ga sunan Madina, cike da zumuɗi ta ɗauki wayar tare da sallama, inda Madina ke sanar da ita security sun hana su shigowa ta zo ta shigo da su.
Cikin zumuɗi ta ce .
"Ammi sun iso."
Murmushi Ammi ta yi tare da cewa ma sha Allah.
Daga nan ta mike ta nufi hanyar fita dan ta shigo da su.
Ko da ta ƙarasa gate ɗin tana ƙoƙarin fita security suka hana ta fita, dan ranar da ta yi niyyar guduwa da akwati Ajmal ya hana su bari ta fita, dan haka suka dakatar da ita, ranta ya ɓaci ta ce masu to idan ba zasu bari ta fita ba ga ƙawayrnta nan su biyu su bari su shigo, nan ma suka ƙi amincewa dan basu zo da shaidar da baƙin gidan ke zuwa da shi ba da zasu bari ta shigo. Ganin yadda suka ɗaure fuska suna sanye da baƙin glass ba mutunci ya sa ta juya baya za ta koma dan ta sanar da Ammi.
Ta ji horn da ƙarar buɗe gate, hakan ya sa ta juya dan ganin waye, duk da baƙin glass ne motar ta gane waye Sabida motar ne Ajmal ya dauke ta suka tafi guest house.
Tun daga nesa ya hangi wucewarta ya ɓata fuska ganin yadda duk maza ne a wajen kuma ba ta saka hijabi ba riga da siket ne na atmafa a jikinta, hakan ya sa ya ji wani iri a ƙasar zuciyarsa, bai bari Direba ya kai shi gate na biyu ba ballantana su ƙarasa ya sa suka tsaya daga nan.
Tsayawa ta yi ganin motar ta tsaya, Direba ta fito ya bude masa bayan motar, a hankali ya fara ziri da ƙafarsa ɗaya waje, kallon farin ƙafar ta yi ta gane waye kafin ya fito da ɗayar ƙafar.
Yana sanye da gezner ruwan coffee da hula broun sai takalminsa broun kanta a ƙasa tunda ta ga ya watsa mata wani kallon da ta ga kamar ransa ya ɓaci, duk da ba ta san laifin da ta masa ba, daddaɗan ƙamshin turarensa ne ya daki hancinta.
Kallonsa take damin Ajmal Allah ya yi masa kwarjini da cikar haiba.
Ƙarasowa yayi cikin takunsa irin na lafiyayyun maza.
"Me kike yi anan?"
Ya yi tamabayar fuskarsa ba walwala.
"Ƙawayena suka zo aka hana su shigowa."
"Shine kika fito a haka ba tare da kin saka hijabi ba bayan jin san duk maza ne anan ko?"
Shiru ta yi dan ita ba ta san me za ta ce masa ba.
"Ka da na sake ganin kin fito a haka ba hijabi a jikinki baki ganin sai kallonki ake yi ko? To ba na so duk za ki fito ki tabbar kin rufe jikinki Indai ba a cikin kike ba."
Jinjina kai kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba.
"Juya ki koma ciki?"
Kamar za ta yi kuka ta ce
"Dan Allah ka ce su bari su shigo."
"Wa kika sani a garin nan da har kika samu kawaye?"
"Lah ma'ikatan asibitinka ne fa, sune suka kula sani bayan an yi Mani tiyata an ciro Baby a cikina."
Dariya ta so bashi amma ya waske inda ta cigaba da cewa
"Ammi ta haɗa ni da su ranar suna suke duka daɓe Mani kewa."
"Koma ciki za su shigo."
Da sauri ta koma ya bi ta da kallo har ta shige, sannan ya kira daya daga cikin security ya ce yaran nan su shigo da aka hana su shiga.
Daga nan ya nufi ciki inda wannan security ya sanarwa wadanda ke bakin gate dan su bari ƙawayenta su shigo.
*Maman Ihsan ce*✍️
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
🤦♀️ *'YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
Ban yarda a karanta mani shi a youtube ko a maida shi audio ba tare da izinina ba.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Page6️⃣7️⃣
Daga nan ya nufi ciki inda wannan security ya sanarwa waɗanda ke bakin gate dan su bari ƙawayenta su shigo.
