su wani ba. Don ta tabbatar makaho ba iya ɗaukar nauyin gidan zai yi ba, don wannan gyaran takalmin da yake yi ba ta tunanin shi kansa zai iya ɗ sa ɗaukar nauyinsa da shi ballantana ya dauki nata nauyin.
"Ma',eesha."
Ta ji ya kira sunanta lokacin da ta kashe Gas ɗin.
"Na'am."
"Don Allah ki daina yawan fita ko wane lokaci yanzu yai kin fita sau nawa a gidan nan?"
Shiru ta yi tana kallon da kafin ta ce.
"Idan ina buƙata abu za ka aje ma ni yaron da zan aika ne?"
"Meye amfanina ina gidan da sai kin fita?"
"Na ding aikenk kenan?"
"Wa ya fi cancanta ya fito ya nemi abun da ake bukata tsakanin ni da ke?"
"Kai ka fi cancanta amma gani nake za ka wahala ga sanda ga kaya a hannun ka."
"Kin manta haka nake fita neman na abinci, hannu daya riƙe da sandar hannu daya riƙe da kayan gyara. "
"Shi kenan dama na mance ban siyo ruwa ba sai ka je ka siyo."
Ta ciro ɗari biyar ta bashi ya karba.
"Wannan nawa ce?"
"Ɗari biyar ce, yanzu tsarin zai canza kamar yadda rayuwa ta ta canza. A baya bottle water nake sha, amma yanzu ba na da halin da zan cigaba da shan sa, ko da na siya yanzu nan da kwana biyu zai gagare ni don haka yanzi zan koyi shan ruwan pure water. Wannan ɗari biyar ka siyo ma na bag ɗaya wato jaka dayatina tunanin bai wuce dari biyar ba."
Ya fita don siyo wa ta bi shi da kallo har sai da ya fice sannan ta ɗauko ƙwai guda huɗu ta ta ɗan jajjaga bayan ta wanke ƙaramin turmi ta daka magi ta yanka albasa, sannan ta ɗauko fry pan ta wanke sannan ta zuba mangyaɗa ta soya.
Da sallama ya shigo gidan ta amsa tana miƙe wa ta karbi jakar ruwan dake hannunsa, ya ƙaraso ciki sai da ya ji ya taɓa tabarmar da sandarsa sannan ya gane ya ƙaraso wajen.
Bayan ya hau tabarmar ne ya zauna tare da yin Bismillah.
Kofuna biyu ta dauko na shan shayi ta ajiye bayan ya wanke da cokula. Ruwan shayin ta zuba wa kanta da nasa ta zuba sugar da milo da madara, ta fifita dai da ya rage zafi ta ajiye ma sa a gabansa da plate ɗin da ta saka ma sa soyayyen kwai ciki ta ajiye ma sa bread.
"Ga breakfast ɗin ka nan a gabanka."
Sannan ta haɗa na ta ta koma kan tabarmar ta zauna a gefensa.
"Na gode Ma'eesha Allah ya biya ki fa gidan aljanna."
"Amin ya Allah."
Ta amsa tana cigaba da cin abincin ta.
_Nadra_
Tana zaune a falon zuciyar ta cike da mamaki da ɗan firgici. Duk abinda take gani a gidan yana gudana tana ɗaukarsa ne na yayarta Sidra ba ta taɓa tunanin ita ce Amaryar ba.
Abba dake zaune kusa da kujerar dake kusa da Nadra dake zaune saman Centre carpet, fuskarsa cike da tsananin tausayin ƴar tasa mai biyayya da bin Umarninsa akan komai.
Idanunsa sun kaɗa sun yi jajir ya ce.
"Nadra yau ce ranar da rayuwarki za ta sauya."
Nadra ta kalli fuskarshi idanunwanta cike da rashin fahimta tana kallon jama'ar falon ɗaya bayan ɗaya.
Idanunta suka sauka akan kakarta mahaifin Abba, sai Gwaggo Maimuna Yar Abba sai Gwaggo Laraba ƙanwar Abba. Sai Yayan Umma wato Alhaji Bashir. Kafin ta mai da dubanta kan Abba.
