Share this page
ta nufi gidan Sady baby dan ta ba ta shawarar yadda za ta ɓullowa lamarin nan. Sallama ta yi wa su Mama da sunan za ta je gidan ƙawarta ba ta da lafiya. Duk da Mama ba ta son yawan fitar da Sidra ke yi sai dai ba ya da yadda za ta yi ta hana ta fita. Mama ta kalle ta ta ce. "Direba zai kai ki ko kuma ke za ki yi driving motar da kanki?" "Mama da kaina zan yi driving." "Okay ki ɗauki key din motar ga ta can, amma don Allah kada ki daɗe." "To Mama in sha Allah." Ta yi maganar tana nufar centat table in da Mama ke nuna ma ta key din motar . Fita ta yi daga cikin falon kafin ta kira wayar Sady baby. Daidai tana ƙarasawa wajen motar ne Sady baby ta ɗaga wayar tana cewa. "Hello ƙawata." Sidra ta ce kina gida ne?" "Eh ina gida ina fatan komai na tafiya daidai." "Hmm gani nan dai zuwa." Daga haka ta katse kiran wayar ta bude murfin motar ta shiga Sady baby ta tashi daga cikin saurayin da suke tare kan gado tana cewa "Ka bar gidan nan kafin ta zo ta same ka." "Wace ce ita da kike tsoron ta haka.?" Dariya ta yi kafin ta ce . "Ba tsoron ta nake yi ba, infact ma amfani da ita nake yi wajen cimma burina na mallakar Namijin da nake so na yake rayuwa da shi." Ya sauka daga kan gadon Yana cewa. "Wani namiji ne wannan?" "Fahad Majidaɗi." "Fahad Majidaɗi fa kika ce?" "Ƙwarai kuwa shi, shi ne Namijin da na dade ina so a rayuwata, wanda na san shi tun kafin Sidra ta san shi, a takaice me ni na sanar da ita ko waye shi da kuma irin son da nake yi ma sa. Wata rana mun haɗu da ita a wajan shopping muna magana sai kawai ga motar Fahad ga ƙaraso wajen. Nake sanar da ita ina masifar son sa amma ya wulakanta ni, madadin ta taimaka ma ni shi ne ta kutsa kanta gare shi, da na ga har suna shirin aure ni kuma ba zan taɓa bari ta mallake shi ba sai dai ni ya sa na ba ta gurguwar shawara, don na ga tana masifar son ta yi suna ta ɗaukaka, na muna ma ta damar zai wuce ta don wata shahararriya ta wulakanta, na yi amfani da damar na sa ta gudu ranar aurenta don rasa shi Ni kuma ba mallake shi. Amma cikin rashin sa'a iyayenta suka ba shi auren ƙanwarta a madadinta." Jinjina kai ya yi tana maida rigar jikinsa ya ce . "Tab shi ya sa sheɗan ya jinjina wa kaidin mace, to ga shi kin rasa ita ma ta rasa." Dariya mai sauti ta yi kafin ta ce. "Ban rasa ba, yanzu haka ina amfani da ita ne wajan ganin ta raba ƙanwarta da Fahad, na ba ta shawarar yadda za ta raba su, idan suka rabu ita ma na tona asirinta wajen iyayensu da shi dole ba za ta rayu da shi ba ka ga na buga wasa na yadda nake so" "Amma ai ba lallai ya so ki ba." "Na san hanyoyin da zan bi dole ya so ni." Ta yi maganar tana nuna ma sa kofar fita, ba musu saurayin ya fice yana jinjina kai Tashi ta yi ta faɗa bathroom don yin wanka. Bayan ta fito ta saka doguwar riga daidai lokacin da ta ji shigiwar motar Sidra. Ta window ta leka ta hange Sidra na fitowa daga cikin motar, sakin baki ta yi tana kallon motar wacce ta san cewa motar Sidra ba ta kai wannan tsada ba. Taɓe baki ta yi tana karasa shirya wa cikin sauri . Sallama Sidra ta hi tare da shogjwa cikin falon, zama ta yi kan Kujera daidai lokacin da Sady baby ta fito tana ma ta murmushi. Oyoyo ƙawata." Ta faɗa tana rungume Sidra tare da ƙaƙaro murmushin dole. