Share this page
sha. Kallon A'isha ta yi kafin ta ce . ,A'isha bari na kira Yaya Khalifa a waya na sanar da shi zan tafi asibiti." Ta ji maganar tana jingine jikinta da bangon ɗakin "To Aunty Ma'eesha." Lambar wayarsa ta lalubo ta danna ma sa kira amma ba ta shiga ba. Dai da ta gwada kira har sau uku kiran bai shiga ba, kallon A'isha ta yi kafin ta ce . "Wayarsa ba ta shiga bari ba aike ki Chemist ki ce ya haɗa ma ki maganin zazzabin maleria." Ta yi maganar tana janyo kuɗi ta ba ta 3k ta ce ta je da shi. Karɓa ta yi tana yi ma ta sallama ta tafi. "Ba jimawa sai ga ta ta dawo da ladar magunguna. Zuwa lokacin ta tarar har ta fara barci . Sai da ta tayar da ita sannan ta tashi ta sha magungunan ta ba ta canjin Naira ɗari biyar. Tana gama shan maganin ta kwanta barci ya dauke ta nan da nan. A'isha ta tashi ta awa taya ta gyaran gidan. Ba iya zazzaɓi ne ke damu ta ba, har da tafiyar makaho ya dame ta, domin kuwa kewar sa na daya daga cikin abun da ke sa tana jin wani iri a tare da ita . Shi ma a nasa bangaren haka ne, domin kuwa tun da ya tuna ya ya kasa cin abinci. Ji yake yi kamar ya rufe idanu ya tsinci kansa a gaban ta. Sai ya ji farin ciki da yake yi da tafiyar duk ya rasa. Duk da cewar yanzu yana a lafiyayen gida na alfarma. Ga komai da ake bukata na more rayuwa amma ji yake yi rayuwa a wancan. Akulkin gidan tare da Ma'eesha yake bege. *Jan hankali.* Wani lokaci mace tana jin kamar idan ta biya wa mijinta bukatu, yi masa girki kala-kala, gyara jiki, , ta tsaftace jikinta ciki da waje girmamawa, ladabi biyayya, kwantar da kai… to zata iya gamsar da mijinta 100%. Sai dai gaskiya ɗaya ce Mace ba za ta iya cika dukkan muradan mijinta ba, kamar yadda shima ba zai iya cika nata ba. Saboda dan Adam bashi da iyaka a bukata. Yau yana son shiru, gobe yana son hira. Yau yana son tuwo, gobe yana son noodles. Yau yana so ki zauna da shi sosai, gobe yana buƙatar sarari. Yau yana so ki yi masa magana da tausayi, gobe yana fushi saboda wani abu da ba ki yi ba, Zuciyar mutum tana canzawa. Rayuwa tana da nauyi. Ki yi niyyar kyautatawa saboda Allah, ba don yawan yabo ba. Ki fahimci cewa mijinki ba kullum yana buƙatar abu iri ɗaya ba, yau soyayya, gobe space. Ki gina kwanakinki da basira ki dinga karanta sauyin yanayinsa. Ki yawaita addu’a sosai. Saboda ko kina da niyyar gamsar da shi, idan ALLAH bai sa kin gane hanyar ba, zai zama kamar ba kya yi. Mace mai basira ba wadda ta iya komai ba ce, Ita ce wadda ta san iyakokinta, amma tana kokari da zuciya ɗaya. Ita ce wadda ta mayar da gida masaukin salama, ko da mijin yana da tabo. Kuma hakan yana da girma fiye da zama kammalalliyar mace. Girmama ƙoƙari shine soyayya. Shi kansa ya san tabbas Ma'eesha na son sa kuma so na haƙiƙa Knocking ƙofar da aka yi ne ya dawo da shi cikin tuanin da ya lula. Mom ce ta shigo da sallama , ya amsa ma ta yana zaune kan gado, yayin da ta zauna saman bed side tana karantar yanayinsa. "Wace ce ita?" Da sauri ya kalle ta yana