na uku wanda shine na ƙarshe.
Bayan motocin su yi parking a parking lot ne da sauri masu tsaron lafiyarta suka ƙaraso gefen da yake, yayin da ɗaya daga cikinsu ne ya yi saurin buɗe masa ƙofa ya fito.
Tsayawa ya yi tare da zubawa ƙofar fitowa daga gidan idanu. Ammimsa ce ta fito tare da wata budurwa a bayanta tana biye da ita.
Murmushi ne ɗauke a fuskar Amminsa tana farin cikin ganin ɗanta ɗaya tilo da Allah ya bata. Tsuke fuska ya yi tare da kauda kansa gefe, ta san dalilinsa dan haka ta rungume shi tare da masa sannu da zuwa.
Tura baki ya yi tare da cewa
"Fushi nake tunda baki ke airport kin tarbo ni ba."
Murmushi ta yi tare da cewa
"Nima ai baka kira ni la sanar da ni cewa yau za ka dawo ba. Ka dai ce a cikin week din nan, ba ka sanar dani za ka dawo da na shiryawa dawowar ta ka."
Surprise ɗinki na yi saboda kullun tambayar ki ita ce yaushe za ka dawo, shi ya sa na ce sai dai ku fanni daga sama ba zato ba tsammani."
Jan dogon hancinsa ta yi tare da cewa
"Kai ko?"
Duk maganar nan da suke a harshen larabci suke yin ta.
Budurwar da ke bayan Amminsa ce ta ƙaraso gabansa ita ma ta rungume sa tare da cewa
"You're welcome to..."
Saurin janye ta ya yi daga jikinsa tare da cewa
"Thank you so much"
Daga nan ya ja hannun Amminsa suka nufi ƙofar da za ta sada su da cikin gidan.
Har sun fara tafiya Ammi ta juyo ta kalli Nihal ta ce,
"Daughter mu je ko?"
Sai a lokacin Nihal ta ƙaraso ta tabi bayansa, dan ba ta ji daɗin abinda Ajmal ya mata ba, kawai dan ta rungume shi zai yi saurin janye ta daga jikinsa kamar ta soka masa ƙaya.
Suna shiga Babban falon gidan ne sai ga jama'arsa sun shigo da jakkuan kayan da ya dawo da su.
Nihal ce ta karbi kayan tare da nufar part ɗin Ajmal. A falonsa ta ajiye kayan wanda ya sha gyara komai sai ƙyalli yake gwanin sha'awa. Idaninta suka ɗauka akan babban hoton da ke manne a falon yana sanye da shiga suit baƙa da ta cikinta fara ya ɗaura necktie baƙi fuskarsa sanye da farin glass yayi matukar kyau yana murmushi wanda duk wanda ya kalle shi ya ga cikakken balarabe ba wanda zai ce shi ruwa biyu ne. Wato mahaifiyarsa balarabiya mahaifinsa bafullatani. Mahaifiyarsa ya dauko sak.
Gaba ɗaya Nihal ta shagala da kallon photonsa, a hankali ta ƙarasa jikin photon tana shafa fuskarsa tana murmushi. Idanunta ne suka sauka a d'ayan photon wanda su biyu ne a photon shi da matarsa Nasreen, sunyi ankon shadda ruwan ƙasa ta tana zaune a kujera shi kuma ya na tsaye ya sunkuyo da kusa da fuskarta ta saka hannayenta duka biyu da tallabo fuskarsa idaninta a lumshe dukkansu suna ta dariya.
Take sai Nihal ta ji ba daɗi sai ta saka hannunta ɗaya ta rufe fuskar Nasreen ya zamana fuskar Ajmal kaɗai take gani.
Ta shagala da kallon kyakkyawar fuskarsa har ya shigo falon bata sani ba, kallo ɗaya ya mata ya ɗauke fuskarsa, kai tsaye ya nufi bedroom ɗinsa, ƙarar rufe ƙofar da ya yi ne ya sa hankalinta dawowa jikinta.
