yana son sanin dalilin yanke wannan hukuncin ba. Tunawa ya yi yanzu lokacin barcin Kakarsa ce ya sa ya juya.
Swimming pool ɗin dake cikin gidan ya nufa, dan akwai tarin damuwa a tattare da shi. Kasancewar ƙananan kaya ne a jikinsa hakan ya sa ba tare da ɓata lokaci ba ya faɗa cikin ruwan.
Tsawon lokaci ya ɗauka a cikin ruwan kafin ya fito kai tsaye part ɗinsa ya nufa tare da faɗawa toilet, wanka ya yi tare da sauya kayan jikinsa.
Cikin ƙanƙanin lokaci ya fito cikin ƙananan kaya har riga da wando threequarter baƙi ya yi kyau sosai gashin kansa sai sheƙi yake. Kyawun surarsa da cikar zatinsa suka ƙara bayyana, ya fito yana tafiyarsa irin na lafiyayyun maza.
Zama ya yi a falon tare da ajiyar wayoyinsa kan tebur dake gabansa, ɗaya daga cikin wayar iphone 15 pro max ya dannawa wata lambar kira.
Ɓangaren Amatullah kuwa tana tsaka da barci ta ji an tokari ƙafarta buɗe idanu ta yi tare sauke su akan na Ummanta. Gabanta ne ya faɗi ganin hawaye akan fuskar Ummanta, gabanta ne ya faɗi ta fara kiran sunan Ummanta yayin da ita ma kukan take
"Umma dan Allah ki daina kukan nan..."
Kafin ta kai ƙarshen maganar ta ne ta ji saukan maruka har guda biyu.
"Ki ka ce na daina kuka? Wato abinda kika yi dai dai ne ko? Kin saka Mani ciwo mai raɗaɗi a zuciyata sannan ki ce ka da na yi kuka? Amatullah kin cuce mu kuma kin cuci kanki ga shaye-shayen ga bin maza Amatullah, wannan shine irin tarbiyyar da muka baki?"
Kuka Amatullah take mai tsuma zuciyar mai saurare, ta riƙe ƙafar Umma tare da cewa
"Umma wallahi summa billahillazi ba na bin maza wallahi ban taɓa aikata zina ba."
"Wannan cikin kuma fa ko a ruwa ne kila jiƙa kika sha?"
"Wallahi Umma ki yarda da ni wannan abun da ya faru zanen ƙaddarata ce, ban isa na goge Abinda Allah ya ƙaddara zai faru da ni ba. Da ace mutum ya na iya sauya ƙaddararsa to da tuni na daɗe da goge tawa ƙaddarar na sauya wani, amma sai dai kasha ba wa bai isa ya canza abinda Allah ya ƙaddara zai faru da shi ba. Haka Allah ya so dani Umma, tunda nake a rayuwata ban taɓa kusantar wani ɗa namiji ba, ban taɓa bari wani ya riƙe ko da ƙumbata ba, Umma bari na ba ki labarin abinda ya faru."
"Na ta kwashe labarin komai ta bata tun daga ranar da Hafsat ta fara ganinta da yadda shige ta har ranar da ta kai waya aka mata wannan aika-aika.
Kuka sosai Umma take yi tare da cewa
"Me ya sa ba ki sanar dani abinda ya faru da ke ba? Ai da kin faɗa mana cewar wata za ki je kai mata da hakan ba ta faru ba, kuma yanzu ba wanda ya isa ya zarge ta tunda ba ki fuskar waye ba kuma ba hujja."
"Umma na ɓoye maki cewar zan je kai mata waya ne saboda na yi maku alƙawarin na daina kula ta shi ya sa na tafi ba tare da saninku ba ashe tsautsayi da ƙaddara ce suka fitar da ni."
"Bayan kin dawo washe gari da kin sanar da mu amma rashin sanar da mu shine babban kuskuren da kika tafka. Yanzu yadda Abbanki ya yi fushi haka ba zai taɓa sauraren kowa ba kuma..."
Muryar Abba suka ji yana kiran Umma, Umma ta kalle ta tare da cewa
"Tashi mu tafi."
