Share this page
yiwa abokin gaba na. Saboda haka ina son ki nisanci Ajmal, abinda ya faru tsakaninki da shi tsautsayi ne, zuwanki gidan nan ba ƙaramin kuskure ba ne, kusancinki da shi tamkar kina kasada da rayuwarki. So ki nisance shi ba shawara nake baki ba gargaɗi ne." Tana gama faɗar haka ta juya ta fita ta bar Amatullah cike da mamakinta. A wannan daren kuma a can garin Minna Hafsat ce a club, kamar yadda ta saba zuwa. Wasu na rawa suna cashewa yayin da wasu ke ta shaye-shaye Abunsu. Munnir ne ya fito daga cikin motarsa yana sanye da ƙananun kaya, ya sanya facing cap da baƙin gilashi sannan ya sa face masks a fuskarsa ya ɓadda kama ta yadda ba wanda zai gane shi. Zama ya yi a cikin club ɗin yana so ya ga Hafsat, dan yau ya zo ne dan ya samu ƙwaƙƙwaran dalilin da zai kafa hujja wajen rabuwa da ita. Dan so yake ya bawa mahaifiyarsa dalilinsa. Kamar yadda ranar ya kama ta tana shan giya haka yake so ya sake kama ta, sai ya ɗauke ta video ta wayarsa ta yadda ba ta da halin da z ta ƙaryata shi. Fitowa ta yi daga filin rawar tana sanye da riga da wando, wanda ya bayyana surar jikinta. Watarta ce ke ruri kasancewar akwai hayaniya da yawa ga sauti na tashi ya sa ta fita daga cikin wajen. Haraba ta fito ta gama amsa wayarta, bayan ta amsa kiran wayar ne har ta juya za ta koma ciki sai ta hangi kamar motar Munnir. Ƙarasawa ta ta yi wajen tare da kallon motar da kyau, ta tabbatar motarsa ce sai ta shi ce sai ta yi murmishi tare da cewa "Kai ba ma'abicin zuwa irin wuraren nan ba ne, to me ya kawo ka? Ritsa Ni Ko?" Shiga motar ta yi da sauri ta bar wajen. Wanda Munnir yana hangen duk abinda take yi. Dafe goshinsa ya yi saboda sai yanzu ya san ta tafka kuksure da ya zo da motarsa. Amma da bai zo da motarsa ba da ba yadda za'ayi ta san yana wajen.cikin sanyin jiki ya koma ciki tare da tunanin sabuwar hanyar da zai fito da ita. Shiga motarsa ya yi tare da barin wajen. Ɓangaren Nasreen kuwa kwana ta yi tana kuka, dan tun da ta ga kowa ya gasgata cewa Abdallah ɗan Ajmal ne ta shiga tashin hankali. Da asuba bayan ya dawo daga masallaci ne ya nufi dakin Ammimsa kamar yadda ya saba. Ya same ta ta idar da azkar tana zaune a saman sallaya. Durƙusawa ya yi cikin girmamawa ya gaishe da ita, ta amsa masa tare da ta bayansa kwanan iyali. Ya amsa mata da Alhamdulillahi. Jin kamar akwai Magana a bakinsa ne ya sa ta tambaye shi cikin harshen larabci. "Na ga kamar akwai Magana a bakin ka ko?" Jinjina kai ya yi tare da y "Dama Dr Fu'ad ne ya kira ni wai yau da safen nan akai Amatullah asibiti, jiya akwai alluran da bai samu ya mata ba." "Okay wane lokaci?" Ƙarfe takwasa na safen nan zai mata alluran. "Okay ba damuwa sai Ahmad ya kai ta." "Nima dama ina so na bashi haƙuri akan abinda na masa a baya a bisa rashin sani. Sai mu tafi tare." "Okay ba damuwa sai ya kai ku tare." Wayarta ta ɗauka ta kira iya ta ba ta umarnin cewa ta shirya Amatullah da babynta za su tafi asibitin karfe takwas na safe. Daga nan ta kashe kiran wayar, ya yi mata sallama ya tafi. Part ɗin Dady ya