Share this page
karantawa. Kallo ɗaya za ka mata kasan cewa ba 'yar ƙasar mu bace ta fito ne daga jinsin larabawa. Ajiye jaridar hannunta ta yi ta ɗauki wayarta, kiran wata lamba ta yi ta kara wayar a kunne, ganin lambar da take kira ba'a ɗaga bane ya sa ta ajiye wayar tare da dafe goshinta. Ƙarar takun tafiya ta ji daga upstairs ta ɗaga idanunta ta kalli mai zuwa, mijinta ne Alhaji Ibrahim Tafida. Ƙarasowa ya yi tare da zama gefenta, ganin kamar tana cikin damuwa ne ya sa shi kiran sunanta. "Hajiya Bilkisu lafiya?" "Ina da lafiya Alhaji tun jiya nake kiran yaron nan a waya amma ba ta shiga, nifa gaskiya na gaji da haƙurin zamansa a wata ƙasa, ya dawo nan kusa da ni shi kaɗai nake gani na ji daɗi." Jinjina kai ya yi tare da cewa "Dama zancen sa na zo maki da shi?" Da sauri kalle shi tare da cewa "Ya kira ka ne?" Girgiza kai ya yi ya ce, "Bai kira ni ba amma na san yana cikin ƙoshin lafiya." "To wace magana ne zamu yi na sa?" Ajiyar zuciya ya yi tare da cewa "Mai girma Gwamna ne ya nemi mu tattauna da shi, bayan na same shi ne yake sanar da ni cewa yana son Ɗanmu Ajmal ya fito takarar Gwamnan jihar nan." Da sauri ta kalle shi tare da cewa "To me ya haɗa ɗana da siyasa kuma? Ko yana ra'ayin siyasar ne?" "Nima ban sani ba amma shi Governor ya kawo mani dalilinsa na zaɓar Ajmal a matsayin ɗan takarar Governor, kuma da na yi nazari na fahimce sa." "Niƙan sam ban amince ba. Domin ɗana ba zai iya daukar nauyin al'ummar jahar nan ba." "Wannan kuma sai dai mu ji ra'ayinsa amma tabbas jaiharmu na bukatarsa." Daga nan ne ya tashi tsaye ya ce, "Bari na fita ina da meeting da zan halarta yanzu." "A dawo lafiya Allah ya tsare." Da Amin ya amsa Sannan ya fice. Ɗaga idanunta ta yi ta kalli photonsa da ke manne a falon, kamar su ɗaya da mahaifoyarsay kamar an tsaga kara, fari ne kuma ba irin farin nan fau ba haskensa na da launin ja, yana da manyan idanu da dogon hanci,bakinsa pink kamar na mahaifiyarsa, gashin kansa baƙi wulik mai sheƙi irin gashin indiyawa da larabawa, sai sahensa wanda ke haɗe da gemu sun kwanta luf sun yiwa fuskarsa ƙawanya, ya yi kyau sosai kasancewarsa ruwa biyu ne mahaifinsa bafullatanin Adamawa ne, mahaifiyarsa kuwa balarabiyar ƙasar Qatar ce murmushin ya ke yi a photon, wanda har sai da wushiryarsa ta fito. A hankali ta ƙarasa wajen photon tare da shafa photon tana magana "Rashin jin Muryarka a waya ya saka ni jin ba daɗi, ka kira ni mana ko zan yi farin ciki ɗana, kai kaɗai Allah ya bani kai nake ji da gani na ji farin ciki a zuciyata. Ga shi ka yi nisa da ni har wata ƙasa. Wayarta ta lalubo tare da cewa "Bari na kira Ammi na tambaye ta ko tana tare da shi." Bayan ta danna kira ne ta saka wayar a kunnenta. *QATAR* Wata tsohuwa ce ke zaune a falonnta tana shan shayi, wayarta ce take ringing, dubawa ta yi ta ga ƴarta ce abin soyuwa a gare ta, murmushi ta yi cikin harshen larabci ta fara mata magana." "Assalamu alaikum ƴata ya kike?" Ajiyar zuciya Hajiya Bilkisu ta sauke tare da cewa. "Lafiya lau Mama, duk na shiga damuwa ne na rashin jin muryar Ajmal. Shine na ce ko yana kusa da ke zan yi magana da shi." Ajiyar zuciya tsohuwar ta sauke tare da cewa "Jiyan nan ya tafi ƙasar London." A cikin sati