zan karba na yi godiya ga Allah, tare da maka addu'a buɗi daga wajensa.
Nan suka cigaba da fira har suka kammala sai da ya yi niyyar yi ma ta wanke-wanke ta hana. Dole ya fita bayan ya ɗauki kayan aikinsa na ɗinkin takalma.
Yana tsaka da tafiya ya ji kamar ana binsa bayan ya yi nisa da layin, kuka da dukkan alamu mota ce ke bin bayansa. Jin hakan da ya ji ne ya saka shi ya tsaya daga tafiyar da yake yi, motar ma ta tsaya, wata baƙar mota ce tinted glass.
Bayan ya fita daga layin ne ya shiga wani layi sai ya tsaya cak da tafiyar da yake yi, motar ma ta tsaya daga bin sa da take daidai lokacin da ya saki sanadar hannunsa.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce ✍️
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page2️⃣2️⃣
Bayan ya fita daga layin ne ya shiga wani layi, sai ya tsaya cak da tafiyar da yake yi, motar ma ta tsaya daga bin sa da take yi daidai lokacin da ya saki sanar hannunsa. Sannan ya saki kayan aikinsa na gyaran keke.
A fusace ya juyo bayansa tamkar mai gani, yayin da matuƙin motar ya yi arba da shi dai ya figi motar a guje tamkar mai gani.
Jin motar ta bar wajen Khalifa Makaho bai yi magana ba ya lalubi sandarsa da basket na kayan aikinsa ya yi wucewarsa in da za shi.
Ya ɗan yi tafiya mai nisa sannan ya ƙarasa bakin wata karama titi. Da sallama ya ƙarasa wajen, yayin da wasu dake wajan suka amsa tare da cewa.
"Ka iso Khalifa?"
"Eh ina kwanaku?"
"Lafiya lau Alhamdulillah."
"Ma sha Allah."
Mutane ne a wajen duk da ba sosai ba, don wajen karamar titi ne, kuma akwai hanyar da za ta sada ki unguwar masu kuɗi wanda hanyar suke bi zuwa cikin unguwanninsu.
Ba Makaho ba ne kaɗai a wajen, akwai mutane ma su kananan sana'o'i a wajen suke zaune. Akwai mai siyar da yalo a wajen, da mai siyar da kifi gangariya a wajen da wani mai baro dake sigar da Aya sai wata mace mai suyan awara a wajen, daga gefe kuma ga mai shinkafa da wake da mai da yaji.
Duk suna wajen saboda babban bishiyar mangwaro ce a wajan ta yi inuwa mai fadi.
Nan ne wajen sana'ar Khalifa nan take zama ƙasan bishiyar. Wata rana kuma yakan bar wajan ya yi ta yawo yana neman wanda takalminsa ya tsinke.
Mai awara ta kalli Khalifa ta yi Murmushi dama ta saba tsokanarsa a wajen.
"Kyakkyawa ya kake?"
Ta fada tana Murmushi.
"Kyakkyawa don Allah ka dinga sakin fuska ma ma kai kenan fuska ɗaure tamau ba murmushi ba dariya kamar wanda aka aikawa saƙon mutuwa."
Bai tanka ma ta ba kamar kullum dama baya tanka ma ta ita ma ba ta fasa tsokanarsa.
Mai siyar da yalo ne ya yi magana ya ce.
"Wai ke Laure ba za ki ƙyale wannan bawan Allah ba ne, kullum sai kin dame shi da surutu, kuma baya tanka ki ."
"Ilu mai yalo ka bar ni, ina son ya yi magana ce na ji muryarsa. Ka san Allah makatntar nan tashi ce kawai cikas ɗinsa. Amma da ba don makaho ba ne wallahi ba na aure shi ko da bai da kudi kuwa. Don ko kyakkyawar surarsa na kalla zan ji daɗi saboda ya haɗu iya haɗuwa rashin idanunsa ne matsalarsa, kuma gaskiya ba zan iya auren makaho ba, don makantar idanun ai mutuwar tsaye ne ba zan iya ba don wahala zan yi da kai. Amma wallahi kana da siffar da kowace mace za ta so ka."
