Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LrTZNGwF35IKXX4sLRvFug 🤦‍♀️ *ƳAR MAYE*🤦‍♀️ (The drug abuser) *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *SANARWA* *Littafin ƴar maye da yawa daga cikin mutane da suka ji sunan littafin sun yi tunanin cewa harkar shaye-shaye ne kawai a ciki, wanda wasu ke tunanin cewa kamar koyawa wasu ne yadda za su dinga shan kayan maye, suna tunanin ba wani darasi da za'a koya acikin labarin. To a zahirin gaskiya littafin ba yadda wasu ke tunanin sa ya ke ba, labarin ne da ke nuna illar shaye-shaye da kuma halin da mutum zai iya riskar kansa a ciki, da kuma illar shaye-shaye. Duk lolacin da zan fara rubuta littafi ina rok'on Allah ya bani ikon rubuta abinda zai amfani al'ummar annabi, sannan idan har akwai abinda ba alkhairi ba kada ya bani ikon rubuta shi idan akwai wani sharri da ke cikin labarin nan kada Allah ya bani ikon rubuta shi. Allah ya bani ikon rubuta abinda zai amfani al'ummar annabi Muhammad (S.A.W)* *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubucirsa ce,da haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *BISMILLAHI RAHMANI RAHIM* Page0️⃣1️⃣ Hadari ne ya haɗu a garin sosai duk da yammaci ne amma yadda garin ya yi duhu za ka d'auka dare ne ya fara yi. Wasu matasan ƴan mata ne da ba za su wuce shekaru goma sha bakwai ba, dukkansu sanye suke da riga da wando tare da dogon hijabi har ƙasa, kalar ruwan toka ne kayan. Kallo ɗaya za ka masu ka gane cewa daga makarantar islamiyya suke, saboda kayan makarantar islamiyya ne a jikinsu, an manna baje mai d'auke da sunan makarantar a hijabinsu. Ɗaya fuskarta na sanye da niƙabi idanunta kawai ake gani, ɗayar kuma bata sanya niƙab ba. Riƙe suke da hannun juna suke sauri-sauri gudu-gudu suke yi, ga iska da ke shirin tasowa, a haka suka ƙarasa bakin titi suna neman abin hawa, sai dai cikin rashin sa'a duk wanda suka tare ba sa tsayawa, da alama suma sauri suke ganin yadda hadari ya haɗu a gari. Mai sanye da niƙab ce ta kalli ƙawaeta ta ce, "Gara da ke gidanku ba nisa, yanzu za ki ƙarasa gida amma ni kuma fa idan ban samu abin hawa ba ruwan saman nan ya faɗo ya zan yi?" "Kada ki damu Amatullah, yanzu za ki samu abin hawa, duk Ni ce na janyo maki da lokacin da aka tashi islamiyya mun tafi gida ai da ba haka ba." Wacce aka kira da Amatullah ta yi murmishi tare da cewa "Ka da ki ɗorawa kanki laifi, ko ba ki ce ba dama ma yi niyyar zuwa duba jikin Jamila, dan dama na sanarwa Ummata cewa daga islamiyya zan mu je mu duba jikin Jamila." Iska ne tare da yayyafi lokaci guda Amatullah ta kalli ƙawarta ta ce, "Fadila ya zan yi ga shi ban samu abun hawa ba yanzu za ki tafi ki barni." "Ba zan tafi na barki ba Amatullah" Dai dai lokacin ruwa ya ƙara ƙarfi tare da iska mai ƙarfi, Amatullah ta ƙanƙame jikinta dama ba ta son ruwa ya dake ta. Wata mota ce ta zo ta tsaya a gabansu a hankali ya sauke gilashin motar tare da kallosu ya ce, "Ƴan mata Ku zo na rage maku hanya, da dukkan alamu daga islamiyya kuke ko?" Amatullah ce ta ce, "Ka barshi mun gode." Ƙwayar idanunta da su kaɗai kake iya hangowa ya ce, "Dan Allah ki yi haƙuri ki shigo, domin kunga ruwa ake yi kuma a irin wannan lokaci abun hawa wuya zai maku dan kowa