Bayan ya isar da saƙon boss ɗin na su ne ya dawo ciki, security da ke bakin gate suka yi wa Su Madina nuni da hannu alamar su shiga.
Da sauri suka shiga ciki, inda suke farin cikin haduwarsu da Amatullah.
Har lokacin Ammi da Nihal na dinning area suna cin abinci. Gaishe da ita Ajmal ya yi sannan ya haura upstairs.
Amatullah ta shigo cikin falon inda Ammi ta taso ta karaso falon, kallon Amatullah ta yi tare da cewa .
"Idan sun ƙaraso kai su dinning table su ci abinci ko?"
Jinjina kai ta yi tare da cewa.
"To Ammi."
Da sallama ɗauke a bakinsu suka yi shigo, inda Ammi da Amatullah suka amsa masu, gaida Ammi suka yi cikin girmamawa, ta amsa masu cikin farin ciki da walwala, sannan suka rungume juna da Amatullah.
Sun ina jin dadin ganin ta ita ma ta yi farin ciki sosai da ganin su.
Nan ta ja hannunsu zuwa dinning area, zama suka yi, har lokacin Nihal na zaune a wajen.
Gaishe ta suka yi ta amsa masu kamar ba ta son yin Magana. Tashi ta yi ta bar wajen gaba daya.
Nan suka zauna Amatullah ta ɗauki plate ta zuba masu abinci suka fara ci, sai da suka ƙoshi sannan ta tashi tare da cewa su taso su shiga daga ciki.
Bayan sun tashi ne ma'ikatan gidan suka zo suka tattara kayan da suka yi amfani da shi wata ta gyara wajen.
Ɗakin Amatullah suka nufa tana gaba suna bin ta a baya.
Nan suka dauki Abdallah da ke ta faman barci, Saliha ta lalle ta tare da cewa.
"Gaskiya ta kamata a san da cewa mu zamu zo gidan nan, dan kin ga wallahi ranar mun zo securitys suka hana mu shiga, sai yau da Musa samu lamabar wayarki muka kira, duk da haka na ga sai da suka jima kafin suka buɗe mana ƙofar.
Murmushi Amatullah ta yi tare da cewa.
"Nima ba su bari na fita ba hana ni fita suka yi."
"Saboda me suke hana ki fita?"
"Wai Ya Ajmal ne ya ce ka da su bari ba fit."
"Akan wane dalili?"
"Kwanakin baya na yi niyyar guduwa daga gidan ne?"
Madina ta kalle ta tare da cewa.
"A wane dalili ne zai sa ki gudu."
"Ina wacce kuka tana cin abinci, mun samu sabani ne na mare ta, sai na ji tsoron abinda zai biyo baya, ashe ma ba yadda nake tunani ba ne, ashe ƴar ƙanwar Dad ce."
Dariya suka yi inda Saliha take cewa.
"Na ga alamar yar rainin hankali ce ita, irin kallon da take mana."
"Share ta kawai."
Amatullah ta faɗa cikin son a kau da zancen Nihal.
Nan suka cigaba da fira har take nuna masu wayarta da Ajmal ya siya mata, nan suka taya ta murna, Saliha ta ce.
"Ƙawata anya ba sonki yake yi ba?"
"Me ya sa kika ce haka?"
Kawai dai na ga wayar nan mai tsadar gaske wanda sai a hannun wani da wani ake ganinsa."
Shiru ta yi kafin ta ɗora da cewa.
"Ba komai kawai dai ya ga bana da waya ce shi ne muka siya wannan."
Murmushi Saliha ta yi tare da cewa.
"A more lafiya."
Madina ce ta amsa da Ameen inda take cewa
"Ai ni so nake A ce yau ga ranar da Sir Ajmal ya aure ki, ba don komai ba saboda yaron da kuka haifa ya taso a gabanku ku rene shi ku bashi tarbiyya tare, hakan zai fi kyau gaskiya."
