Share this page
taba aikata fasik'anci ba Kuma..." Tsawar da ya daka mata ne ya sa ta yi shiru da maganar sai kuka take kamar ranata zai fita. "Ki rufe mani baki idan Kuma ba haka ba zan fesa maki dafin da ba zai fita daga jikinki ba." Tashi ki fita ba na son sake ganin ki, tashi ta yi tana kuka cikin sanyin jiki ta nufe shi ta ce. "Abba ka saka masa albarka sunanka aka saka masa, kuka ina son ka barni na ga Ummata." "Ke yanzu tukuicim da za ki mani kenan? Kiyi ciki ki saka masa sunana?" Kau da kansa yayi tare da cewa. " ki bar gidan nan yanzun nan, idan ba so kike na maki mugun baki ki lalace ba." Da sauri har tana hade hanaya ta fita tana kuka, tana rungume da Abdallah. Tafiya take inda mutane ke tsayawa suna kallonta a layin, sai dai Abdallah na cikin hijabi ta rungume shi. Tana cikin tafiya ta ga Mai Keke nape ya wuce ta Kuma ta hangi Abba a ciki, sai da ta kai karshen layin ta samu k'asar wata bishiyar mangwaro ta zauna. Tunanin inda za ta dosa take yi, dan ba ta San ina zata je ba bata da kowa, ga shi ba ta San masaukin su Ammi ba ballantana ta je ta same su, duk da ta San zasu dawo gidan amma bata nan,gidan ba zasu San inda take ba. fito da Abdallah ta yi daga cikin hijabi ta rungume shi, idanunsa biyi ya Farka fuskarta yake Kallo. Sai ji ta yi an fisge Abdallah daga hannunta, da sauri da daga kai tana zare idanu dan ganin waye. *Ku dinga hak'uri da ni na rashin ganin update akan lokaci. Yanayi ne ya saka haka, addu'ar ku nake bukata.* Bi tashar TASKAR MAMAN IHSAN a WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z 🤦‍♀️ *YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) Page7️⃣4️⃣ Sai ji ta yi an fisge Abdallah daga hannunta, da sauri ta daga kai tana zare idanu dan ganin waye. Ajmal ta gani tsaye ya zuba mata idanu yana kallonta, sautin kukan da take yi ne ya k'aru ta hada kanta da guiwa ta cigaba da rera kuka. Kukan na ta har cikin ransa yake jin zafin kukan, cije jajayen lips d'insa ya yi tare da rintse idanunsa. Bude idanun ya yi akanta tare da cewa. "Meke faruwa?" Cikin muryar kuka ta ce. "Abbana ne ya kore ni ya ce kada na sake dawowa gidansa, baya bukata ta." "Umma fa ina take?" Ya sake tamabyarta yana jiran amsar da za ta bashi. "Nima ban San inda Umma ta tafi ba, har na baro gidan bata dawo ba." Shiru ya yi tare da nazari kafin ya ce. "Ba ki tambayayi makota ba tunda kika je?" Kai kawai ta girgiza masa ba tare da ta sake cewa komai ba, kallonta ya yi kafin ya ce. "Zo muje." Ba musu tabi bayansa har wajen motarsa, da kansa ya bude mata ta shiga, mika mata Abdallah ya yi sannan ya zagaya mazaunin direba ya je motar suka fara barin layin. Idanunsa na kan titi ya maida hankali wajen driving da yake yi ya ce. "Tunda muka bar ki na kasa samun nutsuwa, Dan ban san ya Abba da Umma zasu karbe ki ba, dama na yi tunanin haka tunda ya iya korar ki a baya to yanzu ma ba abun mamaki bane idan aka ce ya sake Koran ki, hakan ya sa na kasa nutsuwa na biyo bayanki ina tafiya ne sai na hange ki zaune ya sa na tsaya ban k'arasa gidan naku