sake bawa Umman ƙarin guiwa tare da kwantar mata da hankali akan cewa Amatullah za ta dawo.
Girgiza kai ta yi tare da goge ƙwalla ta ce.
"Ba ka ga irin duka da koaran kare da mahaifinta ya mata a cikin gidan nan ba ne, idan tana shaye-shaye kuma ta yi cikin shege. korart wai ka da ta dawo masa gida. Kila ma ta tafi kenan."
Ta ƙarasa maganar tana kuka.
"Umma ki daina kuka in sha Allah za ta dawo gida?"
"Dole na yi kuka Munnir yarinyar nan ita kaɗai ce Allah ya bani, kuma ga shi yanzu an Kore ta tsawon watanni goma kenan. Wa ya san halin da take cike tana raye ko ta mace."
Nan ya dinga rarrashinta har sai da ya ga ta saki jiki ta daina kukan sannan ya masu sallama zai tafi.
Bayan ya fita ne ya samu yara a waje ya kira masu ɗan girman.
Kayan abincin da ya siyo masu ne ya ce su kwashe sukai gidansu Amatullah.
Ko da Abba ya fito har Munnir ya tafi bayan ya bawa yara kudi.
Komawa gidan Abban ya yi yana sanyawa Munnir albarka. Yana tuna irin halaccin sa, ga shi Allah ya jarabe shi da son Amatulla. Duk da ta kasance 'yar maye ga abun kunyar da ta aikata na cikin da ta yi bai sa ya guje su ba.
Daddare da misalin ƙarfe goma na dare Ajmal yana sanye da riga da wando fari na barci, ya kasa kwanciya ya yi zaune ya yi tagumi. Ga shi har la lokacin a buƙace yake da mace, dan tun a guest house din nan bai koma daidai ba. Ya sha ƙwayoyin da yake sha idan ya lafa zuwa anjima kaɗan ya tashi. Kamar bai sha komai ba.
Wayarsa ya ɗauka ya kira lambar Amininsa Dr Fu'ad, yana ta ringing bai ɗaga ba, sai da ya kira sau biyu bai ɗaga ba sannan ya ajiye wayar ya cigaba da juyi akan gadon.
Bayan kamar mintuna ashirin sai ga kiran Fu'ad ya ɗaga tare da cewa.
" Yello."
Yaji muryar Fu'ad cikin sauke numfashi ya ce.
"Ya akayi ne kai ba ka san lokacin da ya dace ka kira mai iyali ba? A daidai wannan lokacin ina tsaka da kwasar gara za ka kira ni?"
Jin muryar Fu'ad da yadda yake sauke numfashi Ajmal ya san me yake yi, murmushin gefen baki yayi tare da cewa.
"Afuwa na kira a lokacin da bai dace ba."
"Ba dumuw fadi zancanka da sauri zan koma second round ne Kada ka kashe muna jin daɗinmu dan...."
A fusace Ajmal ya ce.
"Dakata baka bari na fadi dalilin kiranka ba ka fara bani labarin kana kwasar gara za ka je second round na tambaye ka ne? Ko third round ne meye matsala ta da hakan, ai ko ba ka faɗa ba yadda na ji kana sauke numfashi na san halin da kake ciki, ba sai ka bayyana mani ba."
"To ina jin ka me ya saka ka kira ni?"
"Ƙwayoyin nan fa yanzu sun daina mani aiki."
"Wai kana nufin har yanzu da tana kusa da kai sai ka sha ƙwayoyin? Wallahi idan ni ne kai idan ta isa Allah ya tsinen. Kai za ka iya ɗaukar wannan iskancin."
"Tambayarka nake yi cewar magungunan yanzu sun daina mani aiki fa, to gaskiya akwai matsala dan idan na ce zan ɗaura ka akan wani to fa za ka koma kamar mataccen namiji ne."
"To me ye mafita?"
"Mafita ɗaya ce tunda matarka ba ta iya biya maka buƙata sai ka ƙara aure."
"Ba wannan ba tamabaya ba a halin yanzu nake magana, idan kuma babu zan nemi lemun tsami na sha."
