Share this page
zuwan na Baba ba, saboda ya san Umma za ta tayar da hankalinta. Don haka a ɓangaren baƙi ma ya sauke Alhaji Umar Majidaɗi. Duk wani motsi na Sidra Abba na lura, domin ya san wace ce Sidra shi ne mahaifinta. Ya fahimci duk wannan kukan wasan kwaikwayo ne, ba ta yi nadama ba murmushin da ya fi kuka ciwo ya yi lokacin da ya ga tana murmushi. Ita kuma ba komai ya saka ta yin murmushi ba, sanin cewa za ta koma Familyn Majidaɗi, dole ne ta samu kusanci da Fahad da familynsa. Haka Baba ya dawo da ita gidansa, ya yi wa iyalansa bayanin yadda suka yi da Abba. Ya ce Sidra za ta ci gaba da zama a gidan ba wani lokaci har zuwa Allah ya sazuciyar Abba ya yi sanyi. Ya kuma nuna ma su yanzu an zama daya kasancewar ko ba abota yanzu akwai surukantaka aure ya haɗa an zama dangi. Ga Nadra nan tana matsayin sirikar gidan kuma Sidra yarta ce. Haka rayuwa ta cigaba da gudana a cikin gidan, Sidra ta saki jiki da Nadra ta ja ta a jiki sosai, ta nuna ba komai yayin da ta gama duk wani shirin da za ta aiwatar dawowar Fahad kawai take jira don ta aiwatar da shirinta. Don yadda take jin haushin Nadra da kishinta yanzu ta daina ji. Don ta lura kamar Nadra ba ta gaban Fahad bisa la'akari da ko kiran wayarta baya yi. Ko messages baya tura ma ta, hakan ya sa ta ji sanyi a ranta tana ganin ai ba ta gabansa. Saboda kullun sai sun yi waya da ƴan gidan, wata rana ma video call suke yi, zai gaisa da Mama, Baba, Inna, Rumaisa, da Farida. Ko tana Wajen ba zai taɓa cewa a ba ta waya ba, kuma ba zai taɓa tambayar ta ba. Hakan na damun Mama amma ba ta taɓa yi ma sa Magana ba ta zuba ma sa idanu, ta san ta in da za ta kama shi. Ita kanta Nadra hakan na ma ta ciwo a zuciya, duba da yadda ya yi ma ya ya saka kafa ya bar ƙasar bayan ya san tana cikin mawuyacin hali, bai taɓa tambayar ta ya jikinta ba ballanta ya yi ma ta sannu. Amma tana addu'ar Allah ya dawo da shi lafiya za ta ba shi mamaki. Haka take ta rayuwa a gidan ba tare da ta nuna tana da damuwa ba. Ga kayan gyaran jikin da Sunyi Rahama ta kawo ma ta Inna tana sa ma ta idanu don ganin tana amfani da su. Sabulai ma haka da su take amfani har da man shafawa. Hakan ya sa ta yi kyau fatar jikinta sai ƙyalli take yi ta yi kyau kamar ba ita ba, baƙar fatarta dama mai kyau ne sai ta kara kyau. Sai dai abin da ba ta sani ba duk abin da take yi akan idanunsa take yi, don yana kallonta daga can in da yake. Idan ya dawo yana zaune baya komai zai yi ta aikin kallonta, duk abinda take yi. Yana mamakin yadda ta yi kyau ta canza kamar ba ita ba. Haka zai shagala yana kallonta, musamman da yawan tunanin yarinyar ke addabar sa. Haka nan kawai begen ganinta yake yi da son jin muryarta, Mama jin kansa ya hana ya kira wayarta ko ya ce ba ta waya su yi magana. Amma tunanin tariyar ya hana ta sukuni. *BAYAN WATA UKU* Ana gobe Fahad zai dawo ƙasar ne ya kira waya ya sa Mama ta sa ma'aikata su je su gyara ma su gidansu. Mama ta gama sauraren sa