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Pqge5️⃣8️⃣ Ta faɗa tana rungume Sidra tare da ƙaƙaro murmushin dole. "Sannu da zuwa ƙawata ya kike ya hakuri da rayuwa?" "Alhamdulillah." "Ma sha Allah." Zama ta yi gefenta tana cewa. "Meye labari?" "Hmmm ke dai bari na kasa gaskata abubuwan da ke faruwa a rayuwata ji nake kamar mafarki nake yi ba gaskiya ba ne." Tashi Sady baby ta yi ta kawo ma ta ruwar roba da glass cup, zuba ma ta ruwan ta yi ta mika ma ta, karba ta yi ta sha . _Nadra_ Bayan ta tashi da safe ta fara aikace-aikacen gidan, bayan ta gama da sama ta koma zuwa falon ƙasa. Kasancewar tana da ƙoƙarin aiki ba ta gajiya da aiki ba ta da ganda. Ɗakinsa ne kawai ba ta shiga ciki ta gyara ba, sai ta shiga kitchen don ɗora breakfast. Sai karfe tara na safe ya fito ya ji ƙamshi na fitowa daga cikin kitchen ɗin. A falo ya zauna ta dauki system ɗin sa yana amfani da shi. Bayan ta gama ne ta fito dauke da babban faranti da aka jera breakfast akai . Jera su ta yi a dinning table din sanann ta hango shi zaune a falon. Ƙarasawa ta yi gabansa cikin sanyi jiki ta durƙusa ta gaishe shi. "Ina kwana." "Lafiya lau." Ya amsa idanunsa na kan abun da yake yi. Tashi ta yi ta nufi bedroom ɗin ta, ya bi ta da kallo, kamar ta san yana kallonta sai ta juyo suka haɗa idanu, kau da kansa ya yi yana jin takaicin kallon da yake yi ma ta har ta kama shi yana kallonta. Ɗakinta ta wuce kai tsaye ta nufi bathroom don yin wanka. Ta yi wanka ta shirya cikin doguwar rigar material ɗinkin bubu. Sanyayyen ƙamshi ke tashi daga jikinta. Kai tsaye ta nufi falon. Yana in da ta bar shi. "Breakfast na jiran ka Yaya Fahad." Ta faɗa har yau ba walwala ko sakin fuska a tare da ita. Bai tanka ma ta ba kamar yadda ba ta saka ran dama zai tanka ma ta ba. Nufar dinning area ta yi don hada ma sa breakfast. Cikin nutsuwa take yin komai nata har ta shirya ma sa komai. Tana gama wa ya ƙaraso wajen ya zauna, cin abincin ya fara yi yana mamakin yadda ta iya yin girki haka. Ita ba ta wani ci komai ba ruwan Lipton wanda ta dafa shi da kayan ƙamshi kawai ta sha. Bayan ya gama ne ya kalle ta ya ce . "Idan kin gama za mu je gidanku mu gaida su Umma." Farin cikin da ta tsinci kanta ciki ne ya kasa ɓoyuwa, cike da farin ciki ta ce . "Na gode." Bai ce ma ta komai ba ya tashi har zai bar wajan ya ce . "Waye zai gyara mun ɗaki?" "To ina zuwa." Komawa falo ya yi ya zauna. Ita kuma ta fara tattara kayan da suka yi amfani da su ta kai kitchen, sannan ta dawo ta gyara wajan ta goge. Kai tsaye ɗakinsa ta nufa, falonsa fes kamar yau aka gyara, daga nan sai ta nufi bedroom. Toilet ta fara wankewa , sannan ta dawo ta gyara ma sa bedroom ɗin har zuwa falo. Bayan ta gama ne ta fita zuwa