Share this page
saka ita ma ta rungume ta suna yin kukan tare ba tare da ta san komai ba. Tsawon mintuna suka ɗauka suna kuka ba mai rarrashin wani, kafin Nasreen ta zame jikinta daga na Ma'eesha, tana goge ma ta hawaye ta ce. "Me yake faruwa ne, na san ni da ke ba mu ɓoye wa juna komai, don Allah ki sanar da ni kar ki saka kaina ya buga." Nan Ma'eesha ta ba ta labarin komai, tun daga farko kar karshe. Ba abinda Ke tashi sai sautin kukan Nasreen tana tausayin ƙawarta. "Amma Allah ya tsine wa Mamy albarka. Allah ya sa ta shiga wuta, wallahi wannan matar ba za ta ga annabin rahama ba. Gabadaya ta juye wa Daddy tunani sai abinda ta ce. Allah ya jikan Mummy." "Amin ya Allah." Ma'eesha ta faɗa tana goge hawayenta. "Yanzu shi wanann makahon ne zai iya riƙe ki?" Ma'eesha ba ta ce komai ba, don ba ta san amsar da za ya ba ta ba. "Yanzu ke sai kika yarda?" "To ya zan yi Nasreen?" "Ai ba yadda za'ayi a haɗa ki da wannan nakasashen talakar musaki. Haba ke ba za ku nema wa kanki ƴanci ba?" Murmushin takaici ta yi ta ce. "To ya zan yi tun da mahaifina ya aurar da ni ga wanda ya ga dama, ba na da wani zaɓin da ya wuce rungumar kundin ƙaddarata." "Haka ne, amma wannan ai bai dace da ke ba, ta ya ya za'a aurar da ke ga wanda na san ko kuɗin kayan kwalliyarki ba zai iya siye ba ballantana abincin da za ki ci, abun takaici wai sadakinki dubu uku kacal ko kaza yanzu ai ba za'a ce dubu uku ba ballantana mutum, ba kayan lefe ba komai, wanann ke ce kika sigar da wayarki kika kama haya kika siyo abincin da za ki ci kin san wannan auren ba alkhairi a cikinsa. Don haka ki tattara kayan ki yana zuwa ku ci mutuncinsa ki saka ya yi ma ki saki uku, ki zo mu tafi gidanmu ki zauna a can na san iyayena za su karbe ki, kin ga ba ki da kowa a garin nan ba ki san dangin mahaifiyar ki ba, sannan yanzu tun da hakan ya faru ba ki isa ki tafi wajan dangin Daddy ba, don sai abinda ya fada a family suke ɗauka." Ta yi maganar tana tattara kayan Ma'eesha da ta gani a waje, tana saka wa a cikin trolly ɗin ta. "Ba in da zan je." Da mamaki take kallonta. "Da gaske ba in da za ki je?" "Eh haka na ce." "Saboda me?" "Saboda zaman ibada nake yi." Nisa wa ta yi kafin ta ce. " Duk talaucin mijina zan yi haƙuri na zauna da shi cikin kwanciyar hankali da soyayya. Mijin wata bai fi nawa ba duk sunansu mazajen aure, zan yi alfahari da nawa ko a ina ne, domin nawa shi ne nawa, mijin wata ba nawa ba ne. Zan zauna da nawa cikin nutsuwa da kulawa. Ba zan dinga hangen na wasu ko kallon irin abubuwan da yake musu, domin kowacce tana da nata jarabtar. Zan fito in nuna alfahari da nawa, kamar yadda wasu ke yi da nasu. Kila ma na fi su samun kulawa da soyayya. Talauci ba laifi ba ne. Amma boye shi, da zama cikin kima da mutunci, shi ne alkhairi, Idan mijina yana bakin ƙoƙarinsa wajen kula da ni, to zan riƙe shi da kyau. Idan na bar shi, ban san wanda zan haɗu