shigowa. Mama ta miƙe da sauri tare da cewa.
"Yaya!"
Cikin mamaki da al'ajabi, Marka kuwa Murtuƙe fuska ta yi tare da kau da kanta gefe. Sudais da Nihal dama ba sun shi ba ne.
Cikin sanyin jiki suka ƙaraso ciki Dad na gaba Mummy na bayansa, sai Munnira da ke biye da su.
Kai tsaye Dad ya nufi gaban Marka da niyyar zubewa sai ya ga ta miƙe cikin fusata ta kalli Ahmad tare da cewa.
"Mu je ka kai ni gidan Ibrahim."
Ganin yadda fuskarta ya sauya lokaci guda ya bawa Ahmad mamaki, ba musu ya nufi ƙofar fita, tana shirin ɗaga ƙafa sai Dad ya zube a gabanta tare da rike ƙafarta idanunsa sun yi jajir, cikin ƙunar rai ta ce .
"Idan ba ka sake ni ba zan iya furta maka muguwar kalmar da ban yi niyyar furta maka ba, don sai na fesa maka dafin da ba zai fita daga jikinka ba."
Da sauri ya sake ƙafarta ta fice daga ɗakin.
Nan ya cigaba da durƙuso kansa a ƙasa, Mama ce ta fashe da kuka tare da ƙsrasowa gabansa ita ma ta durƙusa sai kuka take yi tana cewa
"Yaya me ya sa?"
Kukan ne ya ci ƙarfinta yayin da shi ma kukan yake yi. Sudais da Nihal sun fahimci ko waye Dad ɗin ta yanayin abinda ya faru yanzu. Tabbas shi ne wan mahaifiyarsu da suka ji labarin ya tafi tsawon shekaru. Ummi ce ta buɗe baki cikin harshen Ingilishi take tambayar su abinda ke faruwa don ba Hausar take ji ba. Sudais ne ya mata bayanin komai, jinjina Kai ta yi tana kallon Dad wanda ke kula kuma ta hango zallar nadama a cikin idanunsa. Munnira da Nihal suma kukan suke yi saboda ganin halin da iyayen nasu ke ciki.
Ummi ce ta taso ta dinga rarrashinsu tare da basu baki, ta kuma yi alƙawari in sha Allah za ta shawo kan Marka ko za ta haƙura.
Mummy kuwa ko a jikinta domin wanda ya yi nisa baya jin kira.
Dad ne ya tashi jin masallacin da ke cikin asibitin suna tayar da sallar azahar. Tare da Sudais suka fita daga masallacin yayin da matan ɗaya bayan ɗaya suka fara shiga toilet da ke cikin ɗakin don ɗauro alwala.
Bayan sallar azahar ne direban Ammi ya kawo ƙaton basket mai ɗauke da manyan kuloli na abinci da plate da cokula. Kamar yadda yake kawowa sau uku a rana.
Dama akwai drinks da ruwa a cikin fridge dake ɗakin, Mama ce ta zubawa kowa ta aje masa abun sha. Dad kam girgiza kai kawai ya yi don baya jin zai iya cin abinci a wannan lokacin.
Har karfe biyar na yamma kowa na cikin ɗakin zuwa lokacin ne Doctor ya shigo. Duba shi ya yi har lokacin bai motsa ba. Doctor ne ya kalli Ammi ya ce yana son ganin ta a office ɗinsa.
Bin bayansa ta yi inda ya mata bayanin ya kamata su fita da shi ƙasar waje saboda kumburin da zuciyarsa ta yi akai shi ƙasar Indiya.
Godiya ta masu ta ce a shirya komai na tafiya.
Ko da Ammi ta koma ɗakin bayanin komai ta yi mas, Inda Dad ke cewa tare da shi za su tafi sai kuma Sudais.
Ko da yamma liƙis ta yi Ummi ce ta ce su koma gida tunda daka Sudais na tare da shi, Dady ma ya ce zai zauna nan don yana son sai Marka ta ɗan huce kafin ya koma wajen ta.