kitchen don ta yi wanke-wanke. Gani ya yi aikin sun yi ma ta yawa don haka take a wurin ya fara tunanin ko a nema ma ta mai taya ta aikin gidan ne. Ɗakinsa ya shiga don shirya wa, wanka ya fara yi ya fito ɗaure da towel yana tsane kansa da wani karamin towel ɗin. Shirya wa ya yi cikin manyan kaya, tsadadden yadi mai ruwan sararin samaniya. Yadin irin mai taushi nan ne ya saka hula wacce ta dace da shigarsa. Sai zuba ƙamshin turare yake yi, ya saka takalmi baƙi wanda shi ma hulɗar ta sa baka ce . Fitowa ya yi daga bedroom ɗin sa ya nufi ɗakinta dan ya sanar da ita idan ta shirya ta same shi a mota. _Nadra_ Fitowarta daga wanka kenan tana ɗaure wanda ya tsaya ma ta iya rabin cinyarta. Nan ya yi tozali da ita wa da hakan ya saka ya tsinci kansa a wani yanayi ma daban. Wani abu ya ji ya tsara ma sa tun daga kansa har zuwa babban yasar ƙafarsa. Wanda bai san lokacin da ya karasa gabanta, wanda ita kam ba ta ma san ya shigo ɗakin ba sai da ta gan shi a gabanta yana kokarin janyo ta jikinsa neta lura da shi. Taga-taga ta yi baya za ta fadi sakamakon santsi tiles cikin zafin mama ya janyo ta jikinsa sannan ya ɗaga ga can ya nufa gadonta da ita a hannunsa. Kuka ta saka ma sa tana ture shi amma ko gezau bai motsa ba. "Ki kwantar da hankalinki kin ji ba zan cutar da ke ba, na yi ma ki alƙawarin zan rayu da ke har zuwa ƙarshen rayuwata, I love you Nadra. Ni za ka yi wa dadin baki saboda kana son ka mori jikina." "Wallahi ba dadin baki ba ne da gaske nake ba zan iya rabuwa da ke ba ina son ki." "To shi ne ban ga kana nuna ma ni so myayya ba sai yanzu?" "Kece ba ki bani dama ba tun dawowa ta kika sauya." Ya yi maganar da kyar yana yana cikin halin buƙatuwa da ita sosai. "Shi ne ba ka bani hakurin laifin da ka yi ma ni ba ko? Wato idan jikin nawa wata masifar ce na jiƙa na sha ko?" Jikinsa na rawa yana ƙara ƙanƙame ta ya ce. "Na ba ki haƙuri tuba nake ba zan sake ba, ni da kaina zan jiƙa kuma na shanye kin ji?" Duk da Halin tsoro da take ciki bai hana ta yi ma sa dariya ba, ganin lokaci daya ya canza ba wannan jin kai da yake da shi ko nuna isa da taƙama yana bin ta duk yadda take so. Tana rike da towel ganin yana ƙoƙarin warware ma ta shi. "Yaya Fahad kada ka gama morar jikina ka wulakanta ni ka sake ni kamar yadda ka ce, na san ba ka so na ka sake..." Ya rufe ma ta baki da yatsarsa ya ce. "Duk abun da na faɗa ma ki yanzu gaskiya ne, zan rayu da ke har ƙarshen rayuwata na amshe ki matsayin matata uwar Ƴaƴana." "To amma Sunyi Sidra fa?" "Kada ki sake kira ma ni sunan ta. Please ki ba ni hadin kai na samu abun da yake halaliya ta ba zan iya jurewa ba, kina da ilimin addini kin san hukuncin matar da ta bijirewa bukatar mijinta ko,?" Hankalinta ya kara tashi ta sani tana cikin tsinuwar Mala'ikun Allah amma ba za ta iya jurewa ba." "Ka yi hakuri tsoro nake ji." "Na gane kuma na yi ma ki alƙawarin ba zan dasu da ke ba sai da amincewar ki, amma ki taimaka ki bari na biya buƙata ta da ke ta hanyar wasa