Share this page
kira ni da Nadra, don kin girme ni ni ce ya kamata na kira ki da Aunty." Murmushi Rumaisa ta yi ta ce. "Ko na girme ki yanzu ke ce sama da ni, sabi'oda Yayana kike aure kenan kin zama Yayata." Mika ma ta basket ɗin ta yi tana cewa. "Sauri neke yi sai Anjima kuma." "To don Allah ki ce wa Mama ta daina aiko ma na da abinci mun gode sosai, zan fara shiga kitchen da kaina." Kai Rumaisa ta jinjina tana cewa. "Zan fada ma ta in sha Allah." Sallama suka yi ta juya ta tafi ita kuma ta shiga da abincin ciki, a dinning table ta ajiye ta shiga bedroom nata. _Ma'eesha_ Farkawa ta yi da asuba cikin barci take ta laluben katifar ko za ta ji shi, amma sai ta ji wayam ba alamar mutum a kusa da ita, bayan ta san a jikinsa da ta kwanta. Kunna torchlight ɗin wayanta ta yi sai ta hango shi can kan tabarma da yake kwanciya akai ya kwanta ya dunƙule jikinsa waje ɗaya. Mamaki ya kama ya kama ta domin ita dai a iya saninta yadda ta yi masa gata ta kawo shi kan katifa ta lulluɓe shi amma bai masa ba ya tashi ya koma kan tabarma. Taɓe baki ta yi daidai lokacin ne kuma aka kira sallah. Shi ma kiran sallar ne ya farkar da shi ya buɗe juyayyun idanunsa wanda suke ajuye sai dai ba sa da amfani tun da baya gani da idanun. Ƙoƙarin tashi ya fara yi ta yi sauri ta sauka tana miƙa ma sa sandarsa. "Ga sandarka nan." Ta mika masa sandarsa ya karba tare da cewa. "Na gode Allah ya yi ma ki albarka." Da Amin ta amsa tana ɗaukar buta ta ba shi buta. "Ya jikin naka?" "Na ji sauƙi." "Allah ya kara sauki." "Amin na gode, matata maganin kukana." Bayan ya yi alwala ya je masallaci yayin da ita kuma ta yi sallar ta a gida. Sai karfe bakwai ya dawo daga masallaci zuwa lokacin har ta kammala breakfast. Doya ta soya ma su sai ta yi source ɗin ƙwai. Da ruwan Lipton wanda ya ji kayan ƙamshi. Don kudin da suke hannunta sun ƙare ƴan canji ne suka rage ma ta. Ruwan Lipton kawai ya iya sha bai ci doyar ba, hakan ya saka ta damu Kasancewar ta san ruwan Lipton ba zai ɗauke shi ba. "Ko na siyo bread ne na haɗa ma ka tea ka sha?" "Kada ki damu hakan ya ishe ni, ba na jin cin wani abu a bakina ne." Cike da tausayawa ta ce. "Ayyah sorry." Kai kawai ya jinjina ma ta ba tare da ya yi magana ba. "Bari na je na kawo ma ka maganininka." Tana fadar haka ba ta jira cewarsa ba ta tashi ta ɗauko ledar maganinsa ta ba shi. Pure water ta fasa ta zuba a cup ta bashi . "Ka sha maganin sai ka kwanta ." Ta fada tana ɓallo ma sa maganin ta bashi, ya karba ya sha. "Zan yi wanka." Ya faɗa yana dafe kansa. "Okay bari na kai ma ka ruwa." Tashi ta yi ta je ta haɗa ma sa ruwan wanka ta kai ma sa banɗaki. Yana zaune ta dawo ta ce. "Na kai ma ka ruwan a banɗaki." "To na gode Allah ya yi ma ki albarka." Amin ta amsa yayin da da shi kuma ya fara lalube cikin jakar kayansa. "Me kake nema?" "Jallabiyata." "Okay bari na duba ma ka." Kafin ya yi magana sai hannunsa ya kai kan jallabiyar sakamakon tana da santsi ne ta fita daban da sauran