Babu yadda Mummy ba ta yi ba don Dad ya dawo da ita ɗakinta amma sam ya ƙi amincewa. Hankalinta bai sake tashi ba sai da Munnira ke sanar da ita cewa kakarsu ta ɗauke ta wai tana zauna a can wajenta saboda ba Mummy. Hankalinnta ya sake tashi yanzu fa shikenan an raba ta da Munnira, don Marka na shirin aurawa jikanta Sudais ƴarta. Ga shi yanzu sun taba ta da Dad shirin ta take ya na tsawon shekaru yau ya ruguje komai ya lalace mata kwaɓarta ta yi ruwa. Dole ma ta zuga Minnir ne don kar ya yarda ya karɓi Nihal a matsayin mata.
Wayarta ta lalubo ta dannawa Minnir kira don kadai ne yake gani zai bi maganar ta, don ta san Munnira ba za ta yarda ta karbi maganarta ba ta san halin yarinyar kamar ba jininta ba. Duk yadda ta so zuga Munnira akan ta bijire amma fir taƙi karshe ma ce mata ta yi idan ba ta daina zuga ta ba sai ta faɗawa Dad. Shi ya sa ta biyo wajen Munnir.
Yana sanye cikin tausasan yadi mai ruwan coffee, hula kalar bround ya saka sannan ya feshe jikinsa da turare, yana ɗaura agogon hannunsa lokaci zuwa lokaci yake sakin siririyar tsuki, wayarsa ta yi ruri ya duba ya ga Mummy ce.
Ɗauka ya yi tare da sallama bayan ya gaishe ta ne yake cewa.
"Gani nan ina shiri saura mintuna talatin jirgin mu ya tashi, Dad ya saka ni gaba aka yau sai na je na haifa Familynsa na kuma gana da yarinyar da zai aura mani."
"Kana nufin zuwa za ka yi?"
Tambayar da ya ji Mummy ta yi masa kenan.
"To Mummy kema fa kin san halin Dad yanzu ya canza ba kamar a baya ba ne. Yanzu idan ya faɗi magana ɗaya ya faɗa kenan babu wasa."
"To akan ka auri wannan yarinyar gara ka auri Hafsat ai."
Murmushin takaici ya yi tare da cewa.
"Ni fa na sha faɗa ba zan taɓa auren Hafsat ba wallahi."
"Eh kana da bakin faɗa mani haka don na ce ka auri ƴar ƙanwata, amma yanzu ga mahaifinka yana so ka auri ƴar ƙsnwarsa ba ka masa gardama ba."
"Ita ma yarinyar ba son ta nake yi ba kuma ba aurenta zan yi ba, Mummy kada na yi missing fly na kusa makara zamu yi magana."
Yana gama faɗar haka ya katse kiran wayar tare da ɗaukar ƙaramar jakarsa ya fice bayan ya saka takalmi.
*ADAMAWA*
Zaune take ta haɗa tagumi gabaɗaya ta faɗa duniyar tunani, tun da aka faɗa mata wanda zai aure ta zai zo su gana. Munnira ce ta shigo ɗakin, ganin yadda Nihal ta yi nisa cikin duniyar tunani ya sa ta dafa kafadarta. Ɗagowa ta yi ta kalle ta, Munnira ta sakar mata murmushi tare cewa.
"Kina tunanin Yayana ne?"
Murmushin ita ma ta sakar mata tare da cewa
"Eh kamar yadda kike tunanin nawa Yayan ko?"
"Kar ki damu yana kan hanya, me za ki girka masa, tashi mu shiga kitchen na taya ki masa girki."
Hannunta ta ja suka fita daga ɗakin.
Lokacin da ya iso Munnira ce ta kira Sudais ya zo suka je suka ɗauko shi, suna kan hanyar komawa gida Munnir na zaune gefen Sudais yayin da Sudais ke driving Munnira sai surutu take dubawa yayan nata, tana bashi labarin yadda take jin daɗin garin sosai.
A harakar gidan Marka Sudais ya yi parking suka fito, Munnira na riƙe da hannun Munnir dayan hannun ta riƙe jakarsa.
