Share this page
wallahi." "Ma sha Allah. To meye labari ?" "Labari mai daɗi kuwa." "Fada mani ina jin ki." "Wadanda ka ce za su ba mu tallafin nan ne suka kawo ma na kudi ma su yawa har Naira dubu ɗari biyar." "Cikin nuna jin dadi da murna ya ce. "Alhamdulillah Allah ya saka ma shi da alkhairi." "Amin Mijina." Yanzu abun da za'ayi ki ɗauki kamar dubi ɗari uku ki shiga da su kasuwa ki je ki siyo kayan abinci ma su kyau da inganci. Kamar yadda kika yi a baya lokacin da kika siyar da wayarki." "A'a wanan fa an ce mu yi sana'a ne aka ba mu jari." "Dubu ɗari biyu da ya rage sau mu yi shawarar sana'a da za mu yi idan na dawo ko?" "To shi kenan yadda ka ce haka za'ayi." Ka isa lafiya? Ka samu danginka cikin wadanda aka ce sun dawo?" "Ba sa ciki ba kowa nawa." Cikin sanyin jiki ta ce. "Allah ya bayyana ma ka su a duk in da suke, Allah ya haɗa fuskokin ku." "Amin na gode." "Yanzu yaushe za ka dawo?" "Ina ganin zuwa jibi motar da na biyo za ta dawo, don haka ita zan biyo." Fira suka tana daga bisani ya yi ma ta sallama ya kashe kiran wayar. _Nadra_ Tana barin ɗakin Sidra koma ɗakin Fahad, ta ji saukar ruwa a bathroom alamar yana wanka. Kitchen ta nufa don ɗora ma su abun da za su ci. Nan da nan cikin ƙanƙanin lokaci ta dafa ma su jallop ɗin superghetti da ya ji kayan lambu da bisashen kifi. Sai farfesun kayan ciki wanda ya ji kayan ƙamshi. Bayan ta zuba a cikin kula ne ta kwashe su ta jera a dinning table. Daidai lokacin ana kiran sallar magrib kenan ta kammala. Fahad wanda ya fito da niyyar zai je masallaci ya ji ƙamshi girkinta. Tana kokarin barin dinning area suka hadu. Murmushi suka sakar wa juna kafin ya ce. "Sannu da aiki." Madadin ta amsa sai ta ce ma sa a dawo lafiya, kafin ta nufi ɗakinta. Wanka ta yi sannan ta ɗauro alwala ta gabatar da sallar magrib. Tana nan jan sallaya ba ta tashi ba, karatun Alkur'ani take yi har sai da aka kira sallar isha'i ta tashi ta gabatar da sallar isha'i ta yi addu'o'i sannan ta mike tsaye ta cire hijabiñ da ya yi sallah da shi . Rigar material ne a jikinta ɗinkin doguwar riga ce. Kai tsaye ta nufi falonta daidai lokacin yana dawowa sallah. Nadfah yunwa nake ji." Kallonsa ta yi alamar ba ta bane sunam danya kira ta sa shi ba ne "Wa na ji ka kira ne?" "Ke na kira ma na, ba ki ji na ce Nadfah ba?" "Shiru ta yi tana nanata kalmar a ranta. 'Nadfah.' Wato farkon sunan ta na nasa ya haɗa kenan NAD+FAH =NADFAH. Nurmushi ta yi sakamakon sunan da ya yi ma ta daɗi sosai da sosai ta ce. "Ga abinci na jiranka. Mu je dinning area na zuba ma ka, daga nan sai na kira Aunty Sidra ta fito mu ci abinci ." Ji ya yi ransa ya ɓaci sakamakon kiran sunan Sidra da ta yi. Amma gudun kada ya ɓata ma ya rai tun da ya fahimci tana son ƴar uwarta sosai ya sa ya ce. "A gajiye nake ba zan iya fitowa zuwa dinning area ba please ki kawo mun nawa a ɗakina, amma fa dai kin taya ni ci." Ya yi maganar yana murmushi. "Ayyah sorry, to bari ba kawo ma ka ko?" Ta yi maganar tana wucewa don kawo ma sa abincin nasa. Shi