da ba ta da isasshen kuɗi amma dole ta cire dubu goma ta siya ma sa karamar waya, da sim card mai register
Ka san me ya sa na siya ma ka waya?"
"Ban sani ba don da wani idon zan yi amfani da shi?"
"Ai bai da wahalar koya, ni zan dinga kiran ka idan ba ka gida lokacin cin abinci idan ya yi ba ka dawowa Sai ka zauna da yinwa shi ya sa na siya ma ka da zaran na gama garki zan Kira ka sai ka zo ka ci abinci. Zan nuna ma ka wajen da za ka danna da zaran ka ji ƙara sai ka laluba ka danna wajen ka kara a kunne daga nan za ka ki murya ta."
Bayan sun tsallaka titi kasancewar ba wani nisa da unguwar su.
Suka kama hanyar dawowa gidan wayar da ta siya masa na cikin jakarta, tana tuna mutumin da ta ga suna daukar su photo a waya ɗazu su waye su me ya sa suke bibiyar su?
Daidai lokacin wayar ta ya soma ringing ta duba ta gani ƙawarta Nasreen ce.
Ta ɗaga tare da sallama.
Daga can bangaren ta ji Nasreen na cewa.
"Abdul ne zai yi magana da ke ta wayata tun da kin yi blocking ɗin sa."
"A kan me zai yi magana da ni?"
"Akan yana son ki cika masa alkawarin auren da kika yi ma sa, kuma dama shi ne ya dace da ke ba wannan musakin ba."
A fusace ta ce .
"Nasreen za mu samu matsala da ke wanda ba za mu taba komawa kamar da can baya ba. Kuka ki ja wa shi wanda ya aiki ki kunne ya fita a sabga ta. Wani irin jahilci ne zai saka ya fara neman matar aure, ko mace na auren maza biyu..."
Maganar nata maƙalewa ya yi sakamakon ganin wato motar ta tsaya gabansu.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce ✍️
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page2️⃣4️⃣
Maganar nata maƙalewa ya yi sakamakon ya yi sakamakon ganin wato motar ta tsaya gabansu.
A hankali ya sauke glass ɗin motar yana sakar ma ta murmushi.
"? Yaya Jamil."
Ta furta cike da mamakin ganinsa a unguwar su, shi kuma tun ranar da Nasreen ta kira ta a waya bayan ta je gidansu ya so ya zo tare da Nasreen sai dai ba ta bashi damar hakan ba. Don haka ya matsala wa Nasreen akan ta kawo shi gidan amma ta ƙi sai dai ta yi ma sa kwatance.
"Ma'eesaha wancan ranar kin bar gida a cikin fushi kina kuka, na so ki tsaya ki saurare ni amma ba ki tsaya ba. Yanzu ina neman arzikin don Allah ki taimaka ku shigo na ajiye ki a gidanku idan ya so sai mu yi magana."
"Yaya Jamil ina ganin mutuncinka don haka ka bar nan unguwar kafin na saka yara su yi ta jifar motar nan sai sun farfasa ma ka gilashin motar."
Murmushi ya yi tare da da fitowa daga cikin motar ya kalle ta yadda ranta yake ɓace ya ce.
"Idan kin saka an fasa kanki kika yi wa Asara. Domin ɗaya daga cikin motocin da mahaifinki ya mallaka ne na ke amfani da ɗaya. Kuma sakin kanki ne cewa ke kaɗai ya mallaka a duniya. Yau idan ƙasa ta rufe idanunsa ya zama babu shi ke ce mamallakiyar dukiyar da ya mallaka babu wanda ya isa ya canza hakan. Ko Mamy mahaifiyata tuminin takaba akwai za ta samu, ni da Laila da muke Agola ba'a maganar mu. Don haka ki yi hakuri ki zo mu tafi gida na zo ne na ba ki haƙuri a madadin mahaifinki da mahaifiyata."