Da alama shine ya shigo kenan sai ta bi bayansa, yana tsaye da waya a hannunsa yana dannawa. Tana shigowa sai ta rungume shi ta baya tare da zagayowar da hannayenta a ƙirjinsa.
Tsawa ya daka mata wanda ya sa bata san lokacin da ta sake shi ta ja da baya ba.
"Me kike yi haka?"
"To mene ne ai na ga kai Yayana ne to ai ba laifi na aikata ba."
"Idan ni yayanki ne to ni muharramin ki ne?"
"Ki tsaya iya matsayinki."
Tura baki ta yi tana kallonsa shima ita yake kallo.
"Tsayuwar me kike yi? Ki fita zan yi wanka ne nima zan fito."
Fuuu ta fita ranta a ɓace, a babban falon ta tarar da Hajiya Bilkisu tana waya da alama da alama da danginta take waya dan ta ji larabci take yi a wayar.
Zama ta yi gefen Hajiya Bilkisu tana ƙunƙuni, bayan Hajiya Bilkisu ta gama wayar ne ta kalli Nihal ta ce,
"Daughter lafiya?"
"Ammi ni ban san laifin da na yiwa Yaya Ajmal ba ya tsane ni."
Shiru Umma ta yi tare da cewa
"Me ya maki?"
"Kawai daga na yi hugging ɗinsa sai ya daka mani tsawa,me ya a ciki?"
Ta yi maganar cikin nuna damuwa da ai ba kuskure ta aikata ba.
Murmushi Ammi ta yi tare da cewa
"Ki san cewa ya duba rashin dacewar hakan ne, sai dai tsawar da ya daka maki ne da ya maki magana yadda za ki fahimta."
"Ammi me ye na rashin dacewar ai Yayana ne."
"Eh yayanki ne uwa ɗaya uba daya kuke da shi?"
Kai ta girgiza alamar a'a. Sannan ta ɗaura da cewa
"Cousin brother na ne."
"To kinga akwai aure a tsakaninku ke ba muharramrsa bace."
Kwantar da kanta ta yi saman cinyar Ammi tare da lumshe idanu.
Bayan kamar mintuna ashirin sai ga Ajamal ya fito sanye da farar shadda da ɓakar hula da baƙin takalmi. Hannunsa ya ɗaura agogon Diamond da zoben Diamond a yatsarsa ta tsakiya kyawunsa da kwarjininnsa haɗi da cikar halitta irin na mazantaka ne suka ga ya karu a idanunsu, sahensa dake kwance luf a fuskarsa sai sheƙi suke pink lips ɗinsa ya ciza gani irin kallon da Nihal ke binsa da shi, ya yi masifar kyau sosai ko namiji ya kalle shi sau ɗaya sai ya sake juyawa ya kalle shi ballantana mace mai hangen nesa zata yi fatan mallakar sa a matsayin mijin aure. Tunda ya fito suka ji ƙamshin turarensa suka zuba masa idanu.
Kai tsaye dinning area ya nufa wanda ganinsa ya sa ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan ƙarasowa dan ta yi service ɗin sa Nihal ta dakatar da ita ta hanyar cewa
"No ki barshi kawai za ki iya tafiya."
Yana zaune ta ƙarasa dinning area ta fara buɗe abinci tana cewa
"Na san yanzu za ka yi breakfast ko?"
Bai ce da ita komai ba idanunsa na kan wayarsa yana dane-danne.
Fried rice with fried chicken ta zuba masa za ta buɗe ɗayan wormer ta zuba masa farfesun ɗanyen kifi da ya ji kayan ƙamari ta zuba masa.
A hankali ya fara cin abincinsa yayin da Amminsa ta ƙaraso wajen.Nihal ta zuba masa lemun kwali da ruwa a galss cup.
Ammimsa ce ta kalle shi tare da cewa
"Son ina zuwa na ga kamar shirin fita ka yi."
"Eh Ammina Dady ne ya sanar da ni cewa na je mu haɗu da mai girma Gwamna yana jira na saboda gobe zai tafi Abuja, yana son mu haɗu kafin ya tafi."