kayan, hakan ya saka da ya kai hannu yake gane abinda ya taɓa. Ɗauka ya yi ya yayin da ita kuma ta fita daga ɗakin. Bayan fitar ta sai ya cire kayan jikinsa ya saka jallabiya. Kayan da ya cire ya fito da su yana cewa. "Ina son na wanke kayan kafin na shiga wanka." "Saboda me za ka yi wanki bayan ba ka da lafiya ?" "Kar ki damu zan iya yi." Nan ta dai suka fara jayayya akan za ta wanke masa ma sa shi kuma ya hana ya ce shi zai wanke. "Kana son na samu lada?" "Eh sosai kuwa Ma'eesha." "To idan har kana son na samu lada to ka bar ni na yi wankin kayan ka domin lada za'a rubuta ma ni." Hakan ya saka ya ce. "Ke me ya saka idan zan wanke ma ki kike hanawa?" "Saboda ni na fi cancanta na yi ma ka ba kai za ka yi mani ba." "Ni kuma ba na son ki wahala bisa la'akari da gidan da kika fito ba ki saba da waɗan nan aikace -aikace ba." Murmushi mai ciwo ta yi tare da cewa. "Haka ne, ka yi gaskiya, tabbas ban saba ba don ma su aiki ke yi ma ni amma hakan ba yana nufin ban iya ba ne. Don haka ko da a ce mijina kana da kudi ka aje ma su aiki to ka sani duk wani aiki naka ba zan taba bari ƴar aiki ta yi ba domin kwaɗayin ladan da zan samu wajan kyautata ma ka." "Kin tabbata?" "Of course, ka jira lokaci za ka ce na faɗa." Murmushi ya yi kafin ya ce. "Wani lokaci zan jira kuka yaushe lokacin zai zo, na so na ga wannan lokacin." Kallo da ta yi tana ɗauke ƙwallar da ta ji ya gangaro ma ta da yatsanata ta ce. "Lokaci yana tafiya a hankali ga masu jira, yana gudu da sauri ga masu tsoro,yana zama dogo sosai ga masu korafi, yana zama gajere ga masu murna, Amma ga masu ƙauna lokaci shi ne madawwamiya." Cikin sanyin jiki ya nufa banɗaki ba tare da ya yi magana ba, saboda yanayin maganar na ta tana gab da yin kuka. Domin ya ji ƙuna a cikin kalamanta. _Nadra_ Ta gama shirinta zuwa register da zai kai ta na sim card ɗin da zai siya ma ta. Haka kawai ta tsinci kanta cikin farin ciki domin ta san ko ba komai za ta ji Muryar Umma da Abba. Fitowa ta yi dan sanar da shi ta shirya, baya Falon don haka sai ta yi knocking da a ƙofar falonsa. Jin shiru ya saka ta yi tunanin cewa yana cikin bedroom ɗinsa. Don haka ta tsaya bakin bedroom tana knocking. Izinin shiga ya ba ta ta tura ƙofar bedroom ɗin ta shiga bakinta ɗauke da sallama. Yana tsaye a gaban dressing mirror ɗaure da towel a ƙugunsa ta shigo. Ganinsa haka nan ta juya da sauri tana barin ɗakin. Ta jikin mirror ya kalle ta ganin yadda ta fita kamar wacce ta ga abin tsoro take guduwa. Tsane ruwan jikinsa ya cigaba da yi. Ita kuma ba ta tsaya ko ina ba sai bedroom ɗinta. Don saura kadan dogon Hijabinta ya haɗe ma ta ƙafa ta faɗi, sai Allah ya taimake ta ba ta fadi ba. Tana nan zaune bayan wasu ƴan minutes ya shigo sanye da farin yadi mara nauyi. Sai ƙamshin turarensa yake tashi a jikinsa. Ganinsa ya sa ta mike da sauri tana kallon sa cike da fargaba, ganin take yi kamar wani laifi ta aikata ma sa ganinsa da ta yi ɗaure da towel. "Ke." Kallonsa ta yi ganin