da kansa ke yi, ga shi nan da kwana uku yake son sake barin k'asar.
Yana zaune ta sake shigowa da sallama har lokacin idanunsa a lumshe, sai dai ta ga ya motsa labbansa alamar ya amsa sallamar amma ba ta ji muryarsa ba.
"Amma kamar ya kamata ka je ka ga Doctor ko?"
Shiru bai ce mata komai ba ta d'auke bai ji ta ba ne sai da ta dake maimatawa ne ta ji ya ce.
"Eh idan na koma masauki zan kira shi "
"To tunda ba ka da lafiya dole sai ka yi tafiyar ne me zai saka ka zo nan garin ba sai ka yi zamanka ba har sai ka samu lafiya kamar tafiyar dole."
Bude idanu ya yi yana kallonta da mamaki, wato shi take fad'a wa haka, shi da gana d'aya ya saka nutsuwa tunaninta da na babynta da take yi kawai ke dawainiya da shi ya kasa samun sukuni gaba d'aya ya kasa jurewa saj da ya zo nan garin duk halin ciwon da yake ji saboda ita, amma take cewa wai me ya sa ya zo tunda bai da lafiya ai tafiyar ba ta dole ba ce. Wato ba ta damu da shi ba kenan saboda tana da wani saurayin da take so shi ya sa ba ta ma yi d'auki ko farin ciki da zuwansa ba take fad'a masa haka, take ransa ya baci Wanda har sai da ta ga jijiyoyin kansa sun tashi, kallonsa ta yi da niyyar sake yin magana sai ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu, tare da bude murfin motar ya nuna mata k'ofar fita alamar ta fita, mamaki ya kama ta za ta sake magana ya kalle ta da rikitattaun idanunsa Wanda take ta ji shakkarsa ta kama ta, jiki na rawa ta fita daga motar ta kulle masa murfin motar, key ya yi wa motar zuciyarsa na masa zafi ya ja motar ya bar wajen.
Mamaki ya kama ta dan ita ba ta ga abunda ta yi masa Wanda zai saka shi bacin rai ba, dan haka ta tabe baki ta shiga cikin gidan.
Bangaren Nasreen kuwa tun ranar da ta isa America wajen iyayenta suka shiga tashin hankali da ganin yanayinta, dan Kallo d'aya zaka mata ka gane tana cikin tashin hankali, ko da ta isa Dad dinta baya nan, Mom dinta ta samu, ta rungume ta tare da sakar mata kuka, ganin yadda take kukan ne ya saka Affan shima yin kukan, nan ta kwashe zance k'arya da gaskiya ta fadawa mom dinta, har da cewa a gaban Ajmal yana Kallo karuwarsa ta mata duka,bayan ya kawo ya d'akin da take sai da ta ji mata ciwo ta fita ya mara mata baya, Mom ta tambaye ta su Ammi sun sani, ta nuna sun sani amma ba su ce komai ba,ran Mom din ya sake baci waya ta d'auka ta kira Dady a waya, ba shiri ya dawo gidan aka sanar da shi abunda ke faruwa, dan Mom ranta ya baci sosai har ta yi niyyar Kiran wayar Ammi ta yi mata bala'i amma Dadyn Nasreen ya hana ta, ya ce ta kyale su amma 'yarsa ba za ta koma ba tunda har suka wulakanta masa 'ya, Kuma sai Ajmal ya gane kurensa, d'akinta ta nufa yayain da Mom ta d'auki Affan suka mara mata baya.
Bayan ya yi parking motar ya shiga cikin hotel din ne ya lalubo lambar wayar Dr Khalil, yana dagawa ya ce masa ya dawo, daga nan kuma ya bude d'akin ya shiga.
Kwanciya ya yi akan gadon idanunsa a sama yana tuna zancen Amatullah, dan shi bai ga ta yi murna da zuwansa ba, dan tunda ta shige d'akin sai da Umma ta kira ta sannan ta fito ta kawo masa ruwa.