nufa nan ma ta gaishe shi sannan ya nufi part ɗin su. Bedroom din Nasreen ya nufa inda ya dinga knocking amma ta ki budewa, haka ya haƙura ya nufi bedroom d'in Affan. Samunsa ya yi yana barci sai ya ja masa ƙofar ya fita,inda ya nufi bedroom d'in sa. Wanka ya yi ya shirya cikin farin gezner fara ɗinkin ya zauna masa a jiki. Inda ya saka baƙar hula da baƙin takalmi. agogon Diamond ya d'aura a hannunsa idanunsa sanye da baƙin glass sai ƙamshin turaren da yake yi. Suna zaune a dinning area suna breakfast suka ji ƙarshen turarensa. Nihal ce ta ke duba hanya tun kafin ya ƙaraso, Nasreen kuwa duk da ta san shi ne amma ba ta ɗaga kai ta kalle shi ba. Dan har lokacin haushinsa da take ji. Ƙarasowa ya yi tare da gaida Amminsa ta amsa tare da tambayarsa ya fito. Affan ne ya kalle shi tare da cewa. "Dady zan je." Murmushi ya yi tare da cewa. "Ka gaishe ni?" Ture baki ta yi tare da cewa "Gud morning." "Morning my lovely son." "Dady mu tafi tare." "Asibiti zan tafi kuma ba'a zuwa da yara. Dan allura suke yi." "Ka zauna ka yi breakfast mana." "Idan na je can zan yi breakfast." "Asibintin ne za ka yi breakfast?" "Eh Ammi tare da Fu'ad za mu yi breakfast." "Okay bari na kira iya ta sanarwa Amatullah ta fito ku tafi." Daga Nasreen har Nihal sai da gabansu ya faɗi lokaci ɗaya suka ɗaga kai suna kallonsa. "Asibiti ba direba da zai kai ta ne sai kai?" Nasreen ta yi maganar cike da takaici. "Ahmad zai kai ta zan bi su ne dan akwai Maganar da zamu yi Fu'ad. Kallomsa ta sake yi tare da cewa. "To akan me ye ba za ka tafi da Affan ba?" "Na saba tafiya da shi harkomina ne?" Bai jira cewar ta ba ya nufi hanyar fita bayan ya sallami Amminsa. Ammi ce ta kira iya ta ce Amatullah ta fito zasu wuce asibinti. Nasreen ce ta ce akan za ta ga likita mene ne sai Ajmal ya bi ta. Ammi ta nuna mata cewar tafiyarsu ce ta zo ɗaya, dan dama shi ma zai je ya ga abokinsa shi ne zai bi su shi da Ahmad da zasu tafi, amma yanzu su uku ne. A cikin motar Ajmal ya zauna bayan Ahmad ya buɗe masa bayan motar. Zamansa da kimanin mintuna biyar sai ga Amatullah. Ahmad ya buɗe mata bayan motar ta shiga, tana rungume da Abdallah. Ganin Ajmal a gefenta ya sa ta kau da kai tare da cewa. "Ina kwana?" Amsawa ya yi da. "Lafiya lau Alhamdulillahi." Shiru ta yi tare da sunkuyar da kai. Daga nan bai sake yin magana ba har suka iso bakin tangamemen wani gida, horn ya yi security dake tsaye a waje ne ɗaya daga cikinsu y ya buɗe masa gate suka shiga. Ko da suka shiga cikin gidan tasyawa ta yi tana kallon gidan , ita dai a iya saninta wannan bai yi kama da asibiti ba.Ahmad ya fito ya buɗewa Ajmal ƙofar motar ya fito. Sannan ya zagaya ya buɗewa Amatullah ta fito tana ƙarewa gidan kallo. Ahmad ya ja motar zai fita daga gidan ne ta kalli Ajmal da ke tsaye a gabanta ta ce. "Nan bai yi kama da asibiti ba, ina ka kawo ni?" "Guest house ɗina." Ya yi maganar yana kallonta tare da sakin murmushi. "Ni ba zan shiga ba." "Ashe ko za ki kwana anan." Ya yi maganar yana jan hannunta dan su shiga cikin gidan. *INA BARAR ADDU'AR KU ALLAH YA BAWA 'YATA LAFIYA YA YAYE MATA LALURAR DA KE DAMUNTA.