Share this page
abunda ke tashi daga cikin motar sai sanyin ac da k'amshin turarensa sanye yake cikin wani lallausan yadi ruwan k'asa wanda har farar singiletin da yake sanye da ita ana gani, Kansa ba hula kwantaccen gashin kansa wanda ya d'an kanannad'e irin na larabawa ke shek'i had'e da lallausan sajensa da suka yi wa fuskarsa k'awanya suka kwanta luf, sai bak'in takalmi da ke k'afarsa, tsadadden agogon hannunsa ya duba tare da kallon lokaci, a hankali ya ziro farin k'afarsa d'aya waje bayan kamar minti d'aya ne ya sake fito da d'aya kafar, sannan ya fito ya rufe marfin motar ya fito cikin takunsa na mazantaka, kallo d'aya za ka masa ka san cewa Allah ya masa k'ira da cikar zati irin na cikakken d'a namiji. K'amshin turarensa ne kawai suka ji ya sa suka waiga suna kallon k'ofar shigowa gidan, wanda hakan ya haifarwa Amatullah da faduwar gaba, Munnir da ke zaune a gefen Amatullah yana ba ta hakuri kan rashin dawowarsa ya d'auke ta ne k'amshin turaren Ajmal ya masa sallama, kallo d'aya Ajmal ya masu ya d'auke Kai gefen. Munnir kuwa kasa d'auke idanunsa ya yi daga kallonsa, don ko waye idan ya kalli Ajmal sai ya sake kallonsa shi namiji kenan ballantana mace, hakan ya saka shi jin wani kishi ya mamaye masa zuciya, musamman da ya ga Amatullah ta zuba masa idanun ko kyafta idanu ba ta yi. Hannu ta mikawa Munnir tare da masa sallama shi ma ya amsa masa dukkansu fuska ba walwala. Kukan da Khalifa ke yi ne ya ziyarci kunnen Ajmal, shiga cikin gidan ya yi bakinsa d'auke da sallama. Sai dai da alama Umma ba ta gidan don dakinta ma a rufe yake. Abba Kam dama yanzu baya nan. Da sauri Ajmal ya karasa bakin k'ofar Amatullah jin kukan Khalifa ya yi yawa yana shiga ya ga Khalifa a k'asa yana kuka da alama fad'owa ya yi daga Saman gadon, don ga bargon baby da aka rufe shi da shi ta bakin gadon alamar an ajiye shi kusa da bakin gadon kenan. Da sauri ya d'auke shi ya rungume shi Takaici ne ya cika zuciyar Ajmal wato Umma da ke kula da shi ba ta nan, ita kuma Amatullah ta yi banza da shi ai tana jin kukan nasa don shima tun da ya mikawa Munnir hannu suka sallama ya ji kukan yaron. Wato tana jin kukan yaron ta yi banza da shi saboda tana tare da saurayin ta ko, fitowa ya yi daga d'akin daidai lokacin da kukan yaron ya karu. Amatullah ce ta kalli Munnir tare da cewa. "Ina ga Khalifa ya farka ga kukansa can." Tabe baki Munnir da tun kafin Amatullah ta ji kukan ya fara ji amma bai ce komai ba, ta mike tsaye da niyyar zuwa ga yaronta sai ga Ajmal ya karaso zauren gidan da Khalifa da ke tsala ihu, hannu ta Kai zata karbi yaron mugun kallon da Ajmal ya jefa mata ne ya Saka hanjin cikinta kad'awa, ba ta san lokacin da ta janye hannunta ba tare da matsawa gefe, wucewa ya yi da yaron ya fice daga gidan, Kai tsaye ta hangi ya Saka yaron cikin motarsa ya zagaya mazaunin direba ya figi motar a guje daidai lokacin da ta karasa wajen k'ura ce kawai ta bud'e ta ko hangen motar ba ta yi. Maman Ihsan ce✍️ 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z 🤦‍♀️ *'YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) Na Zainab Abdullahi K.NT (Maman Ihsan) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page9️⃣1️⃣ Kai tsaye ta hangi ya Saka yaron cikin motarsa, ya zagaya mazaunin direba ya figi motar a guje daidai lokacin da ta k'arasa wajen, k'ura ce kawai ta bud'e ta ko hangen motar ba ta yi. Dafe goshinta ta yi tana tunanin me wannan mutumin yake nufi ne, to ina