da ni kike yi?"
"To ka tsaya na daina."
Zuba ma ta idanu ya yi ya rungume hannayensa a ƙirjinsa.
"Kin ga na fahimce ki ba yadda kike tunani ba ne, na ina nuna ma ki halin ko in kula ba ne, kawai dai yanayin aiki ne ya sa ba na da lokacin da zan dinga kiran ki ko kuma ke ki kira ni ki same ni. Amma ai ba dole sai ta haka nan ne za ki yarda ina son ki ba, ita soyayya a zuciya take, fatan kin fahimce ni, kina zuciyata kowane lokaci kowane hali kar ki manta da wanan ."
"Son lokaci ya yi fa jirgi baya jira."
Ya ji Muryar Abbi yana ma sa magana.
Wayarsa ya ɗauka ya yi ma ta transfer na kudi a account din ta sannan ya ce.
"Sai mun yi waya ki kula da Kanki."
Murmushi ta yi sanan ta bi bayansa suka koma wajen da su Abbi ke jiran su.
_Nadra_
Bayan kukan da ta yi akan abun da Sidra ta yi ma ta ne sai barci ya ɗauke ta a wajen. Kasancewar daren jiya ba ta yi isasshen barci ba.
Sidra kuwa mamaki da al'ajabi ya hana ta cewa komai kuma ta kasa barin wajen. Mamaki take yi shin har ta yi lalacewar da Nadra za ta kalli idanun ta ta yi ma ta magana yadda ranta yake so? Shin sanyi ta yi ne? Ina zafin nata yake, yarinyar da idan ta yi ma ta abun da bai yi ma ta ba za ta ɗaga hannu ta mare ta amma yau ta rike ma ta hannu yayin da take da niyyar marin ta? Sanann ta faɗa ma ta zancen da ranta yake so. Tabbas tura ta kai bango dole ta nema wa kanta mafita kuma ba ta jin za ta iya hakura da soyayyar Fahad.
Tsawo lokaci ta ɗauka a wajen ba ta motsa ba, har aka dinga danna ƙararrawar ƙofar, ba ta ji ba daga farko Sakamakon ta yi zurfi a duniyar tunanin da ta lula.
Daga baya ta sauka downstairs ta nufi kofar da niyyar budewa a tunanin ta Fahad ne Nadra ta sanar da shi abun da ya faru.
Sai dai tana buɗe kofar mutanen da ta gani tsaye a bakin ƙofar ne suka saka hanjin cikinta kaɗawa. Ja da baya ta yi tana kallon Gwaggo Maimaina da ke jifanta da wani mugun kallo, dama tana tsoron ta kasancewar ita ma tana da zafi sosai .
"Ja da baya ta cigaba da yi yayin da Gwaggo Maimaina ta finciko wuyar rigarta tana cewa.
"Munafuka me ya kawo ki zama gidan ƙanwarki, kashe ma ta aure kike so ki yi ko?"
Nan ma girgiza kai ta yi ba tare da ta ce komai ba.
"Tattara kayan ki yanzu ki zo mu tafi."
"Gaskiya ba in da zan ta..."
Kafin ta kai karshen zancen Gwaggo Maimaina ta wanke ma ta fuska fa marin da ya sa ta hantsilawa. Ita dai Gwaggo Laraba ba ta ce komai ba ta yi shiru tana kallon su.
"Har kina da bakin magana eye fitsararriya mara kunya. To wallahi tun da ubanki ya ce ki dawo gida wallahi sai kin tafi."
"To wai shi ya kore ni daga gidansa, kuma kuma danginsa har gidajen ku na ce kuka kore ni sannan wasu sun karɓe ni ina zaune a gidansu a ce na tafi? Sai dai idan wadanda suka ce na zo na zauna suka kore ni daga gidansu shi ne zan tafi ."
"Ƙarya kike yi Sidra ƙafata ƙafarki sai kin tafi kin bar gidan nan ehe!"
Gwaggo Laraba dai ba ta ce komai ba ta haura sama ta nufi ɗakin Nadra.
Knocking ta yi ta ji shiru sai ta tura kofar da sallama a bakinta.
Hango Nadra ta yi kwance saman gado tana barci, ga busashshen hawaye a idanunta da alama sai da ta ci kuka kafin ta yi barci. Cike da tausayin ta Gwaggo Laraba ta karasa cikin ɗakin.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce✍️
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️
(𝙅.𝙒.𝘼)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page6️⃣9️⃣
Hango Nadra ta yi kwance saman gado tana barci, ga busashshen hawaye a idanunta, da alama sai da ta ci kuka kafin ta yi barci. Cike da tausayin ta Gwaggo Laraba ta karasa cikin ɗakin.
