sannan ta bashi wayar?"
"Cash zan baki ko na yi na ki transfer?"
"Cash za ka bani."
Ya ba ta bandir na dubu ɗari guda biyar ta karba ta zuba a handbag suka fice da mai nape
Bayan ya tayar da nape ya ce
" ina za mu je."
"Kasuwa za ka kai ni?"
"Wace kasuwa?"
"In da zan samu kayan ɗaki ma su sauƙin kuɗi. Kamar katifa, pillow da sanin gado leader carpet da labulaye sai sauran kayan aikin da ba'a rasa ba."
"Okay Hajiya Allah ya kai mu lafiya."
Da haka ya dauki hanyar da zai kai Ma'eesha ta yi siyayya.
_Nadrah_
Tafiya take yi kamar mai jin tsoron ƙasa, don tsakanin ya ba ta wuyar tafiya, bugu da kari ga kayan jikinta da ta kasa saukewa a cikinsa.
Abun ya hadu ma ta biyu ga kaya ga takalma, duk sun takura ma ta.
Hannayen ta biyu ta saka tana kare ƙirjinta wanda rigar aka yi shi da gidan breast. Karon farko kenan a rayuwarta da za ta fita babu hijabi ga shi kayan ba yadda take so ba.
Ta cikin mirror Fahad ya kalli yadda take kare ƙirjinta tana tafiya kamar za ta faɗi, gajeren tsuki ya ja yana mai jin takaicin yanayin yadda take yi don za ta iya kunyata shi a gaban jama'a, ga manyan baƙin da abokansa da suke masa kallon wayayye mutum mai ji da kai da aji.
*Mamman Ihsan ce*✍️
09065327995
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce ✍️
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page0️⃣7️⃣
Ta cikin mirror Fahad ya kalli yadda take kare ƙirjinta tana tafiya kamar za ta faɗi, gajeren tsuki ya ja yana mai jin takaicin yanayin yadda take yi, don za ta iya kunyata yi don za ta iya kunyata shi a gaban jama'a, ga manyan baƙin da abokansa da suke masa kallon wayayye mutum mai ji da kai da aji.
Dauke idanunsa ya yi ransa ya na ɓaci, a hankali take tafiya har ta karaso wajen motar.
Da sauri Direban ya fito ya buɗe mata murfin bayan motar ganin za ta buɗe.
Kallonta ta yi ya gaishe ta da cewa.
"Ina wuni Madam?"
"Kai kawai ta jinjina ma sa ba tare da ta iya amsa wa ba."
Shiga bayan motar ta yi bakinta ɗauke da sallama.
"Assalamu alaikum."
Idanunsa na kan wayarsa bai kalle ta ba ya amsa sallamar ciki-ciki wanda ita kanta ba ta ji ya amsa ba shi kadai kawai ya ji kayansa.
Bayan ta zauna ne direban ya rufe murfin motar, ba abinda ke tashi a motar sai sanyin A.C da ƙamshin turarensa.
Duk da cewar tana cikin ɓacin rai da takaici amma haka.n bai hana ta ta gaishe shi ba."
"Ya Fahad ina wuni?"
Kamar ba zai amsa ba har ta fidda ran zai amsa sai ta ji ya amsa da.
"Kina lafiya?"
Ta amsa da Alhamdulillah kanta a sunkuye.
Direban ya ja motar suka bar gidan.
Sun ɗan fara tafiya ta kalle shi ta ce.
"Ya Fahad?"
Sai a lokacin ya ɗago kai ya kalle ta ba tare da ya amsa ba.
"Na ga kamar kana cikin damuwa ko?"
Bai ce ma ta komai ba sai dai ya ɗauka yadda ya saki ransa ba wanda zai gane yana cikin damuwa, tun da ita da yake ma ta kallon ba ta da wayau ta iya karantar yanayinsa ashe tana da wayau. Kuma kowa zai iya karantar yanayinsa. Kallon kayan dake jikinta ya yi wanda ya siya wa Sidra ne last week tare, hatta sarƙar gold ɗin da su warwaro da ɗan kunnen duka seti ne ya siya ma ta.