da shi ba, ba kowanne namiji ne zai iya daraja ni ba zan yi haƙuri na zauna da abina. Da dama daga cikin matan da ake ganin suna rayuwa cikin jin daɗi, lokacin da suka auri mazajensu ba su da komai. Sai bayan aure Allah ya buɗa musu. Ba zan fitar da rai daga rabona, arziƙi na Allah ne, kuma kowa rabonsa ba zai kauce masa ba. Ko ba a sami duniya ba, insha ALLAH za a sami mafi alkhairi a lahira. Zan kula da mijina, danginsa sun zama dangina, zan kama darajata mu rufawa juna asiri. Mu kula da juna cikin mutunci da biyayya.Rayuwa cikin tausayawa da kulawa da juna cikin soyayya da farinciki yafi na rayu cikin arzikin da babu kulawa bare nuna ƙauna." *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page1️⃣2️⃣ "Duk talaucin mijina zan yi haƙuri na zauna da shi cikin kwanciyar hankali da soyayya. Mijin wata bai fi nawa ba duk sunansu mazajen aure zan yi alfahari da nawa ko a ina ne, domin nawa shi ne nawa, mijin wata ba nawa ba ne. Zan zauna da nawa cikin nutsuwa da kulawa. Ba zan dinga hangen na wasu ko kallon irin abubuwan da yake musu, domin kowacce tana da nata jarabtar. Zan fito na nuna alfahari da nawa, kamar yadda wasu ke yi da nasu. Kila ma na fi su samun kulawa da soyayya. Talauci ba laifi ba ne. Amma ɓoye shi da zama cikin kima da mutunci shi ne alkhairi. Idan mijina yana bakin ƙoƙarinsa wajen kula da ni to zan riƙe shi da kyau, Idan na bar shi, ban san wanda zan haɗu da shi ba. Ba kowanne namiji ne zai iya daraja ni zan yi haƙuri zauna da abina. Da dama daga cikin matan da ake ganin suna rayuwa cikin jin daɗi, lokacin da suka auri mazajensu ba su da komai. Sai bayan aure Allah ya buɗa musu. Ba zan fitar da rai daga rabona arziƙi na ALLAH ne, kuma kowa rabonsa ba zai kauce masa ba. Ko ba'a sami duniya ba, in sha ALLAH za a sami mafi alkhairi a lahira. Zan kula da mijina da danginsa sun zama dangina. Zankama darajata mu rufawa juna asiri,zani kula da iyalanki cikin mutunci da biyayya. Rayuwa cikin tausayawa da kulawa da juna cikin soyayya da farin ciki yafi na rayu cikin arzikin da babu kulawa bare nuna ƙauna." Gabadaya kalaman ta ɗin sunana kashe wa Nasreen jiki, don haka ta ce. "Kina son sa kena?" "Ba sonsa nake yi ba, ina tausayinsa ne." "Kin tabbata iya tausayi ne kawai?" "Na tabbata don ba na jin komai a zuciyata game da shi, abu ɗaya na sani shi ne tausayinsa da nake ji a zuciyata." "Ke ce abar tausayi ba shi ba." Kafin ta fuskanci Ma'eesha da kyau ta ce. "Tausayi rabin soyayya ce, amma muje zuwa." Ta yi maganar tana ciro wayarta ƙirar iphone a cikin handbag ɗin ta. Sannan ta ce. "Ya maganar cousin brother na, da kika yi wa alƙawarin aure, kin dai san irin son da Abdul yake ma ki, ya ki kowace mace yanzu haka gobe zai dawo daga ƙasar Canada da mararin zuwa ganin ki, kin san kin yi ma sa alkawarin yana dawowa za ki gabatar da shi a wajen Daddy. Kin san ba kasar nan zai ajiye ki ba