Shi dai Khalifa bai ce komai ba yi ya yi kamar bai ji ta ba.
Tunanin Ma'eesha yake yi, ga wata da ba ƴar kowa ba ƴar talakawa tana cewa tana son sa amma ba za ta iya auren makaho ba. Ta ɗauki makantarsa a matsayin kasawarsa. Amma Ma'eesha gata can ƴar masu kuɗi wacce ta taso cikin kudi da gata da kayan more rayuwa kamar ta amma ba ta ɗauki makantarsa a matsayin kasawarsa ba a haka take son da take faranta ma sa rai ba ta damu da makantarsa ba tana rayuwa cikin farin ciki da walwala.
Bai san lokacin da ya yi wani sanyayyen murmushi ba tare da sanya ma ta albarka a zuciyarsa.
Wani matashin saurayi ya zo wajen sakamakon hangen kayan gyaran takalmin da ya yi ne ya zo.
"Ina mai gyaran takalmin?"
Khalifa ya ce ma sa baki nan."
Ya kalle shi ya mika ma sa takalmin daga ɗan nesa da shi.
Sai ya ga yana lalube yana cewa.
"Ina takalmin yake bawan Allah ka matso kusa mana."
Ganin yana lalube ya saka shi cewa.
"Ban gane ba wai makaho ne yake lalube ko me? Bai ma ganni ba ko?"
",Eh makaho ne amma ya iya aiki sosai zai yi ma ka yanzu."
Cewar Ilu mai yalo yana kokarin karbar takalmin don ya mikawa Khalifa.
"Dalla Mallam bar ni, hauka nake yi ne, ko na yi ma ka kama da mahaulaci ne da zan ɗauki takalmi na ba wa makaho salon ya mayar ma ni da takalmin nakasashshe kamarsa ko? Wannan nakasashshen sai dai ya nakasa tsakalmi ba dai ya gyara ba."
Yana fadar haka ya figi takalmimsa yana barin wajen.
Cike da tausayinsa Ilu mai yalo ya dafa kadarsa ya ce.
"Kar ka damu abokina Allah ya sa ba rabonka ba ne, Allah zai kawo ma ka rabonka ka ji."
Murmushi ya masa tare da cewa.
"Ba komai."
_Nadra_
Tana nan zaune saman gadon sakamakon zufa da ta ji ya karyo ma ta bayan maganin zazzaɓi da Fahad ya ba ta. Ta ji ba wani ciwo garau take ji.
Hakan ya saka ta cire hijabinta ta ajiye a gefe. Ta ji kewar gida tana son ta yi magana da Umma da Abba amma ga Fahad ya karɓe ma ta waya
Tana nan zaune ta yi jigum sai ta ga an turo kofar dakin, ta daga kai ta kalle shi ta ga yana shigowa kai tsaye. Da sauri ta janyo hijabinta ta na sakawa tare da ƙudundune jikinta waje ɗaya.
Mamaki ya cika shi ganin yadda duk ta taburce wurin saka hijabinta bayan tana da riga a cikinta ba wai tsirara take ba, kuma bayan haka nan ai shi mijinta ne halak ɗin sa ne ko da ya ganta tsirara ba ai ta halatta a gare shi amma sai wani noƙe wa take yi cikin hijabi.
Zuba ma ta idanun ya yana tsaye hannayensa suka biyu cikin aljihun jeans ɗin dake jikinsa.
Jin ba ta sake jin takusana ba kuma bai yi magana ba sai ta ɗaga kai ta kalli in da yake. Idanunta ne suka sarƙe cikin nasa.
