Share this page
ba su ji dadin zancen da Laila ta yi wa makaho ba, kuma sun ji dadin hakurin da Ma'eesha ta ba shi, duk da ba su so ta ce Laila ba ƴar gidan ba ne don kar ta ji ba daɗi. Mamy kuwa ta ji haushin zancen ma'eesha ko kadan ba ta so a ce An yi maganar cewa ƴaƴanta ba ƴan gidan ba ne, tamkar gori Ma'eesha ta yi wa ƴar ta. Fuu Laila ta nufi kofar fita za ta fice Mummy ta kira ta. "Laila zo nan." ",Ta karasa gaban Mummy tana kumbure fuska." "Kada ki sake irin abun da kika yi yanzu, ki dinga daraja Ɗan adam ban da wulaƙanci ko cin zarafi akan wata nakasa da yake da ita. Ko da a ce haka ne bai kamata ki fadi haka ba. Ko a ina kuma ga mutum duk yadda yake ki daraja shi kada ki wulakanta shi Ɗan adam daraja ne da shi, ba wai idan ka taka wani matsayi sai ka dinga wulakanta mutane ba." Naj ta ba su labarin Khalifa Makaho da yadda ya taimake ta. Mamy ta jajanta ma su sannan ta yi Dady Barka da dawowa suka koma part ɗin ta ita da Laila. Ran su a ɓace don idan aka ɓata rana Laila dai Mamy ta taya ta fushi. Suna zuwa BQ Laila ta fada kan kujera tana kuka. Mamy ta janyo ta ta rungume. "Yanzu wai ni ban wuce gori a cikin gidan na ba, kullum cewa kuke na ɗauka nan gidanmu ne amma kalli abun da ma'eesha ta yi ma ni s gaban wannan Makaho." "Ki kwantar da hankalinki lokaci kadan ya rage daga Ma'eesha har uwar ta za su bar ma na gidan da me gidan dai yadda muka yi da shi. Ko kin mance abun da ya kawo mu nan ne?" "Ban mance ba, amma sai yaushe za mu yi ta zama a haka ne?" Lokaci kadan ya rage za su zama tarihi a gidan nan, nan ba da dadewa ba ke ce matsayin Ma'eesha yayin da ni kuma zan maye gurbin mahaifiyarta a wajen Alhaji." Dariyar mugunta suka saka su duka wanda sautin dariyar ya da ba su ji sallamar Jamil ba. "Assalamu alaikum." Shiru ba wanda ya amsa sai dariya suke yi Ya shigo ya tsaya gabansu sannan suka yanke dariyar da suke yi. "Lafiya wannan dariyar ai ta wuce na Musulunci." "Ina ruwanka." Mamy ta faɗa don ko da wasa ba za ta bari Jamil ya san shirinta, don ba halinsu daya da shi ba ta sani. Ɗakinsa ya wuce ba tare da ya sake cewa komai ba. Don har ga Allah ya tashi halin mahaifiyar tasa. *Washegari* _Ma'eesha_ Ta fito daga cikin bedroom ɗinta tana gyara mayafin abayar da ta yi rolling kanta da shi. Sanye take cikin doguwar rigar Abaya mai ruwa ƙasa. Hannunta rike da makullin motarta . Part ɗin Mummy ta nufa da niyyar yi ma ta sallama, tun kafin ta karasa ta hango Mamy tana barin part ɗin Daddy cikin sanɗa alamar rashin gaskiya. Da mamaki take tambayaar kanta. 