Haka kawai ya ji zuciyarsa ba dad'i, yana tsaka da wanan tunanin ne sai ya ji knocking k'ofa, bai tashi ya bude ba, sai da wayarsa ta yi ruri sa har sai da ta kusa katsewa sannan ya d'aga kiran ya Kara wayar a kunne, muryar Khali ya ji yana cewa
"Ina waje."
Tashi ya yi ya nufi k'ofar ya bud'e masa ya shigo, komawa ya yi tare da kwanciya kan gadon yayin da Dr Khalil ya ajiye karamin akwatin hannunsa.
"Ya jikin?"
Bai tanka masa ba Kuma bai kalle shi ba, murmushi Dr Khalil yayi tare da bude akwatin da yazo da shi.
Tana komawa gida ta nufi d'akinta tana tunanin me ta fad'a masa da zai sa ya yi fushi da ita, ganin ba ta da Mai bata amsa ya sa ta tabe baki tare da warwara mayafin abayar dake jikinta, zama ta yi akan gadon duk da zuciyarta ba dad'i ganin yanayin yadda ta gan shi.
Magunguna Dr Khalil ya bashi tare da da yi masa allura, sallama ya masa ya na shirin tafiya, don ya ga ya kwanta idanunsa a lumshe a tuaninsa barci yake son yi, sai da Dr Khalil ya bude k'ofar fita sannan ya juyo ya kalle shi ya ce.
" Ya aka yi kazo kai kadai ko amintaccen guard dinka ba ka zo da shi ba?"
"Bai ce masa komai ba ya fit dan shima ya San da wuya ya amsa masa tambayar da ya masa
Yana fita Ajmal ya tashi ya rufe k'ofar bayan ya murza key ya bar key din a jikin k'ofar, zama ya yi a bakin gadon tare da dafe kansa da ke masa ciwo.
Kiran wayar Ammi ce ta shigo cikin wayarsa, Jin ringing din wayar ya San me kira, a kasalance ya bude idanunsa da ke lumshe ya sauke akan wayar, d'auka ya yi cikin cikin yanayin rashin son yin magana ya yi mata sallama,
Ta amsa tare da cewa
"Rabin raina ya kake?"
"Am fine."
Shiru ta yi tare da cewa.
"Ya ka same su Amatullah din da Abdallah?."
"Suna lafiya?"
"Ba ka da lafiya ne na ga yanayin muryarka ta sauya me ke damunka?"
"Ba komai Ammi na kai na ke dan mani ciwo zuwa anjima zai sauka in Sha Allah."
"Kai kadai ka zo ina Ahmad d'in."
"Yana California akwai aikin da na saka shi ya gudanar ne?"
"Okay yanzu yaushe za ka zo don akwai maganar da nake so mu tattauna da kai ne."
"Ammina ko za ki bari sai na dawo ne dan daga nan k'asar china zan wuce."
Shiru ta yi tare da yin nazari kafin ta ce.
"China Kuma?"
"Eh Ammina kinsan ina da hannun jari a babban kamfanin kasuwancin dukkan abubuwan amfani da wutan lantarki. To nan da kwana uku zamu yi zaman tattauna da dukkan masu hannun jari a kamfanin."
Shiru ta yi don tabbas ta San yana da hannun jari a kamfanin da dake k'asar china, kamfani ne da dukkan manyan 'yan kasuwa ke son saka hannun jari a cikinsa.
"To Allah ya taimaka idan ka dawo zamu yi maganar Dan ba ta waya ba ce."
D'an maganar da ya yi ne har ya ji kansa na ciwo don haka ya mata sallama ya katse Kiran wayar.
Umma ce ta fito daga d'akinta daidai lokacin da Amatullah ke fitowa ita ma daga ta ta d'akin, kallonta Umma ta yi tare da cewa.
