shi ne kake ta rawar kafa akanta ko? To wallahi ba za ka kawo mani mugun iri a cikin zuri'a ba."
Kallonta ya yi sannan ya ce.
"Kada rudewar tsufa ya rude ki tsohuwa nifa ba bin ra'ayinki zan yi ba abunda ya dace kawai zan yi, ki zuba idanu ki gani, na barki lafiya."
Ciro kudi yayi daga cikin jakkarsa rafan duba d'aya guda uku, wato dubu d'ari uku kenan ya ajiye mata a Saman center table.
Daga nan ya fita ya barta da baki sake tana kallonsa da mamaki.
Tana fita harabar gidan daidai lokacin da Sudais ke shigowa cikin gidan, Hakan ya saka ya nufi inda motar yake daidai lokacin da Sudais ya fito ya Karbi trolley bag d'insa ya saka a bayan motar, shima Ajmal ya shiga gefensa Sudais ya ja motar suka bar gidan, suka kama hanyar airport.
Da misalin k'arfe goma Sha d'aya na rana iyayen Munnir suka k'araso gidan su Amatullah. Cikin girmamawa Abba da abokinsa Mallam Musa suka tarbe su.
Nan suka gaisa cikin mutuntawa inda aka sauke su a zauren gidan bayan an ajiye masu abinsha.
Abba bai boye masu komai ba ya sanar da su zancen cewa Amatullah tana shayarawa yanzu, kuma sai ta yaye yaron kafin ayi auren, don bai kamata ta je tana shayar da wani yaron ba, nan suka amince da zancensa. Nan ya suka tsaida magana akan watanni goma masu zuwa idan da rai da lafiya za'a yi auren, zuwa lokacin ta yaye Khalifa Wanda a lokacin zai kasance yana da shekara d'aya da watanni biyu.
A ranar aka kawo kayan baiko tun daga kan su goro da sweet's, cingum da Kuma cartoon's din drinks. Haka aka dinga shigowa da su da yawa a cikin gidan da Kuma kudi naira dubu d'ari biyu.
Abba ya yi farin ciki da wanan al'amarin sosai, ita dai Umma ba za ka fahimci yanayin da take ciki ba na farin ciki ne ko akasin haka. Amatullah kuwa gaba d'aya ranta a jagule yake, ita dai ba wai tana k'in Munnir ba ne kuka ba wai tana son sa ba ne, haka dai take Jin shi a ranta, ba ta Jin soyayyarsa a zuciyarta kuka ba ta Jin k'iyayyarsa, damuwarta d'aya da Munnir shine . Yadda yake nuna kiyayyar d'anta a zuciyarsa yana damunta, don ita har ga Allah ba ta Jin dad'in yadda yake nuna ko in an kula akan yaron ta tunda yana sonta ai Yakama ya so danta, don gaisawa na cewa maso uwa yaso d'anta.
Makota sun shigo anyi rabon kayan baiko da aka kawo na Amatullah mutane sai taya ta murna suke da sambarka.
B'angaren Ajmal kuwa kwanaki uku ya yi a k'asar china daga nan ya tafi America, don yana son ya ga d'ansa, tare da Amintaccen bodyguard din sa Ahmad suka tafi. Don ya yi kewar yaron nasa, duk da yana Jin haushin Nasreen yadda ba tare da saninsa ba Kuma bai mata komai ba ta bar k'asar ta dawo gaban iyayenta. Tsawon kwankin nan ko ya kira wayarta ba ta dagawa, hakan ya sa shima ya share ta don bai ga abunda ya mata ba da za ta tashi ta debi jiki ta bar k'asar ta dawo America ta tare gidan iyayenta.