"Yaya Jamil na daɗe da rasa mahaifina yanzu ba na da kowa a wanann duniyar sai mijina shine fitila ta, domin la kira kowa kansa ya sani da rayuwarsa. "
Ta ji maganar tana damƙar hannun makaho za su fara tafiya ya sha gabanta da sauri ya ce.
"Ki tsaya ki saurare ni Ma'eesaha, kin ga ni ba ni na yi ma ki laifi ba mahaifiyata ce ta yi ma ki laifi kada laifinta ya shafe ni, laifin wani baya shafar wani Ma'eesha.
Sai a lokacin makaho ne ya yi magana ya ce.
"Ki bar shi ki ji da me ya zo?"
"Babu wani abun alkhairi da zai zo da shi, domin kuwa babu alkhairi a tattare da su. Daga ranar da mahaifiyata ta taimake su daga rana ta janyo su inuwa me suka aikata ma ta jefa ta a ranar suka..."
"Ya Isa haka nan Ma'eesha ki wuce mu tafi."
Kamar jira yake dama hannunsa na rike da nata ne.
Take suka fara tafiya yayin da mamaki ya cika zuciyar Jamil, wato duk tana daraja mijinta tun da har ya ba ta umarnin ta wuce su tafi lima take ta wuce ba musu ko gardama. Kenan hakan na nufin ta karɓe shi a matsayin mijin aurenta ne.
Jinjina kai ya yi tare da cewa.
"Ni ina can ina faɗi tashi wajan Daddy da Mamy don su raba auren ma don na yi zaton ba za ta taba yarda da auren ba, nayi zaton za ta saka ya sake ta don ta fi ƙarfinsa, amma sai na gansu tare da alama wani wajen suka Fito."
Shiga motarsa ya yi ya fara bin bayansu ta juyo ta kalli motar amma ba ta damu ba sai ta ci gaba da tafiyar da take yi.
Har suka isa ƙofar gidan ta ciro ɗan makulli daga cikin handbag ɗin ta ta buɗe.
Bayan ta buɗe ne ta ja hannunsa suka shiga bakinsu ɗauke da sallama.
Suna shiga daidai lokacin motarsa ta karaso .
Fitowa ya yi daga cikin motar yana ƙarewa gidan kallo yana jinjina wanan al'amari. Wai kamar Ma'eesha Ibrahim Khalil ce take rayuwa a cikin wanan akulikin gidan. Yarinyar da mahaifinta ke da manyan gidaje na alfarma a garin nan, mutumin da yake kyauta da gidaje da motoci wanda ko gidajen da ya raba wa masu ma sa aiki kamar direba maigadi da sauransu to mahaifin Ma'eesha ya siya ma su lafiyyun gidaje amma a ce ƴarsa ɗaya tilo a duniya tana rayuwa a cikin wannan gidan da bai wuce a ce tana kiwon karnuka ba. Amma ita ke rayuwa a nan lallai ma'eesha Allah ya ba ta karfin zuciya.
Yana tsaye yana kallon ƙofar fale-falen da suka bude suka shiga.
Ya ƙsrasa bakin kofar gidan yana sallama.
"Assalamu alaikum."
Daidai lokacin da ma'eesha ke fitowa da tabarma daga cikin dakin ta ji sallamar sa a kofar gidan.
Makaho ne ya amsa ma sa sallamar yana kokarin mikewa
"Please kar ka fita ka rabu da shi idan ya gani da tafi."
Ta fada tana rike hannunsa.
"A'a Ma'eesha ki yi hakuri wannan bawan Allah ba shi ya yi ma ki laifi ba, ki sauraren shi laifin wani baya shafar wani, don haka ki daina hukunta shi da laifin da mahaifiyarsa ta aikata."
Ya fadi haka yana zame hannunsa daga rikon da ta yi masa ya ɗaiki Sandarsa ya nufa hanyar fita.
Yana fita ya ce.
"Waye ke sallama?"
Jamil ya ce .
"Ni ne wanta Jamil."
"Bismillah ka shigo ciki."
Ya yi maganar yana yin gaba yayin da Jamil ya take ma sa baya.