yana kallonta ya saka ta ɗauke idanunta da sauri. "Ina ganin akwai motsi a cikin kanki ko?" Ba ta gane me yake nufi ba don haka ta ce. "Motsi a cikin kai kuma?" "Eh ina nufin ba ki da cikakken hankali ko?" Tura baki ta yi tana kau da kai. Da kika shiga ɗakina me ya saka kika fita a guje?" "To da ka san ba ka da kaya a jikinka me ya saka ka bari na kalle ka haka nan ai bai dace ba." Mamaki ta bashi don haka ya ce. "Shekarunki nawa?" "Goma sha takwas." '18 years no wander ta fiye shirme da yawa, ashe akwai tazara tsakaninta da Sidra, don Sidra yanzu shekarunta ashirin da biyar, an dauki yarinyar da ba ta gama mallakar hankalin kanta ba an hada ni da ita.' Tsuki ya ja a fili wanda sai da ta ɗaga kai ta kalle shi. Sai ta ɗauka shigar da ta yi masa ɗaki ne ya ba shi haushi, don haka ta ce. "Ka yi haƙuri zan kiyaye." "Za ki kiyaye me?" "Ba zan sake shigar ma ka daki haka nan ba ganka ba kaya a jiki ba wannan ma akasi ne." Dafe kansa ya yi ya rasa ya zai nuna ma ta daidai da ba daidai ba. "Kina zuwa islamiyya?" ",Eh mana har walima fa sai da na yi." "Me aka sanar da ku akan hakkin aure?" Shiru ta yi kanta a ƙasa, ya ce "Akwai inda aka ce ma ku ya haramta don miji ya kalli matarsa ba kaya ne ko kuma shi ya kalle ta ba kaya sun aikata wani babban laifi ne?" Girgiza kai ta yi alamar a'a. Sannan ta ce. "An ce mu dinga rufe tsiraicinmu." "Okay to waye aka ce ku baiyana wa tsiraicinku ?" Tura baki gaba ta yi tana kau da kai. "Ni ma ban sani ba." "Okay to bari na nuna ma ki yau za ki sani." Ya faɗa yana nufo tana ja baya, da sauri ta ce. "Mazajen aurenmu ne za su iya ganin surar jikinmu." Ta fada kamar za ta yi kuka, shi kuma ya yi dariya ya ce. "Oh ashe kin sani kike yi kamar wata..." Rurin wayarsa ya saka ya dakata da maganar da yake yi ya duba ganin Mama ce ya ɗaga da sallama. Bayan sun gaisa ne ta cikin wayar take sanar da shi zuwan dangin mahaifinsa zuwa Anjima. Ya ce to ya sani zai kai Nadra ta yi register layi ne ya siya ma ta waya. Mama ta ji daɗin hakan sai sanya masa albarka take yi, ta ce ya ba Nadra su gaisa ya ce tana cikin dakinta idan ta fito zai kira. Ya fadi haka ne don ya ga ta kasa motsi kunya ta ishe ta ba lallai ta yi maganar ba. "Ki same ni a mota." Yana fadar haka ya fice daga ɗakin, ita ma ta bi bayansa. Tsaye ta gan shi a ƙofar fita, tana fitowa ya rufe kofar, har lokacin ba ta yarda ta kalle shi ba. Motar da ya nufa ta bi bayansa, direbansa ya taso ya zo ya buɗe ma sa bayan motar ya shiga ita ma ya bude mata dayan gefen ta shiga sannan ya zagaya ya zauna mazauninsa, ya yi wa motar key suka bar gidan bayan maigadi ya wangale ma su gate. *ABUJA* _Sidra_ Ta fito daga cikin gidan hannunta rike da handbag ɗin ta da wayarta. Wajen motar dake harabar gidan ta nufa. Direban ya saka trolly ɗin ta a but motar yayin da ta zauna bayan motar. Fuskarta ba walwala duk yadda Sady baby ke ta yi ma ta magana ba ta wani kula ta ba, don haushin ta take ji. Kasancewar ita