Bai ce ma ta komai ba kuma kamar bai ji tambayar da ta yi ma sa ba.
Sun yi nisa da tafiyar ne duk ta damu da kayan da za ta shiga cikin jama'a da shi, ta kalli jikinta ta fara maganar zuci wanda ya fito fili ɗin ba ta yi don ya ji ba.
'Mtswww, wannan wane irin iskanci ne ba in da zan fita da kayan nan na shiga cikin jama'a, don ni ba ƴar iska ba ce. Haba sai ka ce ba ƴar musulma ba Aunty Sidra ta zaɓo kayan nan a matsayin kayan da za ta shiga jama'a bayan an ɗaura aure tana matar aure? Kodayake ba laifn ta kaɗai ba ne har da laifin shi Mijin nata ta ya ya Yaya Fahad zai yarda ya siye wannan kayan matarsa ta saka sai ka ce wanda baya da kishin matarsa, zai so a kalli matarsa a haka cikin wanann shigar, kalli rigar ko hannun arziki babu ga ta an yi gaban rigar kamar na bra duk siffar kirjin mace a bayyane yake. Wallahi da na san har da wannan tsinannen Dinner party za'a ce wai na je a madadinta da islamiyya na wuce. Na samu lada da wannan bidi'ar da zan je. Ga Aunty Sidra har yanzu ba ta dawo daga gyaran jikin ba ta je da daɗe duk ita ta jawo Mani wannan abun. Idan Allah ya kai ni ranar aurena da Ya Sayyadina walima kawai za mu yi ayi lectures kan aure mallamai su yi wa'azi amma ba wannan bidi'ar. Ko ya Sayyadina idan ya ganni haka sai ransa ya ɓaci.'
Fahad idanunsa na kan wayarsa ne amma duk maganar da take yi a kunnensa, ita ba ta san a bayyane ta yi maganar ba. Kuma yanzu ne ya tabbatar da cewa iyayenta ba su faɗa ma ta cewa an ɗaura auren da ita ba, to amma ai da sun sanar da ita musamman da suka san akwai saurayin da take so wato Ya Sayyadi. Shi kansa Fahad ya san Ya Sayyadi kuma Ya Sayyadi ya san shi shi ma. Saboda sau tari idan ya zo wajen Sidra ya kan ga Ya Sayyadi tare da Nadra kullum cikin jallabiya yake da hula taɓa ni ka ji hadisi yana zuwa ne da tsohon babur nasa kullun. Har Sidra ta yi ta faɗa wai me na sama zai ci ballantana ya ba na ƙasa Nadra ta rasa wa za ta so sai wannan abar da ba lallai ya iya ɗaukar ɗawainiyar ta ba, in ban da kuɗin Laraba da ke kai wa islamiyya me yake da shi. Ta tsayar da mai kuɗi ta aura cikin ma su son ta sai wannan ya Sayyadin mai gemu kamar na bunsuru, har wata rana Fahad ya yi Sidra faɗar abun da take yi wa Ya Sayyidi.
Yana tsaka da tunanin baya wayar ta fara ringing, sai dai har ta katse bai ɗaga ba.
Aka sake kiran ɗayar wayar nan ma bai ɗaga ba. Ta na kallonsa ta gefen ido a zuciyarta ta ce.
"Sun haɗu sun dace, don ita ma Sidra haka za'a dinga kiran wayarta ba za ta ɗaga ba sai ta ga dama.
Tana ganin an kawo wajen gabanta ya tsananta faɗuwa. Ita ma za ta iya fita a haka ba. Musamman da ta hangi cikar da aka yi, don ma ba ta shiga ciki ba.
Kowa white and black ne maza da mata.
Motar na tsaya wa sai ga mutane sun nufo motar ma su ɗaukar photo da ma su ɗaukar video wasu da wayoyinsu wasu da Camera 📷. An tsaya ana jiran fitowar Amarya da ango.