"Nadra yau aka ɗauara aurenki ba tare da na shawarce ki ko jin ra'ayin ki ba, saboda ina da yaƙinin cewa ba za ki taɓa watsa ma ni ƙasa idanun ba."
A firgice take kallon su ta ce.
"Me kuke nufi wace ce Amaryar?"
Abba ya dube ta cike da kulawa da nauyi ya ce.
"Sidra ta gudu Allah ya kare ta a duk in da take. Amma ki sani rayuwarki aka ɗaure yau."
Nadra ta ji shiru na ɗan lokaci zuciyarta ta yi ma ta nauyi kamar dutse. Ƙwalla ce cike a idanunta ba zato ba tsammani zuciyarta ta fara fahimtar cewa ita ce Amarya. Ta taɓa kafafuwan Abba cikin tsanani ruɗani da firgici. Zuciyarta na bugawa da karfi. Sai ta ɗaga kai ta yi addu'a a cikin zuvuyarta.
"Allah ka bani ƙarfin fuskantar wannan sabuwar rayuwa , ka sa na zama mai haƙuri da biyayya."
Kuka ta fashe da shi mai tsuma zuciyar mai sauraro. Cikin wannan yanayi Nadra ta san cewa babu koma baya, kuma dole ta rungumi a abun da ya zo ma ta. Shin ma waye mijin da aka ɗaura ma ta auren da shi? Tambayar dake kai komo a zuciyarta kenan. Sai ta ji muryar wan Mahaifiyarta Alhaji Bashir yana cewa.
"Dama kana naka ne Allah ya gana nasa. Dama can Allah bai ƙadarto cewa Sidra ce matar Fahad ba sai ke, don haka ki rungum..."
Kukan da ta fashe da shi ne ya saka kowa dakata wa yana kallonta. Kuka take yi wanda ke fitowa can a kasar ranta.
"Ki yi hakuri Nadra na san za ki ji abin a baibai, amma ki sani ba ni da wani zaɓi da ya wuce hakan. Na gayyaci jama'a na tara su an zo daga garuruwa mabanbanta gari ya waye ana jiran rana ta yi a daura aure amma sai Sidra ta nemi tozarta ni da kunyata ni ta nemi zubar ma ni da ƙima a idanun jama'a. Da wani idanu zan kalli jama'ar da na gayyata zuwa auren ƴa ta na ce ma su an fasa daurin auren ƴata ta gudu? Hakan ba zai zubar mani da ƙima ba? Ke kadai ce na san cewa za ki iya kwaso ma ni ƙima ta da ƴar ki ta nemi zubar wa. Tun da na haife ki daga ni har mahaifiyar ki muna alfahari da ke, ba ki taɓa saɓa ma na ba, don haka ba na sa ran wannan karon za ki aikata wani abun da ba daidai ba. Na roke ki da Allah ki..."
Cikin sauri ta ce .
"Abba ka daina roƙo na don Allah ba abinda za ku aikata akaina ku roke ni Ko da hakan na nufin mutuwa ta ce, Abba dan Allah ka daina roƙo na sai na ji kamar na gaza zama ƴa gagari ce a gare ku. Na amince akan duk hukuncin da kuka yanke akaina. Amma Yaa Fahad fa Sidra yake so kuma ita ma na san tana tsananin son sa idan ta dawo ta tarar da..."
Abba ya kira sunanta a kausashe.
"Nadra!"
Ɗagowa ta yi ta kalle shi da idanunsa da suka yi jajir saboda kuka ta ce.
"Na'am Abba."
"Daga yau ba na son sake jin sunan Sidra a bakin ki, a cikin gidan nan ma na hana a kira sunan ta, ba zan yi ma ta baki ba amma na cire ta daga cikin mu, ki ɗauka ba ki da wata ƴar uwa a raye Sidra ta mutu a wajen ki."
Kuka ta saka sosai tana rokon Abba ya yafe wa Sidra amma bai saurare ta ba. Sai ya tashi tsaye ya kalli Nadra ya ce .
