cikin sauƙi_.✏️
Page5️⃣0️⃣
Da kallon mamaki take bin sa har ya fice. Ta rasa gane dalilin da zai saka a duk lokacin da za ta cire kaya ko za ta saka kaya sai ya fita ya bar ma ta ɗakin. Bayan shi ba gani yake yi ba to meye amfanin fitarsa tun da bai da idanun ganinta.
Rigar barci ta saka riga riga ce iya guiwarta ba ta da hannu sai na singileti ta saka sai turaren da ta fesa.
Fitowa ta yi ta gan shi tsaye ya jingine sandarsa a bangon ɗakin ya tura hannayensa duka biyu cikin jallabiyar da ke
Jikinsa yana kallon sararin samaniya. Da dukkan alamu ya yi zurfi cikin tunanin da yake yi. Kallonsa ta yi na wasu daƙiƙu kafin ta ƙarasa wajensa tana murmushi.
"Lafiya ka zo nan ka tsaya kuwa?"
"Lafiya lau, me kika gani?"
"Na ga daga fitowa ta wanka ka yi saurin fitowa daga ɗakin."
"Na ba ki waje ki shirya ne."
"To ni ban damu da ka fito ko kana nan ba, domin ko na cire kaya a gabanka ai ba gani na kake yi ba to me ye amfanin fitowarka?"
Murmushi kawai ya yi wanda shi kaɗai ya san ma'anar sa.
"Mu koma ciki to."
Ta yi maganar tana jan hannunsa zuwa cikin ɗakin ɗayan hannun ta ɗauki sandarsa.
Tunani yake yi a zuciyarsa yadda Ma'eeha ta kamu da son sa. Duk da ba ta san shi waye ba daga ina ya fito, duk da nakasar sa da halin talauci da yake nuna ma ta ba ta taɓa nuna ma sa wani abu da zai tabbatar ba ta son sa ba, kullun halin da take nuna ma sa a aikace shi ne nuna soyayyar ta a gare shi.
Zama suka yi a tabarmar da yake kwanciya akai. Tana fuskantarsa duk da shi kansa kasa yake kallo don daga ita sai rigar barci wacce ko gama rufe guiwarta ba ta yi ba. Kuma kanta ba ɗankwali babu ta tufke gashin kanta.
Wayarta ce ta soma ruri ta ɗan mika hannu ta dauki wayar.
ASP Nasir ne ke kiran wayarta.
Sam ita ta ma mance da shi, kuma ta san kiran nasa yana da nasaba ne da zancen ɓatar mijinta da ta kai rahoto, tun da ya ce za su yi bincike zai su neme ta.
Har wayar ta katse tana tana tana tunani, har sai da Makaho ya ce ma ta.
"Ba kiran wayarki ake yi ba?"
"Eh kira ne ya katse."
Daga haka bai sake yin wata magana ba, sai wani kiran ya sake biyowa baya.
Ɗaga wa tayi tare da yin sallama.
"Assalamu alaikum warahmatullah."
"Wa'alaiki salam."
"Ina wuni ASP ."
"Lafiya lau, ya kika ji da fargaba?"
"Alhamdulillah."
"Kin ji ni shiru ko, to sai dai na ce ki kara hakuri muna nan muna bakin iya ƙo..."
Murmushi da ta yi ne ya saka ya yi shiru, don ya san in dai Ma'eesha da ta zo station na su cikin tashin hankali tana kuma na ɓatar mijinta ce bai kamata yanzu ace tana wannan murmushi ba sai dai idan ya dawo su ba su sani ba."
"Ya dawo gida ne?"
"Eh ya dawo gida yanzu haka yana kusa da ni."
Shiru ta yi na ɗan lokaci kafin ya ce.
"Na taya ki murna."
"Na gode sosai."
"Idan ba damuwa zan iya tambayarki ?"
Ta san zancen da zai ma ta, saboda ta ga mamaki da tarin tambayoyi akan fuskarsa ranar da ta je kai rahoton ɓatar mijinta. Don haka ta ce na sa.
