je su kai Ma'eesha gidan kakannin nata, don haka suka tafi tare da ita.
A nan ne surukin nata ya tambaye ta wace sana'a take son fara wa, nan ta sanar ma sa cewa ko kowace sana'a ce za ta iya.
Nan ya fara ba ta zunzurutun kuɗaɗen da za ta fara sana'a da su, ya ce ta fara da siyar da atamfofi da leshi da su shadda da material.
Nan ta fara sana'a nan da nan Allah ya sa ma ta albarka ta bunƙasa. Ta fada haɗo wa har da takalmomi da haka da su sarƙa da ƴan kunne.
Don a yanzu haka manyan shaguna ne guda biyu yake da su a kasuwa wanda ake kula ma ta da su. Kuma ta samu mutane ma su amana dake kula da su.
Ma'esha na ta shekaru goma sha uku ta sauke Alkur'ani mai girma aka yi ma su walima. Tarbiyya daidai gwargwado ta samu daga wajan mahaifiyarta. Ma ta mai karamci da Dattaku ku , ta san ya kamata ga ta da hakuri juriya da hangen nesa.
Duk da kasancewar tana da masu ma ta aiki a gida hakan bai sa ta bar Ma'eesha sakaka ba tarbiyya ba, don ta koyar da ita duk wasu aikace-aikace aikace na gidan da girki da komai, wai a cewar ta ƴa mace ce gidan wani za ta je ba kowane namiji ke son mai aiki na ma sa komai ba musamman kula da ɗakinsa da kuma yi ma sa girki. Don haka take saka ya tama shiga cikin ma su aikin suna girki tare da Inno wata Dattijuwa dake yi wa Mummy aiki, matar akwai hankali kuma jininsu ya hadu da Ma'eesha.
Har ma'esha ta kai shekaru goma sha takwas iyayen ta ba su sake samun haihuwa ba. Kuma a lokacin ne ta kammala karatun secondry school. Kuma a wannan lokacin Daddynta ya siya ma ta mota.
Aka koya ma ta driving ɗin motar har ta iya wanda lokacin ne Daddy ya so tura ta ƙasar waje ta yi karatu a can amma Mummy ta hana. Ta ce gara yarinyar ta ta zauna a gabanta tana kallon ta hankalin ta zai fi kwanciya akan ta je can wata ƙasa da ba ta san tarbiyya da ɗabi'ar da za ta koya ba, ita dai a bar Ma'eesha a gabanta tana kallon halin da take ciki don ƴa mace tana da rauni. Don ta ba wa Ma'eesha tarbiyya mai kyau ba ta yarda da yawon gidan ƙawayenta. Ƙawarta daya ce a duniyar nan sai dai abokan karatun ta.
Wata rana Mummy ta fito daga gida tana bayan mota direba zai fita da ita zuwa kasuwa ta duba kayan da babu. Don yanzu har Dubai take fita siyen kaya. Sai ta ga wata mata rakuɓe kusa da gidansu ita da yar biyu saurayi daya sai budurwa guda ɗaya.
Ba ta ce komai ba suka wuce, bayan ta dawo za ta shiga gida tana bayan motar, still su ta fara gani, sai wannan matar ta rugo da sauri ta nufi motar, ganin haka ya sa Mummy ta ce wa direban ya tsaya.
Bayan ta sauke gilashin motar ne ta ce.
"Baiwar Allah lafiya daga ina haka, yaranki ne can?"
Ta daga kai kawai ta kasa magana, da ƙyar ta iya cewa .
"Ki taimaka ma na da abinci yunwa, tun jiya ba mu ci komai ba ni da yara na."
Tana gama fadar haka ta zube a wajen a sumammiya, yayin da saurayi da buduwarwar suka ƙaraso kanta suka kiran sun Mamy, buduwarwar har tana kuka. Da sauri Mummy ya fito cikin motar tana salati.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce ✍️
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page1️⃣5️⃣
Tama gama faɗar haka ta zube a wajen a sumammiya, yayin da saurayi da budurwar suka ƙaraso kanta suka kiran sunan Mamy, budurwar har tana kuka. Da sauri Mummy ta fito tana salati.
