Share this page
da kai kuma ya zo. Dama Nasreen gaskiya take faɗa mun cewa kai ba Makaho ba ne basaja kake yi kama raina wa mutane hankali. Abun takaici ma har da ni da ban cancanci ka ɓoye ma komai ba. Na yarda da kai fiye da kowa. Kau da kanta gefe ta yi don ba ta so magana da shi. Ko ganinsa ba ta son yi. Ƙoƙarin tashi zaune take yi duk da kanta na Sara ma ta da ciwo amma ta daure, tana ƙoƙarin taimaka ma ta sai ta ɗaga ma sa hannu alamar dakatar wa. "Kada ka taɓa Ni!" Ta jingina da kyau sannan ta juya ta kalle shi cikin ido, cike da ƙunar rai ta ce. "Zan yi ma ka wasu tambayoyi ka ba ni amsa, wannan karon kafa ka kuskura ka ce za ka yi ma ni ƙarya." "Meye sunanka daga wani gari kake?" "Sunana Jalaluddeen Kabir Arzika, daga Abuja, kuma ni...?" Ɗaga ma sa hannu ta yi alamar ya isa . "Da gaske kai Nasreen ta gani a Abuja tare da wata mace har ta kawo ma ni photon amma na ƙaryata ta bayan ka ce Maiduguri za ka tafi wajen wajen dangin ka amma ka je Abuja?" "Eh nine." "Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un. Nasreen na yi nadamar rashin yarda da ke tun farko ku yi hakuri don Allah." Kauka ne ya ci ƙwrfinta, da zaran ya zo zai taɓa ta sai ta dakatar da shi da hannu. Ɗan tsagaita kukan ta yi kafin ta ce . "Maganar da na ji kana ya a waya da gaske ne ranar juma'a kai ne wanda za'a ɗaurawa aure ta wata mace? " Shiru ya yi kansa a ƙasa don amsar ta yi ma sa nauyi ya faɗa. "Faɗa mun kai ne?" "Eh ni ne amma wallahi ba da..." "Ya isa!" Ta daka ma sa tsawar da sai da ya yi mamaki. "Ba na bukar sake jin komai daga gare ka, iya abun da nake so na sani kenan kuma na sani, saura abu guda nake umartar ka da ka yi ma ni." "Mene ne shi?" "Ka sake ni saboda dama auren namu bai da amfani ba shi da banbanci da babu, sunan aure ne kawai amma ba rayuwar aure muke yi ba, yanzu na fahimci dama ba ja so na kana da wacce ja shirya rayuwar aure da ita, shi ya sa a zamantakewarmu ba ka taɓa nuna mun alamar soyayya ko wani abu da zan yadda kana so na ba. Don Allah ka sake ni." "Ba zan iya sakinki ba Ma'eesha, da za ki bani dama ki saurare ni mu fahimci juna za ki gane ..." "Ba za ka sake ni ba ko? To shi kenan za mu gani. Babu wani dama da xan ba ka na sauraren ka. Da a baya ne ko zan iya sauraren ka saboda na yarda ba za ka yi ma ni ƙarya ba, amma yanzu da gane gaskiya ne wallahi, wallahi, wallahi , ba wata magana da za ta fito daga bakinka na yarda da kai . Ban taɓa danasanin saninka a rayuwata ba sai yau. Na yi danasanin saninka a rayuwata , na yi nadamar zama da kai. Ban taɓa ganin ka da muni ba sai yau, ban taba jin muryar da na tsani ji kamar Muryar ka ba a yau na tsane ka wallahi,. Maƙaryaci, mayaudari...' Kula ne ya ci karfinta sosai har yake ihu tana dukan katifa tana kuka mai cin rai Doctor ne ya shigo yaga halin ta take ciki da yadda take cewa Jalaluddeen ya fita . Lura fay hakan ya sa ya ce ma Jalaluddeen ya fita. Yadda