* *Daga alƙalamIn*✍️ Zainab Abdullahi KNT (Maman Ihsan) 090653279975 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z 🤦‍♀️ *YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) *NA* Zainab Abdullahi KNT (Maman Ihsan) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. Ban yarda a karanta mani shi a youtube ko a maida shi audio ba tare da izinina ba. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHIM* Page5️⃣3️⃣ "Ni ba zan shiga ba." "Ashe ko za ki kwana a nan." Ya yi maganar yana jan hannunta dan su shiga cikin gidan. Ƙoƙarin zame hannunta ta yi daga cikin na sa amma bai ba ta damar hakan ba. Yana riƙe da hannunta ɗaya yayin da ɗaya hannun tana rungume da babynta a ƙafarta. Suka ƙarasa ƙofar falon wanda Ahmad ya buɗe masu. Sakin baki ta yi tana kallon haɗuwar da falon ya yi, dan an kashe kuɗi a wajen, kai gwanin ban sha'awa. Ganin yadda ta saki baki tana kallon ko ina ne ya sa ya koma ya rufe ƙofar da key, sannan ya zare key ɗin ya nufi upstairs. Idanunta ne suka sauka kan wani photon Ajmal babban frame ne na zane take kallo, dan photon ya zamu sosai ƙwararren mai zane ya zana shi. A zuciyarta ta ce 'Allah ya yi maka kyau, dan daga ganinsa ba ɗan ƙasar nan ba ne, daga shi har Amminsa." Idanunta ta cire daga Pic ɗin sannan ta juya inda yake tsaye ta ga ba kowa a wajen.waige-waige ta fara yi ta ga ba kowa. Mamaki ne ya kama ta, mai wannan mutumin yake nufi da ni ne, ya ɗauko ni da sunan zuwa asibiti sannan ya kawo ni nan gidan. Ba ta gama tunanin ba sai ga takunsa tana ji yana saukowa daga upstairs. Idanunsa akanta yayin da ita ma shi take kallo. Ɗauke Idanunta ta yi tare da sunkuyar da kanta ƙasa. Har ya ƙaraso ya zauna kan kujera mai zaman mutum uku sannan ya nuna mata gefensa tare da cewa "Ki zauna mana." Zama ta yi a ƙasa saman Centre carpet kamar yadda take yi idan Ammi ta kira ta. Dan ita gani take ba ta isa ta zauna san kujera su ma suna sama ba, duk da Ammi tana ganin girmanta ba zata iya zama inda take saune ba. Shi kuma Ajmal gani take ai ta fi ƙarfin ta bisa la'akari da yadda kowa ke girmama shi ko ma'aikatan gidan idan da take ganin sun fita da security ɗinsa da ke girmama shi ne ya sa ta ke ganin ya fi ƙarfinta. Tashi ya yi ya karɓi babyn daga hannunta hannunta tare da kwantar da shi a kujerar mai zaman mutum ɗaya. Komawa ya yi zauna bayan ya cire gilashin da ke idanunsa ya ajiye a saman Centre table dake gabansa. Hularsa manya cire sannan ya mai da dubansa zuwa gare ta tare da cewa. "Tashi ki dawo nan gefe na ki zauna." Girgiza kai ta yi tare da cewa. "A'a." "Ba na son musu ki taso mu tattauna abinda ya kawo mu na mai da ke gida, idan ba haka ba kuwa za ki kwana a nan." Jin kalamansa ne ya sa ta tashi da sauri tare da ƙoƙarin zama a kan kujerar da ke bayanta, wanda saman kujerar ne ya kwantar da Abdallah. Ganin za ta zauna akan yaron na ya sa ya janyo ta da karfi, wanda ya sa ta faɗa jikinsa. Gabanta ya faɗi tana ƙoƙarin tashi daga jikinsa amma ya