_Ma'eesha_
Mai keke napep ɗin bai dire ta a ko ina ba sai gaban wasu shaguna dake bakin titi.
"Hajiya yanzu ba'a fito a kasuwa ba, don sai zuwa karfe tara ko goma idan kina son wasu kayan da kike so za ki iya samun su a nan, idan kin kai su gidan sai mu dawo na kai ki kasuwa."
"Okay."
Ta faɗa tana fitowa shi ma ya kashe keken ya zare key sannan ya bi bayanta.
"Shagon katifa ne da su pilows ake siyarwa, ta siye madaidaicin katifa ba mai girma ba, ta siye pillow guda biyu ta biya kuɗin, ma keke napep ɗin ya ɗaure katifar da pillow ya ɗaura a keke nape ɗin, sannan ta shiga shagon dake kusa da wanda ta siye katifa. Ta siye zanin gado kala biyu da labule guda biyu, sannan ta siye leader carpet, saboda ta san shi ne mai sauƙin kuɗi.
Za su wuce sai ta ga shagon dake kusa da in da ta yi siyayya.
Ana siyar da kayan kitchen.
"Ka ga bari na shiga can na duba abind da zan buƙata."
"To Hajiya."
Daga nan ta nufi cikin shagon don ta ga kayan da take buƙata.
Tukunya guda biyu ta cire gefe mai ɗan girma da karami, sai ta siye tukunyar suya sannan ta siye set ɗin food flask mai guda uku a kwali ta siye cokular cin abinci guda shida na cin taliya wato fork guda uku, ta siye plate na cin abinci ma su fadi guda huɗu ma su zurfi ƙanana guda hudu da service spoon, sai babban tire sai kofin shan ruwa huɗu na shan shayi ko kunu guda huɗu. Ta siye rariya da cikakin girki
Lissafi aka yi ma ta ta biya kuɗin sannan mai napep ɗin ya ɗauki kayan da ta siyo ya saka a bayan keken.
Sannan ta tuna da robar zuba ruwa wato duram ɗin roba ta siye da bokitin roba guda biyu da baho madaidaita biyu da robar ɗiban ruwa. Ta gama abinda za ta siya
ta yaya wannan bangaren.
Sannan ta shiga ganin keken ya ya cika da kaya yawa.
"Mallam mu je ka kai ni gidan idan na ajiye sauran kayan sai mu dawo ka kai ni in da zan siye kayan abinci sai ka mai da ni gida ."
"To Hajiya Allah ya kai mu lafiya."
Da Amin ta amsa , daƙyar da ita gane layin, don dama dai ta san sunan unguwar, amma layin ne ya ba ta wahalar gane wa sakamakon lungu ya yi yawa a unguwar.
A ƙofar gidan ya sauke ya tsaya sannan ya fito daga ciki yana fito da kayan.
Kasancewar ba kaya ma su nauyi ba ne, ya saka yana ajiye wa tana ɗauka tana kai wa cikin gidan.
Bakinta ɗauke da sallama ta shiga cikin gida.
Daga cikin ɗakin ta ji muryarsa ya amsa ma ta da
"Wa'alaiki Salam warahmatullah."
Ya fito rike da sandarsa ta jagora, sai dai ya canza kayan jikinsa ba wanda ta bar shi da shi ba ne, wannan farare ne su ma yadi ne ma su sauƙin kuɗi wanda aka cewa Yi shirunka maraya.
"Ma'eesha kin dawo ne?"
"Eh."
Ta fada tana ajiye katifar wanda aka ɗaure su da filo a hannunta a saman barandar.
Komawa ta yi ta ɗako sauran kayan, sau uku tana fita tana kwaso kayan kafin ta gama ta kalle shi ta ga ya yi tsaye yana rike da sandar jagoransa. Kansa a ƙasa kamar mai karantar wani abu.