"Ya tafi ne?"
"Eh na ga kamar baya da lafiya."
Dan Jim Umman ta yi sannan ta ce.
"Allah ya bashi lafiya."
Da Amen ta amsa mata.
Abba ne ya yi sallama Jin Umma na cewa Allah ya bashi lafiya yasa yake tambayar me ya faru, Umma ta sanar da shi Ajmal ne ya zo baya da lafiya ya koma masaukinsa, shima addu'ar ya yi masa sannan ya Kalli Amatullah ya ce.
"In ce dai lafiya, ko akwai abunda ya kawo sa ne?"
"Am ya ce ya zo ganin mu ne wai Kuma me ya saka banyi amfani da motar da ya kawo mana ba, da kudin dake cikin bakin da ta tura ya bani card d'in, na nuna masa ka hana ya ce wai yaronsa ya bawa kudin don ayi masa hidima, motar ma wai ko da bukatar fita ta kama mu sai mu dinga amfani da shi madadin mu nemi abun hawa."
Abba ne ya tsuke fuska ya ce.
"Mota dai ban yarda ace..."
Kafin ya k'arasa suka ji sallamar yaron abokin Abba Kuma makocinsu, Wanda ya kai Umma asibiti lokacin da ba ya da lafiya, masa masa suka yi kasancewar sunan yaronsa Sufiyan ya sa suke kiransa da Baban Sufiyan.
Gai da su Abba da Umma ya yi sai Amatullah ta gaishe shi, ya amsa mata sannan ya Kalli Abba ya ce.
"Abba wannan motar dake zaune a waje tsawon kwanaki a cikin rana ta waye, ya kamata a sauya mata waje saboda tana zai iya lalata motar."
Nan Abba ke sanar masa ko motar waye da hukunci da ya d'auka, sai Baban Sufiyan ke cewa Abba ai tunda ya ba ta motar Kuma ya ce yaronsa ya bawa ka da su Mai da masa su karba kawai shi zai koyawa Amatullah tukin motar, Abba bai goyi bayan ba Sam, sai dai ya amince idan zasu tafi unguwar ta kira Baban Sufiyan idan yana nan ya kai su da motar.
Sallama ya masu ya tafi, daga nan Amatullah ta koma d'akinta bayan ta yiwa Abban sannu da zuwa .
Munnir ne ya fito daga wanka a bathroom dake cikin d'akinsa, shiryawa ya yi cikin wata farar yadi mai ruwan coffee mara nauyi, ya saka hula ya daura agogo sannan ya fesa turare.
Takalmi ya saka ya fito sai k'amshin turare yake yi, Mom d'insa ce zaune a falo tare da Munnirat, Kallo d'aya mom ta masa ta kau da kai tare da tsuke fuska, ya lura da ita dan haka ya zagayo ta gefenta tare da kwantar da kansa a kafadarta ya rungume ta ta gefe, Mom zan fita kiyi mani addu'a samun nasara a inda zan tafi."
"Ina zuwa haka?"
Ta yi maganar idanunta a tv,
" Mom idan na dawo zan fad'a maki sai na dawo."
"Allah ya tsare."
Ta fad'a har lokacin ba ta kalle shi ba, Munnirat ce ta ce
"Yaya a gaishe mani da ita."
.
Ta yi magana tana dariya, zaro idanu ya yi yana kallonta tare da mata alamar ke ko.
Kai tsaye k'ofar gidan su Amatullah ya yi parking, sannan ya fito kai tsaye ya nufi k'ofar gidan, daidai lokacin da Abba ke fitowa daga cikin gidan.
Gaishe da Abba ya yi cikin gairmamawa, Abba ya masa masa cikin fara'a da walwala, don yana ganin kimar Munnir ba kowanne namiji ba ne za'a ce budurwarsa ta fara shaye-shaye kuka ta yi cikin shege ta bar gidan iyayenta, bayan ta haihu ta dawo sanan ace ya cigaba da son aurenta ba. Muryar Munnir ce ta katse tunanin Abba Jin yana cewa.