neman mafaka ya ke yi, na ganku sanye da kayan islamiyya bai kamata Ku tsaya nan ba, dan Allah ku shigo." Fadila ce ta kalli Amatullah ta ce, "Kinga yanzu ba abin hawa gara mu shiga kinga tafiyarki da nisa, kuma idan ruwa ya dake ki zazzaɓi kike Kum...." Kafin ta ƙarasa maganar da take ne Amatullah ta ce, "Ba inda zan shiga a wannan zamanin da muke ciki mutum ba abin yarda bane." A hankali ta yi maganar dan ka da ya ji ta, ashe ya ji ta dan haka ya yi dariya tare da cewa "Kina da gaskiya amma bani da niyyar cutar da ku, wallahi ba komai a cikin zuciyata sai alkhairi." Ganin ta yi shiru ya sa Fadila ta ja hannunta suka ƙarasa jikin motar, buɗe masu bayan motar ya yi suka shiga inda Fadila ke masa godiya. Ita dai Amatullah ba ta saki jikinta ba. Tafiya kaɗan suka yi ya tambaye su unguwar da suke, Fadila ce ta sanar da shi unguwar da take, jinjina kai ya yi ba tare da ya yi magana ba. Ba wanda ya sake magana a cikinsu sai kallon ruwan saman da ke saukowa. Kwanar unguwanrsu Fadila ya ɗauka ya bi duk kwatancen da take masa, har ƙofar gidan ya sauke ta. Fita ta yi tana masa godiya bayan ta yi wa Amatullah sallama. Juya motar ya yi tare da barin wajen, inda ya tambayi Amatullah cewa . "Mallama wace unguwa za mu tafi.?" A hankali ta buɗe baki cikin zazzƙar muryarta ta ce, "Nassarawa." Kumshe idanuwanta ya yi yadda ya ji muryarta, sake tambayarta ya yi inda yake cewa. "Ya sunanki?" Shiru ta yi kamar ba ta ji shi ba, sake tambayarta ya yi a karo na biyu, nan ma shiru. Murmushi ya yi ba tare da ya ce, komai ba inda ya zaro wayarsa, dannawa ya yi tare da karawa a kunnensa ya fara magana. "Hello kina ina ne?" Tsuke fuska ya ya tare da cewa "Me kika sha?" Shiru ya yi tare da yin tsuki ya kashe wayar. Ɗan juyawa ya yi ya kalli Amatullah ya ce, "Mallam dan Allah ki yi haƙuri zamu tsaya nan gaba kaɗan, ƙnawata zan ɗauka a gidan ƙawarta, dama ita zan je ɗaukowa na ganku na tsaya." Ita dai ba ta ce komai ba, gani ta yi ya yi parking a gefen titi, wayarsa ya ɗauka tare da kiran wata lambar ya ce, "Ki fito yanzu nan sauri nake." Bai jira cewarta ba ya kashe wayarsa. Bayan kamar mintuna biyar sai wasu 'yan mata da ba za su wuce shekaru ashirin ba suka fito daga gidan, ba wacce take da ɗankwali, ɗaya na rike da handbag ɗinta da mayafinta a hannunta, sai kitson kalaba da ke kanta,ɗayar ce ba komai a hannunta. Tafiya suke suna layi rangaji suna haɗa hanya tare da harɗe ƙafa, bangaje juna suke a haka har suka ƙaraso jikin motar, karo suka yi da motar kamar wasu makafi. Hankalin Amatullah ne ya dawo kansu jin amma su ba su ganta ba. Dafe goshinsa ya yi cikin takaici ya buɗe murfin motar ya fito, gaban motar ya buɗe mata tare da cewa "Zo ki shiga mu tafi!" Ɗayar ce ta kalli ɗayar cikin maye ta ce, Hafsat ki shiga ku tafi" Wacce aka kira da Hafsat ce ta ce, Ba zan shiga gaban motar ba saboda barci zan yi." Kokuwa ta ke yi da murfin motar ta kasa buɗewa, ganin haka ya sa Amatullah ta buɗe murfin motar a hankali ta fito, ganinta ya sa Hafsat cewa "Me kike yi a motar mijin da zan aura?" Tana magana kamar ƙafar ƙafarta ba za ta iya ɗaukarta ba, Kallonsa ta yi tare da cewa "Munnir me wannan ke yi a motarka?" Bai kula ta ba ya kalli Amatullah ya