"Allah ya yi ma ki albarka ya kare ki a duk in da kike, yadda kike wa iyayen ki biyayya Allah ya sa ƴaƴan da za ki haifa su yi ma ki fiye da yadda kika yi mana. Allah ya zaunar da ke lafiya da mijinki ki yi ma sa ladabi da biyayya kome ya daka ki to kiyi masa matuƙar bai saɓawa addinin Musulunci ba, aljannarki na kasan ƙafansa idan ya daga ki shiga kada ki mance da wannan."
Yana fadar haka ya fita daga falon kamar zai yi kuka, don ba zai iya jurar ganin Nadra n kuka tana rokonsa akan wani abu bai yi ma ta ba, amma wanann karon ba ya jin zai saurare ta akan zancen Sidra.
Sauran jama'ar dake falon kowa nasiha sosai suka ji ma ta akan zaman aure da hakuri da rayuwar aure.
"Dare na yi ya kamata a ɗauke ta a kai ta gidan mijinta."
Cewar Gwaggo Maimuna tana kallon Ammi.
Ammi ta ce .
"To me kuke jira ku tafi a raka ta ma na ga jama'a can a falo suna jiran ku fito, ga motaci jere a waje."
Gwaggo Laraba ce ta ja hannun Nadra da ta kudundune cikin babban mayafin da aka yafa mata.
Part ɗin Umma suka shiga suka same ta ita da ƙawarta Hajiya Turai tana rarrashinta, ganin dunya saka Umma ta yi saurin goge hawayenta.
Kukan Nadra ne ya kara tsananta ta nufi Umma ta shige jikinta ta rungume. Kuka suke yi du duka biyin.
Duk yadda Umma ta so rike kukanta kasa wa ta yi, haka kawai take jin tausayin Nadra ga Sidra da ba su san halin da take ciki ba, damuwa sun yi ma ta yawa. Kula take yi sosai tana ƙankame Nadra kamar za'a ƙwace ma ta ita.
Ammi ce ta shiga ganin halin da suke ciki ta ce
"Me nake gani haka, ke da za ki ma ta nasiha a wuce da ita gidan mijinta shi ne kike kuka?"
Da ƙyar aka ɓanɓare Nadra a jikin Umna suka fita da ita tana kuka tana kiran sunan Umma. Hankalinta ya tashi musamman da ta ji jikin Umman da zafi alamar ba ta da lafiya.
Tana ji tana gani lokaci daya rayuwarta ta juye sama zuwa ƙasa ƙasa zuwa sama. Ko da wasa ba ta kawo wannan ranar ba, ba ta yi tsammanin nan kusa za'ayi aurenta ba kuka da saurayin ƴar ta wacce take ƙauna yake ƙaunarta. Amma yau ita ce za'a ɗauka akai gidan Fahad a madadin Aunty Sidra. Kuka take yi sosai tana ji tana gani aka saka ta a ɗaya daga cikin motocin da suka zo ɗaukar Amarya.
Gwaggo Laraba da Gwaggo Maimuna suka saka ta a tsakiya.
Sauran dangi suka shiga cikin sauran motocin, sai dai ba ƙawar amarya ko ɗaya, kasancewar ba ƙawarta da ta san da zancen auren, ko A'isha Humaira da ta zo ta dai zo ne a matsayin bikin Sidra ba wai ta san ƙawarta ce aka aurar ba.
Sauran yan matan na dangi da kowa sai da motacin suka kwashe su zuwa gidan Amarya.
_Fahad_
Kwance yake a bedroom ɗin sa yana jin yadda abokansa Sadik da mukhatar suke ta yi ma sa knocking ƙofar, amma bai yanka ma su ba sai ma pillow ya saka ya dora a kansa alamar baya son ƙarar ƙofar.
"Fahad please open the door."
Cewar Mukhtar yana bugun kofar. Sadik cikin ƙuluwa da wulaƙancin da Fahad ke yi ma su tun ɗazu ya ce.
"Wai kai wane irin wulaƙanci kake yi wa mutane ne tun ɗazu, sai faman bin ka make yi ka fito mu tafi a raka ka ɗakin amarya ka share mu ka mayar da mu ƴan iska idan ba za ka je ba ai sai ka sanar da mu."