'Me Mamy ta zo yi nan part ɗin, sannan duk falo bai ishe ta ba ko ɗakin Mummy shi ne za ta zo part ɗin Daddy me ta zo yi. Ga Daddy baya nan ya fita.' Ƙofar bedroom ɗin Mummy ta yi knocking aka ba ta izinin shiga sannan ta shiga da sallama. "Assalamu alaikum" "Wa'alaiki Salam warahmatullah." Mummy ta amsa yayin da take nannaɗe sallaya kasancewar sallar walaha ta idar. "Wai har kin fito zuwa gidan su Nasreen ɗin kenan ?" "Eh Mummy da ita na kwana ba ta da lafiya sosai." "Allah sarki, Allah ya ba ta lafiya." "Amin ." Ɗan jim ta yi har sai da Mummy ta tambaye ta. "Lafiya alamar kina da damuwa ko?" "Mummy ." "Na'am." Ta amsa tana tattara hankalinta kacokan kan Ma'eesha. "Me Mamy take zuwa yi nan na?" Cikin nuna gajiya da zancen Ma'eesha kullun na cewa ba ta son zaman Mamy a gidan." "Wai me bayin Allah suka yi ma ki ne Ma'eesha? Ban san ki da mugun hali na rashin son jama'a ba." "Wallahi da na ga Mamy tana sanɗa tana barin part ɗin Daddy ." Da sauri Mummy ta kalle ta tana cewa Ban gane ba wai ita da kanta kika gan ta a part ɗin mahaifinki?" "Eh." Ta amsa a takaice cike da damuwa. "Mummy me ya kawo ta ne?" "Ina zan sani don ban ganta ba. Me yiwuwa nan za ta shigo ta ɓace hanya kin san iyakar ta falo take tsaya wa." "Wannan fa sanɗa take yi alamar ba ta son wani ya ganta." Cikin kawar da zancen Mummy ya ce. "Idan kin je gidan su Nasreen ki gaida ma ni da mahaifiyarta." "Za ta ji." Har za ta wuce ta dawo ta ce "Mummy ba ki tunanin wani mugun abun take ƙoƙarin aikatawa ne?" "Me ya sa kika ce haka.?" "Haka zuciya ta ke raya ma ni." "To ki saƙa alkhairi a zuciyarki." Cikin sanyin jiki ta yi wa mahaifiyarta sallama ta fice daga part ɗin. A falo ta tarar da Mamy tana zaune tana kallonta ta washe baki. "Ƴan matan Mummy ina zuwa haka?" "Gidan ƙawata." "Da motarki za ki tafi?" "Eh." "Am na ce ba?" Sai Ma'eesha ta tsaya tana kallon ta don jin me za ta ce. "Ki dinga fita da Laila tana ganin gari ita ma ko za ta san jama'a." "Yanzu ina sauri next time za mu tafi tare." Ba ta jira cewar ta ba ta fice daga falon. A parking space tana kokarin yin parking motarta kenan ta ga wata sabuwar mota ta shigo cikin gidan. Ba kowa ba ne face Abdul saurayinta da yake mutuwar son ta. Bude murfin motar ya yi ya fito daga nasa motar ya nufi nata motar. Tsaya wa ta yi tana kallonsa da mamaki don ba ta san ya shigo kasar ba. "Kina mamaki ko?" Saukar yaushe a garin?" "Yanzu, ko gida ban je ba daga airport nan na fara zuwa na ga sanyin idanuwana." Murmushi ta yi tare da cewa . "Sannu da zuwa, shi ya sa na ji garin na ƙamshin Egyptian, ashe mutanen Egypt ne." Dariya ya yi tare da cewa. "Yanzu daga ƙasar Canada nake ." "Ma sha Allah. Ya kamata ka je gida ka huta kafin ka zo nan k" "Korata kike yi?". Dariya ta yi tana cewa. "Ba haka ba ne, kawai na ga ba ka je gidan ka huta ba ai." "Okay." Ya buɗe bayan motar ya fito da wasu manyan jakuna guda biyu ya ba ta. Kin karba ta yi sai da ya nuna ɓacin ransa ta amsa tana godiya. "Ba zan bar kasar nan ba sai an sanya ma na ranar aure da ke, don haka ki sanar da Daddy zan zo na gaishe shi." Daga haka ya shiga motarsa direba ya ja suka bar Wajen. Ba ta kai kayan gidan ba sai ta saka bayan motarta ta yi wa motar key ta bar gidan sai ta kama hanyar gidan su Nasreen. Ma'eeha na barin gidan Mamy ta hango abincin Daddy a a dinning table. Tashi ta yi ta kwance haɓar zaninta ta ciro wani kulin magani a leda ta kwance. Sai ta barbaɗa a cikin miyar abincin Daddy ta motsa shi sannan ta motse ta bar wajen bayan ta rufe ta bar wajen in da ta ga Mummy tsaye a falon *Maman Ihsan ce.