_Nadra_
Farin ciki duk ya lulluɓe ta sakamakon ganin ƴan uwanta sun zo.
A nan falon dake downstairs suka zauna.
Durƙusawa ta yi ta gaida dangin nata cikin farin ciki.sannannta mike suka gaisa da ƴan matan dangin nasu. Sai tsokanar ta suke wai ta canza a cikin kwana ɗaya ne me Fahad ɗin ya ba ta ne, ita dai ba ta tanka ma su ba.
Ruwa da lemu ta kawo ma su ta na shirin zuwa kawo ma su cincin sai Gwaggo Laraba ta ce.
"Me kuma za ki kawo ma na?"
"Cincin ne zan kawo ma ku."
"A'a cincin da muka baro shi a gida."
"To bari na je na ɗoraa ku girki don na ga Akwai komai na bukatar."
Daidai lokacin aka danna ƙararrawar ƙofa.
Dama tana sanye da dogon Hijabi kamar yadda ya zamar ma ta al'ada.
Tana buɗe wa ta ga Rumaisa ƙanwar Fahad ce sai dai wannan karon iya kaɗai ce.
Murmushi ta sakarwa Nadra tana cewa.
"Antynmu ya kike ?"
Ta faɗa tana Murmushi. Duk da kasancewar ta girmi Nadra sosai amma ba ta da girman kai.
Nadra ma murmushi ta sakar ma ta tana yi ma ta sannu da zuwa .
Rumaisa ta amsa tana shigewa cikin falon ɗin ta hangi baƙi.
Ta shiga da fara'a tana gaida jama'ar da ta gani a falon fuskarta ɗauke da murmushi.
Suka amsa ma ta cikin sakin fuska da walwala.
Kallon Nadra ta yi ta ce.
"Ga abinci Mama ta ce a kawo ma ki ."
"Okay to na gode a gaishe ta."
"Za ta ji."
Ta faɗa nufar hanyar waje bayan ta yia su sallama.
"Am ba ki ji ba."
Nadra ta faɗa tana kallon Rumaisa kasancewar ba ta san sunan Rumaisa ba ta dai san sunanta ba.
Rumaisa ta juyo tana kallon Nadra ta ce
"Da ni kike yi?"
"Eh, dama basket ɗin da kika kawo da safe ne nake so ki tafi da su."
"Okay."
Nadra ta haura upstairs ta nufi kitchen don ɗauko basket da food flask ɗin da aka kawo da safe.
Dama kafin ta wanke su sai da ta fita ta kai wa masu gadi da sauran ma'aikatan gidan.
Bayan ta kawo ne ta ce.
"Ga shi ."
"Sunana Rumaisa."
Jinjina kai Nadra ta yi tana Murmushi. Daga nan ta yi ma ta sallama ta tafi.
Dama ta bar direba a mota yana jiran fitowar ta. Tana fitowa suka bar gidan.
Bayan tafiyar ta ne Nadra ta ce .
"Ga abinci nan an kawo, na san zai ma isa don na ga da yawa kamar ta san za ku zo."
"Dama ta samu ma na, dole wasu za su zo yau su ganki musamman danginki."
Gwaggo Laraba ta faɗa tana karantar yanayin Nadra. Don ta lura jikina a sanyaye yake.
Kallon ƴarta ta yi mai suna Amal ta ce ta zuzuzba abincin ta ba wadanda za su ji. Ita kuma sai ta ja hannun Nadra tana cewa.
"Muje na ba ki sako ko?"
Nadra ta miƙe suka nufi upstairs.
Har cikin bedroom ɗin Nadra suka shiga ta zaunan a saman gadon sannan ta nuna wa Nadra gefenta ta ce ta zauna kusa da ita.
Ba musu ta zauna Kamar yadda ta umarce ta. Sai ta riko hannun Nadra ta ce .
"Daughter akwai matsala ne?"
Shiru ta yi tana wasa da yatsun hannunta da suka sha jan lalle.