Shiru ta yi tare da cewa
"Shikenan"
"Masana kiran da suke mani akan zancen takara ne dan ya ce yau za'ayi abinda ya dace kafin ya tafi."
"To"
"Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi."
"Ameen ya rabb"
Tashi yayi bayan ta yagi tissue paper yana goge baki da hannunsa.
Sallmarsu ya yi tare barin wajen suka masa addu'a Allah ya tsare.
Gaba ɗaya wunin ranar hala Amatullah ta dinga watangariri a cikin gari ba tare da ta san inda za ta dosa ba. Har karfe goma ta yi ƙafa ya fara ɗaukewa hankalinta ya tashi sosai ga ta da kaya jakkar kayanta tana yawo da su.
Wani kango ta yi karo da shi a gaban ta ta leƙa ta ga ba kowa a ciki, sai ta yi tunanin shiga ciki ta kwana.
Ba tare da tunanin komai ba ta shiga ciki ta shimfiɗa zanenta a ƙasa ta yi filo da jakkarta.
Take sai barci ya ɗauke ta mai nauyi, da misalin ƙarfe ɗayan dare ta ji ana taɓa ƙafarta a hankali ta buɗe idanunta, zaro idanu tayi cikin tsoro tare da buɗe baki zata fasa ihu.
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
Love you oll😍😘
🤦♀️ *ƳAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Dedicated to
*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION*
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubucirsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Page2️⃣0️⃣&2️⃣1️⃣
Take sai barci mai nauyi ya ɗauke ta, misalin ƙarfe ɗayan dare taji ana taɓa ƙafarta a hankali ta buɗe idanunta, zaro idanu ta yi cikin tsoro tare da buɗe baki za ta fasa ihu.
Ɗaya daga cikin mutane ukun da suka shigo kangon ne ya zare mata idanu tare da ɗora yatsarsa a saman bakin sa alamar ta yi shiru.
Ja da baya tayi tare da toshe bakinta tana kuka. Tsoro ne ya kama ta musamman da ta gansu da wuƙaƙe a hannunsu.
Ɗaya daga cikin su ne ya yi dariya tare da cewa
"Maraba gasashshiya inji giwa da ta ga baƙin jimina."
Ɗaya ya kalle ta tare da cewa tsarabar me kika kawo muna ne? Dan nan fadarmu ne a nan muke zuwa mu fake a duk lokacin..."
Tun kafin ya ƙarasa maganar da ya yi niyyar yi ne Amatullah ta fashe da kuka tare da cewa
"Dan Allah kau yi haƙuri Wallahi ban san nan wajenku bane, kawai na shigo ne dan na fake."
"Kinga kawo abinda kike da shi yanzu."
"Na shiga uku ni bana da komai ku rufa mani asiri kada ku tozarta ni."
Ta ƙarasa maganar cikin kuka.
"Rufin asirinki ɗaya shine ki bamu kuɗi da wayar da kike da su ƙara gaba, idan kika muna taurin kai to yanzu zamu ɓarke cikinki da wuƙa ki mutu a banza a sannan kuma mu kwashe Abinda kike da su mu tafi."
Jin haka ya sa ta miƙewa da sauri jikinta har rawa yake tana kuka ta kwaso dukkanin kuɗaɗen da take da su ta miƙa masu. Karɓa suka yi cikin mamaki yawan kuɗin dan sai daga gani kuɗin sun kai dubu arba'in ko fi ma.
Wanda ya karɓi kuɗin ne ya soke wuƙarsa a ƙugu tare da cewa.
"Dama kina da kuɗi shine kika fake a nan? To kawo wayar hannu da kike da ita."
"Wallahi bana da waya."
"To ware daga nan."
Da sauri ta ɗauki jakarta aguje ta bar wajen ko waige bata yi ba.
Sai da ta gaji da gudu ne sannan ta tsaya tana maida numfashi.
Kasancewar ta ƙaraso titi ne kuma ga jami'an tsaro nan ta gani suna ta sintiri a titin yayin da gefe kuma ga motarsu nan sun yi parking a gefe.