ta ba ta goyon bayan abinda ta aikata, a lokacin da Khadijah ke hana ta gani take yi Khadijah ba ta ƙaunar ta, sai ga shi sanadin biye wa Sady baby komai ya lalace ma ta. "Ƙawata Sa mun yi waya, don Allah ki yi hakuri kuma da za ki bi shawara ta ki hakura da Fahad tun da an bashi ƙanwarki ya aura." "Fahad nawa ne ni kaɗai babu macen da za ta mallake shi sai ni kuma zan iya aikata komai a kansa, babu wanda ya isa ya ma ni shamaki da abun so na ciki kuwa har da ƙanwata Nadra" Ta fada cike da ƙasaita. "Direba mu tafi sauri nake yi." "Allah ya tsare hanya." "Amin idan kuma har wata matsala ta biyo baya to fa ki sani ba zan ɗauki fansa ta akanki ba zan taɓa saurara ma ki ba ko kaɗan." Direba ya ja motar suka bar gidan suka kama hanya don zuwa Kaduna. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page2️⃣9️⃣ "Amin. Idan kuma har wata matsala ta biyo baya to fa ki sani zan ɗauki fansa ta akanki ba zan taɓa saurara ma ki ba ko kaɗan." Direba ya ja motar suka bar gidan suka kama hanya don zuwa Kaduna. Amma a zuciyarta fargaba ce ta yadda za ta tunkari iyayenta da maganar dalilin da ya sa ta gudu ranar ɗaurin aurenta. Tabbas ta san mahaifnta na da zafi, idan ya dauki zafi ya hau to saukowarsa abu ne mai matukar wahala cikin sauƙi. Sai yanzu take nadamar wasikar da ta rubuta ta ajiye, domin kuwa da ba ta rubuta ta ajiye ba za ta iya ƙaryar cewa sace ta aka yi yanzu aka sake ta. Amma wannan wasikar shi ne babban kuskuren da sai yanzu ta san ta tafka ta. Cike laɓɓanta ta yi tabbas ba za ta tunkari gidansu ba sai ta fara zuwa wajan ƙawarta Khadijah ta ba ta shawarar yadda za ta yi, wanda a baya ta yi kokarin hana ta guduwa amma ta kasa. Wayarta wacce har yau take kashe ta kalla sai ta kau da kai tana kallon hanya. _Fahad_ Yana zaune a bayan motar Nadra na gefensa , idanunsa na kan wayarsa yana danne-danne ya ce. "Za mu yi baƙi yau, dangin mahaifina ne za su zo ganin ki zuwa anjima." "To Allah ya kawo su lafiya ." Ba wanda ya sake yin magana a cikinsu har suka ƙarasa office na kamfanin MTN don ya siya ma ta sim kuma ta yi register. Suna parking a wajan da aka tanada don ajiye motoci direban ya fito da sauri ya bude ma su bayan motar . Suka fito sai ga wani mutum sanye da Suit ya ƙaraso in da suke cike da girmamawa ya ce wa Fahad. "Ambassador Barka da zuwa." Hannu Fahad Majidaɗi ya mika ma sa suka gaisa. Sannan ya kalli Nadra ya ce. "Madam Barka da zuwa." "Ina kwana?" Ya amsa sannan ya ma su jagora zuwa ciki. Ba ɓata lokaci aka yi ma ta duk abinda ya dace, gabɗayansu san san waye Fahad. Har da ihsani ya yi ma su sannan suka bar wajen suka kama hanyar gida. Ganin sun kusa zuwa ta hanyar da zai sada Nadra da gidan iyayenta ta kalle shi ta ce "Don Allah ka kai ni gida na ga Umma ta ko na mintuna biyar ne." Ka kallonta bai yi ba ballantana ya amsa ma ta. Har suka wuce hanayar unguwar tana kallon hanyar idanunta na cikowa da ƙwalla sakamakon ba ta da lafiya ko ranar auren a kwance