Share this page
ce ta shafi d'ansa, ko da kina gidansa yana wilakanta maki yaro ranki ba zai so ba sai ma idan kin haifa masa nasa na kansa lokacin za ki ga banbanci sosai Wanda zai dinga nunawa yaran Wanda ke Kuma Hakan zai musguna maki, wata kila ma ya hana ki rayuwar farin ciki. Kuma da dukkan alamu bai yarda dake d'ari-bisa d'ari ba har yanzu yana zagin ki Wanda hakan zai iya haifar maku da babban gib'i a cikin rayuwar farin ciki da za ki yi a tsakanin Ku. Don haka ki yi tunani auren Munnir ba zai zame maki farin ciki ba ki watsar da shi kawai don bai san kaddara ba, Kuma kaddara musulmi take ci idan ta ci kafiri ta gida." Girgiza kai Amatullah ta yi ta Kalli Fadeela ta ce. "Idan ban auri Munnir ba duniya za ta zage ni shima zai ce na yaudare shi tunda shi ya fara neman aure na bugu da Kari Mahaifina ya mashi alkawarin bashi aure na, Kuma wallahi Abba ba zai fasa ba idan ya Fadi maganar ba ya canzawa, Hakan ya saka da Ajmal ya fito mani da zancen zai aure ni ban amsa masa ba na ce masa ina da Wanda zan aura. Tsorona d'aya su taba ni da yaron nan, don shima Ajmal ya taba fad'a mani cewa da ransa da lafiyarsa ba Mai rike masa d'ansa, nima ba na son rabuwa da shi wallahi ina don yarona Fadeela." Ta k'arasa maganar tana kuka, nan Fadeela ta dinga kwantar mata da hankali har ta saki ranta. Wayarta ce ta yi ruri ta duba sai ta ga Ammi ce, don dama kullun sai sun yi waya ta ji lafiyarta da lafiyar Khalifa, Jin muryarta kamar tayi kuka ya sa Ammi tamabayarta, ta nuna mata cewa ba ta Jin dad'i. "Subahanalilahi kema ba lafiya shima babu?" Gaban Amatullah ya Fadi ta ce. "Ammi waye ba lafiya?" "Ajmal bai fad'a maki ba ne da ya zo, ga shi Kuna kusa?" Shiru ta yi tare da cewa "Ya fad'a mani Ammi yanzu yana ina ne?" "Yana hotel din da muka sauka da muka zo kawo ki." "Okay Ammi ko za ki tambaye shi lambar d'akin da yake ka da ki fad'a masa ni na tamabaya please." Shiru Ammi ta yi sannan ta ce. "Okay ina zuwa." Daga nan ta katse wayar , Fadeela ta tambaye ta da cewa. "Me ya saka baki son ya sani?" "Idan ya sani ba zai fad'a ba, fushi yake da ni ko kira na baya yi tun da ya tafi wai don na ce me ya saka yazo." Dariya ta yi tare da cewa "Yana da gaskiya mutum ya bar wata kasa ya zo wajenki ko gidansu bai zi ba sannan baki fad'a masa kalma Mai dad'i ba?" ",Hmm zan biya na gaishe shi amma ba zan shiga ciki ba " Ammi ta kira ta ta sanar da ita lambar d'akin, sannan suka ciga da fira ta tafi bayan sun ci abinci. Har wajen napep Fadeela ta raka ta bayan ta shiga ne ita ma ta koma gida. A bakin hotel din mai napep ya yi parking, ta sallame shi ta fito, kai tsaye ta nufi ciki gabanta na faduwa. Munnir ne tare da wasu samari su biyu d'aya na d'auke da jakkar kaya, da alama ya rako su kama masauki ne, ganin Amatullah ya sa shi mamaki, don sai da ya kalle ta da kyau tare da bin bayanta, zuciyarsa na masa zafi. Kai tsaye ta k'arasa wajen d'akin tare da yin knocking. Ajmal dake zaune ya jinginar bayansa da jikin kujerar da yake zaune, idanunsa a lumshe kamar Mai