"Ta san wanann hawayen ba zai rasa nasaba da Sidra ba, domin kuwa ta ɗan Fahad da wuya ya saka ta kuka. Don ko farkon aurensa da ya nuna baya son ta bai saka ta kuka ba ballantana yanzu da yake son ta.
Sunkuya wa ta yi tana shafo fuskarta daidai in da hawayen ya bushe.
A hankali Nadra ta buɗe idanunta ta sauke su akan Gwaggo nata.
"Gwaggo ke ce ko mafarki nake yi ?"
"Ni ce Nadra ba mafarki kike yi ba. Tashi zaune ta yi wasu sabbin hawaye na zubo ma ta .
"Daina zubar da hawayenki kin ji?"
Ai kamar ta ce ta kara ne don kuka ta saka ma ta wiwi. Cikin tashin hankali ta zauna bakin gadon tana rungume ta tare da bubbuga bayanta alamar rarrashi.
Ajiyar zuciya take saukewa kafin ta fara magana cikin rauni.
"Gwaggo meye lafin ƴaƴan da suka yi biyayya ga iyayen su wajen cika ma su burin su? Ya sa hakan zai janyo ma su ƙasƙanci da wulaƙanci a duniyar ma'abota sadaukarwa? Shin laifina ne ko kuma ni ce na ce Abba ya aura ma ni Yaya Fahad ballanta har Aunty Sidra ta ɗora alhakin hakan a kaina?"
Kuka ne ya ci karfinta wanda hakan ya saka Gwaggo Laraba sake rungume ta.
"Gwaggo wallahi Yaya Fahad baya son Sidra yanzu ya tsani ganinta ko maganar ta baya so ina yi ma sa, tana zaune a gidan nan ne don saboda na nemi hakan daga gare shi, wanda shi kuma ba zai ki amince wa bukatata ba. Da a ce na ga yana son ta ko kuma zai iya auren ta wallahi zan hakura na bar ma ta shi su yi rayuwar auren su kamar yadda suka tsara. Amma shi ya ce ya hakura da ita har abada ba zai iya auren ta ba. To meye amfanin na bar ma ta shi bayan ba aurenta zai yi ba?"
Ɗan bubbuga bayanta Gwaggo Laraba ta yi tana cewa.
"Daina kuka ya isa haka nan kin ji, ai ba zai taɓa yiwuwa ba ne a ce ya sake ki sannan ya zo mu ba shi auren Sidra ba, idan ba rashin hankali irin nata ba da rashin tawakkali irin nata ba ai hakan ba mai yiwuwa ba ne."
Nadra ta share hawayenta sannan ta kalli Gwaggo Laraba ta ce.
"Gwaggo me za ki ci ne daga ma ki ne?"
"Hutar da Kanki Nadra mun zo ɗaukar Sidra ne bisa umarnin mahaifinku."
"Abba ya yafe ma ta ne ko?"
Ta yi tambayar cike da farin ciki, dama ita birninta bai wuce Abba ya daina fushi da Sidra ya yafe ma ta ba. Don fushin iyaye masifa ne akan ƴaƴan su.
A tare suka fito daga ɗakin suka sauko downstairs daidai lokacin da Gwaggo Laraba ta tasa Sidra a gaba tana jan akwatin kayan ta .
Cikin girmamawa Nasara ta gaida Gwaggo Maimaina , ta amsa mata cike da murna.
"Nadara ya hakuri da rayuwa ya mai gidan?"
"Lafiya lau Alhamdulillah ya fita."
Kallon Sidra dake jifanta da wani kallo ta yi kafin ta ce.
"Aunty Sidra da alama Abba ya sauko ya yafe ma ki,na yi farin ciki da haka, Allah ya..."
"Dalla rufewa mutane baki munafuka, kin sanar da shi ina gidanki saboda a fitar da ni da..."
Ba ta kai ƙarshen maganar ta ba Gwaggo Maimaina ta finciko wuyar rigarta ta hankada ta waje, sai da ta faɗi. Sannan ta koma ciki ta dauko akwatin kayanta ta fito da shi. Gwaggo Laraba na biye da ita a baya Nadra na n take ma su baya.
"Daughter juya ki koma gida Allah ya yi ma ki albarka, ku gaida mijin naki idan ya dawo."
Tana so ta yi wa Sidra magana amma ta kasa, don ko ta faɗa ma ya cewa ba ita ce ta samar da Abba zaman ta gidan ba yarda za ta yi ba. Don haka ta yi shiru idanunta na cika da ƙwalla, har direba ya ja motar suka fice daga gidan.