"Ban gama siyayyar da zan yi ba, mai napep na jira na a waje, zan koma na karasa sai na dawo na nema ma na abun da za mu yi breakfast. Don yanzu karfe goma ake nema, ni dama ina kai karfe goma sha ɗaya ko sha biyu ban yi breakfast ba, don haka kai nake tunani."
Murmushi mai ciwo ya yi tare da cewa.
"Ma'eesha ke nake ji da sabuwar rayuwar da kika tsinci kanki a ciki, ni kada ka damu da ni, wata rana sau ɗaya nake cin abinci a rana. Ko ina jin yunwa ba na da mai bani abinci, sau ranar da Allah ya saka naje gidanku idan mahaifiyarki ta bani nake ci, duk da ta ce na dinga zuwa kullum ina cin abinci ba na iya wa, sai dai duk sati nake kai mata ziyarar juma'a wato duk ranar juma'a, ranar ne nake ci na ƙoshi , wata rana ai ke take saka wa ki zuba Mani wanda zan tafi gida da shi, Allah ya jiƙanta da rahama ya sa aljanna ce makomarta, halinta nagari ya bi ta."
Kuka ne ya suɓuce wa Ma'eesha tuna mahaifiyar ta da Fahad ya yi ma ta, ji take ina ma tana da dangin mahaifiya da can za ta tafi ko ta samu sassauci abinda yake ranta. Ita kanta ba ta san yaushe ne za ta daina kukan mijin marainiya ba, amma tana ji a ƙasan ranta wata rana za ta yi dariya.
Sallamar mai daidaita sahun dake jiranta ya sa ta goge hawayenta da sauri ta fice daga gidan ba tare da ta sake magana ba.
"Ka yi hakuri na bar ka kana jira na ko?"
"Ba matsala."
Ya fada yana yi wa keken burki suka bar kofar gidan.
Ganin tana ƙwalla ta cikin mirror yake kallonta ya ce.
"Hajiya lafiya?"
Sai sa lokacin ta lauba fuskarta ta ji hawaye ke bin fuskarsta
Da sauri ya goge.
"Ba komai Mallam."
"Anya kuwa ba komai?"
"Eh."
"To na ga kina kuka ne duk na damu."
Murmushin takaici ta yi tana cewa.
"Kawai na tuna da mahaifiyata ce."
"Allah sarki ki Allah ya jikanta da rahama."
"Amin na gode."
"Rayuwa kenan Allah ya ba mu guzurin cin ma su."
"Amin ya Allah."
Ta fada tana kau da kai gefe tana kallon titi.
Still hawaye ne dai ke yi ma ta zarya wanda duk yadda taso dakatar da hawayen ta kasa hakan .
"Yana kallonta ta madubi ya ce.
"Aunty na ki yi hakuri Allah ya jikanta."
Ai kamar ya ce ta ci gaba dai ji ta yi ta fashe da kuka mai tsuma zuciya wanda tun daga kasar zuciyarta take jin ƙuna da raɗaɗin rasa mahaifiyarta, ga wani sabuwar rayuwa da ta tsinci kanta a ciki mai cike da ƙalubale, haƙika mutuwar mahaifiyarta ya durƙusar da duk wani motsi nata, ya gurguntar da tunanin gobenta. Wannan sabuwar rayuwa da ta shiga tamkar hanya ne mai cike da kwazazzaba da ƙayoyi. Jin yadda take kuka kamar za ta shiɗe ne ya saka hankalinsa ya tashi ya yi parking gefen hanya .
*Mamman Ihsan ce*✍️
09065327995
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce ✍️
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page0️⃣8️⃣
Ai kamar ya ce ta ci gaba sai ji ya yi ta fashe da kuka mai tsuma zuciya wanda tun daga kasar zuciyarta take jin ƙuna da raɗaɗin rasa mahaifiyarta. Ga wani sabuwar rayuwa da ta tsinci kanta a ciki mai cike da ƙalubale, haƙika mutuwar mahaifiyarta ya durƙusar da duk wani motsi nata, ya gurguntar da tunanin gobenta. Wannan sabuwar rayuwa da ta shiga tamkar hanya ne mai cike da kwazazzaba da ƙayoyi. Jin yadda take kuka Kamar za ta shiɗe ne ya saka hankalinsa ya tashi ya yi parking a gefen hanya.