riƙe ta sosai. Abinda ba ta taɓa ganin ya faru da ita ba kenan, amma yau ne karo na farko a rayuwarta da ta ji ta haka, ita ce a saman jikinsa haka kiciniyar ƙwace kanta ta shiga yi ta kasa. Dan haka gabanta ya tsananta faɗuwa. Tsoro ya kama ta sai ta saka masa kuka. Ganin haka ya zaunar da ita a gefensa tare da cewa. "Me na maki kike kuka?" Tura baki ta yi tare da cewa. "Ba kai ba ne ka riƙe ni ka haɗa jikinka da nawa." "Ai naga za ki danne babu ne ya sa na janyo ki ba da nufi nayi ba, ganin irin tsoron da ke cikin idanunki ya sa na rike ki dan na cigaba da ganin tsoron. To me ya saka ki kuka?" "Ban taɓa haɗa jiki da wani namiji ba, kawai shi ne tsorona, dan Ummata kullum maganar da take mani kenan na kama kai na, hakan ya sa ba wanda ya taɓa riƙe ko hannuna ne ballantana kai da ka riƙe ni..." Sautin murmushi da yake yi ne ya sa ta dakatar da maganar tare da kallonsa. "Kin san me zan faɗa maki? Ka da ki ma sake faɗar cewa ba namijin da ya taba taɓa jikinki, dan kallon mahaukaciya za'a maki." Mamaki ya sa ta lalle shi tare da cewa. "Wa zai mani kallon mahaukaciya?" "Mutane mana." "To saboda me?" "Saboda idan har namiji bai taɓa taɓa jikinki ba shi wannan babyn fa? A ruwa kika sha kika sha kika haife shi?" Kallon Abdallah ta yi tare da hararsa wanda hakan ya bawa Ajmal dariya. Yana kallonta yana cewa. "Baby bai da laifi ki daina har mani yaro idan ma har ne ni uban babyn za ki harara, dan ni nayi cikinsa shi da har yanzu bai san kansa ba, ki harare ni madadinsa ni na maki laifin." Tsayawa ta yi tana kallomsa da mamaki ko dai yana sane ya yi komai, ba cikin ficewar hayyaci ba ne kamar yadda kowa ke zargi. Ganin irin kallon da take masa ne ya sa shi cewa. " Ka da ki zarge ni dan nima ban san komai ba, abu ɗaya na sani shi ne ni ne uban ɗan ki. Yanzu ka san da haka? To da me ya saka kake zargina da ɓata maka suna?" "Na yarda ne bayan na ga videon da ya tabbatar mani da cewa ni ne nan na yi sanadiyar zuwansa duniya, baban hujjar da ya sa duk da haka ban zargi komai ba shi ne ni ne mutum na farko da ya fara kusantarki a matsayin cikakkiyar budurwar, ni na raba ki da budurcinki." "Amma shi ne kake cewa ba ka san komai ba ya aka yi ka san cewa kai ne na farko da ka fara kusanta ta?" "Jinin da na gani ne, da kuma yanayin da na ga kina yi da fuskar duk da ba kaya cikin hayyacinki, amma alamu sun nuna cewa ke kina jin tsananin azaba mai raɗaɗi." "Yanzu videon da ya ajiye ya naɗi komai shi ne ka kalla?" Jinjina mata kai ya yi alamar eh. Hannu biyu ta ɗora akai tare da cewa. "Na shiga uku, shikenan abuna yabfaru watannin baya shi ne ka gani? Allah ya san iyakar mutanen da suka gani." "Ka da ki damu ya ce ita da ta saka shi ɗaukar videon bai ba ta ba, ya ɓoye ne dan ba zai iya nawa kowa ba shi ma bai kalla ba." "Idan ƙarya yake yi da?" "A halin da yake ciki ba zai iya faɗa wata ƙarya ba." Ya yi maganar idanunsa akanta." "To kai yanzu ka ga komai kenan?" "Ƙwarai kuwa." "Yanzu ka kalli surar jikina a cikin hayyacinka?" "Na ga komai na jikinki gaba da baya, daga