ce, "Mallama dawo nan mu tafi." Ba musu ta shiga gaban motar da ya buɗe mata. Hafsat na da niyyar magana kenan, ya hankaɗa ta motar tare da rufe motar da ƙarfi, zagayawa ya yi ya zauna a mazauninsa ya tada motar ya bar wajen. Ƙawar Hafsat ce ta koma gida tana tangaɗi. Munnir ne ya kalli Amatullah tare da cewa "Wace unguwar ma kike?" "Nassarawa, layi na biyu gida mai lamba goma." Dama ya tuna haka kawai ya ke son sake jin muryarta. Ba wanda ya sake magana sai Hafsat da ke ta sambatu ita kaɗai, a bayan motar A fuskance ya daka mata tsawa tare da cewa "Shutup! Ba dai baki jin magana ba." Tana lumshe idanu alamar barci ne idanunta ta ce, "Ya Mannir ka yarda bansha komai ba, lemu ne na roba kawai nasha kawa." Tsuki ya ya dan ya ga alama raina masa hankali take ko kuma cikin maye ne. Har ƙofar gidan su Amatullah ya yi parking, cikin sanyin muryarta ta tana cewa, "Na gode Allah ya saka da alkhairi." Buɗe maufin motar ta yi da niyyar fita sai ta ji a datse, ya yi Locking ne ba halin ta fita. Kallonsa ta yi yayinda ya zubawa ƙwayar idanunta ya sakar mata murmushi. Ganin irin kallon da yake mata ne ya sa ta yi saurin sunkuyar da kanta ƙasa ta ce, "Ɗan Allah ka buɗe mani na fita, wallahi faɗa za'a mani a gida." Buɗe mata ya ya ta fita da sauri, sai da ya ga gidan da ta shiga ya bar wajen, murmushi ne bayyana a fuskarsa. Yana cikin tafiya kenan sai wayarsa ta soma ruri, bai ɗaga ba har ta katse, sake kira aka yi dan haka ya yi parking a gefen hanya . "Hello Habib ya aka yi ne?" Daga can ɓangaren Habib ya ce, "Abokin ya aka yi kana ina?" "Nassarawa" Wajenwa kuma?" "Wata yarinya na ragewa hanya?" Dariya Habib ya yi tare da cewa "Ko dadai ka yi kamu ne a unguwar?' Murmushi ya yi tare da cewa "Ai abokina kamar ka sani yarinyar ta mani, duk da banga fuskanta ba." "Ban gane baka ga fuskar ta ba, kuma kace ta maka?" "Sosai, ƙwayar idanunta masu ɗaukar hankali ne suka ɗauki hankalina, duk da ta sanya niƙab." "Ta ya za ka gane kyan mace a cikin niƙab." "Ni dai ta mani ina son ta zama uwar ƴaƴana." "To ya za ka yi da Hafsat?" "Kai wai ya ina maganar Amatullah za ka kawo mani zancen Hafsat?" "Gani na yi ita za ka aura kuma da mahaifiyar Hafsat da mahaifiyarka ya da ƙanwa ce?" "To sai me?" "Sai aure ku." "Ada kenan, amma yanzu kam ba zan iya aurenta ba, domin ko Manzon Allah saw cewa ya yi ku zaɓawa ƴaƴanku uwa ta gari, yanzu idan na auri Hafsat ga ta ta yi nisa a cikin shaye-shaye, kullum cikin maye take wace tarbiyya za ta bawa ƴaƴanmu? Bari zancen kawai na ga gidansu nan da kwana biyu zan zo na same ta.Bari na ƙarasa gida mun yi magana." Daga nan ya katse kiran tare da jan motar suka fara tafiya. Horn ya yi mai gadin ya buɗe masa ya shiga da motar, bayan ya yi parking ne ya juya ya kalle ta tare da yin tsuki" fitowa ya yi cikin sa'amai aikin gidan ta fito, kiranta ya yi ya sanar da ita ta janyota su shiga ciki. Bayan ta janyota ta rungume ta ta gefen kafaɗarta, suka far tafiya, har cikin ɗakin barcinta ta kai ta. Zubewa ta yi akan gadon ta cigaba da barcinta. Can zuwa safiya ta farka, daga barcin da take, a hankali abubuwan da suke faruwa suka shiga dawowa, tun daga gidan ƙawartahar abinda ya faru da wayar da Mannir ke yi da Habib ya ke