mamakin tambayar da ta yi ma sa. "Na ce wace ce ita?" Nan ma sake kallon ta ya yi ya kasa cewa komai. "Mom wai akan wa kike magana ?" "Akan wacce kake tunani da har ka kasa cin komai saboda ita ." "Ni Mom ba wacce tunanin ta zai hana ni cin abinci." "Ga shi kuwa na gani." "Eh to ni wace mace zan yi tunanin ta bayan Yasmeen da kika sani, ita kadai ce." Ya yi maganar kansa a ƙasa ya kasa hada idanunsa da mahaifiyar tasa. Murmushi irin ta su ta manya ta yi kafin ta ce. "Idan har tunanin Yasmeen ne a cikin zuciyarka to da ka tashi yanzu ka karasa in da yake ka gan ta, saboda gari daya kuke a yanzu. To ya kamata ka sani ka cire tuanin kowace mace a zuciyarka ka san meye a ƙasa ba sai na faɗa ma ka ba. Ba ka isa ka fito da wani zancen wata mace bayan Yasmeen ba don haka kada ka fara abun da ka san ba zai yiwu ba." Wayar ta ta ɗauka ta danna kira bugu ɗaya aka ɗaga. "Kawo wa Yayanku abinci a ɗakinsa." Daga haka ya katse kiran wayar . "Ba jimawa sai ga Sadiƙa ta shigo da farantin abinci da aka ɗaura kan tire da robar ruwa ruwa da glass cup sai lemu na kwali. Mom ce ta karɓi abincin ganin haka ya sauko daga saman gadon ya zauna akan carpet dake ɗakin. Sadiƙa ta kalle shi ta ce. "Big bro are you okay?" "Am okay" Daga haka ta fita ta ba su waje . Abincin Mom ta ajiye ma sa a gabansa ita ma ta zauna tana fuskantar sa ta saka shi gaba kamar yaro. Sai da ya ci rabin plate ɗin abincin sannan ya sha ruwa lemu ma bai sha ba. Kallonsa take yi tana yi wa Allah godiya, domin kuwa rabon da ya kwana a gidan nan tun bayan da Gwaggonsa ta dauke shi yana ɗan shekara ɗaya, sama da shekaru talatin kenan bai sake kwana gidan ba sai yau. Sai dai ya so ya gaishe su ya tafi .Amma ta san hakan na da nasaba da rashin sanin ita ce mahaifiyarsa sai a cikin shekarar nan da zancen aure sa da Yasmeen ya fito. Kuma zuwa lokacin ba wani zama yake yi ba, ko, amma yanzu ga shi ita da shi nan ya fara sauka kafin ya je gidan Ummeen tasa. Horn ɗin mota suka ji sanan suka ji ƙarar buɗe gate. Hakan ya tabbatar ma su da isowar Dad. "Dad ne ya dawo ko Mom?" "Eh shi ne." Ta faɗa tana tashi ta dauki farantin da plate da ya ci abinci da shi. Ta fita daga ɗakin ya bi ta da kallo. _Fahad_ Ya rage kayan jikinsa kenan zai yi wanka daga shi sai gajeren wando da singileti. Nadra ta turo ƙofar dakin cikin tashin hankali. Da sauri ya juya ya kalli ƙofar ya ce . "Lafiya me ya faru!" "Aunty Sidra ce ta faɗi?" Shiru ya yi kamar bai ji ta ba, ganin ya yi shiru ta karasa dab da shi ta rike hannunsa tana kuka ta ce. "Ka taimaka ma na don Allah Yaya Fahad." "Ni fa ba na ƙaunar ganin wanan yayar taki na tsane ta, amma kin goyi bayan ta dawo gidanki ta zauna, ba yadda na iya Amma wallahi ba da son raina hakan ta faru ba." "To ba yadda zan yi ne shi ya sa, ta nuna nan take so kuma ga abun da Doctor ya ce a guji ɓacin ranta." Jallabiyarsa fara ya ɗauka ya ɗauka ya saka sannan ya nufa hanyar fita ta bi bayansa. Yana zuwa ɗakin baƙi ne ya ganta kwance ba ta