Cikin sanyin jiki Amatullah ta mike ta bi bayan Ummanta suka fita, a tsakar gida suka same shi kasancewar dare ne yana riƙe da torchlight a hannunsa.
"Amatullah kin cuci kanki da kanki dan ba mu kika cuta ba, waye ya maki ciki?"
Kuka ta saka tana bashi haƙuri ya daka mata tsawa tare da sake tambayar ta.
"Abba wallahi ban sani ba ban san ko waye ba dan Allah ku gafarc..."
Saukar marin ta ji lafiyayyu guda huɗu,na ta zuba tana kuka.
"Zan maki tambaya ta ƙarshe ki tabbatar kin faɗa mani Gaskiya, idan har ba ki faɗa ba to ni nasan irin matakin da zan ɗauka akanki wanda kuma ba wanda ya isa ya dakatar da ni duk tsaurinsa kin san idan na faɗi magana ɗaya ta zauna."
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
08168611693
09065327995
Love you oll😍?
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
🤦♀️ *ƳAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Dedicated to
_Mom Irfaan_
_Ilham pinky Dearling_
_Aisha M.B_
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubucirsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Page1️⃣7️⃣&1️⃣8️⃣
"Zan maki tambaya ta ƙarshe ki tabbatar kin faɗa mani gaskiya, idan har baki faɗa ba to ni na san irin matakin da zan ɗauka akanki. Wanda kuma ba wanda ya isa ya dakatar da ni duk tsaurinsa, kin san idan na faɗi magana ɗaya ta zauna."
Kallonta ya sake ki cikin baƙin ciki da takaici ya ce,
"Wa ya maki ciki?"
Sautin kukan ta ne ya ƙari sosai, cikin kuka da magiya take cewa
"Abba wallahi ban san ko waye ba."
Gani yake ta san komai raini ne ya sa ta ce masa haka, tunda yanzu ta fara shaye-4 sannan ga bin maza. Ga shi yanzu ta janyo masa abun kunya.
Kukan kura ya yi tare da nufar inda take gadan-gadan dukanta kawai yake yana ta ko'ina ba kakkautawa, ganin zai iya kashe ta ne ta yi saurin shiga ta tare da sakin kuka mai tsuma zuciyar mai saurare.
A lokacin na Amatullah ta yi ke kwance sai nishi take fitarwa duk ta gama galabaita da dukan da Abba ya mata, tana kwance ta kasa tashi ta ji muryarsa yana cewa
"Ba mu kika cuta ba kanki ne kila cuta wallahi, mai ye ban maki ba daidai iyawata da kuma ƙarfi a? Na maki daidai gwargwado ba ki rasa ci da sha ba baƙi rasa sutura ba ilimin zamanin nan da na Muhammadiya duk na saka ki kin yi su, mun yi iya bakin ƙoƙarin da za mu yi dan ganin kin samu ingantacciyar tarbiyya. Sai lokaci ɗaya kika ruguza ginin da muka yi shekara da shekaru muna gina ta."
Ita dai sai kuka ya kalle ta ya cigaba da cewa
"Ba zan aibata ki da bakina ba, haka kuma ba zan maki mugun baki ba sai dai na ce maki duniya ce ta ishi kowa riga da wando, tunda duniyar kika zaɓa to ga ta nan ga ki, ki tattara kayanki ki bar mani gidana."
Kula ta dage da shugaban wanda ya fi na da sauri tana cewa
"Abba dan Allah ka mani rai ka taimake Ni ka tausayiwa rayuwar da zan shiga idan ka Kore ni ban san yadda zan shiga bamu da kowa a ƙasar nan da za mu zauna a wajnsu."
"Duk inda za ki tafi ki tafi ba damuwata bane, damuwata shine ki bar mani gidana, kafin na ɗauki hukunci."
Rarrafawa ta yi zuwa gaban Umma ta riƙe ƙafarra tana riƙon ta akan ta saka baki ta bashi haƙuri ba ta da inda zata je a halin yanzu. Umma hawaye kawai take zubawa dan ta san halin mijinta kaifi ɗaya ne idan ya faɗi magana ya faɗa kenan ba ya canzawa.