sanar da shi ya fasa aurenta Amatullah zai aura. Hannu ta ɗaura akai tare da yin kuka, zuwa can kuma sai ta fashe da dariya kamar ba ita ke kuka ba. Magana ta fara yi. "Wai ni yake cewa ƴar shaye-shaye bazai aure Ni ba sai mai tarbiyya, to ita wacce yake tunanin tana da tarbiyya ba 'yar maye ba zan bashi mamaki, dan wannan yarinyar na ɗaukar wa kaina alƙawarin cewa sai na koya mata shaye-shaye, za ta wayi gari sai ya kira ta da ƴar maye, ya ja mata bala'i dan wallahi idan har ba ta fara shaye-shaye ba ba sunana Hafsat ba. Wallahi bai isa ya juya mani baya saboda ita ba sai ta koma yadda nake. Na ji ta ce, Nassarawa gida mai lamba goma, kin yi kuskure da kika shiga motarsa har ya kamu da sonki." Tashi ta yi tare da cewa "Bari na yi wanka Amatullah gani nan zuwa gare ki." Maman Ihsan ce Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LrTZNGwF35IKXX4sLRvFug 🤦‍♀️ *ƳAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Dedicated to *JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION* *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubucirsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *BISMILLAHI RAHMANI RAHIM* Page0️⃣2️⃣ "Bari na yi wanka Amatullah gani nan zuwa gare ki" Tashi ta yi ta nufi bathroom don yin wanka, zuciyarta cike da manufofi, dan ta ƙudiri niyyar cewa tunda har Munnir zai iya juya mata baya saboda tana shaye-shaye ya ce wai ba zai aure ta ba, to ita wacce yake so ɗin sai ta saka ta harkar shaye-shaye ta ga yadda zai yi. Ɓangaren Amatullah kuwa jiya da Munnir ya sauke ta a ƙofar gida, sauri-sauri ta nufi gidan sai ta yi kiciɓis da Mallam Abdullahi a zauren gidan.Tsaye ya ke hannunsa riƙe da wayarsu Nokia ya kunna torchlight ɗin wayar, durƙusawa ta yi bayan ta yi sallam ya amsa mata. "Ina wuni Abba." "Daga ina kike a dai dai wannan lokacin? Kuma waye wannan da ya sauke ki a mota?" "Abba daga gidan ƙawata nake dama bata da lafiya ne ta daina zuwa islamiyya, shine na nemi izinin Umma akan cewa za mu je gidanta mu gaishe ta daga islamiyya. Bayan mun bar gidan hadari ya taso shine wannan ya ganmu ya ce mu shiga ya kaimu gida." "Kawai mutum ya tsaya da mota da mota ya ce ku shiga shine kuka shiga motarsa ko?" "Wallahi Abba ba da son raina muka shiga ba, hasalima ban yi niyyar shiga ba Fadila ce ta takura na shiga, ga shi hadari ne ya taso babu ababen hawa ko mun tare da basa tsayawa, ka san kuma ruwan sama idan ya doke ni sai na yi zazzaɓi, hakan ya sa na shiga tunda na ga alamar mutumin kirki ne." "Ta ya ya kika san mutumin kirki ne bayan lokacin kika fara ganinsa? Daga yau ka da hakan ta sake faruwa duk lokacin da aka tashi daga islamiyya ki tabbatar kin dawo gida, Kada ki sake kaiwa magrib a waje." "Ka yi haƙuri in sha Allah Abba ba zan sake ba." Jinjina kai ya yi tare da cewa ta shiga ciki. Sai a lokacin hankalinsa ya kwanta, dan duk inda ya ga ƙarfe shida ya yi lokacin tashin Amatullah daga islamiyya ya yi ya ke zuba idanun dawowarta. Sallam ta yi ta shiga gidan bayan ta gaida Ummanta ta shiga ɗakinta, sauya kayan jikinta ta yi ta fito ta shiga banɗaki ta fito ta yi alwala dan gabatar da sallar magrib. Wasu 'yan mata ne su huɗu zaune a ɗaki, kowacce sai tsuki take, cikin jin haush ta