, zan je ni ma na sanar da nawa dangin da abokan. Da ma su niyyar zuwa su dakata, ni ma zan dakatar da ma su niyyar zuwa. Duk da dai dama akwai wadan da za su zo daga ƙasar waje or ready suna hanya ba zancen juyawa tun da fly ne ba mota ba."
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Abba ya sauke kafin ya ce.
"Ka bar su kawai su zo kar ka dakatar da kowa."
Da mamaki Fahad ke kallon Abba kafin ya yi magana Abba ya ce.
"Sidra ta gudu a ranar aurenka da ita, don haka zan maye ma ka gurbin ta da ƙanwarta Nadra idan har ka amince "
A matuƙar ruɗe Fahad ya kalli Abba ya na girgiza kai alamar a'a.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce ✍️
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page0️⃣3️⃣
"Sidra ta gudu a ranar aurenka da ita, don haka zan maye ma ka gurbin ta da ƙanwarta Nadra idan ka amince."
A matuƙar ruɗe Fahad ya kalli Abba ya na girgiza kai alamar a'a .
Sai a lokacin Ammi ta yi magana ta ce.
"Kai yaro Fahad kake ko, to bari na faɗa ma ka gaskiya auren Nadra da za mu aura ma ka gata muka yi ma ka, ka rubuta ka ajiye wata rana sai ka zo ka durƙusa kana yi ma na godiya, sannan za ka ce gara ma da waccen fitananniyar ta gudu ta bar ka ta gudu. Ka ga waccan da ta gudu masifar, girman kai, isa da gadara, sannan ga shegen taurin kai, ko ka aure ta da ƙyar za ta yi ma ka biyayya saboda ko anan gidan ba ta ganin kowa da gashi sam ba ta san darajar mutane ba. Amma yanzu Allah ya raba ka da ita za ka auri mai hakuri juriya da hangen nesa, uwa uba ilimin addini da tarbiyya."
Shi kam gabaɗaya Fahad ba ya ma gane me suke faɗa, don hankalinsa da tunaninsa na can wata duniyar ne daban. Ya kasa gane dalilin da zai saka Sidra ta aikata haka.
Muryar Abba ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya lula.
"Fahad ban yi ma ka tayin auren Nadra ba sai da na tabbatar da cewa na ma ka sakayya ne akan abin da Sidra ta yi ma ka, in dai har za ka iya zama da Sidra zaman aure to ina mai tabbatar ma ka sai ka fi jin daɗin zama da Nadra akan Sidra. Amma ba zan takura ma ka ba idan har ba ka son ka aure ta shi kenan mu bar maganar kawai Allah ya haɗa kowa da rabonsa na alkhairi."
Shiru ya yi yana nazari shi dai gaskiya ba ya jin son Nadra a Zuciyarsa. Kuma rayuwarta da ra'ayinsa ya sha banban da nata, shi ya fi son wayayyun mata masu aji kamar Sidra, ita kuma Nadra ga ta nan kamar wacce ba ta waye ba, shi tun da yake ma bai taba ganinta babu hijabi ba. Kullum cikin hijabi ko a cikin gida ma saka hijabi take yi kamar wata mai takaba, wani namiji ma zai ga surar jikinta har ta ja hankalinsa ya ce yana son ta, sannan ita baƙa ce shi kuma baƙar mace ba ta burge shi.
"Ba ka ce komai ba."
Sai a lokacin ya daga ya kalli Abba da Umma wacew ta kasa cewa komai, don tun da ya shigo bai ji muryar ta ba, ya san tashin hankali ya yi ma ta yawa. Sannan suna da karamci da mutunci, yanzu indai bai amince ba kamar ya kunyata su ne , domin tabbas da kunya sun tara jama'a a ce an watse ƴar su ta gudu ranar aurenta. Wanann ciwon zai dade bai bar zuciyarsu ba domin sun kunyata a idanun mutane, shi bai damu da kansa ba don an fasa aurensa iyayen ta ne abin dubawa .