Gidansa suka nufa daga airport d'in, abinci da Ahmad ya saka aka kawo masu. Shi dai Ajmal bai ci komai ba abinsha kawai ya Sha sannan ya nufi bedroom d'insa, wanka ya yi ya shirya cikin tsadadden suite blue ya yi masifar yin kyau, tsadadden agogonsa baki ya daura a hannunsa, ya saka takalmi cover shoe baki sai d'aukar Ido yake yi, gashin kansa Mai kyau da sheki irin na larabawa ya sake gyarawa har da tsaga, kwantaccen sajensa da suka yi wa fuskarsa kawanaya suka kwanta luf har shainin suke yi. Ya yi masifar kyau Sosai sai k'amshin turare yake yi, idan har ba Wanda ya San shi ba ba za ka ce ya hada jinsi da 'Yan Africa ba don gaba d'aya mahaifiyarsa ya dauko da ka gan da ka ga cikakken balarabe.
Yana fitowa ya tarar d Ahmad a falo, take masa baya ya yi suka bar d'akin zuwa harabar gidan.
Ahmad a tayar da mota inda Ajmal ya ke zaune a bayan motar suka bar gidan.
Kai tsaye gidan surukansa suka nufa.
A cikin mota Ahmad ya tsaya yayin da Ajmal shi d'aya ya shiga cikin gidan. Doorbell ya danna ba jimawa sai ga Mum din Nasreen ta bud'e k'ofar, ganin Ajmal ne ya sa ta tsuke fuska tare d juya ba. Shiga ya yi bakinsa d'auke da sallama, ciki-ciki ta amsa masa.
Zama ta yi akan kujera yayin da shi kuma ya durkusa yana gaishe da Mum cikin girmamawa, sama-sama ta amsa masa, ganin haka ya sa ya saki murmushi, don ya fahimci inda ta dosa, saboda tun tahowar da Nasreen ta yi bai biyi bayanta ba, ada idan ba ta nan tana gidan iyayenta bayan iya jimawa bai je America ya ganta ba, fadar da Ammi ta masa ne akan cewa wani irin zaman aure suke yi ace mata ta tare gidan iyayenta sai dai shi ya yi ta zarya yana zuwa wajenta kamar ba aurenta yake yi ba, wannan dalilin ne ya saka Ammi cewa idan har Nasreen ba zata dawo Nigeria ba sai dai Ajmal ya Kara wani aure, Wanda hakan ya saka hankalin Nasreen tashi ta dawo ba shiri, sai matsalar da ta samu da Amatullah ya saka ta tafi shi kuka bai waiwaye ta ba.
Ganin yadda Mum ke Shan junu ya saka shi cewa.
"Nazo ne ina son naga d'ana."
Da mamaki ta kalle shi wato ba yazi ba ne din ya basu hak'uri sai ganin d'ansa, ranta a b'ace ta fara magana.
"Ajmal yaushe ka zama haka ne Anya kuwa ba canza ka aka yi ba, tsawon lokaci yarinyar nan ta kwashe a nan amma ba ka zo ba sai yau, yau din ma wai danka ka zo gani ko? Saboda ba ka da kunya har ni za ka iya tambaya ina danka ko? Bayan ka gama wulakanta mani yarinya ka fifita karuwa akan ta har ta kusa illata mani yarinya kake cewa haka ko?"
"Mum ba Wanda na fifita sama da ita sai dai idan ba ta fad'a maku gaskiyar abunda ya faru ba."
"Nan ya kwashe komai tun daga zuwansu k'asar Qatar har zuwa Kano don sada Amatullah da iyayenta, har zuwa yadda ta dinga zagin Amatullah ta ci mata mutunci da zagin iyayen Amatullah da ta yi Wanda ya saka ranta baci har ta bata amsa, Wanda hakan ya saka ta nufi Amatullah gadan-gadan da niyyar dukanta Amatullah ta matsa gefe har Nasreen ta jiwa Kanata ciwo, Wanda ta tayar da hankali akan sai ya rabu da Amatullah shi Kuma ya ce ba zai rabu da ita ba dalilin haka ta bar k'asar ba tare da izunsa ba ta dawo nan.
Sannan ya d'ora da cewa.