ɗaya shaƙuwa ta fara shiga tsakanin Amatullah da Hafsat, dan kusan kullun Hafsat sai ta zo gidansu Amatullah, har islamiyyarsu ta shiga dan ta ƙara kusanci da ita sosai. Kuma yau ne ta ƙudiri niyyar sai ta kai Hafsat cikin club ɗinsu. Dan yau ta yi niyyar fara gwada sa'arta akan Amatullah tunda ta saki jiki da ita yanzu. Ɓangaren Munnir ma yau ne ya shirya zuwa gidansu Amatullah, dan ya gabatar da kansa. *Daga alƙalamin*✍️ Zainab Abdullahi KNT (Maman Ihsan) 🤦‍♀️ *ƳAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LrTZNGwF35IKXX4sLRvFug Dedicated to *JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION* *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubucirsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *BISMILLAHI RAHMANI RAHIM* Page3️⃣&4️⃣ Ɓangaren Munnir ma yau ne ya shirya zuwa gidansu Amatullah, dan gabatar da kansa. Kamar yadda ya zama mata al'ada duk ta idar da sallar asuba ba ta komawa barci, zakar ta fara yi sannan ta yi karatun al-qur'ani mai girma. Da ta ga gari ya waye ne ta tashi ta ta nufi ɗakin Ummanta ta gaishe ta, sannan ta nufi ɗakin Abbanta ta gaida shi. Kitchen ta nufa ta haɗa itace a cikin murhu, ta hura wuta. Ta sha wahala kafin wutar ta kama kasancewar lokacin damuna ne, idan ruwan sama ya daki itace yana wahalar kamawa. Fita ta yi ta kwashi kwanuka ta yi wanke-wanke bayan ta gama ne ta yi gyara ɗakinta ta yi shara ta share tsakar gidan. Koko ta dama sannan ta yi ɗumamen tuwo, wanka ta shiga ta yi sauri-sauri ta fito dan ta makara, ta san yanzu Hafsat tana can tana jiranta a titi, don can titi take ajiye motarta tun ranar da ta kawo Amatullah da mota ƙofar gidan Abbanta ya ganta ya tambaye ta wace ce ta kawo ta da mota , sai ta ce ƙawarta ce daga ranar ne Abbanta ya mata faɗa tare da nuna cewar baya son alaƙarta da yarinyar. To kasancewar ta sanar da Hafsat yadda suka gida Abbanta ta ce tunda bai gabata ba tana cikin mota aje ta tayi ta tafi sai ta kawo shawara za ta dinga mota a bakin titin sai ta ƙaraso a ƙafa. Haka aka yi har yau ba gane ba . Bayan ta gama shirinta duka ne ta sanya Uniform za ta ɗebi koko ne ta ji sallamar Hafsat, amsawa ta yi tare da zuba mata idanu. Alamar ta yi sauri ta fito sun makara ta yiwa Amatullah, jinjina kai ta yi tare da magana a hany ta ce ta bari ta sha koko su tafi. Nan ta nuna mata cewa ta fito kawai su tafi sun yi latti za ta siya mata abinda za ta ci a hanya. Jinjina mata kai ta yi alamar to sannan Hafsat ta fice, fitarta ke da wuya, sai Mallam Abdullahi mahaifin Amatullah ya fito daga ɗakinsa, ganin Amatullah ya ce, "Har yanzu ba ki gama shiri tafiya ba kin makera." Dai-dai lokacin ne Umma ta fito daga ɗakinta. "Amatullah kin gama ko? Sannu da aiki Allah ya yi maki albarka." "Mallam Abdullahi ne ya amsa da Amin. "Umma na kammala komai zan tafi." "Kin ci ɗumamen kin sha kunu?" "A'a Umma na makara zan tafi." "To Allah ya tsare hanya ya baki Sa'a, Adawo lafiya." Da Ameen ta amsa Sannan ta kalli Abba ta masa sallama, amsa wa ya yi tare da ciro kuɗi Naira ɗari biyar ya bata ta amsa cikin girmamawa tare masa godiya ta fice. Can bakin titin ta hango motar Hafsat na jiranta, ƙarsawa ta yi wajen motar tare da buɗe muddin gaban