Ajiyar zuciya ta sauke tare da kallon mijin nata ta fara magana tana cewa.
"Mallam dan Allah ka yi haƙuri ka da ta tafi rayuw..."
Hannu ya ɗaga mata alamar dakatarwa sannan ya ɗora da cewa ka da ki kuskura ki ce za ki bani haƙuri dan na rantse da Allah yarinyar nan yau sai ta bar mani gida."
"Ko da abinda ya faru da ita ba laifin ta bane? Ka saurare..."
"Bana son jin komai daga bakinki."
Kallon Amatullah ya yi tare da cewa
"Kwaso kayanki ki tafi."
Kula take kamar ranta zai fita daƙyar ta iya tashi ta nufi ɗalibta, jakar kayanta ne ta ɗauka tare da kwaso kayan dake cikin 'yar durowar ta zuba a cikin jakar. Anan ta yi kiciɓis da kuɗin da Munnir ya bata, dama bayan ya bata ta nufi ɗakin Umma da niyyar bar ta ga bata nan, sai ta nufi ɗakinta ta ajiye, ta manta ne ba ta bawa Umma ba. Sai yanzu da ta ga kuɗin ta tuna.
Sakawa ta yi a cikin ƙaramar jakarta 👜 ta kulle. Bayan ta rataya ƙaramar jakar ne ta janyo babbar tana tafiya tana kuka.
Ake jakar ta yi ta nufi inda Abbanta ke tsaye, kafin ta ƙarasa wajensa ya ɗaga mata hannu alamar ta dakata.
"Dakata!"
Tsayawa ta yi can daga inda take.
"Idan har kika ƙaraso inda nake na lahira sai ya fiki jin daɗi, ki tafi kada ki ki tunzura ni na yi maki mugun baki, ki kiyayi bakin nan nawa,domin gabar da zata fito sai tafi gobara sharri akanki, dan idan na maki baki kin gama yawo."
Durƙisawa ta yi a wajen tana kuka ta ji ya daka mats tsawa
"Ki fita!"
Juyawa ta yi aguje ta bar gidan sai da ta fita ne ta juyo tana kallon gidan, tafiya take tana waigen gidan. Duk da ba ta san lokaci ba amma ta san dare ya fara yi, dan duk ƙofar gidan da ta wuce sai dai ta ga an tura ƙofar gidan.
Tana tafiya ba tare da sanin ina za ta tafi ba. Bayan ba ta da kowa a gari ba dangin uwa ba na uba.
Yanzu babban tashin hankalinta ina za ta dosa, dan ba za ta iya kwana a waje ba musamman yadda ta ke da tsoro.
Tunani ta shiga yi ina za ta dosa? Ko ta tafi gidansu ƙawarta Fadila ce? Girgiza kai ta yi ba zai yiwu ba, dan idan ta je mahaifin Fadila zai iya zuwa ya samu Abbanta kuma hakan zai kara tunzura shi sosai.
Dan haka sai ta yanke shawarar ta je ta samu Nafeesat duk da kasancewar ita 'yar maye ce amma ita ce ta dan abu da ya faru da ita. Dan haka ta je sanar da ita abinda ya faru a dalilin abinda aka mata.
A bakin titi ta samu mai adaidaita sahu ta shiga ya sanar da shi inda zai kai ta.
Har ƙofar gidan Nafeesat ya kai ta inda ta ciro kuɗi daga cikin wanda Munnir ya bata ta bashi.
Karɓa ya yi tare da yi mata sannu dan ya ga duk rauni ne a jikinta.
Daƙyar ta ja akwatin kayan ta shiga gidan Nafeesat. Da sallama ɗauke a bakinta ta shiga ciki, a tsakar gidan tana ƙoƙarin rufe ƙafa, da alama club za ta tafi.
Kasancewar gidan da take haya kusa da club ɗin ne, jin sallamar Amatullah ya sa ta waiga tare da tare da amsa sallamar.