Saliha ta kalle ta tare da cewa.
"Kin mance halin mazan yanzu ne, idan har suka san mace a waje ba aurenta suke yi ba, saboda sun san komai na ta a waje ba su sha'awar aurenta, sai dai su nemi wacce ba su sani ba suna rawar jikin aurenta."
Murmushi kawai Amatullah ke yi ba tare da ta ce komai ba, ganin rabin hankalin Madina na kan waya ce ya sa Amatullah cewa .
"Wai me kike yi ne a waya?"
Ba tare da ta kalle ta ba ta ce.
"Na shiga social media ne ina ganin me duniya ke ciki."
"To ni ma a buɗe mani mana na shiga gari, kullun sai game kawai nake bugawa da wayar."
Saliha ce ta karɓi wayar tare da cewa.
"Bari na buɗe maki facebook da tiktok."
Nan ta buɗe mata facebook da tik tok, Amatullah ta nemi ta buɗe mata what's up. Shi ma ta buɗe mata shi, sai dai ba ta da contact da yawa lambar mutane hudu ne kawai a wayar, daga Ammi sai Ajmal sai Saliha da Madina. Dukkansu hudu suna what's up.
Bayan Saliha ta gama ta ba ta wayar ne suka cigaba da fira yaushe gamo. Amatullah ta ji dadin zuwan su sosai, duk rabin fitar ta su akan waya ne inda suke nuna mata abubuwa a social media. Sannan suka saka ta a wani group what's up inda za ta ƙaru.
Abdallah ne ya farka daga barci, nono kawai Amatullah ta bashi su Saliha suka dauke shi. Suna yaba tsabar kamannin da yaron ke yi da Ajmal kamar an tsaga kara. Madina ce ta kalle ta tare da cewa.
"Wai ƙawata waye ya siya maki wannan tsadaddiyar waya haka?"
"Ya Ajmal ne ya siya mani ita?"
Ta yi maganar ba tare da ta lalle ta ba tana cigaba danna wayarta. Saliha ta daura da cewa.
"Amma gaskiya na yi mamaki da kika ce ba soyayya kuke ba."
"Eh ba soyayya muke ba sai dai ta nemi na amince na aure shi ni ce ban amince masa ba."
Tare suka haɗa baki wajen cewa.
"Saboda me?"
Murmushi kawai ta yi inda Saliha ta ce,
"Amma kafin bani haushi wallahi, ta yaya handsome man irin Sir Ajmal ya ce zai aure ki har kuma ƙi amincewa? Wani abu kike so a wajen ɗa namiji wanda ba ya da su, Sir Ajmal yana da kyau, yana da ƙira mai kyau, yana da haiba da cikar zati irin na ɗa namiji, uwa uba ga dukiya Allah ya bashi, abun so ne ga kowace mace, duk mace mai hangen nesa za ta yi fatan babu macce da da zai je yana so ta ce a'a sai dai idan ta san cewa ba zata same shi ba shi ne za ta hada da ba ta so.
Taɓe baki Amatullah ta yi tare da cewa.
" Ra'ayin ki kenan, amma ni kam ba na ra'ayin aurensa, hasalima ban saka shi a cikin raina ba, domin ina da wanda zai aure ni, kuma iyayensa sun san da zancen auren Abbana ya bashi izinin zuwa waje na zance. Kin ga idan na ce zan auri wani ba shi ba na yi masa butulci."
Madina ce ta jefo mata wata tambaya
"Ina kuka haɗu da shi?"
Ɗan jim Amatullah ta yi tare da cewa.
"Wata rana ana ruwan sama ya rage muna hanya ni da ƙawata. Bayan kwana biyu ya zo ya damu Abbana da zancen aure, daga nan Abbana ya bashi izinin shigowa ciki domin zance muna cikin haka ne wannan ƙaddara ta same ni."
Jinjina kai Madina ta yi tare da cewa.
"To bayan ya samu labarin cewa kin yi ciki har kin haihu zai iya aurenki a haka kuwa?"