take. Horn direban ya yi maigadi ya wangale ma sa gate ya shiga da motar, parking space ya nufa ya yi parking sannan ya fito ya bude ma su. Bayan sun fito ne ya rufe sannan suka shiga ciki. Bayan sun haura upstairs ne ya kalle ta ce. "Ki haɗiye wannan hawaye naki na faɗa ma ki, idan kuma kukan kike sha'awar yi zan saka ki yi mai dalili." Ya faɗa yans jinjina kai alamar tabbatar wa. Na fada ma ki muna da baƙi idan kika kuskura kika aikata abun da zan ji kunya akan akan gidadanci suka bar gidan nan sai na hukunta ki a cikin gidan nan" Tura baki ta yi tana magana ƙasa-ƙasa tana cewa. "Ni kam ba bagidajiya ba ce, idan mutum baya irin rayuwar da kuke yi sai ku dinga ma sa kallon bai waye ba, to ba na son wayewar ta ku." "Me kike cewa ne?" "Ba abinda na ce da kaina nake magana." Ta faɗa tana kallon wayar dake ajiye a Centre table, ta dauki wayar ta tuna ba ta yi ma sa godiya ba. Ta kalle shi ta ce . "Na gode Allah ya saka da alkhairi ya ƙara ma ka buɗi." Tana fadar haka ta shiga ɗakinta da wayar a hannunta. Shi ma ɗakinsa ya wuce. Tana shiga ta daka sim card ta yi settings komai, tana gamawa ta ga ya tura kofar ya shigo mika ma ta kati ya yi ba tare da ya ce komai ba. Karɓa ta yi ta ga recharge card ne na 10,000 ya siya ma ta cike da murna ta yi godiya ya fice bai amsa ma ta ba. _Makaho_ Bayan ya fito daga wanka hannunsa ɗauke da bokitin ya ajiye a tsakar gidan. Ma'eesha na zaune a tsakar gidan ta ce. "Ka yi a hankali." "Na gode." Ya faɗa yana laluben ƙofar ɗakin kafin ya shiga da sallama. Sai bayan kamar mintuna talatin ta shiga cikin ɗakin da sallama a bakinta. Ya amsa ma ta yana zaune kan tabarm kansa a ƙasa. "Lafiya dai ko ciwon kan ne?" "Ba komai." Shiru ta yi kafin ta ce. "Zan je can bakin layi na dawo?" "A dawo lafiya?" Ya amsa ma ta sannan ta ɗauki gyalen ta yafa ta fice daga gidan. 2k ya rage ma ta a hannunta ga shi yanzu mijin baya jin dadi tana son ta siya ma sa nama ta ɗan yi masa farfesu ko zai ci tun da ya kasa cin abinci. Dubu ɗaya ta cire ta siye naman dubu ɗaya ya rage ma ta dubu ɗaya. Abun da ba ta yi tsammani ba shi ne ganin naman dubu ɗaya yanka biyar ya yi ma ta cikin sanyin jiki ta dawo gidan tana tunanin wanan. 1k da ya rage ma ta idan ya kare ya z su yi, ga shi tana son ta siye Omo da sabulu na wanki. Kafin ta shiga gidan ta tsaya wajen me shagon ta fiye Omo na ɗari biyu da dabulun wanki na ɗari uku aka ba ta canjin Naira ɗari biyar. Ta koma gida gidan in da ta tarar har ya yi barci, don cikin magungunan da aka ba shi akwai wanda zai saka shi barci. Gass ta kunna ta ɗora tukunya ta haɗa ma. Sa farfesun naman wanda ya ji kayan ƙamshi. Ko ɗaya ba ta ci ba ta zuba masa a bowl ta rufe ta ajiye ma sa. Jira take yi ya tashi ko zai samu abinda ya saka a baki, domin rashin cin abinci da bai yi ba ya dame ta _Nadra_ Sabuwar wayarta da Fahad Majidaɗi ya siya ma ta Samsung Galaxy S23 ultra wayar kudinta ta kai kimanin miliyan ɗaya da dubu dari biyu 1,200,000. Kallon