motar ta shiga, gefen Hafsat ta zauna bayan ta mata sallama ta amsa. "Ki yi haƙuri na barki kina ta jirana ko?" Murmushi ta ƙaƙalo tare da cewa "Ai kin wuce haka a wajena." Murmushi Amatullah ta yi tare da godiya. Hafsat ta yi wa motar key tare da barin wajen, yayin da Amatullah ta ciro wani takarda a jakar makaranta tana karantawa. Tsawon tafiyar mintuna goma suka yi, a hankali Amatullah ta ɗago kanta ta kalli Hafsat wacce ke sakin murmushi. "Ba nan bane hanyar mu ko kin ɓata hanayar ne?" Murmushi ta yi tare da cewa "Ka da ki damu zan kai ki ne ki ci abinci saboda ba ki breakfast a gida ba." "A'a indan muka siya sai mu tafi da shi school ɗin idan na samu sarari sai na ci." Jinjina kai ta yi tare da cewa "Okay shikenan." Daga nan ta cigaba da driving yayin da ita kuma Amatullah ke karatu. Ƙofar wani gida ta yi parking, dan haka ta kalli Amatullah ta ce , "Tashi mu shiga ciki." Kallon wajen ta yi tare da cewa "Banga shagon cin abinci wurin ba." "Agida ne mu shiga da mun siya sai tafi nan ba nisa da school ai." Ba musu ta fito suka rufe murfin motar, Hafsat na gaba Amatullah na binta a baya. Turo ƙofar falon ta yi tare da cewa "Hy" Yan mata ne su biyar a falon uku suna kwance suna barci sai sai Nafisa da shamsiya dake fira. Kallonsu Amatullah ta yi sai ta ji hankalinta bai kwanta ba, musamman da ta ga yanayin shigarsu, kallonsu Hafsat ta yi tare da cewa "Wannan ita ce Amatullah da nake baku labarinta." Murmushi Nafisa ta yi tare da cewa "Wow, ma sha Allah kyakkyawar gaske kuwa, da alama ke Fulani ce ko?" Kai Amatullah ta jinjina mata alamar eh, ta ɗora da cewa "Ai na ga zubinki ne son kowa ƙin wanda ya rasa." Yamutse fuska Hafsat ta yi tare da cewa "To su Fulani gane su ake a fuska?" Dariya Nafisa ta yi tare cewa Ki ƙare mata kallo da kyau mana ba ki gant ga ta doguwa ba, fara wuyanta ma dogo ne, ga ta kyakkyawar gaske ƙwayar idanunki ma akwai burgewa wannan ko a cikin niƙabi kike idan mutum ya kalli ƙwayar idanunki sai sun tafi da shi, lallai ba banza ba Munn..." Ganin Nafisa na shirin yin ɓaran-ɓarama ne ya sa Hafsat cewa "Ya isa haka bamu abinci kawai ba ta yi breakfast a gida ba na ɗauko ta." "Okay" Nafisa ta faɗa tare da tashi ta nufi kitchen, Hafsat ma ta bi bayanta, a kitchen ne Nafisa ta kalli Hafsat ta ce, "Gaskiya wannan yarinyar ba ta maki laifin komai ba ka da ki cutar da rayuwarta, da alama tana da nutsuwa da tarbiyya Kada son zuciya ya saka ki aikata abinda zaki yi nadama, dan idan kika cutar da ita ba tare da hakkinta ba za ki ga Allah ya bi mata hakkinta, ba laifinta bane kuma ba ita ce ta sa Munnir ya so ta ba, ka da ki hukunta 'yar mutane da laifin da ba ta aikata ba. Ki kai ta makaranta kamar yadda kuka sanar da ita kuma ki fita harkarta daga ita har Munnir ɗin tunda shi ba autan maza bane balle ki dole sai shi." "Ai ko ita ce mai laifi da har ta yarda ta shiga motarsa, har za kamu da sonta ba zan iya fita harkarta ba domin tana neman yi Mani shamaki da masoyina. Dan haka sai na mayar da ita irina yadda ya ce baya sona ita yake so to ya yai yi idan ya wayi gari yaga ta koma kama ta?" "Wannan fa kuskure kika neman aikatawa." "Na sani daga ni har ke akan kuskure muke. Kema kin sani ai. A