yake ta Surutai duk ta rikice ya da Doctor ya kira nurse ta yi ma ta allurar barci. Sai da ta yi barci sannan suka fita daga ɗakin. Lokacin karfe sha biyun dare. Doctor Kamal ya tafi gida ita nurse ta tsaya a asibitin. *KATSINA* Washegari Bsyan sun sun yi wanka sun yi breakfast suka shirya don zuwa Kaduna. Maude ma an kai ma sa breakfast ɗinsa da sabbin kayan da idan ya yi wanka zai saka, Alhaji Sulaiman ne ya aika ma sa da kayan nasa. Ya yi wanka ya shirya kamar ba shi ba. Ya fito yana jiran fitowar su. Captain Kabeer da Barrister Haidar ne suka fara fitowa. Maude duk da tsufarsa ya durƙsmusa yana gaishe su. Barrister Haidar ne ya amsa Amma Captain Kabeer ma ko kallo bai ishe shi ba ballantana ya amsa . "Amma ba dai da motata za'a tafi da wanan abun ba ko?" Cewar Kabeer yana yi wa Maude wani wulakantaccen kallo. "To Amma da motar ka Alhaji ya ce za mu tafi." "Wanan mutumin ba zai shigar ma ni mota ba wallahi sai dai motarka?" "Anya Kabeer ka san darajar Ɗan adam kuwa?" "Wani irin tambaya ne kake ma ni Yaya Haidar, shi ya san darajar mutane ne, da za'a ba ni dama sai na kashe shi. Amma bari mu gama abun da muke so dai ya gwammace mutuwarsa da rayuwarsa." Cikin Maude ya ɗuri ruwa wani tson wanan sojan ya shige shi lokaci guda. "Shi kenan a tafi da Motata, bari na je na ɗauko makullinta." Ya yi maganar yana tafiya zuwa ɗauko key din motarsa. Dadai sauran mutanen gidan na fitowa. Alhaji Sulaiman da Mahaifiyarsa yana sake kwantar ma ta da hankali. A gefe Hajiya Safiya da Hajiya Saratu ne , sai Lubna da Jamila. A baya kuma Mujahid ne wanda zai wakilci Alhaji Sulaiman yau a wani zama da za su yi da abokan Harkokinsu. "Ina kuma za ka tafi?" "Zan ɗauko key din motata ne." "Ba da miyar Kabeer za mu tafi ba " "Motata za ta fi bari na ɗauko ." "Kafin Ya yi wani magana har ya wuce da sauri." "Ko kuma baƙin halinsa ya sa ya ce ba za'a tafi ma sa da mota ba ,in dai Kabeer ne shi ya fi komai sauki a wajensa bai da mutunci." Cewar Dada tana tafiya da ƙyar saboda ciwon ƙafa. Suna isa sai ga Haidar ya iso da key din motar, ya bude wa Mahaifinsu bayan motar ya shiga, sanan ya ce Maude ya shiga gefe. Yayin da shi ya shiga mazaunin direba. Kabeer ya zaune gefensa wajen me zaman banza. Allah kiyaye hanaya aka yi ma su tare da addu'a Allah ya bayyanar da su. Da amin suka amsa. Horn ya danna maigadi ya wangale ma sa gate ɗin gidan ya fita, har sai da aka rufe gate mutanen gidan suka koma ciki suna addu'ar Allah ya sa a gane inda suke cikin gaggawa. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page8️⃣3️⃣ Horn ya danna maigadi ya wangale ma sa gate ɗin gidan ya fita, har sai da aka rufe gate gate mutanen gidan suka koma ciki suna addu'ar Allah ya sa a gane in da suke cikin gaggawa. _Jalaludden_ Yadda ya ga rana haka ya ga dare. Domin gabdaya bai rintsa ba, ya shiga ɗakin da aka kwantar da Ma'eesha sama da sau goma yana duba ta amma tana barci. Har yanzu allurar barcin ke aiki a jikinta. Har ya kai ya zauna cikin dakin yana gadinta har aka kira sallar asuba ya tashi ya nufi masallaci. _Fahad_ Sake haɗe fuska ya yi ganin yadda Nadra take ƙarasowa wajen sa sanye da dogon hijabinta. Wato ya ba ta kayan da za ta saka ta zo in da yake shi ne ta ɗora wani hijabi a saman kayan. Tama ƙarasowa kanta a sunkuye kamar mara gaskiya. Miƙewa tsaye ya yi yana kallon ta ba ta yarda ta kalle shi ba. Hannunsa ɗaya ya sa ya zare dogon hijabin da ta saka, da sauri ta shige jikinsa ta ƙanƙame shi sosai. Saboda ita har ga Allah tana kunyar ya ganta cikin figaggiyar riga da ya ba ta. Murmushi ya yi sannan ya ɗauke ta ya zauna kan kujerar sanan ya ɗaura ta a saman cinyarsa. Kunya take ji har lokacin, sai ta ɓoye fuskarta a ƙirjinsa. "Nadfah." Ya kira ta cikin sigar raɗa a cikin kunnenta. "Wanan kunyar ta ki fa tana cutar da ni wallahi. Kunyar me ya rage a tsakaninmu? Allah na tuba wani dare ne jemage bai gani ba? Ba abun da za ki ɓoye ma ni wanda ban gan shi a jikinki ba ko ban san shi ba, na san ki ciki da waje har..." Hannunta ta sa ta toshe ma sa baki yana dariya. Cire hannun ya yi yana cewa. "To ka dena faɗa, ke ma ina son ki kasance a yadda nake buƙata ina son ki da dukkan zuciyata, i love You with all my heart." "Love you more..." "Na kusa komawa America next week zan koma in sha Allah, sannan ina so mu tafi tare da ke my sugar." Shiru ta yi tana tunani ba kowa ya faɗo ma ta a rai ba sai Aunty Sidra. Ita ce kullum maganar ta tana cewa idan ta tafi America ita dai Nigeria sai dai ziyarara don can za ta zauna da Fahad. Take yanayin ta ya sauya saboda tuna Sidra, sai take ji a ƙasan ranta kamar ita ce ta janyo komai da yake faruwa a yanzu. Hawaye ne ya cika idanunta. Tabbas ta san cewa tana son Fahad kuma ba ta san lokacin da soyayyan Fahad ya shige ta lokacin guda ba. Amma tana tausaya wa Halin da ƴar uwarta ta shiga a lokacin da ta rasa shi, wanda har yanzu ta san tana son sa amma ba yadda za ta yi. Ba zato ta ji ya kai harshensa a saman kumatunta yana lashe hawayen da ya wanke ma ta fuska. Sai da ya lashe hawayen sanan ya ce. "Kin san na tsani zubar hawayenki ko? Ba na son ɓacin ran ki ballantana har ki zubar da hawaye. Me ya sa kike son sa wannan majidaɗin ne ya ji ba daɗi? Idan tafiyar America ne ba ki so to ni zan tafi ni kaɗai ba zan tilasta ma ki abun da ba ki so ba." Ganin wani hawaye ne ya kai baki ya yana lashewa sai suka ji takun tafiya ƙwas ƙwas ƙwas, ana zuwa inda suke. Cire bakinsa ya yi daga fuskarta ya kalli wace isashshiya ce ta shigo ma su har falo na knocking ba neman izinin. Ita ma kallon ta ta yi sai da gabanta ya faɗi ta yi saurin ɗaukar hijabinta ta saka musamman ganin kallon tsanar da take jifanta da shi. _Sidra_ Bayan Sady baby ta sauke ta ta kofar baya na gidansu ne ta fito daga cikin motar tana tafiya a hankali. Leƙowa ta yi ta tana cewa "Zuwa jibi