" Yanzu barci nake ji."
"Okay good night and sweet dreams."
Daga haka ta kashe kiran wayar. Ta kalli Makahon mijinta ta ce.
"Police ɗin da na kai ma sa rahoton ɓatar ka ne yake kira na."
Kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce .
"Amma da dukkan alamu ba ranar da kika kai rahoton ba ne kika fara saninsa. Dama can kun san juna kuma akwai alaƙa a tsakanin ku."
Kallon mamaki take yi ma sa yadda ya iya fahimta cikin sauƙi.
Shiru ne ya biyo baya kafin ya katse shirun da cewa.
"Lokacin da na ɓata har wajen police kika je kai rahoto."
Murmushin ta yi kafin ta ce.
"A lokacin da ka bata na shiga tashin hankali sosai ba kaɗan ba, na shiga makamancin tashin da na shiga lokacin da na rasa mahaifiya ta. Domin a wanan duniyar ba ni da kowa sai kai ka na mayar fitila ta kuma madubin dubawa ta, idan na rasa ka ban san inda zan tafi ba. Don ba zan iya rayuwa ni kaɗai ba, mahaifiyata Allah ya dauke ta, mahaifina ya juya ma ni baya. Ya nuna baya bukatata danginsa na sun juya ma ni baya. A baya duk da kakata Hajiya Turai da ta haifi Babana ba ta son mahaifiya ta, amma ni tana so na sosai, amma lokacin da mahaifina ya juya ma ni baya ita ma sai ta juya ma ni baya. Ban san inda dangin mahaifiyata suke ba, ban san in da zan samo su ba."
Ta yi maganar tana goge hawayen da ya gangaro ma ta.
"Ita mahaifiyarki ƴar ina ce?"
Tamabayar da ya yi ma ta kenan yana jin ba dadi a zuciyarsa.
"To an ce dai ƴa gidan marayu ta tashi, a ziyarar da kakana je kaiwa gidan marayu yana raba ma su kaya da abinci ne wata rana suka je da mahaifina gidan marayun in da ya ga mahaifiyata ya ce yana son ta. Wanda dalilin haka ya sa kakata Hajiya Turai ta tsani mahaifiya ta saboda rashin sanin asalinta."
Kamar an fama ma ta in da ke ma ta ƙaƙayi sai kuka take yi har da sheshsheƙa.
Shi ya ma rasa me zai ce ma ta da in da zai rarrashe ta. Don shi sam bai iya rarrashin da daɗaɗan kalamai ba.
Ɗan bubbuga bayanta ya yi alamar rarrashi, a hankali take dauke ajiyar zuciya.
Bayan wasu mintuna ta ce
"Har yau ban san tarihin rayuwarka ba, daga ina ka fito su waye iyayen ka suna raye ko ba su raye ban sani ba. Kuma ya kamata na san komai game da mijin da nake aure. Idan ƴaƴan da aka damu da su ne ko aka san danginsa ai ba za'a taɓa aurar da su ga Mutumin da da ba'a san asalin ko waye shi ba an yi bincike ina danginsa suke ba. Amma ka ga ni ba su damu da ko ɗan yankan kai ne ba sun ba da ni sun huta."
Ta yi maganar cikin ƙunar rai.
Tunawa ta yi da yadda Mamy ta shigo rayuwarsu, da yadda Mummy ta karɓe ta ba tare da sanin mugun nufin da ta zo da shi ba
Yau da gobe ba ta canja kowa, sai dai yau da gobe na bayyana ma ka haƙiƙanin mutane.
A hankali take tuna rayuwar ta ta baya tana zubar da ruwan hawaye.
Shi ma Makaho a nasa bangaren tunanin da yake yi daban ne
Soyayya na bukatar wani matsayi na karfi da kulawa tana bukar ɗauakar ɗawainiya ba wai kawai rabon damuwa ba.
Shi kam zai iya cewa ta wannan ɓangaren ya gaza yin duk waɗan abubuwa. Amma ita har yanzu ba ta taɓa ganin gazawarsa ba.