wannan harkar bana shiga hurumin da ba tawa ba, kin kawo mutane a cikinmu ban ƙalubalance ki ba dan haka Please ki cire idanunki kaina. Nafisat ta fita ta koma falo, inda ta samu Amatullah har lokacin tana tsaye, Kallonta ta yi cikin tausayawa ta ce, "Har yanzu kina tsaye ki? Ki zauna mana." Murmushi Amatullah ta yi tare da cewa "Na makara ne ka da na tarar an shiga class." "To ki zauna kafin ta fito ko?" Zama ta yi a Centre carpet dake falon tana wasa da yatsun hannunta. Hafsat ce ta fito ɗauke da faranti mai ɗauke da kofin shayi da bread sai lemun kwali. Hafsat na ajiye mata Amatullah ta miƙe tare da cewa "Ba zan iya jira na sha ba, kin manta na makara na dauka zamu siye abu a hanya ne." "Ki daure yanzu ki sha mu tafi." "Ƙarfe taƙwas yanzu an shiga class, bari na ɗauki biredin kawai idan na tafi sai na ci acan." Haka Hafsat ta dinga lallaɓa ta tare da mata alƙawarin za ta bawa malaminsu haƙuri, daƙyar ta lallaɓa ta har ta zauna ta fara shan tea da biredin. *KADUNA* Wani babban office ne mai ɗauke da babban tebur da kujeru gida goma sha biyu, da alama an tanade su ne don zaman tattaunawa. Mutane goma sha ɗaya ne zaune a kujerun, kowanensu an ajiye masa lemu da ruwan roba da lemu a gabansa. Shugaban jam'iyyarsu ne ya kalli kakakin jam'iya da sakataren jam'iyar ya ce, "Kamar yadda kuka sani cewa bayan zaɓe na ƙaratowa, a cikin wannan jam'iyyar ta mu Alhaji Tanimu Nuhu da Alhaji Shehu Sabi'u sun nuna sha'awar fitowa takara." Kowa ya jinjina kai alamar gamsuwa,inda shugaban Jam'iyya ya ɗora da cewa "Daga gefe kuma ga mai girma Governor ya kawo Ajmal a matsayin ɗan takarar Governor, ya samu goyon baya daga wajen Gwamnati." Alhaji Tanimu ne ya ji ba daɗi a ransa, dan yana da labarin Ajmal Ibrahim Tafida, yana jin irin taimako da gudunmawa da yake bawa al'ummar jihar. Duk da kasancewarsa ba dan siyasa ba amma yana aikin da Yakamata a ce masu muƙamin Gwamnati ne za su yi. Jama'a da yawa suna sonsa musamman talakawa dan yana taimakon su sosai. Idan yana gari ƙofar gidansa bai rabuwa da jama'a masu kawo mukansu gare shi musamman mata. Sau tari ƙofar gidan nan kamar kasuwa yadda talakawa ke cincirindo ana raba masu kuɗi. Takaici ne ya ishi Alhaji Tanimu dan ya san muddin yayi takara da Admar ba zai kai labari ba. Shi kuma ɗayan abokin takarar bai damu ba. Sakataren jam'iyar ne ya ɗora da cewa "Mai girma Gwamna ya nuna cewar Ajmal zai shigo wannan jam'iyar ta mu." Kakakin jam'iya ya ɗora da cewa yanzu tunda mutane uku suka nuna sha'awar fitowa takara sai a fara tsara yadda za'ayi." Shugaban jam'iyya ne ya ɗora da cewa "Yanzu da mutum ɗaya ne ya fito ya nuna sha'awar fitowa takara sai mu goya masa baya, idan kuma sama da mutum ɗaya ne suka fito sai mu yi primary election a cikinmu, a fitar da wanda ya fi cancanta." Jinjina kai ɗaya daga cikinsu yayi tare da cewa "Shi Ajmal ɗin an taɓa fira da shi a gidan tv kan ayyukan da yake yi ko siyasa zai yi, sai ya nuna cewa shi ba ɗan siyasa bane ba ya da ra'ayin siyasar. Amma na ji mamaki da aka ce zai fito takarar Gwamna." Shugaban jam'iyya ya ce, "Ta yiwu ya canza ra'ayinsa ne, amma tabbas mai girma Gwamna ya shaida mani cewar Ajmal Ibrahim Tafida zai yi rajista da jam'iyar