"Idan akwai matsala ko sanar da ni, sai na san ta ina da za'a ɓullowa lamarin."
Ƙwalla ne ya cika idanunta a hankali ta ce .
"Ummata."
"Ummar ki kuma?"
Jinjina kai ta yi ta ce.
"Ya jikinta."
Ta ji sauƙi ta warware, yanzu haka ma ta yi ta kiran wayarki ba ta shiga ."
"Eh ya amshe ma ni waya."
"Ya amshi wayarki saboda me?"
Nan ta ba ta labarin duk abinda ya faru.
Shiru ta yi tana nazari kafin ta yi ajiyar zuciya ta ce.
Eh mu ne muka mance ba mu sanar da shi Sayyadi zancen auren naki ba. Amma yanzu na san dole ya sani. Sannan zan ya ma ki wata magana ɗaya. Kada ki sake yi wa Fahad zancen Sidra."
Da sauri ta kalli Gwaggo Laraba ta ce .
"Idan ta dawo ai sai a daura ma su aure ta zo ta zauna ni kuma na je na auri ya Sayy..."
Mugun kallon da Gwaggo Laraba ta yi ma ta ne ya saka ta yi shiru.
"Ke dakata! Ba na son shashancin banza, ko da Sidra ta dawo to sai dai ta auri wani namijin ba Fahad ba, domin dama wani baya auren matar wani haka wata ba ta auren mijin wata. Don haka ki sa wa rabi cewa zaman aure kika zo ba wai kin zo da niyyar wata rana ki fita ki ba wa wata mijin ki da gidanki ba ne, don ba za mu taba aurawa Fahad Majidaɗi Sidra ba, bayan ya aure ki, don haka ki kama mijinli ki yi ma sa biyayya sau da ƙafa. Ba mu kawo ki nan dan ki fita wata rana ba. Sannan kada na sake jin sunan Sayyadi a bakinki ko tunaninsa. Ki cire shi a ranki dama can ba mijinki ba ne."
Jinjina kai ta yi hawaye na bin fuskarsta. Dosa Gwaggo Laraba ta yi ma ya nasiha mai ratsa zuviya da wasu shawarwari kan dabarun zama da miji.
Wasu magungunan mata da na gyaran jiki Gwaggo Laraba ta fito da su daga cikin jakarta sannan ta yi na ta bayanin yadda za ta sha kowane.
Karɓa ta yi ta ajiye su.
Sai ta ga Gwaggo Laraba ta fito da wani kula a cikin leda ta buɗe kazar amarya ce guda aka dafa ma ta da romonta, daga gani ta ji sassaken magani .
Sai da Gwaggo Laraba ta saka ta gaba ta ci rabin kazar ta sha romon maganin sannan ta ajiye sauran da niyyar kafin su tafi sai ta saka ta ta cinye sauran.
sannan suka koma downstairs, don har sun gama cin abinci.
Daidai lokacin ne suka ji horn ɗin mota. Bayan kamar mintuna biyar aka turo ƙofar falon tare da sallama.
Fahad ne ya shigo ya durƙusa cikin girmamawa ya gaida su Gwaggo Laraba.
Upstairs ya haura zuwa part ɗin sa.
A falo ya zauna kan kujera ya faɗa duniyar tunani.
A can falo Gwaggo Laraba ta ce wa Nadra ta tashi ta je ta sami mijinta ta kai ma sa ruwan sha.
Jin haka sai da gaban Nadra fadi, amma sai dake.
Gwaggo Laraba ta tashi ta ce.
"Mu je kitchen ɗin."
Tashi ta yi ta bi bayansa kamar kazar da ƙwai ya fashe wa a ciki. Suna shiga ta fuskanci Nadra ta ce.
"Wato ba ki ji huɗubar da na yi ma ki ba ne? Na ce da zaran ya dawo ki dinga tashi kina tarbarsa, sannan ki bashi ruwa ya sha idan yana da buƙata. Sannan idan wanka zai yi ki taimaka ma sa. Yanzu ɗauki ruwa da cup ki kai ma sa, sannan ku tambaye shi ko akwai abun da yake buƙata ki kai ma sa ko ki yi masa⁷."
