mata da yaronta."
Tana gama fadar haka ta katse Kiran wayar.
Jiki a sanyaye ya nufi bathroom ya dauraye jiki ya shirya cikin wani farin yadi mara nauyi rigar mai gajeren hannu.
Fita ya yi daga d'akin ya nufi wurin da ma'ikatan hotel din suke, kudi ya ciro daga aljihu ba tare da ya kirga ba ya mikawa d'aya daga cikin ma'ikatan hotel din ya sanar da shi ya ce ya siyo masa riga na yaro d'an watanni biyar da pampers. Sannan ya sanar da shi lambar d'akinsa.
Daga haka ya koma ciki yayin da matashin saurayin ya fita zuwa aiken da Ajmal ya masa.
Ajmal Kuwa ganin lokacin sallar la'asar ta yi
sallar la'asar ta yi ne ya sa shi shiga bathroom don dauro alwala.
Sai da ya idar da sallah sannan ya ji knocking, tashi ya yi ya nufi k'ofar falon ya bud'e.
Saurayin ya gani rike da leda ya Mika masa tare da cewa.
"Yallabai kudin da ka bayar sun yi yawa ga sauran canjinka."
Ya karasa maganar yana Mika masa canjin da kudin za su Kai dubu goma."
"No ka rike canjin kawai."
Godiya ya masa cikin jin dadi ya juya ya tafi.
Komawa ya yi cikin d'akin ya dauki Khalifa ya Kai shi bathroom ya masa wanka da ruwan dumi.
Ya shafa masa man shafawarsa ya Sanya masa pampers don ya iya shirya yaro lokacin da Nasreen ke goyon Affan idan ba ta masa wanka akan lokaci ba ko sai dai ta ce a kira Mai kula da shi, wanda idan Ajmal ya ga haka da kansa yakan gyara yaron indai yana gari bai yi tafiya ba, da haka ya iya.
Yana gama shirya Khali wayarsa ta soma ruri, ganin Amatullah ce ya saki mirmushin gefen baki sannan ya daga ba tare da ya yi magana ba. Cikin kuka ta ce
"Assalamu alaikum."
A can kasan makoshi ya amsa don ba ta ma ji shi ba. Don haka ta ce.
"Hello."
A dakile ya ce.
Ina jinki."
"Wani lokaci za ka kawo mani Khalifa?"
"Ba zan kawo shi ba ke da shi har abada."
"Kuka ta fashe da shi tana cewa."
"Idan ka yi Mani haka ba ka yi mani adalci ba wallahi Ina son sa ba zan iya rabuwa da shi ba sai dai mutuwa ce kadai za ta raba ni da shi."
"Murmushi ya saki tare da shafa gashin kansa ya ce."
" Au da gaske? Saboda saurayin ki ne kika banzatar mani da yaro ya fado yana ihu kina jin sa kuka yi kamar ba ku jin sa ko? Shi bai damu ba ke ma uwarsa ba ki damu da shi ba tun da na iso wajen da kuke zance na ji kukan nasa amma Ke da wancan saurayin naki za ku ce ba ki ji ba?"
"Wallahi ban ji ba sai da ka dauko shi sannan hankalina ya Kai ga kukan nasa."
"Ba ya cikin ranki ne shi ya sa baki ji ba, don haka zan Kai shi Inda za'a kula mani da shi, ko nawa ne zan biya don Ammi ma ta ce ba za ta rike shi ba sai dai na bar shi wajenki kuma hankalina ba zai kwanta da hakan ba, yanzu zan tafi zan Kai shi Inda za'a kula da rayuwarsa."
Yana gama fad'ar haka ta saka ihu wanda jin haka ya saka shi yin tsuki tare da katse Kiran wayar.
*Daga alka'alamin*✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
09065327995
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
🤦♀️ *'YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
Na
Zainab Abdullahi K.NT
(Maman Ihsan)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page9️⃣3️⃣
Yana gama fad'ar haka ya ta saka ihu wanda jin haka ya saka shi yin tsuki tare da katse Kiran wayar.