Ganin Amatullah a cikin yanayin da ta ganta, ne ya sa ta saki key ɗin dake hannunta wanda dama ƙoƙarin rufe ƙofar take.
"Na shiga uku Amatullah lafiya me ya same ki haka? Daga ina kike na ganki da kaya."
A guje ta ƙaraso wajen da Amatullah take ta riƙe ta, Amatullah ce ta saka kuka tare da rungume Nafeesat ta fashe da matsanancin kuka. Take sai Nafeesat ta ji tausayin Amatullah har cikin zuciyarta.
Janyo ta ta yi tare da cewa
"Mu shiga ciki in ya so sai mu yi magana."
Daga nan ne sai ta ɗauko jakar kayan Amatullah suka shigq cikin ɗakin.
Bayan ta ajiye kayan ne ya kalli Amatullah dake kuka ta tambaye ta me ke faruwa. Dan ta ga shaidar duka ne a jikinta.
Nan Amatullah ta kwashe duk labarin abinda ya faru ta sanar da Nafeesat.
Nafeesat ta matuƙar tausaya mata sosai sosai ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa
"To yanzu ina za ki je ki zauna?"
"Nima ban sani ba wallahi."
"Baki da 'yan uwa a nan garin ne?"
"Bani da su."
"Kina nufin ba ku da kowa?"
"Muna da dangi amma ba'a Nigeria ba dangina suna can Niger can ne tushen mu. Sai dai kakannina sun rasu na uwa da na uba ba mai rai, sai dai muna da dangi a can ƙasar kuma mun daɗ bamu je ba tun banyi wayo ba, kuma yanzu ba zan iya kai kaina can ƙasar ba, dan ko na je ban san inda zan fara neman neman su ba."
"To yanzu ya za'ayi? Ko za ki iya zama da ni."
Bata da wani zaɓi dan hala ta gyaɗa kai alamar eh.
"To Allah ya sa ba za ki takura ba, kasancewar kinga falo ɗaya ne sai ɗakin barci guda ɗaya da toilet sai kitchen dake cikin falo."
"Ba damuwa Anty ko nan falon ne zan dinga kwanciya."
"Okay to bari na je na haɗa maki ruwan wanka mai zafi ki gasa jikinki."
Haka ta haɗa mata ruwa mai zafi ta yi wanka sannan ta ba ta magani da ruwa ta sha.
"To ni za. Fita zan je club can zan kwana, ki rufe ƙofar ta ciki idan na zo da safe zan bubbiga maki ƙofar ki buɗe."
Jinjima kai ta yi tare da cewa
"Allah ya kaimu."
"Ameen"
Daga nan ta mike ta fice daga ɗakin.
Tana fita Amatullah ta saka dakata ta rufe ɗakin.
Washe gari suna zaune suna karya kumallo, Hafasat ce ta shigo ganin Amatullah ta saki baki tana mamaki me ya kawo ta nan.
Ko zama Hafsat ba ta yi ba Nafeesat ta kalli Hafsat ta ce,
"Hafsat da waye kika san yi wa yarinyar nan aika-aika ?"
"Wani abin ne kuma ya sake faruwa da kike tuhuma ta."
Ajiyar zuciya Nafeesat ta sauke tare da cewa
"Baya ce dai ta haihu."
"Bana gane baya ta haihu ba."
"Ina nufin akan abinda ya faru da Amatullah har nake maki zancen cewa ko kece kika sa aka yi mata fyaɗe kika ce a'a."
Taɓa baki Hafsat ta yi tare da cewa
"To sai aka yi yaya?"
"Ciki ne da ita?"
Wani irin dariya Hafsat ta sheƙe da shi tare da cewa
"Kai wannan labarin ya Mani daɗi, kunga masu yi dan Allah."
"Kinga ba na faɗl maki bane dan ki tozarta ta ko ki mata dariya. Mafita muke nema.
"To sai ku nemi shi a inda kuka san kun ajiye shi."
Ran Nafeesat ya ɓaci sosai za sosai dan haka ta kori Hafsat ta tafi .