"Ka ɗan bani taƙaitaccen tarihin rayuwarka ma na."
Sai da ya ji gabansa ya faɗi, amma sai ya dake bai nuna hakan ba.
"Na tamabaye ka kwanakin baya akan sanin asalinka amma ba ka sanar da ni ba, kuma ya kamata na san da wa nake zaune, kamar yadda ka san tarihin rayuwata ban ɓoye ma ka ba, wanda ko yau ka tamabaye ni wani abu a shirye nake da na sanar da kai."
"Babu wani abun birgewa a cikin sanin tarihin rayuwata, ba na son tunawa ne shi ya sa ban sanar da ke ba, ki bari idan lokaci ya yi zan sanar da ke."
"Haba wani lokaci kuma zai yi, aure fa muka yi ya kamata na san wani naka ko wani abu naka."
Shiru ya yi kafin ya sauke ajiyar zuciya ya fara magana.
"Sunana Khalifa kamar yadda kika sani, Ni na fito ne daga Jahar Maiduguri a wani ƙauye muke rayuwa da iyayena da dangina duka a kauyen muke. Ina nufin kowa nawa yana cikin ƙauyen. Ni dama ko da aka haife ni da laluran makanta aka haife ni, ma taso ina raywai ni kaɗai ne ba tare da abokai ba, kasancewar ba na gani sai dai idan yara na wasa na kan je nisa da su na zauna ina sauraren su. Don ni ne na fari sai ƙanina guda ɗaya da nake da shi. Mukan yi wasa da shi a gida musamman idan mahaifiyarmu ta hana mu fita takan ce mu yi wasa mu biyu a gida, hakan ya sa ƙanina ya daina fita wasa shi ma. Sai dai shi an saka shi makarantar boko wanda Ni kuma iya makarantar islamiyya aka saka ni. Ina da shekaru ashirin wani iftila'i ya faɗawa ƙauyen mu na rikicin ta'adda ci in da aka kashe mafi yawan ƴan ƙauyen mu. Daga baya kuma gobara ta tashi a kauyen in da aka yi asarar rayuka da yawa har da iyeyena da ƙanina da sauran dangina na uwa da na uba. A ƙwauyen ɗaiɗaiku ne ba su da yawa.
Daga nan kowa ya dinga watse wa ana barin ƙauyen, wanda ni ma na bi sahun wasu har na tsinci kaina a garin nan.
Kuka sosai Ma'eeha ke yi tana tausaya ma su, sai dai ita tana da abu ɗaya, idan mutum ƙarya ya faɗa taka ji a ranta cewa ƙarya ne, shi ya sa lokacin da Mummy ta kawo Mamy gidan nan ba ta goyi bayan ta ba, kamar ta san abun da ke faruwa a kasar zuciyarta.
Haka wannan labarin na makaho duk da ta tausaya ma sai dai a kasar ranta, take ji kamar kada ta amince don haka ta ce.
"Wannan maganar da ka yi Mani na tarihin rayuwar ka idan na gane cewa ƙarya ne to ka sani za mu samu matsala da kai. Na tsani karya da cin amana, idan mutum ya yi ma mi daya daga cikin su ma nakan ji na tsani mutum.
"Kina tunanin ƙarya na yi ma ki?"
"Ban ce ka yi ma ni karya ba, na dai faɗa ma ka ne don ka sani."
_Fahad_
Zaune yake a dinning table shi da mutanen gidan, an loda ma sa kalolin abinci. Inna, Baba, Mama, Rumaisa, Farida, sai kuma Sidra.
Sai kalle-kalle yake yi ya rasa ta ina Nadra za ta ɓullo.
Mama na lura da yanayinsa kuma ta harbo jirginsa. Tsakuran abincin kawai yake yi ya kai wa baki amma ba wai don ya shirya cin abincin ba ne.
Sidra kan idanunta kur akansa ta zuba ma sa idanu kamar za ta cinye shi.