tana kare da waya a kunnen ta kafin ta ce . "Yaushe kake so a gyara ma ka gidan?" "Yau nake so, sanan Rumaisa ta bi su ta gyara ma na bedroom." Shiru kawai Mama ta yi tana tunanin yadda za ta ɓullo ma sa akan halin ko in kula da ya nuna wa Nadra. _Ma'eeaha_ Tana zaune gaban murhun gawayi ta haɗa tagumi, tunanin ta a abun da za su saka wa cikinsu take yi. Tun jiya ba su da abincin da za su ci, kuma ba su da kuɗin siye. Don hatta gawayin da za ta kunna babu ya ƙare. Tashi ta yi ta shiga ɗaki ta dauko farar leda sosai wacce suka siye garin kwaki rabin mudu. Shi suka sha jiya daddare suka kwanta. Yau da safe suka sha koko wanda ko sugar babu. Garin ta ɗiba a kofi ta ɗauki ɗaurin gyaɗar hamsin da ya rage, ta raba gyadan gida biyu ta ɗauki rabi sannan ta ƙulle sauran. Bayan ta jiƙa garin ta zuba gyaɗa tana sha tana ɓata fuska kamar mai shan magani. Sallamarsa ta ji yo daga ƙofar gida bayan ta kammala shan garin. Ta amsa ma sa tana yi masa sannu da zuwa. Ya shigo gidan hannunsa ɗaya rike da sandarsa dayan hannun kuma rike da basket kayan gyaran takalminsa. "Sannu da zuwa." "Yauwa ya gidan?" "Alhamdulillah." "Ma sha Allah." Karɓar kayan gyaran takalminsa ta yi ta ajiye gefe. Sannan ta ɗebo ma sa ruwa ta ba shi ya sha. "Ya kasuwan?" Ta tambaye shi tana kallon kyakkyawar fuskarsa. "Alhamdulillah zan ce, amma yau kam ma kamar jiya, ko mutum ɗaya bai kawo gyaran takalmi ba haka ba gaji da zama na dawo." Murmushi ta yi tana cewa. "Ba komai, kada ka damu duk abin da ba ka samu ba to ba rabonka ba ne, Allah ya kara ma na wadatar zuciya." "Amin Ma'atussaliha Allah ya yi ma ki albarka." "Amin mijina." Sauran garin rogo da ta rage ne nake sha bari na jika ma ka naka." Jinjina kai kawai ya yi ba tare da ya sake magana ba, amma kallo ɗaya za ka ma sa ka gane cikin damuwa yake. Garin ta jika ma sa ta kawo ma sa bayan ta zuba ma sa sauran gyaɗa. Bayan sun gama sha ta ce . "Dama ina son na sanar da kai an kwantar da mahaifiyar Rumaisa asibiti, idan ka amince zan je na duba ta." "To bari na yi wanka sai mu tafi tare." Ya fadi haka yana miƙewa tsaye. Ta zuba ma sa ruwan wanka ta kai ma sa banɗaki.. Kofuna da suka yi amfani da shi ta wanke ta koma ta zauna. Tana nan zaune kan tabarma har ya fito wanka ya shiga ɗakin, sai da ta tabbatar ya shirya ta shiga da sallama. Kayan jikinta take kokarin ragewa lokacin da ya fice daga ɗakin. Yana zaune a barandar kofar ɗakinsu rike da sandar jagoransa, ta fito ta yi wanka cikin sauri ta shirya cikin doguwar rigar Abaya mai ruwan toka, ta yi rolling kanta da mayafin. Fitowa ta yi hannunta rike da wayarta. "Na shirya yallaɓai." "To ranki ya daɗe." "Ka san ba mu da kuɗin abun hawa ko?" "Ba damuwa zan iya tafiya a ƙafa ke nake tunani." "Mu je ai ba mu da nisa da asibiti. Amma fa ka ajiye sandar nan zan rike hannunka har mu tafi." "To ba Kya jin kunyar idanun mutane?" "To ba mijina ba ne?" "Eh haka ne, amma ai su iyayen ƙawarki fa?" Ɗan jim