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Amatullah ta cigaba da zama gidan Nafeesat, ba rashin ci ba rashin sha, sai dai abu ɗaya da ba za ta iya jura ba shine iyashegen da suke yi ba kunya a gaban ko ma waye.
Hafsat kullun tana cikin damuwa da tunani,na rashin iyayenta da ba ta ganinsu, musamman mahaifiyarta da ta fi tausayinta. Kullun za ta yi ta kuka ita kaɗai ba mai rarrashinta. Dan dama Nafeesat b zama take yi ba, sai dai idan suna bukatar shaye-shaye ne suka shigowa ita da ƙawayenta su yi ta shan kayan maye.
Damuwar da take ciki na halin da take ciki. Dan haka sai ta tuna cewa kayan maye da suke sha yana rage masu damuwa ne, kuma ita ga ta kullun cikin damuwar take, dan haka sai ta yanke shawara ta je ta ɗauki Benelin a ɗakin Nafeesat ta sha.
Hakan kuwa aka yi ta ɗauki Benelin ta dinga sha. Haka ta dinga barci.
Har su Nafeesat suka zo suka same ta tana ta barci, kwalaben maganin da suka gani a gabanta ne ya tabbatar masu da kayan maye suka sha. Bugu da ƙari ba ta samun yin barci kwata-kwata, dan ko ta kwanta ta rintse idanu barcin baya ɗaukar ta.
Duk da an ce barci ɓarawo ne amma ita ya kasa samun sace ta.
Ganin yadda take barci ne ya sa Nafeesat ta ji daɗi a ranta, kasancewar ba ta samun barci sai kuka take yi. Hakan ya sa Nafeesat jin daɗi ganin tana barci, wanda a da barci ya ƙaurace mata. Amma yanzu ta samu barci kuma idan ta tashi za ta ji damuwarta sun tafi, sai dai ta wani ɓangare na zuciyarta ba ta so hakan ba, saboda ka da ta san da shaye-shaye bayan ta daina.
Hafsat kuwa ganin yadda Amatullah ta shawo hakan ya faranta mata rai sosai da sosai.
*QATAR*
Zaune yake a katafaren falonsa yana sanye da wata jallabiya ruwan ƙasa, mai gajeren hannu. Na'ura mai ƙwaƙwalwa ne a gabansa yana danne-danne. Gefe ɗaya kuma ga wasu takardun a gabansa.
Wayarsa ce ta yi ruri daga jin kiran ya san cewa Amminsa ce.
Ɗagawa ya yi tare da yin sallama.
"Assalamu alaikum"
Daga can ɓangaren Hajiya Bilkisu ta amsa masa da
"Wa'alaika Salam."
"Barka da warhaka Ammina fatan kina lafiya."
"Lafiya lau farin cikina ya kake?"
"Ina lafiya."
"Ya Nasreen da su Affan har yanzu ba su dawo ba suna can California?"
Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa
"Eh tana can har yanzu."
"To yaushe za ta dawo?"
"Nima tamabayar da na yi mata jiya kenan amma wai bata san ranar dawowarta ba."
"Kamar ya bata san ranar dawowarta ba, kai a matsayinka na mijinta ba ka da ikon cewa ga ranar da za ta dawo ne kuma ta dawo?"
"Ammina tun last week na ce mata ta dawo fa ina ganin sai na je da kaina sannan za mu dawo tare."
Daga nan suka cigaba da magana duk a cikinsu cikin harshen turanci suke wannan magana.
Bayan sun kammala maganar ne sai ya kira ɗaya daga cikin bodyguard ɗinsa ya bashi umarnin ya tattara takardu nan ta kai masa mota.
Daga nan ya tashi ya nufi part ɗin kakarsa dan tana jiransa ya bari ne sai ya kammala abunda yake yi.
Wasa wasa haka Amatullah ta kwashe watanni biyu a gidan Nafeesat, kuma shaye-shaye da take yi sai ya sa ta rage damuwar da ke cikin zuciyarta. Kullun sai ta sha Benelin sannan take samun kwanciyar hankali.