da ke ba tare da ba kusance ki ba har sai ranar da kika yarda." "Kai ta jinjina ma sa tana hawaye." Rintse ifanunta ta yi tare da sakar ma sa towel ɗin da yake kokarin janye wa . Bakinsa ya saka cikin nata bakin ya shiga tsotsa kamar ya samu sweet. Yana sarrafa albarkatun jikinta yadda ransa yake so, kasancer ita ma ta sakar ma sa jiki, sai dai ba abun da take tunawa kamar kalaman Aunty Sidra, su ne suke yi ma ta amsa kuwa a cikin kunnenta. Tambayar kanta take yi shin ya za ta yi? Za ta saɓa wa umarnin Allah ne don ya faranta wa baiwar sa? Ko kuma umarnin Allah za ta bi ta samu lada? Babu biyayya ga abun halitta wajen saɓawa Allah. Wani yanayi ta sake riskar kanta a ciki jin yadda yake tsotsan dukiyar fulaninta kamar jariri yana murnza ɗaya. Tsawon lokaci ya dauke sarrafa ta, ita kanta ba ta san lokacin da ya cire kayan jikinsa ba kasancewar idanunta na a rufe, ba shiri ga bude idanunta sakamakon jin ya kana hannunta ya ɗora a sanadar girmansa. Cikin tashin hankali ta kalle shi za ta janye hannunta ya matse hannun ya rike yadda ba za ta iya cire hannunta ba. Zuwa can ta ji ɗumi a cikin hannunta, ta kalli hannun ta ga abun da ya zuba ma ta. Yamutse fuska ta yi kamar za ta yi kuka yayin da ta mika ma ta toilet peper ta karba tana goge hannunta. Sumbatar gishinta ya yi tare da cewa "Thank you." "Mu je mu yi wanka." Make kafada ta yi tana cewa "Ka tafi kai kaɗai." Murmushi ya yi ma ta ya tashi ya nufi bathroom ya tsarkake jikinsa. Ko da ya fito ta daura towel ɗin ta tana jiran fitowarsa. Ya fito ɗaure da wani towel ya nufi ɗakinsa. Ita ma wankan ta yi sanann ta fito tana gyara gadon ta tattara kayansa da suka yi takure. Shirya wa ta yi cikin Abaya mafi ruwan toka ta dauki handbag da wayarta ta saka takalmi flat shoe. Ta dauki kayansa ta nufi ɗakinsa. Ta same shi ya shirya cikin wata ɗanyar shaddar fara yana ɗaura tsadadden agogon hannunsa sai zuba ƙamshi yake yi. Ta cikin mirror suka haɗa idanu, da sauri ta ɗauke kanta tana sunkuyar da kai. "Ki saka su a cikin washing machine" Kai tsaye ta nufi bathroom ɗin sa ta zuba su ciki kamar yadda ya umarce ta haka ta yi sannan ta fito. Har lokacin ta ƙi yarda su haɗa idanu da shi, dan wani kunyarsa take ji sosai ba kaɗan ba. Key din motarsa da wayoyinsa ya ɗauka sai wasu tarkardu da alama daga can zai je wani wurin ne.' Shi ya rufe ƙofar shiga don ita tuni ta fice. A wajen parking space ya same ta tsaye don ita ba ta san da wata motar zai tafi ba. Ma'aikatan gidan na gaishe ta. Sai a lokacin take lura da motarta sabuwa wanda Baban Fahad ya siya ma ta, duk da ba ta san lokacin da aka kawo motar ba. Ganin tana kallon motar ya ce "Motarki ce aka kawo key na falo dan mun dawo sai i na ba ki ." Ya yi maganar yana buɗe ma ta gaban motar, ta shiga ta zauna sannan ya zagaya wajan zaman direba ya zauna, key ya yi wa motar suka bar gidan. Ba abun da ke tashi daga cikin motar sai ƙamshin turarensa da sanyin A.C kawai ake ji. Kallonta ya yi ganin har