Ya zuba wa kyakkyawar fuskarta idanu, sam ba ta kama da masoyiyarsa Sidra. Don ita Sidra fara ce sol kuka fuskarta doguwa ce idsnunta madaidaita hancinta dogo ne sai bakinta wanda shi ma madaidaici ne ba za ka kira ta mai ƙaramin baki ba kuma ba za ka kira ta mai babban baki ba. Ita kuma wannan Nadra baƙa ce amma baƙinta mai kyau ne irin mai sheƙin nan fatarta tana glowing ne, round face ne da ita, don fuskarta a zagaye yake, idanunta dara-dara ne hancinta dogo ne haka bakinta ma ƙarami ne laɓɓanta pink ne don a zahirin gaskiya ta fi Sidra kyawun fuska, sai dai kasancewar ta baƙa ba kowa ke ganin kyawunta kamar yadda ake ganin kyawun nata ba Ita kuma Sidra hasken fatarta yake kara haska ta don ita Sidra doguwa ce ba ta da cikar halitta sosai saɓanin Nadra dake da hips da kuma manyan nono. Amma kasancewar kullun tana cikin hijabi ya sa ba'a ganin dirin jikinta, ita kuma Sidra ba ta saka hijabi mayafin ma sai ta ga dama take saka shi.
Tura baki ta yi ganin yadda yake kallonta kuma kamar tunani yake yi.
Kara ƙanƙame jiki ta yi cikin Hijabin tana tura baki.
"Ya jikin na naki?"
"Da sauƙi."
Ta fada tana sunkuyar da kai ƙasa."
"Me ke ma ki ciwo yanzu?"
"Ba komai."
Jinjina kai ta yi kafin ya ce.
"Akwai abun da kike buƙata ne?"
"Ba komai."
Daga haka ya nufi hanyar fita, sai ya juyo ya ce.
"San fita na san Mama za ta aiko ma ki da abinci."
Daga haka ya nufi hanyar fita ya fice daga ɗakin.
Daga haka ya nufi kofar fita in da ya nufi parking space, motorsa ya nufa ya shiga.
Tun kafin ya danna horn maigadi ya wangala ma sa gate ɗin gidan.
Yana fita ta mike ta fara ƙokarin gyara ɗakin.
Toilet ta wanke sannan ta zo ta gyara ɗakin tas.
Falo ta nufa kai tsaye duk da ba wani gyara amma haka ta gyara shi, sannan ta shiga kitchen ta yi wanke-wanke ta gyara shi ta goge wajen da ya dace.
Ɗakinta ta koma ta yi wanka ta fito mayyukan shafawar da ta gani an jera ma ta ma su tsada ta shafa, sannan ta saka underwears don singileti ta saka da wando ta duba kayan ta rasa wanda za ta saka. Domin ita tana son saka rigar Abaya ce ko kayan da ya ke rufe jiki kuma ta sake a ciki ba tare da ta takura ba. To nan kayan kuka duk kaya ne da Fahad ya siya da sunan Sidra don irin kayan da take son sakawa kenan ma su kama jiki, sai kuma na gida wanda iyayen su suka siya ma ta ta kai wa tela duk irin kayan da take so ta saka aka yi ma ta.
Rasa kayan da za ta saka ta jan tsuki cike da takaici.
Wani riga da siket ta saka duk da ya kama ta amma sai ta bar shi kasancewar ta san za ta saka hijabi.
Hijabi ta dauka ta saka sannan ta fita zuwa falon.
Ba ta wuce mintuna biyar ba ta sauka downstairs.
Kallon gidan take yi wanda ya haɗu iya haɗuwa. Komai na gidan na musamman ne, gini ne mai kyau da tsari na zamani.
Tuna Sidra ta yi kawai sai ta goge ƙwallar da ta ji ya cika ma ta idanun.
"Ƴar uwa ina kika shiga ne, me ya sa kika gudu kika bar takarda meye dalilin hakan. Ga ni a gidan da ya dace a ce kece kike ciki tare da masoyinki Yaya Fahad. Don Allah ki dawo akan lokaci Abba da Umma suna fushi da ke."
Ta yi maganar tana goge hawayenta.