motsi kamar wata gawa. Durƙudaws ya yi a gabanta ya zuba ma ta idanun na wasu sakanni kafin ya kalli Nadra ya ce. "Ba ni ruwa a fridge." Da sauri ta zuwa falo kasancewar fridge dake nan ɗakin a kashe yake. Nan da nan ta dawo da robar ruwa ta mika ma sa. Ya ɓalle marfin ya yayyafa ma ta amma shiru ba ta motsa ba, hakan ya sa ya ka ya watsa ma ta da ƙarfi wanda ya da ta ja ajiyar zuciya tare da rike hannunsa da ƙarfi tamkar wani zai kwace ma ta shi daga hannunta. Tsuki ya ja a ƙasar ransa kafin ya fusge hannunsa da ƙarfi ya fice daga ɗakin. _Jalaluddeen_ Bayan fitar Mom kenan ya tashi ya fice daga ɗakin shi ma. A falo ya tarar da ƙannen nasa suna zaune sun zubawa tangamemen plasma t.v wanda ya kusa rabin rabin bangon Falon. Sai sanyin A.C da wani sanyayyen ƙamshin turaren wuta da ke tashi a falon Ɗaya daga cikin lafiyayun royal chair dake Falon ya zauna. Kasancewar kujera ma i zaman mutum uku ce nan take Sadik da Sadiƙa suka taso suka zauna kusa da shi suka sanya shi a tsakiya. Fuskar kowannen su ɗauke da murmushi, Sadik ya ce " Yanzu fa daga gobe ka zama ango." Kallon rashin Fahimta ya yi ma sa ya ce . "Kai ba na son shirme fa, waye zai zama ango gobe." "Kai ma na Yaya Jalal, ai Dad ya ce duk ranar da ka dawo garin nan a washegarin ranar za'a ɗaura auren ka da Yasmeen kowa ya san da wanan zancen." " Wani gumi ne ya ji ya karyo ma sa shi da sanyin A.C dake ratsa falon. ,*Maman Ihsan ce✍️ 09065327995 Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page6️⃣4️⃣ Gumi ne ya ji ya karyo ma shi duk da sanyin A..C dake ratsa falon. Ba wanda ya sake magana, su ma ganin yanaynsa ya sauya ne ya sa kowa . Mom ce ga karasa falon ta kalle shi ta ce.. "Ka zo ga Alhaji na son ganin ka." Ta faɗa tana nazartar yanayinsa. "To Mom." Ya amsa tana tashi ya bi bayanta don zuwa amsa kiran Dad. Yana shiga ya tarar da Dad da Mom zaune saman kujerar mai mai zaman mutum uku. Da sallama ya karasa falon ya zube a kan carpet ya gaida Mahaifin nasa. "Barka da dawowa Dad." "Barka dai Jalal ya kake?" "Lafiya lau Alhamdulillah." "Ma sha Allah, ya kuma aikin?" "Alhamdulillah aiki sai an daure." Dariya Dad ya yi yana cewa . "Ya su Ummeen taka?" "Dad ai ban je can ba nan na sauka." "To fa, nan ka sauka?" "Eh na yi kewarku ne Dad." "Allah saekiy, Ummeen taka ta san kana nan." "Ban faɗa ma ta ba Wallahi, don idan ta sani za ta saka ni na koma gidan yau ne, ka san halin ta yanzu za ta iya aiko direba ya ɗauke ni idan ma ban tafi ba." Murmushi Dad ya yi tare de cewa . "Ƙwarai kuwa na san halin ta ba ta san ka yi nesa da ita sai dole. Shi ya sa ba ta ƙaunar wanan aikin da kake yi kullun cikin ƙorafi take. To amma idan ka yi aure ai dole ka bar gidan." "Yauwa Dad ka je kai da Mom kuwa kun ga yanayin tsarin gidan ko?" "Eh mun je gidanm ya yi kyau ma sha Allah, tsarin gidan kamar ba a Nigeria ba a kasar Turai aka yi shi." Cewar Mom tana dariya. Kafin ta ce . "Allah ya kara arziki ya kare ka a duk in da kake, gaskiya ka yi ƙoƙari