wayar take tana Murmushi cikin ledar wayar ta duba ta zaro idanu sakamakon ganin zunzurutun kuɗin wayar wanda ba ta yi zato ba. Umma ta kira don ta ji muryarta amma sau biyar kiran na katsewa ba'a ɗaga kiran ba, sai ta saka lambar Abba ta danna ma sa kira, kasancewar ta haddace lambobin wayar a cikin kanta. Abba ya ɗaga kiran wayar tare da yin sallama. "Assalamu alaikum." "Abba." Ta faɗa muryarta na rawa kamar za ta yi kuka. "Nadra ke ce?" Kai ta jinjina kamar yana ganinta. "Kina lafiya?" "Lafiya lau Abba." "Ma sha Allah, ina mijin naki?" "Yana ɗakinsa?" "Ba wata matsala ko?" Hawaye ta goge kafin ta ce. "Abba nan zan cigaba da zama da shi har zuwa lokacin da Aunty Sidra za ta ..." Tsawar da Abba ya daga ma ta ne ya saka ta fashe da kuka. Tabbas ta san cewa mahaifinta na da zafin zuciya kuma wannan alama ce da ke nuna har yanzu yana fushi da Sidra." Jin sautin kukanta ya saka ya sassauta murya cikin sigar rarrashi ya fara magana. "Nadra, ashe ba na faɗa ma ki cewa kada ki sake yi ma ni maganar Sidra ba, ki mance da ita tun da ta guje mu ta zabi wasu akan mu to ki ɗauka ta mutu. Na san mancewa da ita ba, amma wannan ne karo na karshe da za ki yi ma ni maganar ta. Tabbas ta so ta kunyata ni ta tozarta ni a idanun duniya Allah ya sa ke ce kika fidda mu kunya , hakika ina alfahari da ke Allah ya yi ma ki albarka ƴaƴanki za su yi ma ki fiye da yadda kika ma na." "To Abba." Ta faɗa tana goge hawaye. Kiran wayar Farida ne ya shigo wayar Fahad, nan take sanar da shi sun ƙaraso suna harabar gidan. Nan yake sanar da ita yana zuwa. Fita ya yi in da ya same su a harabar gidan, ƙannin mahaifinsa ne da yayyunsa, sai da wasu dangin mahaifinsa, sai Rumaisa da ta yi ma su jagora Da Farida wacce ta na ce sai ta zo ita ma. Duk da mahaifiyarta Hajiya Jummai ta hana ta zuwa don kada ta zo ta ga abun zai ɓata ranta. Motoci uku suka yi don sun kai su goma sha biyar. A falon dake downstairs suka yada zango. Sai ya gushe su cike da girmamawa abokanan wasansa na tsokanarsa Farida ba ta shigo ba ta tsaya a harabar gidan tana ƙarewa gidan kallo. Tana ina ma ita ce aka kawo wannan gidan a matsayin mayar Fahad Majidaɗi. Cike da ƙunar rai ta shiga falon tana karewa falon kallo. Tabbas ya tsaru gidan Fahad gida ne da kowace mace mai hangen nesa za ta yi fatan ace ita ce matar gidan. Bayan sun gaisa da kowa ne ya kalle su ya ce "Mu haura sama sai ta fito ku gaisa ko?" Ya fadi haka yana haurawa upstairs ɗin wacce ganin haka ya sa Farida ta bi shi a baya. "Yaya." Ta faɗa cikin shagwaɓa wanda ya sa ya tsaya daidai kofar ɗakin Nadra. "Ya aka yi ne Farida, kin gama fushin naki?" Hararar wasa ta yi ma sa tana cewa. "Duk ranar da aka ce na mutu to son ka ne ya yi ajalina." Basar da ita ya yi kamar bai je me ta ce ba, daidai lokacin da zai shiga ɗakin Nadra ta yi saurin rike hannunsa suka shiga tare. Da sallama a bakinsa suka shiga ita kam ko sallamar ba ta yi ba. Hannunsa na cikin na Farida suka