can ƙasar..." Dakatar da ita ta yi ta hanyar ɗaga ma ta hannu. "Ya isa haka nan Nasreen, ya za ki zo kina ma ni wani zancen tsohon saurayina bayan kin san cewa yanzu ni matar aure ce, ko mace ɗaya na auren maza biyu ne?" "Ba ta auren maza biyu kuma ina son na ceto rayuwar ki daga halakar da kike ciki ne, ki auri attajiri ɗan attajirai wanda ya mutu a ƙaunar ki wanda zai jiyar dake farin ciki da jin daɗi ba wai in da za ki zauna kika wahala ba. Look at you yadda kika koma a kwana ɗaya duk kin bi kin fita hayyacinki, nan da wata ɗaya ba za ki ganu ba. Na tabbata har yanzu ke budurwa ce ba abinda ya shiga tsakanin ki da wanann makahon don haka ki rabu da..." "Nasreen tashi ki tafi sai anjima." Kallon mamaki take yi ma ta kafin ta ce . "Ma'eesha ni kike kora daga in da kike, duk shaƙuwa da amincin dake tsakaninmu?" "Nasreen matukar kika cigaba da fadar mugayen kalamanki tabbas zan yi ma ki abun da ba ki yi zato ba. Na rungumi kundin ƙaddarata ban yi jayayya da hukuncin Allah ba na dogara gare shi kuma na san ya isar ma ni, kada ki sake yi Mani magana makamancin wannan, idan kuma ba haka ba za mu samu Matsala." "Ki yi hakuri Allah ya huci zuciyarki, me ya yi zafi, duk wanda ya ce zai haɗiye gatari ɓota zan riƙe ma sa." Daga nan suka shiga wata firar daban. Ganin rana ta yi ma'eesha ta ce. "Me zan girka ma ki ?" "Duk abin da ya samu." Tukunya ta wanke ta ɗira girki bayan ta fitar da gas din ta ajiye shi a baranda. Jallop ɗin taliya da dafa ma su wanda ya ji kayan lambu da bisashen kifi. A plate daya ta zuba ma su ta saka fork guda biyu. Ganin Ma'eesha ta dauko pure water ta zuba a plate ya saka Nasreen kai hannu ta taɓa. "Ya na ji ba sanyi?" "To a wane fridge zan saka ya yi sanyi? Ke ni fa duk yadda rayuwa ta zo ma ni haka zan rungume ta." "Bari na fita na nemo don wallahi ba zan iya ba." Tana fadar haka ta miƙe tana ficewa daga ɗakin. Ma'eesha ta rufe abincin tana jiran dawowarta. Zuwa can ta dawo bakinta ɗauke da sallama. "Assalamu alaikum." "Wa'alaiki Salam warahmatullah." Shigowa ta yi rike da bakin leda ta siyo bottle water guda biyar da maltina guda biyar ma su sanyi. Daga nan suka fara cin abincin. Bayan sun kammala ne sai ma'eesha ta kwashe kayan da aka ɓata ta je ta wanke su tas. Ita kuma Nasreen dama can a gidansu mahaifiyar ta ba ta saka ta aikin komai , sai dai ma su aiki su yi ma ta komai, don haka ba abun da ta iya. Ma'eesha kuwa wani lokacin Mahaifiyarta za ta ce ma su aikin su bari Ma'eesha ta yi saboda mace ce ita gidan wani za ta je wata rana. Bayan ta gama wanke-wanken ne ta saka ruwan ɗumi a wuta ta ke ta yi wanka, da ta fito ne ta ɗauara alwala don yin sallar azahar. Bayan ta idar Nasreen ma ta fito da niyyar yin alwala, yamutse fuska ta ji lokacin da ta ga banɗakin, duk da ba datti amma ita gani take yi ta fi karfin ta shiga wannan banɗaki. Alwala ta yi sannan ga shiga ɗakin, don