"Yaya sati nawa za ka yi a garin nan?"
Harararta ya yi tare da cewa
"Ke za ki je ki Mani aikin da zan yi a can?"
Sudais na biye a bayan ta tsaya tana riƙe da hannun Munnir ta ce.
"Yaya ga mijina nan ku ƙara gaisawa."
Irin kallon baki da kunyar nan ya yi mata, sannan ya ce.
"Anan za mu gaisa ba sai Mun shiga ciki ba, na ga fa kanki na rawa."
Ɓoye fuskarta ta yi a damtsen hannunsa tana dariya ta kalli Sudais, idanunsa ɗaya ya kashe mata ta kawar da kai da sauri.
Da sallama suka ƙarasa falon yayin da Munnira ke ƙwalawa Marka da Nihal kira.
Marka ce ta fito tana washe baki.
"Angon nawa ne ya iso?"
Gaida Marka ya yi sannan ya zauna akan kujera. Ta amsa cikin farin ciki da ganin jikan nata wanda har farin ciki ya kasa ɓoyuwa a fuskarta.
Nihal ce ya fito daga ɗakinsu ta ƙaraso wajen, cikin sanyin murya ta ce
"Sannu da zuwa Ya Munnir."
"Yauwa sannu."
"Ina wuni an zo lafiya?"
"Lafiya lau."
Munnira ce ya taba ƙafarsa, kallonta ya yi ta masa alama da Nihal. Cikin raɗa ta ce.
"Your wife to be..."
Hararar da ya mata ne ya sa ta fara dariya.
Marka ce ta ce a kai shi ya yi wanka ya ci abinci.
Washegari yana zaune a falo Marka ta turo masa Nihal don su fahimci juna. Kallonta ya yi tare da cewa.
"Me ma kike da suna?"
"Nihal."
Ta bashi amsa.
"Okay to Dad ya faɗa mani shawarar da suka yanke na haɗa mu aure ke ce kika ce kina so na?"
"Ba ni ba ce nima haka suka sanar da ni ba tare da sun yi shawara da ni ba."
"To kin anince kenan?"
"Ba na da jayayya akan maganar su."
"Kina so na kenan?"
Shiru ta yi don jin ta yi amsar ta mata nauyi a baki. Sai da ya sake tambayarta ta ce .
"Ai ba zan ƙi ka ba."
Taɓe baki ya yi tare da cewa.
"Ina son ki sanarwa iyayen mu cewa ba ki so na a fasa zancen auren nan."
Da sauri ta kalle shi tare da cewa
"Saboda me?"
"Saboda ina da wacce nake so kuma ba zan iya hakuri da ita ba, shawara da zan baki ku lalata zancen auren nan idan kuma kika bari aka ɗaura auren nan har aka kai ki gidana to za ki sha baƙar wahala, don sai kin gummaci zaman gidan yari akan gida na."
Ƙwalla ne suka cika mata idanu ta yi saurin mayar da shi sannan ta ce .
"To ai kai ya dace ka sanar da su gaskiya ba ni ba."
Murmushin gefen baki ya yi tare da cewa
"Da alama ba za ki iya ba ko? Shikenan ki fara tausayin kanki tun yanzu."
Marka ce ta fito ta same su ta kalle su ta ce.
",Nihal ki kai shi ya gaisa da Mamanki da Abbanki ko?"
"To."
"Minnir ka je ka gaida surukanka kuma Gwaggonka."
Murmushi ya yi tare da cewa.
"To ba damuwa."
Makullin mota ta mika masa ta koma ciki.
Kallon Nihal ya yi wacce kanta ke sunkuye.
Shirin tsuki ya ja ya miƙe ya nufi hanyar fita
Kasancewar akwai mayafi a jikinta ta mara masa baya.
Gidan Mama suka je suka gaishe ta cikin sa'a kuwa suka samu Abban Nihal a gida, sun ji daɗin ganinsa, kuma bai nuna masu wata alamar cewa baya son hadin auren ba. Kuɗi ya basu kyauta lokacin da za su wuce, Mama ta ce da Nihal ta kai shi ya ga Baffa da wani ƙanin Mahaifin Nihal. Ba musu ita take nuna masa hanaya har suka tafi ko ina da ya dace.