Cikin sanyin murya ya ce.
"Na amince."
Gabɗaya suka saki ajiyar zuciya tare da saka ma sa albarka.
Tashi ya yi ya ma su sallama ya yi ficewarsa.
Abba ya kalli Ƙanwarsa ya ce.
"Kada a sanar da Nadra wannan zancen sai bayan ɗaura aure."
"Me ya saka haka to Yaya, tun da an ji ra'ayinta shi ma ya kamata a ki nata ra'ayin."
"Ba sai an ji ba, domin na san yarinya ce ita mai biyayya, ba ta taɓa tsallake magana ta ba, idan na ajiye kara na ce kada ta tsallaka ba za ta tsallaka shi ba. Ba ta da ra'ayi in da iyayenta muna so, don haka na hana a fada ma ta ne saboda tana da raunin zuciya, za ta shiga tashin hankali da damuwa wanda zai tona asirin abun da muka binne. A bar zancen akan cewa dama Nadra ce Amaryar ba Sidra ba, an yi mistake wajen saka sunan ne. Ko ita Nadra kada ta san cewa ba Sidra ta gudu ballantana hakan ya shafi walwalarta."
Jinjina kai Goggo Laraba ta yi ta fice daga part ɗin.
Kai tsaye ɗakin su Sidra da Nadra ta nufa, bakinta ɗauke da sallama.
Nadra tana waya da Ya Sayyadin ta, wato Mallamin su na islamiyya ke son ta suna son juna duk da cewar shi talaka ne, amma hakan bai dame ta ba.
Ganin Goggo Laraba ta ta ce.
"Zan kira ka Ya Sayyadi."
Daga haka ta katse kiran wayar tana kallon Goggon tasu.
_Ma'eesha_
Kallon Mallam Iro mijin Larai Dillaliya ta yi tana cewa.
"Mallam ina bukatar gidan hayan nan a yanzu ba sai Anjima ba. Amma gaskiya ina son na zaman mutum ɗaya ne kuma ya kasance akwai toilet da kitchen a ciki ."
"Hajiya idan na fahimce ki ginin zamani kike so ko? To gaskiya babu a unguwar nan. Gidan haya mai zaman mutum ɗaya da na sani akwai a ƙasa yaba can farkon layin kamar yadda na fada ma ki, sai dai ƙarami ne gidan, kuma ɗaki ɗaya ne tal ba barci bai da falo, sai kitchen a tsakar gida, toilet ma a tsakar gidan ba cikin ɗaki yake ba, kuma tsohon gida ne ba na zamani yadda kike so ba, idan dole sai ba zamani sai dai ki je ki nemi manyan dillalan gidan haya."
Cikin gajiya ta ce.
"Yanzu shi wanann da kake magana akwai a ƙasa nake so yanzu nan, amma ba na da kudin yanzu a ƙasa."
Kallon ta ya yi ya tabbata ba ta yi kama da wacce za'a ce miliyan ma ya fi karfin ta ba ballantana dubu hamsin.
"Hajiya ai wanan ba matsala ba ne za ki iya transfer."
"Account ɗina ya samu matsala sai dai na cire kuɗi da ATM card amma ba na iya transfer, sai na je banki akan matsalar."
"Yanzu yanzu ya kike so ayi dubu hamsin ne za ki iya zama ?"
"Idan ba za ka damu ba, ina son ka ka bani gidan yanzu, in sha Allah zuwa gobe da rana ka zo ka karbi kuɗin hayar gidan. Don ba kuɗi ba kuɗi hannuna 4k ne kawai."
"Ba damuwa mu je na kai ku gidan ga shi can farkon layin ba nisa gida uku ne ya shiga tsakanin da wanann gidan da aka ba makaho ɗaki kyauta kin ce ba kya iya zama."
Yana gaba suna bin sa a baya har suka wuce gidan uku, a na huɗun ne ta ga ya tsaya a ƙofar wani karamin gida dake da kofar fale-fale.