shiga, shi a ganinsa ba wani abu ba ne kamar yadda Rumaisa ke rike shi haka Farida ke ma sa duk da kasancewar ita ba maharramarsa ba ce akwai aure a tsakaninsu. Daidai lokacin da Nadra ta ɗago kai tana kallon ƙofar, ta sauke idanunta a kansu ta yi saurin goge hawayenta. Hannunsu dake sarƙe cikin na juna ta kalla sannan ta kalli fuskar Farida sai ta ga ba ta san ta ba kuma ba Rumaisa ba ce wacce suke uwa daya uba ɗaya, iya saninta Rumaisa ce kawai ƙanwarsa. Harara mai cike da tsana Farida ke jifan Nadra da shi. Nadra kam ba ta ma san tana yi ba, dan kallo ɗaya ta yi ma ta ta kalli hannunta da take rike da na Fahad ta ɗauke kai. Wayar Fahad ce ta fara ruri ya kalli Nadra ya ce. "Sun iso suna falo." Daga haka ya daga kiran wayar yana mai zame hannunsa daga cikin na Farida. Fita ya yi daga ɗakin yana amsa wayar. Farida ta tsaya ta rike ƙugu tana ƙare wa ɗakin Nadra kallo. _Ma'eesha_ Bayan ta gama duk wasu aikace-aikace da take da su har wankin kayan ta da na Makaho sai da ta wanke su. Ta shiga ɗaki ta same shi zaune ya haɗa tagumi. "Ka tashi ?" Ta fada tana zama a gefensa. Hannun ta ta daura a saman goshinsa zuwa wuyansa ta ji ba zafi. "Alhamdulillah da alama ka ji sauki ko?" Kai kawai ya jingina ma ta ba tare da ya ce komai ba. "Na san kana jin yunwa ko?" "Eh." Ya faɗa a takaice. "Bari na kawo ma ka abin da za ka ɗan fara ci." "Bari na wanke baki." Ya faɗa yana mikewa tsaye. "Ina na ajiye Sandar tawa ce?" "Ga shi nan gabanka ai bai yi nisa da kai ba." "kin san ban gani nake yi ba, kuma ban laluba ba." "Allah sarki wata rana za ka gani, in sha Allah wata rana idanunka za su buɗe ka ganni ka ga yadda wannan duniyar ta mu take." Ɗan jim ta yi kafin ya ce . "Ba na jin zan iya gani, domin Wannan lalurar da ita aka haife ni, kin san kuka duk wata lalura in dai har da ita aka haife ka to ba wanda zai iya ba ka magani ko aiki ka samu lafiya. Sai dai wadanda suka samu lalurar daga baya ne to ana iya dacewa." "Ikon Allah ya fi gaban mamaki." Fita ya yi ya je ya wanke baki, ko da ya dawo ta ajiye ma sa farfesun naman nan da ruwa sai lemu na gora da take da shi ajiye. Da sallama a bakinsa ya shigo cikin ɗakin, don haka ta amsa tare da cewa "Na ajiye ma ka abinki ka yi a hankali." Ta fada tana rike hannunsa da taimakonta ya zauna. ƙamshi ya daki hancinsa ya yi shiru kafin ya ce. "Me kika dafa." Farfesun naman rago ne." "Ina kika samu nama?" Murmushi ta yi tare da cewa. "Siya na yi ma na, ina zan samu nama?" "Na ɗauka kudin ki ya kare." "Eh ya ƙare yanzu haka ma ɗari biyar ne ya rage ma ni." Dafe kansa ya yi tare da furta kalmar. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un." Ga ni yake yi ya gaza tun da har kudin hannunta suka kare bayan ɗawainiyar da take yi na gidan da shi kansa, yanzu ina zai shiga ya fita don samawa kansu mafita, yadda kudin suka kare haka wata rana ma kayan abincin da ta ajiye ma su a gida za su ƙare." Ganin lokaci ɗaya ya shiga cikin

Chapter 18 of 49