."Ba na da masaniya ko zai iya aurena,
"To kin gani ko, ba ki da tabbacin zai aure ki. Ko da zai aure ki gara kin auri uban ɗan ki ku ba shi tarbiyya tare kuma shi ne kadai zai iya kuka da shi ba tare da ya aikata maku wani abu da zai tabbatar da cewa ɗan ba ubansa ba ne, kuma ba za ki fuskanci ƙalubale daga danginsa ba.
Nisawa ta yi kafin ta daura da cewa.
"Kuma a labrinki na ji kin ce wajen Mahifinki Munnir ya zo neman aurenki, bai fara neman soyayyar ki da amincewar ki ba idan kin anince za ki aure shi ba, kawai sai ya kama ƙafa da Abbanki , daga nan Abbanki ya bashi izinin zuwa zance, kina fita kuna zance ne kawai da umarnin Abba ba wai dan kina son sa ba, haka ne?"
"Waye ya sanar da ke cewa ba na son sa?"
Murmushi Saliha ta yi tare da cewa.
"Ba wanda ya faɗa na fahimci umarnin Abba ne kawai kike bi."
"Hmmm to ai Munnir ɗin ma ba baya ba, yana da nagarta da mace za ta so shi."
Tana magana Idanunta na kan waya ta shiga facebook, kwatsam sai ta yi arangama da photon Munnir a profile na shi na facebook, ba ta san lokacin da ta kira sunan Saliha da ƙarfi ba, tana cewa.
"Lah kin gan shi nan!"
Da sauri suka matso dab da ita suna tambayarta akan me take magana.
"Kun ga muna maganarsa sai ga shi na gani photonsa a facebook."
karɓa suka yi suka duba photon,inda Madina ta ce.
"Ashe kina da gaskiya shi ma da gaskiya ya haɗu sosai wallahi,sai dai idan kika haɗa shi da Sir Ajmal za ki ga bai kama ƙafar Ajmla ba a wajen kyawu da haɗuwa."
Saliha ta ɗora da cewa.
"Tabbas ya hadu sosai duk inda namiji ya kai shi ma ya kai, sai dai idan kika kalli Sir Ajmal kika kalle shi za ki ga bai kai can ba. Amma a wajen da ba Ajmla kam ya haɗu maƙura."
Karɓar wayarata ta yi tare da cewa.
"Ku dai kuka sani, amma ni kam ya Mani a haka."
"To ai ba kushe shi muka yi ba kuma mun san ya yi Allah ya zaɓa maki mafi alkhairi a cikinsu."
Daga nan ta tura masa friend request. Nan suka cigaba da fira inda ta kawo masu kayan ciye-ciye da drinks acikin fridge ɗinta da ke cikin ɗakin.
Suna ta cin snack kenan sai ga Affan ya shigo cikin ɗakin, Madina ta kalli Affan ta ce.
"Da alama ɗan sir Ajmal ne ko?"
Amatullah ta kalle shi tare da sakar masa murmushi ta ce.
"Eh ɗansa ne."
"Na ga yana kama da Dad ɗinsa, sai dai ba sosai ba Abdallah ya fi daukar kamanninsa."
Amatullah ta mikawa Affan hannu ya karaso wajenta ta ce.
"Ka dawo daga school ɗin ne?"
"Eh Anty Dad ya ce a kawo Abdaiya."
Dariya suka saka gaba ɗaya yadda maganarsa ya ke fitowa, wato Abdallah shine ya ce Abdaiya."
Amatullah ta ce ,
"Ina Dad ɗin?"
"Yaya fayo ya janna ya ce a kawo Baby."
"Okay gani nan zan kawo shi."
Affan ya fara saka mata kuka da rigima shi dole sai an bashi Abdallah.
"Anty kawo ci jan kai ci."
Saliha ta ce
"shekarun yaron nan nawa?"
Amatullah ta ce.
"Na ji an ce shekarunsa huɗu."
Ta yi maganar tana dirowa daga kan gadon. Hannunta riƙe da Abdallah ga kuma Affan na kuka, hakan ya sa ta ce.