"Baiwar Allah lafiya?"
Direban ne shi ma ya fito daga cikin motar yana cewa.
"Suma ta yi ya kamata mu yayyafa ma ta ruwa watakila ta farfaɗo."
Da sauri Mummy ta ce .
"Kawo ma na ruwan ko?"
Da sauri ya bude murfin motar ya dauko robor ruwa ya zo ya yayyafa ma ta, ajiyar zuciya nauyi ta sauke sannan ta fashe da kuka tana cewa.
"Yauwa wayyo na shiga uku na lalace ku taimaka ma ma da abinci."
Jin haka ya saka Mummy ta ce .
"Ba damuwa mu je ciki za ku ci abinci."
Laila ta kama mahaifiyar ta ta da taimakon ta ta tashi tana rike da hannunta. Mummy ta ce wa direban ya ja motar zuwa ciki ita za ta karasa shigowa da ƙafa .
Ya shiga cikin motar ya ya tayar suka bi bayansa da ƙafarsu, budurwar na rike da Mahaifiyarsu.
Bayan Mummy ta murɗa handle ɗin kofar ta shiga da sallama ta ce su shigo. Suka shiga ciki kowa ya zauna akan Centre carpet.
"Haba ku tashi ku zauna akan kujera ma na."
Mummy ta fada tana Murmushi. Suka hada baki wajen cewa.
"A'a nan ma ya yi."
Ɗaya daga cikin masu aikin gidan ta kira ta ba ta umarnin kawo abinci wa ɓakin.
Mau aikin ta gaida su ta wuce don cika umarnin matar gida.
Ba jimawa aka cika ma su gabansu da kayan ciye-ciye, ta yi servin ɗin su abincin da za su ci.
Sannan ta zuba ma su farfesun a cikin bowl huda uku kamar yadda ta zuba ma su abinci. Kasancewar ta hana mai aikin ta zuba ma su abinci da lemu.
Ta koma ɗakinta ta basu wuri don su sake su ci abincin.
Tana barin wajen jiki na rawa kowa ya dauki plate ɗaya na abincin suka hau ci cikn haɗama.
Nan da nan suka cinye suka ɗauki farfesun shi ma suka cinye suka shanye romon da lemu suka sha ruwa.
Laila ta buɗe ƙular ta ha sauran abinci ta kara masu duka suka cinye suka lashe plate.
Bayan sun shanye lemu sun sha ruwa ne suna zaune sai ga Mummy ta fito da fara'a tana ma su sannu da zama.
Nan suka hau yi ma ta godiya.
Horn ɗin mota suka ji a bakin gate, nan fa nan maigadin gidan ya bude gata.
Motar ta cinno kai ta shiga cikin nutsu ake driving motar.
Bayan an yi parking motar ne sai mamallakiyar motar ta ziro fararen ƙafarta ta fito daga cikin motar. Hannunta daya riƙe da makullin motar ɗayar hannun kuma rike da handbag ɗin ta.
A hankali take tafiya kamar mai jin tausayin ƙasa.
"Hajiya Ma'esha kin dawo?"
"Eh na dawo ina wuni?"
"Lafiya lau ya karatun?"
"Alhamdulillah."
Daga nan ta shiga cikin ga gidan ta tura kofar falon da sallama.
"Assalamu alaikum"
Gabanta ne ya faɗi sakamakon ganin wannan matar da yaranta ke kiranta da Mamy.
Amma sai ta dake ta karaso ciki ta gaida Mummy.
"Ina wuni Mummy?"
"Lafiya lau kin dawo?"
"Eh Mummy na gaji."
Murmushi ta yi sannan ta ce .
"Ba ki ga baki ba ne?"
Ma'eesha ta kalli Mamy wacce ta ji sam matar ba ta kwanta ma ta ba.