Wata rana ta kwanta tana barci sai ta yi mafarki da Ummanta tana mata faɗa akan ta daina shaye-shaye,ba shi zai gyara rayuwarta ba sai dai ma ya kara lalata mata rayuwa ta bar wannan wajen da take ta yi nesa da su in sha Allah za ta samu mafita, a kullun tana cikin mata addu'a."
Bayan ta farka daga mafarkin ne ta ji ana kiran sallar asuba. Tashi ta yi ta shiga bedroom ɗin Nafeesat ta ɗauro alwala ta zo ta yi sallah.
Har gari ta waye ba ta kwanta ba ta fara haɗa kayanta ta yi a cikin jakkarta. Wanka ta yi ta sauya kaya.
Da safe da Na Nafeesat ta dawo ta yi mata godiya na halaccin da ta mata, ta kuma sanar da ita yau za ta bar garin nan za ta yi nesa da shi.
Hankalin Nafeesat ya tashi sosai ta yi iya ƙoƙarin ta na hana Amatullah tafiya amma abu ya gagara.
Ta tambaye ta ina za ta je tunda ba ta da kowa a ƙasar nan, ta ce ita ma bata sani ba duk inda Allah ya kai ta za ta je.
Sallama ta mata ta raka ta har ƙofar gida suna ɗagawa juna hannu ta tafi.
Keke napep ta tara ta ce ya kai ta gare ku inda za ta hau mota.
Babban tashar mota ya kai ta tana zuwa ta ga motocin da jama'a.
Wani ya hange ta ya ce,
"Hajiya Kaduna za ki je?"
Hala kawai ta tsinci kanta da cewa
"Eh."
Ya amshi jakar hannunta ta bishi a baya aka saka a bayan mota.
Yunwa take ji dan haka sai ta ta hangi mai fanke ta siya da lemun roba. Kasancewar motarta cika dama mutum ɗaya ake jira
Kuɗin mota ta biya cikin kuɗin da Munnir ya bata Naira dubu hamsin ce.sai dari biyar da ta bawa mai napep da ya kaita gidan Nafeesat. Da kuma wanda ta hau ya kawo ta gare ji.
Ƙarfe bakwai da rabi motarsu ta tashi zuwa Kaduna.
Ƙarfe ɗaya na rana suka isa garin Kaduna. Bayan mota ta tsaya kowa ya fita ya dauki jakarsa, itama ta ɗauki jakarta ba tare da ta san inda ta dosa ba.
Tsayawa ta yi bakin titi tana tunanin ina za ta bi.
Wasu rantsatstsun motoci su biyar ne suka dannao kai, sakin baki ta yi tana kallon motocin guda biyar sai dai ta tsakiyar ce duk ta fi su kyau da haɗuwa. Kowace mota wajen lambar ta ga an rubuta Ajmal 1, sai ta biyu ta ga an rubuta Ajmal 5, sai ta tsakiyarsa yake ciki aka rubuta Ajmal 10, sai ta hudu kuma Ajamal 2,sai ta ƙarshe aka rubuta Ajmal 4, a cikin zuciyarta ta ambaci sunan
'Ajmal'
Kenan suka motocin mutun ɗaya ne, wahala ta yi ta ga yadda mutane ke ta jin daɗi suna cewa ga Garkuwar su nan ya dawo ubansa maganin kukansu, haka suka dinga jin daɗi wasu na cewa ai tunda yau ta iso gobe ƙofar gidansu ba masaka tsinke.
Haka kawai sai ta tsinci kanta da faɗuwar gaba wanda bata san dalili ba.
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan )
08168611693
09065327995
Love you oll😍😘
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
🤦♀️ *ƳAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Dedicated to
*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION*
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubucirsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Page1️⃣9️⃣&2️⃣0️⃣
Haka kawai ta tsinci kanta da faɗuwar gaba wanda bata san dalili ba.
Hangen wata mata mai suyan masa ta yi daga can gefe. Dan haka cikin Sauri ta ƙarasa wajan da mai suyar masar take.