za ki ga sakamako aikin da zai yi ma ki, kuma zan je na karɓo ma ki wasu saƙon da ya ce zai ba ki." Ba ta ce komai ba, ta bude ƙofar bayan ta shiga cikin sanɗa. Sannan ta saka sakatar ta rufe. Sady baby ta ja motarta ta bar wajen, sai dai ba ta lura da wata motar da take bin su a baya tun lokacin da suka bar unguwar da suka je wajen Mallaminta. Sai da ta bar wajen sanan motar da ya biyo su tun daga can ya sauke baƙin glass ɗin motarta ya kalli gidan da kyau, sanan ya zagaya ta gaban gidan ya kalli gidan sannan ya ja motarsa ya bar wajan. _Ma'eesha_ A hankali ta buɗe idsnunta da suka yi ma ta nauyi ta sauke shi a kan fuskarsa. Cike da takaici ta rintse idanunta. "Kin farka ya jikin naki?" Idanunta a rufe kamar me barci amma ba barci yake yi ba. Kanta ke Sara ma ta kamar zai tsage gida biyu. Ga jikinta sam ba ƙarfi ko kaɗan a jikin nata. Wayarsa ce ta soma ruri ya fito da wayar daga cikin aljihunsa ya duba mai kiran wayar. Idanunta suka sauka an tsaddadiyar wayar tasa ta miliyoyin kuɗi. Lumshe idanunta kawai ta yi kamar tana barci . Ɗan matsawa gefe ya yi yana amsa wayar. Duk da a hankali yake magana amma tana jin abinda yake faɗa.. "Hello." Can cikin wayar ya ji muryarta tana cewa. "Gud morning my Sweet Yaya J." Cikin yanayin rashin son magana ya ce. "Kin shirya ne?" "Eh kai nake jira." "Ba zan samu zuwa ba zM turo a zo a ɗauke ki a kai ki airport." Kamar za ta yi kuka ta ce . "Please mu tafi tare ma na, ja ga dama ba mu yi tsare-tsaren bikin ba." "Kin ga ba na son magana, ki shirya a zo q ɗauke ki kada ki rasa jirgi." Daga haka ya kashe kiran wayar. Ya kira yaronsa da ya kai su gidan jiya, ya sanar da shi ya je ya ɗauko Yasmeen ya kai ta airport. Daga nan ya kashe wayar ya sa a aljihu, yana tuna diramar da Ma'eesha ta yi yana kuma tuanin yadda zai iya shawo kanta ta saurare shi . Tunani kawai take yi na neman mafita don shi ne a gabanta yanzu ba komai ba. Damuwa bata da amfani akan duk abinda ba ta da ikon koma wa baya ta canza shi, ko kuma ta hana faruwarsa, sai dai ta cinye ma ta lokaci, ta hana ta amfanar damarta ta yau wajen aikata abunda zai amfa ne ta a duniya da lahira. Za ta yi haƙuri, ta fuskanci al'amuranta ga Allah , zai kawo miki sauyi da mafita a mafi dacewar lokaci. Doctor ne ya shigo cikin ɗakin idanunsa akan Ma'eesha da ta lumshe idanu. Sanan ya kalli Jalaluddeen. "Assalamu alaikum." Jalaluddeen ya kalli Doctor dake shigowa sanan ya amsa sallamar. "Wa'alaika salam." Hannu ya ba shi suka yi musabaha sannan sannan ya ce. "Da alama ko barci ba ka yi ba ko?" Bai amsa ba idanunsa na kan Ma'eesha. "Ka ci abinci kuwa, na ga kamar kai ne mai jinyar jikin daga jiya zuwa yau har ka rame." Gajeren murmushi kawai ya yi nan ma bai amsa ba. "Ya jikin nata?" "Da sauki." "Ta farka kuwa?" "Da safen nan ne ta ɗan farka ta kuma rufe ido amma na tabbatar ba barci take yi ba." Doctor ya karasa wajan gadon ya ce. "Assalamu