"Ya fi maka, ƙaddararka ce haka."
Bai ce komai ba ya katse kiran wayar ya sauko daga kan gadon tare da saka takalmin rigar barcin sa.
Falo ya fito ba kowa dan dama bai sa ran ganin kowa ba, dan Nasreen na rufe a ɗakinta, Affan ma na ɗakinsa.
Kitchen ya duba ba lemun tsami dan dama Nasreen ba shiga kitchen take ba, shi ya sa kitchen ɗin ta ba komai sai dai masu aiki idan sun girka a kitchen dake downstairs ta sauka ta ci a can tare da su Ammi.
Da ya sauka a downstairs ba kowa tsit da alama ma ma'ikatan kitchen ɗin sun gama sun nufi part ɗinsu.
Ya nufi kitchen ɗin kenan sai ya ji magana daga bayansa.
"Me kake buƙata na taimaka maka da shi?"
Muryar Nihal ne ya ji ba tare da ya juyi ba ya ce.
"No need."
Shiga kitchen ɗin ya yi yana dube-dube a cikin tangamemen kitchen ɗin bai ga lemon tsami ba, ya rasa ina suka ajiye ɗan dama ba shigowa yake ba sai dai idan yana buƙatar abu ya sanarwa ma'aikatan gidan. Ga shi yanzu ƙarfe sha ɗaya duk sun tafi.
Nihal ce ta shigo tare da cewa.
"Na ga ka jima ne me kake nema ne?"
"Lemon tsami."
"Shi kaɗai kake so ko zan haɗa maka da salad ne?"
"Okay ka tafi zan matse ruwan na kawo maka."
Ta faɗa tana bin sa da kallon sha'awa. Dan ko da ta kalli idanunsa da yanayinsa ta gane halin da yake ciki.
Juyawa ya yi ya nufi ɗakinsa yayin da ta nufi ɗaya daga cikin fridge dake kitchen ɗin ta buɗe. Lemon tsamin da ke cikin fridge ɗin suna da yawa sosai. Ta ciro guda uku ta matse ruwan a cikin cup sannan ta nufi hanyar fita kitchen tana addu'ar Allah ya sa ta cimma burinta akan Ajmal. Madadin ta kai masa sai ta koma ɗakinta ta sauya kayan barcinta zuwa wata arniyar rigar barci wacce da ita da babu kusan ɗaya ne, dan ba abinda ta ɓoye kamai na jikinta a bayyane suke.
Ta reshe jikinta da wasu irin turarruka masu ƙamshi sannan ta nufi upstairs.
Yana kwance a ɗakinsa lokaci ɗaya sai murƙususu yake yi, ta shiga bakinta ɗauke da sallama. Zuwa lokacin abun da yake ji ya fara tsananta.
A hankali ya ɗago ya kalle ta da idanunsa da suka rikiɗe zuwa ja, cikin karairaya, yadda ya kalli jikinta ne ya kauda kansa da sauri.
Ta iso dab da gadonsa tare da cewa.
"Ka tashi ka sha."
"Yunƙurawa ya yi ya tashi zaune da ƙyar ga mararsa da yake ji tana masa ciwo ta yi tauri.
Miƙa hannu ya yi da niyyar ta bashi madadin ta bashi sai ta saki kofin ruwan lemun tsamin ya zube a ƙasa.
Sai ta ruɗe kamar ba da niyya ta yi ba ta fara magana.
"Subhanahi ya aka yi ba ka karɓa ba ya zube. "
Shi dai ko magana ya kasa mata sai ta ce to yanzu ya za'ayi?"
Da ƙyar ya iya cewa.
"Ki je ki kawo mani wani lemun tsamin yanzu."
"Ayyah ga shi kuma yanzu ba wani lemun tsamin sun k'are, wannan ukun ma da ƙyar na samo su ba wasu."
Cije laɓɓansa ya yi ba tare da ya ce komai ba, haurawa ta yi saman gadon ra riƙe damtsen hannunsa a hankali ta fara magana .