ba. Ita dai Jin sa kawai take yi ba ta San me zata ce masa ba, dan gana d'aya ba ta cikin hayyacinta. Wani restaurant ya gani a gefen titi, Hakan ya saka shi yin parking a gaban restaurant din. Kallonta ya yi tare da cewa. Na San baki ci abinci ba dan haka ki fito kici abinci sai na kai ki masauki wajen Ammi, kafin daga baya sai a San abun yi. Duk da bata ci komai ba amma bata Jin zata iya saka komai a cikinta, dan ba ta Jin cin abinci ko kadan. Girgiza kai kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba. ",Kina nufin ba za ki ci abinci ba na San Kuma kina jin yunwa?" Duk yadda ya yi da ita akan ta ci ko kadan ne ta ki yarda Sam, hakan ya sa dole ya hakura ya barta suka kama hanyar zuwa masauki. Bayan ya yi parking ne suka fito Abdallah na rungume a hannunsa, d'akin Ammi suka nufa har ya fara yin knocking ya tuna ta ce idan ta yi sallah zata kwanta zuwa la'asar sai ta tashi Dan a gajiye take. Baya son katse mata barci ya sa ya ce. "Na tuna Ammi tana barci sai dai na kai ki d'akin da Nasreen take ki zauna kafin Ammi ta Farka ko?" Shiru ta yi dan gaskiya ba ta son zuwa kusa da Nasreen, dan ta san irin kiyayyar da take mata, amma ba yadda za ta yi dole ta yi shiru suka tafi. Key yasa ya bude d'akin yana gaba da Abdallah a hannunsa, ita Kuma tana biye da shi baya . A falo ta zauna Saman sofa shi Kuma ya nufi bedroom d'in, ya tarar da Nasreen ta yi d'ai d'ai akan gado tana barci, Affan na gefenta shima har lokacin barci yake yi. Falo ya dawo inda take zaune ta yi tagumi idanunta na kan tv. Amma a zahirin gaskiya ba tv. take Kallo ba tunani kawai take yi. Jin motsin ya fito ne ya sa ta d'aga kai ta kalle shi, a hankali ta ce. "Ina Auntyn?" "Tana barci." Ya bata amsa tare da zama d'aya daga cikin kujerun dake falo. "Ban yi sallah ba." Ta fad'a tana kallonsa. "Okay." Ya fad'a yana nuna mata k'ofar toilet dake falon, dan dama akwai toilet a nan bayan Wanda ke cikin bedroom. Ba tare da ta cire hijab ta ta shiga cikin toilet din, bayan ta shiga ne ta cire hijabin ta rataye a inda ta ga an rataye towels. Sai da ta yi alwala ta idar sannan ta mai da hijabin dake jikinta, fitowa ta yi ya nuna mata darduma ta shinfida ta gabatar da sallah. Tana idarwa ta ji ana Kiran sallar la'asar, dan haka shi ma ta gabatar, bayan ta idar ne ta ji muryarsa yana cewa "Bari na je masallaci na dawo ko?" Yana rufe baki sai ga Affan ya fito daga bedroom d'in, da zai nufi Dad d'insa amma ganin Amatullah ya sa ya saki murmushi tare da cewa. "Anci." Murmushi Amatullah ta sakar masa tare da cewa. "Na'am d'an gidan Aunty." Dama ko da ya fito hannunsa rike da chocolate da biscuit ya fito, zama ya yi akan cinyar Amatullah dake zaune kan sallaya ya yi yana mika mata biscuit,karba ta yi ta bud'e tana bashi a baki yana ci. Ajmal dai fita ya yi ya barsu nan Abdallah na kan kujera yana sana'ar barcinsa. Bayan ta gama bashi biscuit da chocolate ya Sha lemu tunda dama shi ba mai son cin abinci ba ne sai kayan zak'i. Sai surutu yake zuba mata ita Kuma tana dariya tana biye masa, har ta saki