irin wannan gidan haka?" ",Gaskiya kam Jalal ka narka dukiya a gidan nan Allah ya da yawan rai aka yi wa." Cewar Dad yana jinjina kai. Nan suka cigaba da fira har dare ya yi don karfe sha daya ne a lokacin. Kafin ya yi ma su sallama ya koma part ɗin sa. Wanka ya yi sannan ya kwanta kan gadon daga shi sai gajeren wando da singileti. Har ya dauki waya zai kira Ma'eesha ganin karfe goma sha daya da mintuna arba'in ya sa ya fasa don yana tunanin yanzu tana barci. _Nadra_ Tun da ta ga Sidra ta yi ajiyar zuciya ta dawo hayyacinta ta saki murmushi tana goge hawayen da ke kwance a idanunta. Fahad da ya fice daga ɗakin ta zuba wa idanu har sai da ya banko ƙofar da ƙarfi sannan ta dawo da kallon ta kan Sidra. "Sannu Aunty Sidra."O Ba ta tanka ma ta ba ta kau da kai tana kallon yadda jikinta take jin sanyi. Don gabaɗaya Rigar jikinta sun jiƙe, kamar da gayya ne Fahad ya watsa ma ta ruwan. Ba tare da ta damu da yanayin yadda Sidra ta tsuke ma ta fuska ba ta kama hannunta ta janyo ta tana cewa. "Sannu Aunty ba ki ji ciwo da faɗuwar da kika yi ba? Ba abun da ya same ki ko?" Zare hannunta ta yi daga na Nadra tana kokarin barin wajen kenan sai Nadra ta riƙe ta tana cewa. "Bari na taimaka ma ki muje banɗaki daga nan sai ki yi wanka." "Ba ta ce ma ta komai ba, ta shige banɗaki ta bar ta tsaye. Nadra ta nemi mopping stick ta goge wajen da ruwan ya zube. Sannan ta sanya ma ta sabon zanin gado ta gyara gadon. Sidra na fitowa ta kalli Nadra ta ce . "Sannu da aiki." "Yauwa sannu Aunty ya jikin naki?" "Da sauki Alhamdulillah." "Ma sha Allah, duk da yamma ta yi bari na je na samu abun da zan sarrafa ki samu ki ci na san yunwa kike ji ko?" Kai kawai ta jinjina ba tare da ta yi magana ba. "Yauwa Aunty don Allah kada ku saka wa ranki wani tunani ko damuwa, maganar Doctor ba maganar Allah ba ne, don haka ina sha Allah muna tare da ke har jikokin ki sai mun gani. Kuma ina son mu je mu roki Abba ya yafe ma ki kura-kuranki ki koma gida ki ci gaba da rayuwar farin..." "Nadra!" Yadda ta kira sunan ta sai da gabanta ya faɗi. Ta kalle ta da sauri ba tare da ta karasa maganar da take yi ba. "Na'am Aunty." "Tun ba'a je ko ina ba har kin gaji da ni kina kora ta na koma gida na yi rayuwar farin ciki, saboda na zo gidanki gidan aro ko?" Cike da mamaki Nadra ke kallon ta tana nanata zancenta a zuciyarta, wato zancen cewa su je su nemi yafiyar Abba ne ba ta so ta ce tana korar ta . Sannan kuma me take nufi da gidan aro, wato duk da ba ta gaban Fahad da yanayin ta take nuna ma sa bai saka ta ta shiga hankalin ta ta fita daga lamarinsa ba, har yana cewa gidan aro. Murmushi kawai Nadra ta yi kafin ta ce. "Allah ya ba ki haƙuri Aunty ya huci zuciyarki ba haka nake nufi ba. Bari na je na nema ma na abun da za mu ci ki samu ki sha magungunan ki." Tana faɗar haka ta fice daga dakin tana murmushi. _Jalaluddeen_ Washegari da safe bayan sun kammala breakfast ya shirya don zuwa gidan Ummeensa. Sanye yake cikin cikin cikin cikin wani