*✍️ 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page1️⃣7️⃣ Tashi ta yi ta kwance haɓar zaninta ta ciro wani kulin magani a leda ta kwance. Sai ya barbaɗa a cikin miyar abincin Daddy ta motsa , sannan ta rufe ta bar wajen in da ta ga Mummy tsaye a falon. Sai ta hau kame-kame cikin rashin gaskiya ta ce. "Dama Wai fridge nake so na ɗauko ruwa na sha." "To ai ga fridge nan a bayanki ko kin manta ba a dinning area fridge yake ba." "Lah ko me ya hau kaina na nufi can oho, bari na je na ɗauko kawai." Ta nufi fridge ɗauki ruwa roba guda ta ta dawo falon ta zauna. Ita ma Mummy zama ta yi ba tare da ta kawo zargin komai a zuciyarta ba, duk da maganar da Ma'eesha ta yi ma ta kuwa. "Ko abinci za ki kara ci ne akwai shi a kitchen fa." Cewar Mummy tana kallon Mamy. "A'a Hajiya ba abinci nake bukata ba, ai an kai ma na ga shi can na baro shi ba mu cinye ba, Allah dai ya saka ma ku da alkhairi ya ƙara arziki, mun gode sosai." "Haba don Allah ki daina yi ma na godiya, ai mun zama ɗaya." Ƙarar horn ɗin motar Daddy suka ji da ƙarar bude gate ɗin gidan. "Bari na tashi na tafi tun da maigidan ya dawo ko?" "Tashi kuma ki zauna ma na na ga kallo kike yi ai, na manta ban fada ma ki ba za mu tafi aikin Umrah cikin satin nan in sha Allah." Washe baki Mamy ta yi tana cewa. "Alhamdulillah Allah ya kai ku lafiya ya karbi ibada?" "Ke da Alhaji za ku tafi ne?" "Mun saba duk shekara tare da shi da Ma'eesha muke zuwa mu uku, amma wannan karon ba zai samu zuwa ba ni da Ma'eesha kawai za mu tafi, shi ma wata ƙasar zai tafi." "Allah ya tsare ku za mu sha kewa." Dariya Mummy ta yi tana cewa. "Idan Allah ya kai mu za ku je aikin Hajji ke da yaranki duka." Kukan farin ciki ta saka tana yi wa Mummy godiya, ita kuma tana cewa ta daina kuka. Daidai lokacin da Daddy ya shigo da sallama. "Subhanallah me ya faru ne take kuka?" "Don na yi ma ta albashir ɗin zuwa aikin hajji ita da ya ranta shi kenan fa." Murmushi ya yi ya ce. "Ikon Allah , ai addu'a za ki yi ba kuka ba." Yana gama fadar haka ya nufi part ɗin sa, duk kukan da Mamy ke yi bai hana ta satar kallon Daddy ta kasan idanunta ba. Mummy ta bi bayan mijinta ganin cewa Mamy ta yi shiru. Da harara ta raka ta sanan ta mike ta nufi BQ. Ko da Mummy ta shiga part ɗin ta ta samu Daddy ya fara rage kayan jikinsa zai yi wanka. Ta taimaka ma sa ya cire kayan sannan ta haɗa ma sa ruwan wanka. Kafin ya fito ta cire ma sa jallabiya mai gajeren hannu, kasancewar in dai yana gida to ya fi saka jallabiya. Ya fito ta taimaka ma sa ya shirya cikin jallabiyar ganin yanayinsa ta san a gajiye yake. "Ka gaji ko?" Murmushi ya yi yana cewa. "Bari kawai aiki ne ya ma ni yawa tun safe har yammacin nan." "Allah sarki mu je ka