Share this page
Ko su na ba barinsu zan yi ba za mu dawo nan ne su nemi sana'ar yi." "Amma ina tsoron zama gida ni kaɗai ba kowa a kusa da ni." Shiru ya yi yana nazarin abun yi kafin ya ce . "Zan yi magana da Mallam Liman ya taimaka ma na da jikarsa A'isha, na ga jininki ya haɗu da yarinyar sosai har takan shigo ko?" Jingina kai ta yi tana cewa "A'isha mutumiyata ce ita takan shigo ita da kakarta, lokacin da nake siyar da gawayi ita take ɗaura mun." "Haka ne, zan nemi Alfarma wajen Mahaifinta ." "To na gode." Ta faɗa tana murmushi. "Yauwa kina ji na ko?" "Eh ina ji." Ta tattara hankalin ta da nutsuwar ya zuwa gare shi. "Akwai wata mata da take ba wa mata tallafin kuɗi domin su yi kasuwanci, jiya mun je tare da abokan zamana na wajen sana'ar. Mun same ta ta kuma yi alƙwarin taimakawa ma na, wato za ta ba Matayen mu jarin da za su yi sana'a. In sha Allah ina saka ran kina ciki. Na bayar da sunan ki da lambar wayarki za ki iya jin kira kowane lokaci. Cike da farin ciki take kallon sa tana murmushi. "Allah ya sa mu ji alkhairi." "Amin ya Allah." "Bari na je masallaci idan na hadu da Mallam Liman zan sanar da shi komai . Ruwa a buta ta kawo masa a buta ya yi alwala ya nufi masallaci. A daren ranar bayan an gama sallar isha'i ya sanarwa Mallam Liman zancen A'isha . Kai tsaye ya amince ma sa tare da yi masa addu'ar Allah ya sanya alkhairi. Washegari tun da asuba ya yi wanka ya shirya. Ya nufi masallaci don yin sallar asuba. Ana idar da Sallah bai zauna Kamar yadda ya saba zama ba, kasancewa tafiya da zai yi. Duk wasu muhimman abubuwan da zai bukata dama tun cikin dare ya haɗa su a cikin jakar kayansa . Sai kayan sakawar sa kala ɗaya ya ɗauka, su ma kayan ya ɗauka ne saboda kada Ma'eesha ta yi magana kai. Ba ta yi kokarin haɗa ma sa breakfast ba kamar yadda ta so, shi kuma ya ɗauka saboda zai yi asubanci ne ba ta yi ba, yayin da ita kuma ta ɓangaren ta babu komai a gidan na ci ne da za su ci ya saka ba ta yi wani yunƙuri ba. Kuma ta san ko da ta faɗa ma sa babu abun da za su ci a gidan bai da kudi sai dai ya kara shiga damuwa. Don haka ya yi shiru ba tare da da nuna damuwa ba. Ta rike ma sa jakar yayin da shi kuma ya lalubi sanadar jagoransa ya fara tafiya. Suna zuwa kofar gidan ya haka ta fita ya ce ta koma ba sai ta raka shi ba. Gani take yi kamar idan ya tafi ba zai dawo ba. Har ya fara tafiya sai ta rike hannunsa, ya kalli hannun ya kalle ta. "Gani nake yi kamar idan ka tafi ba za ka dawo ba, ina tsoron wani abu ya same ka yadda ka bani labarin garinku na tsorata da shi, idan na rasa ka ya rayuwa ta za ta kasance a wanan duniyar fa ba na da kowa?" "Kina da kowa Ma'eesha, ki jira lokaci in sha Allah wata rana sai labari, na yi ma ki alkawarin zan nemo ma ki dangin mahaifiyar ki s duk in da suke a faɗin duniyar nan." Murmushi ta yi tana goge hawaye ta ce . "Ta ina za ka fara neman su? Wacce ko ita mahaifiyar rawa ba ta san komai ba akan ta, tun tana yarinya karama aka kai ta gidan marayun, wanda ita ma bude ido ta yi ta ga kanta a cikin gidan. Kada ka yi ma ni alkawarin da ka san ba za ka iya cika shi ba." "Zan iya ." Ya faɗa cike da kwarin gwiwa. Murmushi kawai ta yi don ta san ba abu