Mum da Munnira suka bisu sai Mama da Nihal suka bi su.
Mum ta shiga bayan motar dirabansu da ya kawo su yayin da Munnira ta zauna gefenta.
Ammi da Mama da Ummi suka shiga bayan motar da Ahmad ke driving, Nihal ce ta zauna a gefen Ahmad ya ja motar, yayin da direban Dad ya mara masu baya.
Tun daga bakin gate Mummy ke kallon gidan cikin mamaki na haɗuwar gidan, ga wasu securitys da ke kofar gidan kamar gidan wani ƙusan gwamnati. Suka shiga gate ɗin farko bayan security da ke kula da ƙofa sun bude masu, har suka shiga gate na biyu kallon gidan kawai Mum ke yi tana mamakin yanzu Ibrahim ne ya yi arzikin tara wadannan kuɗaɗe da ya narka su s gidan nan haka, ita da take taƙama da suna da arziki ashe ba komai ba ne idan aka hada gidansu da wannan.
Parking space babba wanda ta hangi motoci da yawa kuma tsadaddun gaske sun fi kala goma.
Ba ta ida mamaki ba sai da ta ga sun shiga falon gidan. Ganin kar a ga ƙauyancinta ta faske.
Zama suka yi a falon Ammi na ƙara masu ya gajiya.
Ammi ce ta ƙwalawa ɗaya daga cikin masu aikin kira. Bayan ta zo ta bata umsrnin ta kai Mummy da Marka ɗakunan da zasu zauna a nan downstairs. Kuma kowacce ɗakinta daban za ta kai ta.
Cikin girmamawa ta amsa yayin da ta masu jagora suka bita a baya.
Mummy ta fara kaiwa ɗakinta sannan ta kai Munnira ɗakin da ke kallon na Mummy. Dukka ɗakunan manya ne kuma kowane ɗaki yana ɗauke da babban gado da wardrobe babba na zuba kaya, da dressing mirror da sai drawers. Ga kuma madaidaicin tv dake manne a jikin bango daga gefe kuma ga fridge nan.
Toilet Mummy ta shiga inda nan ma ba ƙaramin haɗuwa ya yi ba. Taɓe baki ta yi sannan ta dawo bakin gadon ta zauna.
Munnira kuwa ita ma zama ta yi zuciyarta cike da farin ciki, yau karo na farko a rayuwarta ga ta cikin dangin mahaifinsu.
Washegari da kuwa jirginsu ya tashi zuwa ƙasar India, daga Sudais sai Dad suka tafi da Ajmal can don duba lafiyarsa.
A cikin sati ɗaya Munnira ta saba da kowa a gidan, don haka take fitowa a cikinsu ayi fira da ita, saɓanin Mummy da kullun tana cikin ɗaki, ko abinci ba ta fitowa ta ci sai dai Ammi ta saka mai aiki ta bita da shi har ɗakinta. Munnira kuwa tunda ta ji an ce Marka ce ta haifi Dad ɗinta sai ta dinga shishshige mata tun Marka na ɗaure mata fuska har ta fara sakar mata fuska, don wani lokaci haka za ta ce a ɗakin Marka za ta kwana ita da Nihal, ba yadda Marka ta iya haka za ta bar masu gadon su biyu ita ta ajiye katifa a ƙasa ta kwanta.
Sosai shaƙuwa ta shiga tsakanin Nihal da Munnira har fita suna yi tare su je shopping, kasancewar Nihal ta san garin sosai.
Satin su Ajmal biyu a India suka dawo Nigeria, ya samu sauƙi Alhamdulillah. Ahmad ne suka dauko su daga airport Dady ma a ranar ne ya dawo.
Haka gidan aka shirya liyafa Dady ma ya yi farin cikin dawowa musamman da ya ga ɗan uwansa, rungume juna Dady da Dad suka yi suna kuka.