Kuma ya ƙara tabbatar wa Nihal baya son auren ta janye amma shi ba zai iya ba, ita ma ta nuna ba za ta iya ba, ya mata alkawarin zaman ƙuncin da za ta yi da shi.
Kwanansa biyu a Yola ya tafi ya bar garin.
Wasa-wasa yau saura sati ɗaya bikin na su an kai lefen Nihal da Amatullah sai na Munnira. Murna a wajen wannan family ba'a magana. Amma Nihal kam ba ta cikin walwala duk da ya ga dangi kowa murna yake yi, kuma yau ne aka ce ya kira Minnir a waya su tsara yadda za su yi shagalin nasu bikin.
Munnira da Saidais kuwa soyayya suke zubawa ba kama hannun yaro. Ajmal ma yau ya shirya zuwa wajen Amatullah.
Lokacin da Nasreen ta ji labarin auren hankali a tashe ta diro ƙasar.
*Maman Ihsan ce*✍️
🤦♀️ *YAR MAYE*🤦♀️
(_the drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page 1️⃣0️⃣5️⃣
Lokacin da Nasreen ta ji labarin auren hankali a tashe ta diro ƙasar, ba wanda ya san da zuwanta. Ammi da mahaifiyarta Ummi sai wasu danginsu larabawa su biyar suna zaune a falo sai suka ga Nasreen kamar an jefo ta. Gabaɗaya zuba mata idanu suka yi suna kallonta, wata ƙanwar Ummi ce ta yi magana cikin harshen larabci suke magana.
"Wannan ba ita ce matar Ajmal ba, daga ina take?"
"Ammi cikin takaici ta ce daga wajen iyayenta."
Wata kuma ta ɗora da cewa
"Wai har yanzu iyayenta ba za su daina wannan abin ba sam basu san darajar aure ba "
Taɓe baki Ammi ta yi tare da cewa.
"Su dai suka sani ba sai su yi ta riƙonta ba, idan wata masifar ce. Tunda yanzu in sha Allah ya damu wacce za ta kula da shi ai shikenan."
Murmushi Ammi ta sakarwa Affan dake riƙe da gefen rigarta.
Da sauri kamar jira yake ya ƙarasa jikin Ammi yana murmushi. Nasreen ganin kamar maganarta suke ya sa ta sakin trolley bag ɗinta, s hankali ta ƙaraso gabansu tare da zubar da guiwar ƙafarta a ƙasa. Cikin kuka ta ke magana.
"Dan Allah ku saka baki ku hana shi auren nan wallahi zan kasance duk yadda yake so na yi alƙawari, don Allah a janye zancen auren nan na tuba, na bi Allah na bi ku."
Ammi ce ta riƙo hannunta tare da cewa
"Kin ga Nasreen ki kwantar da hankalinki wannan auren ki ɗauke shi ƙaddara ce, haka Allah ya so, ki yi wa mijinki addu'a Allah ya bashi ikon yin adalci a tsakaninku, ya baku zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba."
Fisge hannunta daga rikon da Ammi ta mata ta yi sannan ta wuce ko ta kan trolley da ya shigo da shi ba ta biyu ba, a guje ta haura upstairs tana kuka., shi ko Affan bin bayanta kawai yake yi da kallo har ta ɓacewa ganinsa.
"Allah ka kyauta."
Ammi ta faɗa sannan ta kira ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan ta zo ta durƙisa cikin girmamawa sannan ta ce
"Ga ni Hajiya.".
Umarni ta b ta kan cewa ta ɗauki trolley na Nasreen ta haura mata da shi part ɗin su, sannan ta kira wacce ke kula da Affan ta bata umarnin ta je ta masa wanka ya ci abinci.
To ta ce cikin girmamawa sannan ta tashi ta ja hannun Affan suka tafi.