"Ina wuni?"
Washe baki ta yi tana amsa wa Ma'eesha gaisuwar. Sai ta kalli dayan saurayin za ta gaishe shi ya yi saurin cewa.
"Ina wuni ranki ya daɗe."
Murmushi ta ɗan yi sannan ta amsa ma sa cikin fara'a, sai budurwar ita ma ta gaishe ta, ta amsa ma ta cike da fara'a.
Matar ta kalli Mummy ta ce .
"Hajiya taimaka ma na za ki kamar yadda Allah ya rufa ma ki asiri mu ma ki rufa ma na."
"Me kike so na taimaka ma ki da shi in dai bai fi ƙarfina ba zan yi ma ki in sha Allah."
"Ba mu da wajen zama, gidan hayan da muke ciki maigidan ya Kore mu saboda ba mu da kuɗin da za mu biya shi na haya, ga mijina ya rasu yara biyun nan nake da su to ba abun yi tun da ba su damu damar yin karatu ba. Don Allah Hajiya ki taimaka ma na ko za ki samar ma na wajen da za ki raɓa mu za mu dinga yi ma ki aiki dukkan mu, ko ba ki biya ki komai ba in da za ki ba mu abincin da za mu dinga ci muna so Hajiya."
Ta karasa maganar tana fashewa da kuka. Cikin tausaya wa Mummy ta ce kar ki damu ba aikin da muke bukatar ayi mana , ma'aikata sun ishe mu, amma ba na da ikon ba ki wajen zama a gidan nan ba tare da izinin maigidan ba. Amma za ku zauna a B.Q na gidan nan kafin ya dawo sai a san abun yi."
Gabadaya suka haɗa baki wajen yi ma ta godiya suna farin ciki da wannan ni'imar da Allah ya yi ma su.
Mummy ta kalli Ma'eesha ta ce.
Tashi ki kai su BQ ɗakin da ba kowa sai su zauna a ciki.
"To Mummy."
Cewar Ma'esha ta fada tana mikewa tsaye, duk da dai hankalinta bai kwanta da lamarin mutanen ba. Ba yadda za ta yi ne ta hana mahaifiyar ta taimaka ma su amma jiki ta ya ba ta akwai wani abu mara daɗi da zai faru da su a dalilin mutanen nan.
Tana gaba suna bin ta a baya har suka ƙarasa BQ ɗin gidan.
Ta bude kofar ta shiga suka bi ta a baya. Madaidaicin falo ne da ɗakuna biyu a ciki da toilet da kitchen dake nan cikin dakin. Akwatin set ɗin kujeru a falon ɗakina biyu suka kowane akwai katifa a ciki.
Fitowa ta yi ta bar su suka ta jin daɗi suna yaba wajen.
Part ɗin su ta koma ta samu Mummy na waya Da Daddy, sai da ta bari sun gama sannan ta kalli Mummy ta ce.
"Mummy hankalina bai kwanta da wannan matar ba, don Allah idan taimakon su za ki yi ki ba su kudi su je su nemi haya su zaiuna, ki ba su kuɗin da za su ja jari amma ba na son zaman su a nan."
Shiru Mummy ta yi tana nazarin maganar ƴarta, ita dai iya sanin ta da Ma'eesha ba ta da ƙyamatar mutane duk yadda suka kai ga lalacewa kuwa. Ta san darajar Ɗan Adam Sosai, amma sam ta rasa dalilin da ya sa hankalinta ya kasa kwanciya da mutanen nan. Cikin sigar rarrashi ta ce.
"Shi kenan zan yi tunani akan hakan, amma ba kya ganin ita nan ta nemi mu ba ta ta zauna ba wai a ba ta kudi ta je ta nemi haya ba?"
"Eh na sani Mummy, amma ba ta da hujjar cewa anan dole za ta zauna, ai taimako ne ko gida aka ba ta a wata unguwar za ta zauna ai."
"Je ki huta za mu yi maganar daga baya."