ci abinci ka huta na san ba ka ci komai ba." "Haka ne, a tare suka nufi dinning area yana jin kansa na ɗan sara ma sa. Abinci ta zuba ma sa ya ci ya sha lemu da ruwa. Kallon time ya yi. "Ya kamata a ce Ma'eesha ta dawo gida haka nan, tun yaushe ta kira ni zancen zuwa gidan ƙawarta da ba lafiya shi ne ba ta dawo ba." "Za ta dawo in sha Allah. Ka san ba ta daɗe da wucewa ba, ka dawo kuma ka san ba ta da ƙawar da ta wuce Nasreen." Duk da haka sai da ya kira waya ya ce ta dawo gida. A ranar sai ga Khalifa Makaho ya zo gidan, kamar yadda Mummy ta ce ya dinga zuwa kowace rana, amma bai zuwa kowace rana sai dai duk sati yana zuwa. Ziyarar juma'a, bayan an yi sallar juma'a daga masallaci yakan je gidan ya kaiwa Mummy ziyara. Kuma takan karrama shi sosai da sosai a cika ma sa gabada da abinci kala-kala da abun sha. Wata rana har take away take yi ma sa. Kamar kullum yau juma'a ya zo gidan, bayan maigadi ya bude ma sa ƙaramar ƙofar m *Bayan sati ɗaya.* A ranar ne su Mummy da Ma'eeha suka wuce ƙasa mai tsarki don yin umara. Shi kuma Daddy nan da kwanaki biyar, zai tafi ƙasar da zai je don gudanar da harkokin sa.Farin ciki ya cika zuciyar Mamy saboda yanzu ne lokacin da za ta shirya mummunar kudirin ta kai. Don yanzu wani sabon salo Mamy ta tsiro da shi, sai ta bar BQ da sassafe ta zo man main house din ta ce da ma su aiki su dinga dafa abinci na su kaɗai, ita za ta dafa nata ita da yaranta da na maigidan wato Daddy. Ba yadda suka iya haka suka zuba ma ta idanun take yin abun da ta ga dama. Abincin Dady kuma kullum safe da dare sai ya barbaɗa ma sa magani a ciki. Gabɗaya ya canza kamar ba shi ba. Tafiyar da zai yi ma ya ce ya fasa zuwa. *Bayan sati biyu* Motar da ta ɗauko su na tafiya akan titi suna baya direban na zaune mazaunin sa yana driving hankali kwance. Cikin damuwa Ma'eesha ta ce. "Mummy tsawon sati ɗaya kenan ba mu ji daga Daddy ba, kuma yana ƙasar nan, abun ya ba ni mamaki shi bai kira ba kuma idan mun kira baya ɗaga wa." "Kar ki damu me yiwuwa aiki ne ya ma sa yawa." "Ba na tunanin akwai aikin da zai ma sa yawa da har zai saka shi ya mance da iyalansa. Yanzu haka na ɗauka za mu gan shi a airport ya zo ɗaukar mu." "Ki yi ma sa uzuri Ma'eesha." Daga haka ba wanda ya sake yin magana har suka ƙarasa gidan. Horn direban ya yi maigadi ya bude ma sa kofar gate ɗin ya shiga ya yi parking. Abun da ya kara ba su mamaki ganin motocin Daddy duka a wajen. Sauran ma'aikatan gidan suka ƙaraso suna yi ma su sannu da zuwa. Mummy ce ta amsa ma su, don Ma'eesha gabaɗaya hankalinta ya koma ga mahaifinta so take yi ta gan shi ta kuma ji dalilin da ya sa ya share su na tsawon kwanaki. Direban ne ya shigo ma su da kayansu, suna shiga cikin falon ba kowa sai sanyin A.C dake tashi a falon. Sautin dariya suka ji yana fitowa daga ɓangaren Daddy. A tare suka juya suna kallon ɓangaren Daddy wanda daga nan suke jin dariyar . Da mamaki suke kallon Mamy tare da Daddy suna fitowa