Murmushi ya saki kuma ya tabbatar da cewa maganar Ammi gaskiya ne tana k'aunar d'ansa , ya ji dadi jin haka, d'aukar Khalifan ya yi suka fito falo, key din motarsa ya d'auka sannan suka fice ya rufe k'ofar.
Yana driving yana tunanin dole ya san abun yi, don yau ya yanke shawarar tunkarar Abba da zancen auren Amatullah, duk da ya san abun ne mai matukar wahala Abba ya amince masa amma ya shirya tunkarar sa, don ba ya jin zai ita hakura da Amatullah, Kuma yana da yakinin cewa Amatullah ba son Munnir take yi ba umarnin Abba kawai take bi.
Yana wannan tunanin har ya karaso wani katafaren shagon da ake siyar da kayan yara.
Sai da ya tsaya ya siye masa kayan wasa masu kyau da tsada kama daga kan keken zama kayan wasa wanda ya san yaro dake zaune zai yi wasa da su da Kuma kayan sawa da su pampers da madara duk ya siya masa.
A haka har ya karasa k'ofar gidan ya yi parking din motarsa, fitowa ya yi daga mazauninsa sannan ya zagayo gefen da Khalifa yake daukarasa ya yi hannunsa rike da wani abun wasa na yara duk da ba iya wasa da shi ya yi ba.
Komawa ya yi cikin motan ya zauna yana rike da Khalifa, wayarsa ya d'auka ya tura wa Amatullah sakon text message cewa yana waje.
Tana zaune ta yi tagumi a dakinta yayin da Fadeela ke zaune a gefen ta tana bata baki.
Shigowar message din ne ya sa ta saurin d'aukar wayar ta duba, don dama duk bayan minti d'aya sai ta duba wayar ko za ta ga Ajmal ya neme ta, ganin abunda ya rubuta a text message ne ta tashi da sauri ta zari hijab ta saka tana nufar hanyar waje tana cewa.
"Fadeela ina zuwa ya kawo mani shi."
Bin ta kawai ta yi da kallo tare da yin murmushi.
Tana fita ta hango motarsa a k'ofar gidan, tunda ta fito yake kallonta fuskarta d'auke da murmushi kamar ba ita ce ta dinga masa kuka a waya ba, da sauri ta karasa wajen tare da knocking glass din motar, a hankali ya sauke glass din motar tare da zuba mata dara-daran idanunsa, ita ma dara-daran idanun nata ta zuba masa karaf suka hada idanu, da sauri ta d'auke idanunta saboda kaifin da idanunsa ke da shi.
"Idan ba za ki shigo ba ki juya ki koma."
Ta ji saukar muryarsa a cikin kunnenta.
Da sauri ta zagayo gefensa ta zauna. Ba wanda ya yi magana a cikinsu face sallamar da ta masa ta shigo.
Lumshe idanu ya yi bai ce mata komai ba tsawon mintuna biyar, hakan ya sa ta zubawa masa idanu tana kallonsa, ba tare da ya bude idanu ba ya ce.
"Kallon mene ne haka?"
Kunya ya kamata amma ganin ai bai kama ta tana kallonsa ba ne ya sa ta ce.
"Ni ban kalle ka ba."
A hankali ya bude idanunsa tare da zuba mata su ya ce.
"Haba."
Sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da yatsun hannunta, sai ji ta yi yana magana.
"Ki yi hauri na d'aga maki hankali ko?"
Murmushi kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba. Cigaba ya yi da cewa.
"Na dauka ba ki damu da shi ba ne shi ya sa kike banza da shi hakan ya Saka raina ya baci na d'auke shi na so raba ku, ashe kina son sa na dauka haushinsa kike ji."
"Meye laifinsa da zan ji haushinsa, wallahi Ina son da ba zan iya rabuwa da shi ba."
"Ya zama dole ki rabu."
Da sauri ta kalle shi tare da cewa.