lokacin kanta a kasa tana wasa da yatsun hannunta da suka sha jan lalle sun yi kyau. Yana mamakin irin kunyar da Nadra ke da shi. "Nadra." "Na'am Yaya." "Kada ki sake kira na da Yaya domin ba Yayanki ba ne, yau na ji kalan dangi." "To me zan kira ka?" "Ki zaba ma Ni sunan da kika ga ya dace." "Ni ban san sunan da ya dace ba." "Okay to kira ni da Fahad." "Wallahi ba zan iya ba ." "To zaɓi suna na masoya ki saka mun. " "Kunya nake ji " Dariya ya yi yan cewa. "Da sannu sai na raba ki da wannan kunyar da kike ji." "Ta ya ya?" " Da sannu zan mayar da ke mara kunya." *Tab wallahi ba na son rashin kunya da fitsara." "Ba irin wannan rashin kunyar ba, irin kunyar nan nawa da kike ki zan raba ki da shi, don zai iya ciyar da ni." Ba su yi tafiya mai nisa ba ya ya yi parking a wani gabanb super market. Kallon wajen ta yi don ba ta san me yake sunyi w wajen ba. "Me za ki siya wa su Umma tsaraba da su Ammi da Abba?" "Ba na da kuɗi." Ta yi maganar kanta a ƙasa, don kam ba ta da kudi ko da suka yi aure kudin sadakinta ne kawai a hannunta, kuma ta ranar wajen sallamar baƙi da ta dinga yi. "Ba ni account number naki." Ba musu ta karanta ma sa account number ɗin. Shigowar alert ta ji na Naira miliyan uku. A firgice ta kalle shi don kudin sun yi ma ta yawa. Za ta yi magana ya ce . "Fito mu je." Yana faɗa ya fita daga cikin motar zuwa cikin supermarket ɗin. _Makaho_ Bayan ya fito da safe zai je wajen sana'arsa, hannunsa ɗaya rike da kayan gyaran takalminsa, ɗaya kuma rike da sandar jagoransa, sai sauri yake yi kasancewar akwai wani jami'in da zai zo karbar rahoto daga hannunsa. Kuma idan jama'a suka taru a wajan za su iya fahimtar wani abu. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Pqge5️⃣9️⃣ Bayan ya fito da safe zai je wajen sana'arsa hannunsa ɗaya rike da kayan gyaran takalminsa. Ɗaya hannun kuma rike da sandar jagoransa, sai sauri yake yi kasancewar akwai wani jami'in da zai zo karɓar rahoto da daga hannunsa. Kuma idan jama'a suka taru a wajen za su iya fahimtar wani abu. Cikin ƙanƙanin lokacin ya isa wajen sana'ar sa, sai sai akwai mutane duk da bai yi tsammanin zuwan kowa ba. Ya gaisa da mai Yalo da sauran mutanen da suke wajan . Zama ya yi bakin aikinsa, sai ga wani karnin yaro ya kawo takalminnsa gyara. Karba ya yi ya gyara ma sa yaron mai kimanin shekaru shida a duniya. Bayan ya gyara ma yaron takalmi ne yaron ya ba shi dubu ɗaya ya ce . "Uncle ga shi ka ba ni canji." "Ya yi maganar yana miƙa ma sa dubu dayan da ke hannunsa. Karba ya yi yana cewa. "Nawa ne nan?" "Dubu ɗaya ne uncle." "Ba na da canji." Ya yi maganar yana miƙa ma sa dubu ɗayan." "To uncle Ina za mu samu canji." Murmushi ya yi saboda yaron ya burge shi ya ce . "ka tafi ba bar ma ka kudin gyaran." "To uncle na gode." Yaron ya tafi yana murmushi, mai faci dake gefe ya ce . "Dama canji ka nema ka karɓi ko Naira hamsin ce, don na san waye uban yaron nan yana da rufin asiri, kudin da yake samu a rana ɗaya sai ka yi wata ɗaya