tsadadden yadi mai ruwan sararin samaniya. Ɗinkin ya zauna ma sa a jikinsa ya ma sa kyau. Sallama ya yi wa mutanen gidan gidan sannan Sadik da ya shirya zuwa asibiti ya dauke shi a motarsa, da niyyar idan ya kai shi gidan sai ya wuce asibiti daga can. Horn ya yi a ƙofar gidan, security ya leƙo ganin su ya sa ya wangale gate ɗin da sauri, kasancewar ya san motar Sadik. Bayan ya yi parking kusan a tare suka fito daga cikin motar . Ma'aikatan gidan na ganin Jalaluddeen suka nufo shi da sauri suna gaishe shi. Ya amsa ma su cikin sakin fuska da walwala. Suka nufi ƙofar da za ta sada su da ƙofar shiga babban falon gidan. Kararrawar ƙofar Jalaluddeen ya danna wanda ya sa gabaɗaya ilahirin jama'ar dake ciki suke kallon ƙofar cike da mamaki. Saboda sun san idan har suka ji yanayin bugun kararrawar Jalaluddeen sun san shi ne. Ummee da Abba sai Yusuf da suke a dinning table suna breakfast suke kallon ƙofar. Ma su aikin da ke falon ma suna kallon ƙofar suna mamakin yaushe ya dawo. Hatta Yasmeen da yanzu farkawar ta daga barci kenan ta ji ƙarar ƙofar masoyinta sai da ta miƙe zumbur. Da sauri Yusuf dake cin abinci a dinning area sai ya tashi kafin ma su aikin su buɗe har ya riga su isa ya buɗe. Cike da mamaki yake kallon Jalaluddeen ya ce. "Yaya Jalal kai ne yanzu haka?" Gajeren murmushi ya yi tare de cewa. "Ga shi kuwa kana gani." Ba su hanya ya yi suka shigo cikin sannan ya rufe kofar daidai lokacin da Yasmeen ta fito daga part ɗin ta. Daga ita sai rigar barci wacce ta tsaya iya guiwarta, kanta babu ɗankwali kanta babu ɗankwali sai kitso calaba da ke kanta. Ganin da gaske ba ƙarya kunnen ta yi yi ma ta ba ta nufe shi da gudu za ta rungume shi ya yi saurin dakatar da ita da hannu ya ce. "Koma ki saka kaya!" Ya faɗa babu wasa a fuskarsa . Da sauri ta juya tana tura baki Dariya Yasuf ya yi don ya san a fadin gidan nan Jalal ne kawai zai yi ma ta magana sau ɗaya ta aikata abun da ya umarce ta ba tare da gardama ba. Ummee ta kalli Jalaluddeen ta kalli Sadik dake rike da jakar kayan Jalaluddeen dake hannun Sadik. "Daga ina kuke haka da safiyar nan? Na san dai ba ka isa a ce har ka bar garin Kaduna ka iso nan ba ." Kafin ya yi magana sai Sadik ya ce . "Daga gidanmu yake, tun jiya ya iso na je na dauke shi a airport na yi ma sa bazata. Daga airport na kai shi gida ya kwana yanzu na dawo da shi gidansu." Ya yi maganar yana dariya. Su ma dariyar suka yi ban da Ummee. Kafin ta ce. "Son za ka dawo ko ka sanar ma na dawowarka sai dai na gan ka daga sama wasu ne ka sanar." 'Wasu?' Sadik ya faɗa a ransa yana mamakin Gwaggon tasu. Gaida su ya yi sama-sama ya ce zai tafi aiki yana sauri, daga nan ya fice daga falon. Yasmeen ce ta dawo sanye da rigar after dress ta saka hula a kanta. Cikin farin ciki ta ƙaraso wajensa da niyyar ta rungume shi. Da idanunsa kawai ya gargaɗe ta wanda gane nufin sa ya sa ta tura baki tana fushi. Zama ta yi akan kujera mai zaman mutum biyu dake Falon. Kasancewar ba wanda ya san abun da ya