Maza ne mafi yawancin wandanda ke zaune a wajen, sai mata kuma wadanda suke taya matar aiki.
Da sallama ta ƙarasa wajen gaba ɗaya suka juyo suna Kallonta tare da amsa mata sallamar. Sunkuyar da kai ƙasa ta yi dan sai kunya ya lulluɓe ta musamman yanzu da cikinta ya bayyana, gani take kamar duk wanda ya kalle ta zai san cewa cikin bai da uba.
Mai masar ce ta kalle ta tare da cewa
"Ƴata mai kike so?"
"Masa nake son siya."
"To ta nawa kike so?"
Ta nawa za'a baki? Naira ɗari-ɗari ce kowace guda ɗaya."
"To bani da ɗari biyar."
"To amma sai kin ɗan jira ga wuri can ki zauna kafin na saka maki."
Matar ta ƙarasa maganar tana nuna mata wata bishiyar dake gefensu, ba kowa a wajen sai saya ma'akaciyar dake taya matar wanke-wanke. Kwanoni take wankewa sai waɗanda aka gama cin masar da su.
Zama ta yi a ƙasar bishiyar tana tare da gaida yarinyar da ke wanke-wanke wajen. Yarinyar ta amsa wacce ba zata wuce sa'ar Amatullah ba.
Zama ta ta yi ta haɗa tagumi tana tunanin duniya.
'Yanzu ya rayuwarta za ta kasance a wannan garin da ba ta da kowa kuma bata san kowa ba, ita dai ta yi mafarkin Ummanta ta ce ta yi nesa da wajen da take zaune cikin masu shaye-shaye, amma ba ta san yadda aka yi ta tsinci kanta da cewar Kaduna zata nufa ba. To yanzu ina ta dosa ina zato yada zango ina zata kwana?'
Ta yi zurfi cikin tunani har aka kawo mata masar ma bata sani ba, wacce ta gama wanke-wanke ce ta kawo mata tana magana shiru, sai da ta dafa kafaɗarta sannan ta ɗago da sauro ta kalle ta. murmushi yarinyar ta sakar mata tare da cewa
"Wannan tunani haka 'yar uwa ta lafiya ne, ki rage mana ko kina tunanin Baban baby ne?"
Da sauri ta ɗago kai ta kalli yarinyar tare da yin tunani wani Baban Baby kuma? Yarinyar ta sake yin murmushi tare da cewa
"Na ga kamar baki gane nufina ba kar ki ce na saka maki idanu dan haka mutane ke cewa ina da saka idanu wa mutane, na ga kamar ba ke kadai bace shi ya sa na ce kina tunanin mijinki wanda Baban babyn cikinki ne."
Ta ƙarasa maganar tana murmushi tare da ajiye mata masar a gabanta cikin plate, hawaye ne suka cika idanun Amatullah ta sunkuyar da kanta ta goge."
"Subhanahi dan Allah 'yar uwa kiyi haƙuri wallahi ba da nufi n yi maganar ba, ban san za ta ɓata maki rai ba."
Girgiza kai ta yi tare da cewa
"Ka da ki damu ba komai."
'To na gode."
"So zan samu ruwan sha?"
"Eh bari na kawo maki pure water."
Daga nan ta tafi ba komawa ta zo da ledar ruwa biyu ta bata, ta amsa tare da miƙa mata kuɗin masar ɗari biyar ta karɓa sannan ta ciro Naira ɗari ɗari biyar kuma ta sake bata.
"Ga na ruwan sai dai bani da canji."
"Karki damu na siya maki ne."
"To godiya nake ƴar uwa."
Daga nan ta tafi yayin da Amatullah ta wanke hannu ta fara cin masa bayan ta yi bisimillah.
Gate ɗin farko aka buɗe wa danƙarar motocin suka kunna kai a cikin tangamemen gidan.
Motar farko ta shiga sai ta biyu su ta shigo sannan ta uku wanda Jamal ke cikinta.
Suka ƙarasa gate na biyu aka wangale masu suka shiga sannan gate
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 51