Har lokacin Marka ba ta sauko ba don India Dad na wuri bata zama wajen sai dai ta bar wajen, ya yi roƙo da magiya amma ba ta saurare shi ba. Don ta lura matarsa har yanzu ba ta sauya ba, kuma hakan ya sa Marka ya sake jin ba daɗi. Don tsugunne ba ta ƙare ba .
Ɗakin Mummy Dad ya shiga ya umarce ta da ta bawa Marka haƙuri amma ta ce sam ba wanda ya isa, don ko sau ɗaya ba ta taɓa gaida Marka ba tunda suka zo garin. Buɗar bakinta ta ce ita da Marka har abada, wanda hakan ya saka Dad cewa ta ce gida ya sake ta saki ɗaya.
Kalmar da ba ta taɓa tunanin Dad zai iya furta mata ba kenan ko a mafarki ne, ta shiga tashin hankali Amma sai ta yi ƙoƙarin ɓoyewa. Akwatin kayanta ta ɗauka ta fito, ba kowa a falon duk suna sama wajen Ajmal don duba shi.
.
Tana fit direban Dad ya taso ta dakatar da shi da hannunta. Don ta san motar Dad ne.
Dad ya samu Dady ya sanar da ita rabuwarsa da Mummy, ya ji ba dadi amma ya riga ya faru. Daƙyar Marka ta hakura da fushin da take yi da Dad ganin yadda yake kuka yana ba ta hakuri kuma ta lura wani abun ba yin kansa ba ne,kuma ta ji rabuwar da Dad ya yi da matarsa.
Dad ya sanar da cewa gobe za su je su janye auren Munnir da Amatullah, sannan za'a nemawa Ajmal auren nan da wata yake so a saka bikin, kamar yadda aka tsara na Munnir ɗin.
Dad ne ya kalle shi ya ce.
"Tunda jibi Munnir zai dawo s jira ya dawo idan ya amince to. Kada ya zo bai amince ba ."
Dad ya dage ba komai ya san Munnir zai hakura, sannan ya nuna cewa idan har ba'ayiwa Nihal miji ba to yana so a bawa Munnir sai a haɗa bikin rana ɗaya.
Kowa ya yi farin ciki da hakan musamman Marka don yanzu kan ahalinta ya haɗu. Ko da Marka ta samu Nihal da zancen ta ce ba ta da zabi Allah ya sa hakan ne mafi alkhairi a gare su.
Dady da Dad suka je suka samu Abban Amatullah da zancen janye neman auren Amatullah da Munnir ke yi tare da nemawa Ajmal auren.
Abba ya amince kasancewar ya ga mahaifin Munnir ne da kansa, kuma ba za'a canza rana ba ranar da aka saka da shi za'ayi.
Ranar aka sanarwa Amatullah farin ciki a wajenta baya misaltuwa. Ta yi kiran wayar Ajmal amma sai ta ƙi shiga.
A ranar Dady ya dawo Kaduna Dad kuma ya koma gida, yana komawa ya tarar da Munnir ya dawo har yana cin abinci a dinning table shi da Munnira.
Bayan sun gaisa yake tambayar ina Mummy kasancewar bai sanar da su rabuwarsu ba ya ce ta yi tafiya. Minnir ya kira ba ta daga ba
Bayan sun kammala sun dawo falo Dad ya kalli Minnir ya sanar da shi dangantakarsu da Ajmal. Sannan ya bashi labarin halin jinyar da Ajmal ya shiga sakamakon rashin Amatullah, daga karshe ya sanar da shi ya janye saboda ya nemawa Ajmal auren ta yanzu.
A matukar firgice Munnir ya kalli Dad tare da miƙewa tsaye.
"Wallahi Dad ba zan iya bar masa ita ba, ba zan iya ba."