"Saboda me?"
"Saboda wani kike son ki aura ba mahaifinsa ba, wanda ni Kuma ba zan iya bari ki tafi gidan wancan shashashan da yarona ba wallahi. Don ba zan taba barin yarona a Inda za'a wulakanta masa rayuwa ba, don haka ki sawa ranki cewa matukar wani za ki aura to rabuwa da Khalifa wajibi ne dan sai dai na d'auke shi ba za ki gidan wani da ni tunda kin ce ba ki so na ko?"
"Ai ba ta san lokacin da furta.
"Ina son ka fa."
"Sai ta rufe fuskarta da tafin hannunta."
Ya ji dadi har cikin ransa don haka ya ce.
"To me yasa kika dinga wahalar da ni, tun a Kaduna nake bunki da ki karabi soyayya ta amma sam baki karba ba."
"Abba nake tsoro saboda ya riga ya wa Munnir alkawainn ba shi aurena, Kuma na san halinsa akan magana idan ya kafe.
"To amma da farin cikin Munnir ya fiye masa farin cikinki ne?"
"Bai Fi ba amma kimarsa baya so ta zube a idanun wani."
Shiru ya yi kafin ya ce.
"Yau zan same shi zan sanar da shi maganar aure na da ke, kuka zan kawo masa dalilai kema Ina son ki fiti ko sanar da shi abunda ke zuciyarki, ki fad'a masa cewa ni kike so ba wani ba."
Gabanta ne ya yi dukan uku-uku, don har fargaba ta kama ta. Cikin sanyin murya ta ce.
"Tsoro nake ji."
"Ba abunda zai faru Kar ki damu fita mu je."
"Abba ya yi tafiya yau sai wani sati ya ce zai dawo."
"Shikenan zan dawo in Sha Allah idan ya dawo don ba zan iya hakura da ke ba wallahi, ke tawa ce saboda ni aka yi ki ke kadai."
"Kai kuma saboda wa aka yi ka?"
Tsayawa ya yi yana kallonta kafin ya ce.
"Saboda ke mana."
"Nima sabida ni kadai aka yi ka?"
Murmushi ya yi sannan ya ce.
"Ina kika ajiye Nasreen?"
Shiru ta yi kafin cikin sanyin murya ta ce.
"Mu shiga ciki ko?"
Saboda ta Kau da zancen, take gabanta ya fadi saboda ta tuna da Nasreen sai dai hakan ba zai hana ta kaunarsa ba ai namiji mijin mace hud'u ne ko da bai auri Nasreen ba ai ba za ta taba sakankancewa ba zai mata kishiya ba tunda namiji ne shi. Sai dai kowacce da halinta za ta zauna.
Har ta fito ta nufi cikin gidan yana kallonta ganin ta sauya daga Kiran sunan Nasreen, murmushi ya yi yana addu'a Allah ya sa kishinsa take don yana daga alamomin soyayya."
Tsayawa ya yi daga zaure yana jiran ta masa iso wajen Umma.
Ba jimawa ta fito ta sanar da shi ya shigo, da sallama ya shiga cikin gidan.
Har k'ofar d'akin Umma ta raka shi ya shiga bayan ya yi sallama yana rungume da Khalifa. Ita kuma ta nufi dakinta ta samu Fadeela na danne-danne da wayarta kallonta ta yi tare da cewa.
"Lafiya kuwa na ga kin canza."
Kasancewar tana neman mai ba ta shawara ya sa ta zauna gefen Fadeela. Labarin Nasreen ta bata wanda ta sani a zaman da suka yi tare, sannan ta sanar da ita abunda Ajmal ke Shirin yi idan Abba ya dawo. Ga mamakin ta sai ta ga Fadeela na dariya tana cewa.