Sannan kuma ki daina daka wannan dogon hijab kamar mai takaba ya isa haka nan, daga ke sai mijinkine idan an yi baƙi maza ."
Faranti ta ɗauka ta dauki ruwa roba guda da glass cup ta fito ta nufi upstairs.
Knocking ta yi a kofar falon sai dai ji shiru. Sai da ta sake yi sannan ta ji ya ya ba ta izinin shiga sannan ta shiga.
Yana zaune kan sofa a ƙasan ƙafarta ya fara dauke idanunsa, yatsunta da suka sha lalle ne kawai ake iya gani. Don dogon Hijabinta har ya rufe ƙafarta. Ɗauke idanunsa ya yi ya mayar kan wayarsa yana daddanna wa
Har ƙasa ta durƙusa ta ce.
"Sannu da dawowa."
Share ta ya yi kamar bai ji ta ba ya ci gaba da danna wayarsa.
Duk da haka dai ta sake cewa.
"Ina wuni?"
Nan ma shiru ya ma ta bai amsa ma ya ba.
Glass cup ɗin da ta ajiye ne ta buɗe robar ruwa ta tsiyaya ma sa ta mika ma sa ta ce.
"Yaya ga ruwa."
Ta yi maganar tana mika masa cup ɗin. Sai a lokacin ya ɗago kansa ya sauke idanuntsa kan kamilalliyar fuskarta. Idanunsu ne suka sarƙe cikin na juna, da sauri da janye idanunsa saboda kwarjininsa.
Kamar ba zai karɓa ba sai kuma A hankali ya mika hannunsa ya karɓa tare da cewa.
"Thank you."
Ya faɗa yana kai ruwan bakinsa ya sha.
"Mama ta aiko ma na da abinci na kawo ma ka ne?"
Kai ya girgiza sannan ya ce.
"Am okay, you can go."
Tashi ta yi nufi ƙofar fita ta fice.
*Maman Ihsan ce*
09065327995
https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce ✍️
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page2️⃣5️⃣
Tashi ta yi ta nufi ƙofar fita ta fice.
Sai dai bayan ta fita kafin ta rufe ma sa ƙofar ya ce.
"Come here."
Dawowa ta yi ciki ta tsaya tana jiran me zai ce.
Kallon Hijabin da ke jikinta ya yi ya tuna duk sanda zai ganta da hijabi ne ko da ya je zance ne a wajen Sidra. Sai ya ɗauka ko don saboda zai shigo ne duk da ita wance yake zuwa wajan nata ba ta saka wa. Har wata rana suna hira da da Sidra a falon saukar baƙi sai ga Nadra ta zo wuce wa ta fito daga ɗaya daga cikin ɗakunan dage part da dogon Hijabinta idanunta ya sauka akan Fahad da Sidra da suke zaune a kujera mai zaman mutum biyu, hannunsa sarƙame cikin na juna ta kwantar da kanta a kafaɗarsa suna kallon wani abu a wayarsa. Girgiza kai kawai Nadra ta yi don ta sha ganinsu rike da juna kuma manne da jikin juna girgiza kai kawai ta yi tana taɓe baki ta zo za ta wuce bayan ta gaida Fahad sai Hijabin ya ja kofin ruwan da Sidra ta ajiye wa Fahad. Ruwa ya zube ran Sidra ya ɓaci har tashi za ta mari Nadra Fahad ya dakatar da ita ta hanyar cewa.
"No."
"Ka bar ni na koya ma ta hankali tun da ba ta da shi kullun tana cikin hijabi kamar mai fita takaba, wani namiji ne zai yi sha'awarki a haka? Yarinya kamar wata bagidajiya sai ƙauyanci, ban ga ranar da yarinyar nan za ta waye ba."
Sai a lokacin da kalli Yayar tata ta ce.