Sautin takalmi ne suke ji alamar ana zuwa waje da suke. Da sauri Fahad ya juya yana kallon wajen. Aunty Rahama ce da Nadra suka gani suna nufar dinning table idanun Fahad kur akanta ko ƙyafta idanun baya yi.
Da sallama suka ƙaraso wajen, gabadaya suka amsa ma su sallamar.
Zama suka yi kan kujeru biyu da suke jere wanda ba kowa akai.
Nadra ta gaida su suka amsa ma ta, yayin da ɗaya daga cikin ma su aikin ta fara sevin din su.
Ko da wasa ba ta ɗaga kai ta kalli in da Fahad yake ba. Shi kuma idanunsa na kanta, tambaya kasa yake yi.
Ya aka yi ta yi wani haske ta washe, ga fatarta sai ƙyalli take yi, ta kara cika ta zama babbar mace. Ɗaga kansa ya yi ya kalli Mama, yaga shi take kallo.
Kansa ya mayar kasa yana cigaba da cin abinci nasa.
Nadra ma ba wani cin abincin kirki ta yi ba ta tashi ta nufi ɗakin Mama.
Yana ganin ta shiga cikin ɗakin, ya mike tsaye yana cewa.
"Alhamdulillah."
Farida da Rumaisa suka ɓata fuska Farida na cewa .
"Ya ba ka ci abincina ba, Ni na dafa ma ka abincin don na burge ka fa?"
"Ayyah sorry anjima ki ɗumama ma ni zan ci."
Murmushi ta yi tana cewa.
"Zan saka ma ka a microwave oven na kawo ma ka shi."
"Yaya nawa fa ba ka ci ba."
"Ke ma har da ke?"
"Jinjina ma sa kai ta yi."
"Me kika dafa ma ni?"
"Faten doya."
Yadda ya yamutse fuska ne ya saka mutanen dake wajen yin dariya.
Takaici ta ji wanda ganin haka ya sa ya ce.
Zai ci ita ma. Wanda hakan ya sa ta saki ranta ta daina jin haushi.
Hankalinsa na kan Nadra da ta nufi part ɗin Mama.
Don haka part ɗin ya nufa kai tsaye.
Tana zaune kan kujera tana tana chatting da wata mata da Aunty Rahama ta haɗa su a waya, ita ce Aunty Rahama ke siyen kayan gyaran jiki a wajen ta tana ba wa Nadra. Kuma Aunty Rahama ta sanar wa matar halin da Nadra ke ciki. Kuma matar tana ba ta shawarwari. Wanda ta taimakon su ne ma Nadra ta daina sigar manyan hijabai da take yi a baya.
Yanzu ma tana sanar wa matar ne dawowan Fahad. Duk da tana son ta rabu da shi ne sa koda yayarta na son da har yanzu, sai dai matar da Aunty Rahama suna ɗora ta akan hanyar da za ta mamaye zuciyarsa ne.
Ƙamshin turarensa da ta ji ne ya haifar ma ta da faɗuwar gaba, wanda hakan ya sa ta ɗaga kai ta kalle shi. Yana tsaye ya zuba ma ta Mayun idanunsa.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce✍️
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page 5️⃣1️⃣
Ƙamshin turarensa da ta ji ne ya haifar ma ta da faɗuwar gaba, wanda hakan ya sa ta ɗaga kai ta kalle shi . Yana tsaye ya zuba ma ta mayun idanunsa.
A hankali takowa ya fara yi zuwa gabanta cikin takunsa na ƙasaita.
Miƙewa tsaye ta yi sai dai ta kasa kallon cikin idanunsa. Har sai da ya matso dab da ita.
"Ba ki ga na dawo ba ne?"
"Na gani."
Ta faɗa tana kallon gefe fuskarta ba walwala."
"Okay kin ganni amma ba ki iya gaishe ni ba? Saboda kin raina ni ko saboda me? Saboda kin ga gadon barcina ko?"
Kafin ta yi magana Mama ta turo ƙofar ta shigo.
"Lafiya?"