ta yi kafin ta ce. "To rike sanadarka mu tafi." Ta yi maganar tana dariya. A tare suke tafiya gwanin sha'awa, har suka kai asibitin kasancewar ba su da nisa da Asibitin da unguwar su. Kasancewar Nasreen ta yi sanar da ita in da aka kwantar da mahaifiyarta ya sa ta nufi wajen kai tsaye. Mahaifiyar idanunta biyu Nasreen na ba ta magani tana sha. Sai wasu mata guda biyu. Da ƙawayen Ma'eesha su uku. Sai kuma mahaifin Nasreen. Bayan sun gaishe su tare da yi ma su ya jiki suka amsa cikin dakin fuska. Kasancewar duk sun san Ma'eesha kuma sun ji labarin auren nata da makaho. Don haka suka zuba ma ta idanu suna yi ma ta kallon tausayi. Khalifa ya ma su sallama ya fice yana jiran Ma'eesha har sai ta fito su tafi. Ganin kallon da ake ma ta ya sa ba shiri ta yi masu sallama za ta tafi. Mahaifin Nasreen ya ba ta 10k ta ki karba sai da ya nuna ɓacin ransa ta amsa tana godiya. Ta yi farin ciki da kuɗin kasancewar ba su da kudi ba su da abinci. Ko da ta sanar wa makaho ya ce Allah ya saka da alkhairi. Bayan fitowar su daga cikin wata ɓakar mota ta fara bin bayan su. A hankali motar ke tafiya tana bin su, sai dai matukin motar ya yi parking motar ya fito yana bin bayansu, kasancewar hanyar da suka bi mota ba za ta iya bi ba, don hanyar tafi sauri ya sa ba su bi titi ba. Sai dai hanyar ba mutane sosai. Idan sun ɗan yi tafiya kadan makaho sai ya tsaya. Kafin ya cigaba da tafiya. Ita dai Ma'eesha ba ta ce komai ba. Daidai lokacin da wani mai keke nape ya biyo ta gabansa. Makaho ya sa hannu ya tare shi, sai ya tsaya yana cewa. "Ina za ku je?" "Ma'eesha ki shiga ya kai ki gida." Da mamaki ta kalle shi kafin ta ce. "Kai kuma fa." "Kada ki damu zan kula da kaina." "Ba zan bar ka kai kaɗai ba." Tsawo ya daka ma ta yana cewa. "Na ce ki shiga!" Yadda ya daka ma ta tsawa sai da ta firgita ba ta san lokacin da ta shige ba. Tana shiga ya yi wa mai nape alama da hannu ya tafi, take ya ja keken suka bar wajan. Suna tafiya ya cire baƙin glass ɗin dake idanunsa ya juya bayansa cike da karsashi yana jifan mutumin da ke bin su da wani mugun kallo wanda da sai da hantar cikinsa ta kaɗa. Baya ya fara ja kafin ya juya zai gudu, tsalle ɗaya Makaho ya yi ya dira a gabansa. Shaƙo wuyansa ya yi cike da ƙaraji yake cewa . "Kai har kana da zarrar da zan ka dinga bibiya ta?" Idanunsa sun firfito waje saboda shaƙar da ya yi ma sa. Daidai lokacin wayar mutumin dake gaban aljihun rigar suit ɗin sa ta fara ruri. Sake shi ya yi sannan ya zaro wayar dake gaban aljihun suit ɗin mutum yana kallo. MADAM shi ne sunan da ta bayyana akan screen din wayar. Amsa kiran wayar ya yi sannan ya yi ma sa da alama ya yi magana. Kafin ya yi maganar suka ji muryar me kiran na cewa. "Ka ga fitowan su daga asibitin ko har yanzu suna ciki, sannan na ce ka yi mani bincike akan yarinyar da ka tura ma ni photon su kwanaki ta rike ma sa hannu suna tafiya, meye a tsakanin su, kuma shi da yarinyar ne yau ma suke tare ko wata ce