kuma ya shiga cikin bedroom ɗin sa. Bayan kamar mintuna biyar sai ga ta ta dawo da ba tire a hannunta wanda ta jera abincin da abun sha da kofi da spoon. Yana zaune yana jiranta daga shi sai singileti da gajeren wando. Yana zaune kan sofa dake cikin bedroom ɗin nasa. Ajiyar abincin ya yi kafin ta janyo stool dake gefe ta ajiye a gabansa danna ta ɗora abincin. Jallop ɗin superghetti ne da ta dafa ya ji kayan lambu fa busashshen kifi. Ta zuba ma sa lemu da ruwa sannan ta ce. "Ina zuwa?" "Ai tare za ki zauna mu ci ." "Okay just 5 minutes zan dawo." Ta faɗa tana murmushi ta fice daga ɗakin hannunta rike da wayar ta. Ƙasa ta sauka ta nufi ɗakin baƙi. Nan ta samu Sidra na ta kai wa da komowa. "Assalamu alaikum." "Wa'alaiki salam." Zama ta yi bakin gadon tana cewa. "Sannu Aunty Sidra." "Yauwa sannu. Na ga kin dade baki dawo ba ko kina tare da Fahad ko?" "A'a Aunty da na bar nan kitchen na je ba yi girki, da na gama ne na aka kira sallar magrib na je na yi, kuma kin san baka tashi daga magrib sai na yi isha'i. Yanzu na fito don na tambaye ki nan zan kawo ma ki abincin ki ne?" "Ku a ina za ku ci?'" "Ya ce tare za mu ci a ɗakinsa?" Sai da ta ji zafi a zuciyarta kamar an watsa ma ta garwashin wuta kafin yi ƙoƙarin daidaita nutsuwarta ta ce. "Yanzu zuwa wajansa za ki yi?" "To Aunty Sidra ya zan yi?" "Hmm yanzu haka za ki bar ni ki je can wajensa ki bar ƴar uwarki da take cikin halin jinya tana bukatar taimakon ki? Kuma kin san bai kamata ki bar ni na kwana ni ƙaɗai ba, saboda ba'asan me zai faru cikin dare ba ko ciwon nawa zai iya tashi ba kowa a kusa da ni, wata kila ma sai dai ki ga gawata da safe." Ta yi maganar tana fashewa da kuka. Cikin rauni Nadra ta rungume ta tana rarrashin ta. "Dan Allah Aunty Sidra ki daina fadar haka ba abun da zai same ki ina tare da ke in sha Allah." Tana gama faɗar haka ta fice daga cikin ɗakin yayin da Sidra ta zauna sai cika take yi tana batsewa. Ba jimawa sai ga ta ta dawo da tire a hannunta wanda ta jera wa Sidra abinci. "Aunty ga abincin nan ki fara ci kafin na dawo." Sai da ta buɗe ma ta abincin ta saka ma ta fork ta zuba ma ta ruwa da lemu sannan ta fice daga ɗakin. Da sallama ta shiga ta samu Fahad na zaune waya yake yi abincin na nan gabansa bai fara ci ba. Zama ta yi gefen sa tana kallon sa har ya gama wayar sannan ta ce . "Yaya ba ka ci abincin ba." 'Ke nake jira." Murmushi ta yi kafin ta saka fork cikin plate ɗin abincin. Shi ya dinga ba ta a baki har sai da ta ƙoshi. Ganin haka ita ma ta fara ba shi suna fira har ya ce ya ƙoshi. Tattara kayan ta yi ta kai kitchen ta wanke sannan ta dawo. Sanin halin ta yanzu za ta yi ma sa zancen Sidra ko ta ce za ta tafi wajen ta ya sa ya rufe ƙofar ya murza key. Za ta yi magana ya ce. "Na yi ma ki dukkan wasu alfarma da kika nema akan Yayar ki. To yanzu lokaci na ne, dama ai kin yi ma ni alƙawari kin tuna? Rashin lafiyar Yayarki ya tsayar da komai." Shiru ta yi tana tuna kalaman Sidra. Ba ta ankare ba ta ji ya ɗauke ta ya yi sama da