"Mum tsakani da Allah me na yi mata a nan ki wani ya mata da zai sa ta..."
"Dakata Ajmal kai ma ka San 'yata tafi karfin ka hada ta wannan 'yar matsiyatan don haka muka hana ta komawa."
Kallonta be ya yi tare da cewa
"Mum ina Affan?"
Kallonsa take yi da mamaki don ba ta ga alamar zai basu hak'uri ya Kuna janye kudirinsa akan Amatullah ba. Sai da ya sake tambayar ta ne ta sanar da shi yau ne birthday din Nasreen suna can tare.
Sallama ya mata ya fita kasancewar ya san wajen duk shekara anan take yi bikin birthday party dinta.
Bayan ya fita ne ta sanarwa Ahmad inda zasu je.
A harabar wajen suka yi parking Ahmad ya fito ya budewa boss d'insa murfin motar ya fito, kai tsaye suka nufi cikin wajen Inda ya hago Nasreen sanye cikin k'ananan kaya farar t-shirt da bakin wando crazy har ana ganin garar fatar cinyarta, an rubuta sunanta a gaban rigar. Kanta ba huka ga Karin gashin attached din da ta saka ya dauko har gadon bayanta.
Ga k'awayanta da zagaye da ita, ga samari da 'yan mata kowa na cashewa, ransa ne ya baci sosai ganin shigar da ke jikinta sai murna take yi tana fara'a. Wai matarsa kenan da igiyoyin aurensa akanta take wannan iya shegen, wani Abu mai d'aci ne ya hadiye.
Yana tsaye yana kallonta ransa a b'ace ya ji an rungume sa ta baya, Jin iya kafar aka rike ya sa ya juya yana kallon kasan ta baya, Affan ya gani yana sakar masa dariya yana Kiran Dady.
D'aukar yaron ya yi yana sumbatarsa a goshi, shima sai ya sumbarci Dad d'insa yana dariya.
"Dad Mum tana birthday nima ta ce next month zan cika five years za ka zo birthday dina ko?"
Murmushi ya saki yana d'aga masa kai alamar eh, kallon Ahmad ya yi tare da masa alamar su tafi, nan suka bar wajen ba tare da Nasreen ta lura da Hakan ba.
Sai da zata yankan cake ne ta nemi Affan ta rasa, nan hankalinta ya fara tashi, nemansa suka fara yi cikin tashin hankali, Abu kamar wasa ba alamar Affan ma a kusa da wajen, tambayar security suka yi ya sanar da su mutanen da ya ga sun fita da yaro.
Nan ta fara masifa tana masa fad'a, ya nuna mata cewar yaron da kansa ya biyi mutumin da alama sun San juna, ba ta tsaya saurarnsa ba t fara ihun Kiran sunan Affan kamar wata zararriya, wata k'awarta ce ta kira Mum din Nasreen ta sanar da ita halin da ake ciki. Da hankalin Mum din ya tashi amma da ta tuna Ajmal ya zo ganin d'ansa Kuma ta sanar da shi inda suke yasa ta sanarwa Nasreen don hankalinta ya kwanta.
Amma ina hankalinta bai kwanta ba duk da haka sai dai ta daina fargabar da take yi. Cake din da bata tsaya yankawa ba ko ta kansa ba ta bi ba ta nufi barin wajen hankalinta a dan tashe.
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
🤦♀️ *'YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
8️⃣8️⃣
Amma ina hankalinta bai kwanta ba sai dai ta daina fargabar da take. Cake din da bata tsaya yankawa ba ko ta kansa ba ta bi ba ta nufi barin wajen hankalinta a dan tashe.
Mai taxi ta tsayar ta shiga ciki tana Sanar masa inda zai kai ta.
Bangaren Ajmal kuwa tunda ya d'auki Affan suka bar wajen gidansa suka nufa, bayan Ahmad ya yi parking ya fito ya bude masu bayan motar, d'aukar yaron ya yi suka shiga ciki gidan.