rai ta rage bacin ran da take ji azuciyarta, kamar daga sama taji an daka mata tsawa an ce. "Ke!" A firgice ta dago kai tana kallon Nasreen dake tsaye tana jefa mata mugun Kallo. Karasowa ta yi ta janye Affan dake zaune a Saman kafarta tare da cewa. "Uban me ya kawo ki nan?" Kanta a kasa ta ce. "Kiyi hak'uri Aunty Abban Affan ne ya ce na..." Katse ta ta yi ta hanyar cewa. "Abban Affan ya kawo ki, ko Kuma kika kawo kanki kin kasa zaman gidan ubanki saboda kin Saba da karuwanci, abin naku har ya kai ya kawo ki a d'akin da nake? Me ya sa bai kama maki naki d'akin ba kuje can ki karata da iskancin Ku." Kuka Amatullah ta ke yi kafin ta ce "Wallahi Aunty ba yadda kike tunani ba ne Sam..." "Yi mun shiru Mallama me za ki ce mani ne, duk abunda zai fito daga bakin ki k'arya ne. Ba dai na maki gargadi akan cewa ki fita daga harkar mijina baki ji ba, to shikenan mu zuba mu gani zan ga Wanda zai yi nasara ni da ke." Ta na nufi inda Abdallah ke kwance ta daga shi da hannu d'aya tare da wurga wa Amatullah shi, da ba don ta yi zafin nama ta rike shi da sauri ba da ya fad'i. Gigitaccen kuka ya sake na tsoratar da ya yi inda Nasreen ta cigaba da cewa . "Karbi shegen d'anki mara asali ki bar nan kafin na nuna maki kalata. Ta juya baya tana kokarin fita kenan sai ga Ajmal ya shigo, ganin irin ihun da Abdallah ke yi ne ya saka shi cikin tashin hankali. "Subahanalilahi! Me ya same shi?" Amatullah ta Mai da kwallar da ya cika mata idanu ta ce. "Ba komai." Mai da dubansa ya yi zuwa ga Nasreen dake cika tana batsewa ya ce. "Me kika yi masu?" Ya yi tamabyar fusakarsa a tsuke, ita ma tsuke fuska ta yi tare da cewa. "To me zan masu, sai ka tambaye ta ai gata nan." Tayi maganar tana watsawa Amatullah harara. Sake tambayar Amatullah ya yi tare da cewa. "Amatullah me ya samu d'ana?" "Fad'owa ya yi daga kan kujera shi ne yake kuka." Cikin rashin yarda da maganar ta ya ce "To ina kike kokarin zuwa?" "Zan je na duba Ammi ne." Duk yadda ya so Jin ta bakinta Sam ta ki fad'a masa, dan haka dole ya kyaleta ganin Abdallah ma ya yi shiru ya daina kuka. "Okay ki jira na fito ina zuwa, ki zauna yanzu zan fito." Yana gama fadar haka ya nufi bedroom, inda Amatullah ta juya tana kokarin fita ta ji muryar Nasreen na cewa. "Daga karshe ina sake jaddada maki ki fita harkar mijina fa, dan indai a kansa ne ba abunda ba zan iya aikatawa ba, zan iya yin komai a kansa zan iya illata rayuwarki ba ke kadai ba har da matsiyatan iyayen ki." A fusace Amatullah ta Kalli Nasreen Jin zan zagi iyayenta. Cikin kakkusar murya ta ce "Duk abunda za ki yi ki tsaya iya kauna kada ki saka iyayena a ciki, Dan na san darajar su, Kuma da kika cewa na fita harkar mijinki aj ba ni ce na ke shiga harkarsa ba shi ne yake bibiyata idan har kin isa Kin cika mace to ke ce za ki hana shi kula ko wace mace sai ke, domin idan kin yarda da kanki ba za ki ji tsoron wata mace ta rab'i mijinki Hakan zai tabbatar mani da kin cika mace ba wai ki zo kina tumasanci wai ke Mai kishi ba, tabbas kishi halak ne amma ki yi kishi irin na matan