Yana gama faɗar haka ya nufi bedroom ɗinsa cikin ɓacin ran hukuncin da Dad ya yanke.
*Maman Ihsan ce* ✍️
09065327995
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*🤦♀️'YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi KNT
(Manman Ihsan)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page1️⃣0️⃣4️⃣
"Wallahi Dad ba zan iya bar masa ita ba, ba zan iya ba."
Yana gama faɗar haka ya nufi bedroom ɗinsa cikin ɓacin ran hukuncin da Dad ya yanke
Da kallo Dad ya bishi tare da mamakin abinda yake faɗa masa, don ya ɗauka idan ya masa bayanin komai da ke faruwa da dangantakar da ke tsakaninsu da Ajmal da halin da ya shiga dalilin ɓacewarta. Amma sai ya ga ba haka ba, amma zai bashi kuma lokaci zuwa gobe ya san lokacin ya sauko.
Ganin Dad ya shiga damuwa ya sa Munnira sakin murmushin ƙarfin hali ta ce.
"Dad kar ka damu na san zai sauko zuwa anjima zan ƙara masa bayani."
Jinjina mata kai ya yi cikin son ɗabi'unta ya ce .
"Allah ya yi maki albarka."
Da Amin ta amsa ta tashi ta bar wajen.
Da misalin ƙarfe tara na dare Munnira ta yi knocking a ƙofar ɗakin Munnir, har sau uku bai amsa ba, sanin ya ji ta ya sa ta shigo bakinta ɗauke da sallama. Tana riƙe da tire a hannunta wanda ta jero masa abincinsa akai.
A saman tebur dake ɗakin ta ajiye abincin, kallon sa ta yi yana sanye da farar singileti sai wanda three quarter sai faman Safa da marwa yake yi a ɗakin.
"Yaya ga abincin ka nan na ga baka fito cin abinci ba ne ga shi har dare ya fara."
"Ba na jin yunwa."
"Yaya dan Allah ka bani mintuna biyu."
Zama ya yi tare da zuba masa idanu..
"Yaya don Allah ka yi haƙuri ka bi maganar Dady, ya yanke wannan hukuncin ne saboda yana da yaƙinin cewa ya isa da kai kuma za ka masa biyayya. Ya yanke wannan hukuncin ne saboda ceton rayuwar masoya biyu, wanda ke barazanar tarwatsewa, idan ka ga halin da Ya Ajmal ke ciki wallahi sai ka tausaya masa."
Kallonta kawai yake yi ba tare da ya yi magana ba, in da ta cigaba da cewa.
Sannan ita kuka Nihal din da aka baka fa na dan za ka so ta, wallahi kyakkyawa ce ita ma fara ce zubin Fulani. Ka ga kamar yadda aka faɗa maka zancen auren Nihal ba tare da ka san ta ba ita ma haka aka sanar da ita zancen, ba ta san ka ba amma ta yi biyayya ga iyayenta ta ce ta amince Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi. Ta burge ni har nake ce mata ba ki san Ya Minnir b kin anince , buɗar bakinta ta ce ba sai na gan shi ba na san iyayena ba zasu zaɓa mani abinda zai cutar da ni ba, kuma ko ba komai ɗan uwana ne ba zan ƙi shi ba. Don Allah kai ma kada ka watsawa Dad ƙasa a idanu da mahaifiyar Nihal da Dad ɗin mu da Dad ɗin Ajmal uwa ɗaya uba ɗaya suke. Nima fa ko da aka sanar da ni zancen auren Ya Sudais amincewa na yi fama ɗaya daga haɗa da na ku da na Ya Ajmal.
"Waye Saidais?"
"Shine Wa s wajen Niha ƙwnwsrsa ce ita 'ya'ya ne a wajen Mama wato autar su Dad ka ga anyi one one kenan ko? Kai za ka auri ƙanwar Ya Sudais shi ma zai auri taka ƙanwar."
Tsawa ya daka mata tare da nuna mata ƙofa, da sauri ta fita tana tura baki.