ba ka tara shi ba!" Bai tanka ma sa ba ya yi kamar bai ji shi ba. Wani mutum ya zo ya yi sallama . "Assalamu alaikum." Gabadaya suka amsa ma sa da . "Wa'alaika salam." "Na kawo gyaran takalmi ne." Ya yi magana yana nuna ma makaho tsakaninsa. Jarɓa makaho ya yi cikin hikima da basira da Allah ya yi ma sa ya saka hannu cikin aljihun wandonsa ya ciro wani micro SD makaho ya manna shi a ƙasan takalmi da wani ƙarfe kamar ƙugiya a tafin takalmi. Cikin ƙwarewa ya manna shi da jikin takalmin ya nannaɗe shi da zare ya ɗinke takalmin. Miƙa ma sa ya yi tare cewa. "To yallaɓai na gama." "Nawa ne kudin aikin ka?" "Naira ɗari ce ." Ya ciro Naira ɗari daga cikin aljihun wandonsa ya a mika ma sa, makaho ya ba shi takalmin ya karba ya tafi . Yana barin wajen makahon ya kira waya yayin da yake shiga cikin motarsa. Ana ɗauka daga can ɓangaren ya ce . "Hello sir." Daga can ɓangaren aka ce . "Ka samu ganin Jalaluddeen?" "Eh yanzu haka ma bayanan suna hannuna ya ba ni." "Gud job, aikinsa yana kyau. Ka kama hanyar Abuja yanzu kada ka ɓata lokaci." "Okay sir." Ya faɗa yana yi wa motar key ya bar wajan . _Nadra_ Tana ganin ya ya fita bayan ya ce ta fito su je ta bishi ita ma. Zuciyarta cike da mamakin yadda Fahad Majidaɗi ya tura ma ta Naira miliyan uku. Ta saka a ranta za ta yi wa Ummanta siyayya da Abba har da Ammi. Suna shiga ciki ya ce . "Ki duba tsarabar da kika ga ya dace ki siya ma su." Jinjina kai ta yi har lokacin tana mamakin sa. Shi kuma ɓangaren kayan abinci ya nufa. Ita kuma tana bangaren wajen kayan sakawa. Atamfofi guda biyar da ɗaukarwa Ummanta. Da mayafaiya ma su kyau da tsada, sai sarka da Ɗan kunne ma su kyau kala biyu. Ta ɗaukarwa Abba shaddodi kala uku ma su kyau da tsada.. sai huluna da suka shiga da kowane kaya. Ta ɗaukarwa kakarta Ammi atamfa kala biyu ma su kyau. Bayan ta gama cire wa ta waiga ta kalli bayanta , sai ta ga Fahad ne yake kallonta . "Kin gama ne?" Kai ya jinjina ma sa alamar eh. "Okay mu je." Ɗaya daga cikin ma'aikatan wajen ya tura kayan da ta zaɓa. Ko da aka yi lissafin Kudin tana shirin bude handbag ɗin ta don ta fito da ATM card nata sai ta ga Fahad ya mika nasa ATM card ɗinsa. Kallonsa take yi da mamaki yadda ya tura ma ta kuɗi har Naira miliyan uku wanda ita a tunaninta da su za ta yi tsarabar iyayenta, amma sai ta ga ya biya. A bayan mota aka zuba ma su kayan,abun da ya kara ba ta mamaki shi ne yadda ta ga uban kayan abinci da ya siya aka zuba a motar, kama daga kan buhun shinkafa biyu buhun semovita biyu spaghetti da macaroni da cus-cusvhar zuwa indomie komai bibbiyu galan man ja da man gyaɗa haka aka tara komai har zuwa su maggi da kayan tea. Ta kasa magana har ya bude ma ta gaban motar ta zauna a gefen sa, sannan ya yi wa motar key suka bar wajen. Kasancewar ba su da nisa da wajan da suka yi siyayya da gidan Abba. A kofar gidan ya yi horn maigadi ya leƙo ganin Fahad ya magale gate ɗin yana ta fara'a. Ma'aikatan gidan da farin ciki suka ƙaraso wajen motar