Ƙarar ƙararrawar ƙofa ta ji ya saka ta gyara zaman Hijabin jikinta ta nufi ƙofar ta buɗe.
Cike da murna ta ce.
"Gwaggo Laraba."
Ta rungume ta tana dariya. Sannan ta kalli saura mutanen duk danginsu ne da suka zo daga ƙauye bikin auren.
Cike da murna ta tarbe su ta yi ma su iso zuwa ciki.
_Ya Sayyadi_
Tun da Fahad Majidaɗi ya yi masa gargaɗi akan Nadra ya kasa ƙwaƙwaran motsi. Shin me ye zai saka Fahad da da yake auren Sidra ya ma sa haka, yana da wannan ikon da zai ma sa barazana. Me ya taka ne ko iyayen Nadra sun san da zaman sa amma ba su ma sa shamaki da ita ba sai shi bare a wajenta, kawai don yana auren Yayarta. Har yana cewa zai saka a Kamo shi duk in da ya shiga a faɗin ƙasar nan.
Jiki ba ƙwari ya shirya cikin jallabiya da ɗagaggen wando ƙwaurin ƙafarsa a waje.
Babur ɗinsa ya ɗauka ya tayar ya nufi gidan su Nadra.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce ✍️
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page2️⃣3️⃣
Babur ɗin sa ya ɗauka ya tayar ya nufi gidan su Nadra.
A ƙofar gidan ya tsayar da babur ɗinsa sannan ya tsaya yana danna horn. Maigadin na jinsa ya share shi har sai da Direban ya yi magana .
"Ba ka ji ana horn ba ne?"
"Rabu da ɗan wahala."
"Waye wai?"
Direban ya sake tambayar maigadi.
"Oh kai ba ka gane ko waye ba, ai ni tun da na ji wannan ƙarar babur ɗin kamar an tayar da injin ɗin markaɗe na san wannan Ustaz ɗin ne dake son Nadra. Ni idan ba shi da tsarin idanun ba ina shi ina neman aure a wannan katafaren gidan. Ai ruwa ba sa'an Kwando ba ne, yana talaka da shi ko sutura arziki bai da ita kayansa fa kala uku ne jallabiya uku yake da su daga wata fara sai baƙa da wata Blue su kenan kayan nasa sai hular taɓa ni ka ji hadisi da wani takalmin robarsa da ta so ta yi ma sa yawa."
Dariya direban ya saka yana cewa.
"Kai Mallam Musa ba ka da dama, haka ka sa wa Ya Sayyadi idanu?"
"Ba dole ba, saboda ina jin takaici a ce wai kamar ƴa a gidan nan ba ƴar aiki ba ƴar ma su gida a ce ita yake so. Ita kuma Nadra da yake ba ta damu da rayuwar duniya ba kuma ba ta duba girma da ta fito ba amma ta yarda ta karbi soyayyarsa haka zai zo ta fito har ta kawo ma sa ruwa da Abinci. Idan da Sidra ce ya isa ya ce yana son ta ai wargi ma wuri yake samu."
Dariya direba ya yi ya ce.
"Har ka tuna ma ni ranar da Sidra ta mare shi saboda ya bugar ma ta mota ."
Maigadin ya saka dariya ya ce.
"Dama ita Sidra ai ba ta da hakuri ban san yadda aka ji aka fasa auren Sidra ba aka ɗaura da Nadra."
Kafin ya yi wata magana suka ji ana buga gate ɗin gidan da ɗan ƙarfi, hakan ya saka maigadi ya tashi da sauri yana cewa.
"Waye ke damun mutane a wajen?"
Ya faɗa yana buɗe karamar ƙofar.
"Assalamu alaikum warahmatullah."
Ya faɗa yana miƙa wa Maigadi hannu don su yi masabaha.
Maigadin ya mika ma sa hannu tare da cewa
"Wa'alaika Salam."
"Ma sha Allah, ya lokaci ya kuma aiki?"
"Ga shi Muna ta yi."