sahabbai na farantawa mai gida ba na hauka da jahilci ba. Kina zaune ba ki San yadda za ki ja hankalin namiji zuwa gare ki ba, baki San yadda za ki mallaki zuciyarsa ba ki hana shi kallon kowace sai ke ba, ba soyayya nake da mijinki ba tsautsayi ya saka na damu cikinsa nake rainon d'ansa amma kiga yadda yake ke rawar kafa akaina, a haka kenan ina ga ace na amince masa na fara soyayya da shi ina bashi kulawa ta ai wallahi kina ji kina gani mijinki zai fi karfinki ya dawo tafin hannu na sai yadda na yi..." Kafin ta k'arasa maganar Nasreen ta yi kukan kura ta yi cikin Amatullah, daidai lokacin da Ajmal ya fito, Amatullah na ganin haka ta ja gefe da sauri cikin zafin nama, Hakan ya saka Nasreen ta yi karo da bango, Amatullah kuwa tayi ficewarta dan ta gaji da abunda abunda Nasreen ke mata. Nasreen kuwa tana kai hannunta ga goshinta ta ji jini yana zuba a goshinta, kuka ta sake cike da takaici. Ganin junin da ke zuba Ajmal ya fara magana yana cewa. "Wai me ke damunki haka ne, kin yi hauka ne?" Kuka take tana zagin Amatullah in tana cewa "Wallahi ko ni ko ke sai na ga abun waye ya tsaya maki a garin nan, kin San waye ni kuwa? Kin San waye ubana? Zan sa a batar da ke ko na kashe ki Kuma na kashe banza, wallahi ba zan kyale ta ba." Kokarin fita take daga d'akin Amma Ajmal ya rike da dan idan ta fita a haka akwai matsala, waya ya d'auka ya kira abokinsa dake nan garin wato Dr Khali Wanda likita ne, ya masa bayanin komai ya sanar da shi hotel din da yake da lambar d'akin. Fita yayi ya rufe ta da key ta ciki sannan ya fita Amatullah ya samu tsaye ya ce mata "Muje wajen Ammi Dad ma ya iso sai ku gaisa,da murna tabi bayansa Ya yi knocking d'akin Ammi ta bud'e ya ce ta shiga yana zuwa, da sauri ya koma d'akin da Nasreen take dan ya ji yadda take dukan k'ofar Bi tashar TASKAR MAMAN IHSAN a WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z 🤦‍♀️ *'YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) Page7️⃣5️⃣ Ya yi knocking d'akin Ammi, ta bud'e ya ce wa Amatullah ta shiga yana zuwa. Da sauri ya koma d'akin da Nasreen take dan ya ji yadda take dukan k'ofar d'akin. Yana isa yasa key ya bud'e k'ofar, tun kafin ya shiga take jan k'ofar tana kokarin fita daga d'akin, sai dai bai bata damar hakan ba key ya saka ya rufe k'ofar tare da zare key din ya saka a aljihunsa, ganin haka ya sa ta fara jan handle din k'ofar da karfi kamar zata b'alla. Ganin ba ta da damar fita ne matukar ba shi ya bude ba ya da ta isa gabansa ga jiri da take ji kanta na juyawa, Hakan ya saka ya janyo ta jikinsa tare da kokarin yin magana, sai ji ya yi tana cewa. "Wallahi ba zan barta ba sai ta San ko wace ce ta tabo." Zaunar da ita ya yi gefensa ya fara magana. "Kin ga yanzu kiji da kanki kafin daga baya kiyi wani abun, ya kamata ki nutsu baki ganin yadda kike fitar da jini ne?" A fusace ta ce "Eh bana gani!" Girgiza kanta ta yi cikin takaici ta ce. "Ka damu da halin da nake ciki ne, a gabanka wannan yar matsiyatan yarinyar ta ji mani ciwon, sannan ta saka kafa ta fita bayan ta zage ni