ita, kai tsaye bathroom suka nufa. Wanka suka yi a tare sannan suka fito daga banɗaki ya naɗo ta cikin towel kamar baby. _Jalaluddeen_ Da misalin ƙarfe huɗu da rabi na yamma bayan ya dawo masallaci, wanka ya shiga ya yi sannan ya fito sanye cikin bathrobe (Rigar wanka) yana tsaye a gaban dressing mirror yana kallon kansa. Wayarsa ya ɗauka gaban dressing mirror ɗin wacce yake waya fa Ma'eesha. Kira ya danna ma ta bugu biyu ta ɗaga. Cikin zazzaƙar muryarta ta yi ma sa sallama . Sai da ya lumshe idanu cike da kewarta ya amsa ma ta sallamar. "Ina wuni mijina?" "Lafiya lau ya kike ya gidan?" "Gaskiya duka ba lafiya ba. Don ta ina zan yi lafiya ba ka tare da ni, sannan kuma gidan ma duhunsa nake gani domin fitilar dake haska ma ni gidan baya tare da ni?" "To ina fitilar ya faɗa ai sai ki neme shi?" "Kai ne fitilar ai, idan ba ka nan gidan Lami ne, sai yanzu nake jin maraici a tare da ni." "Kuyi hakuri zan dawo in sha Allah. Kin siya abincin ?" "Wani abinci ?" "Kin manta na ce ma ki cikin dubi ɗari biyar din nan ki cire dubu ɗari uku ki siye kayan abinci kamar yadda kika siye da kika siyar da waya." "To an ce mu yi sana'a ne, idan ba mu yi sana'ar ba kuɗin karewa za su yi." "Allah na nan, kuma ba haka za mu dawwama ba." "Na sani amma Allah ya ce ka tashi in taiamake ka, kai ga ka ba gani kake yi ba, ballantana na ce za ka yi sana'a da kuɗin, mutane cutarka kawai za su yi . Sai dai..." "Ma'eesha." "Na'am." Ta amsa tana sauraron abu zai fito daga bakinsa. "Ki yi abun da na ce ma ki." "To sh ke nan, yadda ka ce haka za'ayi ." Sallama ya yi ma ta ya katse kiran wayar. Ya shafa tsadadden man shafawarsa sannan ya shiga ciinin closet ɗin sa . Ba nunawa ya fito sanye da cikin rigar suit baƙa na cikin fari ya ɗaura tie Black and white. Sai ƙamshi yake bazawa. Ya ɗaura tsadadden agogon hannunsa. Wayarda Samsung Galaxy Z fold 5 wacce kuɗin wayar Naira miliyan biyu da dubu ɗari Shida. 2, 600,000. Ya saka a aljihun rigar suit ɗinsa. Bayan ya saka Safa da makami ne ya saka baƙin glass a idanunsa. Daidai lokacin Yasmeen ta yi knocking. Izinin shigowa ya ba ya ta shigo da sallama. Ya amsa ma ta ba tare da ya kalle ta ba, yana duba sako a cikin wayarda ta aiki. Reply ya yi sannan ya sa wayar a aljihun wandonsa. Kallon Yasmeen ya yi ta yi shirin ta cikin material fari da baƙi don shi ne ankon da suka yi . Ganin kayan ya matse ta ne ya sa ya ce. "Ki ke ki sauya kayan jikinki ?" Kamar za ta yi kuka ta ce . "Yaya Jalal wallahi wanan ne ankon ka yi hakuri don Allah." "Ban hana ki fita da kayan da suka matse ki ba?" "Ka hana?" "Ban isa ba kenan shi ya sa ba ki daina ba." "Wallahi ka isa ka yi yawa ma, amma wanan ne ankon kuma tailor din ne ba ni na ce ba." "Ki je ki saka after dress." Da sauri ta fita sanan ya nufi hanyar fita. A falo suka hadu ya yi gaba ta bi bayansa. Don Ummee ba ta gidan ma. Ɗaya daga cikin motocinsa wanda ya sa aka wanke ma da ne ya shiga. Ita ma ta shiga ta zauna gefensa, sai dai ba walwala a fuskarta ganin ta rufe