ƙarshe ma na shiga cikin jikin me ya rage? Na ga wani tabo kamar na duka a gefen haƙarƙarinki na dama, me ya same ki?" Kunya kamar ta nitse ƙasa kuka ta saka tare da cewa. "Me zai saka ka tsaya kana kallon tsaraicin wata?" "Kin ga ni sam bana kallon tsiraici kowa infact ma na tsani masu kallo, wannan ya zama dole ne dan na tabbatar da cewa na aikata ko ban aikata ba, wanda ta hakan ne kaɗai ne yarda cewa na aikata." Kuka take yi sosai na takaici. Kiran waya ya yi ya sanar da cewa yana da baƙuwa. Zuwa can sai ga wani mutum ya zo hannunsa dauke da faranti da kayan ciye-ciye da na sha. Gaida ita mutumin ya yi ta amsa masa, bayan ta goge hawayen da ke fuskarta. Ya dire masu a gabansu. Wayarsa ce tayi ruri ya duba D.P.O ne daga Minna. Da sauri ya ɗaga tare da cewa. "Kun kama yarinyar ne?" Kallon Ajmal Amatulla ta yi jin zancen da yake yi. Daga cikin wayar ta ji ana cewa. "Ba mu kama ta ba, amma dai yanzu zamu tafi da yaron zuwa hotel ɗin, duk da ya ce bai san sunanta ba, yana dai ganinta idan ya ganta zai gane ta. Amma ita ma Amatullah ɗin ka tambaye ta ko akwai wacce take zargi ko sun taɓa fada da wata? Hakan zai sa ta iya yiwuwa ita ce ta aikata mata haka." Shiru Ajmal ya yi tare da cewa. "Okay bari na tambaye ta." Daga nan ya katse kiran wayar tare mai da kallonsa ga Amatullah ya ce, "Ko akwai wacce kike zaton cewa ta aikata maki wannan abun?" Ba tare da ta lallee shi ba ta ce, "Zato zunubi ne ko da ya kasance gaskiya,ba ne zargin kowa." Kiran D.P.O ya yi bayan ya ɗaga ya masa bayanin abinda ta ce, sai ya nemi da ya bata wayar. Karɓa ta yi tare da cewa. "Assalamu alaikum" Daga can ɓangaren D.P.O dake zaune ofishin sa riƙe da waya a kunne ta amsa da. "Wa'alaiki salam warahmatullah." "Ina kwana yallaɓai." "Lafiya lau ya kike?" ", Alhamdulillahi." "A cikin ƙwayenki ko wadanda kike mu'amala da su ba wacce kika taɓa samun saɓani da ita?" "Babu." Ta bashi amsa a taƙaice. "To ba wacce kuke rashin...." Katse shi ta yi ta hanyar cewa "Yallaɓai ba abinda na sani Allah shi ne mafi sanin daidai, dan haka ko ma wace ce na barwa Allah, dan Allah mu bar wannan maganar tunda ba ku san wace ce ba." "Ba zan taba bari ba ko wace ce sai ba hukunta ta daidai da abinda ta aikata muna." Ajmal ne ya yi maganar yayin da yake karɓar wayar daga hannunta. Ya kara wayar akunnensa tare da cewa. "DPO ku yi fiye da ƙoƙarin ku dan Allah sai kun binciko ta." "Kada ka damu tunda yaron na hannunmu ita ma zamu kama ta." Daga nan suka yi sallama ya katse kiran wayar. Kallonta ya yi tare da cewa. "Me ya saka ba ki bada haɗin kai wajen amsa tambayoyin da yake maki ba, kika ce a bar maganar?" "Dole na ce a bar maganar dan ba na tabbacin ko wace ce, tunda ban sani ba, abinda ya faru ya riga da ya faru ƙaddara ta ce ta zo a haka. Ban isa na sauya zanen ƙaddarata ba, saboda rubutaccen al'amari ne daga Allah." Shiru ya yi tare da cewa. shikenan tunda haka kuka ce, amma dai bincike ba zan ce su dakatar ba, idan kuma suka gane ko su waye ke da hannu sai sun ɗaɗani kuɗarsu. Haka kawai