ba abunda ka iya yi mata ko? Saboda ta fini a wajen ka ya sa ko me ta yi daidai ne a wajen ka ko?" "Kin ga duk abunda ya faru kece kika janyo wa kanki, daidai lokacin da nake fitowa na ga kin nufe ta ita kuka ta kauce zuwa gefe, yayin da kika jiwa kanki ciwo sai ki Dora mata laifi, kare kanta ta yi ganin yadda kika nufe ta me ye laifinta a ciki? Ke ce kika janyo wa kanki da kanki." Wayarsa ce ta yi ruri inda ya d'aga Dr Khali ke sanar da shi ya iso, fita yayi ya shigo tare da Dr Khalil. Gaishe ta Dr Khalil ke yi da kyar ta amsa Dan kowa haushinsa take ji. Kayan aiki ya ciro inda ya fara yi mata treatment. Ammi kuwa tayi mamaki ganin Amatullah, bayan ta karbi Abdallah ne suka zauna ne take tambayar ta abunda ya faru, nan Amatullah ta bata labarin yadda suka yi da mahaifinta, jinjina kai kawai ta yi tare da sake kwantar mata da hankali, dan ta hangi tashin hankali cikin kwayar idanun Amatullah. Bayan Dad ya dawo daga masallaci ya shigo, nan Ammi ta sanar da shi halin da ake ciki, nan ya nuna cewa ai da tun farko Ammi ba ta barta ba ta dawo da ita, bisa la'akari da korar da ya mata a baya, ba zai hakura cikin sauki ba. Ammi ta tambaye ta ko ta ci abinci ta ce ba ta ci komai ba, ba za ta iya cin abinci ba, ko da Ammi ta matsa mata sai dai kawai ta dauko ruwa a fridge ta sha, ta ce ba zata iya cin abinci ba. Sai k'arfe biyar Dady ya kira Ajmal a waya ya bashi umarnin ya fito su tafi. Lokacin Dr Khalil ya gama kula da Nasreen har ya mata allurar barci, tana barci Ajmal ya janyo hannun Affan suka fito daga d'akin bayan ya rufe ta waje da key. Kiran Ahmad ya yi a waya ya sanar da dayan direban zasu futa, kafin ya yi knocking d'akin da su Ammi suke , bayan ya shigo Ammi ta kalle shi tare da cewa. "Ina Nasreen din take?" Shiru ya yi kafin ya ce. "Tana barci." "Okay." Ta fad'a yayin da ta d'auki gyalen ta da handbag, sai a lokacin ta tuna da wayar Amatullah ta bata wayar. Tare suka fito gaba d'aya dan zuwa gidan su Amatullah. Dama Ahmad da dayan direban suna jiransu a mota, Ammi suka zauna dayan motar ita da Amatullah da Affan, sai Dady da Ajmal suna bayan da dayar motar, sauran security Ajmal ya ce su yi zaman su. Bangaren Abba kuwa bayan an sallamo su daga asibitin suka dawo gidan, inda Mai nape ya kawo su har k'ofar gida, suna shiga ya yi sauri ya shinfida wa Umma tabarma, sannan ya shiga d'akin ya kawo mata filo ya jingine a bango ta kishingida. Ruwa ya debo a ranada ya kawo mata, tana shirin Sha ne suka ji sallamar yaro, amsawa suka yi su duka, yaron ya gaishe su sannan ya ce. "Wai ana sallama da kai." Ya yi maganar yana kallon Mallam Abdullahi. "Wa ke sallama da ni?" "Wasu mutane suka zo cikin motoci suna waje." Yaron ya yi maganar yana kallon Mallam Abdullahi, Dan Jim ya yi tare da cewa. ",Ka ce ina zuwa." Yaron ya fita ya samu Dady, inda Dady ya ciro kudi ya bawa yaron, ya tafi yana Jin dad'i. Mallam Abdullahi ya fito yana kallon mitocin tare da kallon Dad da mamaki, shi dai bai taba ganin wannan mutum ba amma ko ba'a fad'a masa ba ya San babban mutum