Sakata kawai ya cire ya tura kofar suna bin sa a baya .
Ƙaranin gida ne sosai ba wani wadancan tsakar gida. Kuka tsakar gidan ma ƙasa ne ba'a shafa siminti ba, hatta ƙofar ɗakin ma na fale-fale ne sai karamin window shi na ƙofar fale-fale ne.
Barandar ƙofar ɗakin dai siminti ne sai cikin ɗakin siminti ne sai dai an shafa siminti a bango.
Daga tsakar gidan ga toilet nan karami shi ma siminti ne a ƙasa, sai kitchen wanda ba wai gina shi aka yi ba, fale-fale aka buga aka killace wurin ya zama kitchen, aka masa ƙofa.
Godiya ta yi ma sa ya fice yana ma su sallama.
Akwatunan kayanta ta kalla ta kalli ko ina na gidan, kasancewar lokacin sanyi muke ciki gidan duk ya yi ƙura.
Ga shi ita ba wani aikin kirki yake yi ba a gidansu .
Masu aiki ke gyara ma ta daki da gado su wanke ma ta toilet, ayi ma ta wanki da guga, girki kawai take yi shi ka Mahaifiyar ta ce ta ce sai ta koya, gidan mijinta wata rana za ta tafi ba kowane namiji ke cin abincin masu aiki ba.
Ta ina za ta iya rayuwa ba wanda zai yi ma ta waɗan nan ayyukan?
"Dole na je banki gobe na samu na yi transfer ɗin kuɗaɗen dake cikin account ɗin na, za su iya kai miliyan goma. Zan nemi gida kamar na miliyan uku na siya mai kyau da zan iya rayuwa a cikinsa. Sannan zan ja jari na fara sana'a ko da Naira miliyan biyar ne, saura miliyan biyu da zai rage ma sai na siya kayan daki da kayan kitchen da abinci ma su sauƙin kuɗi."
Tana cikin wannan maganar ta ji karar shigowar sako a wayarta, sai da gabanta ya faɗi. Tana dubawa ta ga messages ne daga banki, jikinta na ruwa ta duba in da ta ga miliyan goma da ke account ɗin ta an kwashe su duka.
Salati ta saka tare da sakin wayar ta faɗi ƙasa, dubawa ta yi akan guiwar ya tana riskar kuka.
Tabbas ta san cewa mahaifinta kawai ya san Pin ɗin ta na cire kuɗi, kuma Mamy ce ta karbi ATM card ɗin lokacin da ta shigo ta ga tana tattara kaya. Kenan Mamy ta tambayi Mahaifinta Pin ɗin ya fada ma ta kenan, sun kwashe kudin don sun san za ta iya transfer suka riga ta.
Cikin kuka ta ce .
"Innalillahi wa 'inna ilahir raji'un, Allah humma ajirni fi musibati wa'a khalifni khalifan min ha."
"Shi ke nan Mamy kin ruguza Mani rayuwa Allah ba zai bar ki ba. Allah ga ni gare ka ka da kai na dogara ya zuljalalu wal ikhram."
Kuka take yi sosai ana kiran sallar magrib ta ga ya fita da sandarsa yana dogarawa ya fice daga gidan ba tare da ya ce ma ta koma ba.
Ta dade tana kuka kafin ta mike tsaye tana goge hawayenta ta ce.
"Daina kuka Ma'eesha ki daina ɓata hawayenki anan zaluncin da aka yi ma ki, ki rungume ƙaddarar da ta zo ma ki Allah yana tare da ke. Kuka ba bali ba ne ki shirya fuskantar sabuwar rayuwar da kika tsinci kanki a ciki."
Ita kadai take magana kamar wata zararriya.
Fitilar wayarta ta kunna kasancewar akwai duhu kuma ba wutar nepa.