",Muje idan na bude maka ƙofar sai na baka shi ko?"
Suna isa bakin Kofar ta mika masa babyn duk da Saliha sun hana ta haka ta bashi ya kaiwa Ajmal.
Tana kallonsu ganin yadda ya rike babyn da kyau yana tafiya ta bar shi ya tafi.
Ajmal na zaune ababban falon gidan yana jiran Amatullah ta kawo masa Abdullahi,aka kawai sai ya ji Muryar Affan na cewa.
"Dady Dady ga ci."
Juyawa ya yi dan ganin mad Affan ke cewa, sai ya yi arba da Affan na dauke da Abdallah.
Zumbur ya mike da sauri zuciyarsa cike da fargabar kada yaron ya faɗi.
Karɓar yaron ya yi idanunsa har sun kadaita inda yake cewa.
"Affan waye ya yi kasadar ba ka yaron nan?"
Dan shi a tuninsa Amatullah ba za ta yi gigin ba shi yaron ba, sai dai ko baƙin da suka zo wajenta, abun mamaki sai ya ji Ajmal na cewa.
"Anci ta bani Baby."
Kallon mamaki yake masa jin me yake cewa, rungume babyn ya zauna kan kujera, Affan ma ya zaune gefensa yana kallon Baby.
Wayarsa ya ɗauka tare da lalubo lambar Amatullah ya sannan ya danna mata kira.
Amatullah suna nan suna firar su wayarta ta yi ringing, ta dai san sabon layi ne, ba wanda ya san lambar sai Ajamal dan haka sai tayi tunanin shi ne.
Ɗauka ta yi tare da cewa.
" Assalamu alaikum."
Daga can ɓangaren ya dauka tare da cewa.
"Wa'alaikumus Salam, kina cikin hankalinki kuwa? Ta ya ya zaki ɗauki baby ki bawa Affan? Yanzu idan ya faɗi ko ya faɗar da shi da? Me za ki ce? Ko da yake dama ba ƙaunarsa kike ba ba ki damu da yaron ba shi ya sa kika ɗauka kika bawa Affan, ko me zai same shi ba ruwanki ko? To ba na son na sake ganin shi kin ɗauka kin bashi dan bai da wayon da zai riƙe shi da kyau."
Kwantar da murya ya yi cikin sigar rarrashi ya dora da cewa.
"Please ki daina bawa shi ka da su faɗi kin ga jikinsa bai yi ƙwari ba kin ji?"
Shiru ta yi tana sauraronsa da ya fara faɗa yanzu ya dawo yana rarrashin ta, jinjina kai ta yi tare da cewa.
"Ba zan sake ba in sha Allah."
"Yauwa na gode."
Ya faɗa tare da katse kiran wayar.
Sai yamma likis sannan su Saliha suka tafi gida.
Amatullah kuwa sai tana yawan tunanin halin da Hafsat ke ciki, ta tuna maganar da ta mata a waya, tana roƙonta gafara ta yafe mata. Sautin kukan Hafsat take jiyowa a kunnenta, inda Hafsat ke kuka tana cewa.
'Amatullah ki duba girman Allah da Manzonsa ki yafe mani'
Goge hawaye ta yi take sai ta ji zuciyarta ya karaya, da haka ta miƙa tsaye tare da zagaye ɗakin tana Safa da marwa. Daga karshe ta turawa Ajmal text message cewa tana son suyi magana mai mahimmanci.
Bayan ya ga sakonta sai ga reply ya mata cewa bayan sallar isha'i su haɗu a lambun dake cikin gidan.
Da yammacin ranar ita ta zo ta yiwa Abdallah wanka kamar yadda ta saba, tunda Amatullah ta bashi nono ya sha ta kwantar da shi ya cigaba da barci.
Har aka yi sallar isha'i bai farka ba, Amatullah ta fito zuwa dinning area, ganin anyi sallar isha'i ya sa sauri-sauri ta kammala cin abinci ta nufi lambun dake cikin gidan.
Zaune ta same shi a saman daya daga cikin kujerun da ke wajen.