Ya juya ya kalle ta sai ya ga ta jaɗa kanta guiwarta, wato ta ɗora ƙafarta tana cigaba da kuka.
"Hajiya ki yi hakuri don Allah addu'ar ki take buƙata ba kuka ba. Domin wannan kukan ba zai amfane ta ba."
Ɗago kanta ta yi ta goge idanunta sa suka yi jajir sannan ta ce.
"Mu tafi."
Kunna nape ɗin ya yi sannan ya fara tuƙi a hankali don shi ma jikinsa ya yi sanyi sosai, yana son ya tambaye ya amma yana tsoeon amsar da za ta ba shi. Musamman da ya ga wayar da ta siyar ya san wace irin waya ce. Sannan ga shi yanzu bayan ta siyar da wayar irin kayan da take siye, kuma yadda ya ga take yi kamar ita ce za ta yi amfani da kayan, ga gidan da ta kai kayan sam gidan bai dace da ita ba.
Har suka ƙarasa kasuwa ba wanda ta sake yin magana s cikinsu.
Bayan ya yi parking a In da ya dace ne ya zauna ciki. Ta kalle shi ta ce.
"Mallam ko za ku je ka taimaka ma ni ban taɓa shigowa kasuwar ba, don ban san ta ina zan bi da ake siyar da kayan abinci kamar su shinkafa da sauransu."
"Okay mu je na nuna ma ki na ha kamar ke baƙuwa ce a garin."
Ya yi maganar ne don ya tabbatar da abun da ke ransa, ita kuma ba ta ce ma sa komai ba. Har suka ƙarasa wani layi.
"Yauwa Hajiya ga wani shagon za ki iya samun komai a ciki."
"Toh na gode Allah ya saka da alkhairi."
Da Amin ya amsa sannan suka shiga cikin shagon da sallama a bakinsu.
"Assalamu alaikum "
Wa'alaiki Salam warahmatullah."
Cewar wani matashin saurayi dake kusa da su. Don shagon babban shago ne mutane biyar ke sigar da kaya a ciki har da Alhaji me shagon yana zaune kan kujera yana lissafa babban calculator.
Matashin saurayin ya ce .
"Me da me za'a kawo?"
Ya yi maganar yana ajiye ma ta plastic chairs ta zauna tana ma sa godiya.
Bayan ta zauna ta ƙare wa shagon kallo dake da masu siyen kaya a ƙalla za su kai mutane goma.
"Ka bani karamin buhun shinkafa, da katon ɗin taliya da makarani kowane guda ɗaya."
Ta yi maganar tana nuna ma sa kalar wanda take so.
Ya dauko shi kafar da taliyar da macaroni ya ajiye ma ta .
"Ka kawo ma Ni buhun semolina da kuma cus-cus."
Ta ce ya kawo ma ta wani madaidaicin galan manja da man gyaɗa, sai wake mudu biyar.
Sannan ta saka shi ya kawo ma ta ledar Maggi know da kuma star, sai gishiri da su kayan ƙamshi . Sannan ta ce a kawo kwalin indomie.
Total aka yi ma ta ta biya sannan mai napep ɗin ya ɗauki kayan tana bin sa a baya rike da wanda za wanda za ta iya ɗauka. Suka nufi wajen keke napep ɗin.
Bayan sun saka kayan a baya ne ya kalle ta ya ce
"Ki zauna a ciki bari na kwaso sauran kayan."
Ba musu ta shiga ta zauna ya koma ya kwaso sauran kayan , sau biyu yana ki komawa.
A na karshe sai ga shi ya dawo tare da Alhajin nan mai shagon, wanda da dukkan alamu shi ne mamallakin wannan shago.