"Aunty Sidra Indai wayewa irin ta ku ne ba na buƙata wayewa ta addinin Muslunci nake buƙata bar ni a haka ban saɓa wa Allah ba."
A fusace Sidra ta wanke wa Nadra fuska da mari wanda sai da ta durƙusa wajen tana kuka.
"Ni za ki yi rashin kunya wani saɓon Allah na yi ko saka hijbi da suturta jiki ne tsoron Allah da ba na da shi? Sau nawa ma su daka hijabin suke aikata ɓarna wanda wacce ba ta saka wa ba za ta iya yi ba?"
Tashi ta yi tana kuka ta bar part ɗin.
"Wai me ya saka kin fiye zafin rai ne?"
"Don Allah Mallam kar ka sake ɓata ma ni rai, ya za'ayi ta Mani rashin kunya na ƙyale ta?"
Ta yi ma sa maganar cikin ɓacin ran da take ciki.
"Ba'ayi ma ni tsawa ki iya bakinki ki san kalaman da za ki dinga faɗa mani, idan ba haka za mu samu matsala da ke."
Jin haka ta sassauta murya tana bashi haƙuri.
Tari da ta ɗan yi ne ya dawo da shi duniyar tunanin da ya lula.
Ya kalle Nadra da kyau wacce ko a mafarki bai taba tunanin ita ce za ta zamo matarsa ba Sidra ba.
Maida idanunsa ya yi kan wayarsa cikin muryarsa mai amo ya ce.
Ba na buƙatar sake ganin ki da hijab matuƙar ba wai namiji ne ya shigo gidan nan ba ko kuma za ki fita zuwa wani waje. Okay?"
Kai ta jinjina ma sa sannan ta fita daga ɗakin.
Kitchen ɗin ta koma in da ta tarar da Gwaggo Laraba tana ƙara gyara wa wasu kayan wajen zamansu.
Ganinta ya sa ta dakata ta ce.
"Abinci za ki kai ma sa?"
"A'a cewa ya yi ya ƙoshi na tafi."
Shiru Gwaggo Laraba ta ce.
"Dole fa sai kin yi hakuri, domin har yanzu akwai tabon da Sidra ta yi masa a cikin zuciyarsa. Domin ba daɗi a ce ranar aurenka matar da kake so ta gudu ta bar ka. Kin ga dole har yanzu ransa ya kasace a ɓace. Ke ce za ki yi ƙokarin dasa ma sa soyayyarki a zuciyarsa. Ta hanyar kyautata ma sa, dama ita zuciya an halicce ta ne bisa ga son wanda ya kyautata ma ta, da kuma ƙin wanda ya munana ma ta. Shin ya nuna ma ki tsana ne ko hantara ?"
Kai ta girgiza alamar a'a kafin ta ce.
"A rayuwar aure ko soyayya, akwai abu guda da ya kamata mace ta gane,
Ko wani namiji yana da irin nasa hali.Kuma yadda yake sonki, haka yake nuna fushinsa idan wani abu ya bata masa rai, ba wai saboda baya sonki ba ne, a’a, saboda ya damu da ke sosai ne.Don haka ke dai ki fahimci irin namijin da kike tare da shi Idan mijin kirki ne, zai yi fushi saboda yana son ki gyaru, ba don ya cutar da ke ba Idan mai saurin ɓacin rai ne, ki gane cewa yana magana ne da zuciyarsa, ba wai yana ƙin ki bane.Idan mai shiru-shiru ne, fushinsa yakan zama nesa da magana, amma zuciyarsa tana cike da damuwa, Idan mai gaskiya da tsauri ne, yana fushi saboda ya san abin da ya dace da abin da bai ya dace ba. Idan mai tausayi ne, fushinsa zai zo da nutsuwa, amma zai so ki gane kuskurenki ba tare da ya takura miki ba, a kowane hali, rarrashi na mace shi ne sirrin da ake so mace ta sani.Ki saurari damuwarsa ba tare da tsawatarwa ba. Ki nuna masa kin gane abin da ya dame shi. Ki yi magana cikin ladabi da natsuwa.Ki yi masa nasiha cikin taushi, ba da jayayya ba, Ki nuna masa kulawa, ko da da kananan abubuwa ne.namiji baya buƙatar mace cikakkiya,
yana buƙatar mace mai fahimta.