ba ne mai sauƙi. Sai da ya tabbatar ya kwantar ma ta da hankali ta samu nutsuwa sannan ya yi ma ta sallama ya tafi. Yana tafiya rataye da jakar da ya karba a hannun ta fatan hannunsa da sanadar jagoransa. Tana kallon sa har sai da ya ɓacewa ganinta sannan ta koma cikin gidan tana fashewa da kuka. Yana fitowa daga layin kasancewar gari bai yi gama haske ba, don haka ba mutane. Wata baƙar baƙar mota ce take gefen titi, kai tsaye ya nufi motar, kafin ya karasa matuƙin motar ya fito da sauri ya zo ya bude ka sa bayan motar. Shiga ya yi sannan ya rufe masa murfin ya zagaya mazaunin direba ya shiga tare da yi wa motar key. Kai tsaye hotel suka nufa, yana shiga ɗakinsa ya yi wanka. Ya shirya cikin tsadaddun suit black shirt din ciki White me sai tie Black and white. Sai ƙamshin tsadaddun turarensa yake yi, ya daura agogon hannunsa ya sanya takalmi. Ba jimawa ya gama shirin sa. Sai dai ya canza jaka, ba wacce ya bar gida da ita zai tafi ba, sannan kayan da ya dauko a can gidan ma ya bar su a can bai zo da su ba. Wayoyinsa da mahimman abubuwan da zai bukata ya ɗauka. Wayarsa wacce Ma'eesha ta siya ma sa ce ya ɗauka yana kallon wayar kafin ya kashe ta. Futowa ya yi ya nufi motar kai tsaya, direban ya bude ma sa da sauri cikin girmamawa. Kai tsaye suka nufi airport, wanda isar su ba jimawa jirgi ya tashi. Direban ya juya da motar ɗin don komawa, bayan jirgin su ya ɗaga. Ba wanda ya sanar wa zancen dawowar sa, don haka ba wanda ya yi tunanin dawowarsa. Sai bayan saukar jirgin su ne ya fito daga cikin jirgin. Cike da mamaki da al'ajabi yake kallon motar gabansa. A hankali ba cikin motar ya ziro ƙafarsa wajen yana sakar ma sa sanyayyen murmushi. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page6️⃣2️⃣ Sai bayan saukar jirgin su ne ya fito daga cikin jirgin. Cike da mamaki da al'ajabi yake kallon motar gabansa, a hankali na cikin motar ya ziro ƙafarsa wajen yana sakar ma sa sanyayyen murmushi. "Sadik?" "Na'am Yaya Jalal." "Wa ya faɗa ma ka tasowa ta?" "Babu na dai ritsa ka ne. Tun shekaranjiya da kuka yi waya fa Mom ka sanar da ita za ka dawo nan fa kwanaki biyu, shi ne yau na ce ko kwana ne sai dai na yi a airport amma sai na je na ɗaukoka." Ya yi maganar yana rungume Yayan nasa, hakan ya sa shi ma ya rungume shi . Sake juna suka yi yayin da da Sadik ya karɓi jakar hannun Jalaluddeen ya sa a bayan motar. Sannan ya bude wa Jalaluddeen gaban Mota wajen me zaman banza yayin da shi kuma ya zagaya mazaunin direba ya yi wa motar key suka bar airport ɗin. Yana tsaka fa driving yayin da shi kuma Jalaluddeen ya ya kunna wayoyinsa, amma bai kunna na wajen Ma'eesha ba. Hankalinsa na kan waya ne ya ɗago yana kallon Sadik, saboda ya san airport da gidan Ummee ba nisa, ya ci a ce sun karasa gida. Da mamaki yake kallon Sadik yana kuma kallon hanya,." "Kai Mallam ina za ka kai Ni ne?" "Gida mana." "Wannan ne hanayar gidan?" "Eh ma na, hanyar gidan iyayen asali ba na iyayen riƙo ba. Haka kawai kullum idan ka dawo daga tafiya sai ka sayka can?" "Sadik kana da rigima, yi ina kake so na sauka idan ba can ba?" "A'a gaskiya Yaya Jalal tun da Allah ya sa ka san cewa ba Ummee ba ce ta haife ka Mom ce ko? To