Waige-waige take yi nan ta lura ashe akwai rijiya a gidan can karshen gidan
Handbag ɗin ta ta duba ta ciro karamin bottle of water wanda ta shiga shagon saloon da shi ba ta sha ba.
Alwala ta yi sannan ta duba cikin akwatin kayanta ta dauki Ɗankwali ta shimfida ta gabatar da sallar magrib.
Tana cikin addu'a aka kira isha'i ta tashi ta gabatar.
Tashi ta yi bayan ta yi addu'a ta nufi kofar fita gidan hannun ta rike da handbag.
Wani shago dake kusa da gidan ta tambaye shi in da ake fitar da tsintsiya da faka ya ce wata bayarabiya ce kuma tun karfe shida take rufe shago ta wuce gidan.
"Cikin damuwa ta ce .
"Ba wani wajen kuma?"
"Gaskiya sai dai ki bari da safe ."
"Yanzu nake bukata wallahi."
" Daren nan kuma?"
Ya tambaya yana mamakin yadda ta dage.
"Eh yau muka tare a wancan gidan, ya yi ƙura dole sai na share kafin mu kwana a ciki."
"Allah Sarki, bari na ara Maki na shagona zuwa da safe sai ki dawo Mani da shi ko?"
"To na gode."
Ya mika ma ta tsitsiyar da faka ta amsa ta tafi.
Har ta fara tafiya ta dawo ta fiye ruwar roba gida biyu ta wuce.
Ko da ta koma ta samu makaho tsaye a tsakar gidan hannunsa rike da sandarsa.
Ba ta kalli in da yake ba ta shiga cikin ɗakin.
Yanar gizo-gizo ta fara cire wa a silin da bango, sai da ta kakkaɓe sannan ta share ɗakin ta kwashe dattin cikin faka tana kai wa waje can karshen bangon gidan.
Sannan ta fito ta share simintin barandar ƙofar.
Tsakar gidan ta fara share wa, sai dai kasancewar kasa ce ba siminti ba ƙura ya addababe ta ta fara atishawa da tari sakamakon kuran.
Gefen mayafin abayar dake jikinta ta sa tana toshe hanci da daya hannun daya hannunta tana shafa har ta gama.
Fita ta sake yi tana tari da atishawa ta koma wajen me shagon.
Ganin akwai mutane ta tsaya gefe tana jiran a rage, bayan an rage ta samu ta karasa bakin kofar shagon.
"Hajiya kin dawo?"
"Eh dama ina son ne ka bar mun tsintsiyar nan da zuwa gobe sai na siya maka wata, saboda zan wanke toilet da shi ne kuma bai dace na dawo maka da ita ba bayan na wanke toilet."
"Ba damuwa ki rike duka na bar ma ki."
"To na gode sosai."
"Ina son ka ba ni detergent da hypo ne."
Daidai lokacin da wani mai siyar da robobi yake dawowa daga talla.
"Dakata mallam."
Sai ya tsaya ta karasa wajensa ta siya madaidaicin bokintin roba na 1k ta detergent da hypo dama ta siye ruwa Roba biyu ta kashe 1k ta zuba su a roba ta koma cikin gidan.
Handbag ɗin ta ta duba tana tafiya ta ga 2k ya rage ma ta cikin 5k da ga bar gidan da shi
Cire kayan ta yi daga cikin bokitin sannan sai ta karasa wajan rijiyar duk da ba ta da tabbacin cewa akwai guga.
Ta haska torchlight na karamar wayarta ya ga an daure guga jikin karfe dake jikin murfin rijiyar.
Abinda ba ta taɓa yi ba a rayuwar ta jan ruwa daga rijiya .
Kamilalliyar muryarsa mai cike da kamala ta s ji ya ce.
"Me kike ta yi a daren nan ne?"
Kamar ba za ta amsa ma sa sai ta ce .
"Ruwan zan ka a rijiya zan wanke ɗakin ne da kuma toilet, don ba zan iya amfani da su a haka ba."
"Bari na taya ki jar ruwan, ki je dakin sai na kawo ma ka."