tashi ta ƙarasa wajen kujera ta zauna, shisha ta ɗauka ta fara busa hayaƙi. Ɗaya daga cikin ƴan matan ne ta ce, "Wallahi Tukur ɗin nan ɗan rainin hankali ne, tun ɗazo ya kawo mana kayan aiki ya na ɓata mana lokaci." Tana rufe baki sai ga Tukur ya yi sallama ya shigo, ba su amsa sallamar da ya yi ba ɗaya daga cikinsu mai suna Shamsiya ta ce, "Dalla can ka je ka shanya mu muna jiranka." "Wallahi daƙyar na samo maku maganin nan, mutumin da na fara zuwa wajensa ɗanyawa ne wallahi, wai ba zai sai da mani da kwalabe biyar ba, shaye-shaye zamu yi." Tsawa ta daka masa tare da cewa "Kai wane irin wawa ne, ba cewa na yi ka ce wai yara ne suke tari da mura ba?" "Haka na ce wai ƙarya ne sai dai ya siyar mani da kwalba ɗaya. Shine fa ya bani codolin kwalba ɗaya sai da na je wani waje na samo maku wannan." Amsa ta yi kowaccensu ta cire ɗaya ta buɗe kwalbar ta fara sha. Nafisata dake shan shisha ce ta tashi ta nufi fridge ta buɗe ta ɗauko kwalbar giya mai sanyi ta buɗe ta fara sha. Wayarta ce ta fara ruri, ta ɗauka tare da karawa a kunnenta ta ce, "Hafsat ya kike." Ajiyar zuciya Hafsat ta sauke tare da cewa. "Wata yarinya ce nake son na janyo ta cikinmu." Wace yarinya kenan?" "Sunanta Amatullah." "Dama tana shaye-shaye ne ko kuma tana da sha'awar farawa?" "Ba wai tana da sha'awar farawa bane, wato ina da manufa akan yarinyar ne, yanzu zan tafi gidansu idan na samu ta karɓe ni komai zai tafi yadda na tsara." "Okay sai kin iso zan ji yadda za'ayi." Hafsata ce ta fito, sanye da dogon hijabi har ƙasa, mahaifiyarta Hajiya Laila wacce take kira da Mom ce ke zaune a falo, kallon Hafsat ta yi da mamaki, son Hafsat ba ta taɓa fita da hijabi ba Indai ba Sallah za ta yi. Amma yanzu ga ta sanye da hijabi har ƙasa. "Yau ke ce da hijabi za ki fita? Ina za ki je ne?" "Mom wani waje zan tafi sai na dawo." Ba ta jira cewar Mom ɗinta ba ta fice, don dama hala suke za ta fita duk lokacin da ta ga dama kuma ta dawo lokacin da ta ga dama, idan ta kama ta kwana waje ne haka za ta kwana waje sai washe gari ta dawo gida. Amatullah ce zaune a saman sallaya a ɗakinta tana karatun al-qur'ani mai girma, suratul kahfi take karantawa kasancewar ranar juma'a ce. Sanye ta ke da hijabi ta ji sallama a bakin ƙofar ɗakinta, dama ayar ƙarshe take karantawa don haka sai da ta kai ƙarshen aya ta amsa sallamar tare da rufe al-qur'anin. Wani yaron maƙotansu ne ya kalle ta ya ce, "Anty Amatullah ana kiranki a waje." Gabanta ne ya faɗi rass jin wai ana kiranta, dan ba ta kula kowa balle har a biyo ta gida. Ummanta da fitowar ta kenan daga banɗaki ta kalli yaron ta ce, "Wane ne ke nemanta." "Wata ce a waje nima ban san ta ba." Jin mace ce ya sa Ummanta cewa "Ka je ka ce wai ta shigo" Yaron ya fita bayan ya masu sallama, bayan fitarsa da mintuna uku sai suka ji sallama daga ƙofar gida. "Assalamu alaikum" Gaba ɗayansu suka amsa mata sallamar tare da zuba mata idanu. Itama kallonsu take don ba ta san Amatullah ba, dan jiya ba ta ga fuskarta ba kasancewar ta na sanye da niƙab. Don ko gidan ma dan ta tuna sanda Amatullah ta je gida mai lamba goma ne ya sa ta gane. Da fara'arta ta k'araso har da durƙusawa ta gaida Umman Amatullah, abinda ba ta taɓa yi ba kenan a rayuwarta amma