adonta. "Ina ne wajen taron?" Ta sanar da shi tana ɓata rai. Kamar bai san tana yi ba ya yi wa motar key yayin da maigadi ya wangale ma su gate ya fice daga gidan. Kai tsaya wajen taron suka nufa. Ya yi parking a wajen da aka tanada na parking motoci. Daidai yana fitowa daga cikin motar suka yi idanu biyu da Nasreen ƙawar Ma'eesha, tana sanye da ankon irin na Yasmeen ,wacce fitowar ta kwanan daga wata motar da aka yi parking. Sakin baki ta yi tana kallon Jalaluddeen da matsanancin mamaki. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page6️⃣6️⃣ Daidai yana fitowa daga cikin motar suka yi idanu biyu da Nasreen ƙawar Ma'eesha, tana sanye da ankon irin na Yasmeen, wacce fitowar ta kenan daga wata motar da aka yi parking. Sakin baki ta yi tana kallon Jalaluddeen da matsanancin mamaki. 'Khalifa Makaho?' Ta faɗa a ranta idanunta akansa. Tabbas ya shiga ruɗu sakamakon ganin aminiyar Ma'eesha. Amma dai ya dake ya basar kamar bai taba sanin ta ba. Yanayinsa ba zai taba nuna halin da ya shiga ba, amma tabbas ya yi nadamar zuwa wajen nan. Kau da kansa ya yi ya rufe murfin motarsa ya yin da Yasmeen ta fito ta zagayo gefensa tana murmushi. "Mu shiga ciki." Ta yi maganar tana rike hannunsa suka fara tafiya. Dariya Nasreen ta yi har yana tafa hannu tana kallon su har suka shige ciki. _Fahad_ Bai sauke Nadra ko ina ba sai tsakiyar gadon. Daga nan ya haura saman gadon shi ma ya ja ma su bargo ya rufe su. Towel din jikinta ya warware za ta yi magana ya haɗe bakinsu waje ɗaya. Hannu ya kai jikin kan gadon ya rage hasken ɗakin, take duhu ya mamaye ɗakin. Tsoro da fargaba suka ziyarce ta amma idan ta tuna huɗubar da Aunty Rahama ta yi ma ta sai ta fara kokarin kawar da tsoron da take ji. Bakinsu ya haɗe waje guda ya fara aika ma ta da zazzafar kiss, wanda babu ɓata lokaci ta fara mayar ma sa da martanin abun da yake yi ma ta. Take saƙon ta ya fara isa gare shi ya kuma yi tasiri a jikinsa. Tsawon mintinan shida suka dauka suna yi tsotson bakin juna cikin raɗa ya ce . "I love You Nadra." "Love You too Yaya Fahad." Hannunsa ya sa ya shiga shafa fatar jikinta daga sama har ƙasa ta ko ina a jikinta. Musamman ƙirjinta da yake cike da dukiyar Fulani masu ɗaukar hankalin mai kallon su. Ya kai bakinsa ya fara tsotson su har jikinsa na rawa kamar mazari. Ita kanta yau ta ji tana bukatar mijinta, don magungunan gyaran da Sunyi Rahama ke ba ta ne yake yi ma ta aiki. Don ba karamin ni'ima ya sakar ma ta ba. Duk ta gama jiƙewa. Sai da suka kai junan su ƙololuwar buƙatuwa da juna sannan ya karanto addu'ar saduwa da iyali ya shige ta. Sai da suka yi ihu tare ita na zafin da ta ɗan ji shi kuma na daɗi ya yi. _Sidra_ Jin Nadra shuru ba ta dawo ba ya sa Sidra hankalin ta ya tashi. Don yanzu ta fara tsorata da wanan lamari. Don tabbas ta fara hango soyayyar Nadra a idanun Fahad kamar yadda ta ga soyayyar Fahad a idanun Nadra. Ta tasa yaushe ne suka kamu da soyayyar juna. Don kama yanzu ba tsana ko ƙiyayyar ɗaya daga cikin su akan ɗaya. Haka