Komawa ta yi ciki tana rusa kuka wanda ita kanta ba ta san ko na mene ne ba.
_Ma'eesha_
Da taimakon A'isha wacce ta taya ta aiki ta gudanar da komai. Girki kaloli suka yi saboda tarbon Makahon mijinta. Bayan sun kammala ne ta zuba a kulolli tana kiran dawowarsa. Kasancewar ya ce ma ta garin da nisa dai yamma zai iso. Ta zuba wa A'isha ta ce ta ɗauka ta tafi da shi gida, sannan ta ba ta kudi 5k cikin kuɗin tallafin da aka kawo ma ta.
A'isha na barin gidan dai ga Nasreen ta yi sallama ta shigo kamar an jefo ta daga sama.
"Assalamu alaikum ina Ma'eesha take ?"
"Wace'alaiki Salam warahmatullah . Lafiya wannan kiran haka Nasreen."
Ba ta ce komai ba ta janyo hannun Ma'eesha suka shiga cikin ɗalo .
Ita dai ma:eesha ya tsaya na kallon ikon Allah.
Wayarta ta danna sai ga photon Makaho shi da Yasmeen.
Sannan ta ga video shi da Yasmeen ta rike ma da hannu sune tafiya . Sai ta ga na washehari.
"Na gani amma gaskiya Allah ya yi halitta kin ga wani kamanni da na gani? Gaskiya kamar ta yi yawa."
Wani banzan kallo Nasreen ta yi ma ta kafin ta ce.
"Wani irin kamanni to ba wani kama wanan mijinki ne Khalifa Makaho ."
"Ba yadda haka. Za ya yiwu mijina makaho ne baya gani kuma tallka ne wanda idan muka samu abun da muka ci na yau na gobe sai mun nema, ba don da Allah ya rufa ma na asiri muka samu kudin tallafin nan ba har muka samu wadata ai da sai dai kawai hamdala. Ki duba wanan na jikin hoton hutu da jin dadi sun nuna a jikinsa. Ki dubi ko kayan jikinsa sun fi karfin miliyan ɗaya, kalli takalmin da agogon sa, kalli wayarsa fa kalli motar da ya fito ciki a ƙalla za ta miliyan ashirin. Don Allah ki bar wannan zancen mara tushe."
"Ba yadda za'ayi kama ta yi yawa haka, ki bude idanun ki da kyau , wanda duhu da makantar zuciya ta sa kike yi wa kallon haske. Ni dama tun ranar da na fara ganinsa bai yi kama da mutumin da ya sha wahala ko kuma wata gwagwarmayar rayuwa kamar yadda ya yi ma ki ƙarya ba. Domin hutu da jin dadi abu ne wanda ba sa ɓoyuwa. Duk wanda ya taso cikinsa sai ya nuna kansa. Mijinki ki kiyaye shi ba makaho ba ne, wata manufa yake da ita a Kanki da ya sa ya yi ma ki basaja a matsayin makaho, yana da wata mummunar manufa a Kanki ki zama mai taka tsantsan wajen kula da kanki, don gaskiya hankali na bai kwanta da shi ba maƙaryaci ne mayaudari ne..."
"Ya isa!"
Ta faɗa a tsawace. Wanda sai da Nasreen ta kalle ta da sauri .
"Dan Allah ki tashi ki tafi idan abin da ta kawo ki kenan. Mijina mai gaskiya ne ba zai yi ma ni karya ba."
Ba ta ce komai ba ta bude handbag din ta sanan ta ciro wasu hotuna guda biyu na kati da aka yi. In da yake zaune tare da Yasmeen da wanda yake fitowa daga cikin mota Yasmeen na rike da hannunsa.
Ga waɗan nan ki ajiye a wajen ki za su yi ma ki amfani.
Daga nan ta mike ta nufi bakin kofar fita sanann ta juyo ta kalle ta.
"Na yi ma ki alkawarin sai ba binciko abun da yake ɓoye wa."
Daga nan ta fice daga cikin gidan ranta a ɓace.
_Jalaluddeen_
Bayan ya sauka a airport Taj ya je ya ɗauko shi. Kai tsaya ya bashi umarnin ya kai shi hotel.
Ba su zame ko ina ba sai hotel ɗin da yake zama. Ba ɓata lokaci suka fito daga cikin motar Taj na rike da jakar uban gidan nasa.
Suna shiga ciki ɗakin Taj ya ajiye ma sa jaka, cikin girmamawa ya ce .
"Barka da dawowa sir."