ko da ta shiga har ma'eesha ta idar da sallah. Nan ta ba ta wuri ita ma ta yi sallar Mayyukan shafawarta ma ma su kanshi da tsada ta shafa. Sannan ta shafa turare sannan ta shirya cikin riga da siket na atamafa, ta yi daurin Ɗankwalinta mai kyau, ba ta yi kwalliya ba powder kawai ta shafa da man leɓe. "Hmmm yanzu ko kin yi kwalliya aikin banza ne fa, don da wani idanun zai gani ballantana ya yaba ya san cewa kin yi kyau." Tsuke fuska ta yi ganin haka ya saka Nasreen cewa . "Tuba nake yi. Ba zan sake ba." Daga nan ne wayar ma'eesha ya yi kara, bayan ta duba mai kiran ne sai ta katse kafin ta yi danne-danne a wayar kafin ta ajiye wayar gefe. Daga nan suka ci gaba da fira, sai wayar Nasreen ta yi ruri. Gani. Mai kiran ya saka ta yi Murmushi tana cewa . "Barka da warhaka yallaɓai." Daga cikin wayar ta ji muryarsa yana cewa. "Barka dai ya kike ?" "Lafiya lau Alhamdulillah. Tun jiya nake kiran lambar ƙawarki tana ringin ba ta ɗaga wa, sai na sake kira na ji a kashe, yanzu ma na kira ba ta ɗaga ba da na sake kira ina zato ma ta ji blocking ɗina ne. Kuma saboda ita zan shigo ƙasar gobe, da ba don haka ba sai nan da watanni uku zan dawo ƙasar." "Yaya Abdul ka yi haƙuri da Ma'eesaha kawai." "Ban gane ba, ko dai ta samu wani ne ta yar da Ni?" "Hmmm." "Ban gane hmmm ba talk to me." Ya ji maganar cikin wata irin murya mai cike da karaya. "Ma'eesha ta yi aure jiya, don haka ka zauna ƙasar Canada ka gama abun da ya kai ka." "Ke b na wasa da ke kada ki fara yi a yanzu." "Ba karya nake yi ma ka ba, wallahi wallahi da gaske nake yi ta yi aure." Wani sauti ta ji daga cikin wayar kafin ta ji shiru. Cikin sanyin jiki ta ajiye wayar tana mai tausaya wa cousin brother nata. Dan ba ta mance wa sanadin ta ya haɗu da ma'eesha. Wata rana da ya kammala karatun master digiri ɗin sa ya dawo ƙadar ya biyo gaida mahaifiyar Nasreen nan ta ga Ma'eesha ta zo wajan Nasreen ya nuna yana son ta, ita ma ta amince ma sa suka fara soyayya da Abdul. "Wai yana kiran wayarki baya shiga." "Eh na yi blocking ɗin sa ne. Don bai dace na dinga waya da shi ba." "Allah ya kyauta." Da Amin ma'eesha ta amsa ba tare da ta kalle ta ba, kanta a sunkuye da alama tunani take yi. Da misalin karfe huɗu saura kwata ya shigo da sallama a gidan. Gabadaya suka amsa ma sa, Muryar mutane biyu da ya ji ya tabbatar ma sa cewa ma'eesha ta yi baƙuwa. Yana rike da sandarsa ta jagora Da hannu daya ɗaya hannun kuma yana rike da basket da ma su gyaran takalmin ke yawo da shi. Ya ɗaura wani bakin leda a saman kayan aikin." "Sannu da dawowa." "Yauwa Ma'eesha sannu da gida. Baƙuwa kika yi ne?" "Eh ƙawata ce sunan ta Nasreen." Nasreen ta zuba ma sa idanu tana ƙare ma sa kallo. Tabbas makanta ce kawai cikas ɗin sa sai kuma talauci domin da ace na makaho ba ne kuma ba talaka ba ne za ta iya cewa ƙawarta ta yi mijin nuna wa Sa'a. Domin kuwa ya hadu iya haɗuwa ta ko ina baya