"Sau nawa na fada kowa ya watse, sauran sun tafi ku ma ku tafi ba in da zan je Allah ya ba mu alkhairi."
Cikin takaici suka fito kowa ya nufi motarsa suka bar gidan.
_Nadra_
Har suka isa katafaren gidan Fahad ba ta daina kuka ba.
Motacin duka suka shiga cikin compound ɗin gidan.
Babban gida ne sosai mai girman gaske ga manyan fitilu da suka haska gidan ya koma tamkar rana ne ba dare ba.
Faɗar kyau da tsaruwan gidan ma ɓata lokaci ne, gini ne na alfarma kuma na zamani.
"Fito da ƙafar dama."
Cewar Gwaggo Laraba tana riko hannun Nadra dake kuka.
A hankali ta yi Bismillah ta fito da ƙafar dama.
Tana rike da hannunta suka nufi main door nan ma ta ce ma ta ta shiga da addu'a.
Ta dan jira kafin ta ga ta saka ƙafar dama ta shiga ciki.
"Ma sha Allah."
Shi ne kalmar da kowanen su yake faɗa wasu a zuciya wasu a fili.
Ɗaya daga cikin manyan kujeru dake downstairs aka zaunar da ita. Yayin da suka dinga shiga suna leƙa ko ina na gidan suna yaba kyawun gidan.
Daga karshe dai suka kai Nadra ɗakin da ya kasance mallakinta ne a downstairs.
Saman katafaren gadonta suka zaunar da ita.
Nan suka dinga yi ma ta nasiha sosai da da kuma kara nuna ma ta mahimmancin haƙuri.
Sannan suka yi ma ta Sallama suka fice, kuka take yi sosai kamar ranta zai fita. Hakan ya saka suka dawo suka dinga rarrashinta. Ganin kukan na ta ba na tsaya wa ba ne ba ne.
Sallama suka yi ma ta suka ce da safe za su dawo. Suka bar gidan suna ta santin kyawun gidan.
_Mama_
Tana zaune ita da Aunty Rahama da ƙanwar Mama mahaifiyar Farida wacce suke kira da Aunty Jummai.
Farida na kwance a jikin Mahaifiyarta tana sharar ƙwalla.
Aunty Rahama ce ta kalli Farida tana cewa.
"Ki yi hakuri Farida wannan kukan ya isa, Allah ya zaɓa ma ki ma fi alkhairi, idan Allah ya nufa ke matar Fahad ce wata rana sai ki ga Allah ya karkato da hankalinsa zuwa gare ki ya aure ki, auren nan nasa ba wai yana nufin ba ya da damar auren ki ba ne, ai namiji mijin mace huɗu ne."
Haka Aunty Rahama ta dinga rarrashinta duk da ta san cewa ba yadda Fahad zai yarda ya auri Farida saboda ba ya son ta kwata-kwata amma ta faɗi haka ne don ta kwantar ma ta da hankali.
Mama ne ta kalli Rahama ta ce .
"Ki je ki duba ko sun tafi don karfe goma da rabi yanzu, don motocin da suka kai Amarya tuni sun dawo."
Rahama ta miƙe kenan sai ga kiran Sadik ta shigo wayarta.
Amsa kiran tayi bayan ta ji sallama ta ce .
"Sadik kin kai abokin maku ne?"
"Ina fa Aunty, rashin mutunci ya ma na muka bar shi."
Nan ya sanar da ita yadda suka yi da shi. Kuma ya kira ne don a je a saka shi ya tafi kada ya bar yarinya ita kadai a gidan.Bayan sun yi sallama ta kashe kiran wayar.
Nan ta sanar da Mama yadda suka yi sai Mama ta dauki waya ta kira Fahad. Amma wayoyinsa a kashe. Don haka ta mike fita Aunty Rahama ta bi ta a baya suka nufi part ɗin Fahad.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LrTZNGwF35IKXX4sLRvFug
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce ✍️
*🎉Happy new year*🎉
Ina ma na barkan shigowa sabuwar shekarar 2026 lafiya. Allah ya ba mu zaman lafiya mai ɗore wa a ƙasar nan.