alaiki." "Wa'alaika salam." Ta amsa isanunta a rufe tana yamutse fuska tare da ɗan dafe kanta. "Doctor kaina kamar zai fashe nake ji." "Sorry, za ki samu lafiya in sha Allah. Bari wanda ya kawo ki ya taimaka ma ki ki tashi zaune sai ki wanke baki, za'a kawo ma ki breakfast ki ji sai ayi ma ki allura za ki samu sauki." Duk da halin da take ciki amma sai da ta ce "Ba na son ganinsa Doctor don Allah ya fita, sanan ka tura Mani nurse mace ta taimaka ma Ni zan yi wanka na yi sallah." "Na ga shi ya kawo ki, me ya sa ba ki son ganinsa? Meye alaƙar ku da shi?" "Ban san shi ba, taimaka ma ki kawai ya yi da ya ga na fadi, ya kawo Ni asibiti na gode ya fita don Allah ya kama gabansa." "Ka ji abun da ta ce Yallaɓai." Doctor ya yi maganar yana kallon Jalaluddeen. Bai ce komai ba ta fita daga ɗakin, wanda hakan ya sa shi ma Doctor ya fita don tura ma ta nurse kamar yadda ta bukata. Ba jimawa wata Nurse ta shigo ta taimaka ma ta ta shiga toilet ta yi wanka ta dauro alwala. Kayan hijira ta sake sakawa sanan ta bude kofar. Nurse din ta taimaka ma ta ta yi tafiya zuwa inda ta shimfida ma ta sallaya ta mika ma ta hijab ta yi Sallah. Fita ta yi sai ga ta ta dawo ta breakfast da aka jero a faranti . Tea da bread ne sai soyayyen ƙwai. Da kyar ta iya shan ruwan tea kadai sanan Nurse din ta yi ma ta allurar da Doctor ya sa ta yi ma ta bayan ta kwanta. Ba nunawa barci ya yi awon gaba da ita, da ba don maganin ya sa ta barci ba da damuwar da take ciki ba za ta iya bari ta yi barci ba. Bayan ta yi bacci Jalaluddeen ya shigo dakin ya tarar tana barci . Wayarsa ce ta yi ruri Mom ce ke kiransa . Ya daga tare da sallama . "Assalamu alaikum." "Wa'alaika salam warahmatullah. Na ji muryarka da damuwa." Murmushi mai sauti ya kirkiro sanan ya ce . "Ba komai Mom, barci na tashi ne" Ya yi maganar yana jin dadin yadda Mahaifiyar tasa ke lura da yanayinsa ko ba sa tare. "To albashirin ka!" "Goro" ya faɗa kamar an ma sa dole ya ɗauka zancen auren sa da Yasmeen za ta ma sa. "An gano ƙanwata da aka sace tun tana jaririya." "Ban gane ba " Sai ta tuna shi bai san zancen ba, saboda ba hannunta ya girma ba, kuma sau biyu ya taba zuwa Katsina ya gaida dangin mahaifiyar tasa. Sadik da Saddiƙa da suka tashi a wajen Mahaifiyarsu ne suka san labarin bacewar ƙanwar mahaifiyar tasu. "Mom ban gane ba." "Wato yara uku Dada ta haifa na farkon shi ne Yaya Sulaiman da ka sani mahaifin su Kabeer, sai ni nake bin sa, to akwai mace da Dada ta haifa bayan ni sai dai tun tana jaririya aka sace ta. An yi neman ta da cibiya har an gaji. Duk da mahaifin mu har ya rasu bai cire ran cewa tana raye ba wata rana za ta dawo. Ko da ya rabar ma na da dukiyarsa har da nata kason wanda dukiyar nan nan Yaya Sulaiman na kula da su. To yanzu zanen ya fito wai tsohon maigadin gidanmu a lokacin ya sace ta yanzu dai suna hanya zai kai su inda ya kai ta. Shi ne nake cewa tun da kana gari sai gobe za ka