mu." Bayan Amatullah ta kammala shan taea da biredin da Hafsat ta kawo mata ne ta tashi da niyyar su tafi, haka Hafsat ta lallaɓata akan ta sha lemun kwali da ta kawo mata, ganin ba ta matsa ya sa a ɗauka ta fara sha,wani shu'umin murmushi Hafsat ta yi mai cike da manufa. A nan gidansu Amatullah kuwa kasancewar karfe biyu suke tashi daga makaranta, kafin ta dawo gida ƙarfe biyu da mintuna ashirin ko talatin ta yi. Wasa-wasa har ƙarfe huɗu Amatu ba ta dawo gida ba, hankalin Ummanta ya tashi sosai, har ta kira Abba ta sanar da shi, ya nufi makarantar ta su amma ba ta nan ba kowa sai mai gadi, kuma ya tabbatar masa da cewa ƙarfe biyu dai-dai kowa aka tashin. Ya koma gida ba ta nan ga shi ba ya bari ta riƙe waya. Abba ta na nan tsaye a ƙofar gidan da misalin ƙarfe biyar na yamma wata danƙarareriyar mota ta yi parking a ƙofar gidan.Mallam Abdullahi ne ya zubawa motar idanu yana tunanin me ya kawo motar nan ƙofar gidansa, mamallakin motar ne ya bude murfin motar ya fito yana kallon mahaifin Amatullah. *Daga alƙalamin*✍️ Zainab Abdullahi KNT (Maman Ihsan) Love you oll😍😘 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LrTZNGwF35IKXX4sLRvFug 🤦‍♀️ *ƳAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Dedicated to *JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION* *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubucirsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *BISMILLAHI RAHMANI RAHIM* Page5️⃣&6️⃣ Mamallakin motar ne ya buɗe murfin motar ya fito yana kallon Amatullah. Ƙarasawa ya yi a gabansa cikin girmamawa ya durƙusa ya gaishe shi bayan ya masa sallama, amsa wa yayi ba yabo ba fallasa. Shiru yayi ya rasa ta ina zai fara, Mallam Abdullahi ya kalle shi ya ce, "Yaro me ke tafe da kai?" Ɗan jim yayi sannan ya kalli Mallam Abdullahi ya ce, "Baba ina fatan kai ne Baban Amatullah." Gabansa ne ya faɗi ya kalli Munnir da sauri ya ce, "Eh ni ne mahaifinta me ya faru da ita?" Munnir ya cigaba da cewa "Dama na zo ne ina neman izininka idan ka yarje mani zan zo wajenta ko Allah zai sa mu fahimci juna." Shiru Mallam Abdullahi ya yi sannan ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ina ka haɗu da ita?" Nam Munnir ya bashi labarin ranar da suka haɗu da Amatullah, har ya dauko ta mota ya aje ta a ƙofar gida. Nam Mallam Abdullahi ya fahimci cewa shine ranar ya ajiye Amatullah a ƙofar gida, ranar da ya mata faɗa akan shiga motar saurayi. "To yanzu ita nake nema ko kana da masaniyar inda take, dan ba ta taɓa daɗewa irin na yau ba." "Daga ina kenan Baba?" "Tun safe da ta tafi makarantar boko ba ta dawo ba, kuma yau ƙarfe biyu suke tashi." "To Bana an tamabaya a makarantar an tabbatar ta shiga makaranta? Ba wani abu bane ya faru wanda ya sa ba ta samu ƙarasawa makarantar ba?" "Ban bincika ba sai dai na san da wani abun ne ya faru da ita da na sani." Ajiyar zuciya ya yi tare da cewa "Allah ya sa tana lafiya" Mallam Abdullahi ya amsa da Amin. Daga nan Mallam Abdullahi ya cewa Munnir ya tafi kawai shima gida zai shiga. Munnir yayiwa Mallam Abdullahi sallama ba da son ransa ba ya tafi. A can ɓangaren Amatullah kuwa tunda ta sha lemun kwali da Hafsat ta kawo mata sai ta ɓingire da barci, ba