kawai ta ji jikinta bai ba ta ba wanda hakan ya sa ta tashi da sauri ta fita daga ɗakin. Ta baya ta zagaya daidai saitin window na ɗakin Nadra jin shiru ne ya sa ta zagaye ta window na ɗakin Fahad. Abun da kununuwan ta suka jiyo ma ta ne ya yi sanadiyar ɗaukewar numfashinta na wucin gadi. Domin numfashin su take ji gami da gurnanin mai haɗe da ihu da Fahad ke yi ya wanda hakan ya sa Sidra shhga tashin hankali. Toshe bakinta ta yi dan kada sautin kukan nata ya fito ta bar wajen a guje. Ikon Allah ne ya kai ta ɗakinta wanda shigar ta kenan ta faɗa kan gado tana fashewa da matsanancin kuka mai ƙona zuciya. "Shi kenan ta ƙare mun na shiga uku na lalace. Ya mafarkina ke shirin rugujewa lokaci daya ne? Dama na zo gidan nan ne don na kwashi bakin ciki da kunci?" Kai ta girgiza da sauri tana cewa. "Ina ba zai yiwa ba Wallahi hakan ba za ta faru ba, Nadra ba za ta taba yin nasara ni kuma na fadi ba. Saboda ba abun da ta fi ni da shi." Haka ta dinga kuka tana Surutai ita kaɗai kamar wata mahaukaciya. _Nasreen_ Cike da mamaki da al'ajabi na Khalifa Makaho da ta gani a wajen taron Centre ta ciro wayar ta a jaka. Lambar ya wayar Ma'eesha ta lalubo ta danna ma ta kira, sai dai cikin rashin sa'a har sau biyu tana kiran wayar Ma'eesha ba ta ɗaga kiran wayar ba. Saurayin da suka zo tare ne ya ce . "Lafiya kuwa?" Sai da ta yi dariya sanan ta ce . "Kada ka damu, ƙawata ce aka yaudara aka cuce ta nake son sanar da ita gaskiyar da ba ta sani ba." "Ban gane ba." "Ba za ka gane ba dama. Ka manta kawai ba zai amfane ka da komai ba." Tana gama faɗar haka ya ja hannunta suka shiga cikin wajan taron. Suna shiga ciki ta hangi Angon na dosowa wajan Jalaluddeen, yana isowa ya rungume shi yana cewa. "Jalaluddeen kana ƙasar nan dama?" "Wai dama kai ne kake aure yau?" "Eh ma na na ɗauka saboda ni ka zo." "A'a rakiya kawai na yi ban san mai ne ango ba ma." " Tun da muka gama karatu fa ba ku sake haduwa ba ko? Mun hadu ma na sau ɗaya a ƙasar Canada." "Haka ne to ya aiki ya iyali?" "Ban yi aure ba har yanzu ina dai kan hanya." "To ma sha Allah, Allah ya kawo lokaci na alkhairi." Daga nan suka rabu ango ya koma wajen da aka tanadar dan shi da amaryarsa. Yayin da Jalaluddeen ya koma ya zauna kusa da Yasmeen. Yana zama sai ya lura da Nasreen na ɗaukar su photo. Ya basar kamar bai ganta ba. Ana ta Shagali mawaki ya waƙe amarya da ango an yi rawa da waka. An yi wa amarya da ango liƙin kuɗaɗe ciki kuwa har da Jalaluddeen. Don ba karamin kudi ya yi ma su liƙi ba kuma ƴan dubu ɗaya ne kuɗin da ya yi ma su liƙi. Bayan wani lokaci an fara cin abinci yayin da kowa ke cin abin da ransa ke so ne Nasreen ta zagaya ta wajan Amarya. "Ke kalli wancan Mutumin kin san shi ne?" "Ta yi maganar tana nuna ma ta Jalaluddeen wanda ke kare da waya a hannunsa tana magana." Dariya ta yi sannan ta ce "Okay Jalaluddeen kike nufi ki? Kin ga handsome guy kin ƙyasa ko? To ki cire rai domin ana shirin aurensa kwanan nan ne. Da ba don tsaiko da aka samu ba su da yanzu ya