A falo kan kujera ya dire Affan inda ya shiga ciki sai ga shi da su chocolate ya kawo masa, karba ya yi tare da kwanciya akan doguwar kujera yana cewa
"Dady barci nake ji."
Ya yi maganar yana lumshe idanu, murmushi ya yi tare da gyara wa yaron kwanciya sannan ya shiga cikin bedroom d'in yana rage kayan jikinsa, bathroom ya nufa don shi baya gajiya da yin wanka.
Mai taxi ya kawo Nasreen har k'ofar gidan sannan ta sallame shi ta nufi cikin gidan. Wanda ke kula da gidan yana gaishe ta ba ta amsa ba sai tambayar sa ta yi cewa Ajmal na ciki, ya sanar da ita eh.
Tura k'ofar falon ta yi Sam ba ta lura da Affan ba, don yana kwance cikin doguwar kujera, hankalinta bai kai ta lura da shi ba. Bedroom d'in Ajmal ta nufa baya ciki, tana shirin juyowa ta fito sai ta ji karar bude k'ofar toilet d'in, juyawa ta yi idanunta suka sauka akan faffaden k'irjinsa hannunsa rike da karamin towel yana tsane ruwan dake kansa, Kallo d'aya ya mata ya d'auke kai kamar bai ganta ba, juya bayansa ya yi yana zama akan kujera ya juya mata baya yana busar da gashin kansa. Bayansa ta zubawa idanu tana kallon farar fatarsa Mai shek'i da haske har d'aukar idanu take yi,kallonsa kawai take yi ba ta ce komai ba shima bai yi mata magana ba ya dauko man shafawarsa zai fara shafawa, da sauri ta k'arasa gabansa tana cewa.
"Bari na taimaka maka."
Kokarin karbar man take yi da niyyar shafa masa, wani mugun kallon da ya jefa mata ne ya saka ba ta San lokacin da ta janye hannunta ba, don sai da gabanta ya Fadi, matsawa ta yi gefe tana kallonsa.
Har ya gama shiryawa cikin kananun kaya ya fesa turare tana nan zaune a bakin gadon. Ganin ko kallon inda take bai yi ba ne ya saka ta tashi ta tari gabansa, din niyyar fita ya bar mata d'akin yake da niyyar yi, tsayawa ya yi ba tare da ya ce mata komai ba.
"Yaushe ka shigo?"
Bai ce mata komai ba ganin haka ya saka ta zuba masa idanu ta na kallon kyakkyawar fuskarsa, son sa take sake ji a cikin zuciyarta, ga wani Abu da take ji yana fisgarta.
"Ka yi mani magana mana ko zan ji dad'i."
"Kinsan Allah Nasreen ki kama kanki kafin na baki mamaki."
Da saru ta kalle shi bakinta sake da mamakin me ta masa, ko don ta taho ba tare da saninsa ba ta tare a gidan iyayenta.
"Ta ina zan iya rabuwa da kai ina matarka."
"Ina matar take."
Ya yi maganar yana jufanta da wani Kallo.
"Ke baki ji kunyar cewa ke matar aure ba ce, Kalli kayan dake jikinki kalle ki daga sama sama har kasa."
Kallon wandon dake jikinta ta yi crazy jeans ne Wanda har ana ganin farar fatar cinyarta, kafarta sanye da wani shegen takalmi Mai tsini k'umbarta ko Kuma na ce farcen kafarta sunyi tsayi sosai ga wani Jan fenti da ta shafa har da farcen hannunta, ga gashin dokin da ta saka har gadon bayanta.
Tabbas da ta San zata gan shi a yau da bata yi wannan shigar ba, don ta San baya so Kuma duk ta yi bata fita ba a gida take zama duk da ya Sha fad'a mata ya tsani wannan Karin gashin idan ya Kalli k'umbarta farcenta sai ya ce baya da sallah don ba yadda za'ayi ruwan alwala ya taba wajen. Bata damu ba da maganar sa tunda dama sai abunda ta ga dama take yi.