suka sa mutuncina da ƙimata ya zube a idanun jama'a." Kallonta ya sake yi tare da cewa. "Ki ci abinci ga shi nan an kawo maki." "Na ƙoshi." "To ki sha abinsha." Yayi maganar yana tsiyaya mata abinsha a cup. Tsayawa ta yi tana kallon kwalbar, dan ba ta taɓa ganin irinsa ba. "Wannan kwalbar kamar kwalbar giya ce." Dariya yayi har sai da dimple ɗin sa ya lotsa, haushi ne ya kama ta dab ta tsani ayi mata dariya. Dan haka ta tsuke fuska kamar ba ta taɓa dariya ba. Ganin sauyawar fuskata ne ya sa dakatar da safiyar tare da cewa. "Ba giya ba ne ki sha." Girgiza kai ta yi tare da cewa. "Iya ta ce ka da na sha abu mai sanyi sai na kai watanni biyu." Sai a lokacin ya tuna da cewa ai jego take yi . "Na baki mara sanyi ki sha." Nan ma girgiza masa kai ta yi tare da cewa "A'a." "Abdallah ne ya yi kuka alamar ta farka daga barci. Da sauri ya ɗauke shi tare da rungume shi yana kallonsa. Sumbatar yaron yayi a goshinsa tare da cewa. "Allah ya raya ka ya sanya maka albarka." Kallon Amatullah ya yi tare da cewa "Ina son yaron nan, idan ya girma sai kamar ni zai koma saboda kamanninmu ɗaya. "Ni kuma ba na son ya girma." Da sauri ya lalle ta jin kalamata. "Tun yana cikin ciki nake addu'ar Allah ya sa baya da rai, dan ba na son na haife shi, dan ban san me zan ce masa ba dangane da asalinsa ba. Ba ta hanyar halak na same shi ba, me zan faɗa masa idan ya girma ya tambaye ni mahaifinsa yana ina?" Kallonta yake da mamaki jin kalamata, kuma bai ji dadin kalaman ba. "Ka da na sake jin kin yi masa addu'ar mutuwa. Idan ke baki ƙaunarsa Ni ina sonsa, na taɓa jin cewa wai uwa ta haifi ɗa ta ce bata son sa." "Idan ya tashi ya tambaye ni ina mahaifinsa fa?" "Idan kuma ya tashi a gaban uwarsa da ubansa da?" Rashin gane inda zancensa ya dosa ya sa ta cewa "Kamar ya?" Dawowa ya yi ya zauna gefenta tare da cewa. "Idan muka yi aure ya tashi a gabanmu fa?" Gabanta ne ya faɗi jin kalamansa, dan haka sai ta ce, "Aure kuma ?" "Ƙwarai kuwa zan aure ki, ɗanmu zai tashi a gabanmu, za mu tarbiyyartar da shi yadda ya dace. Idan kika yi la'akari da abinda ya faru a tsakaninmu ai ba har da ɗa ba kowane namiji ba ne zai iya zama da ke ya baki farin ciki ke da ɗanki ba." "Sai dai idan ba son tsakani da Allah yake mani ba, idan har yana so na fisabilillah zai zauna da ni har ya riƙe ni da yaron da na haifa." "Hakan zai faru ne idan ba na raye, amma matukar ina da rai da lafiya ba wanda zai riƙe mani ɗana." Taɓe baki ta yi tare da cewa. "Ai shikenan dama ban damu da ɗan ba. Kuma ba zan iya auren ubansa ba, hasalima ina da wanda iyayena suka zaɓa mani kafin ƙaddara ta faɗo mani, sai dai ban sani ba ko zai canza ra'ayinsa akaina bayan ya san na yi cikin shege na haihu." Cije laɓɓansa na ƙasa ya yi tare da rintse idanu. Kukan Abdallah ne ya tsananta inda ya lalle ta tare da cewa "Ki bashi nono ya sha." "Bazan iya ba." "Saboda me ba za ki iya ba?" "Ban yi niyyar shayar da shi ba ne, tun da aka haife shi ban taɓa bashi nono ba, madara yake sha." "To saboda me ba za za ki shayar da shi ba, shima ai ɗa