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page1️⃣1️⃣
Nan ta sanar da Mama yadda suka yi, sai Mama ta ɗauki waya ta kira Fahad. Amma wayoyinsa , don haka ta miƙe ta fita Aunty Rahama ta bi ta a baya suka nufi part ɗin Fahad.
Ba kowa a fakon sai sanyin A.C dake tashi a falon.
Bedroom ɗin sa suka nufa Mama ta fara buga ƙofar da ƙarfi. A tunanin Fahad su Sadik ne ba su tafi ba, don haka a fusace ya fara magana.
"Wallahi idan ba ku rabu da ni ba zan tafka ma ku rashin mutunci idan na fito."
"To Bismillah ma ta mutunci kawai."
Muryar mahaifiyarsa da ya ji ne ya saka shi zaro idanunsa waje.
"Ya Salam. Mama ce?"
Tasowa ya yi cikin rashin kuzari ya zo ya bude kofar ɗakin.
Kallonsa ta yi fuska a tamke ta ce
"Me kake yi har yanzu da ba tafi gidanka ba ka bar baiwar Allah ita kaɗai."
Har ya buɗe baki zai yi magana sai Mama ta ɗaga ma sa hannu alamar dakatar wa.
"Ba na son jin komai, mintuna goma kada ka sake yi a cikin gidan nan ba ka tafi ba."
Tana gama fadar haka ya juya ta fice, yayin da Aunty Rahama ma ta mara ma ta baya suka fice a tare.
Kamar zai yi kuka haka yake ji.
Key ɗin motarsa ya ɗauka, sai system ɗin sa da wayoyinsa ya nufi hanyar fita zai fice.
Har ya murɗa handle ɗin kofar zai fice sai ya juya yana ƙare wa ɗakin kallo sannan ya dawo ya kashe komai na dakin .
Ficewa ya yi zuwa farlon nan na ya kashe duk wani kaya na Elections sannan ya fice.
Kai tsaye wajen motocinsa ya nufa, ya shiga ɗaya daga ciki bayan ya ajiye laptop dinsa a kujerar zaman banza. Sannan ya yi wa motar key bayan maigadi ya wangale ma A ya bar gidan.
_Makaho_
Suna zaune bayan sun gama yin breakfast, ruwan tea ya shanye amma bai cinye bread da ƙwai ba.
Tattara kayan ta yi ta haɗa su a can gefen kayan wake-wake da suka ɓata.
"Ma'eesha me kike yi ne?"
"Ba komai wake-wake zan yi."
Sandarsa ya ɗauka ya karasa in da yake jin motsinta ya ce.
"Ba ri na wanke je ki kawai."
"A'a ba za ka iya ba."
"Ba abinda za ki iya yi wanda ni ba zan iya ba, domin nakasa ba kasawa ce "
Lalube ya fara yi har ya ji in da kayan suke , tana kallonsa yana wanke wa yana ɗauraye wa har ya kammala.
Ta kwashe kayan ta je ta jera su a in da ya dace.
Bayan ya shigo ɗakin ne ya ce ma ta .
"Yanzu me zan yi ma ki?"
"Ba komai na gode."
"Na san ke ƴar hutu ca ba ki saba da ayyuka ba, ma su aiki ne suke yi ma ki aiki, to don me ba za ki bari na taya ki ba ?"
Gajeren murmushi ta yi ta goge ƙwallar da ya cika idanunta ta ce.
"Haka ne, duk da ma su aiki ke yi ma ni aikin komai amma hakan bai saka Mahaifiyata koyar da ni ba. Ta na cewa ba lallai mijin da zan aura ya so a ce mai aiki ce ke yi ma sa gyaran ɗaki ko girki ba. Wani namijin sai matarsa kawai take yi ma sa hidima."
Kasancewar ta buga labule ta shimfiɗa leda ta ajiye katifar ta gyara. Ba wani aikin da ya rage. Hakan ne ma ya sa ta tuna ina z ta damu room freshener spray ko turaren wuta ta turaran wuta da za ya sa a ɗakin ya yi ƙamshi , dole ta nemo ba z ta iya zama daki ba ƙamshi.