"Abba lafiya dai ko?"
Murmushi Abban ya yi tare da cewa
"Lafiya lau, bari na turo maka ita ko?"
"Ai Abba wajenka nazo."
Jin haka Abba ya ce to yana zuwa, shiga cikin gidan ya yi ya fito da tabarma ya shinfida masu a zauren gidan.
Bayan sun dake gaisawa Munnir ya kalle shi ya ce.
"Abba dama cewa na yi zan turo magabata na ayi maganar aurenmu da Amatullah."
Murmushi Abba ya sake yi tare da cewa.wanman ba komai ba ne, zai shiga ciki zasu yi shawara da Mahaifiyar yarinyar, idan ya so sai ya sanar da shi duk yadda suka yi, ina Sha Allah ba abunda zai gagara, yanzu ma don ba ta gida ta tafi dubiya ne."
Daga nan Abba ya tashi tare da cewa.
" ko a kira maka ita ne?"
"Ba damuwa Abba bari na kira ta a waya."
Daga nan Abba ya fita ya nufi k'ofar gidan makocinsa inda sukan zauna suyi fira.
Amatullah tana tsaka da yiwa Khalifa wanka sai ta ji wayarta na ruri, ba ta kula ba kasancewar a tsakar gidan suke wanka gashi sai kuka yake yi duk ya rud'a ta, shi ya sa ba ta kula da Kiran wayar ba ta cigaba da yi masa wanka.
Sau uku ana Kiran tana katsewa, sai da ta kammmala ta nade shi towel sannan ta nufi d'akin, daidai lokacin Kiran wayar ta sake shigowa.
Dagawa ta yi don yaron ya yi shiru tun bayan da ta gama masa wanka, d'auka ta yi tare da yin sallama, amsawa ya yi tare da cewa.
"Ina fatan lafiya ina ta kira ba ki daga ba ."
"Lafiya lau wallahi Khalifa nake yi wa wanka."
"Okay ina waje."
Ya fad'a yana katse Kiran wayar, sauri-sauri ta shafa masa Mai ta Sanya masa pampers da kaya ta fesa masa turare sannan ta d'auke shi bayan ta saka hijabi suka nufi hanyar waje.
Yana zaune a Saman bencin da suke zama suna zance, da sallama ta k'arasa ya amsa mata, sannan ya dago kai ya kalle ta, bayan ta gaishe shi ta zauna gefensa tana rungume da Khalifa.
"Har ina shirin tafiya don na ga kin dade."
"Na tsaya shirya shi ne dama na masa wanka."
Kau da kansa ya yi tare da Mai da dubansa ga agogo ganin yamma ya yi ya ce.
"Ai kin kusa hutawa da rainon yaron nan."
Cikin rashin gane inda zancensa ya dosa ta ce.
"Kamar ya yaron da watanninsa uku da sati uku ne na kusa gama rainonsa?"
"Eh mana maganar aurenmu na zo yi wa Abba kika bana son a d'auki lokaci Mai tsayi kuka dole ki Mai da yaron wajen Ubansa ko ki bawa Umma Dan ba za ki zo da shi gidana ba."
Gabanta ne ya fad'a don ta lura yana son raba ta da yaron ne Wanda ita Kuma yadda take ji a zuciyarta ba za ta iya rabuwa da yaron ba, tana son sa sosai.
"Amma Munnir ai bai kamata ka raba uwa da d'anta ba ko?"
"Really."
Ya mata wani irin kallon da ta kasa gane manufarsa kafin ya ce.
"Da shegen yaron za ki zo mani gida a matsayin sa na waye a gare ni da zan rike shi.?"