"Kayi hak'uri Dad din Affan ban San zaka zo ba ne."
"Okay sai idan bana nan kike abunda kika ga dama ko, ko da yake San baki yi kama da kamilakkiyar matar aure ba, don yanzu ba Wanda zai d'auka ke musulma ce kuka bahaushiya sannan matar aure, ko dayake ba sanin darajar auren kika yi ba tunda ban isa dake ba sai abunda kika dama kike yi, a cikin kaso dari ko kaso ashirin baki kai ba na sauke hakokkokin aure da yake ka kanki..."
"Please ka yi hak'uri ka bar wannan magana."
Zama ya yi a bakin gadon har lokacin bai saki fuskarsa ba, wayarsa ya duba ganin ana kiransa, amsa wayar ya yi na tsawon mintuna biyar, wani abokin harkokinsa ne.
Bayan sun gama wayar ne ya mike tsaye tun kafin ya d'aga kafarsa ya ji an rungume shi ta baya.
"Am sorry ka yi hak'uri tuba nake yi."
Bai ce mata komai ba don ya Saba Jin haka daga gare ta, ko ta bashi hak'uri ba ta canzawa. Jin ya mata shiru ne ya sa ta sake k'ankame shi a jikinta, hannu ta saka ta zagayo da shi zuwa k'irjinsa, tana shafar sa a hankali, zagayowa ta yi ta gabansa kasancewar sa dogo ne ita ma duk da ta saka dogon takalmi har yanzu ba ta kai sa tsayi ba, daga kafarta ta yi yadda suka yi daidai bakinta da nasa ta hade, a hankali ta fara kissing d'insa, lips d'insa na sama da na kasa take kissing, idanunta a lumshe, shi dai yana jinta bai taya ta ba Kuma bai hana ta ba, tsawon mintuna goma ta d'auka tana kissing d'insa, ta so ya biye mata ta hanyar maida masa da martanin abinda yake mata, amma sai ta ga ita kadai ke kid'inta take rawarta kuka har lokacin tana romance d'insa, Jin ya share ta ne kuka ta San yadda ta dade bata tare da shi dole ya bukace ta Musamman da ta San ba wani hak'uri ne da shi ba, don sai tari sai dai ta dinga masa complain ya fiye jaraba, idan ba ta ga dama ba, idan Kuma ta ga dama ko bai bukace ta ba idan ta masa haka tana kissing d'insa da romance to take jikinsa zai soma rawa ta har sai ya samu biyan bukatar sa, amma yau sama da mintuna goma kenan tana masa abun fa zai daga masa hankali amma ko enjoying bai yi ba, bude idanunta da suke lumshe ta yi tana kallonsa sai taga shima ita yake Kallo, mamaki ya kama in ta, bata gaja fita da mamaki ba sai da ta ji wani azababben zafi ya ratsa kanta, Kara ta saki daidai lokacin da ya fisge gashin attached din ta ta jona akanta, rintse idanunta ta yi saboda zafi, sannan ta bud'e su daidai lokacin da yake cillar da gashin a cikin kwandon da yake zuba datti, sannan ya hankad'ata ta fad'a Saman gadon, bai bi ta kanta ba ya yi ficewarsa daga d'akin ya barta, kukan takaici ta saki akn wannan wulakancin da Ajmal ya mata.
Ya fita har lokacin Affan na kwance yana barci, fita ya yi daga da falon ya zagaya baya, wajen wasu kujeri, wayarsa ya lalubo lambar wayar Ammi ya danna mata kira.
Bugu biyu ta d'aga suka gaisa tsawon lokaci suka d'auka suna fira, take tambayarsa ya ga matarsa da dansa, can ya sanar da ita yanzu haka suna cikin gidan, fira suka yi sosai kafin ya mata sallama ya katse Kiran wayar.