"To me na d'aga hankali akan irin wannan sha sha shan kishiya da za ki auri mijinta wacce ba ta san yadda ake kula da miji ba da yadda ake tarairayarsa ba ba abunda ya sani sai kishin hauka da jahilci, ai mancewa za ki yi da ita ki rungumi mijinki da d'anki ki kyautawa iyayensa mance da ita da ita da babu duk d'aya za ki d'auke su."
Murmushi Amatullah ta yi tare da cewa
"Ai ita ma mace ce..."
Muryarsa ce ta Saka ta dakatawa tana sauraren sa jin yana wa Umma sallama Kuma tana masa gidiya da SA albarka da alama kudi ya ba ta jin haka ya sa ta leko, karaf suka hada idanu ya sakar mata tsadadden murmushinsa mai tsayawa a zuciya.
Da sauri ta koma ciki bayan ta saki labulen ta komai ciki tare da sakin labule ta koma ciki zuwa can bayan kamar mintuna biyar da fitarsa sai ga yaran mokota sun yi sallama amsawa ta yi ta fito daga d'akin ganin su da kayan wasan yara nik'i-nik'i ne ya sa ta sakin baki cikin mamaki, sannan ta ce .
"Ku shigo nan da su."
Daidai lokacin da Umma ta fito daga cikin d'akinta, ita ma mamakin kayan ne ya kamata ganin ga wasu nan da yawa da basu yi amfani da shi ba sannan ya karo wasu kamae wanda bai san zafin kudi ba.
Bayan yaran sun gama ne suka koma wajen Ajmal ya ciro kudi daga cikin aljihunsa wanda bai san nawa ba ne ya dai Mika masu ya ce su raba.
Amsa suka yi cike da farin ciki suka bar wajen suna godiya.
Zama ya yi cikin motarsa yana jiran fitowar Amatullah.
A can kuwa mamakin kayan ya kama Fadeela ta ce,.
"Amma yana son yaronsa."
"Ai shi dama yana son yaransa, kin ga ko Affan ma yaron Nasreen d'aki guda aka ware masa na kayan wasansa, Kuma sai kin shiga za ki yi mamamakin kayan wasan da ke ciki."
"Muje na gabatar da ke wajensa ko?"
"A'a ki tafi ke kadai Ina jiranki anan?"
Tayi magana tana kokarin kunna datar wayarta.
"Ai baki Isa ba sai mun tafi ta kamata na sanar da shi ga kawata d'aya tilo da nake da."
"Ta d'an yi dariya tare da cewa
"Har na tuna ranar farkon had'uwarki da Munnir ranar da muka dawo daga islamiya muga buya dubiya ruwa ta mana duka sai ga Munnir ya tsaya a gabanmu da niyyar taiamako ashe 'yar kyakkyawa ya gani yana so."
Dariya kawai Amatullah ta yi tare da jan hannun Fadeela suka fita bayan ta sanarwa Umma, har lokacin Khalifa na barci.
Fita suka yi hannunsu a sarke cikin na juna, kallo d'aya ya masu da ya hangi fotowarsu sannan ya maida Kai zuwa ga wayarsa yana danne-danne.
Kasancewar gilashin motar a sauke suke ya sa suka yi sallama amsawa ya yi ba tare da ya dago Kai ba tare da cewa.
"Lafiya lau ya kike?"
"Alhamdulilllah."
"Ma Sha Allah."
Kawata ce d'aya tilo da nake da ita, sunan ta Fadeela."
Jinjina Kai ya yi tare da cewa
"Hakan na da kyau ba amfanin tara k'awaye, Allah ya bar ku tare."
"Ameen ta amsa."
Fadeela ta kalle shi tare da cewa.
"Sai an jima Allah ya tsare."
Da Ameen ya amsa ta shhga cikin gidan.
"Ki shigo ciki mana."
Ba musu ta shiga cikin motar, tsawon mintuna biyu yana danne-danne da waya kafin ta ajiye ya ce.
"Zan tafi gobe in sha Allah, idan Abba ya dawo ki sanar da ni nazo muyi Mai yiwuwa a bani matata ko?"
Yayi maganar yana kashe mata ido d'aya.