ne. Da sallama ya k'araso wajen tare da yin sallama, Dad ya amsa masa tare da mika masa hannu suka gaisa, dama Dady ne kawai ya fito sauran kowa na cikin mota. Bayan sun gaisa ne Dady ya ce. "Kai ne Mallam Abdullahi?" "Eh ni ne." Abba ya fad'a yana jiran me Dady zai ce, sai ji ya yi yana cewa. "Idan ba damuwa ko zamu iya shiga ciki tare da iyalina nake." Ya yi maganar yana kallon Mallam Abdullahi. "To ma Sha Allah, Ku shigo ba damuwa." Ya yi maganar yana nufar hanyar cikin gidan, inda Ajmal ya fito sai Ammi ta fito rungume da Abdallah, Affan na rike da hannun Dad d'insa. Amatullah ce ta kasa ko motsi sai da Ammi ta mata magana sannan ta motsa tare da ziro kafarta a waje ta fito. Abba na shiga ya ke sanarwa Umma sun yi baki, sannan ya dauko tabarma guda biyi ya shinfida masu. Da sallama suka shigo gidan Abba na ganin Amatullah annurin fusakarsa suka d'auke, Ammi kuwa murza idanunta ta yi Dan gani take kamar gizo ne ba Amatullah ba ce, ganin idanunta garau suke ta zaro idanu cike da mamaki ta ce. "Amatullah tawa ce nake gani ko mafarki nake yi?" A guje ta ruga ta rungume Umma tare da fashewa da matsanancin kuka Mai tsuma zuciya, Umma ma ta kasa hak'uri sai kukan take yi. Abba ya Kalli Ammi da Ajmal da Dady dake tsaye ya ce. "Bisimillah Ku zauna mana." "Ajmal ya durkusa ya gaida Abba cikin gairmamawa, ya amsa masa cikin sakin fuska da walwala. Bayan sun zauna ba abunda ake ji sai sautin kukan Amatullah, da kyar Umma ta tsaida nata kukan sannan ta rarrashi Amatullah, itama shiru ta yi amma tana manne da jikin Umma tana addu'ar Allah ya sa kada Abba ya kore ta. Bayan wajen ya yi tsit ne Dad ya fara magana tare da yiwa Allah godiya. Sannan ya sanar da su haduwarsu da Amatullah da irin zaman da suka yi tare da ita, bayan nan ya bawa Amatullah damar ta sanar da iyayenta abunda ya faru da ita, Wanda mahaifinta Sam bai ba ta damar hakan ba. Tana kuka ta fara basu labarin abunda ya faru da ita, tun farawar ta shaye-shaye da yadda aka yi ta samu ciki, sannan ta basu labarin rayuwar da ta yi lokacin da Abba ta kore ta da ciki, lokacin da ta zo Kaduna da irin wahalhalun da ta sha da kalubaken da ta fuskanta na rashin abinci da wurin kwana da yadda sai ta yi bara sannan take samun abincin da za ta ci, ga ciki ga yunwa da zaman da ta yi tana kwana a primary school da ranar da yunwa ya hana ta barci ta fito cikin dare tana neman abunda za ta ci a ranar da Ajmal ya Kade ta da mota ya kai ta asibiti aka mata aiki aka cire baby komai ta Sanar da su. Umma rungume Amatullah ta yi tana kukan tausayin rayuwar da yar ta ta fad'a, kuka take yi Amatullah ma na kuka, hatta Abba da ya kore ta sai da ba ya ji an tausayin ta tare da haushin kansa na yanke hukunci cikin fushi ba tare da yin bincike ba. Nan Dad ya masa nasiha tare da bashi lafin korar da ta mata, dan hannunka baya rubewa ka yanke ka yar, duk abunda ta aikata bai dace ya kore ta ba, saboda zata iya fad'awa cikin wani hali Kuma shi ne sanadi, nan Abba ya gane kuskuren abunda ya aikata tare da cewa in Sha Allah hakan