saboda basaja yau ta yi shi. Cikin sakin fuska Umma ta amsa mata tare da kallon Amatullah ta ce, "Ba ita ce ke sallama da ke ba?" Kafin Amatullah ta yi magana Hafsat ta yi saurin cewa "Eh ni ce Umma." Jikin Amatullah ne ya yi sanyi dan tabbas ta gane ita ce wannan yarinyar da take maye jiya. Amma iya ta ɗauka wanda ke maye baya tuna komai, amma yanzu me ya kawo ta? Ba ta gama tunani ba ta ji kuryar Umma na cewa "Amatullah ya kika barta a tsaye?" Murmishi ta ƙaƙalo tare da cewa, Sannu da zuwa mu shiga ciki" Ta ƙarasa maganar nuna mata ɗakinta. Shiga suka yi inda Amatullah ke gaba Hafsat na binta a baya, tsayawa Hafsat ta yi tana ƙarewa ɗakin kallo tare da yamutse fuska. Madaidaicin ɗaki ne sai katifar kwanciyarta ta ta gyara daga gefe kuma ga ƙaramar dorowar saka kaya, sai leader carpet sake shimfiɗe a ɗakin, ƙamshin turaren wuta ne kasancewar Amatullah yarinya ce mai tsafta da son ƙamshi. Zama ta yi a gefen katifar inda ta zubawa Hafsat idanu ta ce, "Bisimillah baiwar Allah ki zauna." Zama Hafsat ta yi ta na sakin murmushi, Amatullah ta ce, "Ina wuni Anty." "Wace ce Antyn?" "To ai kinga bansan sunanki ba kuma ai ke ba sa'ata bace kin girme ni, shi ya sa na kira ki da Anty." "To daga yau karki sake kira na da Anty domin ina so mu zama ƙawaye ne da ke?" "Ai ke ba kin girme ba zan iya ƙawance da ke ba." "Saboda me? Ai ba sai sa'anki ne za ku yi ƙawance ba, ko wacce ta girme ki ma za ku yi ko ta haife ki ma ba wani abu bane." Shiru Amatullah ta yi dan halankalinta bai kwanta da Hafsat ba, inda Hafsat ta ce, "Ni so nake kowane lokaci mu kasance a tare, kullun ya kasance barcin dare ne kawai ke iya raba mu da ke." Murmushin yaƙe Amatullah ta yi tare da cewa ai hakan ba mai yiwuwa bane, domin kinga ina zuwa makarantar boko da islamiyya, rana ɗaya ne kawai za ki iya samu na a gida irin yau juma'a. Idan na dawo school ina gida dan kinga ko jiya Alhamis ma duk da bamu da islamiyya na je islamiyya karatun haddan al-qur'ani, a hanyar dawowa ne muka haɗu da wanan da na ji kina cewa mijin da zai aure ki." "Ada ne zai aure ni amma yanzu ya fasa." "Me ya saka shi fasawa?" "Saboda wani dalili muka fasa." "Amma yanzu na ji ya ce yana neman wacce zai aura." Jinjina kai Amatullah ta yi tare da cewa "Allah ya zaɓa maku abinda ya fi zama alkhairi a tsakaninku" "Ameen, yanzu dai ina neman amincewar ki ki ɗauke ni ƙawarki aminiyarki, kullun muna tare. Zan dinga zuwa ina kai ki School da safe, Wane class kike ne?" "S.S 2 nake yanzu." "Okay ashe next year za ki gama secondary school." "Eh in sha Allah, amma ba na son takura maki, ba zai yiwu kullun ki dinga zuwa kaini school ba, dan..." Katse ta ta yi tare da cewa "Wannan ba wani abu bane, ba na zuwa ko ina, don tunda na kammala University na yi bautar ƙasa har na fara aiki na watanni biyu kuma na ga ba zan iya wahala ba na daina." *KADUNA* Babban gida ne ƙayatacce da gani na faɗa, girman gidan tamkar wani masarauta. Tsayawa misalta maku haɗuwar gidan ma ɓata lokaci ne. Wata mata ce mai kimanin shekaru hamsin da biyar ke zaune a saman royal chair, sanye take da baƙar abaya ta ta yafa mayafin abayar a kanta, tana sanye da farin glass a idanunta, hannunta riƙe da jarida tana

Chapter 1 of 51