Tashi ta yi ta nufi bedroom ɗin ta cikin sanyin jiki.
Haka nan su Mamy suka ci gaba da zama cikin gidan, ba abinda suke yi a cikin gidan, kullun da safe ma su aiki za su mai ma su abincin breakfast a part ɗin. Sannan da rana ma a kai ma su can part ɗin haka dare za'a kai ma su .
Ranar da suka cika sati daya a ranar ne Daddy ya dawo daga tafiyar da ya je.
Bayan ya yi wanka ya ci abinci ya huta ne Mummy ta ba shi labarin Mamy da yaranta da yadda suka yi . Kallon ta Daddy ya yi tare da cewa.
"Kin san daga ina suka fito ne?"
"Ban sani ba wallahi, amma dai abu ɗaya na sani shi ne suna bukatar taimako kuma na taimaka ma su."
"To yanzu ya kike son a yi da su?"
"Duk yadda ka ce haka za'a yi yallaɓai."
Murmushi ya yi sannan ya ce.
"A'a duk yadda kika ga ya dace sai ki yi na ba ki wuƙa da nama."
"To me zai hana mu zauna da su a nan gidan?"
Ɗan jim ya yi kafin ya ce .
"Nan gidan kuma?"
"Eh yallaɓai, na ga kamar tana son zama nan ne, don ba ta ce a ba ta wani gidan ko kuɗin siyen gida ko haya ba. Sannan kuma ai tana can BQ ba nan za ta zauna kusa da mu. "
"To ai ba ta da zaɓi muhalli take nema da Abinci, idan ta samu ko ina ne ina ne ai buƙatar ta dai ta samu mu abun da take nema."
"Haka ne, amma zan so a ce ta zauna kusa da mu, tana da yaro saurayi idan bai yi karatu ba sai a saka shi kasuwanci. Macen kuwa sai a saka ta a makaranta."
"Shi ke nan Allah ya mana jagora."
Da Anin ta amsa daidai lokacin da Ma'eesha ke ƙarasowa fakon hannunta da karamar jaka ta fito daga wajan kakarta da ta je yi ma ta weekend.
Ganin Dad ɗin nata ta saki jakar cike da murna ta karasa wajensa ta rungume shi.
"Daddy yaushe ka dawo ba wanda ya sanar da ni?"
"Yau na dawo Mamana ya kika bar su Hajjaju."
Da yake sunan da suke kiran da shi kenan.
"Hajjaju na can na bar ta da masifarta."
Mummy da Daddy a tare suka yi dariya.
"Daddy idan na masifa ba ta za ta ce wai na je na kwaso sauran kayan na dawo gidan nan da zama?"
"Yaushe aka yi hakan?"
Cewar Mummy tana kallon Ma'eesha, duk da ta san cewa Hajjaju ba ta ƙaunar ta har yanzu kuma ba ta nuna ma ta tsana yanzu, domin soyayyar da take yi wa jikar ta ya ɗan saka ya shafi mahaifiyar ta. Domin tana ƙaunar Ma'eesha sosai kamar ranta, ko don Ma'eesha kadai ce jikarta ɗaya da ta fito daga tsatson tilon Ɗants guda ɗaya da ta mallaka a duniya, ga shi ɗan nata shi ma Ma'esha kadai ya mallaka a duniya. Don haka tana ƙaunar Ma'eesha amma ta kasa ƙaunar mahaifiyar Ma'eesha har yanzu , amma tana amsa mata ba yabo ba fallasa idan ta zo gaishe ta sai dai ba ta wani sakin jiki da ita. Ita ma kamata Mummy yanzu abun ya daina damunta.
"To ai ba wani abu idan kin koma gidan nata da zama?"
Cewar Mummy tana Murmushi.
"To idan na koma can da zama ku fa ai ba ku fa kowa a nan, sai ku zauna haka daga ku dai ma su aiki?"
Murmushi Mummy ta yi tana cewa.