bar garin ka taya su neman inda za'a samo ta." Kallon Ma'eesha dake barci ya yi . "Mom ki yi hakuri ina da wani abu mai mahimmanci ne a gaba na, wanda ba zan iya barin sa ba. Amma tun da shi wanda ya sace ta ya san in da ya kai ta komai zai zo ma su da sauki ba za su sha wahala ba." "Okay ba damuwa, na sanar da su kana garin, ko da sun kira sai ka sanar da su uzurinka. " "To na gode Mom." "Ba komai, ka tabbatar ka gama abun da kake yi zuwa gobe, wanda ba ka samu damar ƙarasawa ba sai ka bari bayan auren naka sai ka yi. Ka tabbatar ka dawo gobe." "To Mom." Ya amsa yana kallon Ma'eesha. Bayan sun gama waya da kamar mintuna talatin sai ga kiran wayar Haidar ya shigo wayar Jalaluddeen. Amsa kiran ya yi ta hanyar sallama, bayan ya amsa ya ce . "Kana ina ne Bros ga mu a Kaduna." "Okay daidai ina kuke ne?" "Yanzu muke shigowa, na ji an ce hotel kake ko za ka iya sanar da mu?" Duk da baya cikin hotel ɗin amma sai ya sanar da su, ya san ba nisa da asibitin. Fita daga asibitin ya yi bai tsaya kiran waya a zo a ɗauke shi da mota ba ya tari mai nape. Yana isa hotel ɗin ya yi wanka sauri-sauri ya shirya cikin ƙananan kaya. Kira ne ya shigo wayarsa ya duba ya ga Haidar ne. "Barrister kun iso ne?" "Eh mun iso, Ni da Kabeer ne kawai muka zo, shi mahaifin mu ya tafi wajen abokinsa Sanatar garin nan shi da mutumin da ya san inda take yake. Ya amsa da ba damuwa , lambar ɗakin ya sanar da su sannan ya katse kiran wayar. Knocking aka yi ya ba su izinin shiga ciki. Suka gaisa sanan suka zauna kan sofa. "Me zan sa a kawo maku?" "Ba komai kada ka damu." Cewar Kabeer yana danne-danne a waya. Haidar ne ya gyara zama ya kalli Jalaluddeen ya fara magana . "Ka san zanen da ya kawo mu garin nan ko?" "Eh Mom ta kira ni ta sanar da ni, sai dai ba zan samu damar bin ku ba sakamakon wani uzurin da nake sa shi." "Ban yi mamakn jin haka daga bakinka ba, domin ba ka ɗauke mu ƴan uwan ka ba." Kabeer ya yi magana yana kallon wayarsa kamar ba shi ne wanda ya yi maganar ba. Jalaluddeen bai kalle shi ba ya lumshe idanunsa tare da kwantar da kansa jikin kujerar da yake kai. Haidar ya kalli Kabeer ya ce. "Duk bai kai can ba." "Dama ni ban taɓa saka shi a cikin mu ba, duk da ba mu dade da sanin cewa muna da dangantaka da shi ba. Amma na tabbatar da dangin uwar da ta rike shi ne da ya bar abun da yake yi ya tafi. Amma wanan da muke nema fa da mahaifiyarsa da shi uwa daya Uba ɗaya, ana neman ta yana faɗin baya da lokaci? To shi kenan idan kuma har muka same ta na ga ka taka ƙafarka ka je Katsina sai na yi ma ka rashin mutunci!" Sai a lokacin Jalaluddeen ya ce . "Waye kai? Me kake da shi? Me kake taƙama da shi? To shi kenan ka rubuta ka ajiye ni Jalaluddeen sai na taka ƙafata cikin gidanku cike da isa da alfahari idan ka isa ka dakatar da ni." "Haka ka faɗa?" Banza ya yi fa shi ya miƙawa Haifar hannu tare da yi ma sa addu'ar Allah ya bayyana ta. Daga haka ya fice ya