Kwance take a ɗakinta tana kallon Khalifa da ke wasa da kayan wasansa, kallon sa take tana murmushi cike da ƙaunar yaron, saboda tsantsar kamannin da yake yi da Mahaifinsa. Komai nasa irin na Ajmal ne. Hotonsa da ke wayarta ta duba tare da turawa hoton idanu tana shafa fuskarsa tana murmushi.
"Ko yaushe za ka zo na saka ka a idanuna, kullun cikin tunaninka da begenka nake, na ɗauka tunda aka mayar da aurena da kai za ka zo gare ni."
Tunawa da ta yi yana da wata matar sai ta turo baki tana cewa.
"Kila ma ni ce kawai na damu da shi tunaninsa ya hana ni sukuni, yanzu haka yana can wajen matarsa shi ya sa tsawon kwanki bai kira ni ba, kuma idan na kira shi wayar ba ta shiga."
Wayarta ce ta yi ruri, har ta katse ba ta ɗauka ba kasancewar ta ajiye wayar bayan ta gama kallon pics ɗinsa.
Sai da aka sake kira a karo na biyu sannan ta duba ganin Ajmal ne jikinta har ɓari yake hannunta na makarkata ta ɗaga tare da yin shiru. Shima shirin ne ya yi ganin ba ta da niyyar yin magana ya sa ya daki murmushi wanda har sai da ta ji sautin murmushin nasa
.
Tura baki ta yi tana kunkuni.
"Me kike cewa ma? Wato kina kishi da matata ko?"
Mamaki ya kama Amatullah wai shi dai kamar wani aljani da idan ta yi magana yakan ji, kuma ya na sanin ta fita. Ba ta gama tunanin da take yi ta ji ya ce
"Ina ƙofar gida?"
Cike da farin ciki da ɗoki ta ce.
"Ƙofar gidanmu?"
"Eh, ki fito Mani da yarona na ya missing ɗinsa ."
Nan da nan ta fito waje cikin rawar jiki ta ɗebi ruwa ta shiga bayi ta yi wanka, tana fitowa sauri-sauri ta goge jiki ta shafa man shafarwarta mai ƙamshi ta shafa a jiki da turarurruka da humra masu daɗin ƙamshi. Ta shirya cikin atamfa holland mai ruwan ganye, ɗinkin riga da siket sai farin mayfi da ta yafa a kanta madadin ɗankwali, powder ki ta shafa sai manbaki.
Ɗaukar Khalifa ta yi tare da ficewa ɗakin fuskarta ɗauke da annuri ta nufi ɗakin Umma, lokacin Umma na zaune a saman kujera tana waya da Abba, ganin Amatullah da alamar fita za ta yi ne ya saka ta yin sallama tare da katse kiran wayar.
Smsa sallamar da Amatullah tayi tare da zuba mata idanu din jin me za ta ce.
"Umma Ya Ajmal ne ya zo yana waje."
"To ki gaishe shi."
Da to ta amsa yayin da ta nufi ƙofar gidan. Yana jingina da jikin motarsa. Yana sanye cikin wata tsadaddiyar shadda mai ruwan sararin samaniya, kansa ba hula gashin kansa sai sheƙi yake yi har zuwa keantaccen sajen da suka yi wa fuskarsa ƙawanya. Sai sheƙi suke alamar ana kulawa da su.
Lallausan murmushin da ba ta san ya iya shi ba ne ya sakar mata, ita ma ba ta san lokacin da ta maida masa martanin murmushi tana kallon sa kamar ta riuga ta rungume shi take ji s jikinta. Sai dai ta ga ya yi 'yar rama ba kamar yadda ta san shi ba..
A hankali ta ƙarasa wajen da yake tsaye jikin mota ya zuba hannayensa a cikin aljihu '.
Karbar Khalifa ya yi daga hannun Amatullah yana sakar masa murmushi. Sumbatar goshinsa ya yi . Sanin cewa ba ta yarda da fira a mota ya saka ya ce su je ciki, a saman bencin suka zauna. Fira suka fara yi sosai cikin son juna da ƙaunar juna.
"Ya Ajmal na ga ka rame."
"E rashin lafiya n yi."