ya kamata ko sau ɗaya ka yi ma ta abun da za ta ji cewa ita ma uwa ce tana da kai, ba komai ba nake so ka yi illa iyaka ka sauka a gidan kuma ka kwana tare da mu, mun gaji da sai dai ka zo ka gaishe mu na mintinan ka tafi. To yanzu ba wanann zuwan kana tare da mu dai gobe ka tafi can gidan. Amma fa ka kashe watoyin ka." Kafin ya yi magana har sun iso gidan Horn Sadik ya yi a kofar gidan , yayin da wani security taso ya wangale ma su katafaren tangamemen gate din gidan. Ya cinna hancin motar a katafaren gidan, kai tsaye parking lot ya nufa, in da aka tars manyan motoci na alfarma. Ke wajan . Fitowa ya yi bayan Sadik ya bude ma sa murfin motar Sadik ya ɗauki jakar kayansa suka nufi cikin gidan.. Ma'aikatan na ma sannu da zuwa ga hannu kwanan yake amsa ma su. Yana tura kofar tare da sallama. Mom wacce ta fito don uwa asibiti ta amsa tana kallonsa da mamaki. Don ba ta san ya iso ba, kuma ba ta yi tsammanin ganinsa a gidanta ba, don ko da ta faɗawa Sadik dawowar Jalal ta ɗsuka asibiti ya tafi ashe shi ɗauko Yayansa ya je ba. Ganin Sadik da jaka ya sa ta game cewa ɗaukimo Jalaluddeen ya tafi. "Mom ba ki ga yae8n ki ba, can na tafi na ce ko zan kwana a can sai na je na ɗauko shi na kawo shi nan zuwa gobe ya tafi can." "Yaushe wanna Gwaggon ta ku Maryam za ta bar shi ya kwana s nan." "Ba za ta san ya zo ba, ko ta sani ma menene ne ai ina ce nan ne guda. Mahaifinsa na asali ta isa ta hana shi shi ne?" "Amma yanzu ...." Sai ta fasa maganar da za ta yi . "Ya karasa har cikin falin Mom na kallonsa duk da ta ga ya nufo ta amma ba ta san nufin sa ba sai da ta ji ya rungume ta. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta saki, shi ma wani ƙaunar mahaifiyar tasa ne yake Ratsa zuciyarsa . Ya durƙuda kasa ya gaishe ta, ta amsa tana tambayar da aiki, ya amsa da Alhamdulillah. "Ka je ka yi wanka ka fito ka ci abinci." "Ina Sadduƙa?" "Ta tafi school." Ya nufi ɗakin da ya ga Sadik ya kai ma sa kayansa. Ta bi shi da kallo tana jin ƙaunar ɗan nata har ranta. _Fahad_ Bayan an yi discharging na Sidra a asibiti ya dauke ta ita da Nadra zuwa gida, kamar yadda Nadra ta buƙata. Baba da Mama da Inna kuma suka nufi gida tun da Sidra ta ki yarda ta bi su kuma Nadra ta roki Fahad ya amince ta bi su, ba shi da wani zaɓin da ya wuce ya amince ko don farin cikin Nadra. Yana driving Nadra na gefen sa yayin da Sidra ke bayan motar. Shiru ba abun da kake ji a cikin motar sai sanyin A.C da mayen turaren da Fahad ke amfani da shi. Har suka karasa gidan kowa ya kasa cewa komai. Horn ya yi Maigadi ya wangale ma sa ƙofa ya cinna hancin motar a cikin gidan. Bayan ya yi parking ne Nadra ta fara fitowa daga motar, sannan ta bude wa Sidra ta fito. "Sannu Aunty." Ta faɗa cike da kulawa. A hankali Sidra ta fito tana jinjina ma ta kai ba tare da ta amsa ba. Kayan da suka dawo da su daga asibitin Nadra ta dauka a bayan motar. Fahad ya fito ba tare da ya ce komai ba ya nufi kofar shiga fakon. Sai sam babu walwala s fuskarsa . Bude ƙofar ya yi ya matsa gefe alamar su shiga ciki. Da sallama a bakin Nadra ta shiga Sidra na bayanta, shi kuma ya take ma su baya. Kai tsaye upstairs ya nufa suna bayansa ƙarar taka step ya ji ya