"To Ya Ajmal yanzu wane taimako zan maka na ga kana cikin wani hali?"
Girgiza kai kawai ya yi alamar ba komai.
"Gaskiya ba zan iya barinka cikin wannan halin ba, zan kashe maka ƙishin ruwan da kake ji, ka ɗauka matsalarka ta kau a wannan daren na zama mallakinka janyo yadda ka ke so da ni, so na ke na yaye maka haushinka a daren yau, zan mantar da kai damuwar da kake ciki ."
Ta yi maganar tare da shafa kwantaccen sajen fuskarsa.
*Daga alƙawarin*✍️
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
09065327995
Comments & share
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
🤦♀️ *YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
Ban yarda a karanta mani shi a youtube ko a maida shi audio ba tare da izinina ba.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Page5️⃣6️⃣
Tayi maganar tare da shafa kwantaccen sajen fusakarsa. Ka sancewar ba ya da wani ƙarfi a jikinsa ya sa shi miƙewa ya nufi bathroom.
Ganin bai Kore ta ba bai ce mata komai ba ya sa ta zauna tana jiransa zuciyarta cike da farin ciki, dan ta saba da ta taɓa shi zai mata faɗa ko ya dakatar da ita,amma wannan karon sai ta ga bai mata faɗa ba, kuma ga shi a buƙace yake. Hakan ya sa ta kwanta tana zaman jiransa.
Tana shiga bathroom ya sakarwa kansa ruwa, ya jima a ciki tana ta sakarwa jikinsa ruwa, sai ya ɗan ji sauƙin cikin ikon Allah.
Tana kwance ta ji ƙarar ƙofa alamar ta fito daga wanka, ta shi zaune ta yi tana kallonsa tana sanye da white bathrobe a jikinsa, hannunsa da ƙaramin towel yana goge yalwataccen gashin kansa.
Fuskarsa a tsuke ba ta damu da hakan ba, ta k'arasa gabansa da niyyar kai hannunta jikinsa.
Lafiyayyun tagwayen maruka ta sauke mata guda biyu a kumatunta. Ƙara ta saki tare da durƙusawa wajen.
Ni idan kika kalle ni na yi maki kama da irin mazajen da za ki dinga kawo wa hari ne? To wallahi ki kiyaye ni idan ba haka..."
Katse shi ta yi tare da cew
"dan ba haka ba me? Ai ko kai ka yi kama da mazan da za'a kawo wa hari, ba ma ni kaɗai ba ko wace mace ma idan ta samu dama ba ta bari ba. Ya Ajmal kana da kyau kana da sura mai kyau da cikar zati irin na lafiyayyun maza. Duk mace mai hangen nesa zata yi fatan mallakar ka a rayuwarta. Na kwaɗaitu da kai ko ba ka aure ni ba fatan mu kasance a..."
Hannu ya ɗaga mata alamar dakatarwa. Sannan ya nuna mata hanyar fita.
"Ba zan fita ba sai ka faɗa mani ita waccan yarinyar mai ɗan shegen Amatullah take ko wace ce me kake yi da ita? Har zuwa gust house kuna sheƙe ayarku? Shin ni ba mace ba ce? Matarka ta yi fatali da buƙatar ka ni na zo dan na taimaka maka amma jin kai irin na ka ya sa i watsar da ni ko?"
"Nihal ki fita daga ɗakin nan dan idan na fusata sai kun yi da na sanin abinda kika yi yunkurin aikawa wa."
Tsayawa ta yi tana kallon da hannunta a saman kumatunta da ya mare ta.
Juya baya ya yi ya ba ta san me yake yi ba, sai da ta ji takunsa yana zuwa gare ta ta juya da sauri, ganinsa ta yi hannunsa riƙe da belt alamar dukanta zai yi da shi. Dan haka a guje ta fita daga ɗakin.
"Ai da kin tsaya ƙaramar mara kunya."
Bathroom ya koma ya ɗauro alwala ya fito, jallabiya ya saka ya shimfida sallaya ya tayar da sallah.