daban?" "Duk ita ce Madam." Ya yi maganar yana kallon idsnun makaho. "To ka tabbatar daga yau zuwa gobe ka samu duk wasu bayanai kafin ka bar garin nan." Cike da ɓacin rai da takaici makaho ya cije leɓansa na kasa wanda sai da ya Fahe jini ya fito." *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page4️⃣9️⃣ Cike da takaici da ɓacin rai da takaici makaho ya cije leɓansa na ƙasa wanda sai da ya fashe jini ya fito. Sannan ya saka hannu ya katse kiran wayar mutumin. "Duk wani shirin ku ina sane da shi, kuma duk bibiya ta da kake yi na sani, daga kai har sauran mutanen da suke bibiya ta na san komai, ni ba shashsha ba ne. Wato har ka tura ma ta da photon mu ko?" Shiru ta yi yana kallonsa da idanun sa da suka kaɗa suka yi ja. "Wato kai ne me zarrar da kake bibiya ta ko? Har ja ɗauki photon mu ka tura da shi ko? Akan aikina ma sai an saka ma ni idanu ?" Cike da tsoro mutumin yake kallonsa, ganin da ya yi ya ma sa kama da mayunwacin zaki. "Idan har kana son rayuwarka da ladiyarka to ka fita daga cikin wannan sabga, domin kuwa shine zamanka lafiya, idan ba so kake yi na binne ka da ranka ba. Idan kuma kaƙi ji ka cigaba da bibiya ta ko yarinyar da ka ganni da ita , sannan ka nemi sanin alƙar da ke tsakanina da yarinyar ka sanar ma na ta to fa ka sani shi ne kuskure mafi muni da za ka tafka a rayuwarka." "Ka gafarce ni yallaɓai ni ma umarni nake karɓa ba yin kaina ba ne." Cikin ƙaraji makaho ya ce . "Shi ya sa na ce ma ka ka daina." "Ba zan iya ba yallaɓai domin ina dai akan Madam ne raina fansa ne a gare ta." Wani gajeren murmushi makaho ya yi kafin ya ce . "Shi ke nan za mu gani." Ya yi maganar yana saka ƙafarsa ɗaya ya kwashe ƙafafuwan mutumin wanda hakan ya saka ya zube a saman guiwoyinsa da ƙarfi, wanda sai da ya saki wata ƙarar azaba, don ji yake ba yi kamar guiwoyinsa sun daina aiki." Makoho yana huci ya bar wajen, yana mai mayar da baƙin glass din sa ya ɗauki sanadar jagoransa ya fara tafiya yadda makafi ke yi. Tun mutumin na ganinsa har ya ɓacewa ganinsa, har lokacin ya kasa miƙewa ya tashi. _Ma'eesha_ Sam hankalin ta ya kasa kwanciya, ganin yadda makaho ya shi ne ya daka ma ta tsawa cikin wata iriyar Muryar da ba ta san yana da ita ba. Da ba ita ya yi wa ba ko ba a gabanta aka yi ba da sai ta ce ba Khalifa mijinta ba ne ya yi ma ta wannan tsawar. Don za ta iya cewa ko mijinta ko yatsa aka saka ma sa a ba su ki ba zai an iya cikawa ba, amma yau ta ga a abun da ya ba ta mamaki sosai ba kadan ba. "Hajiya ina za mu je ne?" Ta yi zurfi cikin tunani sai da ya sake magana sannan hankalinta ya dawo jikinta, ta sanar da shi in da zai kai ta, don dama ba su da nisa da Asibitin da suka je. Bayan ya sauke ta ƙofar gida ne cikin kudin da mahaifin Nasreen ya ba ta ciki ta ba shi dubu ɗaya, ya ba ta canji ɗari biyar kasancewar ita kadai ya ɗauka. Ƙofar gida ga nufa ta bude kofar langalangan su ta bude . Ta shiga gidan bakinta dauke da sallama. Zama ta yi saman