Jinjina kai Nadra ta yi cikin gamsuwa ta ce .
"Gwaggo Laraba baya sakar ma ni fuska fa."
"Ya ma ki wani abu ne yanzu da kika kai ma sa ruwa?"
"Cewa ya yi wai kada na sake saka hijabi in dai ba wani namiji zai shigo ba ko fita zan yi."
Murmushi Gwaggo Laraba ta yi sannan ta nuna ma ta yadda za ta zuba da shi da kuma kiyaye abinda baya so.
Sai yamma suka shirya za su bar gidan suna fita harabar gidan dama motoci biyu suka zo da su na Gwaggo Laraba da ta Abba daya wacce daya daga cikin ƴan matan ta yi driving.
Daidai lokacin Fahad ya dawo daga sallar la'asar ya ga suna shirin tafiya. Sallama ya ma su sannan ya ce Nadra ta zo ta karɓar ma su saƙo. Ko da ta ke 200k dubu ɗari biyu ya ba ta ya ce ta ba su yana ma su Allah ya kiyaye hanya.
Ta zo ta ba su suka yi ma ta godiya tare da cewa ta isar ma su da sakon godiya suka tafi.
_Ma'eesha_
Sallamar Yaya Jamil da na mijinta ne ta san cewa ya shigo da shi ne. Don haka ya tsuke fuska ta tashi daga kan tabarma ta koma kan kujerar tsuguno yayin da Makaho ya zauna a gefen tabarma shi ma Jamil ya zauna.
"Ki girma baƙonki hadisin Manzon Allah (s.a.w) ne."
Cikin sanyin murya ta ce.
"Yaya Jamil ina wuni?"
Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke sannan ya amsa mata cike da farin ciki ta sauko.
Tashi ta yi ta je ta kawo ma sa ruwan pure water guda biyu ta ajiye ma sa. Wanda ya san cewa yanzu ne ta fara shan pure water. Don a gidan su ruwan roba ake sha. Shi kan shi tun ranar da suka zo gidan su Ma'eesha suka ji sallama da kowane ruwa sai na roba. Bayan ya sha ruwan pure water leda ɗaya ne ya kalli Ma'eesha ya ce.
"Ina mai ba ki haƙuri a madadin mahaifiyata, na san ta cutar da rayuwar ki cutarwa mafi muni ..."
Kasa karasa maganar ya yi ganin yadda ta mike zumbur.
"Yaya Jamil na roƙe ka dan girman Allah ka tashi ka tafi ba sai ka sake dawowa ba, kuma ba na bukatar ka sake jin an tayar mani da wannan zancen ya riga da ya wuce cutarwa dai an ya mana sai dai sakayyar Allah."
Tana faɗar haka ta shige daki tana fashewa da kuka.
Tana shiga ɗakin Jamil ya cire kuɗi 100k ya ce wa makaho ga kudi nan ya ba wa Ma'eesha amma makaho ya ƙi karba saboda ya ji tsana da ɗaci da a cikin Muryar Ma'eesha ya san ba za ta so kudin ba don haka ya ki karba. Sai ya mayar da kudin cikin aljihunsa sannan ya cire 3k ya ce ka ba ta wannan kudin sadakinta ne da ta ki karba shi ne na karɓa a hannun Laila hakkinta ne ka ba ta."
Wannan kam makaho ya amsa suka yi sallama ya fita.
Ma'eesha na jin fitar Jamil ta fito daga cikin ɗakin ta zauna waje.
Wayar da ta siyo wa Makaho ne ta ciro ta buge wayar don battery akwai caji. Ta saka sim card ɗin da ta siya ma sa ta mika ma sa, nan ta dinga nuna ma sa yadda zai danna idan an kira shi waya. Ta gwada kiran wayarsa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 49