Sallolin nafila ya dinga yi sai da ya raba dare sannan ya sallame tare da yin addu'o'i. Daga nan kuma ya fara karatun Alkur'ani mai girma. Sai ƙarfe huɗu sannan ya ɗan kwanta,barcin awa ɗaya ya samu ƙarfe biyar ya farka ya nufi bathroom. Watsa ruwa ya yi tare da ɗauro alwala, wata jallabiyar ya kuma sakawa ya nufi masallaci dan yin sallar asuba.
Bayan an idar da sallar zama ya yi sai da ya yi azkar ƙarfe shida ya dawo gida.
Kai tsaye bedroom ɗinsa ya nufa ya kwanta. Nan da nan barci ya ɗauke shi .
Ba shi ya farka ba sai ƙarfe goma na safe. Wanka ya sake yi ta shirya cikin ƙananan kaya. Jar riga da baƙin wando, downstairs ya sauko dan ya san zuwa yanzu kowa na can a babban falo.
Suna zaune a dinning area suna yin breakfast, Ammi ce da Nihal sai Nasreen da Affan. Dad dama bai cika zama yin breakfast anan ba, sai dai Ammi ta kai masa a sashensa.
Daidai lokacin da Ajmal ya ƙarasa wajen ne ya ji Ammi na cewa Nihal.
"Wannan ba shaidar yaɗuwa ba ne, ga shatin hannu yatsu biyar sun kwanta a saman fuskarki. Wsye ya kare ki a gidan nan? Dan dai na san ba ki fita ba ballantana na ce ko a can ne wani ya mare ki."
Da sallama a bakinsa ya ƙaraso wajen,Ammi ce kaɗai ta amsa masa sai Affan da ya fara murnar ganin Dad ɗin sa.
Gaisar da Ammi ya yi ta amsa masa cikin sakin fuska da walwala, duk da ta ga ba walwala a tattare da shi.
Nasreen ta gaishe shi ya amsa kamar ba wani abu a tsakaninsu, Nihal ta sunkuyar da kai ƙasa tana juya cokali a cikin kofin shayi.
Ammi ta kalli Ajmal ta ce,
"Dubi fuskar Nihal kamar shatin hannu ne wani ya mare ta, amma na tambaya ta ce wai faɗuwa ta yi, kuma wannan ba shaidar faɗuwa ba ne."
Ba tare da ya kalle ta ba lokacin da ya ja kofin shayi da Nasreen ke zuba masa ya ce.
"To Ammi tunda ta ce ba wanda ya mare ta a tafi a haka mana."
Kallon zargi Amma ta masa tare da cewa.
"Ko dai kai ne ka mare ta?"
Gajeren murmushi ya yi tare da cewa.
"Ammi ai gata nan ta faɗa maki gaskiya mana."
"Tsuke fuska Ammi ta yi tare da cewa
"Ba kowa a gidan nan, daga ni sai kai da matarka da ɗan ka, to Dad ɗinka ne zai mare ta?"
Kallonta ya yi ba tare da ya ce komai ba. Ammi ta cigaba da cewa.
"A cikin gidan nan a ma'aikatan gidan nan akwai wanda yake da zarran da zai iya marinta ne?"
Nihal tana tsoron Ammi ta bankaɗo abinda take ɓoyewa dan haka ta ce.
"Ammi ba Ya Ajmal ba ne , Hasalima ai a idanunki na shiga na kwanta, to me zai haɗa ni da shi."
Tashi ta yi ta bar wajen ganin irin mugun kallon da Ajmal ke jifanta da shi.
"Ina za ki je ne?"
"Am okay."
Ta faɗa a takaice tare da barin wajen.
Shiru ba wanda ya sake magana kowa ya cigaba da yin breakfast ɗinsa.
Bayan sun kammala ne Ajmal ya kalli Amminsa tare da cewa.
"Wai yaushe yarinyar nan za ta tafi ne?"
"Wace yarinyar?"
Kamar ba zai faɗi sunanta ba kafin ya ce
"Nihal."
Nasreen ta yi saurin cewa.