Nasreen kuwa sai da ta ci kuka har ya ishe ta sannan cikin bakin ciki sa takaici ta bar d'akin, a falo ta tarar da Affan ya tashi zaune yana Kiran sunan Dady. Ganinta ya sa cewa
" Mummy ina Dady?"
Ba ta ce mata komai ba ta nufi inda yake.
"Mummy ne ya same ki ke kuka?"
Nan ma shiru sai gage hawaye kawai take yi,
"Mummy Daddyna fa?"
Tsawa ta daka masa tana cewa.
"Shut up idan ka sake tamabaya ta Dady sai na maka duka, stupid."
Kwalla ne ya cika masa idanu bai sake magana ba, Jan daukarsa ta yi suka fice daga gidan.
Bayan kwana biyu, Munnir ne ya sanarwa Amatullah ta shirya zai kai ta wajn Mom d'insa ta gaishe ta, don ta matsa ya kawo mata matar da zai aura, ba tare da tunanin komai ba Munnir ya sanarwa Amatullah ta shirya da misalin k'arfe biyar zai zo ya kai ta wajn Mom d'insa.
Haka kawai ta ju bata son zuwa don haka ta ce masa bata Jin dad'i nan da kwana uku sai ya zo ya d'auke ta idan ta sanarwa su Umma.
Duk da ba haka ya so ba amma ba yadda zai yi sai ya ce mata Allah ya kai mu.
Kamar yadda ta ce kuwa ta sanarwa Umman da Abba ta sanar da su, kuka suka amince ta je ta gaida su.
Haka kuwa aka yi bayan kwana uku sai da misalin k'arfe biyar na yamma, motar Munnir ta yi parking a gidan Mallam Abdullahi.
Cikin motar ya tsaya tare da lalubo lambar wayar Amatullah ya sanar da ita cewa ya k'araso, kasancewar sun ajiye lokaci ita ma ashirye take tana jiran karasowar tasa.
Shirye take cikin doguwar riga ta atamfa kalar yellow da orange color anyi nata ratsin lemon green, dinkin stones work aka zuba mata, kayan sun karbe ta sosai ba wani kwalliya ta yi ba powder ce ta shafa sai lips glow da ta shafa, sai turare ta da feshe jikinta da shi Mai sanyin kamshi. Hijabi ta saka Mai launin lemon green, sai takalmi da jakka bak'i.
Bayan Munnir ya sanar da ita zuwansa ne ta fito daga d'akin ta sai ta nufi d'akin Umma, ta sanar da ita zuwan Munnir, zasu tafi, nan Umma ta sanar da ita kada su dade tunda ga Khalifa na gida duk da yana Shan Madara ko Amatullah ba ta bashi Mama ba, baya damuwa, da Addu'a ta fita a bakinta, zaune ta hango shi cikin mota ta k'arasa tare da yin knocking din glass din motar, sauke glass din ya yi yana sakar mata murmushi, itama murmushi ta maida masa da martani tare da gaishe shi.
Zuba mata idanu ya yi ganin yau sai ya ga ta Kara masa kyau, bude mata murfin motar ya yi ta shiga tare da rufo murfin motar, k'amshin turarenta ya shaka tare da lumshe idanunsa, yana sauke ajiyar zuciya.
"Barka da yammaci kyakkyawar gimbiyata."
Ya yi maganar yana sakar mata murmushi. Murmushi kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba.
Ganin yana kallonta ne ya sa ta ce.
"Mu tafi yamma na yi Umma ta ce kada mu dad'e."
"To 'yar Umma."
Yayi maganar yana tayar da motar tare da sakin murmushi.
A k'ofar gidan su ya yi horn inda mai gadi ya fito daga d'akinsa ya ja wangale gate din gidan. Shiga cikin gidan ya yi ya yi parking a harabar gidan. Fitowa ya yi itama ma ta fito daga gefensa.
K'ofar da zata sada su da falon gidan suka nufa, bakinsu d'auke da sallama, ba kowa a d'akin sai sautin tv da sanyin Ac dake tashi a falon.