zai kai yaron, kenan fushi ya yi ko me? Sanin ba ta da wannan amsar ne ya sa ta koma cikin sanyin jiki, zuciyarta babu dadi, kallo d'aya ta yi wa Munnir ta ce. "Ka yi hakuri ka tafi ba na jin dadi zan shiga cikin gida." "Saboda ya yi fushi da ke shine kika shiga wannan halin ko, wai shin bayan ya kasance uban d'anki kina da wata alak'a da shi ne, akan me don ya yi fushi za ki shiga damuwa da har zai shafi fitar da muke yi? Ki barshi ai d'ansa ne duk yadda ya ga dama ya yi da shi, ni idan burge ni zai yi ka da ya sake waiwayar ki ya je can ya k'arata shi da shegen d'ansa." Rintse idanu Amatullah ta yi da karfi cikin jin zafin kalmarsa ta k'arshe, ta tsani a kira Khalifa da shege duk da cewar ba ta isa ta hana a kira shi da wannan sunan ba amma a gabanta idan wani ya kira ranta k'una yake yi sosai ba kad'an ba, kallonsa ta yi da idanunta da suka kad'a ta ce. "Munnir Kai da bakin ka kake Kiran Khalifa da shege?" "To k'arya na yi? Ki fad'a mani an d'aura maki aure da Ajmal ne kafin kika samu ciki? Gaskiya ne dole ne a fade ta ko da ba zai maki dadi ba, don na lura ba ki son gaskiya, zaman yaron nan a wajen ubansa shi nr daidai don ki tsira da zagi da maganganun mutane da zasu dinga yi a duk lokacin da suka kalle ki da wannan yaron Kuma..." Dakatar da shi ta yi ta hanyar daga masa hannu. "Ya Isa!" Da sauri ya kalle ta cike da mamaki. "Cikin bacin ran da bai taba ganin ta a ciki ba ta ce. "Ba shege ba duk sunan da ka ga dama ka kira Khalifa da shi hakan ba zai rage zunzurutun kaunar da nake masa ba, ina son shi fiye da kowa da komai ba ruwa na da maganar mutane da Kuma zargin masu zargi su je can su yi ta yi sune a wahala ba abunda ya dame ni, Ina son yarona haka zalika ubansa na kaunarsa kakaninsa da suka haifi ubansa suna matukar kaunarsa haka zalika iyaye na ba'a barsu a baya ba, don haka su kadai sun ishe Khalifa gata idan ya so duka duniyar nan su taru suna tsanarsa bai dame ni ba." Goge hawayen dake kwance a samun kuncinta ta yi kafin ta dora da cewa. Hakika d'an Adam ba shi ke tsarawa kansa yadda rayuwarsa za ta kasance ba sai yadda Allah ya tsara masa, da mutum ke tsarawa kansa yadda rayuwarsa za ta kasance hakika da ban tsara rayuwarta a haka ba, da Ina da dama to da na mayar da hannunsa agogo baya. Daga nan ta shige cikin gidan tana sakin kuka. Da idanu ya bita har ta shige cikin gidan, motarsa ya nufa ya shige ya bar k'ofar gidan. Amatullah fadawa ta yi kan gadonta tare da rera sabon kuka, gaba d'aya sun raba mata hankali ya za ta yi ne. Bangaren Hafsat kuwa rayuwar ta mata zafi, don tun ranar da ta ji Mamanta na sanar da ita Munnir zai kai matar da zai aura ta gaida Mum hankalinta ya tashi, ga shi yanzu Maman ba ta barinta fita tunda ta fahimci shaye-shaye da take yi ne ya ke Saka ta wasu abibuwan, ada da Munnir ya fad'a ba ta yarda cewa Hafsat na shaye-shaye ba cewa ta yi karya yake mata. Allah ya sani tana son Munnir kuka za ta iya aikata komai akan son da take masa, yanzu abu d'aya take so ta gane shi ne wace ce Munnir zai aura har aka saka masa rana da ita, ga shi Mamanta ba ta sanar da ita ba, ga wayarta ta bace run ranar da ta dawo gidan cikin maye ko da ta dawo hayyacin ta ba ta san Inda wayar take ba, ga shi an hana ta fita dole yau kam ta fita ga shi ta fara jin wani iri a jikinta sakamakon rashin shan kayan mayen da take yi. Dole ta saci hanya ta fice daga gidan ko za ta samu nutsuwa. Don haka ta na jin karar rufe k'ofar