haɗa su ya sa Abba cewa. "Yasmeen ba ki ga Yayanki ba ne?" Kamar tana jira sai hawaye dariya Yusuf ya yi yana cewa. "An dai ji kunya." "Ke lafiya me yake faruwa ne haka, ba na son sakarci." "Ummee bar ta ni da ita ne." Jin haka ba su sake magana ba, ya gaida su cikin girmamawa, sannan Yusuf ma ya gaishe shi. "Tun jiya kake garin nan Son shi ne ba mu sani ba?" "Ummee ki yi haƙuri ke ma kin san ban saɓa sanar da tafiya ta ko dawowa ta ba, muna waya da Mom ne nake sanar da ita dawowa ta anan Sadik ya ji shi ne ya je ya taro ni." "To me ya sa da muka yi waya ba ka sanar da ni ba?" "Bayan mun gama waya da ke lokacin ban yi tunanin dawowa ba." Murmushi ta yi kafin ta ce. "You're welcome." Murmushi kawai ya yi yana kallon Yasmeen dake cika da batsewa. "Amma ya kamata ka canza wanan aƙidar taka Son, a ce ba ka sanar da kowa duk abun da ya shafe ka? Yanzu fa iyali kake shirin ajewa ko ba haka ba, duk rashin damuwa da mutane idan kana aiki dole za ka canza ko don iyalinka." "In sha Allah Ummeena." "Yauwa Ɗan gidan Ummeensa." Gabaɗaya suka saka dariya. Ta kalli jakarsa ta ce wa Yasmeen. "Kai ma sa jakarsa ɗakinsa." Ta ɗauki jakar ta nufi part ɗin nasa dake upstairs. Da kallo ya bi ta kafin ya kalli su Ummeen ya ce . "Bari na fito Ummeena." Murmushi ta yi kafin ta ce. "Ya aiki ya hanya?" "Lafiya lau Ummee aiki ba sauƙi." "Shi ya sa ba na son wanann aikin naka, ka ajiye shi ka fara kula da Kamfanin..." "A'a kin san kowa da hanyar cin abincin sa, na san dai saboda rashin zamansa ya sa ba ki son aikin." "Ki kwantar da hankalinki Ummeena." Ya faɗa yana nufar part ɗin sa. Yana tura ƙofar falon ya yi kiciɓis da Yasmeen dake ƙokarin fitowa. Kau da kanta ta yi gefe idanunta na kara cikowa da ƙwalla. Hannunta ya rike yana cewa . "Meye kuma na kuka?" "Ka daina so na ka daina ƙauna ta." Ta saki kukan da take riƙe wa , kafin ya kalle ta ya ce . "Me ya sa kike tunani na daina son ki?" "Ai a baya ba ka ƙyamata ta dai yanzu, da idan ka dawo za ka yarda na yi ma ka oyoyo idan na ji kwarara amma yanzu sai ka hana." Dariya ya yi kafin ya ce. "Da da yanzu ba daya bane Yasmeen, a baya ina na ki kallon jini daya ne ni da ke ina ma ki kallon Muharrama ta amma daga baya sai muka fahimci ba haka ba ne, daga ranar da na fahimta cewa ba Ummee ta haife ni ba na canza yanayin zamantakewar da nake yi da ke, domin akwai iyaka tsakanin mu. ga shi har ana shirin yi ma na aure, ai addini bai yarda na haɗa jiki da ke ba har sai kin halatta a gare ni. Ina fatan kin fahimce ni?" Kai ta gyaɗa ma sa alamar eh kafin ta ce. "Za ka raka ni wajen bikin ƙawata?" "Wata ƙawarki?" "Maryam da ka sani Aminiya ta." "Har bikin ya zo?" "Eh kuma mun shirya taro kowace za ta je da saurayinta ko mijinta, dama saboda ba ka nan na ce ba zan je ba, tun ja ka dawo dai mu tafi karfe biyar na yamma." Shiru ya yi kafin ya ce. "To Allah ya kai mu. Amma ba na son zuwa irin Wuraren nan fa." "Please Yaya Jalal ka raka ni." "Okay Allah ya kai mu." Da murna ta