juyo ya kalle su. Ganin alamar cewa a sama Nadra ke niyyar ba wa Sidra masauki ne ya sa shi cewa. "A ƙasa masaukin baƙi yake ko kin manta ne?" "Yaya Fahad Aunty Sidra ce fa Yayata ce?" "Na sani shi ya sa nake tunatar da ke a ƙasa masaukin baƙi yake, ba wai don yayarki ba ko Yayata ce ta zo a ƙasa za'a sauke ta. Nan saman iya na ma su gidan sai ɗakunan yaran da za mu haifa in sha Allah." Yana gama faɗar haka ya ci gaba da tafiya zuwa ɗakinsa ya shige. Murmushi Nadra ta ƙaƙaro don son ta kwantarwa da Sidra hankali ta ce. "Na tuna ma Aunty ba ɗaki a nan sai ƙasa mu sauka na raka ki?" Wani kallo Sidra ta yi wa Nadra kafin ta ce . "Ban gane ba ɗaki ba, ko kin manta ni na faɗi irin tsarin da nake so sannan aka bi tsarin da na so wajen gina gidan . Ko kin manta da suna na aka gina gidan? Ɗakuna biyar ne a ciki, ɗaki ɗaki ɗaya naki ɗaya nasa sauran ɗakuna uku ba kowa a ciki shi ne ba za ku iya bani ɗaya na, ta yadda za ku dinga jin motsina ba? Ba komai na gode." Tana faɗar haka ta juya da sauri ta fara sauka daga matattakalar kai tsaye ta nufi ɗakin baƙi ta shige da sauri. _Jalaluddeen_ Yana shiga cikin ɗakin ya zube kan tangamemen gadon dake cikin ɗakin. Sanyin A.C da ƙamshin room freshner na ratsa shi. Kasancewar Sadik ya gyara ma sa ɗakin. Sai da ya kwashe tsawon mintuna ashirin kafin ya mike ya fara rage kayan jikinsa. Bathroom ya shiga ya wanda shi ma kansa abun kallo ne, tsaya wa ya yi yana kallon kansa a jikin tangamemen mirror dake jikin bangon banɗakin. Shi kansa ya san ya ɗan rame. Daidaita ruwan 🚿 dake bathroom din ya yi daidai yadda yake so bai yi zafi ba kuma bai yi sanyi ba . Shower gel ya ɗauka ya yi wanka da shi. Dai fa ya kammala wankan sannan ya fito sanye da bathrobe sai wani karamin towel da yake goge ruwan kansa. Jakar kayansa ya bude ya fito da ƙananan kayan da zai saka. Ya shirya cikin ƙananan kayan da ya zo da su a jaka ya fesa turarensa mai ƙamshi. Babu tunanin da yake yi kamar na Ma'eesha yadda ya fito daga gidan take kuka. Tausayinn ta mai tsanani ne ya kama shi . Ɗaya daga cikin wayoyinsa ya ɗauka ya lalubo wata lambar ya danna ma ta kira. Bugu ɗaya aka ɗaga daga can ɓangaren aka ce. "Barka da rana yallaɓal." "Barka dai Adamu ya kake?" "Lafiya lau sir." "Yauwa kamar yadda na faɗa ma ka za ka nemi mata guda biyu wadanda kake mu'amala da su, ka ba su Naira dubu ɗari biyar ₦500,000 su kai kuɗin zuwa ga gidan da na sanar da kai su faɗa wa matar gidan cewa tallafi ne wanda mijinta makaho ya sanar da ita za'a ba su." "Okay sir, yanzu ba sa nan sai zuwa yamma za su shigo garin, in sha Allah zuwa gobe da safe saƙon ka zai isa zuwa gidan da ka ce." "To na gode." "Ba komai Yallaɓal." Sallama suka yi ya katse kiran wayar. Yana ajiye wayar sai aka turo ƙofar da ƙarfi, ba kowa ba ce illa Sadiƙa ta shigo aguje ta shigo rungume shi cike da murna. "Yaya Jalala you are welcome." "Thank you." Sakin sa ta yi tana murmushi tare da cewa. "Wallahi yanzu Yaya Sadik ya kira ni yake sanar da ni, ai tuni na bar school na dawo gida saboda kai." Daidai lokacin Sadik shi ma ya shigo yana cewa "Food is ready." Gabadaya suka fita daga ɗakin suka nufi dinning area. Mom na zaune tana kallonsa