"Subhanallah me ya same ka?"
",Ciwon son ki."
Murmushi ta yi don ba ta yarda ba, kallonta ta ji tare da cewa.
"Me da me kuke buƙata ne, sannan kuma ki fadawa Abba da Umma ba ka buƙatar ko cokali su kawo ki da shi a gidana. Ko mai d ke yi wa 'ya mace ni zan maki ba bukatar su wahalar da kansu. Ke kawai nake bukatar a akai Mani sai yarona
Tsananin farin ciki da ke zuciyarta ta kasa ɓiyewa, yana rungume da ɗansa daga shi har ita kun san cewa suna cikin farin ciki.
"Ya Ajmal ya aka yi aka mayar da aurena a kanka?"
Nan ya sanar da ita komai dake tsakanin su a Minnir da hukuncin da Dad ɗin Munnir ya yanke.
"Yanzu kai da Munnir dangi ne?"
Jinjina mata kai kawai ya yi tare da sakin Musulmi.
Kamar daga sama suka ga Munnir tsaye gabansu fuskarsa. Murtuƙe, mamakin ganinsa suke yi '
Ajmal ya mika wa Minnir hannu don su yi mussbaha har yana sakar masa murmushi tare da furta kalmar Assalamu alaikum.
Kau da kai Munnir ya yi bai amsa sallamad ba ballanta ya saka ran miƙa masa hannun. Ganin take-takensa ne ya sa ya mayar da hannunsa, wasa ya cigaba da yi wa yaronsa wasa.
Munnir ya kalli Amatullah tare da cewa.
"Zan yi magana da ke."
Yana gama faɗar haka ya fita.
Kallon mamaki take binsa d shi kafin ta mai d dubanta ga Ajmal ta ce.
"Ina zuwa Please."
"Je ki dawo "
Ya fada fuskarsa ba walwala.
Bayan Amatullah ta fita ne ta samu Munnir tsaye yana jiranta.
"Tabbas na hangi tsantsar da kaunar da kuke yi da juna ke da Ajmal, na hang soyayyar da kike yi wai Ajmal a idanun ki."
Murmushin da ya fi kuka ciwo ya yi sannan ya ce.
",Albishirinki."
Kallon sa kawai yake ta kasa cewa komai.
"Ki shirya ko na ce ku shirya kyauta ta musamman da zan ba ku daren ranar d aka ɗaura maki aure sure da angonki, ranar za ku gane me nake nufi, kar ki manta da wannan."
Yana gama faɗar haka ya koma cikin motarsa ya figi motar ya bar wajen.
Cikin sanyin jiki da rashin gane inda zancen sa ya dosa ta koma ciki.
Firar da ba su cigaba ba kenan kowa ransa, tashi y yi ya nufi motarsa ya fito da wata babbar jaka y mika mata.
"Ga wannan kuɗi ne, Naira miliyan uku ne kuyi hidima na biki da kuɗin, na faɗa maki kada a kawo ko cokali zan ƙi maki komai fatan kin gane."
Tsabar farin ciki har da ƙwalla sai da ta yi, don dama ba abunda ya tsayawa Abba a rai kamar kayan ɗaki da kayan gara har yana tunanin siyar da gonarsa.
Kallon Ajmal ta yi wanda tun zuwan Munnir ta lura da yanayinsa ya sauya, ƙsrshe ma sallama ya mata ya ce gobe zai dawo ya gaida Abba da Umma.
Khalifa ta karɓa tare da jakkar kuɗin ta shiga cikin gidan.
Umma ta yi mamaki yawan kuɗin inda farin ciki ya bayyana, take ta kira Abba ta sanar da shi, don ya fasa siyar da gonar da suka dogara da shi.
Ɓangaren Minnir kuwa duk yadda Munnira ke ba bin shi akan events da zasu yi cewa ya yi ba abinda zai yi. Har ta tambaye shi cewa ya yi wa Ajmal godiya na akwatuna da kayan lefen da ya siya masa, ƙarshe sai ya rufe ta da faɗa ya kashe wayarsa. Jikinta ne ya yi sanyi don ta lura sam Nihal ba ta gabansa, ga Nihal ɗin Duk ta koma ba walwala a tare da ita, duk yadda Marka da Mama suka tambaye ta cewa ta ji ba komai.