"Barka dai ya aikin da na saka ka komai ba tafiya daidai?"
",komai na tafiya yadda ka tsara. A yanzu haka ta kawo ma ni kaso ma su yawa a cikin dukiyar mahaifin Ma'eesha. A yanzu haka akwai wasu takardun da za ta kawo ma ni a cikin kwana biyu."
Jinjina kai ya yi alamar gamsuwa sannan ya ce.
"Thank you, za ka iya tafiya."
Taj ya fita ya bar masa ɗakin.
Laptop ɗin sa na aiki ɗauka ya fara amfani da shi.
Sai yamma ya shiga wanka ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa, wsyarsa wacce Ma'eesha ta siya masa ya fara kunnawa.
Take kuwa kamar tana jira sai ga kiran Ma'eesha ya shigo cikin wayar.
Amsa kiran ya yi tare da yin sallama. Ta amsa ma sa tare da cewa.
"Ina wuni mijina."
Murmushi mai sauti ya yi sanan ya ce .
"Lafiya lau mar'atussaliha."
"Kana ina ne yanzu?"
"Yanzu motar mu ya sauka ga ni nan zan nemi abun hawa ba iso gida."
"Alhamdulillah na gode wa Allah da ya dawo mun da kai lafiya. Allah ya dawo da kai gida."
"Amin ya Allah."
Daga haka ya katse kiran wayar. Sauri -sauri ya shirya cikin kayan yadinsa ma su arha cikin wanda ya saba sawa.
Sannan ya dauki jakar kayansa da ya ajiye a hotel ɗin ya tafi Abuja da wasu. Sanadar jagoransa ya ɗauka da baƙin glass da aka fi sanain sa da shi. Sannan ya dauki jakar kayan ya ya fito daga cikin ɗakin rike da wayarsa ta wajen Ma'eesha. Takalmin soso ya saka da hularsa taɓa ka ji hadisai ya fito daga hotel ɗin .
Yana fita zuwa titi ya tara mai keke nape, bayan ya sanar da shi in da zai kai shi.
Shiga ya yi mai nape din ya ja keke nape ɗin suka bar wajen.
Har ƙofar gidan ya sauke shi. Ya biya shi kudinsa sannan ya shiga cikin gidan bakinsa dauke da sallama.
Ba ta tsakar gidan don haka ya ya shiga dakin yana dogara sandarsa.
Tsaye ya yi yana kallon ta da mamaki, ganin yadda ya dinga sallama ya ji shiru ba ta amsa ba. Da a da ne yana sallama za ta fito ta tare shi. Abun da ta zuba wa idanu yake kallo, kara zaro idanun ya yi yana kallon hotunan da tasa a gaba tana kallo da maɗaukakin mamaki a kan fuskarta. Ɗago da jajayen idanunta ta yi tana ma sa wani kallo mai wuyar fassara.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce✍️
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️
(𝙅.𝙒.𝘼)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page7️⃣0️⃣
Tsaye ya yi yana kallon ta da mamaki,ganin yadda ya dinga sallama ya ji shiru ba ta amsa ba. Da ada ne yana sallama za ta fito ta tare shi, abun da ta zubawa idanu yake kallo , kara zaro idanun ya yi yana kallon hotunan da ta sa a gaba tana kallo da maɗaukacin mamaki akan fuskarta . Ɗago da jajayen idanunta ta yi tana ma sa wani kallo mai wuyar fassara..
Ganin kallon da take ma sa ne ya sake jefa shi cikin tashin hankali. Sai ya yi ya maza ya dake kasancewar tana yi ma sa kallon makaho ne ba ta san yana gani na shi ha sa ya share ya ɗaga murya yana ƙwala ma ta kira.
"Ma'eesha !" Ma'eesha!" Ina kiks shiga? Ko tana banɗaki ne!"
"Na'am gani nan a gabanka."
"Gaba na kuma kuma?" Lafiya nake ha sallama ba ki amsa ba?"
"Ka yi hakuri ban ji ba ne na tsaya kallon wani abun mamaki ne?"
"Wani abun mamaki?"
"Duba ka gani."
Ta yi maganar tana nuna ma sa hotunan sa da na Yasmeen. In da ya fito daga motarsa Yasmeen ta rike ma sa hannu sa kuma,. Kallo ɗaya ya yi hoton ya cije lips din sa na ƙasa kafin ya ce.
"To ni fa nake makaho fa wani idanun zan gani sai dai ki bani labari."
"Mu bar zancen kawai, sannu da dawowa Mijina."