yadda suka fito a jere fuskar kowannen su ɗauke da annuri. Farin ciki ne yake ji har kasan ranta. Masu aiki biyu ne tsaye a wajen suna jiran ma su gidan su buƙaci abun da za'a zuba ma su sai su zuba ma su. Sadik ne ya ja wa Ya Jalal kujera ya zauna sanan suka zazzauna. Ma su aikin ne suka yi serving na su bayan sun faɗi abun da suke so su ci. Kasa cin komai ya yi sakamakon tuna Ma'eesha da ya yi, shin ta samu abun da ta ci ko ba ta samu ba, don ya lura kwana biyun nan sai kame-kamen abinci take yi. Tsintar kansa ya yi cikin yanayi na rashin jin dadi wanda take komai nasa ya sauya. Tashi ya yi daga dinning area din ya nufi ɗakinsa. Da kallo suka bi shi ganin yadda ya sauya nan take. _Ma'eesha_ Bayan tafiyar mijinta ta zauna ta ci kuka ta ƙoshi, babu mai rarrashinta. Har sai da ta ji kanta ya fara ciwo sannan ta dakata, hatta idanun ta a kumbure suke. Gani take kamar za ta rasa shi, kuma su ma su motar duk da ya ce ma ta motar kaya ne a saman kaya zai zauna shin zai iya kula da kansa a matsayin sa na makaho a wanan doguwar tafiyar. Da wanan tunanin ta yini har rana ta fito ba ta yi breakfast ba. Bugu da ƙari ba ta da komai a gidan da za ta ci, kuma ba ta da ko sisi da za ta siya abun da za ta ci. Wasa-wasa har karfe biyu na rana ba ta ci komai ba, karshe ma zazzaɓi ne ya rufe ta ta kwanta saman katifarta. Wayar ta ta janyo ta lalubo lambar makaho amma switch off. A haka har ya fara rawar sanyi ta duƙunƙune kanta. Addu'o'i kawai take yi a cikin zuciyarta tana addu'ar Allah ya yaye ma ta ya kare ma ta mijinta a duk in da yake. _Sidra_ Tana nufar ɗakin baƙi maganar Fahad ne ke yi ma ta amsa kuwa a cikin kunnenta. 'Nan saman iya na ma su gidan ne dai ɗakunan yaran da za mu haifa in sha Allah.' Tana shiga dakin ba ta rufe kofar ba ta zube a ƙasa, Nadra da ta kasa motsi ta jiyo sautin faɗiwar abu timm. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t 🌲🌳🌿☘️ *TALLAH!* *DA MAGANI A GONAR YARO!!* *08089965176* *07084653262* *Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.* *Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.* *07084653262 ko* *08089965176* *SIYAN NAGARI!!!!!!* *A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH* 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page6️⃣3️⃣ Tana shiga ɗakin baƙin ba ta rufe kofar ba ta a ƙasa. Nadra da ta kasa motsi ta ji yi sautin faɗiwar abu timm. Da hanzarin ta sauko daga matattakalar, ɗakin ta nufa kai tsaye har da ɗan gudun ta, tana shiga ta yi tozali da Sidra kwance ba ta motsi . Durƙusawa ta yi akan ta tana kuka tana jijjiga ta tare da kiran sunan ta . "Wayyo Allah na Aunty Sidra ki tashi don Allah Aunty Sidra ." Ta mike daga durƙuson da take ganin Sunyi Sidra ba ta mike ba ya sa ta nufi upstairs tama ihun kiran sunan Fahad. _Jalaluddeen_ Tun da ya kasa cin abinci a dinning area ya shiga ɗakinsa ya zauna kan gadon. Sai kuma ya mike ya tashi ya rufe kofar ta hanyar mirza wa kofar key ya bar key din a jikin ƙofar. Wayar da Ma'eesha ta siya ma sa ne ya ɗauka tare da lalubo lambar wayar ta. Kira ya danna ma ta zuwa lokacin gabansa ya ji yana faɗuwa. _Ma'eesha_ Tana nan kwance tana rawar sanyi ne ta ji ringing din