Washe ba ki ya yi ma ta yana cewa.
"Ƴan mata ya za ki tafi bayan kin sace ma ni zuciya."
Kallo ɗaya ta yi ma sa ta dauke kai.
Murmushi ya yi tare da cewa.
"Da alama wannan ƴan matan akwai jin kai, to a jiƙaina ko lambar waya a bani ba "
Kallon mai napep ɗin ta yi ta ce.
"Mallam mu tafi ma na."
"Don girman Allah ki saurare ni."
"Matar aure ce ni."
Ta fada a takaice.
"Subhanallah don Allah ki yi hakuri ban sani ba."
Daidai lokacin mai napep ya ja suka bar wajen.
"Yauwa na mance ina buƙatar Gas ƙarami kamar 3kg."
"To Hajiya zan kai ki in da za ki samu, ko za ki hada da murhun gawayi saboda yau da gobe wata rana Gas zai kare ba za ki iya fita ba sai ki zuba gawayi ki cigaba."
Ita dai ba ta san yadda za ta yi amfani da shi ba, amma ta amsa mai da to.
Ya kai ta ta siye Gas, a wajen da ta siye aka cika ma ta shi da Gas.sannan ya kai ta inda ta siye murhun gawayi da kuma wani ɗan ƙaramin buhu da aka zuba gawayi, ta siye ya ɗauka ya saka ma ta suka bar wajen.
"Mallam ina zan samu kayan miya?"
Daga cikin keken ya nuna ma ta . Ya zauna yana jiranta.
Ba jimawa ta dawo da manyan ledoji guda biyu cike da kayan miya, sannan ta kalle shi ta ce.
"Bari na siye dankalin turawa a can ."
Ta juya ta siye dankalin turawa da ƙwai kiret daya sannan ta dawo, ya ja napep suka bar wajen."
"Yanzu ina za mu je?"
Gida Mallam za ka kai ni "
_Nadra_
Ganin yadda ka zagaye motar da take ciki sannan ga ma su ɗaukar photo da video sun zagaye su ne ya saka ta kasa yunƙurin fitowa .
Sai sake noƙewa take yi ba ta ma da niyyar fitowa.
Direbansa ne ya zagayo ya bude ma sa bayan motar, a hankali ya ziro ƙafarsa ɗaya waje, sai da ya ɗauki seconds kafin ya dake ziro da ɗaya kafar waje. Sannan ya fito cikin takunsa na ƙasaita fuskarsa ba yabo ba fallasa.
Daidai lokacin Aunty Rahama ta karaso wajen tana Murmushi.
Da ido ta ma sa alamar ya riko hannunta su karasa wajan a tare.
Zagayawa ya yi gefen da take ya yi ƙasa da kansa saitin fuskarta ya yi magana ta yadda ita kadai za ta ji.
"Ko sai an fito da ke ne, ka da ku kuskura ko da wasa ki yi mani gidadanci anan, na san ki kamar bagidajiya haka kike, ina mamakin yadda zama da Sidra bai saka kin waye ba. Nan cikin jama'a ne akwai manyan mutane nan da suka halarci wannan taron har daga ƙasar waje wasu suke, ka da ki kunyata ni, be careful."
"Ƙwalla ce ta cika ma ta idanu."
"Kada ki mani kuka anan."
Ya faɗa yana ciro hankaci cikin aljihun Suit ɗin sa ya goge ma ta ƙwallar.
Tafi wasu suka hau yi don an ɗauka kalaman soyayya yake yi ma ta musamman da fuskarsa ke daf da tata.
Tana fitowa daga cikin motar aka fara watsa ma su wani fure mai ƙamshi.
"Ma sha Allah."
Aunty Rahama ta fada lokacin da ta yi tozali za Nadra.
Kasa ɗaga ƙafa Nadra ta yi sakamakon hangen jama'a da suke a cike a wajen, ga wasu na ɗaukarta video da photo.