Ajiyar zuciya ta sauke ga ɗan da ke cikin cikinta sai motsi yake shafa cikin ta yi tare da fashewa da matsanancin kuka.
Zama ta yi a bakin titin dan tana da tabbacin zamanta a wajen ba wanda zai zo dan ya cutar da ita. Ga hasken sola ya gauraye titin kamar rana ne ba dare ba.
Ɗaya daga cikin jami'an tsaron ne ya ƙaraso wajenta hannunsa riƙe da bindiga.
"Ke!"
A firgice ta ɗago da kai ta kalle sh, amma sai dai wannan tsoron da take ji ya kau, saboda ta san cewa ta zo wajen da ke da tsaro.
"Me keke yi a nan."
Haka kawai sai ta tsinci kanta da cewa
"Dama ni ban san amma na mance inda zan sauka shine na tsaya a nan zuwa gobe da safe zan tuna sai na tafi."
"Daga wane gari kike?"
"Minna Niger state."
"Me ya sa da kika zo baki kira lambar wayarsu sun kwatanta maki ki su zo su ɗauke ki."
"Bana da waya "
"Kawo lambar wayar na kira maki su duk da cewar dare yayi."
"Ai bana da lambar wayarsu."
"Ke wace irin sakarai ce za ki zo babban gari kamar wannan alhalin baki da adireshinsu ko lambar wayarsu? Zuwanki bai da amfani ki tattara gobe da safe ki koma inda kika fito.
"To ba damuwa zan koma amma kuna nan zan iya zama ba matsala?"
"Eh zuwa asuba zamu bar nan."
"To yallaɓa nima da asubar zan bar nan."
Daga nan ya koma yake sanar da ogansu yadda suka yi da ita.
Daga nan ta kwantar da kanta a saman jakkar kayanta ta fara barcin wahala, ga sauro da suka addabe ta. A haka har asuba ta yi aka yi kiran sallar farko.
Ɓangaren Ajmal kuwa duk wani shiri da za'ayi an yi shi, inda ya fito takarar Gwamnan jiharsu nan a ƙarƙashin jam'iyar mai makulli Nasara party.
Aƙaddaamar da zaɓen ciki wanda su uku ne suka fito a ƙarƙashin jam'iyar ta su. Alhaji Shehu sabi'iu da kuma da suma Musa Muhammad sai Ajmal Ibrahim Tafida. Su uku nan sune suka fito takara Gwamna a ƙarƙashin jam'iyar ta su ta Nasara party.
Bayan gudanar da zaɓen ciki ne inda Ajmala ya lashe zaben. Dan haka tunda ya fi su yawan ƙuri'a dole suka janye suka bar masa kowa ya mara masa baya.
Nan sai aka shaida Ajmal Ibrahim Tafida shine wanda ya fito takarar Gwamna a ƙarƙashin jam'iyar. Sai su abokan karawarsa da suka fito daga wasu jam'iyun
Gaba ɗaya jikin Ajamal ya yi sanyi kasancewar dama ba son mulkin yake ba. Dan shi a tunaninsa tunda shi ba wai siyasa ya ke ba kuma su wadanda suka zaɓe shi ta hanyar dangwala masu ƙuri'a tunda ga abokan siyasrsu da sun yi shekaru suma tare, amma shi da yake baƙo ne shi suka zaɓa. Amma fa duk wannan ya faru ne saboda Ajmal ya samu goyon bayan Gwamnatin jihar ne.
Motocinsa biyar ne suke kan hanyar komawa gida, biyu a bayan ta sa motar biyu a gaban ta sa motar kowace mota ɗauke an rubuta sunan *AJMAL* da kuma number motar. Yana zaune a bayan motar ya kwantar da kansa a jikin sit ɗin motar, sanyin AC ne ke ratsa shi sai sautin karatun Alqur'ani da ke tashi a cikin motar.
Ji yake kamar wani nauyi ne ke shirin hawa kansa. Idanunsa a lumshe kamar mai barci amma ba barci yake ba a zahiri.