Ɓangaren Mummy kuwa duk yadda ta so Dad ya mayar da ita sam yaƙi yarda ya saurare ta ƙarshe ma sai ya yi blocking ɗinta.
Bayan Ajmal ya koma gida yana zaune a bedroom ɗinsa yana danne-danne a laptop Nasreen ta banko ƙofar da ƙarfi ta shigo, ko ɗaga kai bai yi ba ballantana ya kalle ta, don ya san ko wace ce.
Gabansa ta tsaya tana huci, ni za ka yi wa kishiya Ajmal, ni za ka haɗa da waccen 'yar matsiyatsn da ba ta isa na yi kishi da ita ba? To ko wacce ta fita ba zan taba barin ka aure ta ba ballantana wannan ƙasƙantacciyar yarinyar da ba ta isa na hada kafaɗa da ita ba. Kwanciyar hankalin ka da zaman lafiyarka shi ne ka janye zancen auren nan, idan kuma ba haka ba sai na kashe yarinyar nan, kar ka ɗauka wai barazana nake maka, ba barazana ba ne gargaɗi ne, idan har kana son ta cigaba da rayuwa a doron ƙasa to ka rabi da ita, idan ka yi watsi da magana ta to tabbas sai dai ka auri gawarta don sai na kashe ta kuma na kashe banza wallahi.
Haka ta cigaba surutu kamar wacce ba ta cikin hayyacinta, ganin bai kula ta ba ne ya sa ta kai hannu ta jefar da laptop ɗin da yake aiki akai. Sai a lokacin ya dago ya kalle ta ganin yadda idanunsa suka yi ja ne ya sa ta ɗan tsorata, bai kula ta ba ya ɗauki laptop ɗin ya ajiye sannan ya nufi kofar fita, don baya son ya biye mata, har ya kai bakin ƙofa ya ji tana cewa.
"Wadancan shegun akwatunan da ka kawo Mani wai na fadar kishi ko danne kirji ne oho maka, ka kwashe su ka kai mata ita ce ke fatarar sutura ba ni ba, 'yar iska karuwa macijiya da ba ta ramin kanta."
Ficewa ya yi ya barta ganin bai kula ta ba ta zube a wajen tana kuka.
Ana saura kwana uku ɗaurin aure Ajmal ya turo masu decorations suka zo gidan a wani part dake bayan na su Ammi, anyi sabon fenti an ƙawata shi, madaidsici ne sai dai bai kai na su Ammi ba, don da ya ce gidanta daban zai kai ta ba zai haɗa su gida ɗaya ba, Ammi ta bashi shawarar ya ajiye ta a anan. Falo biyu ne sai ɗakuna guda huɗu kowane ɗaki da toilet a ciki, sannan akwai wani a falo, sai dinning area da kitchen sai store.
Fentin white and purple ne ya yi kyau sosai, hatta labulayen da aka saka kalar fentin ne da Centre carpet kujerun ma kalar labulayen ne s ɗayan falon ne aka saka kujerun blue, ɗakuna uku aka zubawa furnitures masu kyau, ɗaya ɗakin duk yafi haduwa da alama na amarya ne, ɗayan ɗakin kuma a rufe yake.
Ba wani shagalin da zasu yi a nan don Amatullah ta ce walima kawai za ta yi, ba ruwansu da bidi'a. Amma ya ce idan aka daura auren sai an fara kawo ta gidansa da ke garin nasu kafin su zo Kaduna.
Nihal ma Iyayenta sun bayar da kuɗi idan an zo garin Minna a siya mata kayan ɗaki a can, saboda Adamawa da nisa. Haka kuwa aka yi wasu 'yan uwan mahaifin nata da na Mama suka zo suka sauka a gidan Dad.
Shi da kansa ya sa aka kai su gidan Munnir don su fara zuwa su gani gidan.