Kunya ta kama ta tana kokarin fita ta ji motar a kulle.
"Ina za ki tafi?"
"Gida zan shiga."
"Na ga yanzu kika zo ko har kin gaji da ni ne?"
"To ai Kai ne kake saka ni jin kunya."
Murmushi ya yi kafin ya ce.
"Na daina."
Fira suka d'an taba duk da dai shi ba mai yawan magana ba ne sai jefi-jefi yake mata magana, ita kuma daga eh sai a'a don kwarjininsa ke hana ta iya kallonsa har ta masa wani magana."
"Har yanzu 🏧 card da na baki dan ki dinga cire kudi idan kina bukata ba ki fara amfani da shi ba ko?"
"To ba na bukatar kudin ne."
"Ki cire ki bawa masu bukata."
Kudi ya ciro bandir din dari biyu dubu ashirin kenan ya Mika mata.
"Ki bawa kawarki ta hau abun hawa, idan bikini nata ya tashi ki tuna mani sai na turo maki abunda za ki bata."
Godiya ta masa ya ciro wani karamin box ya bud'e, wani had'ad'd'en zobe sai d'aukar idanu yake yi.ciro shi ya yi tare da cewa bari na saka maki."
Ba musu ta mika hannunta ya zira mata a yatsarta ta tsakiya.
Murmushi ta yi ganin yadda zoben ya mata kyau sosai.
Godiya ta masa sanan ya bude mata motar har za ta fita ta ji ya ce
"Ki kula mani da yarona, Kuma ki kuka mun da kanki."
"Murmushi ta yi sannan ta fice daga motar, sai da ya ga shigarta gidan sannan ya tada mota ya bar wajen.
Bayan ta shjga ne ta bawa Fadeela kudin da ya ba ta, karba ta yi tana godiya kafin ta ce.
"Wannan mutumin yana da jiji da Jai ko?"
Dariya Amatullah ta yi ta kalli Fadeela ta ce.
"Me kika gani?"
"Na ga fa ko da muka fita ko kallonmu bai yi ba, ko da ace ke ya sanki ai ni bai sanni ba, ba wani fara'a ce da shi ba ko da ya je shagon da nake aiki haka ya ke magana ma kamar dole ta zame masa."
"Kada ki damu haka yake."
Daga nan suka cigaba da firar yadda Shirin nikin zai kasance.
Da misalin karfe goma na dare Ajmal ne ke magana da Ammi a waya.
"A gaskiya Ammina jira nake Abbanta ya dawo dole na nemi auren Amatullah, ba zan iya hakura da ita ba, don wallahi sai na cutu."
"Wai ni Kam wai har yanzu ka kasa d'aukar matakin da ya dace akan matarka ko? Wane irinn rayuwa ne wnnan, a baya na maka maganar Karin aure hankalinta ya tashi ta dawo, amma yanzu ta koma ko?"
"Hmm Ammina lamarin Nasreen sai addu'a kawai na dauka saboda soyayyar da take mani zai sa ta canza amma ba wani canji, Ammi wallahi na Fi ki damuwa da lamarin Nasreen tin yana bani tsoro har ya daina, gaba d'aya ba ta da tarbiyya amma duk da hakan bai dame ni ko da na aure ta sallah da wankan tsarki ba ta iya ba sai da na koyar da ita, na neaman nata malamar addini ta koyar da ita amma ta ce ba ta so ba yadda na iya na rabu da ita haka Ammina ke kanki shaida ce yadda take waifantar da aure na ta dinga tafiye-tafiye duk kasar da take so ba tare da izinina ba za ta bar Inda nake ta tare a gidan iyayenta tsawon watanni ba ta ba tare da ta dawo ba sai ta ga dama haka za ta dinga yawo sakaka kamar wata tinkiya Ammina Ina tsoron yarona ya tashi ba sani akan addininsa. Ammina Nasreen ba za ta canza ba ba zan sake ta ba amma ya zama dole na Kara aure, dan Allah ki taya ni addu'a Allah ya sa mahaifin Amatullah ya amince mani na aure ta."