Mama ya sa ta leko, ganin kuwa da gaske ta shiga daki ne ta saka ta fito daga cikin dakinta, sanye take cikin cikin riga da siket na atamfa dinkin ya kama ta ko kanta ba dankwali, wani karamin gyale ta dauka ta yafa don ma kada ta dauki key din mota Mama ta gane ya saka ba ta dauka ba handbag dinga kawai ta dauka ta saka takali ta fice daga d'akin. Cikin sanda take tafiya a falon har ta fice. Karamin k'ofar gate din ta nufa Maigadi zai taso da sauri ta dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu tana tana watsa masa harara. Da Kanta ta bude a hankali ga fice daga gidan. Bangaren Ajmal kuwa bayan ya bar unguwar su Amatullah ya nufi Inda yake siye wa Khalifa Madara, nan ya siye masa madara da bulunboti ya bukaci karamin flask na zuba ruwan zafi sai ya ke tambayar matar Inda zai samu ruwan zafi, nan kuwa take ta kira d'aya daga cikin yaran shagon ta wata budurwa ce ta zo ta unarce ta da ta dauki electric kettle din da ta sa ruwa, nan ta nufi wani corridor sai ga ta da shi a hannu, karba matar ta yi bayan ta wanke flask din da ruwan zafi ta cika masa shi ya biya ta kudin da ta ce har da k'ari ya mata ta yi godiya ta kira wani yaron ta ce ya bishi da kayan a mota don ta ga yana rungume da Khalifa, sai dai zuwa lokacin ya yi shiru. Fita ya ya aka saka masa kayan a bayan mota shi kuma ya ajiye Khalifa gefen me zaman banza, sannan ya zagaya mazaunin direba ya tayar da motar suka bar harabar wajen. Bayan ya tafi ne budurwar da ta kawo ruwan zafi ta bishi da idanu, wayarta ta ciro daga cikin aljihun doguwar rigarta ta danna wa wata lambar kira. Yana ta ringing ba'a daga ba, ganin haka ya Saka ta tura text message tare da mayar da wayar a aljihu tana murmushi. Ajmal kuwa Kai tsaye hotel din da ya sauka ya nufa, vip ne ya kama Kai tsaye ya nufi room dinsa. Hafsat kuwa ba ta tsaya ko Ina ba sai bakin titi, mai napep ta tare ta sanar da ita Inda zai kai ta. Daga nan ta shiga cikin napep din ya kai ta Inda ta bukata. Kudi ta ciro a jaka ta biya shi ya tafi sannan ta nufi wani gate dake kusa da Inda ta sauka. Knocking ta yi maigadin ya leko ganin ita ce ya budd mata ta shiga. Tun a harabar gidan sautin Waka ke tashi, Kai tsaye ta nufi k'ofar falon. Maza guda biyu ne d'aya na zuk'ar hayakin shisha d'aya na shan giya. Sai mata guda uku kowace rike da kwalban maganin tari na yara, d'aya cikinsu tana shan maganin Kuma tana zuk'ar tabar sigari. Tana shigowa Nafeesat ta ajiye kwalbar da ke bakinta ta na kallon Hafsat tare da cewa. "Dama kina nan?" Ta yi maganar cikin muryar maye, Hafsat ta galla mata harara tana cewa. "Mutuwa na yi na dawo." Tana fadar haka ta nude wani karamin fridge da ke falon ta ciro wata karamar kwalbar maganai ta balle marfin sai da ta Sha rabi a wajen sannan ta dawo ta zauna gefen wanda ke shan shisha, don yana zaune ne a saman kijera mai zaman mutum biyu, sai da ya zuki hayakin kafin ya ce. "Babban yarinya kin yi wuyar gani ga wayarki ba ya shiga, kin saka na kawo maki kayak kin bace." "Bari kawai John matsala aka samu, amma yanzu komai zai yi daidai." Kallonta Nafeesat ta yi tare da cewa "Kamar da damuwa ko kawata?" "Babbar damuwa ma kuwa Munnir ne aka tsayar da ranar aurensa da wata." Zaro idanunta Nafisa ta yi cike da mamaki ta ce. "Ban gane da wata ba ke fa?" "Cikin takaici Hafsat ta kwankwade kwalbar maganin duka tare da daukar wata da ta gani kan center table da ke gabansu ta ce. "Bai Isa ba wallahi." Junjina Kai