ne kamar kowane jariri." "Eh na san cewa ɗa ne amma ba ɗan halak ba." Fuskarsa ba walwala ya zauna Abdallah da ke hannunsa idanu cike da tausayin yaron, dan da dukkan alamu uwarsa ba ta ƙaunarsa dan ya ga alamar tana jin haushin yaron. "Kin ga yaron nan bai san komai ba kuma bai maki laifin komai ba hasalima yanzu ban san kansa ba haifarsa aka yi ba shi ne ya yi kansa ba me ya laifinsa?" "Tura baki ta yi tare da cewa. "Shi ne sanadin da Abbana ya Kore ni ya raba Ni da gidan ina da Ummata." Kallonta ya yi tare da cewa "Shekarunki nawa?" "Goma sha bakwai." Ta faɗa tana kallonsa. Jinjina kai ya yi tare da cewa. "Ke ƙaramar yarinya ce akwai ƙuruciya a tare da ke, amma kin manta wahalar da kika sha a lokacin haihuwarsa ko?" "Ban manta ba duk da ba da kaina na haife shi ba tiyata likitoci suka yi suka ciro shi daga cikina." Murmushi ya yi tare da cewa "Baki sha wahala ba kenan tunda ba ki san zafin naƙudarsa ba ko?" Kukan Abdallah ne a tsananta inda ya ce, "To yanzu ina madarar?" "Ban ɗauko ba saboda da niyyar asibiti na fito." Shiru ya yi tare da cewa "Kinga daga nan zuwa gida akwai tafiya sosai kuma kukansa ya yi yawa, ko na aika a siyo madarar ne?" "A'a yanzu zan koma ka mai da ni." Ganin kukan yaron ya yi yawa ne kuma kafin a siyo madara zai dauki lokaci ya sa shi miƙa mata yaron tare da cewa. "Ɗan riƙe shi." Ba musu ta karɓe shi tare da cewa. "Mu tafi." "Dole sai ya yi shiru kukan ya yi yawa." Tana ƙoƙarin tashi ya janyoya jikinsa tare da cire mata hijabin jikinta. Mamaki ne ya kama ta take ta fara ƙoƙarin tashi daga jikinsa, sai dai ba hali dan riƙon da ya mata ba na wasa ba ne, zif ɗin rigarta ya zuge da hannu ɗaya, yayin da ɗaya hannun yana rike da ita, ya zagayo da ƙafarsa ɗaya ta bayanta ɗaya ƙafar a gabanta ya saka ta a tsakiya ya matse ƙafarsa yadda ba za ta iya tashi ba. Bayan ya zuge zip ɗin rigar ne ya sa hannu ɓalle rigar maman ta da ta saka, take manyan nononta suka bayyana, dan haka sai ya gyara Abdallah a jikinta tare da saka masa maman a bakinsa. Take kuwa ya yi shiru da kukan da yake ya fara tsotson Maman Wani irin zafi ne ta ji daga kan mamanta wanda sai da ta yi 'yar siririyar ƙara. Hawaye ne ke fita daga Idanunta ta fara magana . "Dan Allah ka bari wallahi akwai zafi cizo na fa yake yi." "Baya da haƙorin cizo ko kin manta jariri ne." A can gidan kuwa motar Dr Fu'ad ce ta yi parking, fitowa ya yi ya nufi cikin falon, da sallama a bakinsa ya shiga falon. Ammi ce da Nihal sai Nasreen da saukowar ta kenan daga upstairs. Gaba ɗaya suka amsawa Dr Fu'ad sallama. Inda ya durƙusa ya gaida Ammi cikin girmamawa. Nihal da Nasreen suka gaishe shi. "Ammi ya mai jikin?." Da mamaki ta kalle shi tare da cewa. "Waye kuma ba lafiya?" "Amatullah na zo dubawa." "Ban gane ba, tun safe abokinka ya ce, ka ce wai akai ta asibiti suka fita da niyyar zuwa asibitin na ɗauka tare kuka shigo." "Ikon Allah yanzu na bar asibiti kuma ba su je ba. Ko suna hanya ne bari na bi su ko za mu haɗu." "Wane hanya kamar mai barin gari, sun kai awa

Chapter 18 of 51