Kallon mamaki ta masa ta ce.
"Da wake idanun za ka gani ruwan kuka har ka kawo mani?"
Ganin bai yanka ta ba kuma kamar ransa ya ɓaci ta wuce ta ba shi wuri."
Laluben rijiyar ya yi har hannunsa ya sauka akan gugar ya janyo ta ya ji nauyi, don dama igiyar na ɗaure a jikin karfe guga na cikin ruwa .
Sau uku ya janyo ya cika bokitin.
Ya kai tana mamaki ya karba ta wanke dakin bayan ta zuba hypo da detergent.
Sau biyar yana ciki bokitin yana kawo wa tana wanke wa tana sharo ruwan a waje, tana kashewada faka har ta gama ta wanke barandar.
Daga nan kuma ta nufi toilet ɗin, nan ma siminti ne irin toilet na tsuguno na gargajiya.
Sai dai ya kawo ma ta ruwa bokati uku ta ɗauraye toilet ɗin bayan ta wanke.
Tana kallon ikon Allah makaho da ɗibar ruwa a rijiya, yana rike da bokitin a daya hannu yayin da daya hannun kuma yake dogara sandarsa ta makafi.
*KADUNA*
Bayan Nadra ta katse kiran wayar da take yi da Ya Sayyadinta.
Cikin ƴar damuwa ta ce .
"Goggo har yanzu ban san in da Aunty Sidra ta shiga ba, tun dazu nake zagaye gidan nan, ko dai ta fita ne?"
"Eh kada ki damu ta je gyaran jiki ne kuma a'ba za ta dawo da wuri ba."
"Allah ya dawo ma na da ita lafiya."
"Amin ya Allah. Yauwa ki tashi yanzu nan direba zai kai mu wajen gyaran jiki da kitso."
"Waye za'a yi wa?"
"Da ni da ke."
"Goggo ke ma kin san ba na son kitso, saboda gashin kaina yana da yawa sosai, tsayin kitson ma yana damuna."
"Sai da an yi shi don haka ba baƙi mintuna Talatin ki yi breakfast ki fito."
"Toh."
Ta fada duk da ba ta son kitso sai dai ta dunƙule kanta kanta ta cusa cikin hula ko Ɗankwali. Amma kasancewar ta ba mai musu ko gardama ba ne ya saka ta tashi ta nufi bathroom don yin wanka.
Bayan ta fito ne ta shafa man ta mai sanyin ƙamshi ta shafa, wanda yake karɓar baƙaar fatarta mai sheƙi. Ta shirya cikin kayan doguwar rigar material ta saka. Sannan ta sanya dogon Hijabinta ta dauki handbag da wayarta ta fice bayan ta saka flat shoe.
Wayar Sidra take sake kira har lokacin switch off.
Part ɗin mahaifiyar ta ta nufa saboda tana son sake duba jikinta. Sai dai an fada mata Umma na part ɗin Abba. Kamar sa ta bi ta can sai ta fasa
Tana fitowa ta ga jama'a kowa na kallonta jama'ar dake falon dangin Abban ta ne.
Wata ma daga cikin su ta ce.
"Allah Sarki Nadra rabon dai ke za ki riga yar taki aure.?"
"Ni kuma ?"
Ta tambaya cikin mamaki. Matar za ta sake magana kenan sai Goggo Laraba ta dakatar da ita ta hanyar girgiza ma ta kai."
Hakan ya saka matar ta fahimci Nadra ba ta san da ita za'ayi auren ba.
Shagwaɓe fuska ta yi ta ce
"Goggo lalle kawai nake so jiya fa na je saloon aka gyara mun kai na "
Murmushi Gwaggo Halima ta yi ta ja hannun ta suka nufi ƙofar fita suka fice .
Direba ne ya kai su har shagon da Gwaggo Laraba ta sanar da shi
Bayan sun fita ya tsaya jiran su yayin da suka shiga.