Rintse idanunta ta yi cike da Jin zafin kalamansa take k'walla ya cika mata idanu,ta tsani a kira shi da shege amma wai Wanda zai aure ta ne yake fadin haka akan d'an da ta haifa take Jin sonsa sama da kowa da komai a rayuwarta, take k'walla suka cika idanunta .
Bi tashar TASKAR MAMAN IHSAN a WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
🤦♀️ *YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
Page8️⃣1️⃣
_Assalamu alaikum warahmatullah, ina maku fatan alkhairi masoyana ku cigaba da hak'uri da ni akan rashin ji na akai-akai da Kuma katancin update, in Sha Allah na kusan kammmala abunda nake yi, Wanda hakan zai saka Ku ji na akai-akai. Sannan ku dinga hak'uri da typing error bana da lokacin tsayawa nayi editing dan na dinga gyra typing error, amma na San sa ku fahimci sakona yadda nake so. I love you all my fan's_
Rintse idanunta ta yi cike da Jin zafin kalamansa, take k'walla suka cika mata idanu. Ta tsani a kira shi da shege amma wai Wanda zai aure ta ne yake fadin haka akan d'an da ta haifa take Jin sonsa sama da kowa da komai a rayuwarta take k'walla suka cika idanunta. Kau da kai ta yi gefe tare da goge kwallar sannan ta kalle shi ta ce.
"Amma idan har kana so na bai kamata ace ka nina kiyayyar ka akan d'an da na haifa ba, ai maso uwa ya so d'anta, idan har kana so na ya kamata ace ka so abunda nake so, wannan abun fa jarabawa ce daga Allah ba da so na ba ne na haifi yaron nan ta hanyar da ba ta dace ba tsautsayi ne ni ba fasika ba ce ban taba aikata haka ubansa ma ba fasiki ba ne mun fad'a tarkon mugu..."
Dakatar da ita ya yi ta hanyar cewa.
"Kin ga ba abunda za ki fad'a mani na yarda da ko na canza ra'ayina akan yaron nan, abu d'aya nake rikewa yake mani yawo a zuciyarta shine. Wani namiji ba ni ba ya kusance ki Kuma har ya maki ciki kin haifa masa yaro shine kawai abunda na sani, Kuma shine take matukar kona mani zuciya."
"Yanzu kana nufin ba ka yarda da abunda na fad'a maka a baya ba kenan, kuma kai da bakinka ka fad'a mani cewa Hafsat ta fad'a maka cewa ita ce ta saka a zuba masa magani a cikin tea ya sa bayan ta saka an mani alluran da..."
"Kin ga Amatullah ban ce ki maimaiata abunda Hafsat ta fad'a mani ba,dan ita ma Kanta maganar ta ba abun yarda na ne dan alama ya nuna shaye-shaye ya fara taba mata kwakwalwa dan gaskiyar yar shaye-shaye kadan ce."
"Me kakar nufi kana nufin ni ce na bada kai na ga Ajmal har da son rai na?"
Make kafada ya yi alamar oho, take hawaye suka dinga sintiri akan kumatunta. Jin muryarsa ta yi yana cewa.
"Ki daina kukan da kike yi tsaninin son da nake maki ne ya kawo haka nake kishin ki, kema kin San idan har ba son da nake maki ba wani namiji ne yana tare da budurwar da zai aura kwatsam ya ji labarin ta yi cikin shege an kore ta daga gidan iyayenta bayan sun gano tana da ciki Kuma tana shaye-shaye, duk da haka ban daina son ki ba duk ba bayan tsawon lokaci na ji labarin cewa kina can kin tare a gidan Wanda ya maki ciki har kun fita k'asar waje da shi kafin ya kawo ki gaba n iyayen ki, kina tunanin ko wanj namiji ne za ki aikata haka ya yarda ya aure ki?"
Ya k'arasa maganar idanunsa akanta.
Murmushin da ya fi kuka ciwo ta yi sannan ita ma ta kalle shi cikin idanu ta fara magana.