"Ba abun da zan yi ma ki kafin na fita, kada na fita kuma ki buƙata wani abu."
"Kada ka damu girki ne kawai kuma Anjima kaɗai zai ɗaura, kuma ba aikin ka ba ne."
"To ba kaya ma su datti da zan yi ma ki wanki?"
"Babu."
Ta fada tana kallon kyakkyawar fuskarsa.
"To zan je na zagaya ko Allah zai sa na samu."
"Ka huta kawai da yawon gyaran takalmin nan ga rana, kuma ba kudin kirki ba?"
"Kin fi so ba zauna ke ce ɗauki ɗawainiya ta ne, ke ce mijin ni ne matar, ba zan iya ba"
"Amma yanzu wanan uwar rana fa, gyaran ma kamar nawa ake gyara takalma?"
"Idan tsinkewa ce Naira hamsin nake ɗinke wa, amma idan sauran gyararrakin ne ya danganta yanayin aikin."
"Please ka bar shi ka hutarwa kanka, a ƙalla muna da abincin da zai kai mu watanni uku muna ci, to me ye na wahalar da kai cikin wannan ranar ka yi ta yawo, kudin da ba na kirki ba, da babban sama'a ce ma da sauƙi. Amma wanann sana'ar ba..."
"Kin raina sana'ar ko? Kina ganin kamar asara ce ko? Duk wanda kika ga ya yi nasara a rayuwa, to akwai tarin asarori da faɗi-tashi da karyewar jari da ya fuskanta waɗanda ba ka gani ba. Sai dai asara ba ta hana shi ci gaba da neman nasara ba, faɗuwa ba ta hana shi sake yunƙurawa ba, karyewar jari bai karya masa zuciya ba. Wahalar da kike sha a yau, ita ce farashin nasarar da kake so ta tabbata gobe. Domin duk nasarar da ba a wahala wajen tabbatar da ita ba, ba ta ƙarko."
Ya ɗauki kayan aikinsa ya fice ba bishi da kallo.
Huɗubar mahaifiyarta take tunawa, in da take cewa .
"Ya ke ƴata Ki zaɓi namiji mai kyakkyawan zuciya, komai matsayinsa, komai kuɗinsa ko rashin kuɗinsa.
A cikin gaskiyar rayuwar aure, za ki gane cewa kasancewa cikin babban gida ko tarin kuɗi mai yawa ba su da muhimmanci kamar yadda ake tunani.
Za ki fi son wanda za ki iya tattauna komai da shi, wanda kuma zai zama uba nagari ga ’yayanku, wanda ba ya yaudara, wanda za ki iya amincewa da shi.
Iyali masu farin ciki ba su da farashi. Kada ki ji tsoron auren namiji da ke cikin hanyar gyara kansa. Amma ki guji na miji marar sana'a kuma bai damu ya tashi ya nema ba."
Wayarta ta ji yana ringin ta duba ta ga ƙawarta ce Nasreen Ibrahim. Tana ɗaga wa ta ji muryarta cikin tashin hankali tana cewa.
"Ƙawata kina ina?"
Ɗan jim ta ji kafin ta ce.
"Lafiya?"
"Na zo gidanku ne nake jin wani zancen da ya ruɗa ni akan kin yi aure."
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce.
"Kina ina yanzu?"
"Ga ni a ƙoafar gidanku ."
Ta cikin wayar ta ji muryar Laila na cewa.
"Nam ba gidansu ba ne ki je can in da take yanzu ita da musakin faƙirin mijinta can ne gidanta yanzu."
"Laila kika dake ma ni wanta magana anan wallahi dai na ci uwar ki a wajen nan."
"Ba dai uwa ta ba Wallahi, cire wayar Nasreen ta yi za ta yi cikin Laila sai ta gudu ciki tana cewa .
"Shegiya ce ni da zan tsaya ki dake ni? Mai ƙirar samudawa ai sai ku kashe ni. Wacce kike zuwa wajen ta yanzu ba ta nan dai a koma in da take mun kora ta ni da uwata.