daga ɓangarensa tana rike da jakarsa, alamar tafiya zai yi. Mutuwar tsaye suka yi suna kallonsa. Wanda shi ma su yake kallo sai dai ba za ka iya shaida halin da yake ciki ba. Cikin rawar baki Ma'eesha ta ce. "Daddy." Ba tare da ya kalli kowa cikin su ba ya ce. "Kun dawo?" "Ba su iya amsa ma sa ba, shi ma bai sake cewa komai ba ya nufi hanyar fita, Mamy na binsa a baya tana ta wani shu'umin murmushi. "Yauwa zan yi tafiya maybe zuwa next week zan dawo." Sai a lokacin Mummy ta yi karfin halin cewa. "Alhaji ba na ganin dacewar abun da na gani a yanzu, me wannan matar take yi a part ɗin ka?" "Oh haba!" Ta jingina kai sannan ta ce. "Meye tsakanin ku da har za ta fito tana yi ma ka rakiya?" "Kamar yadda kike matsayin matata a gidan nan to haka ita ma matata ce ita auren ta nake yi." Rintse idanunta Mummy ta yi sakamakon wami zafi da raɗaɗin kalmar da Daddy ta ki shi kamar an watsa mata ruwan dalma a zuciyar ta. Ma'eeha kam tamkar saukan aradu haka ta ji. "Alhaji yaushe hakan ya faru ba tare da sanina ba." "Ke uwata ce da dole sai na yi shawara dake wajen aiwatar da abun da na yi niyya?" Jinjina kai ta yi tare da yin murmushi da ya fi kuka ciwo ta ce. "Haka ne, Allah ya sanya alkhairi." "Amin, dama ke kika kawo ta kin san halinta kun saba da juna don haka ki karbe ta ku zauna lafiya don ba zan juri tashin hankali da kishin hauka da wasu matan ke yi idan mijinsu ya kara aure." Yana fadar haka ya fice shi da Mamy tana ma sa Allah ya tsare. Ma'eesha kuwa sulalewa ta yi a wajen tana kuka, ganin mahaifinta ko kallon arziki bai yi ma ta ba, bayan san cewa ita ce sanyin idanunsa. Yana masifar son ta baya son ɓacin ranta, amma yau an wayi gari ko kallo ta ba yi ba bayan tsawon kwanaki da suka shafe ba su ga juna ba. Mummy ta yi kokarin danne abun da take ji ta hau rarrshin Ma'eesha. Suna nan da na Mamy ta dawo tana taunar cingum. Ƙafa ɗaya kan ɗaya ta ɗaura tana danna waya tsadaddiyar wayarta sabuwa fil. Mummy ta kalli Mamy ta tuna ranar da ta zo ƙofar gidan neman taimako ita da Jamil da Laila. Wai yau ita aka wayi gari ta aure ma ta miji. Kuka sosai Ma'eeha ke yi ranta na ma ta zafi. "Aure dai an riga an ɗaura ba yadda mutum zai yi da ikon Allah, ni ma ba son raina ba ne aka aikata hakan. Alhaji ne ya matsa." Daga haka ta yi shiru tana ƙwalawa daya daga cikin masu aikin gidan kira. "Inno! Inno! Inno!" "Na'am Hajiya." Ta amsa tana fitowa, ganin Ma'eeha na kuka hankalin ta ya tashi ta nufi Ma'eesha tana tambayarta lafiya. Tsawar da Mamy ta daka ma ta ne ya saka ta ɗago da sauri. "Inno!" "Na'am." "Aikin da na saka ki kin gama ne?" "Eh Hajiya." Daga nan ta kama Ma'eesha suka nufi ɗakinta da ita. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, a cikin gidan, abubuwa marasa daɗi na faruwa. Bangaren Daddy ma gabadaya ya tattara hankalinsa ya mayar kan Mamy da yaranta, su ya mai da madubin sa. Sam bai damu da Mummy ba ballantana ƴarta ɗaya tilo a duniya. Da abun ya ishe Ma'eesha wata rana da ta je week end gidan Hajiya Turai ta kakarta sai take sanar da ita halin da suke ciki a cikin. Amma sai ta tarar da Hajiyar ita ma ba ta da labarin cewa wai Ɗanta da ta haifa ya iya yin aure ba tare da ya sanar da su ba. Daka jiran zuwa nasa take yi a baya kullum zai zo ya gaishe su, amma tun da ya auri Mamy bai je ya gaishe ta ba. A cikin kwanakin nan ne Mummy ta dinga fama da rashin lafiya. Yau lafiya gobe ciwo. Sai dai duk rashin lafiyar ba ta bari a kai ta asibiti ba, a cewar ga wai ciwon ba na asibiti ba ne. Ga Daddy ya fita ba zuwa ƙasar. _Makaho,_ Kasancewar yau juma'a ne kuma daga masallaci gidan su Mummy yake son zuwa don ya gaishe da Mumm. Kasancewar sun tafi aikin Umara ya san dai yanzu sun dawo. Don haka bayan ana idar da Sallah kai tsaye ba gidan su Mummy ya nufa don gaishe su kamar yadda ya saba. Doguwar tafiya ya yi kafin ya ƙaraso gidan. Sai da ya sa hannu ya shafa gate ɗin gidan ya tabbatar gidan ne kafin ya yi knocking. Maigadi ya bude kofar ya ga Makaho ne ya ce. "Ma sha Allah makaho ne ke tafi?" Bai tanka ma sa ba ya yi gaba yayin da maigadin ya bishi da harara. "Wannan mishkilancin naka Allah ya ga abin da ya gani da ya hana wa jaki ƙaho. Ana ma sa magana yana share Mutane wannan da yana da kudi da an ga gadara." Makaho kam bai ma san yana yi ba ya nufi cikin gidan. Daga bakin kofar falon yake knocking, ɗaya da cikin ma su aikin ta fito . Ganin shi ne ya sa ta ce. "Bari na sanar da su. Tana shiga ta yi sallama sai aka amsa ma ta tare da ba ta izinin shiga. Ta shiga Mummy na barci Family doctor nasu ma hi ma ta ƙarin ruwa. Ƴar aikin ta kalli Ma'eesha ta ce . "Aunty wannan makahon da ke zuwa ranar Friday ne ya zo " "Okay Ina zuwa." Bayan ƴar aikin ta fita da kamar mintuna biyu sai Ma'eesha ta tashi ta fita ganin Mummy na barci. A hankali take tafiya har ya buɗe kofar falon. Yana tsaye a ya jingina bayansa da bango . Tana daga kanta ta sauke idanunta a kansa. Ya nunkuyat da kai ƙada ya haɗa kai da Sandarsa. Cikin siriryar murya Ma'eesha ta yi masa sallama. Ya ɗago kansa kamilalliyar fuskarsa mai cike da haiba ta bayyana. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page1️⃣8️⃣ Ya ɗago fuskarsa kamilalliyar fuskarsa mai cike da haiba ta bayyana. "Wa'alaiki Salam warahmatullah." Ya amsa ma ta cikin muryarsa mai amo. "Ina wuni?" "Lafiya lau Alhamdulillah." "Ka shiga ciki." Tana gaba yana bin ta a baya dama idan ya zo bangaren baƙi Mummy ke cewa a kai sa. Bayan ta tura ƙofar falon n ta shiga ne shi ma ya zo ya shiga yana mai yin sallama. Sai da ya ɗan laluba ya ji kujera sannan ya zauna da Bismillah. Ina Mummyn taki take ne?" Cikin sanyin murya ta ce. "Ba ta da lafiya." "Subhanallah me ya same ta?" "Zazzaɓi ne." "Allah ya ba ta lafiya." "Tana ina ne?" "Tana bedroom ɗin ta. Ita ce ta ce na shigo da kai." "Allah sarki, Allah ya ba ta lafiya." "Amin ya Allah." Ta amsa tana mai nufar ƙofar fita ta ce. "Bari