"Ai ba Nihal kadai za ka tambayi yaushe za ta wuce ba, cewa za ka yi yaushe za su wuce?"
"Ita da wa kenan?"
Ya yi tambayar ba tare da ya kalle ta ba.
"Ita da waccan tsintacciyar mai kama da sadaka yalla."
Ba tare da ya kalle ta ba ya sake cewa.
"Akwai abinda ta tare maki a gidan nan ne? Ko. Saman kanki take zaune?"
Kallonta ta mai da zuwa ga Ammi sannan ta ce.
"Ammi a gaskiya ta kamata yarinyar nan ta bar gidan nan? Dan ba ga amfanin zamanta a nan ba."
Murmushi Ammi ta yi tare da cewa.
"Nasreen kenan, in ban da abunki ai Amatullah ko za ta koma gidan ba yanzu ba, kuma idan muka sallame ta ban san wani hali za ta faɗa ba, a gabanki aka yi zancen nan, ta rabu da iyayenta mahaifinta ya Kore ta a halin yanzu bai kamata ta koma a yanzu ba. Idan lokacin da ya dace ya yi da kaina zan mai da ta a gaban iyayenta na basu hakuri da sanar da su dukkan abubuwan da suka faru ba laifinta ba ne shi ma ba laifinsa ba ne sai su yi hakuri su yafe ta."
Farin ciki a wajen Ajmal ba'a magana, kamar ya zuba ruwa ƙasa ya sha.
Sai dai bai nuna yana cikin farin ciki ba amma yau km taburge shi.
Nasreen shiru ta yi dan ba haka ta so ba har cikin ranta.
A can hotel kuwa tunda aka shiga da inda kuɗinka ciki ya tabbatar da cewa lallai yarinyar da a ke magana tana gwamna zuwa
Daga nan DPO ya saka Jami'ai duka shiga lungu da saƙo ne ake nemansu.
Jami'an hotel ɗin ne suka shiga cikin hotel ɗin a wasu kuma s cikin club ɗin. Haka aka dinga fito da su ɗaya bayan ɗaya.
Tara su aka yi bayan an sanar da jami'an da ke tsaren ƙofa cewa. Ba shiga ba fita. Har sai sai. Sun gama .
Gaba daya sai da ka aka bincike matan da ke cikin hotel ɗin, da club ɗin.
Hatta Nafeesat da take jiran Hafsats ta ƙaraso sai da aka yi kanta.
Dukkansu INDAKUƊINKA ya ce ba ta nan. Har aka gama INDAKUƊINKA bai nuna kowa ba.
DOO ya tashi ya yi bayanin dalilin tara su a wajen, sannan kuma duk wacce ta san yadda abun ya faru a wancan lokacin ko.
Nafisat ta fara zargin anya ba Hafsat ba ce, saboda washe garin ranar da abun ya faru ita ce ta ga Amatullah tana tafiya daƙyar jini na biye jikinta, da kanta ta gasa mata jiki ta taimaka mata da kayan da za ta saka, sakamako na ta sun yage. Jikinta ne ya yi sanyi sakamakon zargin da take wa Hafsats, dan ko a lokacin da abun ya faru ita Hafsats ta ƙaryata lamarin gaskiya.
Shiru ta yi tana tunanin abun yi. Tana tsaka da tunani ta ji mauryar DPO na cewa.
"Duk wacce ta faɗa mana inda yarinyar take taimaka wajen sanar da mu inda za ku samu yarinyar nan za mu ba ta kyautar Naira miliyan biyu."
A firgice ta ɗago kai tana kallon DPO da yake rike da speaker yana magana.
*Kuyi hakuri da wannan ba na da caji ne Kuma na san a kuna ta jira na, yafi babu dai*
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
090653327995
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
🤦♀️ *YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
Ban yarda a karanta mani shi a youtube ko a maida shi audio ba tare da izinina ba.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Page5️⃣7️⃣
A firgice ta ɗago kai tana kallon DPO da yake riƙe da speaker yana magana.