ba zata sake faruwa ba. Ammi ce ta mika wa Umma Abdallah tare da cewa. "Ga mijin naki." Murmushi ta yi tare da karbar yaron tana kare masa Kallo, Dad ya cigaba da cewa. Sannan muna rokon gafara a wajen Ku na abunda yaronmu ya aikata wa yarinyar Ku, duk da cewa ba laifin su ba ne shiryayen al'amari ne na muguwar k'awa ya zama dole mu nemi yafiyar Ku." Nan suka amsa da ba komai ai kaddara ce ba laifinsa ba ne ita Kuma da ta yi masu haka za ta hadu da mahallicinta. Nan Ajmal ya Kara gaishe su tare da basu hak'uri duk da kunya ta kama shi. Amatullah ta yi farin cikin dawowar ta gida, ganin ga iyayenta sun yafe mata, dan ba ta yi zaton haka ba. Godiya suka masu tare da cewa gobe zasu dawo, bayan sun fito ne Ajmal ya sa yara suka dinga kwasar kayan Amatullah da na Abdallah da suka baro a Kaduna, dama Ahmad ya zo da kayan da Kuma tsarabar k'asar Qatar da Amatullah ta dawo da su. Umma da Abba mamakin run yawan kayan suke mota biyi aka ciko daga kayan sakwa sai kayan wasan Abdallah, da keken zama da godon kwanciya da suka wasu takarce nasu. Bayan an gama shigar da kayan ne sai suka ga wata mota ta yi parking, Dad ya ce su tafi Ajmal ya ce zai biyo su a baya yana so suyi sallama da Amatullah ne, murmushi kawai suka yi suka tafi da Affan suka bar shi nan tare da Ahmad. Wanda ke cikin motar da ya iso ne ya fito daga motar tare da zubawa Ajmal idanu, kallon-kallo suka yi wa junan su kowa ya gane kowa, Ajmal ya gane Munnir ne Wanda ya je gidansa neman Amatullah, shima ya gane shi sarai kau da kai Ajmal ya yi daga kallon juna da suke yo. Ajmal ne ya ciro wayarsa ya tura mata Text message cewa ta fito su yi sallama zai tafi, tana kokarin shigar da kayan ne ta ga sakon sa, Dan haka sai ta nufi k'ofar fita bayan ta sanarwa wa Umma tana zuwa. Daidai bakin k'ofar fitowa gidan ne tana hango Ajmal fusakarsa d'auke da murmushi sai ta ga Munnir a gabanta ya sa hannu ya tare k'ofar fita gidan ba halin ta fita. Murmushi ta sakar masa tare da cewa "Ya Munnir kai ne?" Shima murmushi ya yi tare da cewa "Ni ne masoyiyata." "Sannunka da zuwa." Make kafada ya yi tare da cewa. "Ba zan amsa ba na yi fushi da kika yi nesa da ni tsawon lokaci." "Ka yi hak'uri bari na je na sallami Ya Ajmal." Yamutse fuska ya yi tare da cewa. "Saboda ya fini a wajnki ko me, tsawon lokaci ina kewarki amma hakankalinki na wani wajen." "Ba haka ba ne minti biyi yanzu zan dawo." Tayi maganar tana kokarin raba gefen shi ta wuce, hannu ya kai zai riko hijabinta ya ji Ajmal ya rike masa hannu. *Na ji sakon Ku masu cewa na k'ara yawan typing da masu cewa kullun na dinga typing, Ku yi hak'uri da ni zuwa wani lokaci Kuma maneji da wannan*🙏🙏🙏🙏 Bi tashar TASKAR MAMAN IHSAN a WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z 🤦‍♀️ *'YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) Page7️⃣6️⃣ Tayi maganar tana kokarin raba gefen shi ta wuce, hannu ya kai zai riko hijabinta ya ji Ajmal ya rike masa hannu. Kokarin kwatar hannunsa yake yi daga rikon da Ajmal ya masa amma ya kasa, dan ya fi

Chapter 32 of 51