barandar ɗakin ta haɗa tagumi. Tana jiran shigowarsa. Jin shiru ne ya sa ta kira wayarsa don ta ji lafiyarsa amma sai ya kasance wayar na gida. Don ta ji sautin wayar a cikin ɗaki. Hankalinta ya kasa kwanciya tuna kwanakin baya an sami waɗanda suka yi garkuwa da shi, cikin ikon Allah ya kuɓuta. Har ta ji an kira sallar Magrib sannan ta tashi ta yi alwala ta fara gabatar da sallah. _Makaho_ Da Kafa ya ƙaraso unguwar yana tafiya yana saƙa abubuwa da yawa aransa. Yana shigiwa unguwar ana kiran sallar Magrib, don haka ya tsaya ya gabatar da sallar Magrib a cikin jam'i a masallaci ya yi sallah. Bayan an idar jama'a sun fara watsewa me Mallam Liman ya karasa gaban Makaho. "Assalamu alaikum Mallam Khalifa." "Wa'alaikium Salam Mallam Liman kai ne?" Liman ya mika masa hannu akan su yi masabaha. Bayan sun gaisa ne Mallam Liman ya bar Khalifa zaune, har lokacin ɗaxu yake ji. A ransa. Don haka ya fara karatun alƙur'ani mai girma. Kuma ya ji sa'ida a cikin ransa, don kaso hamsin na baƙin cikin da yake fama da shi ya ragu. Bayan an yi sallar Isha'i ne ya tashi ya nufi hanyar gida. Da sallama ya shiga cikin gidan. Ma'eesha dake zaune kan sallaya ta fito da sauri tana kare ma sa kallo. Kasancewar akwai wutar nepa. Hannayen sa duka biyu ta rike tana cewa. "Kana lafiya ko? Me ya faru ne ka ce na dawo kai na ga ka tsaya? Bayan cewa a tare suke tafiya kafin y aikata wannan abu . "Kada ki damu kawai na tausaya ma ki ne ya saka na yanke shawarar je ki Hau keke nape ni zan je da ƙafa. "Amma me ya sa za ka wahalar da kanka bayan akwai kudi a hannuna?" "Kada ki damu na dawo cikin ƙiahin lafiya. Don a masallacin unguwar nan ne na yi sallar Magrib sa Isha'i. "Alhamdulillah." Ta faɗa tana ja ma sa hannu suka shiga cikin ɗakin. Bayan sun zauna a tabarma ne ta kalle shi tana yi ma sa sannu. "Ka san ba mu da abinci a gida nan , lokacin da na dawo gidan ba na da nutsuwa da na girka ma na wani abun. Amma yanzu bari na siya indomiee na girka ma na zai fi sauki." "Sannu da ƙoƙari Allah ya ma ki albarka." Sai a lokacin ta lura bakin Khalifa ya fashe. Cikin tashin hankali ta kai hannu ta kan fuskarsa tana cewa . "Subhanallah me ya same ka ne?" "Kada ki damu ina cikin ƙoshin lafiya. Kamar za ta yi kuka ta ce. Bakinka da ya kumbura." "Eh ba damuwa ba zafi ai, hakori na ne ya ya datse leɓen." "Haba mijina kamar ƙaramin yaro ne mai z ka datse baki haka?" Bai ce komai ba, ita ce ta tashi tana cewa ina zuwa yanzu xan dawo." "Ina za ki je a daren nan." "Zan siyo indomie ne nan shagon waje." Jinjina kai kawai ya yi ba tare da cewa komai ba.. _Nadra_ Tana zaune a part ɗin Fahad kamar yadda ya bar ta har tsawon wanan lokacin ita ke rayuwa a ɓangaren. Kasancewar ta har yanzu ta kada sake wa da mutanen gidan sosai. Tana yi ma su kallon surukai take yi ma su. Sallamar Mama ce da Aunty Rahama suka shigo falon. Bayan ta amsa ma su sallama. Ba ta yi mamakin ganin Aunty Rahama ba kasancewar ta ji ana