na kawo ma ka abinci ko?" " A'a ki bar shi kawai tafiya zan yi, na zo ne dama na gaishe ta." "Ka yi hakuri ka zauna zan kawo ma ka abinci ko a cikin take away ne dan idan Mummy ta ji ban kai ma ka abinci ka tafi haka nan ba za ta ji dadi ba." Tana fadar haka ta fice daga falon. Ba jimawa ta dawo da leda mai ɗan girma ta mika ma sa. "Ga shi na zuba ma ka abincin da abun sha sai snacks." "To na gode Allah ya kara arziki ya ba Mimmy lafiya ." "Amin ya rabbil izzati na gode." Ya mike ya fice daga falon tana binsa a baya. Ya nufi hanyar fita ita kuma ta shiga falonsu cikin matsanancin faduwar gaba da sanyin jiki wanda ta ji ya dirar ma ta lokaci guda. Mamy ne a falon tana waya, amma tana ganin Ma'eesha ta yi saurin katse kiran wayar ta ajiye wayar tana kau da kai. Ma'eesha dai ba ta kalli gefen da take ba kai tsaye bangaren mahaifiyarta ta koma. Ta same ta idanunka a lumshe tana tuna yadda Daddy ya canza ma ta, kamar ba mutumin da baya son ɓacin ranta ba, kamar ba wanda yake shiga damuwa idan ba ta da lafiya ba, amma yau ga ta kwance ko ya zo sai dai ya tsaya daga bakin kofar ya yi ma ta magana baya shigowa ciki. Kuma duk a sanadiyar matar da ta taimaka da zuciya ɗaya a a rayuwa. Matar da ta ɗauke ta kamar ƴar uwa take ƙaunarta da zuciya ɗaya. Kalli rayuwar nan abar tsoro ce. A hankali ta bude idanunta akan Ma'eesha tana tausayin rayuwar da yarinyar za ta fuskanta bayan babu ita a duniya. Don ba ta da in da za ta je, Daddy ya ma ta shamaki da danginsa, dole ta zauna gidan ubanta. Kuma ba za ta yi rayuwar farin ciki da jin dadi ba. Dama a ce ta aurar da ita ga miji nagari da ba ta da wani damuwa, ta san tana zaune gidan mijinta ba za ta zauna a wannan gidan ba. Ta kira sunanta a hankali. "Ma'eesaha." "Na'am Mummy." "Kar ki sa a ranka duk wanda kike tare dashi a yau ba zai iya rabuwa da ke a gobe ba, dan haka karki sa rai da mutum kowa ki so shi saffa-saffa. Saboda wanda muke tare da su yanzu anjima babu su. Ɗan adam yana iya rabuwa da ke a duk yanda kike da shi, shi ya sa da kowa ma ki zauna da shirin rabuwa da shi ko wane ne, ke dai ki zauna da kowa da zuciya ɗaya, duk wanda ya tafi ko ba yanzu ba wata rana sai ya ga amfanin ki ko ya tuna ki saboda son da kila ma sa da ALLAH da kuma zaman da kika yi dashi dan Allah. Allah ya sa ki dace duniya da lahira, Allah ya haɗa ki da masu son ki da zuciya d'aya wa 'yanda suka san kina sonsu, Allah ya raba ki da wanda duk yanda za ki so su ko daidai da rana ɗaya ba su tuna kin taɓa sonsa ko ka ta6a masa alkhairi ko wani abu naki a rayuwa, in dai mutum ya samu wata dama kai ma sai ya rabu da kai saboda yana ganin ya fi 'karfin ka shi ya sa sai Allah ya kwace daman shi kuma saboda shi da zuciyan kowa yake amfani. Allah ya haɗa ki da masoyan gaskiya." Cikin sanyin jiki ta ce. "Amin Mummy." Mummy idanunta a kafe kamar tana kallon sama, sai Ma'eesha ta ce. "Mummy na ba shi abincin ya tafi da shi ya ce

Chapter 12 of 49