Tana fita sai ga kiran wayar Mummy ya shigo wayarsa ɗauka ya yi ya ƙara a kunnensa bayan ya yi picking.
Sallama ya yi bayan sun gaisa ne ya ce
"Mummy yaushe za ki dawo duk da ilna san kin san komai."
"Ba abinda na sani,domin Dad ɗin ku ya sake ni."
A firgice Munnir ya miƙe tsaye.
"What?"
Katse kiran wayar ya yi inda ya fito ya tarar da Dad da Munnira.
"Dad me ka aikata haka akan me za ka daki Mum a wannan shekaru na ku?"
Sai s lokacin Munnira ta sani. Kuka take yi kamar ranta zai fita.
Sai da suka dauki mintuna kafin Dady ya ce.
"Matukar na cigaba da zama da mahaifiyar ku yi bani ba dangina, ga fushin iyaye da ke kaina sama da shekaru talatin, wanda ban ji dadin rayuwar da nake ciki ba sai yanzu da na shirya da ahalina, wanda Mummynku ba ta so hakan ba, shi ya sa na yake hukumcin da ya dace."
Yana gama faɗar haka ya bar wajen.
Bangaren Amatullah sosai Umma ke gyara ciki da waje, tun daga kan kayan mata har zuwa gyaran jiki. Kuma har lokacin ko ta kira wayar Ajmal ba ta shiga, haka ta hakura ta ƙyale shi.
Ɓangaren su Marka kuwa yau suka shirya don komawa Yola, Marka, Mama, Saidais da Nihal. Gabaɗaya suka wuce inda Ammi da Ummi Kakar Ajmal sai Dady suka taka su har airport. Ɓangaren Ajmal kuwa duk da ya samu sauƙi Alhamdulillah amma bai koma walwalarsa kamar baya ba, yana ƙoƙarin ɓoye damuwarsa ne don kar su Dady su sani.
Ganin haka ya sa suka sanar da shi zancen auren sa da Amatullah, dama surprise suke so suyi masa sai ranar da aka ɗaura su sanar da shi, amma taron kada ya shiga wani halin suka sanar da shi. Ranar farin ciki kamar zai kashe shi dama ashe Munnir ɗan uwansa ne basu sani ba, duk da ya san Dad da Munnira da suka wuce ya san matsayin su a wurinsa amma bai san cewa Dad mahaifin Minnir ba ne tunda ba tare suka zo ba.
Ji y yi ba abinda yake bukatar sama da jin Muryar Amatullah. Dai dai ya ta kiran wayarta ba ta shiga. Ita kuwa kasancewar wayar Ajmal ba ya shiga kuma ga Munnir da ya dame ta da kira da text messages ya sa ta lashe wayar gabaɗaya.
Tsabar farin ciki Ajmal ya ce a sanarwa Minnir da Sudais kada su siya kayan lefe, shi da kansa zai haɗa masu lefe iri ɗaya. Sudsis ya yi farin ciki da jin haka, Munnir kuwa ya ce su dole tunda yana son ƙwace mani mata kuma bai isa ba wallahi.
Ajmal ya bawa Ummu da Ammi kuɗi mai masu yawa suka je Dubai don haɗo lefe kala uku masu kyau. Akwatuna kala ɗaya sai dai na Minnir da Sudais guda takwas yayin da na Ajmal guda goma sha biyu.
Marka ta saka Dad cewa ya kawo mata Munnir ta zauna a can tunda Mum ba ta gidan ga biki ya matso. Haka kuwa ka yi Marka ta haɗa su d ma Nihal tana masu gyaran Amarya.
Sosai Umman Amatullah ke gyara ta kasancewar ta haihu, duk da ba da kanta ta haihu ba tiyata aka yi mata aka cire yaro amma tana bukatar gyara. Don haka sosai take gyara 'yarta.
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 48 Chapter of 51