Da sallama ɗauke a bakinta ta ƙarasa wajen, yana danne-danne a waya ya amsa mata sallamar ba tare da ya ɗaga idanu ya kalle ta ba.
Cigaba da danna wayarsa ya ke yi, ita kuma kallonsa kwai take yi. Jin ba ta da niyyar yin magana ne ya sa ya ɗaga kai ya kalle ta, karaf suka haɗa Idanu.
"Dama kallona kike yi?"
Kau da kanta ta yi gefe kamar ba kallonsa take yi ba.
"Kin ce kina son Magama da ni to ina jin ki."
Shiru ta yi dan ta rasa ta ina za ta fara, ta dauki tsawon mintuna biyu kafin ta fara magana.
Dama tun lokacin da muka yi magana da Hafsat a waya ne na shiga damuwa, saboda yadda na ji tana kuka tana roƙona akan na yafe mata, wallahi abin ya tsaya mani rai, ni na yafe mata shine kai ma nake roƙon..."
Kafin ta kai ƙarshen maganar da ta yi niyya ne ya dakatar da ita ta hanyar cewa
"Ka da ki fara cewa na yafe mata, domin ba ta cancanci yafiya ba sai na saka an hukunta da bisa laifin da ta aikata. Ke bari ma ki ji kotu zan saka a tura ta ta girbi abinda ta shuka."
Mai da hankali ya yi kan wayarsa ya cigaba da danne-danne.
"Kada ka manta ko Allah da ya halicce mu idan muka yi masa laifi muka tuba yana tafe mana, to me ya sa kai ba za...."
Katse ta ya yi ta hanyar cewa.
"Kin ga na sani, amma Hafsat ba ta cancanci yafiya ba, sai an hukunta ta daidai da abinda ta aikata, dan kotu..."
Saukowa ta yi daga zaune da take ta durƙusa kan guiwarta, ta fara magana tana cewa.
"Dan Allah ka da ka fita daga cikin salihan bayin Allah, masu godiya da duk ƙaddarar da Allah ya aiko masu da ita, mai kyau ko mara kyau, mai dad'i ko mara daɗi duk zafi da radaɗinta su haɗiye ta, ko ka mance cewa duk wani abinda ya samu bawa da sanin ubangijinsa ne?"
Nisawa ta yi kafin ta ɗora da cewa.
"Iya abinda yake rubuce cikin Ƙaddarar rayuwar Ka, Shine Iya abinda zai Same Ka. Masoyi Ko makiyi babu wanda zai iya sauya maka Komai."
Goge hawayen fuskarta ta yi sannan ta ɗora da cewa
"Ka yi haƙuri kuma ka yafewa waɗanda suka yi muka ba daidai ba, ana shiga Aljanna ne kaɗai da kyakkyawar zuciya."
Kallonsa ta yi da kyau kafin ta ɗora da cewa.
"Duk lokacin da ka shiga cikin tsananin wahala da kuma damuwa, kar ka manta da abubuwan nan guda bakwai
1. Ka tuna cewa Jarrabawa ce daga Ubangininka, wanda yafi kowa Sonka da Kaunarka.
2. Ka tuna cewa Ubangijinka yayi maka haka ne don ya Kankare maka Zunubanka, ko kuma ya d'aukaka maka darajarka.
3. Ka tuna cewa an jarrabi Annabawa da manzanni da Salihan bayin Allah wadanda suka zo kafin ka.
4. Ka tuna cewa tun kana cikin mahaifiyarka kafin ta haifeka an riga an rubuta maka duk abinda zaka samu aduniya, da kuma dukkan abinda zai same ka. Mai dadi ko Kishiyarsa.
5. Ka tuna cewar rungumar ƙaddara kowacce iri, yana daga cikin ginshikan Imaninka. gwargwadon yadda kake rungumar ƙaddara, gwargwadon haka imaninka yake.
6. Ka tuna cewar kowanne tsanani yana tare da sauki guda biyu. (Ga lada, ga kuma yayewar tsananin).
7. Ka tuna cewar Allah shine ARHAMUR RAHIMEEN (MAFI TAUSAYIN MASU TAUSAYI) kuma yafi komai kusa dakai, Kuma yafi kowa tausayinka. Kuma zai amsa dukkan rokonka.