barci ya ji ana knocking, tashi ya yi ya k'arasa Jikin k'ofar tare da kai idanunsa inda zai hangi Wanda ke tsaye jikin k'ofar, ganin ta ba karamin mamaki ya bashi ba don bai yi tunanin zuwanta ba. Kasancewar daga shi sai singileti da Wanda 3quater ya sa shi shigewa cikin bedroom, jallaniya ruwan coffee Mai gajeren hannu ya saka sannan ya nufi falo ya zo ya bude mata k'ofar, kallonta ya yi yana mamaki sannan ya Kalli bayanta sai dai bai ga kowa ba don Munnir lekenta yake yi bai shigo kwantar dakunan dake wajen ba. Cikin muryarsa da yanayin rashin son magana ya ce mata "Bisimillah." Kin shiga ta yi tare da girgiza masa kai tayi alamar a'a. "Ba sai na shiga ba na zo ne kawai na duba ka da jiki." Tayi maganar tana kallon cikin idanunsa, karaf suka hada idanu da sauri ta sunkuyar da kai saboda wani irin kwarjinin dake cikin idanunsa. Bi tashar TASKAR MAMAN IHSAN a WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z 🤦‍♀️ *'YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) Page8️⃣2️⃣ Tayi maganar tana kallon cikin idanunsa, karaf suka hada idanu da sauri ta sunkuyar da kai saboda wani irin kwarjinin dake cikin idanunsa. "Ba ni yarona na gansa idan ba za ki shigo ba sai ki tafi" "Na tafi na barshi wajenka idan ya yi maka kuka fa?" "Sai na nemo masa Madara tunda kina tsoron ki shigo na cinye naman jikinki ko?" Jin haka ya sa ta kokarin shiga d'akin yayin da ya matsa mata ta shiga sannan ya rufe k'ofar. Zama ya yi a Saman kujera Mai zaman mutum d'aya yana kallonta yadda duk ta ki sakin jiki kamar wacce zai ce ke ta ruga a guje. Ita Kuma ba wai don tana tunanin zai cutar da ita ba ne sai dai tana duba rashin dacewar abunda ta yi ne a ce ta biyi shi hotel har cikin d'akin da yake daga shi sai ita bai dace ba. Daga kai ta yi ta kalle shi ta shima kallonta yake dan haka ta sunkuyar da kanta ta saka hannu cikin hijabin jikinta ta kwance zanin goyon, bayan ta ciro Khalifa daga bayanta ne ta k'arasa inda yake zaune ta mika masa yaron. Karb'arsa ya yi fuskarsa d'auke da zallar farin ciki, don yana Jin son dansa har cikin zuciyarsa, murmushi ya sakar masa tare da sumbatar goshinsa sannan ya rungume yaron a k'irjinsa. Dubansa ya maida zuwa ga Amatullah da ta yi tsaye ta kasa zama, zuciya da sak'e-sak'e har ta fara tunanin yanzu yadda daga shi sai ita idan ya tarihi ya maimaita kansa fa, wancan karon tsatsauyi ne da makircin muguwar k'awa wannan karon Kuma ai ganganci ne. Kallonsa ta yi ta ga sai d'aukar Khalifa photo kawai yake yi, sannan ya fara masu selfie tare. Ba ta San lokacin da ta saki murmushi ba ta na Jin dad'in yadda yake masifar son yaron da kula da shi, duk da cewar ba ta hanyar da ta dace ya bi ba wajen Samar da yaron amma yadda yake nuna masa so da kauna ko Dan da ya haifa na Sunna iyakacinsa kenan. Wasa yake yi da yaron sosai kamar wani babba, har ta fara tamabyar kanta Anya akwai alamar rashin lafiya a tattare da mutumin nan kuwa. Dan gaba d'aya sai nishadi yake yi, tana tsaka da tunanin ta ji muryarsa yana cewa. "Khalif tunda na kalle