suna yi ma su sannu da zuwa. Don sunji kewar Nadra. Fahad ya fara fitowa sanann ya buɗe wa Nadra ta fito fuskarta ɗauke da murmushi tana kallon Baba maigadi da direban gidan da suke nuna farin cikin zuwanta. Cikin girmamawa durƙusa ta gaida su, suka amsa suna ma ta Allah sanya alkhairi ya ba su zaman lafiya. Ciki suka nufa yayin da ta ɗauki ledar tsarabar su Umma ta shiga falon. Fahad ya tsaya daga waje yana jiran a yi ma sa iso. Da sallama ta shiga ciki, ta yi Sa'a kuwa kowa na nan, Abba na gida bai fita ba, Umma na zaune a gefensa, sai Ammi dake kwance kan doguwar kujera mai zaman mutum uku. Gabadaya suka amsa sallamar fuskar kowa dauke da farin ciki. Nadra ta rungume Umma tana kuka. "Ikon Allah, to me ye abun kuka kuma?" Cewar Ammi tana mamakin Nadra. Ganin haka Abba murmushi kawai ya yi , don duk wanda ya kalli Nadra ya san ba ta cikin tashin hankali. Ta ciko ta yi kyau sosai. "Ina shi Fahad ɗin yake?" Kuka kawai take yi ta kasa magana. Su kuma sai dariya suke yi ma ta. Wacce ke yi wa Umma girki ne ta fito za ta je kasuwa, ta gaida Nadra lokacin da ta tsagaita kuka. Tana fita ta ga Fahad waje ta dawo take cewa . "Nadra kika bar mijinki waje ba ki ma sa iso ba?" Sai a lokacin ta tana da shi yayin da Ammi ke salati. "Ya kika bar shi waje kuma?" Cewar Abba yana miƙewa tsaye. Yana bude kofar ya ga Fahad yayin da Fahad ya durƙusa ya gaida Abba cikin girmamawa. Ya amsa cikin da farin cikin ganinsa, hannunsa ya ja suka shiga ciki. Ya gaida Ammi da Umma sannan ya kalli Nadra dake goge hawaye. "Ka ga sakaryar matarka kukan shagwaba take yi saboda ta ga Ummanta." Murjushi ya yi tare da cewa. "Umma ya karfin jikin?" "Alhamdulillah na ji sauƙi Fahad." ,"Allah ya kara lafiya." Ya faɗa yana kallon Nadra da take wani narkewa a jikin Umma.. Ruwa da lemu mai aikinsu ta kawo ma su. Fahad ya sha ruwan kawai . Abba ya kalli Fahad ya ce . "Ya aiki yaushe ka dawo?" "Juya na dawo Abba." "Ma sha Allah, Allah ya taimaka." "Amin ya Allah." "Yauwa a kara hakuri da Nadra ka san yarinya ce karama, don Allah ka kara hakuri da ita komai zai yi daidai." Kafin ya yi magana ne Ammi ta bude baki ta ce. "Wani hakuri zai yi da Nadra, ai Allah ne ke son sa da gata. Yanzu da ba don Allah yana son ka ba ai da waccen gantalalliyar ya bar ma ka a matsayin matar aure, da yanzu kana nan kana ta fama da ita kila da yanzu na zuwan ka sai ka kawo ƙarar ta. Amma da Allah ya so ka da rahama da kwanciyar hankali ya ba ka Kamilar yarinya ai da yanzu kana nan kana tagumi." "Umma ta yi shiru tana goge ƙoƙarin ɗauke ƙwallar ta ta je sun cika ma ta idanu. Fahad ya kalle ta cike da tausaya yana ayyyana girman soyayya irin ta uwa akan ƴaƴanta. Cikin sanyin murya ya ce . "Mama ki daina damuwa Sidra tana gidan Mahaifina cikin ƙoshin lafiya. Tana sakewa ta yi rayuwata da kowa, yadda ba mai takura ta a gidan nan haka adabi ma ba mai takura ma ta za ta yi rayuwarta yadda yake so , sai dai kewa da ba'a rasa ba. Jinjina kai

Chapter 34 of 49