Jinjina kai ta dinga yi tare da tunani,tabbas miliyan biyu ba ƙaramin kuɗi ba ne. Amma dai kuɗi zai sa ta tona asirin ƙawarta ba. Tunawa da ta yi lokacin da ta sa mu Hafsat da maganar akan abinda ta yi wa Amatullah sai ta nuna ita ba ta san da zancen ba, ba abinda ta aikata mata.
Maganar zuci ta fara yi .
'To tunda bana da tabbas akan akan cewa Hafsat ce ta aikata hakan, idan ya kasance ba ita ba ce fa me zan ce.'
Haka dai ba wanda ya amsa cewa ya san wace ce kuma ba ta cikin wajen.
DPO ya nemi da cewa idan da hali ko za'a iya samun ɗaukar cctv camera wanda ko za'a gane ta. Kafin manajan Hotel ɗin ya yi magana ne INDAKUƊINKA ya yi saurin cewa.
"Ba za'a gane ta ba, saboda ba ta ƙarasowa nan kusa, daga can take tsayawa ta kira ni sai na je na same ta muyi magana."
"Ba cctv camera da aka Saita wanda zai dinga hasko masu shigowa?"
Manajan ne ta amsa masa da cewa.
"Tsawon lokaci baya aiki, ya samu matsala."
Dafe goshi DPO ya yi cikin takaici ya ce.
"Amma ya kamata ace kuna kula saboda gudun matsala."
"Afuwan yallaɓai mun yi sake kasancewar wata matsala ba ta taɓa faruwa ba ne ya sa ba mu kula ba, amma yanzu in sha Allah za mu kula tunda hakan ta faru.
Sallama suka masu tare da sanar da su cewa ko wane lokacin zasu iya dawowa.
A yammacin ranar Ammi na falo ita da Affan dake ta zuba mata shirme irin ta su ta yara, dariya take masa tana biye shi, tare da tambayarsa abinda aka koya masu a school.
Ganin lokacin kallon news ya yi ne ta canza channel. Tahin farko ta ga DPO yana magana inda yake cewa.
"Dangane da zargin da ake yi wa ɗan takara Gwamna Ajmal Ibrahim Tafida na cewa yana aikata fasiƙanci da 'yan mata, musamman wadanda suke zuwa gidansa neman taimako. Zargin ya faru ne lokacin da aka gan shi ɗauke da wata mai ciki ya kawo ra asibiti a motarsa, daga shi sai ita, hakan ya sa wasu suka dinga yaɗa jita-jitan cewa ksruwarsa ce wasu na cewa dadironsa ce."
Amma ta ɗauki wayarta dan kiran Ajmal ya kunna tv. Sai ga Ajmal ya shigo falon da sallama, ƙurawa tv ido ya yi jin ana ambatar sunansa. Inda D.P.O ya cigaba da cewa.
Wanda sakamakon gwajin a gaban jama'a Doctor ya shaida cewa ɗan Ajmal Ibrahim Tafida ne. Wanda hakan ya sa mutane da yawa suna dinga fadar albarcin bakinsu da kuma son ransa. To yanzu za ku ji gaskiyar lamari akan wannan shi ne ske kira INDAKUƊINKA komai zai maka."
Camera ta hasko inda kuɗinka wanda hawaye ke zuba daga idanunsa.
Nan ya fara bada labarin duk abinda ya faru, da kuma wacce ta bashi kwangilar yin hakan. Ya kuma rantse da Allah Ajmal bai san komai ba su ne suka shirya masa.
Shi kuma ya rantse da Allah bai yi hakan dan ɓatawa Ajmal suna ba, dan bai san waye shi ba sai da hakan ta faru ya san cewa ba ƙaramin mutum ya taɓo ba, kuma shi bai san dalilin da ya saka aka bashi wannan aikin ba, saboda a ɓatawa Ajmal suna ne ko dan a ɓata rayuwar yarinyar, bai sani ba. Shi dai ta biya shi ne kuma ya mata aiki.
Ɗaya daga cikin 'yan jaridar ne mai suna Fareeda ta kalle inda ranka ta ce,
"Amma Allah ya tsine maku albarka daga kai har ita."