Komawa bayan Mama ta yi tana kuka, shi kuma ya saki baki yana kallonta da mamakinta.
"Me ka yi ma ta?"
"Ba abun da na yi ma ta. Na zo ne na sanar da ita ta tattara kayanta za mu koma gidanmu."
Wani kallo Mama ta yi ma sa kafin ta ce .
"Ta tattara me?"
Sanin ba magana mai daɗi zai fito daga bakin Mama ba ya sa ya juya ya fice daga ɗakin. Don baya son Mama ta yi ma sa fada gaban wanan yarinyar.
Tana fita Mama ta kalli Nadra wacce daga kukan shagwaba zuwa na gaskiya, sakamakon jin Fahad ya ce za su koma gidansa wanda ita kam ba za ta so hakan ba.
"Mama zan zauna tare da ke ba zan bi shi ba."
"To kada ki damu kina tare da Mamanki ."
Nan ta cigaba da rarrashinta har sai da ta saki jiki.
"Shiga ɗaki ki kwanta ki huta."
"Ba musu ta nufi bedroom ɗin Mama dan ta kwanta. Sai da Mama ta ga shigarta sannan ta nufi ƙofar fita.
A corridor da zai sada ka da part ɗin Mama ta same shi tsaye ya rungume hannu a ƙirji ya zuba wa ƙofar idanu.
"Lafiya kuwa?"
"Mama wai me kike nufi da ni akan wanan yarinyar ne, na ga ta takan raina ni ne sannan kina goyon bayanta."
"Au haba? Zaginka ta yi ko me?"
"Na shirya ta zo mu koma gida."
"Ba in da za ta je."
"Saboda me Mama?"
"Tun da ka bar ƙasar nan ka tafi daidai da sau ɗaya ka taba kiran ta a waya ka ji lafiyar ta? Ko ka taɓa tamabayar wani cewa ya take, ba ka san da ita ba sai yanzu da ka dawo ne take da amfani a wajen ka? To bari ka ji ka tattara naka ka koma kai kaɗai dama can ka ce ba son ta kake yi ba."
Tana faɗar haka ta nufi main falon gidan. Kallon ƙofar ɗakin Mama ta yi kafin ya karasa ya tura ƙofar, ba ta falon sai ya nufi bedroom kai tsaye.
Kwance take a saman gadon Mama ta juyawa ƙofar baya.
A hankali take tafiya cikin ɗakin, har sai da ya karasa dab da ita sannan ta ji ƙamshinsa.
Tsoro ne ya kamata tana kokarin ja da baya ya yi saurin janyo hannunta ya riƙe.
Tsuke fuska ta yi tana kau da kai, da mamaki yake kallonta ganin yadda ta murtuke fuska.
"Yaushe kika raina ni har haka ne?"
"Tun ranar da ka nuna ma ni ko kai waye."
"Ni?"
Yayi tamabayar yana nuna kansa.
"Yaya Fahad me kake tsammanin gani daga gare ni? Na yi farin ciki da murnar dawowarka? Idan ba ka sani ba ka sani ba na farin ciki da dawowarka ba na ƙaunar ganin fuskarka a kusa da ni."
"Da gaske?"
Kai ta jinjina ma sa alamar eh. Gajeren murmushi ya yi kafin ya ce.
"Why?"
Kamar tana jira ta fashe ma sa da kuka tana cewa.
"Ka mance da abun da ka yi ma ni a daren da za ka tafi? Ka mance azabtar da ka gana ma ni, babu imani da tausayi ka saka ƙafa ka bar ƙasar nan ba tare da ka iya bude baki ko sannu ka ce ma ni ba ballanta ka taimaka ma ta ni? Kai kawai kanka ka sani ko na mutu buƙatar ka ta biya ko? Ka bar ƙasar ba ka da damu da halin da nake ciki ba ballantana ka kira ka tamabaye lafiyata akan halin da ka saka ni, amma kake tsammanin zan yi farin ciki da dawowarka?"