Daga can ƙofar gidansa kuwa jama'a na cike ana ta dandazo, duk da cewar ba baƙon abu bane dan ƙofar gidan ta tara jama'a ba, amma yau ba ranar zuwansu bane. Security har sun kore su sun gaji amma ba su tafi ba, maza da mata kowa ya halarta.
Sai murna suke dan sunji ance ya fito takarar Gwamnan jihar, sai farin ciki suke sosai dan bai fito takara ba ma ya zame masu garkuwa ina ga yanzu da ya fito takara. Shekaran jiya haka ya rabawa maza dubu goma-goma duk wanda ya ce ƙofar gidan, jiya kuma mata aka rabawa dubu biyar-biyar.
Kasa ƙarasowa motocin suka yi kasancewar ƙofar gidan ya cika da jama'a ba yadda za su iya ƙarasawa ballantana su shiga motocin su.
Buɗe idanunsa dake kunshe ya yi jin ana dukan gilashin motar. Ganin mutanen ne ya bashi mamaki sosai.
Sai ɗago masa hannu suke yi duk da baya jin me suke cewa kasancewar gilashin motar a rufe suke.
A hankali ya sauke gilashin motar sai a lokacin ya ji muryar jama'a na cewa
"Sai ka yi!. Sai ka yi.
!. Sai ka yi!"
Ɗaga masu hannu ya yi alamar gaisuwa da godiya.
Ganin yanayinsa ba walwala da farin ciki ne ya sa security suka sallame su akan cewa ba ya jin daɗi su tafi.
Su ma ganin yanayinsa ne ya sa suka yarda dan ba su ga yana murmushi ba kamar yadda ya saba.
Watsewa suka fara yi tare da masa addu'a, sai a lokacin motocin suka samu shiga cikin gidan.
Bayan motocinsa sun yi parking ne amintaccen security ɗinsa da ke gaban motar da yake ciki ya fito da sauri tare da buɗe masa bayan motar.
Take masa baya suka yi yayin da suka tsaya a ƙofar shiga falon shi kuma ya shiga ciki.
Ba kowa a babban falon dan haka ya nufi part ɗinsa, zama ya yi akan kujera tare da cire bukata ya ajiye a san table da ke gabansa. Wayoyinsa ma ya ajiye tare da jingina bayansa da jikin kujera yana tunanin abinda ke gabansa.
Ammimsa ce ta shigo tare da sallama, kasancewar idan ya dawo gidan idan bai ganta a babban falon ba sai ya nufi part ɗinta ta duba ta kafin ya nufi part ɗinsa.
Tunda ta ji horn motocinsa bata ga ya shigo ba ta san akwai abinda ke damunsa.
Shafa gashin kansa ta yi da sauri ya daga kai ya kalle ta tare da janyo hannunta. Zama ta yi gefensa ya ƙwayar da kansa a saman cinyarta.
"Ammina bana da karfi da jarumtar da zan iya ɗaukar nauyin al'ummar jihar nan ba, kada Allah ya tsare ni ranar..."
"Ka da ka damu rabin raina, ka da ka karaya kai jarumin gaske ne ba abinda ba za ka iya ba matuƙar ka sa hakan a ranka, kuma ina sha Allah zan kasance kullum a cikin yi maka addu'a nake ina sha Allah komai zai tafi daidai."
Shiru ya yi kafin ta kalle shi tare da kiran sunansa.
"AJMAL"
Yadda ta kira sunansa ya san cewa maganar mai mahimmanci ce, dan haka ya tashi zaune tare da Kallonta ya ce.
"Na'am Ammina."
"Ni wannan auren naka na shiririta ban gane kansa ba, tsawon shekaru huɗu kenan amma ta wace fuskar ba ka da banbanci da wanda bai da aure.