Wani ya ce.
"Kai wane irin mutum ne akan Naira dubu ɗari kacal zaka ɓata rayuwar wasu?"
Wani ya ce.
"Amfanin me kuɗin za su yi maka ne?"
'Yaridar nan Fareeda wacce ta kasance ƙawar Nasreen har a baya ta dakatar da Nasreen gani za ta tonawatamijinta asiri ta sake tambayar INDAKUƊINKA cewa.
"Ka san wani hali ka saka wannan bawan Allah da iyalinsa kuwa? Kamilin mutun ka ɓata masa suna a faɗin jahar nan kowa na masa kallon mutumin banza,girmansa da ƙimarsa da ake gani ka sa sun zube lokaci guda. Ta baka tsirarun kuɗi yanzu ya za ka yi da hakkin da ke kanka na Ajmal da ita yarinyar?"
Tuni wajen ya cika da jama'a ana cincirindon zuwa wajen. Wasu dake nan sai duwatsu suka ɗauka suna kifar INDAKUƊINKA. Wanda har goshinsa ta fashe ya fara zubar da jini. Nan da nan DPO ya bada umurnin a shiga da shi ciki, ganin za su illata shi.
Nan jami'an 'yan sanadar dake wajen suka shiga da inda ranka ciki.yayin da Jama'a musamman matasa ke cewa.
"Ku bari mu lashe shi barinsa cikin al'umma ba ƙaramar hatsari ba ne annoba ne shi."
DPO ne ya fara magana wanda hankalin 'yan jaridar ya dawo kansa.
"Kunga bamu tara ku nan dan ku yi mana hayaniya ba, na tarasku ne da ku san gaskiya. Ya kuke neman ɗaukar doka a hannunku,to fa ku sani duk wanda wanda ya kashe shi kamar yadda na ji kuma faɗa shi ma shi ma kashe shi zamu yi dokar kenan, dan haka ku bari mu binciko yarinyar a'a haɗa su masu hukunci daidai da abinda suka aikata."
Wani ɗan jarida ne ya ce.
"Yallaɓai zuwa yaushe ne za ku kamo yarinyar?"
"Da zaran mun kamo ta za ku sani, ana kan nemanta ne."
Daga nan bai sake magana va ya bar wajen.
Wani ɗan jarida ya ce.
"To jama'a muna nan muna zuba Idanu a kamo yarinyar nan a hukuntata daidai da abinda suka aikata."
Amma ta zubawa tv Idanu fuskarta ɗauke da farin ciki, yanzu jama'ar gari za su daina yiwa ɗanta kallon mutumin banza, gaskiya ta yi halinta. Ajmal ma idanunsa na kan tv yana murmushi ganin yanzu ya wanku a idanun mutane.
Komawa ya yi wajen Ammimsa ya zauna kan carpet a gabanta ya ce.
"Alhamdulillahi."
Murmushi ta masa tare da cewa.
"Ma sha Allah."
Wayarsa ce ta yi ruri, dubawa yayi Dr Fu'ad ne ya ɗauka, inda yake masa murna, kafin ta gama ɗaya wayar ta fara ruri, ɗayar ma haka. Suna sallama da Fu'ad wayar da suka yi magana ma ta fara ruri, haka duka wayoyinsa uku ke ruri gaba ɗaya ya kashe su. Dan ya san dalilin kiran da suke masa. Dan su masa maganar fitar da aka yi da INDAKUƊINKA ne.
.Tashi ya yi tare da tambayar Ammi ko yau ta ga jaririn Amatullah?
Murmushi Ammi ta yi tare da cewa.
"Ai ba ranar da ba zan je na duba lafiyarsu ba."
Sunkuyar da kansa ya yi yana ɗan sosa ƙeya a hankali ya ce.
"Ammi ko zan iya zuwa na duba shi?'
"Why not."
Ta shi ya ya ya nufi ɓangaren su Amatullah. Ba kowa a falon, kasancey yamma ce duk sun nufi kitchen dan girkin abincin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 51