"Ma sha Allah, Allah ya taimaka ya yi jagora."
"Bai amsa ma sa ya ce.
"Ustaz ka shigo."
Ya fada yana ba shi hanya, ya shigo da babur ɗin nasa ciki ya ajiye a harabar gidan daga gefe.
Sannan ya ƙarasa wajen da Direban yake suka gaisa. Maigadin ya ce .
"Ka zo ka yi bankwana da mu ne?"
Cikin rashin fahimta Ya Sayyadi ya ce .
"Bankwana aka me fa?"
"To dama me za ka sake zuwa yi a nan, tunda wacce kake zuwa dominta ta yi aure."
Wani kallo ya yi wa Maigadi kafin ya ce.
"Amma ba ka cikin hayyacinka ko? Yarinyar da babu wanda take so sai ni ne ta yi aure? Wannan da'ifin labari ne bari na je na ji sahihin labari daga bakin da baya ƙarya.
Ya tafi zuwa cikin gidan yana tafiya kamar zai kife a ƙasa.
"Assalamu alaikum."
Daidai lokacin da LUBE mai aiki ta buɗe kofar, ganinsa ya sa ta gaida shi, bai amsa ba ya ce ta sanar da Abba ya zo yana son magana da shi.
Ta nufi part Abba ta same shi shi da Gwaggo Maimuna da Ammi.
Ta gaishe su sannan ta sanar da su saƙon ya Sayyadi. Sai da suka kalli juna Abba da Gwaggo Maimuna sannan Abbabyq ce a sanar shi ya shigo.
Bayan ya shigo ya gaida su suka suka amsa cike da kulawa.
Nam yake sanar da Abba Fahad Majidaɗi ya yi masa rashin mutunci har da ka sa barazanar idan ya sake kiran wayar Nadra sai ya sa a ɗauko ma sa shi a fadin ƙasar nan, wai idan bai daina ba ba shi ne kuskure mafi muni da zai tafka a rayuwarsa.
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Abba ya sauke sannan ya ya yi wa Ustaz ɗin takaitaccen bayanin abin da ya faru, sannan ya bashi haƙuri akan cewa ba su da wani zaɓi ne da ya wuce su aura ma sa Nadra a madadin Sidra. Ba za su bari alsu kunyata ba a idanun duniya mutuncinsu ya zube taron da jama'a suka zo wasu daga wasu garuruwa a ce sun watse haka nan ba tare da an yi ɗaurin auren da suka taro domin sa ba.
Kuka wiwi Ustaz ke yi na rashin Nadra da ya yi a rayuwarsa, yarinya mai hankali da tarbiyya, wacce ta so shi duk da tana gidan ma su rufin asiri shi kuma gidan talakawa ba ta ƙi shi ba, ya san ba zai samu mace kamar Nadra a rayuwarsa ba.
Ba tare da ya cewa kowa komai ba ya nufi kofar fita yana kuka har da majina. Ammi ta raka shi da harara don dama ba ƙaunarsa take yi ba. Kullum sai ta zuga Nadra akan ta Kore shi amma ba za ta yi ba sai dai kasa ta yi ma sa murmushi.
Dama daga Ammi sai Gwaggo Maimuna suka rage a gidan, don su Gwaggo Laraba da sauran dangi sun tafi gidan Nadra su ga gida kuma su yi ma ta sallama don gobe za su watse zuwa garuruwansu.
_Sidra_
Ta gama haɗa kayanta a cikin akwatin kayanta tana jiran Direban da zai kai su Sady baby ya zo ya ɗauke ta su kama hanyar Kano. Amma sai ta ji shiru tun da suka fita da sunan zai kai su Sady Unguwa ya dawo shiru.
Ta kira wayar Sady baby bai shiga ba. Don ba ta son shiga motar haya, don haka ba ta da wani zaɓin da ya wuce ta ta jira su. Ba ta da wani zaɓin da ya wuce ta jira su har sai sun dawo.