Nisawa tayi tare da cewa
"Kana rayuwar aure da matarka ne kawai amma baka san mene ne so mene ne so mene ne ƙauna ba, ba ka fahimci shauƙin da ma'aurata ke ji ba, har yanzu ka kasa samun kulawar da kowane magidanci ke samu daga wajen matarsa. Kai kana wata ƙasa daban matarka tana wata ƙasa can daban ba za ta iya zama tare da kai na wata ɗaya ba za ta bar ƙasar da kake ta tafi wata ƙasa can daban ta kwashe tsawon watanni uku a can, ko ta dawo wajensa ta daɗe wata ɗaya na yi maka maganar cewa haka ba mai yiwuwa bane dole ta zauna zaman aure a..."
Ammi ce ta yi shiru ya dakatar da maganar da take yi dan ta ga fuskar Ajmal ya sauya.
"Ba za ka taɓa ganin laifin matarka ba, kamar yadda ba ka so a faɗi laifinta. Ta ya ya ace kana da mata wai ba za ta zauna a kasar Qatar inda kake zaune ba tunda ta ce ba za ta iya zamar ƙasar nan ba? Ta tare a gidan iyayenta a can US a gaban iyayenta, da ke suma iyayen nata ba hankali ne da su ba shine suka barta da igiyar aure tana zaune a gabansu, sannan suka saka yaronta a makaranta sai idan yaro ya samu hutu ne za ta zo kasar da kake, da zaran hutun ya ƙare ta koma can? Ganin ba ka damu bane da kuma nuna son abinda kake so ya sa na yi shiru to ya ishe ni haka, idan zaman aure za ta yi to dole ta bar wajen iyayenta ra kasance tare da kai ko kuma ka ƙara aure."
A firgice ya kalle ta tare da cewa
"Ammina wallahi ba zan iya kara aure ba, amma zan sa ta dawo, idan ta dawo shikenan ba zancen karin aure ko?"
"Eh haka nake nufi."
Daga nan ta fice ranta a ɓace dan ta gaji da ganinsa haka kamar mara aure, lokaci ya yi za ta kawo karshen wannan lamari.
A cikin kwana biyu Amatullah ta rame ta fita hayyacinta, ga lailai yanzu ne ya fara saka ta gaba, jikinta sai a hankali ga rashin kuɗi bare ta je asibiti abincin da za ta ci ma wuya yake mata. Wajen kwana kuwa sai dai ta yi ta raɓewa a tashar mota cikin masu kwana dan asubancin yin tafiya.
Tana tsaka ta tafiya sai ta hangi kofar wani gida an fito da abinci ana rabawa almajirai abinci . Da sauri ta juya dan ƙarasawa wajen ko za ta samu a bata itama ta ci, dan ba ta da banbanci da su.
A hankali ta juya ta tsaya tana jiran ababen hawa su rage sai ta tsallaka titin.
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
09065327995
08168611693
Love you oll😍😘
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
🤦♀️ *ƳAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Dedicated to
*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION*
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubucirsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Page2️⃣2️⃣&2️⃣3️⃣
A hankali ta juya tare da tsayawa tana jiran ababen hawa su rage sai ta tsallaka.
Dara ga ababen hawa yanzu sun yi nisa da ita ne sai ta tsallaka.
Cikin hanzarin ta ƙarasa wajen ta shiga layin da almajirai ke bi ta tsaya a bayansu.
Sai dai bata san yadda za ta yi na kasancewarta ba ta da robar da za'a zuba mata abincin, kuma ga shi yanzu kowane almajiri sai dai ya miƙa roba a zuba masa.
Cikin rashin sa'a kuwa almjirin da ke gabanta akansa abincin ya ƙare, ana kwashe masa na ƙasar kular abincin ya ƙare.
Ganin haka ya sa ƙwalla ya cika idanun Amatullah, dan tana bala'in jin yinwa ga shi ba ta da ko sisi ballantana ta siya abinci.
Mai raba abincin ne ta kalle ta ganin tana kuka ka ga ta da ciki tausayinta ne ya kama ta. Dan haka ta kalli ta tare da cewa
"Ina zan zuba maki abincin."
Sai Amatullah ta tara mata hannayenta guda biyu, alamar a cikin hannayen za'a zuba mata.