ka sai na ji na warke daga rashin lafiyar da nake yi, kamar dama kai ne maganin cutar dake damuna." Ita dai ba ta ce komai ba sai kallonsu take yi kuka har lokacin ta kasa zama, ganin yadda ta ki yarda ta zauna ne ya saka shi kallonta tare da cewa. "Karbe shi bari na shiga na yi wanka sai na mayar da ku gida." Shafar fuskar Khalifa ya yi kafin ya sake cewa. "Mom d'inka tsoron Dad d'inka take yi ka taba ganin inda Hakan ta faru?" Yana maganar yana kallon Khalifa kamar yana magana da wani babban mutum. Hannu ta mika masa alamar ya ba ta yaron, tsayawa ya yi yana kallon hannunta fararen da zara-zaran yatsun hannunta da suka Sha Jan lalle. Ganin kamar ba zai bata yaron ba ne sai kallon hannunta da yake yi ne ya sa ta janye hannunta da niyyar mayarwa cikin hijabi, daidai lokacin da yake mika mata yaron. Karba ta yi ta rungume shi yayin da shi kuma ya nufi bedroom, ganin ya shiga bedroom ya sa ta zauna a d'aya daga cikin kijeran dake falon. Munnir kuwa daga inda ya labe yake kallon Amatullah da Ajmal ya bude k'ofar ta shiga ya rufo k'ofar ya sa shi hankalinsa tashi, dan sai ya sake dasa alamar zargin da yake mata acikin zuciyarsa, yana tunanin ai dama da walakin goro a Miya. Jin an dafa kafadarsa ne ya saka shi juyawa ya ga abokinsa ne da ya rako a hotel d'in, tambayar sa ya yi abunda yake neme ya nuna ba komai, don ba zai iya ya sanarwa kowa wannan zancen ba, da Kuma abunda ya shafi Amatullah a yanzu. Barin wajen suka yi zuciyarsa cike da bakin ciki . Amatullah na zaune rungume da Khalifa da ya fara barci ta ji k'amshin turarensa, daga kai ta yi tana kallon kofar bedroom d'in, karaf suka hada idanu duk da cewar idanunsa na sanye cikin farin gilashi ne,amma sai da idanuwansu suka sarke cikin na juna. Sanye yake cikin shadda gezner sky blue da hula nevy blue ya yi kyau Sosai, hannunsa daure da tsadadden agogo, sai bakin takalmi da ya saka. Ya yi matukar kyau Wanda kwarjinin sa da haibarsa suka Kara bayyana, ga tattausan sajensa sa da suka yi wa fuskarsa kawanaya sun kwanta luf sai sheki suke yi da dukar idanu. kallonsa take yi gana d'aya ta kasa d'auke idanunta a kansa. Yana tsaye idanunsa akan wayarsa da alama message yake rubutawa, gaba d'aya ta kasa d'auke idanunta daga kansa, Wanda har shi da kansa ya ji a jikinsa tana kallonsa, ba tare da ya kalle ta ba ya ce "Wannan kallon fa kamar za ki cinye ni." Kunya ce ta kama ta ganin ya kamata tana kallonsa, don haka ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsun hannunta. Karbar Khalifa ya ji tare da cewa . "Ka ga Mom d'inka tana ta kallona Kuma idan na ce mata muyi aure sai ta ce wai ba ta so na." Ya yi maganar yana kallonta sai ta tura baki tana kallon gefenta, sai ta ji muryarsa yana cewa. "Ni kuma ba zan taba bari ki tafi da d'ana gidan wani da sunan gidan aure ba, don ba zai yiwu a wulakanta mani yaro ba da gatansa, da raina da lafiya ta ba Wanda zai rike mani yaro, don wannan saurayin naki ba hankali ne da shi ba." Ita dai ba ta ce masa komai ba har ya nufi bakin k'ofar fita tana