"To rabin raina Allah ya tabbatar Maka da abunda ya fi zama alkhairi a gare ka."
"Ameen Ammina."
"Wato ganin ka ya mani wuya ko?"
"Ba haka ba ne Ammina zan yi wata yar tafiya ne daga nan zan biya na ga Affan zai yi birthday na cika shekaru biyar."
"To Allah ya jibanci lamuranka ya raya Affan Ina gaishe shi."
Sallama suka yi ya kashe wayar.
Bangaren Amatullah lokacin da Fadeela ta tashi tafiya gida ne ta ce Amatullah ta raka ta karbo dinki shagon Mai dinkin da take bawa dinki, ba wani nisa da unguwar da Amatullah suke, izinin Umma ta nema suka fita bayan ta Saka dogon hijab. Suna tafiya daidai sun kawo bakin titi ne zasu tare abin hawa sai wayar Amatullah ta yi ruri, ganin Ajmal ne ya sa ta d'aga da sallama. Jin muryarsa tayi yana cewa.
"Ba na fad'a maki bana son kina hawa abin hawa na haya ba, meye amfanin motar da na baki na ce zan nema maki direba kika ce baki so ko? To ni Kuma ba na bukatar kina yawo kina neman abin hawa don haka ki juya ki koma yanzu zan turo maki direba ki bashi key din motar.
.juyawa ta yi tana waige-waige ba ta ga alamar motarsa ko mai kama da shi ba, to ya aka yi ya sani ko dai Aljani ne shi?
09065327995
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
🤦♀️ *'YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
Na
Zainab Abdullahi K.NT
(Maman Ihsan)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page9️⃣4️⃣
Juyawa ta yi tana waige-waige ba ta ga alamar motarsa ko Mai kama da shi ba to aka yi ya sani ko Aljani ne shi?
Daidai lokacin da wani mai napep ya yi parking a gabanmu ganin Fadeela ta tsayar da shi, Amatullah ta cewa Ajmal to shikenan ta ji, katse wayar Amatullah ta yi ganin kamar ita suke jira, shiga suka yi Inda Fadeela ta sanar da shi inda zai kai su.
Daidai k'ofar shagon telan suka Sauka, Fadeela ta biya shi suka shiga shagon da sallama, teloli ne guda uku a shagon sai yaran da ke koyan aiki su biyar. Gaishe su suka yi suka amsa Inda Amatullah ta Kali Aminu wanda shi ne telan da ta bawa dinki.
"Aminu na zo ka bani kayan ko?"
"Eh sannu da zuwa ku zauna mana ko ruwa ku sha."
"Kar ka damu tafiya zamu yi yamma na yi."
Shi dai gaba d'aya hankalinsa na kan Amatullah, sa kallonta yake yi. Zuwa can ya ce
"Hajiya ke ba ki kawo kayanki ba ne?"
"A'a."
Ta bashi amsa a takaiice.
"Yaushe za ki kawo?"
Share shi ta yi kamar ba ta ji me yake cewa ba, Fadeela ce ta ce.
"Don Allah ka bani kayana mu tafi tunda Kai ka ce yau na zo na amsa ka kammala."
"Akasi aka samu ne Fadeela, amma saura kad'an ki yi hakuri yanzu na k'arasa maki zan ajiye duk wannan aikin da nake yi ko saboda wannan kyakkyawar k'awarki."
Ya yi maganar yana ciro kayan Fadeela da ya rage kad'an ya karasa su."
"Ma Sha Allah la k'uwwata illah billah."
Ya karasa maganar yana kallon Amatullah tare da cewa.
"Kyakkyawa ki zauna mana kada ki gaji da tsayuwa wani abun Sha za'a kawo maki?
"Girgiza Kai ta yi tare da cewa.
"Ba komai na gode."