Nafeesat ta yi tare da cewa. "Ka da ace duk wahalar da kika sha saboda Munnir da ruguza rayuwar Amatullah da kika yi ya tashi a banza." "Wahala ta ba za ta tashi a banza ba har fa kama ni aka yi na Sha wahala a cell duk akan wannan shegiyar Amatullah kuka duk sabida siyayyar Munnir ai ban san Ina ta samu gata har wani zai iya bunciko ni ya sa a kama ni saboda ita." "To ai babban mutum kika tabo fa wanda har saboda abunda kika aikata ya shafi takarar siyasar sa na neman kujerar Gwanna aka dakatar da shi ai dole nemo ki." "To ai ni ban san da shi aka yi amfani ba amma na lura Amatullah na da babban matsayi a wajensa ita ce ta Saka baki har ya sa aka sake ni, amma fa gaskiya gayen kyakkyawa ne ajin farko." Ta k'arasa maganar tana lumshe idanu kafin ta kara da cewa "Sam baya kama da 'yan Africa kamar wani balarabe wai sunansa Ajmal ko waye ma oho." Shanye sauran kwalbar ta yi tare da nufar wani daki ta shiga ta zube kan katifar. Idanunta a lumshe tana ambatan sunan Munnir. Budurwar da ta kawo wa Ajmal ruwan zafi ne ke tsaye a corridor da ke shagon supermarket din jin ba'a kira ba ya sa cikin kagara ta ja tsaki tare da sake Kiran lambar bayan ta tura sako, abunda kunnenta ya jiyo mata ne ya sa ta zaro idanu tare da kallon sama. Yawan like da comment yawan typing ehe🥹 *Kuyi hakuri da wannan* Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z 🤦‍♀️ *'YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) Na Zainab Abdullahi K.NT (Maman Ihsan) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page9️⃣2️⃣ Abunda kunnenta ya jiyo mata ne ya sa ta zaro idanu tare da kallon sama, lumshe idanunta ta yi tare da Kiran sunan Amatullah jin tana kuka. "Amatullah subhanallah me ke faruwa kike kuka, ko dai akan Khalifa ne?" Amatullah da ke zaune saman gadon ne take amsa wayar Fauziyya da sai da ta mata missed calls uku sannan ta iya dagawa, jin ta ambaci sunan Khalifa ne ya sa ta saurin cewa. "Fadeela ya aka yi kika sani?" "Duk ba wannan ba ina Khalifa yake?" Cikin kuka ta ce. "Mahaifinsa ya raba ni da shi." Kuka take yi har da sheshshek'a, duk yadda Fadeela ta so ta mata bayani ta gagara jin haka ya sa Fadeela cewa na ga Khalifa tare da wani mutum Kuma Ina zaton shi ne mahaifinsa don kamannin dake kan fuskarsa ya b'aci." "Dan Allah ki sanar da ni Inda suke yanzu na zo na same su, walkahi ina son Khalifa kada Ajmal ya hukunta ni ta hanyar amfani da son da nake wa yaron. Suna Ina ne?" "Gaskiya yanzu ban San inda ya nufa da shi ba sai dai na tabbata Khalifa ne don madara yazo siya a supermarket da nake aiki ya bukaci ruwan zafi ya Saka shi a mota suka tafi." "Shikenan ya raba ni da shi Fadeela." "Bai raba ku ba Amatullah wata rana da kika zo gidanmu ba Amminsa ta kira ki a waya ba, ta sanar da bai da lafiya kuma ta fad'a maki hotel din da ya Sauka, ina ganin idan kika tafi hotel din za ki same shi." "Ta ya ya zan same shi a can Fadeela, tunda bansan lambar d'akin da ya kama ba. Ai ba lallai wancan d'akin da ya kama yanzu ma ace shi ya samu ba na dai san vip yake sauka." Jinjina Kai Fadeela ta yi tare da cewa "Kada ki damu na san zai dawo maki da shi har gida." Kuka kawai Amatullah ke ta kasa magana dan ita dai ta tsorata da yadda ta ga fuskar Ajmal a lokcin, katse Kiran wayar ta yi tare da hada kai da guiwa tana kuka. A haka Umma ta dawo ta same ta jin sautin kukanta da sheshshek'a ya sa ta shiga d'akin da sauri. Cikin tashin hankali ta nufe ta tare da dago ta "Ke lafiya kike kuwa meke faruwa?" "Umma ya raba ni da shi." "Wa ke nan,ina Khalifa yake?" "Umma Abbansa ne ya d'auke shi ya tafi da shi, Umma wallahi ba na son ya raba ni da yaro na." "Wai don ya d'auke shi ya tafi da shi hakan ya Saka kike kuka?" "Gyada mata Kai kawai ta yi." "Haba Amatullah ke baki raina abin kuka ne, to meye na kuka da har za ki rera kuka haka sai ka ce wacce ka ce Khalifa mutuwa ya yi." "Umma wallahi fushi ya yi ya d'auke shi ba wai haka kawai bane, har fa tara masa hannu na yi don ya bani Khalifa amma sai ya hana ni ya fita a fusace." Shiru Umma ta yi tana nazari kafin ta ce. "Akwai abunda ya faru kenan?" "Ba komai Umma wai don ya ji khalifa na kuka lokacin Munnir ya zo muna fira ni kwata-kwata ban ji kukan nasa ba sai daga baya, lokacin ne na tahi zan dauko shi sai na ga ya dauko shi ransa a bace, ya bani shi amma ya hana haka na bishi wajen motarsa haka ya figi motar har yana watsa mani k'ura." Jinjina Kai Umma ta yi idanunta akan Amatullah. "Kin san yana son d'ansa, yana tunanin da gangan kina ji yana kuka ne kike wulakanta masa yaro, hakan ya sa ya d'auke shi." "Umma ai ba na wulakanta shi." "Shi bai sani ba ai tunda baya tare da ke, amma na San nan da jimawa kad'an zai dawo maki da yaron." Haka dai ta kwantar mata da hankali har ta tsagaita kukan sai dai sheshshek'a. Bangaren Ajmal kuwa yana bude d'akin hotel din ya Maida k'ofar ya rufe tare da murza key, ledar hannunsa ya ajiye kan center table dake tsakiyar falon sannan ya kwantar da Khalifa kan doguwar kijera mai zaman mutum uku. Barci yake yi hankali kwance, sai da ya summbace shi a goshi sannan ya bar falon ya nufi bedroom, har ya murda handle din k'ofar zai shiga sai ya tuna cewa yaron zai iya fadowa, don haka ya koma ya d'auke shi da niyyar Kai shi bedroom kan gado. D'aukar shi ya yi suka nufi bedroom din, kwantar da shi ya yi a tsakiyar gadon sannan ya kunna AC sai ya rage karfin saboda Khalifa. Kayan jikinsa ya rage sannan ya nufi bathroom don yin wanka. Shap-shap ya yi wanka sannan ya dauro alwala kasancewar lokacin sallah ya yi na azahar sai ya Saka jallabiya mai ruwan kasa mai gajeren hannu, anan cikin d'akin ya yi sallah ko masallaci bai je ba saboda Khalifa da ke kwance. Umma ce ta shigo ta ce wa Amatullah ta tashi ta yi sallah, hakan ya sa ta tashi ta fito ta dauki buta ta debi ruwa ta nufi band'aki. Bayan ta fito ne ta d'aura alwala ta shiga cikin dakinta don gabatar da sallah. Tana idar da sallah ta ji wayarta ba ruri ba ta kula ba sai da ta yi addu'oi sannan ta shafa. Daidai lokacin da wani Kiran ya sake shigowa, ganin sunan Munnir ne ya sa ta yin tsuki don gaba d'aya haushinsa take ji, don ta lura baya son Khalifa, don ita Kam duk wanda yake son ta ai yakama ya so d'anta. Har ta katse babta daga ba sau uku yana kira ba ta dagawa. Bayan kamar mintuna uku sai ga text message ya shigo, kamar ba za ta duba ba sai Kuma ta dauka ta bude ta fara karantawa. 