da cikas, don ba za'a hada shi da Abdul ba, domin ya yi ma sa zarra nesa ba kusa ba ya fi shi duk wasu qualities da macen da ta san kanta za ta bukata daga wajen ɗa namiji. Taɓa ta da Ma'eesha ta yi ne ya saka ta dawo duniyar tunanin da ta lula. Jin muryarsa mai amo ta yi yana cewa. "Sannu da zuwa ina wuni." "Lafiya lau ya ƙokar" "Alhamdulillah." Ta amsa tana ɗauke kai daga kallonsa. Ma'eesaha ta karbi kayan hannunsa ta shiga cikin ɗakin, da lalube shi ma ya shiga ya zauna jan tabarmar da ya ji ya taka. "Sannu da dawowa ya rana?" "Sannu da imani Ma'eesaha, ya hakuri da rayuwa?" "Alhamdulillah." "Ba ri na kawo ma ka abinci ko?" "A'a sallah zan yi . Sai na dawo masallaci." Ya yi maganar yana ciro ledar da ya dawo da shi. "Ga tsarabar yalo na kawo ma ki ko za ki iya ci?" "To na gode Allah ya kara budi." Cike da jin dadi ya amsa duk da ya san ba cimar su ba ne, ba Apple da ta saba ci ba ne. Tashi ya yi tana cewa. "Na ba ka buta ne?" "Eh na gode." Suka fito ta miƙa ma sa buta cike da ruwa. Ya sa ya nufi banɗaki ya shiga. Bayan ta fito ne ta damu wuri a gefe ya yi alwala ya fice zuwa masallaci. Ledar yalon ta buɗe ta zuba a mazubi ta wanke, sannan ta dawo da zauna kusa da Nasreen tana cewa. "Ƙawata ko kin iya ci?" Taɓe baki ta yi kafin ta ce. "Ai ko ke ba ki iya ci ba ballantana ni." Daga haka ta cigaba da danne-danne a wayarta. Ma'eesha ba ta sake bi ta kanta ba ta ɗauki guda ɗaya ta kai baki. Ɗaci da ta ji ne ya saka ta ɗan yamutse fuska sannan ta haɗiye. Nasreen na kallona ta gefen idanu ba ta ce komai ba, zuwa can ta mike tana cewa. "Zan tafi gida sai wani lokacin." "To na gode ki gaida su Mom don Allah." "Za ta ji." "Ba za ki tsaya ki yi sallar la'asar ba." "Idan na je gida zan yi." Tana tsaye bakin ƙofar tana kallon Nasreen har sai da ya ga tashin motarta sannan ta saki kofar ta koma ciki. Buta ta ɗauka ta shiga banɗaki ta yi tsarki sannan ta fito ta daura alwala. Tana alwala tana jin muryarsa mai amo yana rera karatun sallah a masallacin, da alama shi ne liman ɗin. Bayan ta idar da alwalar ta shiga dakin ta gabatar da sallar la'asar. Addu'o'i ta yi ta yi azkar na yamma daga nan ta kwanta a saman sallayar. Bayan kamar mintuna talatin ya shigo gidan da sallama. Da lalube ya kai bakin kofar ya yi sallama ta amsa tana tashi zaune. In da ya saba zama ya laluba wato kan tabarma ya zauna tare da Bismillah. "Ƙawarki ta tafi ne?" "Eh ya tafi." "Allah sarki, Allah ya kai ta gida lafiya." Maltina da ruwa ta ajiye gabansa ta ce. ,Ga Maltina nan da ruwa na ajiye ma ka, bari na kawo abinci." "To na gode amma ki bar abincin nan, sai zuwa dare." "Me ka ci da rana." "Ba komai dama ni ban saba cin abinci sau uku ba, sau biyu nake ci wata rana ma idan ban samu sau biyu ba idan na ci na rana zuwa dare ruwa kawai zan sha na kwanta." "Wanan ya wuce yanzu akwai sai ka ci idan babu ne sai ka san cewa babu ka yi