"Ku jira na ku sakamakon."
Cewar Jamil yana watsa ma ta wani mugun kallo. Tura ba ki ta yi tana cewa
"Yaya Jamil kawar Aunty Ma'eesha ce za ta dake ni."
Bai ko saurare ta ba ya nufi motarsa. Jin Muryar Nasreen na cewa.
"Ma'eesha ban gane wannan kwatancen naki ba, idan na kawo titin zan kira ki sai ki fito ki shiga da ni cikin layin, don ban zo da Driver ba ni nake yin driving ɗin."
Jin haka ya saka Jamil tsaya wa yana kallon tana yana cewa.
"Ba ni ita Please ta yi Mani kwatancen sai mu tafi tare."
"
Jin haka ya saka Ma'eesha cewa
"Wallahi kuka zo da shi gidana ba zan yafe ma ki ba."
Jin haka ta ce.
"Ba zan zo da shi ba kar ki damu."
Daga haka ta kashe kiran ta kalli Jamil ta ce
"Ka yi haƙuri ba ta yarda na je da kai ba, amma next week zan kira ka sai ka zo mu tafi tare ka ga ni yanzu ba ta yarda na je da kowa ba."
"Ba damuwa ki gaishe ta zuwa next week ina jirab kiran naki."
Daga haka ya shige motarsa ita ma ta shiga tata motar suka bar gidan a tare.
Horn ya danna ya tsaya kasancewar shi ne a gaba, ita ma ta tsaya .
"Ban lambar wayar taki ko?"
Ya fada bayan ya sauke glass din mota tasa.
Ta karanta ma sa lambar sannan ta ja motarta ta bar wajen zuciyata cike da tarin tambayoyi.
Kwatancen da ta faɗa ma ta nan ta je ta tsaya a gefen titin, ba ta ga Ma'eesha ba, can ta hango ta tana ƙarasowa wajen motarta. Sai dai kallo ɗaya ta yi wa ma'eesha ta ga ta rame ma ma ta a cikin kwanaki biyun da ba su haɗu ba.
Tana zuwa ta buɗe front sit ta zauna tana yi ma ta sallama.
Amsa wa ta yi tana ma ta kallon mamaki,sai dai ta haɗiye tambayoyin ta ta yi wa motar key ta ni hanyar da ta ga Ma'eesha ta fito.
Tana nuna ma ta hanyar tana bi har suka ƙarasa ƙofar gidan.
A tare suka fito ta ga Ma'eesha ta buɗe ƙofar ta shiga, ita dai Nasreen mamakin ta ƙara hausawa yake yi .
"Bismillah shigo ciki."
Ta yi magana lokacin da ta shiga ɗakin.
Da sallama Nasreen ta shiga cikin ɗakin, ta tsaya tsaye tana ƙare wa ɗakin kallo.
Ba ta zauna ba duk da Ma'eesha ta ce ta zauna saman katifar.
"Zaman me kike yi a nan, wannan kangon wanda bai kai na a ce kina kiwon karnuka a ciki ba?"
Ta yi maganar tana karewa ɗakin kallo, sannan ta fito taskar gidan tana kare ma sa kallo, hatta banɗaki da kitchen ɗin fale-fale dake tsakar gidan sai da ta leƙa.
Sannan ta dawo ta kalli Ma'eesha dake zaune a bakin katifa ta ce.
"Lafiya kike zaune a wannan kangon kuma me kike yi?"
"Zaman aure nake yi ."
Da mamaki take kallona ta ce.
"Zaman aure kuma?"
"Eh."
Ta ba ta amsa ba tare da ta kalle ta ba.
"Wani irin zaman aure kuma da waye mijin naki?"
"Zaman aure da kowace macen aure take yi a gidan mijinta."
Dafe kai ta yi tana cewa
"Am confused about how..."
Kukan da ta saka ne ya saka Nasreen kasa ƙarasawa maganar da ta yi niyyar faɗa, domin kuwa tausayin ƙawar tata ce ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 49