"Masoyiyata zauna bari na kira Mum ta zo ku gaisa ko?"
D'akin Mum ya nufa yana Kiran sunan ta.
Amatullah ta zauna a kasa Saman center carpet kanta a sunkuye kamar tana gaban Mom din.
Fitowa suka yi Munnir a gaba Mum ta na binsa a baya, fuskarta ba yabo ba fallasa, zama ta yi akan kujera dake facing Amatullah.
Cikin girmamawa Amatullah ta gaishe da Mum, ta amsa mata ba yabo ba fallasa.
Mai aikinta ta kira tare da bata umarnin ta kawo ma Amatullah abun Sha.
"'Yan mata ki tashi daga kasa ki zauna kan kujera."
Murmushi ta saki don har lokacin bata d'aga kai sun hada idanu da Mum ba, duk da Mum ta so ganin fuskarta amma ta ki yarda su hada idanu sai sunkuyar da kai take yi tamkar wata mara gaskiya.
Tabe baki Mum ta yi tare da kau da Kanta gefe,
"Bari na baki waje ko na ga ko ruwa kin kasa shansa."
Tana gama fadar haka ta mike ta nufi bedroom d'in ta. Juyowa ta yi tare da cewa.
"Yauwa Munnir zo ka karbo mani sako wajen Hajiya Kubra."
Tana fadar haka ta shige d'akinta, bin bayanta ya yi ya shiga d'akin tare da zuba mata idanu ya ce
"Mum yarinyar ta yi ko?"
Cikin danne bakin ciki da takaici ta ce
"Ba laifi tunda ta maka ai shikenan."
Cikin yanayin damuwa ya ce.
"Mum ko dai baki sauka ba ne."
Murmushi ta yi Wanda ita kadai ta San ma'anarsa ta ce
"Kada ka damu yanzu sauri nake yi ka je gidan Hajiya Kubra ja amso mani sako."
"Mum ga Amatullah nan fa kin San gidan Aunty Kubra akwai nisa magrib zata iya yi fa kafin na dawo, kuma Ummanta ta ce kada ta dade, ko kin manta tana da yaron goye ne Yakama ta koma gida da wurii."
Kada ka damu turarurruka ne da cosmetics ita zan bawa tsaraba a matsayin ta na surukata, kayi sauri ba damuwa yanzu zan je muyi fira da ita "
Ba yadda ya iya haka ya fito ya sanar wa Amatullah yana zuwa daga nan ya fice daga gidan.
Tana nan zaune har mintuna talatin Mum bata shigo ba, har lokacin tana zaune a saman center carpet, duk ta gaji da zaman. Kamar daga sama ta ji muryar Mum tana cewa.
"Duk d'an kirki Wanda ya San mutuncin kansa ba zai taba zabar mace kamar ki a matsayin matar aure ba."
Da sauri ta daga kai tana kallon Mum, sai a lokacin itama Mum ta ga fusakar Amatullah, sai da ta girgiza da ganin tsantsar kyau irin na Amatullah, ga shi tana da jini Mai gudu a jikinta, tabe baki ta yi tare da cewa.
"Nagartacciyar mace tamkar alewa ce da ke killace a cikin ledar ta, Wanda duk Wanda ya San abunda yake yi ne zai d'auke ta, amma ke kamar budaddiyar alawa ce wacce k'uda da k'wari suka gama yawo akanata suna lashewa, kings kuwa ai Wanda ya San abunda yake yi ba zai taba daukarta ba."
Kwalla ce ta cika ma Amatullah idanunta har suna zarya akan kumatunta.
"Ina fatan ba zakiyu jayayyaya da ni ba a lokacin da na ce maki ki fita daga harkar d'ana, don yar mutunci nake so ta zama surukata ba karuwa ba 'yar shaye-shaye duk wani namiji Mai nagarta ba zai taba aurenki ba, don
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 39 Chapter of 51