firan daowarasa kuma sai shirye-shirye ake yi a cikin gidan. Gaishe da Mama ta yi ta amsa sannan ta gaida Aunty Rahama. Ita ma ta amsa tana ƙara jinjina kayan gyaran jikin da take kawo ma ta. Mama ta kalli Aunty Rahama tana cewa. "Ki tabbatar da ta tattara komai na ta an mayar da su ɗakina, sannan ita ma ta biyo ki kamar yadda na ce." "To Mama, ki ɗan turo ma na daya daga cikin ma su aikin nan ko da Laraba ce ta zo ta taya mu kwashe kayan." "Kin san baya son ma su aiki na shigar ma sa ɗaki ko?" "Eh ta tsaya ƙofar falo." "Okay." Mama ta amsa tana fita. Aunty Rahama ta kalli Nadra ta ce. "Yar gatan Mama, Mama ta ce ku tattara komai na ki za ki koma ɗakinta da zama. Ki yi Sauri za mu fita." Cikin fadin ciki Nadra ta fara tattara duk abin da ta san nata ne." Aunty Rahama ta fara fita da akwatunan kayan tana kai wa bakin kofar falo,sai Laraba ta dinga ɗauka. Sai da suka gama fitar da komai sannan Laraba na kashewa tana sauka da su sannan suka fito. Kai tsaye ɗakin Mama suka nufa suka tarar ta jera akwatunan a in da ya dace Da sallama suka shigo Mama ta amsa sannan ta ce. "Ya kamata yanzu ku tafi ko?" "Eh Mama yanzu za mu tafi." Ta juya tana kallon Nadra kafin ta ce . "Ƙanwata shirya za mu je gyaran gashi kuma ayi ma ki lalle." "To Aunty Rahama na shirya hijabi kawai zan saka." "Okay saka mu tafi." Dogon hijabinta ta saka, kasancewar yanzu ta daina saka dogon hijabin da ta saba sakawa a gida. Hakan ya faru ne saboda taimakon Aunty Rahama don sai da ta yi da gaske sannan Nadra ta daina yawo da hijabi a gida. Don gara ta dinga bayyana adonta ga mijinta ba kullum zama da hijabi kamar mai takaba ba. Bayan ta shirya suka fita tare, a motar Aunty Rahama suka je. Gidan sai ƙamshi girke-girke ake yi na tarbar Fahad. Bayan kamar awanni biyu da fitar su ne suka dawo gidan. Bayan an tsara wa Nadra Lalle me kyau zaben dukawar baƙi da ja aka yi ma ta. Dai gyaran gashi kasancewar ba ta cika son kitso ba ita. Sosai ta yi kyau ga gashin ya zubo sai sheƙi da wani kanshi take yi. Wanka ta yi addu'a lokacin da ake kokarin zuwa ɗauko shi a airport. Da taimakon Aunty Rahama ta shirya tsaf, cikin wani tsadadden leshi ɗinkin riga da siket ya ɗan kama ta, ya zauna ɗagwas a jikinta. Ta so saka Abaya Amma Aunty Rahama ta hana ta ce ta bar shi wanan ya fi ɗaukar hankal, kuma ba kowane namiji a gidan. Dole ta bar shi. A don ranta ya so ba . Wani turare ta fesa ma ta a jiki wanda shi na musamman ne. Horn suka ji daga bakin gate wanda hakan na nuna sun iso, Rumaisa da Farida suka je tarbon sa,. A tare suka fito daga bayan motar sun saka shi a tsakiyar suna ta farin ciki. Mama da Sidra ne a falon suna farin ciki da shigowarsa. Sidra ma ta ci kwalliya cikin dogon rigar atamfa ɗinkin fitted goun ɗinki ya matse ma ta jiki. Yana shigiwa suka mike tsaye ya karasa ya Side hug ya yi wa Mama sannan ya karasa wajen Inna dake zuwa ita ma ya yi ma ta yana dariya. Sidra ta gaishe shi ya amsa a yabo