"Daga mu sai ma su aiki mana, to su ba mutane ba ne, ga kuma ƙarin wasu ƴaƴan na samu saurayi da budurwa."
"Ok ina suke?"
"Baƙin da kika raka su BQ nake nufi."
Take fara'ar dake fuskarta ta ɓace ɓat.
"Mummy please a ba su wani gidan su zauna can a ba su abinci, amma jikina ya na ba ni zuwansu gidan nan ba alkhairi ba ne.,"
"Ban san me ya sa ba ki ƙaunar mutanen nan ba."
Shiru Ma'eesha ta yi don a ya san me za ta ce ba. Don haka ta mayar da hankalinta ga Daddy ta ce.
"Daddy me ka dawo ma ni da shi tsarabar tafiyar ?"
"Mamana komai na kawo ma ki sai abin da ba ki so ne kawai ban siya ba."
"Thank you so much Daddy."
"You are welcome ."
Daga nan rayuwa ta cigaba da tafiya a hankali sabo da shaƙues ya fara shiga tsakanin Mummy da Mamy. Don ta sa Daddy ya kai Jamil kasuwa a ɗaya daga cikin shagunan ta yana siyar da kaya. Laila kuma an saka ta a makarantar secondary school kasancewar ta gama primary.
Sannu a hankali shaƙuwa ta fara shiga tsakanin Mummy da Mamy wanda kullum a bangaren Mummy mamy ke wuni kullun suna tare, Mamy kan bar BQ ta zo nan main house din su yi ta fira da da Mummy. Tun Ma'eesha ba ta sakin jiki da Mamy har yau da gobe yadda Mamy ke jan ta a jiki ta saki jiki da ita amma ba sosai ba.
Wata ranar talata da misalin karfe biyar na yamma Mummy ta dawo daga kasuwa, sai dai ba tare da dirbanta take ba ita kadai ce take driving. Don ranar direban bai da lafiya yana gida ta ce ya huta.
Kasancewar yanayin unguwar ba yawan mutane da yawa. Tana tsaka da tafiya ta ga mutum ya tsaya a gaban motarta, cikin azama ta taka birkin motar. Su biyu ne suka zagayo gefen me zaman banza ya zauna yana nuna ma ta wuƙa yana cewa.
"Ki bi umarnin da zan ba ki."
Daidai nan ɗayan ya shiga bayan motar ya zauna suka nuna ma ta hanyar da za ta bi, wanda ba ta da wani zaɓin da ya wuce bin maganar su.
Duk hanyar da suka nuna ma ta nan ta bi har suka shiga unguwar da ba mutane don sabbin gine-gine ne a unguwar su ma ɗaiɗaiku ne ba da yawa ba.
"Tsayar da motar."
Ta tsayar suka fito suna waige-waige.
Fitowa suka yi sannan suka ba ta umarnin ta fito ita ma. Fitowa ta yi tana rokonsa da kada su cutar da ita. Don ba ta san nufin su akanta ba, sun yi yi haka ne don su kawo ta wajen da na mutane su kashe ta ko sun yi haka ne don su yi ma ta ƙwace.
Tana ganin wata zabgegiyar wuƙa da suka fito da ita ya sa ta ruga a guje, ganin haka suka mara ma ta baya a guje suka bi ta.
Tana cikin gudu duk ta gaji ga numfashinta kamar za su ɗauke ta ji ta yi karo da mutum a gabanta.
Sai a lokacin ta lura da mutumin da ta yi karo da shi. Saurayi ne maji ƙarfi yana da siffa irin na zaratan maza. Bayansa ta laɓe tana rike rigarsa ta baya, domin ba za ta iya cigaba da gudu ba.
"Saurayi don Allah ka taimaka ma ni kada su cutar da ni."
Dariya samarin da suka biyo ta suka yi sannan ɗaya ya ce.
"Ta ya makaho da ba ya gani zai iya taimaka ma ki?"