Nadra ta zauna yayin da Goggo Laraba ta yi wa mai saloon maganar uzuri suna sauri kuma amarya ce za su je reception ne, take ta kira ɗaya daga cikin yaran aiki ta ta karasa yi wa wata lalle, ita kuma ta fara tsantsara wa Nadra lafiyyarnb zanen lalle mai dauker hankali.
*Maman Ihsan ce.*✍️
09065327995
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce ✍️
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page0️⃣4️⃣
Nadra ta zauna yayin da Goggo Laraba ta yi wa mai saloon maganar uzuri suna sauri kuma amarya ce za su je reception ne. Take ta kira ɗaya daga cikin yaran aikinta ta karasa yi wa wata lalle, ita kuma ta fara yi wa Nadra lafiyyarn zanen lalle mai ɗaukar hankali.
Kamar yadda ta nuna ba ta son kitson haka aka yi ba'ayi ma ta ba, sai sai gashin na ta ya sha gyara sai sheƙi da wani ni'imtacen ƙamshi take yi.
Abun da ya sake ba ta mamaki bayan na gama ma ta sai ta ga Mama Laraba ta ce su je ta shiga ciki za'ayi ma ta gyaran jiki.
"Mama wani gyaran jiki kamar wata Amarya?"
"Ai ke ƙanwar Amarya ce ya kamata duk abin za'a yi ma ta a yi ma ki?"
"Amma Mama ban taɓa jin in da aka yi haka ba."
Ganin za ta ba ta ma su lokacin kuma tana son su koma gida akan lokaci ya sa ka ta ce.
"Nadra ki shiga don Allah ana jiran mu."
"To Goggo Dinner da za'a yi ai sai bayan an ɗaura aure ne, karfe biyar aka..."
Ganin yadda Goggon nata ta tsuki fuska ya saka ta ja bakinta ta yi shiru, kasancewar tana da gudun ɓacin ran mutum.
Shiga ciki ta yi aka ce ta cire kayan jikinta. Aka ba ta wasu ƙananun kaya ta saka aka shigar da ita wani ruwa mai kumafa da ƙamshi.
Matar sai lallaɓa ta take yi tana cewa ban san har da gyaran jikin nan za'a yi ma ki ba da shi muka fara yi kafin muka yi lalle.
Ita dai ba ta ce komai ba sai faɗuwar gaba da take tsintar kanta a ciki.
_Makaho_
Sai da ya gama dibar ruwar yana daukar hannu daya da bokitin ruwa hannu daya da sandar dogarawa har ya gama.
Don sai da Nasara ta wanke banɗakin nan tas da detergent da hypo. Duk da cewar ba tile ba ne a toilet ba ne siminti ne.
Bayan ta gama ne ruwan karshe da ya kawo ta ajiye a banɗakin ta fito.
Duk abinda take yi hawaye bai tsaya daga tsiyayar da take a idanunta ba.
Kiran sallar isha'i ake yi don haka ya ce ma ta .
"Zan je masallaci."
Ba ta ce ma sa komai ba, shi ma bai jira cewar ta ba ya fice.
Tsayawa ta yi tana kallon ɗakin da take haskawa da wayarta, tana tunanin dakin zai dauki lokaci kafin ya bushe.
Kawatin kayanta ta buɗe ta ɗauki wani rigar sanyinta da yake da kauri ta san zai kashe ruwa, ta dauka ta dinga goge ɗakin har ya tsane ba ruwa a kasan simintin dakin.
Ɗankwalinta ta shimfida sannan ta fita ta ɗauro alwala ta fito ta gabatar da sallar isha'i.
Bayan ta idar ta tsaya ta yi addu'o'i tana kai kukanta ga Allah ya ba ta karfin zuciyar cinye wannan jarabawar.
Tana zaune ta ji ya yi sallama.
"Assalamu alaikum."
"Wa'alaiki Salam."
Ya dinga lalube har ya ji ɗakin sannan ya shiga bayan ya cire takalminsa a waje.