Wayarta ce ta yi ruri, Ajmal ne ya kira don haka ta d'aga tare da fita wajen shagon.
"Assalamu alaikum."
Daga can bangaren ya amsa tare da cewa.
"Amatullah wato ba ki ji magana ta ba sai da kika yi abunda ranki ke so ko? Shin a baya Ina ce duk Inda za ki fita sai kin lullube fuskarki da nik'ab idanunki kawai ake gani, amma yanzu kin daina haka kike fitowa wasu 'yan iska na yabawa da kyan fuskarki ko?"
Lamarin Ajmal yanzu ya Kara Saka ta cikin kokonto. Tsoro ma ya fara ba ta, cikin sanyin murya ta ce.
"Me ya faru ne, Kuma ya aka yi ka san ban saka nik'ab ba, dazu ma kana mani zancen cewa zan hau abun hawa na haya ya aka yi ka san da haka?"
Bai ba ta amsa ba ya ce.
"Yamma ya yi ki yi sauri ki koma gida kafin magrib ya yi don yanzu ba jimawa lokacin sallar magrib zai yi."
Yana gama fad'ar haka ya katse kiran wayar, ta bi wayar da kallo tana mamaki, ba ta koma cikin shagon ba ta cigaba da zama a wajen har Fadeela ta fito ta same ta suka tafi.
Telan ya so karbar lambar wayar Amatullah, ganin ba ta bashi fuska ba ya sa shi barinta.
Suna hanya ana Kiran sallar magrib, sai da aka fara ajiye Amatullah a k'ofar gidansu sannan aka wuce da Fadeela gidansu. Bayan ta shiga d'akin Umma ta gaishe ta ne ta debi ruwa dan yin alwala.
Da misalin karfe tara na dare tana zaune a d'akin Umma bayan ta gama cin abinci wayarta ta yi ringing, tana dubawa ta ga Munnir ne yake Kiran wayar, Khalifa da ke hannunta ta kwantar a Saman gadon kasancewar wata ran a d'akin Umma yake kwana, idan ya farka sai ta bashi madara ya sha.
Dakinta ta koma zuwa lokacin har wayar ta yanke ya sake kira, zama ta yi a bakin gadonta daidai lokacin da wata Kiran ta sake shigowa wayar, dauka ta yi tare da yin sallama cikin zazzakar muryarta.
"Assalamu alaikum warahmatullah"
"Wa'alaiki salam Gimbiyata."
"Ina wuni?"
"Lafiya lau fatan kina lafiya?"
"Alhamdulilllah."
"Na so na zo don na sake rarrashin ki amma ban samu zuwa ba sabida wani dan aiki da ya rike ni, amma duk da haka ko da ban han ki ba idan na ji zazzak'ar muryarki mai narkar mani da zuciya."
Ba ta San sanda ta saki murmushi ba tana cewa.
"Munnir kenan. Kana da abun dariya."
"Ba wani abun dariya wallahi ni ji nake watanni da Abba ya d'iba na saka ranar auren mu sun yi mani yawa wallahi, ji nake fa kammar shekaru goma ya saka, da Ina da sama to da na dawo da nesa kusa, fatana na ga an dauko ki an kawo ki a matsayin matata."
"Ka da ka damu ai kamar gobe ne, Abba ma yana da dalilin sa, ka ga bai kamata a ce ayi aure Ina shayar da yaro ba Kai ma ai ba za ka so a ce Ina amarya Ina shayarwa ba."
"Wai kina nufin dama da yaron nan za ki zo zaman aure a gidan?"
"Eh mana don gaskiya ba zan iya nesa da shi ba."
"Ni Kuma ba na da ra'ayin rike d'an kowa ba. Dan ba zan iya hada soyayyar da zan yi wa d'ana da na wani ba, kada ki ce ban yi maki adalci ba daga baya shi ya sa na fad'a maki gaskiya ta, fatan za ki fahimce ni."
Shiru ta yi na lokaci ta kasa cewa komai, wanda hakan ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 42 Chapter of 51