abinda take sai barci Hafsat ma kwalbar codolin ta ɗauka ta fara sha. Dukkansu barci suke har ƙarfe huɗu na yamma Amatullah ta farka daga barci. Mamaki ne ya kamata yadda ta tsinci kanta a wajen duk da ta san cewa sun zo wajen. Agogon hannunta ta kalla ta ga har ƙarfe biyar na yamma ta yi. Da sauri ta tashi ta na kallon kowa dake kwance a falon sai barci suke, kalle-kalle ta fara yi ta hangi wata ƙofa kamar ta toilet, ƙarasawa ta yi wajen kofar a hankali ta tura ƙofar toilet ɗin ta shiga. Alwala ta ɗauro ta fito idanunta ji take duk sun mata nauyi, sosai ga kanta da take jin sa wani iri. A haka dai ta gabatar da sallar azahar da la'asar cikin wani irin yanayi da bata taɓa jinta a ciki ba. Tana idar da sallar ne sai ta ta miƙe a hankali kanta na juyawa ta tashi ta kama tafiya ba tare da ta ɗauki jakkar makarantarta ba ta nufi hanyar fita. A bakin titi ta tsaya ta tara mai keke napep ta sanar da shi unguwar da zai kai ta. Shiga ta yi suka fara tafiya har ƙofar gida ya sauke ta, fita ta yi ta fara tafiya ba tare da ta ce masa komai ba, fita yayi a guje ya bi bayanta tare da shan gabanta. "Tunda ba tsohonki bane ya siya mani ai sai ki kuɗi." Kallonsa take kamar wata sokuwa ta ce, "Kuɗi?" Hannu ta saka a cikin aljihun wandonta ta fito da kuɗi naira ɗari ɗari biyar da Annabta ya bata ta miƙa masa. Karɓa ya yi tare da yin tsuki ya juya yayin da ta fara takawa za ta shiga gida. Kiciɓis ta yi da Abbanta dake tsaye a ƙofar gida, kallonsa ta yi tare da cewa "Abba ina wuni." Ta durƙusa har ƙasa tana gaishe shi. Bai amsa mata ba ya koma cikin gida, Umma na ganinsa ta ce, "Mallam lafiya ka dawo yanzu ko ka gan..." Kafin ta ƙarasa ta ga Amatullah na shigowa gidan. Kafin ta yi magana ne ta ji muryar Abba yana magana da kakkausar murya "Daga ina kike?" "Abba daga gidan ƙawata na..." Saukar marin da ta ji ne ya sa ta haɗiye sauran maganar, dafe kumatunta ta yi tare da zubewa wajen . "Amatullah yaushe kika fara wannan ɗabi'ar? Har za ki tashi daga makaranta ki biya gidan wata ƙawa ba tare da sanin mu ko izinin mu ba?" Sai gabanin magrib za ki dawo duk kin bi kin tayar muna da hankali?" Ɗaga hannu ya yi da niyyar sake kai mata duka Ummanta ta yi saurin tarewa tana bashi haƙuri. Fita ya yi a fusace. Ummanta ta ja hannunta ta kaita ɗaki tana rarrashinta tare yi mata nasiha da nuna mata kura-kurenta. A daren ranar ya dawo ya yi sallama Mallam Abdullahi ya fita, ya ga she saurayin ɗazu ne ya dawo. Cikin girmamawa Munnir ya gaishe da Mallam Abdullahi, ya amsa masa cikin sakin fuska, dan Munnir ya burge shi yadda ya fara zuwa neman izini a wajensa kafin ya zo wajen 'yarsa. Mallam Musa ya nuna masa cewa yanzu yarinyar karatu take yi, amma ya nemi amincewar Amatullah idan ta aminta da shi to shi bai da matsala. Dan haka yanzu ya je idan ya sake dawowa Sai su gana. Godiya ya masa tare da sallama ya tafi, dan a ransa ya so ganin Amatullah. A cikin sati biyu Hafsat ta mayar da Amatullah 'yar shaye-shaye, dan gaba ɗaya ma ta daina zuwa makarantar boko da islamiyya. Idan Hafsat ta dauke ta d zummar zuwa makarantar sai ta wuce da ita wajen shaye-shayensu sai lokacinn tashi yayi sannan sai ta dawo. Wata ranar asarar ce bayan ta fita gida