Ta karasa maganar tana kukan da yake fitowa daga ƙasar ranta, wanda ke nuna ƙuncin da zuciyarta ke ciki.
Shiru ya yi yana kallonta, wato abun da ya yi ma ta ya tafi ta rike shi a ranta duk tsawon watannin da ya yi a can, dama tana jin haushi da baya kiran wayarta kenan ko ya tambaye ya take. Shi kansa ya san bai kyauta ba, amma kuma ya zai yi .
Janyo ta ya yi a jikinsa ya rungume yana bubbuga bayanta alamar rarrashi.
"Ko ban ta fi ba idan ina ƙasar ba abinda zan iya yi ma ki, domin ko ina nan Innar dai da na kira ma ki ita ce zan sake kira ma ki ita. To banbanci da ina nan ko ba na nan, sannan da ban kira ki ba kin damu da ni ne, ko kin taɓa cewa bari ki kira ni ko tura ma ni saƙo?"
Tsabar takaici ture shi ta yi daga jikinsa tana ja baya, wato har yanzu girman kan nasa da jin kansa yana nan ba abun da ya sauya. Wato ba zai ba ta hakuri ya yarda ya yi ma ta laifi ba ko, sannan tsabar ya raina ma ta wayo ita ce za ta kira shi .
Ganin ta tura shi ta cigaba da kuka ya share ta ya yi fice daga ɗakin. Don shi baya jin zai iya ba ta haƙuri..
Goge hawayen ta yi ta na mamaki girman kai da jin kai irin na Fahad Majidaɗi.
Har ya fita ya dawo ya kalle ta ya ce.
Ki shirya mu koma gidanmu anjima."
Ina za fice Daga cikin dakin.
_Makaho_
Har karfr goma sha biyu ba dare suna fira da Ma'eesha, ita kanta ta san cewa ba su taɓa dadewa suna fira irin na yau ba. Ganin karfe goma sha biyu ya yi ne ya sa Ma'eeha ta rufe ƙofat ɗakin.
Nan kuwa zafi ya fara yi ma su sallama. Wanda ya sa ya Ma'eesha jan gajeren tsuki , Makaho ya ce
"Me ya faru ne kike tsimi?"
"Zafin nan ne yadda ya addabe mu."
"Kada ki damu za ki yi barci me daɗi."
Kan katifarta ta nufa ta hau sai da ta yi addu'ar kwanciya barci sannan ta kwanta .
Kwanciyarta ke nan ta ɗauki mefeci a gefen filon sannan ta kashe hasken da ta kunna, dama torchlight ɗin wayarta ce ta kunna.
Tana ɗan fifita idan barci ya kama idanun nata sai ta saki mafecin ya faɗi, daga nan kuma zafi zai sa ta farka ta kasa barci.
Ji ta yi ana lalubarta cikin barci, cikin tsoro ta ce.
"Yaya Khalifa?"
"Na'am ba ni mafecin na yi ma ki fifita."
Sai a lokacin ta saki aniyar zuciya tana cewa.
"A'a ka bar shi kai ma na san barci kake ji."
"Kada ki damu ba na jin barci, idan ma ina ji to zan kwanta."
Ba musu ta mika masa mafecin, ya fara yi ma ta fifita wanda ya sa nan da nan barci me daɗi ya ɗauke ta.
A daren ranar bai rintsa ba kwana ya yi yana yi ma ya fifita kamar yadda ya saba yi ma ta. Ita har mamakin yadda baya barci take yi. Ai dare mahutar bawa ne, ko ta hana ta ce ya yi barci baya yi.
Da Asuba ne ta farka daga barci tana mamakin sa.
"Ma'eesha kin tashi ne?"
"Eh na tashi sannu da ƙoƙari."
Wanka ya je ya yi sannan ya ɗauro alwala ya wuce masallaci.
Ita ma wankan ta yi ta ɗauro alwala ta gabatar da sallar asuba.
Sai da safe karfe shida da rabi ya dawo gidan.
Ƙamshin girkinta ne ya yi ma sa sannu da zuwa.