Ganin ta coge tana tunani ya saka ya sakala hannunsa cikin nata. A bazata ta ji lalluasan hannunsa cikin nata hannun.
"A'uzubillahi minash a
shaiɗani rajim."
Ta furta tana kallon sa a razane, shi kam bai kalle ta ba yana kallon tarin jama'ar da bai yi zaton gani ba.
Koƙarin kwace hannunta take yi ta kasa.
Saboda riƙon da ya yi ma ta ba na wasa ba. Ba yadda ta iya haka ta dinga binsa kamar Raƙumi da akala. Sai dai kamar za ta yi kuka cike da shagwaɓa take cewa.
"Yaa Fahad please ka sakar ma ni hannu ba kyau haramun ne namiji ya taɓa wacce ba maharramarsa ba, ba Aunty Sidra ba ce ni ce fa Nadra haramun ne."
Bai kalle ta ba ya yi kamar baya jin ta. Ana ta watsa ma su fure me ƙamshi ana ma su feshi.
Jin yadda idanun mutane ke yawo a likita ya saka ta fara kokare kare jikinka ta hanyar ɗan shigewa jikinsa ta yadda ba za'a ga ƙirjinta da take ɓoye wa ba, wanda bai tsaya kusa da su ba zai ɗauka ta haɗa jikinsa da nata ne, amma a zahiri sun dai yi kusanci amma jikinsu bai haɗu ba, sai dai har lokacin yana rike da hannunta cikin nasa.
Kuma yana tafiya a hankali ganin yadda take tafiya ita ka sai yake bin ta a haka.
MC na bayani yana sanar da idowar amarya da ango ga wani sanyayyen kiɗa na tashi a hankali.
Har suka ƙarasa wajen zamansu suka zauna , ana ya saukar su photo.
Kowa dake wajan kayan jikinsa White and black ne maza da ma ta.
Taro ya kai taro jama'a da ba'ayi zato ba sun zo.
Waƙar auren na tashi sai dai abin da ya ba Fahad mamaki ya san dai waƙar auren da sunan Sidra aka rera, amma yanzu sai ya ji sunan Nadra ne ba na Sidra ba, duk da wakar ɗaya ce sunan kawai aka canza, bayan shi ba abinda aka canza daga sunan iyaye da dangi duka suna nan. Fahad ya san wannan ba aikin kowa ba ne sai Aunty Rahama. Ita ce za ta saka ayi wannan a kankanin lokaci.
Kamar yadda ka tsara haka aka yi aka kira abokin ango ya zo ya bayar da tarihin rayuwar ango da halayyarsa.
Daga nan aka bukaci ƙawar Amarya ta fito ta ba da tarihin rayuwar Amarya. A nan ne Nadra ta daga kai saboda ta san saboda ta san ba wata ƙawar da take da ita da ya wuce A'isha Humaira kuma ba ta zo wajan nan ba. Dama Khadijah ƙawar Sidra ce za ta bayar da labarin Sidra. Yanzu kuma tun da an fasa auren da Nadra ai ba zai yiwu ƙawar Sidra ta zo ba.
Ga mamakinta sai ta ga Khadijah ƙawar Sidra ta fito ta zo ta tsaya. Haɗa idanu suka yi ta sakar ma ta murmushi. Sai dai Nadra ta kawar da mamaki ne lokacin da ta tuna cewa ai labarin Amarya za ta bayar amarya kuma Sidra ce, dole za ta bayar da labarin Sidra, dama duk cikin ƙawayen Sidra ba wacce hankalin ta ya kwanta kamar Khadijah. Don tana ba ta shawara na kwarai tare da fada ma ta gaskiya. Shi ya sa ba wuya sun yi faɗa ita da Sidra saboda fadar gaskiyarta.
Cike da mamaki Nadra take kallon Khadijah ƙawar Sidra, jin ta ta ambaci sunan ta ba sunan Aunty Sidra ba kila tarihin rayuwar Nadra take bayar wa .
Sai dai ba ta ce komai ba kuma ba ta kawo komai a ranta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 49