Ya ALLAH ka yaye mana dukkan tsanani don hasken Alqur'aninka, don rahamar nan taka wacce ta yalwaci dukkan halittunka (saw)"
Daga nan ta tashi ta koma ta nufi hanyar fita daga lambun Idanunta na zubar da hawaye,ita kanta ya ji ciwon abinda ya faru da ita amma ta fauwalawa Allah lamuranta.
Jikinsa ne ya yi sanyi da kalamanta, dan tabbas gaskiya ta faɗa amma sai ya kai zuciyar sa nesa kafin ta aikata haka. A cikin zuciyarsa cewa ya yi.
'Haƙiƙa kin cika mar'atussaliha ke abun so ne ga kowane namiji, dan duk namijin da ya same ki a matsayin matar aure ya yi Sa'a a rayuwarsa.'
Murmushi ya yi shima ya tashi ya bar lambun.
A wanann dare kowannensu ya kwana da tunanin juna, ita ta kwana tana addu'a Allah ya da ya amince ya sa a saki Hafsat da aka kama.
Shi kuma ya kwana da tunaninta da kalamanta masu tsayat a rai, tabbas zai so a ce ya mallaki Hafsat a matsayin matar aure a gare shi, sai dai har yanzu taƙi amincewa da buƙatar sa, duk da dai bai san dalilinta ba amma ya tabbata komai ta aikata tana da dalilinsa.
Washegari da sassafe Munnir ya shirya tafiya zuwa Kaduna. Inda ya dauki abokinsa Sadik dan ya raka shi, zuciyarsa tam da farin ciki ya san idan ya sanarwa Hafsat cewa iyayenta sun yafe mata za ta dawo gidan, kuma ya san cewa Ummanta za ta yi farin ciki.
Su biyu suka kama hanyar Kaduna, da motar Munnir suke tafi, inda Sadik ke driving.
Bayan sun isa garin Kaduna, duk yadda Sadik ya so su kama hotel su ci abinci su yi wanka kafin su tafi, amma fir Munnir ya ce bai san zancanka, dole sai ya ga Amatullah kafin komai.
Sadik na da aboki a Kaduna dan haka ya kira shi dan ya yi masu jagoranci zuwa gidan.
Suna zaune a mota abokin Sadik mai suna Hashim ya karaso inda ya same su suka gaisa. Bayan sun gaisa Munnir ya kalle shi tare da cewa
"Dan Allah ko ka san gidan Ajmal Ibrahim Tafida?"
Dariya Hashim ya yi tare da cewa.
"Garin nan waye bai san shi ba, ai sanannen mutum ne ba ɓoyayyen mutum ba."
Jinjina kai Munnir ya yi tare da cewa.
"Ma sha Allah, can gidansa za ka kai mu?"
"Okay b damuwa."
Daga nan ya masu jagora zuwa gidan.
Tun daga nesa suka hangi gidan da da ke zagaye da security.
Bayan sun yi parking ne suka fito su duka.
Ƙarasawa suka yi wajen security, bayan sun gaisa ne Munnir ya ce
"Amatullah muke don gani."
Security biyu dake bakin ɗin suka nuna basu dan wata Amatullah ba, ran Munnir ya ɓaci gani yake kamar raina masa hankali suke.
Nan ta tada husuma Akan cewa sai an fito da Amatullah. Suna cikin wanan yanayin ne sai ga motar Ajmla ta ƙaraso za ta shiga gidan .
Ganin security har biyu ga mutane uku baƙin fuska ya sanya ya yi parking, dan dama bai fita da Direba ba.
A hankali ya sauke gilashin motar tare da tamabayar abinda ke faruwa.
Nan ɗaya daga cikin security ya masa bayanin abinda ke faruwa, kallon Munnir AJMAL ya yi tare da cewa.
"Lafiya za ka zo har kofar gidana ka
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 27 Chapter of 51