ba fallasa. Sannan ya nufi part ɗin sa da tunanin ko Nadra na can. Su Rumaisa suka bi shi da kayan part ɗin sa suka ajiye a falo. A tunanin sa Nadra na bedroom amma ya ga ba ita ba komai nata. Bincike ya yi a CCTV camara ya ga komai. To ina suka kai ta ko dai tana sabon gidansa ne da aka gyara jiya. Da wannan tunanin ya yi wanka ya fito, shirya wa ya yi cikin ƙananan kaya sai zuba ƙwmshi yake yi . _Ma'eesha_ Kafin ta je ta siye indomie sai da ta fara zuwa Chemist ta siye wa makaho Khalifa magani na rage zugin ciwo sannan ta tsaya ƙofar wani gida da ta ga an ɗaura gawayi a leda suna ajiye a kofar gidan. Ta siye gawayin wajen yaran da ke kofar gidan sannan ta nufi shago ta siyo ma su indomie da ƙwai biyu ta nufi gida. Ta same shi a tsaye a tsakar gidan rike da sandarsa, ya amsa sallamar da ta yi. "Lafiya na gan ka tsaye haka?" "Bayan ki zan bi na ji ko lafiya daga nan zuwa Wajan me kanti siyen indomie na ji shiru, shi ne na ce bari na bi bayan ki ko lafiya kika daɗe?" "Na ke Chemist na siye ma ka magani ne, na tsaya na siye gawayi kafin na zo wajen mai Indomie." "Allah sarki to na gode ƴar aljannah." Murmushi ta yi ta ajiye kayan a kofar ɗaki, maganin kuma ta mika ma sa shi . "Me zan taya ki da shi ne?" "Ba komai ka zauna ka huta idan na gama sai kawai ka ci." Kujera ta ajiye ma sa a tsakar gidan tana cewa. "Bari na ajye maka kujera ka huta muna fira har na gama." Ta taimaka ma sa ya zauna kan kujerar, ita kuma tana huta wuta har ya tashi ta wanke tukunya ta ɗira ta zuba ruwa, da kayan Hadi, ƙwani ɗin ma ta saka shi bayan ta wanke su don su ma dafaffe za su ci ƙwan. Har ta gama suna fira sai dai ta lura tun da ya dawo baya da walwala da alamar damuwa a tare da shi. Sai dai ta danganta hakan da ciwon da ke bakinsa ne. Har ta gama ta ɗora ma su ruwan wanka da za su yi idan sun kammala cin abinci. Pure water ta ɗauko cikin leda ta ajuye ma su, sannan ta shimfida tabarma ta ajiye abincin jan tabarma ta taimaka ma sa ya dawo kan tabarma ta ajiye ma sa abincin a gabansa. Suka fara ci don dama ta riga ta ɓare ɓawon ƙwan, baya jin cin abinci amma haka ya daure ya ci sakamakon idan bai ci ba za ta shiga danuwa, shi kuma baya son damuwarta. Bayan sun gama ta ba shi magani ya sha da ruwa. "Bari na zuba ma ka ruwan wanka ko?" Tashi ya yi ya shiga ɗakin ya duba kayansa ya ciro jallabiya wacce idan ya yi wanka ita zai saka a banɗakin. Koda ya fito ta hada ma sa ruwan ta kai ma sa, shiga ya yi ita kuma ta fara wanke-,wanke. Bayan ya fito ita ma ta shiga ta yi wankan nata. Yana ganin ta fito ya fito cikin ɗakin don ya ba ta damar shirya wa ta saka kaya. Da kallon mamaki take bin sa har ya fice. Ta rasa gane dalilin da zai saka a duk lokacin da za ta cire kaya ko za ta saka kaya sai ya fita ya bar ma ta ɗakin. Bayan shi ba gani yake yi ba to meueye amfanin fitarsa tun da bai da idanun ganin jikinta. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma

Chapter 29 of 49