Sai a lokacin ta lura da sandar jagoransa dake hannunsa, sannan ga wani baƙin gilashi da ya sa a idanunsa.
Cikin dakakkiyar murya ya ce .
"Ku bar wajan nan."
Dariya suka sake yi kafin ɗaya ya ce.
"Kai makaho ja sandarka ka yi gaba kafin na ƙarasa illata ka."
Cike da ƙwarin guiwa Makaho ya ce wa Mummy.
"Kwantar da hankalinki ba abin da da suka isa su yi ma ki."
Daidai lokacin ɗaya saurayin ya yi kukan kura ya nufo makahon a fusace, yayin da makahon ya ji yakin gudunsa ya ɗaga sandarsa daidai yana kawo wa ya buga ma sa Sandar a kai, wanda ya sa ya faɗi ƙasa yana birgima.
Ɗayan ma na ganin haka ya zo da karfinsa, nan ma makahon ya yi bugu ɗaya ya yi ma sa shi ma ya zube a wajan.
Ganin haka ya sa ta ce.
"Mu je ka bar wajan nan kar su tashi su illata ka."
Ta faɗa cike da tsoro.
"Sai sun ɗauki tsawon lokaci kafin su koma daidai. Ki wuce ki bar nan."
"Kai kuma fa?"
"Kada ki damu da ni."
"Ba zan bar ka anan ba, don Allah ka zo mu ke ka ji."
Haka ya bi bayanta suka isa wajan motarsa ta bude ma sa gefen mai zaman banza ya shiga.
Da sauri ta ja motar suka bar wajan tana godewa Allah.
"Ya sunanka."
"Khalifa."
"Na gode da cetona da ka yi. Mu je gidana duk abinda kake bukata zan ba ka ko meye, zan kai ka asibiti a yi ma ka aikin idanunka ko da ƙasar waje ne."
"Haka idanuna suke, haka aka haife ni ba aikin da za'ayi ya bude kuma."
"Ayyah na ɗauka lalura ce ta same ka."
"A'a."
Ya ba ta amsa a takaice. Ba wanda ya sake magana har suka isa gidan, ta danna horn maigadi ya bude ma ta ta shiga da motar zuwa parking space ta yi parking.
"Hajiya ni zan koma gida, ba na bukatar komai."
"To na ji mu je ka gaisa da iyalina ga mijina ma ya dawo ƴata ma ta dawo ina son na ma su bayanin komai a gabanka."
Daga haka suka fito tana gana yana bin ta da sanadar jagoransa suka shiga ciki.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce ✍️
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page1️⃣6️⃣
Daga haka suka fito tana gana yana bin ta da Sandar jagoransa suka shiga ciki.
Da sallama ta shiga falon, Daddy da Ma'eesha dake zaune a falo suna jiran dawowarta suka mike suna ma ta kallon mamaki. Ganin yanayin ta da kuma wanda take tare da shi.
"Lafiya kuwa Mummy, yanzu Daddy ke shirin kiran wayarki sai muka ji ƙarar motarki."
Murmushi ta yi tare da cewa.
"Na auna arziki ne yau."
Da sauri Daddy ya mike tsaye yana kallonta.
"Subhanallah ba abun da ya same ki ko?"
Murmushi ta yi ta ce
"Ba komai Daddyn Ma'eesha Allah ya kare ni fa ya tura mun wannan bawan Allah ya taimake ni."
Sai a lokacin ne suka lura da Makaho, cikin sakin fuska da fara'a Mummy ya kalli Makaho ta ce.
"Ƙaraso ma na Bismillah."
Sai a lokacin Makaho ya karaso ciki ya zauna a saman carpet.
Nan Mummy ya ba wa Daddy da Ma'eeaha labarin duk abinda ya faru da ita a hanya da haduwarta da makaho.
Sun jinjina lamarin sosai nsannan Daddy ya ɗebi kudi ya mikawa Makaho yana cewa.
"Ga wannan kudin ka damu na kashe wa ko?"