bar su a cikin ɗakin. Cikin takaici Kabeer ya ce . "Kana ganin wulaƙancin da ya yi ma na ko? Ba lafinsa ba ne kai da ka saka muka zo kai ka ja ma na wulaƙanci. Idan ba don ina duba dangantaka ba har ya isa ya faɗa mun magana na kyale shi?" "Kabeer ba ka da hakuri, ba ja san uzurin da ke gabansa ba, tun da ya fadi haka sai a tafi a haka ma na, meye na ɓacin rai a ciki, daga kai har shi kowa na ji fa izza da isa shi ya sa ba ku jituwa da shi." Bai ce komai ba ya tashi ta fita. Haidar ma ya bi bayansa suka fita a tare . Suna fita sai ga ɗaya daga cikin ma'aikatam hotel ɗin ya zo ya rufe ɗakin kamar yadda Jalaluddeen ya ba shi umarni." *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page8️⃣4️⃣ *Ku dinga haƙuri da typing error ba na samun lokacin yin editing.* Bai ce komai ba ya tashi ya fita. Haidar ma ya bi bayansa suka fita s tare. Suna fita sai ga ɗaya daga cikin Ma'aikatan hotel ɗin ya zo ya rufe ɗakin kamar yadda Jalaluddeen ya ba shi umarni. _Sidra_ A hankali take tafiya cikin sanɗa har ta shiga ta ƙofar baya na kitchen ta wuce zuwa ɗakinta ta cikin corridor da zai sada ta da ɗakinta. Ajiyar zuciya ta sauke ganin har ta shiga ba wanda ya ga shigowar ta Bathroom ta shiga ta haɗa ruwan zafi tana hawaye ta shiga ciki. Kuka take yi sosai ta yi nadamar abun da ta aikata. Sai da ta daure ta gasa jikinta sosai sannan ta yi wanka ta ɗauro alwala sannan ta fito. Doguwar riga ta saka tana jin ƙuna a ranta, ta tabbatar da a gidan aurenta ne mijinta na Sunnah ne da yanzu yana nan yana tausaya ma ta da lallaɓa ta kuma lada za ta samu. Amma wanan ga tarin zunubin da ta kwasarwa kanta, duk a dalilin soyayyar Fahad ta kai ta ga wanan halin. Sallah ta gabatar bayan ta idar ta mike dama ita ba mai yawan yin addu'o'i da azkar ba ne, ballanta karatun Alkur'ani. In da suka sha banban da Nadra Kenan. Domin Nadra akwai yawan addu'a da azkar da karatun Alkur'ani. Amma Sidra tana idar da sallah za ta tashi. Tana cire hijabinta sai ta hau saman gadon ta kwanta tana tunani. Umma ce ta turo kofar ɗakin ta shigo. Ba ta yarda sun hada ido da Umma ba don kar ta gane ta yi kuka. "Sidra." Cewar Umma tana zama bakin gadon. "Na'am Umma." "Ɗazu na zo na sanar da ke za mu fita da Ammi sai na yi knocking ba ki bude ba." "Eh Umma na yi barci ne, sannun ku da dawowa." "Yauwa sannu. Na tambayi ma su aikin gidan sun ce ba ku fito kin ci abinci ba lafiya?" "Umma na ƙoshi, na ci snacks dake cikin fridge." "Amma ba za ki ci abinci ba." "A'a Umma na ƙoshi ." "Akwai abun da ke damun ki." "Ba komai Umma ina lafiya." "Sidra." "Na'am Umma." Ya kamata ki shiga hankalin ki ki nutsu, hakika ina cikin damuwar hukuncin da mahaifinki ya yanke na cewa nan da wata ɗaya zai aurar da ke ga duk wanda ya ci karo da shi a ƙauyen su. Shawara ta ki fito da miji kafin lokaci ya kure ma ki. " "Umma duk samarin da suke cewa suna so na na wulaƙanta su, na kore su

Chapter 47 of 49