dade da angocewa ba." "Ba sunan sa Khalifa ba? Sanan yana gani ba Makaho ba ne?" Sai da ta yi dariya kafin ta ce "Wani Khalifa kuma wani Makaho kuma? Ko dai ya yi ma ki kama da wani ne?" "Ba wani kama na tabbatar shi ne kuma sai na toni asirinsa ." Dariya kawai ta yi don tana yi wa Nasreen kallon wacce ba ta cikin hayyacinta. Kafin a tashi taron Jalaluddeen ya ce wa Yasmeen ta tashi su tafi yamma ta yi. Ba musu za su bar wajan duk idanun Nasreen nan kan su. Ita kanta ta matsu su bar wajan saboda ta lura da yadda Nasreen ke yi wa Jalal kallon ƙurilla wanda ya da ran Nasreen ɓaci. Don kishinsa take yi, a tunanin ta Nasreen na kallon Jalaluddeen ne saboda tana son sa. Har sun yi nisa ta juyo ta watsawa Nasreen wani banzan kallo mai haɗe da gargadi sannan ta bar wajan. _Mamy_ Cikin tashin hankali take bincike a cikin ɗakinta. Gabaɗaya gwala-gwalai da ta tara babu ko ɗaya, hatta kuɗaɗen da take ɓoyewa a ɗakinta ba ko sisi. Cikin tashin hankali ta nufi in da ta ajiye ƙadarorin Dady. Kasancewar yanzu baya da kataɓus a gidan sai abun da ta ce ya da ta karɓi takardun fiye da ƙadarorinsa da ta mallaka. Wasu ma sunan Ma'eesha ne a jikin takardun. Ɗora hannu ta yi a saman kai tana fadin ta shiga uku. Domin ta san ba mai shigo ma ta cikin ɗaki sai Laila. Ita kadai ce take shigo ma ta ɗaki don ko Jamil bai cika shigo ma ta ɗaki ba. Cikin tashin hankali ta lalubo lambar wayar Laila ta danna ma ta kira, sai dai har ya katse ba ta ɗaga ba. Sau uku tana kira ba ta ɗaga ba. "Allah ya sa yarinyar nan ba ta salwantar da ƙadarorin nan ba." _Laila_ Tana zaune a gaban motar Taj ta kalle shi ta ce . "Wai yaushe za mu bar ƙasar nan ne mu tafi ƙasashen da aka ce yawon shaƙatawa. Sannan kuma yaushe ne za mu yi auren?" "Kada ki damu idan kin gama tattaro duka dukiyar muka tara su na tabbatar za mu ishe mu mu yi rayuwar mu a can ba tare da har jikokin mu sun yi talauci ba." "To zan dai sake bincikawa amma na tabbatar na kawo ma ka kaso saba'in na dukiyar gidan." "Ba iyakar su kenan ba ki sake gwada wa ki tabbatar kin gama kwashe komai kuɗaɗe da kadarori da gwala-gwalai. Ba kin ce yanzu ba komai a wajen Dady ba duk Mamy ta amshe komai?" "Eh na kawo ma ka duk wasu takardun duk rabi na takardun sunan ƴarsa Ma'eesha ya saka, kuma yanzu na Mamy ta raba shi da ƴarsa Ma'eesha ka ga ba mai gadon dukiyar ko?" "Mu za mu gaje su mu je mu yi bushasha" "Don Allah kada sai na gama tattara komai na mallaka ma ka don mu je mu yi rayuwar mu a can kamar yadda ka ce daga baya ka juya ma ni baya ka guje ni" "Haba ni ba bututu ba ne, ki daina tunanin hakan ?" Murmushi ta yi tare da cewa. "I love You?" "Love you more." Kallon takardun da ta kawo na sa yau ya yi sannan ya ce. "Ana jira na zan iya tafiya?" "Eh za ki iya sai gobe idan mun hadu sai mu sake tattaunawa." Fitowa ta yi daga cikin motar ta shiga motarta wacce a baya mallakin Ma'eesha ce kafin su raba ta da shi . Tana fita ya fara duba takardun sannan ya kira Jalaluddeen a waya." Lokacin Jalaluddeen