da sunan za ta je islamiyya, Ummanta na neman biro za ta rubuta wasu lambobi da ta ji a gidan redio. Tana cikin neman biro ne ta ji wasu abi a leda, a hankali ta ciro abun tare da ajiyewa a gefe, kwancewa ta yi tare da dubawa. Zaro idanu Umma ta yi cikin mamaki tare da sakin ledar tana furta "Inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un"." *Na daina yin dogon typing tunda baku yin comments, wasu da ba sa cikin group ɗina ne suke mani comments na. Dan haka ba zai yiwu na ajiye abinda nake ina maku typing amma godiya na minti ɗaya ya gagare ku ba. Idan kun canza za ku ga canji yawan comments yawan readmore* *Maman Ihsan ce*✍️ Love you oll😍😘 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z 🤦‍♀️ *ƳAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Dedicated to *JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION* *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubucirsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *BISMILLAHI RAHMANI RAHIM* Page7️⃣&8️⃣ "Inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un, kar dai a ce yarinyar nan ita ke shan waɗannan magungunan? To me suke yi a cikin jakarta?" Tunani ta shiga yi a hankali ta fara tunanin tabbas ɗabi'un Amatullah sun canza, ba irin tarbiyyar da suka ba ta ba ne, yanzu idan ta fita ba ta dawowa gida akan lokaci. Ko makaranta idan ta tafi ba za ta taɓa dawowa a cikin lokaci ba. Duk sanda aka tambaye ta ina ta tsaya sai ta kawo wani uzurina yarda da ita ne ya sa duk uzurin da ta kawo take yarda da shi. Ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ta tuna kwanan nan Amatullah ba ta da wani aiki sai dai barci, ada ita ke dukkan aikin gidan nan amma yanzu barci ma ba ya bari ta yi aiki. Kenan shaye-shayen da take ne ke sanya ta yawan barci? Kwalbar Benelin ta ɗaga da Tutolin sune a ciki. Sallamar Mallam Abdullahi ta ji tana zaune dirshan ta kasa amsawa. Jin shiru ba'a amsa sallamar ba ne ya sanya shi cewa "Ba kowa a gidan ne?" Sai a lokacin ta buɗe baki ta amsa sallamar kallon ƙofar ɗakin Amatullah ya yi jin daga can muryar Umma ta fito. Jin muryarsa ta yi ya na cewa "Umman Amatullah lafiya kuwa ko ba ta tafi islamiyya ba ne?" Cikin sanyin jiki ta fito daga ɗakin hannunta riƙe da kwalaben maganin ta miƙa masa, kallon hannunta da take miƙa masa maganin. "Me ye a cikin ledar ne?" "Karɓi ka duba daga cikin jakar makarantar Amatullah na gansu." Da sauri ya karɓar cike da fargaba, dan yadda ya ga yanayin Umman ta saka jikinsa jin wani iri. Kwalaben ya ciro ya duba salati ya saka tare da nufar ɗakinsa ya kasa magana. Yana ƙoƙarin shiga ɗaki ne ya ji sallamar Fadila ƙawar Amatullah, tana sanye da kayan makaranta. Tsayawa ya yi suka gaisa dan ya san Fadila da Amatullah. Fadila ce ta ƙarasa ta gaida Umma. "Ina wuni Umma?" "Lafiya lau Fadila ya su Umman ta ki?" "Suna lafiya lau Umma." "Ma sha Allah haka ake so, na ganki sanye da kayan makaranta daga makarantar kuke kenan ko?" "Eh ai ni kaɗai ce." "Ina ita Amatullah take ba'a tayar da su ba ne? Ai na ɗauka ajinku ɗaya." "Eh Umma ajinmu ɗaya sai dai ban gane inda maganar ki ta dosa ba ne , na ji kina tambaya ta Amatullah ne?" Kallon rashin fahimta Fadila

Chapter 2 of 51