Hannu ya daga ɗaga alamar ba zai karɓa ba. Nan Mummy da Daddy suka yi suka yi ya karba kudin amma sam ya ce ba zai karɓi ko sisi daga wajan cikin kudin da suka ba shi ba. Mamaki suka yi ga shi makaho kuma bai yi kala da wanda yake da kudi ba. Don sai da Mummy ta kare ma sa kallo. Kuma ta rasa me za ta bashi da zai kaba a matsayin tukuicin ceton ranta da ya yi.
Abinci ta saka Ma'eesh ta kawo ma sa. Sai dai ya ce ba zai ci ba.
Kallon Ma'eesha dake rike da tire da ta kawo abinci Mummy ta yi kafin ta ce.
"Mayar da abincin ki hada ma sa take away ya tafi da shi."
"To Mummy."
Ta faɗa tana nufar hanyar kitchen, don dama ba kowane lokaci Mummy ke sanya ma sai aiki yin abu ba, wani lokacin Ma'eesh take saka wa.
Daddy ya kalli Makaho ya ce.
"Bawan Allah ya sunanka?"
"Sunana Khalifa."
"Ma sha Allah, amma me ya saka ba ka karbi kuɗimda la ba ka ba, ko sun ji kadan ne?"
"A'a Alhaji ba haka ba ne, na yi komai saboda Allah ne, idan na karbi kuɗin ku ai ya zama kamar na kudi kuka biya Ni, kuma ba na yi don ku biya ni ba ne na yi saboda Allah ne."
Murmushi Mummy ta yi tare da cewa.
"Iyayen ka suna raye?"
"A'a ba sa raye Allah ya yi ma su rasuwa tun ina yaro."
"Yanzu a ina kake zaune?"
"Gidan wasu bayin Allah ne sauka ba ni ɗaki nake zaunar fisabilillah."
"Za ka iya zama da mu a baka ɗaki can bangaren mazan da ke mana aiki?"
"A'a Hajiya na gode ki bar shi kawai."
Jinjina kai ta yi kafin ta ce.
"Ina neman wata alkfaea a wajen ka."
Faɗi ina dai bai fi ƙarfina ba in sha Allah zan yi ma ki."
"So nake kullun ka dinga zuwa gidan nan ka na karɓar Abinci."
"Eh to kada na ce a'a ki ga laifina komai na ƙi karba, amma dai zan dinga zuwa duk ranar juma'a in sha Allah ina karbar abinci ko na ci."
"Sauran ranakun da?"
"Ba tabbas zan iya zuwa. Amma idan na damu sarari jefi-jefi za ki dinga ganina"
Daidai lokacin Ma'eesha ta karaso rike da leda da ta hadi take away da abin sha da su snacks."
Mummy ta karɓa ta miƙa ma sa ya yi godiya ya nufi hanyar fita daidai lokacin Mamy ta shigo tare da Laila suka yi sallama.
Gabadaya suka amsa ma su sallamar.
Laila na ganin makaho zai fita ta ce.
"Yaushe mabarata suka fara shigowa har cikin gidanmu ne?"
Cak ya tsaya wanda kallo ɗaya za ka yi wa fuskarsa ka san cewa ransa ya ɓaci.
"Ni na mabaraci ba ne, duk da cewar ina da makasa to ba kasashshe ba ne, ina d abun yi kira na aka yi dole na zo gidan nan, kuma ban zo gidanku don a wulakanta ni ba. Na ɗauka gidan karamci da sanin darajar Ɗan adam na zo."
Ma'esha ta yi saurin cewa.
"Ƙwarai kuwa gidan karamci da sanin darajar Ɗan adam ka zo, kuma ka ga yadda muka karrama ka, ita wacce ta yi ma ka maganar ba ƴar gidan nan ba ce cin arziki ta zo, ka yi haƙuri Yaya Khalifa."
Har ga Allah ya ji dadin zancen Ma'eesh sai dai bai ce komai ba ya fita.
Hatta Daddy da Mummy
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 49