wayar , duk da dai ba ta ga ko sunan waye ba amma dai ta lulubi wayar ta sannan wajen amsa kira tana kara wayar a kunne. "Assalamu alaikum warahmatullah." Ta ji saukar muryarsa mai amo a cikin dodon kunnenta. Ba ta san lokacin da ta bude kumburarrun idanunta ba tana cewa. "Wa'alaika Salam warahmatullah." Muryarta da ya ji ba ta fita sosai kuma tana wayar kamar wacce take a galabaice ya saka shi cewa. "Ma'eesha lafiya kike kuwa?" Da kyar ta iya cewa . "Lafiya lau nake kada ka sami damuwa ba komai." "Kamar ua ba komai bayan muryarki ma ta nuna cewa kina cikin mawuyacin hali , ba ki tana yi ma ni karya ba kada ki soma a yanzu ." Dafe kanta dake sara ma ta ta yi kafin ta ce. "Kaina ke ciki amma kada ka damu zan wartsake In sha Allah." "Kin ci abinci ne?" "A'a ban ci ba." Shiru ya yi kafin ya ce. "Ba abuncin ko?" "Eh." Ta ba shi amsa a taƙaice. Wanda take idanunsa suka sauya ya katse kiran wayar . Daya daga cikin wayoyinsa ya ɗauka ya kira wata lamba, ana ɗagawa cikin bayar da umarni ya fara magana . "Adamu ba lokacin da zan tsaya jiran sai wasu sun dawo. Yanzu ba sai an jima ba ka nemi wasu matan guda biyu ja ba su saƙon ka sanar da su yadda za su yi sannan idan sun fito daga gidan ja biya su hakkin aikin da suka yi. A tare za ku je ka jira su a wajen gidan. Yana gama faɗar haka ya kashe wayarsa ya ajiye gefe, tausayi da kewar Ma'eesha suka addabe shi. Ma'eesha kam dama da kyar take amsa ma sa don haka ta saki wayar tana dafe kanta Bayan kamar mintinan arba'in kenan sai ta dinga jin sautin sallama a tsakar gidan , Da ƙyar ta iya amsawa da muryarta da ba ta fita sosai. Ta yunƙura ta tashi zaune, hijabiinta ta laluba ta saka, sannan ta dafe bango tana tafiya . Ta bude kabulen daidai lokacin daidai lokacin da suke sake yin sallama. Ta amsa suna haɗa idanu da matan guda biyu. "Sannun ku bayin Allah." "Yauwa sannu." "Nan ne gidan Khalifa Makaho?" "Eh nan ne." "To ina fatan ya sanar da ke zancen tallafin kuɗi da ake ba wa mata don su yi sana'a su dogara da kansu." "Eh ya sanar da ni ya bayar da sunana ina sha Allah za mu samu." "Haka ne." Wata karamar jaka suka mika ma ta suna cewa ta samu dana'ar da za ta yi don dogaro kai. "In sha Allah.." Ta karba tana yin godiya zuciyarta cike da murna Komawa ta yi cikin ɗakin ta juya kuɗin. Bandir ɗin Naira dubu ɗaya ne guda biyar, wato Naira dubu ɗari biyar kenan. Farin ciki ya cika ta ta ɗebi wasu daga cikin kuɗin ta mayar da saura.n a leda ta saka cikin akwatin kayan ta . Daidai lokacin ta ji sallame A'isha. Hamdala ta yi tana jingina da bango ta amsa sallama. A'isha ta shigo tana cewa. "Sannu Aunty ina wuni ." Ta amsa na ta sanan ba kuma ma ta dubu ɗaya ta ce . "Ki siyo mun milo da madara da sigar." "Aunty bread fa,?' "Ba zan iya ci ba ku siyo mun kawai na sha yunwa nake ji ban karya ba." ,"subhanah har rana ta yi?" "Ba na jin dadi ne." Da hanzarin A'isha ta fita daga gidan don zuwa siyo manta kayan tea. Ba jimawa ta dawo ta shigo da kayan tea din a cikin baƙar leda. Ta duba flaks cikin ikon Allah ta samu akwai ruwan zafi a ciki. Nan da nan ta haɗa ma ta tea. Ita ta taimaka ma ta ta je ta wanke baki, sanan ta ba ta ruwan tea ɗin ta

Chapter 36 of 49