na driving za su koma gida shi da Yasmeen, ya ga kiran yaron aikinsa ya shigo wayarsa. Parking ya yi a gefen hanya sannan ya fito daga cikin motar ya bar Yasmeen a ciki. "Hello Taj." "Hello sir, barka da yammaci sir." "Yauwa Barka dai , an kara samun wasu abubuwa daga yarinyar ne?" "Eh Yallaɓal ga wasu takardun nan yanzu ta kawo, wasu sunan Ma'eesha ne a jiki, wasu kuma sunan Mahaifinta bai Mallaka ma ta su ba." Jinjina mai Jalaluddeen ya yi kafin ya ce . "Da kyau Taj aikinka ya yi kayu, dama na san za ka iya shi ya sa na saka ka. Ka ajiye takardun zuwa jibi zan dawo sai ka kawo ma ni su na haɗa su tare da waɗan can da ka karɓo.." "Okay Sir." "Yanzu a cikin waɗan nan takardun da ka kawo ma ni ba takardar Kamfani a ciki?" "Gaskiya babu." "Zuwa gobe ka bincike ta ta nemo ma ka wannan takardar, don Ma'eesha ta taɓa ba ni labarin kamfanin, duk da ya zama mallakin Mahaifiyarta ne shi mahaifin dama ko da ya siye kamfanin fama kamfanin ya mutu sai an raya shi, kuma amma takardun suna gidan duk yadda za'ayi ka saka ta nemo wannan takardar." "Ina tunanin daga ita har Mamy ba su san da kamfanin ko takardun su ba." "A yadda suka mayar da Dady ba zai ɓoye ma ta komai ba, don haka ka sa ta nemo shi yana da mahimmanci sosai." "Okay sir, in sha Allah zan saka ta kawo su." Sallama suka yi ya katse kiran wayar sannan ya shiga motar ya yi ma ta key ya fara tafiya. Kallonsa Yasmeen ta yi ganin lokaci daya yanayinsa ya sauya sai ta fasa ma sa maganar da ta yi niyya, don ta san halinsa idan ransa ya ɓaci ba za ta ji dadi ba, barinsa shi ne mafi sauki." Har suka isa gidan ba wanda ya yi magana, horn ya yi maigadi ya wangale ma sa gate ya shigar da motarsa ciki. Satar kallonsa ta yi kafin ta ce . "Thank you my husband to be..." Kallon ta ya yi ta fita da sauri tana murmushi. Tura hannunsa ya yi cikin suman kansa yana yamutsawa. Sannan ya kifa kansa kan sitiyarun motar. Tsawon mintuna biyar har motar Abbi ya shigo direban Sa ya yi parking ya buɗe ma sa ya fito. Har zai wuce ciki ya lura da motar Jalal da ke kunne. Ya karasa jikin motar ya yi knocking glass ɗin. Sai a lokacin Jalal ya ɗago tare da sauke glass ɗin motar. Ganin Abbi ne ya sa ya bude murfin motar ya fito. Cikin kulawa Abbi ya ce . "Son kana lafiya dai ko?" "Alhamdulillah Abbi ." "Ka tabbata ba wata matsala?" "Bo komai Abbi kawai dai na gaji ne." A tare suka jera suka shiga cikin gidan suna fira. *Washegari* Suna zaune a babban falon gidan suna fira. Abbi, Ummee, Jalaluddeen, Yusuf, da kuma Yasmeen. Fira suke yi cikin nishadi, kafin suka ji horn ɗin mota. " Ganin karfe uku ne ya sa Ummee cewa. "Ko Yaya ya iso ne?" Ta yi maganar tana kallon Abbi. "Ina ganin ya iso don lokacin da ya faɗa kenan yanzu." "Lafiya dai ko Abbi?" Cewar Yusuf yana kallon Abba. "Lafiya lau Alhamdulillah, abun farin ciki ne ma za mu ƙulla." "Alhamdulillah. Wani abun farin ciki muka samu?" "Muna son gobe a ɗaura auren Jalal da Yasmeen yake so a tattauna." Da sallama Dad ya shigo

Chapter 38 of 49