biye da shi a bayansa ta ji yana cewa. "Zan so ki amshi tayin soyayyar da na maki, domin ba wai ina alfahari ba ne amma a gidansa kawai na San za ki samu farin ciki ke da danki, ba Wanda zai nuna maki tattali ke da danki sama da ni, ko kadan ba zan taba ganin aibunki ba ko tunanin cewa wani ne ya Riga ni saninki a matsayin 'ya mace, saboda na San nine sanadi Kuma d'ana ne kika haifa zan kauna ce shi da bashi kulawa da tarbiya tare da sauran 'yan uwansa da zasu biyo baya ba tare da nuna banbanci ba, kema kanki rufin asirinki ne ba Wanda zai yi tunanin cewa ina Baban yaron da kika haifa Wanda na San za'a dinga kiransa da suna wadanda basu dace ba Kuma na San ba za ki so Hakan ba kiyi tunani na baki kwana biyu." Murmushin takaici ta yi tare da cewa. "Ba wani tunani da zan yi domin Abba ya Riga da ya yi wa Munnir alkawarin aure na, Kuma na San idan ya yi magana ba zai taba canzawa ba, nima ba zan iya bijirewa maganarsa ba, sai dai idan Munnir ne ya ce ya fasa aure na." "Kina son sa ne?" "Ko ba na sonsa dole na aure shi ko don halaccin da ya nuna mani a rayuwa, don haka tilas komai rintsi aure na da Munnir ba fashi." Kallonta ya yi tare da cewa. "Ko da Hakan na nufin bakin cikinki ne?" "Ko da Hakan na nufin mutuwa ta ce." Bai sake magana ba ya bude k'ofar d'akin ta shiga gaba yana binta a baya hannunsa rungume da Khalifa, bayan ya rufe k'ofar suka bar wajen. Sam ta ki yarda su jera sai tsayawa take yi a bayansa, kamar ba tare suke ba, ita Kuma ganin hotel ne ya sa take baya-baya don kar ayi mata mummunar fahimta, duk da cewar duk Wanda ya kalle su sai ya yi tunanin ma'aurata ne ganin baby a hannun Ajmal. Sai burge mutane suke yi saboda sun dace da juna sosai. Sai da ya bude mata murfin motar ta shiga sannan ya zagaya mazaunin direba ya zauna a gefenta, har lokacin yana rike da Khalil, da kanta ta mika hannu ta karbe shi, ta jikin mirror dake gefen motar ne Ajmal ya hango Munnir tsaye ya rungume hannayensa a kirji, kallonsu yake yi, tabbas Ajmal ya ganshi dazu bayan Amatullah in ta yi parking ya bude mata k'ofar, ya ga Munnir na lekensu yanzu sun fito ma yana kallonsu, shin bibiyar Amatullah yake yi saboda bai yarda da ita ba ko me Hakan ke nufi, tabe baki ya yi tare da yiwa motar key suka bar wajen. Ba gida suka nufa ba gani ta yi sun yi wata hanyar daban, daga kai ta yi ta kalle shi tare da cewa. "Ina za ka kai ni Kuma?" "Zan je na siyar da ke ne." Ya yi maganar ba tare da ya kalle ta ba idanunsa na kan hanya. Kallonsa ta yi za ta sake magana a karo na biyu ta ga fuskarsa a tsuke, Hakan ya saka ta ja bakinta ta yi shiru tana kallon iKon Allah. Bakin wani katafaren supermarket ya yi parking, bayan ya kashe motar ne ya kalle ta tare da cewa. ",Muje." Girgiza kai ta yi ba tare da ta kalle shi ba. "Ba abunda muke bukata na ga last week da ka zo ka Siya mana komai tun daga kayan abinci kala-kala har kayan sakawa da da duka wani abin da muke bukata daga ni har Abdallah,Kuma ko kwata bamu yi amfani da shi ba kada ka bata kudinka hatta tsarabar k'asar