_Fahad_
A kofar gidan Mahaifinsa ya tsaya yana yin horn ɗin motarsa, yanayin sannan horn din da Maigadin ya yi ne ya gane cewa Fahad ne ya iso.
Da gudu-gudu ya nufi gate ɗin gidan ya wangale ma sa.
Parking lot ya nufa ya yi parking motarsa. Gidan har yanzu akwai baƙin da suka zo bikin don ga motocinsu nan a jere.
Fitowa ya yi daga cikin motar yayin da ma'aikatan gidan ke gaishe shi.
Ya amsa ma su ba yabo ba fallasa.
Tun daga ƙofar da zai sada ka da falo yake ji yo hayaniyar ƴan matan da ke cikin falon.
Firarsu kawai suke yi suna dariya.
Mirɗa handle ɗin kofar ya yi ya shiga wanda ƙamshinsa kaɗai ya isar da saƙon zuwansa.
Kowace ta nutsu suka fara gaishe shi, ya amsa ma su ba yabo ba fallasa. Ya kalli Rumaisa ƙanwarsa da Rahina da Sahiba da suka je gidansa suka dawo suka ce wai Nadrah ba ta iya tafiya ya kasance ta.
Ganin kallon da ya yi masu ne suka sha jinin jikinsu. Daidai lokacin wayarsa ta yi ringing.
Ya duba ganin abokinsa Sadik ne ya saka ya yana cewa.
"Ya aka yi ne?"
Maganar mintuna biyar suka yi sannan ya katse kiran wayar .
Ko da ya duba bai ga su Rumaisa da Sahiba da Rahina ba sun sulale sakamakon ganin kallon da ya jefa ma su.
Sauran ƴan matan duk ba garin suke ba zuwa bikin suka yi. Amma duk ƙannensa ne.
Part ɗin Babansa ya nufa in da ya same shi tare da kawunsa.
Gaishe su ya yi sukaasa sannan suka ɗora da yi ma sa nasiha akan zaman aure da hakuri.
Bayan ya bar part ɗin ya nufi part ɗin ya nufi part ɗin Mama. Farida ce kawai a falon daga ganin idanunta ta sha kuka sosai.
Idanu suka haɗa da sauri ta ɗauke kai tana juya ma sa baya. Shi ma kansa ya sani Farida na tsananin son sa da ƙaunarsa amma shi baya son ta, bayan so na ƴan uwantaka da yake yi ma ta ba wani abu a ransa. Da a ce bayan guduwan Sidra iyayen ta ba su bashi Nadra ba to da zai iya auren Farida. Amma a yanzu kam baya jin zai iya aurenta kuma.
Ƙarasa wa ya yi ya zauna kusa da ita. Ta zuba ma sa idanunta tana kallonsa kamar za ta cinye shi. Kafin kuka hawaye ya fara zuba a idanunta sharr kamar an bude famfo.
"Ki yi haƙuri kin ji."
Tashi ta yi a guje ta bar falon ta nufi ɗakin dake kusa da na Mama.
Daidai lokacin Mama ta fito ita da Aunty Rahama.
Bayan sun gaisa ne Mama ta ce.
"Ya za ka fito ka bar ƴar mutane ita kaɗai bayan ka san condition ɗin da take ciki?"
Ka tashi ka koma zuwa gobe iyauenka za su zo ganin gida don jibi suka ce za su tafi, don yau suka ji niyyar zuwa amma na ce su bari sai gobe."
Ya dai yi shiru ba tare da ya sake yin magana ba.
Kallon Baby Zahrah ya yi wacce take ma sa dariya tana kiran uncle.
Alama ya ma ta da ta zo ya zaunar da ita kusa da shi wanda ganin haka ya saka Mama cewa.
"Fahad ba ka da niyyar tafiya ko? Ai bai kamata ma ka bar gidan ba, ka je ka haɗa ni da ita a waya ko ka bani lambar wayar ta.
Sanin cewa ya karɓe wayarta ya saka ya ce .