daka tsalle tana yi ma sa godiya. Fita ta yi daga part ɗin zuciyarta fara tas. Tsaye yake yana ƙarewa ɗakin nasa kallo wanda ya ƙawatu da kayan more rayuwa, babu wani wadataccen haske a cikin dakin, ya ɗauki wani remote ya danna, take ɗakin ya gauraye da hasken wasu fitilu da suka ƙara ƙawata ɗakin. Tangamemen gadonsa wanda aka gyara ya kalla gadon circle ne a zagaye yake ba irin gamagarin gadon da kowa ya sani ba ne. Jakar kayansa ya ɗaura kan gadon ya cire wayoyinsa na aiki da kuma wacce Ma'eesha ta siya ma sa ya ajiye saman gadon ya rage kayan jikinsa ya shiga bathroom don yin wanka. Shower 🚿 ya sakar wa kansa yana wanka yana tuna yadda Ma'eesha take dafa ruwan zafi ta kai ma sa banɗaki ya yi wanka. Sauri-sauri ya yake yi ya fito domin ya kira ta a waya domin ya ji halin da take ciki. Ummee ce ta yi sallama ta yi knocking ƙofar ɗakin nasa, jin shiru ya sa ta tura kofar da sallama. Sai dai ta ga baya cikin bedroom ɗin nasa. Amma jin saukar ruwa a banɗaki ya sa ta gane cewa wanka yake yi. Har za ta fita sai ta ji ƙarar waya kamar calculator ta juya ta kalli wayar dake kan gado yana ruri. Kallon wayar ta yi cike da mamakin yadda aka yi mutum kamar Jalal yake amfani da wayar da talakawa ke amfani da su. Ƙarasawa ta yi jikin gadon tana kallon wayar. Ganin sunan da ke jikin wayar ne take kiransa wato MAR'ATUSSALIHA ya sa ta cika da mamaki. Kiran ya tsinke take wani kiran ya sake shigowa wayar, da sauri ta kai hannu kan wayar... *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page6️⃣5️⃣ Kiran ya tsinke wani kiran ya sake shigowa wayar, da sauri ta kai hannu kan wayar da niyyar ɗauka sai ya riga ta ɗauka cikin zafin nama. Kallonsa ta tsaya tana yi yana sanye da rigar wanka kansa na ɗigar da ruwa da towel a hannunsa. Yana ɗaukar wayar sai kiran ya tsinke, ya kalle ta ya ce. "Ummee kina buƙatar wani abu ne?" "Wace ce mar'atussaliha?" "Abokiyat aikina ce ita." "Ba ta da wani suna se wannan?" "Tana da shi, amma haka ake kiranta saboda kyawun halinta da nagartarta." "Okay ka fito ka ci abinci na ga ba ka fito ba ne na biyo bayanka." "Ummeena yanzu na ci abinci a gidan Mom, sai zuwa anjima." "Okay ka huta, ko kana bukatar wani abu ne?" "Ba na bukatar komai Ummeena." Murmushi suka yi wa juna a tare sannan ta fita tana cewa. " ka kwanta ka huta kada ka takura kanka da zancen aikin nan." Yana dariya ya amsa sannan ya goge kansa da towel na hannunsa. Kiran Wayar ne ya bi ya danna ma ya kira . "Bugu biyu da ga tare da yin sallama cikin nitsatsiyar muryarta. "Assalamu alaikum warahmatullah." "Wa'alaiki salam warahmatullah Mar'atussaliha mayar mijinta." Murmushi mai sauti ta yi wanda sai da ya ji sauti nan cikin kunnensa. "Ina wuni' "Lafiya lau ya kike" "Alhamdulillah ga ni ina gama da kewar ka, har ciwo.n kai na yi sai da A'isha ta zo ga siyo Mani magani na sha. Bayan na tashi barci ne sai na ji sauƙi. "Ya Salam, to yanzu ya kike ji a jikin naki?" "Alhamdulillah na ji sauƙi sosai

Chapter 37 of 49