Gidan ba laifi ya yi kyau sosai sabon gini ne ya yi na zamani ɗakuna huɗu sai BQ daga baya.
Munnira kuwa gida ɗaya za su zauna da Mama ƙanwar Dad ɗinta kuma mahaifiyar Sudais. Sai dai kowa da part ɗinsa.
Ita ma ranar aka gyara mata ɓangaren da za ta zauna, sai dai suka dangin Dad ne ba ɗan uwan Mummy ko mutum ɗaya.
Amatullah na zaune a ɗakinta ita da ƙawarta Fadeela sai kuma wata ƙawarta mai suna Husna, tana cin kazar da aka dafa mata na maganin mata wanda take jin wani bauri tana yamutse fuska, sai dariya suke mata, Fadeela ce ta ce.
"Ai Gara ki ci ko wacce ba ta haihu ba ana gyara ta ballantana ke."
Dariya ta yi tare da cewa
"Ai ko ni ban haihu ba don farkawar na yi na ga an yanka ni har an ciro baby, har yanzu a matse nake."
Hararar ta Husna ta yi tare da cewa.
"To ta ina shi Ajmal din ya bi har kika samu yaron tunda s matse kike?"
Dukan wasa ta kai mata tare da cewa.
"Abinda sau ɗaya ne kuma..."
Fasa ƙarasa maganar ta yi lokacin da wata ƙawar Umms ta shigo da wani kofi da magani ta ce .
"Karbi ki shanye yanzu ki bani kofi."
Haka ta karɓa tana sha tana rufe idanu har ta shanye.
Bayan ta fita ne wayar Amatullah ya soma ruri, ganin Munnir ne ya sa ta ƙi ɗagawa. Zuwa can sai ga shigowar saƙo, buɗewa ta yi tare da karantawa. Dari idanu ta yi tana kallon messages ɗin. Zunbur ta miƙe Kamar wacce aka tsikara.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
*🤦♀️'YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*_SAURA PAGE ƊAYA NA GAMA BOOK 1 ZAMU SHIGA BOOK 2 WANDA SHI KUMA BA FREE BA NE KAMAR BOOK 1_*
Page1️⃣0️⃣6️⃣
Bayan ta fita ne wayar Amatullah ya soma ruri, ganin Munnir ne ya sa ta ƙi ɗagawa, zuwa can sai ga shigowar saƙo, buɗewa ta yi tare da karantawa. Zare idanu ta yi tana kallon messages ɗin. Zunbur ta miƙe Kamar wacce aka tsikara.
Kallonta Husnah ta yi tare da cewa
"Me yake faruwa?"
Ƙoƙarin daidaita mutuwarta ta yi tare da cewa.
"Ba komai."
Zama ta yi tana ƙara duba wayarta kallo ɗaya za ka mata ka san a firgice take. Amma sai ta yi ƙoƙarin ɓoyewa saboda ba ta so kowa ya sani.
Hafsat na zaune ita da ƙawarta bayan sun gama shaye-shaye sun tashi barci, kallonta Nafeesat ta yi tare da cewa.
"Ni dai a shawara da zan baki ki haƙura da Munnir kawai tunda saura kwana biyu a ɗaura masa aure."
"Ba zan taɓa hakura da Munnir ba, kar ki manta akan son da nake masa ne na saka rayuwar Amatullah cikin garari, ko kin manta saboda yana sonta na lalata rayuwarta, me kike tunani zan iya aikatawa akan macen da ta yi kuskuren aurensa?"
Kallonta Nafeesat ta yi tare da cewa.
"Hafsat hakkin Amatullah ma kaɗai ya ishe ki, saboda haka ki bar Munnir da matar da zai aura kema ki yi addu'a Allah ya baki wanda ya fi shi. Don duk da kasancewar ki ƴar ƙanwar Mamansa kuka Mamansa ba ta son auren amma ba yadda ta iya to wace ce ke da za ki yi wani abu akai."
"Ni Hafsat ba zan taɓa barin su ba, kuma zancen Amatullah ai ta yafe Mani."
Wayarta ce ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 49 Chapter of 51