'Baby lafiya ina ta kira ba ki dagawa har kin saka hankali na tashi, Ina fatan ba fishi kike har yanzu da ni na. Am so sorry ba zan sake ba.' Tana gama karantawa ta ajiye wayar Daidai lokacin da Umma ta kawo mata abinci. Indomie ce ta dafa mata sai dafafden kwai guda biyu akai. Duk yadda Umma ta so ta ci abincin ba ta ci ba don haka sai ta barta ta ce bari ta hado mata complex Kasancewar tun kayan abincin da Ajmal ya lodo masu ba su kare ba don ba karamin kayan abincin ya jido ba ba abunda suka nema suka rasa da ya danganci abunci. Bayan ya idar da sallar ne yana addu'a Khalifa ya farka, yana kuka yana cilla k'afarsa sama, murmushi ya yi tare da mikawa daga saman sallayar ya nufi kan gadon, d'aukar Khalifan ya yi ya zaunar da shi, kasancewar yaron bai da k'yuya, bottle water ya dauko mara sanyi ya bawa yaron, take kuwa ya fara sha. Sai da ya cire baki ya barshi sannan ya d'auke shi suka nufi falon, a saman center carpet ya ajiye shi ya dauko flask na ruwan zafi ya hada masa madara a cikin bulunboti ya Kai masa baki ya saka masa, shiko tunda ya zuka sai d'aya ya ji zafi sosai ya kwala ihu, cikin tashin hankali ya d'auke shi ya rungume yana rarrashinsa, don ya fahimta ya masa zafi ne shi Kuma bai yi tunanin ya tantance zafin ba, don haka sai ya rasa yadda zai yi da yaron, suna cikin haka Kiran Ammi ya shigo cikin wayar, duk da yana ji amma ba halin ya d'auka saboda kukan Khalifa ya yi yawa. Dak'yar ya samu yaron ya yi shiru zuwa lokacin madarar dumi ne kawai ba zafi, sai ya fara bashi, take ya dinga sha sai ya kusa shanyewa sai ya fara zubo da shi alamar ya koshi. Tissue paper ya damu ya goge masa baki, ga jallabiyar da ya saka duk ya b'aci kasancewar bai iya ba yaro madara ba, ga jikin Khalifa ma duk ya b'aci da madara ga ba kayan da zai canza masa Kuma ba zai iya fita da shi a haka ba, don haka kawai sai ya yanke shawara aikar d'aya daga cikin ma'ikatan hotel din ya siyo masa kayan yaro. Wayarsa ya tuna da Kiran da Amminsa ke masa bai samu ya daga ba, don haka ya dsuki khalifa suka koma bedroom din, don ya kashe sauran wayoyinsa don baya son damuwa, waya d'aya ya bari a kunne wacce ya san makusantarsa ne kadai zasu iya kiransa da ita. Bayan ya zauna akan gadon ne ya ajiye Khalifa ya kira lamabar wayar Ammi . Bugu d'aya ta d'aga ta fara cewa "Lafiya kuwa Ina kira ba ka daga ba, na Shiga damuwa fa." "Ammina lokacin Khalifa na kuka ne shi ya sa Kuma na rasa yadda zan yi da shi " "Kamar ya?" "Na dauko shi ne daga wajen mahaifiyarsa zan kawo shi wajenki gobe nake so mu biyo jurgin safe mu taho." "Akan me ya saka ka aikata haka?" "Ammina mahaifiyarsa fa ba sonsa take yi ba, ba zan zuba Ido ana wulakanta mani yaro ba wallahi." Murmushi Ammi ta yi tare da cewa. "Me ya faru?" Nan ya sanar da ita komai da ya faru. Murmushi ta yi tare da cewa. "In banda wata uwa ce za ta haifi yaro ta ce ba ta sonsa, ko ta fad'a ai k'arya ne." "Ammi Kar ki manta tun tana hannunki ta nuna kiyayyar ta ga yaron nan, yadda kowa ce uwa ke shayar da yaro nono ita fa sam cewa ta yi ba za ta shayar da shi ba, ko kula shi fa ba ta yi Iya shugaban masu aikin gidan ke bashi Madara bayan ta yi fama da Amatullah kan ba bashi Mama ta ce Sam ba za ta shayar da shi ba, sai daga baya fa ta fara shayar da shi, ko yanzu ma ba wani shayar da shi take yi ba sau tari madara yake sha Ko ranar ina ji Ummanta na mata magana wai tun safe ba ta bashi nono ba sai madara." "To Banda abin ka ai madarar ma abinci ne tunda yana Sha ya koshi, yaran da suka rasa iyaye ba madarar suke sha ba?" "Haka ne Ammi amma duk da haka ba ta kaunarsa zan kawo maki shi ." "Kada ka kawo mani shi domin ba zan taba raba uwa da d'anta ba, ka Fi ta son yaron ne?" "Eh na fita mana." "Kar ka manta wahalar da yarinyar nan ta sha a rayuwarta dalilin cikin nan ka san komai sannan kake tunanin za ta iya juya masa baya, ba wanda zai so shi kamar ita da ta fi kowa sanin wahalar sa don haka ka mayar

Chapter 41 of 51