"Munnir da ka San wace ce Amatullah da ba ka fara wannan tunanin akai na ba, kasan halin da na shiga bayan Abba ya kore ni? Gidan Nafeesat na koma da zama Wanda hakan na ga yana neman mayar da ni ruwa, don damuwa da bakin ciki ya saka na cigaba da shaye-shaye don na rage damuwa, daga baya Kuma na ga zama a cikinsu zai ruguza mani rayuwata na tashi na nufi tashar mota kudin da kake bani na yi amfani da shi na hau mota na nufi garin Kaduna ba tare da na San kowa ba, a kango nake kwana washegari na fito na nemi abincin Siya, fuskantar barazana ne ya saka na bar kangon na koma ina yawo da kwana a titi inda na San ko ihu na yi jami'an tsaro na kusa za su kawo mani d'auki. Na koma bana da abunda zan ci ga ciki ga yunwa inda almajirai ke zuwa Suna layi ana basu abinci nima nake shiga cikinsu na bi layi, ranarda da ban samu ba nayi kuka don bana iya jure yunwa sai da na kai na kawo sai na yi bara nake samun abincin da zan ci, a haka wata tana ina yawo na hangi wata makarantar gwamnati ta primary, nan nake zuwa daddare na kwana bayan na ruki Mai gadin, ya amince na dinga shiga cikin class ina kwana da safe na fita sai wani dare. A haka har na gane wani gida da ake rabon kudi da kayan abinci, nima nake zuwa gidan ina bin layi duk da yawan mutane amma haka nake jure bin layi don na samu kyautar dubu biyar biyar da ake rabawa ko ban samu buhun shinkafa ba ban damu ba ina yawan yiwa Mai gidan addu'a akan alkahairinsa ashe ma shine uban d'an dake cikina ban sani ba, sai wata rana da ya Kade ni da mota ya kaini asibiti, kasancewar shi sannannen mutumi ne Kuma shine d'an takarar Gwamnan jihar, Wanda ana ganin ya dauko ni aka dinga d'aukar mi photo ana yadawa a social media Wanda sandin haka aka dinga bincike saboda korafin da ake yi akai Wanda hakan ya taba kimarsa a idanun mutane..."
Sheshshekar kukanta ne ya k'aru, kafin ta cigaba da bashi labarin komai har daukarta da Ammi ta yi da binciken da Ajmal ya sa aka yi har gaskiya ta fito ba abunda ta boye masa har da dakatar da shi da aka yi akan takarar Gwamnan da yake yi har zuwa k'asar Qatar da suka je don Kakarsa ta nemi ganisu da dawowarta komai ta Sanar da shi.
Mikewa tsaye ta yi da idanunta da suka yi jajir ta nufi hanyar shiga gidan ba tare da ta juyo ba ta ce.
"Ka na da damar yanke hukuncin da ka ga ya dace, ka daina mani wani mummunar fassara kana kallona da siffar da ba ta wa ba, idan kana ganin alfarma za ka mani ka aure ni to don Allah ka janye maganar aure na da kai, ka duba cancan ta."
Daga nan ta saka kai ta nufi cikin gidan zuciyarta na mata zafi.
Har dare ta kasa rintsawa ta rasa da wa za ta yi shawara, don haka da safe ta samu Abba kafin ya fita kasuwa ta ce tana son zuwa gidan Aminiyarta Fadeela, sanin cewa kowa ya san ta ya San Fadeela da irin zirga-zirgar da ta dinga yi a gidan bayan tafiyar Amatullah ya sa Abba ya amince mata.
Bayan ta kammmala aiyukan gidan Umma ta yi wa Khalifa wanka ta shirya shi yana barci ta kwantar da shi, Amatullah ma ta shirya cikin Riga da siket na atamfa koriya yana da ratsin pink da orange color, sarka da dankunne ta saka sai hijabin orange color kalar kwalliyar atmafar, ta saka bakin takalmi da bakar jaka, kyakkyawar abun goyon Khalifa ya ciro shi sabo a cikin ledar shi ta goya Khalifa ta fito, bayan ta saka wayarta da kudi a cikin jakar.