Qatar da Ummi ta yi mana ba muyi amfani da su ba, kayan kwalliya da tirareukan ma na rasa inda zan saka wasu. Bai sake magana ba ya fita ya barta a cikin motar, don ta San ba abunda ke cikin nan da za ta bukata Wanda bai Siya mata ba. Bayan wasu mintuna ya fito da ledoji masu kamar jaka guda biyu, kayan ciye-ciye ne kawai a cikinsu. Bayan motar ya bude ya ajiye suka kama hanya inda ya ji parking a wani wajen ta ga ya sake fita, tana kallonsa ya siye dankwala-fankwalan kaji guda uku aka zuba masa a Leda ya dawo ya ajiye a bayan motar, Jan motar yayi suka bar wajen suka kama hanya gida. Wayarta ce ta soma ruri inda ta duba ta ga Ummanta ne ke kiran wayar, dagawa ta yi inda Umma ke sanar da ita cewa yamma ya yi ya kamata su dawo, ta sanarwa Umman suna hanya. Ko da suka yi parking a k'ofar gidan suka ga motar Munnir, yana zaune cikin motar yana danne-danne a wayarsa. Ajmal ne ya Karbi Abdallah daga hannunta ya ce ta d'auki ledojin ta shiga da su, idan t dawo sai ta karbe shi. Har zata masa musu akan kayan da ya siyo sai suka hada idanu Wanda kaifin da ta gani a cikin idanunsa ya sa ta kasa ce masa komai ta fita, bayan ta fita ne ta bud'e bayan motar ta d'auki kayan sannan ta nufi hanyar shiga gidan, da niyyar idan ta dawo sai ta karbi Abdallah ta tsaya su gaisa da Munnir. Ashe hakan da ta yi ne ya yi masifar Sosa ran Munnir. Da sallama ta shiga gidan inda ta tarar da Umma a tsakar gidan ta gama shara, amsawa ta yi bayan Amatullah ta gaishe ta ne take tambayarta inda ta dawo da Leda, ba ta boyewa Umma ba ta sanar da ita komai duk da dai ta ga yanayain fusakarta kamar ba ta so ba. Sanar da ita ta yi Munnir na waje za ta je su gaisa ne ya sa ta daga mata kai sannan ta kai kayan d'akinta ta sake fita. Ta gefen Ajmal ta bud'e ta karbi Abdallah sannan ta masa godiya ya ja motar ya bar wajen. K'arasawa ta yi wajen Munnir tare da masa sallama, ciki-ciki ya amsa sannan ya fito suka k'arasa inda suke fira, kallonta ya yi bayan sun zauna Wanda ko gaisawar da take masa bai amsa ba ya jefo mata tamabaya. "Daga ina kike?" Ya yi maganar fuskarsa ba annuri tare da watsa mata wani irin Kallo *ADAMAWA* Kwance take a saman cinyar Marka sai kuka take yi ita dai Ajmal take son gani, hankalin Marka ba karamin tashi ya yi ba da Jin zancen, duk da tana son tattauna matsalar da Dad din Ajmal. "Kinga zan saka ya zo ki ci abinci dan Allah." Kuka ta saka "Wallahi ba zan iya cin komai ba waya sani ko yana wajen karuwar nan yar maye wacce ta ce ya mata ciki, wallahi idan ban gansa ba sai na kashe kaina.".. Tayi maganar da iya karfinta nan da nan hankalin Marka ya tashi. "Subahanalilahi kisan kai?" Waya ta d'auka tare da mika mata tana cewa. "Nemo mani lambar ja'iri Mai Kiran nasara. Akan me Zaki kashe kai akansa ai dole ya aure ki ko in dagawa ubansa nono." Lambar Ajmal Nihal ta lalubo ta danna masa kira har sau uku bai daga ba, nan da nan ta sake saka mata kuka tana cewa. "Bai daga ba Marka za ki rasa ni." "Subahanalilahi kiyi hak'uri sake kira." Gaba d'aya ta gama dagawa