"Ba ta da waya."
"Kamar ya ba ta da waya?"
"Eh wayar ta ɓace ne."
"To ka siya ma ta wata wayar yau ɗin nan ka tafi ma ta da shi, na san dole za ta so yin magana da iyayenta."
"To Mama."
Aunty Rahama ta ce .
Da take ganin kamar rashin fahimta ce don ita ba ta yi tunanin cewa ƙanin nata zai kusanci Nadra ba wanda daren juya daƙyar ya tafi yana fushi. Ganin shi ma bai ce komai ba ita ma ta yi shiru amma tabbas tana da shakka akan hakan don ta fi kowa fahimtar ƙanin nata.
Sallama ya masu sannan ya nufi part ɗin baƙi ya gaishe da kowa. Sai dai ƙanwar mahaifiyarsa Hajiya Jummai mahaifiyar Farida ce ta share shi ba ta amsa ba, shi ma bai damu ba ya yi ficewarsa
_Ma'eesha_
Tana ɗora girki ta ji sallama daga kofar waje, ta amsa yayin da da take kwarara amai ta taimaka ma ta da ruwa kuma ta gyara wajan a gidan Mallam Liman da aka ba Makaho ɗaki.
Da fara'a ta tarbe su suka shiga cikin ɗaki ta shimfida ma su tabarma.
Bayan sun gaisa ne ta kawo masu ruwan pure water guda biyu.
Nan Dattijuwar take gabatar ma ta da kanta ashe ita ce matar da ta ga za su bar gidan lokacin da Ma'eesha ta fice Makaho na bin bayanta take tambayar makaho ina za su je ya ce suna zuwa.
Yana girki suna taɓa fira don ganin su ne ya saka ta canza tukunyar ta saka babba.
Kafin ta gama Dattijuwar da jikarta mai suna A'isha suka yi ma ta sallama za su tafi.
Ta yi daga da su akan su tsaya ta gama girki su tafi da shi amma ba su zauna ba.
Da ta kammala ta zuba a food flask sauran da ya rage ta zuba a wani food flask shinkafa da wake ne jallop wanda ya ji bisashen kifi.
Tun karfe biyu take jiran Khalifa ya dawo ya ci abinci shiru. Har karfe huɗu sannan ya dawo.
Ta yi ma sa ƙorafin rashin dawowa ya ci abinci akan lokaci. Ƙarshe ma ta ce ya gama su tashi su ke ta siya masa karamar waya.
Ta sanar da shi zuwan Baba mayar Liman da jikarta da suka yi.
Bai so ba haka ta matsa ma sa dole ya yarda suka shirya za su fita don ta siya ma sa karamar waya.
Da zai ɗauki sanadar jagoransa hanawa ta yi ta ce sai dai su tafi haka nan ita ce ƴar jagora.
Duk da bai so ba amma baya son yi ma ta gardama don tana da ƙima sosai a idanunsa.
Hakan ko aka yi bai rike sanda ba ita ce ta rike ma sa hannu suka fita. Tana sanye da doguwar rigar Abaya blue ta yi rolling kanta da mayafin abyarta sannan ta saka facemask da farin glass a idanunta.
Hannunsu na sarƙe cikin na juna suke tafiya duk wanda ya san Khalifa a unguwar sai dai ya saki baki yana kallon su da mamaki. Ganinsa tare da wannan zugegiyar budurwa tana rike da hannunsa suke tafiya.
Sai dai idan har ba idanunta karya suka yi ba ta hangi wata motar a gabansu wani na zaune gefen me zaman banza yana ɗaukarsu hoto.
Cike da mamaki ta yi niyyar nufar motar sai ta ga an figi motar a guje an bar wajen.
"Ka ga wanda ya ɗauke mu photo?"
Ta yi tambayar tana kallon Khalifa.
"Ni da ba idanu gare ni ba da wani idanun zan kalle su?"
Har suka je wani shagon siyar da waya ta siya masa wata karamar waya keypad, duk
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 49