Sallama ta yi wa Umma ta fito daga gidan bakinta d'auke da addu'a.
Tsayawa ta yi bakin k'ofar gidan tana Jin kunyar mutane da zasu gan ta da yaro bayan sun San ba aure ta yi ba, ta dade kusan mintuna goma kafin ta fito daga gidan.
Tun kafin ta k'arasa bakin titin ta samu Mai napep, tare shi ta yi tare da sanar da ita unguwar da zai kai ta, shiga ta yi ta zauna ya ja suka kama hanyar unguwar.
Tunani take yi yadda suka rabu da Munnir ga Ajmal ya tafi kamar yana fushi da ita tunda ta ga bai kira ta a waya ba, wata zuciyarta Kuma ta ce maybe jikinsa ne don dama ya tafi jikinsa da zafi, kawai sai ta ji ba dad'i don a tunaninta tashin lafiyarsa ne ta yi tsanaini yasa bai kira wayarta ba.
Sai da suka shiga unguwar yake tambayar ta daidai ina za ta sauka sannan hankikinta ya dawo ta ce.
"Nan ya isa."
Don sun kawo k'ofar gidan su Fadeela. Kudinsa ta bashi ya tafi ta nufi cikin gidan.
Da sallama a bakinta ta shiga gidan, Maman Fadeela dake fitowa daga kitchen ta amsa tare da zubawa Amatullah idanu. Cike da mamaki Maman Fadeela ta ce.
"Wa nake gani kamar Amatullah."
Fadeela dake zaune a d'akinta tana waya da Wanda za ta aura Jin an ambaci Amatullah ya sa ta ajiye wayar tare da nufo waje, daidai lokacin da Amatullah ke sanarwa Mama murmushi ta ce.
"Eh ni ce Mama."
Aguje Fadeela ta k'arasa tana rungume Amatullah a tare suka saki kuka, yadda ta kankame Amatullah ne ya sa Khalifa d'auke goye a bayanta sakin kuka don ta matse shi, sai a lokacin Maman Fadeela ta k'araso ta saka hannu ta warware zanin ta ciro Khalifa.
Jan hannunta Fadeela ta yi suka shiga cikin d'akin, nan ma kuka suka dinga yi ba Mai rarrashin wani. Mama ce ta ji kukan ya yi yawa ya shigo ciki tana basu baki har suka yi shiru ta fita.
"Amatullah ina kika shiga, me ya saka da Abba ya kore ki ba ki zo gidanmu ba kika shiga duniya, kinsan halin da na shiga lokacin da na dinga zuwa ba na samunki, sai da Ummanki ta ga zirga-zirgar ta yi yawa ta sanar da ni komai, dama na tunda na ga kina mu'amala da wannan yarinyar Hafsat hanklina bai kwanta da ita ba, amma kin ki ki gane sai da ta kai ki ta baro."
Murmushi Amatullah ta yi tare da cewa.
"Kaddarata ce."
Daga nan Amatullah ta bata labarin komai danya faru tun daga farko har karshe, tana kuka ita ma Fadeela kuka take yi.
Daga nan Amatullah ta sanar da ita halin da take ciki tsakanin Ajmal da Munnir. Ajyar zuciya ta sauke tare da cewa.
"A gaskiya ki share zancen Munnir ki faka shi a gefe, don ba za ki ji dad'in zama da shi ba, Musamman yadda kika ce ba za ki iya rabuwa da yaronki ba, ka da ki je yana wulakanta maki yaro kina ji kina gani, don yadda na lura a labsrinki ya tsani Ajmal Wanda tsanarsa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 35 Chapter of 51