hakuri. " "Ba na jin yunwa bari na sha wannan kawai kada ku damu." Daga nan ba ta sake magana ba ta koma ta kwanta a saman sallayar. "Bari n je na yi wanka." "Okay bari na zuba ma ka ruwa na kai ma ka." "Don Allah ki huta na gode, zan iya ɗiba da kaina, ai na gama sanin kan gidan, bayan kin ke kasuwa ai har fita na yi na dauko jakar kayana. Na san komai na gidan nan, ba na bukatar ki yi ma ni wani aiki sai dai ni na ji ma ki." "Ai lada nake nema kuma aljannata nake nema." "In dai Aljanna ce in sha Allah za ki shige ta Ma'eesha, Allah ya yia ki albarka ." Da Amin ta amsa ta koma ta kwanta. Bayan ya ɗebi ruwa ya kai banɗaki ya dawo wajen kayansa zai ɗauka, kasancewar ya san shi ba ya gani ita kuma tana ganinsa ba zai iya cire kaya a gabanta ko ya canza ba, don haka ya dauki kayan da zai saka da sabulu ya fita ya je banɗaki da su. Bayan ya yi wanaka a banɗaki ya goge jikinsa ya sauka kaya ya fito bayan ya zuba wanda ya cire a cikin bokitin wankan . Ruwa ya ɗeba ya sa ido ya wanke kayan ya shanya. Sannan ya koma dakin, ta daga kai ta kalle shi ta ga ya sauya kaya. "Ina kayan da kika cire na wanke ma ki?" "Ka bar shi na gode." Duk da dama tana tunanin wanki na ba ta wuya, don ba ta saba ba sai dai a wanke ma ta, ma su wanki ke wanke ma ta. Ko underwears ɗinta a warahing machine take wanke wa . Idan na cire, yau dai ta wanke underwears ɗinta banɗaki da ta cire bayan ta ji wanka. Lalube ya fara yi ganin ya matsa ta ce ba basket da ta zuba nan bayansa, ta dauka ta fita bayan ta bashi sabulu, ya je ya wanke ma ta su y shanya ma ta kayan. _Sidra_farkawar ta kenan daga barci ta farka da kuka, sakamakon mafarkin da ta ji wai an kai Nadra gidan Fahad da ya gina da sunanta, irin tsarin da take so, kuma ga kayan ɗaki da kayan kitchen ɗin da aka je aka zuba da sunan ta sun zama mallakin Nadra. Da kanta ta nuna wa Umma irin funitures da take so aka yi order daga ƙasar waje, sannan Abba ya ba ta kudi je Dubai ta siyo irin kayan kitchen da take so, yanzu shi ke nan an mallaka wa Nadra kayan kitchen ɗin ta da kayan ɗakinta da kuma mijinta.? "No ba zai yiwu ba wallahi, na san wannan duk aikin Ammi ce ita ce za ta ziga Abba akan ya ƙwace komai nawa ya ba Nadra. Dama ba ta ƙauna ta kullun cikin zagina take yi wai ni ba na da kunya da tarbiyya kullum Nadra ce ya yarinyar kwarai a wajen kowa wannan karon zan nuna kowa rashin tarbiyyar da suke kira. Mani za su gan shi muraran kuma ziryan, wallahi ba zan yi biyu babu ba, ba zan rasa burina da nake da shi ba sannan kuma na rasa mijin da nake so ba, ba zan yi biyu babu ba wallahi sai dai ayi mutuwar kasko." "Ba ni wayarki.." Ta yi maganar tana kallon Sady baby, ta mika ma ma ta wayar ta shiga TikTok account ɗin abokin Fahad Sadik. Na ci karo da videos ɗin bikin Fahda da Nadra. Da in da yake ba ta cake daga bakinsa zuwa na ta, rintse idanunta ta yi tare da kokarin cilli da