tsohuwar hankali don ta lura Hakan ne zaisa ta so abunda take so. Sai a karo na hudu ya d'aga daidai lokacin da ya koma d'akin hotel din. "Hello." "Yauwa Ajmal kana ina ne?" Mamakin tambayar ya yi tare da cewa. "Lafiya kuwa Marka." "Ba lafiya ka zo Adamawa goben nan idan ba so kake ka yi kisan kai ba." "Wane irin kisan kai ko dai kin fara rudewa ne da wannan tsufar taki?" "Kazo na fad'a maka?" "Ki fada mani abunda ke faruwa." "Idan ka zo ka gani." "Bana da lokacin zuwa k'asar ma zan bari zan tafi china ne." "Lallai ko me ye a gabanka ka ajiye ka zo." Duk yadda ya so fahimtar da ita ta kasa ganewa, don haka ya ce mata ba zai zo ba, daga nan ya katse Kiran wayar, ya barta cike da mamakinsa. Sake kiransa ta yi har sau biyar bai daga ba, daga karshe Nihal ta zuga ta wai ta sa Dad ya bashi umarnin zuwa gobe, ba zai tsallake maganar mahaifinsa ba. Nan ta kira Dad ta daga masa hankali wai ya bawa dansa umarnin zuwa ya same ta gobe, idan ba haka ba ran kowa zai baci, Hakan ya saka ya fahimtar da ita cewar Ajmal zai tafi k'asar china yana da tattaunawa da zai yi da kamfanin da yake da hannun jari na kera kayan amfani da wutan lantarki nan da kwana biyu zai je, ta ce ya zo yau ko gobe, duk yadda Dad ya yi ta fad'i dalilin Kiran ta ki fad'a. Dad ya kira Ajmal ya sanar da shi duk yadda za'ayi gobe ya tafi wajen kakarsa tana son ganinsa, baya iya jayayyaya da maganar mahaifinsa don haka ya amsa da to sannan ya katse Kiran wayar ransa a b'ace. Bi tashar TASKAR MAMAN IHSAN a WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z 🤦‍♀️ *YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) Page8️⃣3️⃣ Dad ya kira Ajmal a waya ya sanar da shi duk yadda za'ayi gobe ya tafi wajen kakarsa tana son ganinsa, don haka ya amsa da to sannan ya katse Kiran wayar. Mamaki ne ya kama shi akan wani dalilin ne zai saka tsohuwar nan ta saka shi gaba akan sai ya zo wajenta, me ma zai maata ne idan ya tafi wajen nata. Ki yayi gana d'aya ransa a jagule yake duk da bai San dalilin Kiran wayar nata ba, dole gobe ya bi jirgi ya isa garin Adamawa, Dan ba don komai ba sai don cika umarnin mahaifinsa. Jin ta yi shiru ne ba ta bashi amsa ba ne ya saka sake jefa mata tambayar a karo na biyu. "Daga ina kike?" "Daga gidan k'awata Fadeela" Ta bashi amsa ba tare da ta kalle shi ba. "Wace ce Fadeela?" "Ita ce ranar da ka fara gani na muma tare har ka rage mana hanya, dama tunda na dawo bamu hada ba na nemi izininka zuwa gidansu." "Yaushe kika da fara k'arya Amatullah?" "K'arya Kuma?" "Eh mana." "Me zai saka na maka k'arya?" "Saboda ba za ki iya fitowa fili ki fad'a mani cewa kin je hotel ne wajen masoyinki uban d'anki, to bari kiji ba wani ne ya fad'a mani ba da idanuna na ganki kin tafi har d'akin da ya kama a vip kin yi knocking ya bude maki ba, kika saka kafa kika shiga ya maida k'ofar ya rufe duk ina kallonku. Tsawon lokaci kuka d'auka a ciki Allah kadai ya san abunda kuke aikatawa sai da kika gama abunda kuke yi sannan kuka fito bayan ya ji wanka ya sauya kayan jikinsa, sannan kuka fito daga d'akin hotel din kuka shiga mota, kai tsaye supermarket kuka nufa kafin ya dawo dake gida ko ba haka bane?" Kallonsa kawai take yi fuskarta d'auke da mamaki yadda aka yi ya San ta tafi hotel, bibiyarta yake yi saboda bai yarda da ita ba ko me. Tana tsaka da tunanin ta ji muryarsa yana cewa. "Baki da abun fad'a ne?" Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa. "Tabbas haka ne amma ba yadda kake tunani ba ne, na bar gidan nan da niyyar zuwa wajen k'awata bayan na nemi izinin iyaye na. Daga can ne muna waya da Ammi mahaifiyar Ajmal take sanar da ni bai da lafiya, Hakan ya saka na je don na duba jikinsa kwata-kwata ban je da niyyar shiga cikin d'akin nasa ba, amma..." Katse ta ya yi ta hanyar cewa. "Amma me? Kina son ki fad'a mani ba ki yi niyyar shiga ba ya d'auke ki ya saka ko me? Amatullah ina son ki haka ina kishin ki Kuma duk lokacin da na tuna cewa ba ni ne na fara saninki a matsayin 'ya mace ba ina Jin zafin Hakan a zuciyata. Duk yadda kike na yarda zan aure ki saboda kaddara ce ta sa duk abubuwan da suka faru dake suka faru, amm ki sani ba zan iya jurewa ace ki cigaba da mu'amala da mutumin da kika ce abunda ya faru a tsakaninku tsautsayi da kaddara na ne, domin idan abunda kuka aikata a baya ya zama tsautsayi har kuka haifi wannan yaron to abunda kuke aikatawa yanzu Kuma fa shima tsautsayi ne ko son zuciya? Ba zan d'auki wannan abun ba ki sani tun yanzu gudun abunda ka iya zuwa ya dawo ." "Shin ba ka da hak'urin da za ka iya saurara ta ne ko me? Kana ta maganar da ta fito daga bakinka ba ka bani damar kare kaina ba ballantana ka yi mani uzuri. Kai a tunaninka fasik'anci muke aikatawa ko me?" Afusace ya ce. "To me kika je yi har hotel din karatu yake koya maki?" Ranta a b'ace ta ce. "Na gaji da Jin wadannan kalaman naka, kai kullun sai dai ka dinga zargina ko tuhuma ta? Na Sha fad'a maka cewa ni ban taba aikata fasik'anci ba wancan karon ma tsautsayi ne da Kuma rabon zuwan Khalifa a duniya kuka ba da son ranmu ba ne daga ni har shi na gaji da maimaita maka wanan maganar don ko karatu ne ya ci ace ka haddace su." Ta k'arasa maganar hawaye na gangarowa a Saman fuskarta, ganin hawayen nata ne ya saka jikinsa ya yi sanyi, cikin kwantar da murya ya fara mata magana. "Kiyi hak'uri ba wai ina nufi bata ranki ba ne, ki yi tunani ko ke ce a matsayina fa, ai bai dace a ce an ganki a hotel kin je wajen saurayi har d'akin hotel din da ya kama ba, Ku dauki mintuna ya fito bayan ya sauya kayan alamar ya yi wanka kenan Ku fito na ganku ya zan ji? Son ki fa nake yi da aure fiye da shekara ina dakon sonki a zuciyata lokaci d'aya kaddara ta yi mani yankan kauna. Ki yi hak'uri kin ji." Ya k'arasa maganar cikin sigar rarrashi. Goge hawayen dake fuskarta ta yi tare da cewa. "Ba komai zan shiga gida." Gyada mata kai kawai ya yi ba tare da ya sake yin magana ba. Sai da ta shige ciki sannan ya tashi cikin sanyin jiki ya nufi wajen motarsa ya shige,tayar ta moyar ya yi tare da barin layin. Ko da ta koma cikin gidan ba

Chapter 36 of 51