"A hannu kuma zai ƙosar da ke ne?"
Sai ta janye hannunta ta tattaro ƙasan hijabinta alamar a ciki za'a zuba mata.
Matar ta kalle ta tare da cewa
" Bari na shiga na kawo maki ko? Zan sanar da masu gidan akwai mutum ɗaya da danni ma ƴar aiki ce a gidan.
Jinjina kai ta yi alamar to.
Bayan matar shiga da kamar mintuna biyar sai ga ta ta dawo hannunta riƙe da bakar Leda ta miƙa mata.
Hannunta na rawa wajen karɓa tana godiya, murmushi matar ta yi sannan ta shiga ciki gidan ta turo ƙaramar ƙofar gate ɗin.
Buɗe ledar Amatullah ta ta ga robar takeaway ne guda biyu da robar ruwa guda ɗaya.
A wajen jikinta na rawa ta buɗe ledar ta ciro robar takeaway d'aya ta buɗe ta saka cokali, hannu baka hannu ƙwarya ta ke cin jolllop din shinkafa ne da mama guda ɗaya.
Tana tsaka da ci sai ga wata baƙar mota mai baƙin gilashi ta danno kai, dai-dai saitin da take cin abinci motar ta tsaya, da alama ita me motar ke kallo.
Sunkuyar da kanta ƙasa ta ya dai-dai lokacin da me motar ya fara danna-horn, mai gadi na ya tashi da sauri yana fadin
"Barka da dawowa yallaɓai."
Ya buɗe masa gate sannan ya shiga da motarsa.
Bayan ta gama cin abincin ne sai ta ji kamar ba ta ci komai ba, wani sabon yunwa take ji. Dama ta lura tunda ta fahimci tana da ciki sai cin abincin da take yi ya karu, ga shi ba wuya ta ji yunwa yanzu.
Nan da nan ta buɗe takeaway ɗin da ya rage nan ma ta cinye shi tass ta sha ruwa.
Wani irin kasala take ji da barci wanda ji take ba zata iya jurewa idan ba ta yi barcin ba.
Tana tafiya tana hamma ne sai ta hangi wani primary school na gwamnati, makarantar akwai girmama sosai ka yau asabar ba makaranta, mai gadin makaranta ta gani zaune a benci yana barci.
Duk da cewar duk inda take yawo da jakkar kayanta ne take yawo a hankali ta suɗaɗa ta shiga cikin makarantar yadda mai gadin ba zai ganta ba.
Wani class ta shiga ba kowa sai kujera da tebur na zaman ɗalibai.
Can k'arshe ta shimfiɗa zaninta ta kwanta bayan ta ajiye jakarta karkashin kujerar da ta kwanta.
Nan da nan sai barci ya ɗauke ta a wajen.
Ɓangaren Ajmal kuwa tunda ya ji zancen Amminsa ya kasa samun nutsuwa. Wayarsa ya ɗauka iphone 15 pro max ya kira Nasreen video call.
*CALIFORNIA*
Kwance take akan makeken gadon da ke dakin barci yake hankalinta kwance.
Ƙarar wayarta ce ta sa ta farka, tsuki ta ja tare da katse wayar, sai sa aka kira har sau uku sannan ta ta shi zaune.
Ɗauka ta yi tare da jingina wayar da jikin gadon.
"Barka da tashi sarauniyar barci."
"Barkanka Sarkin takura."
"Au haka ne?"
"Eh mana barci fa nake yi ka katse ni."
"Bari na faɗa maki abinda ya sa na kira ki idan ya so sai ki cigaba da barcin."
"Ina jin ka."
"Ammina ta ce ta gaji da zaman da muke yi a haka, ko ki dawo inda nake ko ta aura Mani wata mat..."
"No ba zai yiwu ba kawai ace wai ka auri wata mace bayan ni, ka da Ammi ra mani haka bana so."
"Idan har baki so ya zama dole ki dawo ina nake, nima na gaji da wannan rayuwar na gwauranci."
"Ya kake magana kamar wanda bai da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 51