wayar sai Sady baby ta yi saurin karbe wayarta. Don ta san idan ran Sidra ya ɓaci idanunta rufe wa yake yi. Ta fama hannunta dake zubar da jini tana cewa. "Wallahi ba zan haƙura da Fahad ba, domin nawa ne shi ni kaɗai, ruwa da iska ba abinda zai ma ni shamaki da abun so na ciki kuwa har da ita Nadra, zan iya aikata ma ta komai don na mallake sa." Kallon ta da tsoro Sady baby take yi kafin ta ce. "Ko da hakan na nufin bakin cikin ƙanwarki ce?" "Ko da hakan na nufin mutuwarta ne." Ganin yadda take zubar da jini ya saka Sady baby kokarin taimaka ma ta, amma ta fisge hannunta tana cewa . "Sai na aikata abinda ke raina in dai akan Fahad ne?" "Na sani Sidra za ki iya, ko me kika ce za ki aikata na san za ki iya. Amma ba ki ga yadda kike zubar da jini ba ne?" *Maman Ihsan ce.*✍️ 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page1️⃣3️⃣ "Na sani Sidra za ki iya, ko me kika ce za ki aikata na san za ki iya. Amma ba ki ga yadda kike zubar da jini ba ne?" "Ban damu da jinin ba, kuma bam ji zafin hakan ba, amma kuma abinda aka yi ma ni na raba ni da Fahad shi ne ya fi yi ma ni zafi." Nan ta dinga rarrashinta sosai da ba ta baki har ta hakura ta yi shiru da surutun nata. "Ba ni wayata." "Me za ki yi da ita, bai kamata ki kunna waya yanzu ba." "Ina bukatar jin Muryar Fahad." "Kada ki kira shi da wayarki, domin kuwa ba mu san abun da za mu ce ya faru da ke ba har kika bar gida. Ki kira shi da wata lambar don gudun tonuwar asiri ki." Ta yi magana tana mika ma ta wata karamar waya a hannun ta. Karba ta yi ta saka lambar wayar Fahad kasancewar tana da lambar wayarsa a cikin kanta . _Fahad_ Driving yake yi zuciyarsa babu daɗi, sam bai taɓa kawo ranar nan da za ta zo ba wai zai tare a sabon gidansa ba tare da Sidra ba. Yana driving ɗin kamar wanda zai ɓalle sitiyarin motar. Saboda yadda ya rike shi da ƙarfi, har yanzu ya kasa gane dalilin da ya saka Sidra ta aikata haka bayan ya san tana tsananin son sa. Wayarsa dake gefe ya kalla da idanunsa da suka canza launi zuwa ja ya yi, ganin baƙuwar lamba ce ya saka bai ɗauka ba. Sidra dake jiran ya dauka ko ta ji muryarsa ta cire wayar daga kunnenta don ta san ba lallai ne dama ya dauka ba. Sai da ta yi masa 3 missed call bai ɗaga ba, sai a na huɗun ne ya ɗaga wayar na ajiye ya yi picking call ɗin ba tare da ya yi magana ba, yana jiran me kiran ya yi magana. Jin shiru ya katse wayar don ita ma Sidra ta ƙi ta yi magana. Dama shi haka yake in dai bai san me kira ba to ba zai yi magana ba sai dai ya katse kiran wayar. Hawaye ne suka wanke ma ta fuska ta juya ta kalli ƙanwarta ta ce. "Kila yana can tare da ƙanwata ko? Me yiwuwa ma yana nanne da ita? Kuma zai iya yin sex da ita ko?" Sai a lokacin Sady baby ta yi magana ta ce. "To me zai hana shi yin sex da ita tunda matarsa mallakinsa ce kuma an kai ma sa ita har gida, ai ba kowane lafiyayyen namiji zai iya

Chapter 9 of 49