Shiru ne ya biyo baya har tsawon mintuna biyar ba wanda ya yi magana a cikinsu.
Maganar zuci da take yi ya fito fili ba tare da ta sani ba.
"Mamy ba zan yafe ma ki ba, kin aurar da ni in da kike ganin zan tagayyara, kin san cewa rayuwata za ta iya inganta ta hanyar amfani da kuɗaɗena. Kin amshe ATM card kin je kin kwashe kudint.
Makaho ya gyara tsayuwar sa tare da jingine sandarsa a jikin bango ya ce.
"Ba lallai sai ta ATM card kawai ba, ta yi multiple withdrawal (cire kuɗin sau da yawa a ATM daban-daban. Ko ta yi transfer ta amfani da USSD (*737# *901# da sai sauran su saboda ta san Pin ta samu damar yin hakan. Ba zai yiwu ta fitar da miliyan goma a ATM lokaci guda ba amma a cikin awa biyu za ta iya gama komai . Don idan har lissafi na ya yi daidai lokacin da kika fahimci ba kudin a cikin asusun ki an yi awa biyu da barin mu gidanku. Ta kwashe kudin ne ta hanyoyi daban-daban (ATM + Transfer kasancewar ta san Pin da bayanan asusun. Saƙonnin bankin sun nuna cewa kuɗin sun fita ne ta hanyoyi daban-daban a cikin awa biyu duk da sahihin Pin?"
Da mamaki take kallonsa kafin ta ce.
"Saƙonnin bankin sun nuna mani cewa ba ciro kudin aka yi ba, an kwashe kudin ne ta USSD da canja wuri (transfer) a cikin awa biyu duka da sahihin Pin."
Mamaki ya kama Ma'eesaha ta ce.
"Ya aka yi ka san irin waɗan nan tsarukan na banki?"
"Ba abin mamaki ba ne, don ni ma wasu na ji suna fira ina kwance a masallaci ina jin su."
"Su waye?"
" Da wani idanun zan gane su? Wata rana bayan an sallame sallah ɗaya yake faɗa wa wani an kwashe ma sa miliyan goma ta hanyar amfani da ATM card na shi to wannan da aka fada wa ya fadi bayanin nan da na maki."
Shiru ta yi dai tana kau da idsnun ta daga kallonsa, ita babban damuwar ta yadda idan Mallam Iro ya zo karɓar kudin haya wani bayani za ta ma sa kan dubu hamsin, bayan ya ma ta taimako a daren nan ba ba su gida. Su zauna.
Ganin ga lokacin na tafiya kuma tauna ya addababe ta ne ga karfe tara da ta yi ne ya saka ta mike tsaye ta ɗauki handbag ɗin ta sauran 2k ɗin da ya rage ta dauka ta rasa me za ta siyo da za su ci a daren.
Ita kanta ta san 2k ya yi kadan ya siya ma ta irin abincin da za ta ci ballantana ga makahon mijinta. Kuma idan ta kashe kudin duka da me za su yi breakfast da safe?
Don haka ta ɗauki ɗauki 1k ta fita da shi sannan ta bar 1k a cikin handbag ɗin ta.
Wajen me shagon dake kusa da gidan ta nufa, yanzu ma yana da jama'a. Don haka sai ta jira daga gefe har aka rage.
"Mallam nawa ne coke na roba?"
"Hajiya ɗari huɗu da hamsin ne."
Shiru ta yi idan ta siye guda biyu kudin ba zai isa ba, don haka sai ta ce.
"Ka bani guda ɗaya nawa kake siyar da bread. Biredin nan akwai na dubi daya da ɗari biyar, akwai na dubu daya da ɗari uku akwai na dubu daya, akwai na ɗari biyar dai kuma karamin nan na ɗari uku."
"Ka bani na ɗari biyar ɗin."
Ta amsa bayan ya saka ma ya a leda ya ba ta canjin Naira hamsin.
Tana tafiya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 49