Ruwan Lipton ne wanda ya ji kayan ƙamshi take dafa ma su, don ta siyo kayan tea da biredi wanda ta siyo a shago da safiyar nan.
"Assalamu alaikum warahmatullah."
"Wa'alaika salam warahmatullah. Sannu da zuwa."
"Yauwa sannu da ƙoƙari Ma'eesha ."
Tabarma ta shimfida ma sa tana cewa.
"Ga tabarma nan daga cikin baranda na shimfida ma ka "
Ta ja hannunsa zuwa wajen tabarmar ya zauna, sannan ta durkusa cikin girmamawa ta gaishe shi, ya amsa ma ta cikin farin ciki da sanya albarka.
Ruwan shayin ta zubaa sa da madara pick powder na sachet da milo sachet ɗaya ta zuba sugar kadan ta ba su shi.
Dole ce ta saka yake cin abinci a gidan, ba wai don komai ba sai don gani yake yi da kunya ya zauna mace ke ciyar da shi.
Ita ma ta zuba na ta ta zauna gefen sa tana sha
Bayan sun gama ta ce
"Alhamdulillah . Ka ga jiya ba mu da abincin da za mu ci ba mu da kuɗin siye, amma yau Allah ya rufa ma na asiri ko?"
"Haka ne, Allah ya kara rufa ma na asiri duniya da lahira."
Ya faɗa yana kokarin tashi.
"Yau zan fita da safe."
"Lafiya dai ko?"
"Lafiya lau, kin san wata rana akan samu kasuwa da safe ne kawai."
"To Allah ya bada sa'a ya sa a samu abun da ake so."
"Amin ya Allah. Na yi wanka kafin na tafi sallar asuba bari na tafi yanzu."
Ta mike ta ɗauko ma sa basket kayan gyaran takalminsa, har kofar gida ta raka shi sai ta ba shi kayan tana yi masa addu'ar Allah ya tsare ya bada sa'a.
*ABUJA*
Wata hamshaƙiyar mara ce mai kimanin shekaru hamsin. Tana sanye da wani tsadadden leshi a jikinta. Kunnenta da wuyanta ɗan kunne ne da sarƙa na gold. Lokaci zuwa lokaci takan kalli mutumin da ke gefenta wanda yake sanye cikin suit.
Cikin ɓacin rai ta miƙa ma sa hannu alamar ya ba ta, mika ma sa wayar da ke hannunsa.
Ta karɓa ta fara duba wa hotunan Makaho ne tare da Ma'eesha. Wanda aka ɗauke su lokuta mabanbanta na farkon wanda aka ɗauke su ne da suka fito tana rike da hannunsa ranar da za ta siya ma sa waya. Da kuma wanda aka ɗauke su ranar da za su je asibiti gaida mahaifiyar Nasreen har ya sa Ma'eesha ta shiga keke ya ma sa duka.
Ranta a ɓace take kallon mutumin wanda ake kira da Jimoh ta yi kafin ta ce.
"Yanzu dan ya gano kana bin bayansa shi ne ya yi ma ka wannan shaƙar?"
"Ai Madam da ba don kiran wayar da kika yi ma ni ba da Allah kadai ta san abun da zai ma ni, kin ga yadda ya dimfaro ni kamar mayunwacin zaki?"
"Me suka je yi asibitin? Sannan kuma har yanzu ka kasa gano wace ce wanan yarinyar da kuma abun da ke tsakaninsu da ita?"
"Ban gano ba sai dai akwai wani a unguwar da suke an ce shi ya ba su hayan gidan da suke zaune a ciki shi da yarinyar."
"Okay, a unguwar da suke zaune shi ma a anan yake da zama?"
"Eh a nan yake da zama , sai dai ina jin tsoro."
Wani kallo ta yi ma sa saboda ta san me zai ce.
"Tsoron me kake ji?"
"Kada ya sake kama ni a karo na biyu, Madam yaron nan naki fa ba shi da sauki."
"Wancan karon
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 30 Chapter of 49