Ta yi maganar tana karɓar jakar da ke hannunsa. Yayin da ya fara lalube da sandarsa har ya zauna kan tabarma da ke shimfide a ɗakin ya zauna.
Yana lura da yanayin ta duk taa shiga ruɗu, ruwan sanyi da ke cikin jug wanda A'isha ta siyo ma ta ta ajiye a gamda sannan ta zuba a kofi ta mika masa.
"Bisimillah ga ruwa ja sha.*
Ta yi maganar tana kai ma sa ruwa saitin bakinsa ya buɗe ba ki ya sha har cikin ransa ya ji sanyi.
"Na gode." Ya faɗa yayin da yake kau da kansa gefe.
Hakan ya sa ta gane ya ishe sa Kenan. Ajiye kofin ta yi sannan ta ɗauko farantin da ta jera ma sa abici ta ajiye a gabansa.
"Ga abinci wanne zan zuba ma ka?"
Ta kalle shi tana murmushi tana tuna mutum na cikin hoton. Amma kasancewar ta yarda da mijinta ɗari bisa ɗari.
"Na yi ma ka masa da miyar tasushe sanann ga tuwon semovita da miyar kuɓewa. Na san kana son su ko?"
Murmushi ya yi yana sa ma ta albarka yayin da ya buƙaci ta saka ma sa tuwon ya ci.
Har da kunun aya ta ta saka ma sa ƙanƙara ya yi sanyi ta zuba ma sa.
Fitowa waje ya yi ya zauna saboda ɗakin zafinsa yake ji kamar gidan biredi.
A tare suka ci abincin suna ci tana yi ma sa fira. Sai dai ya lura da cewa duk da Nasreen ta kawo ma ta pics din su da Yasmeen bai yi tasiri a wajen Ma:eesha ba, saboda ta yarda da shi sosai kuma ta yarda da kalaman sa.
"Wai na tambaye ka ma na Yaya Khalifan."
"Ina jin ki."
Ya ba ta amsa cike da fargaban tambayar da za ta yi masa.
"Wai dama ana ana samun mutane biyu da kamanni ɗaya, komai na su iri ɗaya kuma ba tagwaye ba ne?"
"Eh ana samu sosai ma kuwa. Ai kowane mutum a duniya akwai irin sa a wani wurin?"
Shiru ta yi kafin ya ce.
"Da ace kana gani da na nuna na ka wani hoton wani mutum mai kama da kai kamar an tsaga kara."
"Allah sarki, sai ya kasance ba na gani ballantana na san meye banbancin mu."
"Wata rana in sha Allah idanun ka zai bude za ka fara gani tamkar yadda kowa ke ganin ka "
"Allah ya nuna ma ni ranar da idanun mijina za su buɗe ya kalle Ni na kalle shi."
"Amin ya Allah"
Ya amsa ma ta da shi sannan ya tashi yana yi ma ta godiya tare da yaba girkin nata.
Zai shiga ɗaki kenan ya ji muryarta tana cewa.
"Kana bukatar wani abu ne?"
"A'a lokacin sallar magrib ya yi zan je na yi sallah."
"Okay Ina zuwa .
Ya tsaya bakin kofar ga shiga ta dauko ma sa sandar jagoransa. Ta zuba ma sa ruwa a buta ya je ya shiga banɗaki.
Bayan ya fito ya yi alwala ya ya nufi masallaci don yin sallar magrib.
_Sidra_
Kuka take yi a bayan motar Gwaggo Laraba na gaban motar yayin da Gwaggo Maimaina ke baya ita da Sidra.
Ba abun da ke tashi a cikin motar sai sautin kukan Sidra. Ba wanda ya kula ta ballantana ya ce ta yi shiru ko ya ba ta hakuri.
Har suka isa gidan ba wanda ya yi magana a cikinsu.
Horn direban ya yi maigadi ya wangale ma sa gate ya shigo da motar ciki ya yi parking.
Gwaggo Laraba ta fito daga gaban motar yayin da Gwaggo Maimaina ke dakawa Sidra tsawa wanda ya sa dole ta fito, don ta san idan ta yi ma ta taurin Kai ba wani abu ba ne a wajen Gwaggo Maimaina sai ta gaura ma ta mari a gaban ma su aikin gida .
Fitowa ta yi ta nufi hanyar shiga ciki fuuu.
"Uban waye kika ajiye da zai ɗaukar ma ki akwatin kayanki?"
Gwaggo Maimaina ta yi maganar ranta a ɓace..
Tura baki Sidra ta yi saboda ba ɗabi'ar ta ba ce ɗaukar kaya idan ta dawo ko ba nauyi sai dai ta saka a shigo ma ta da shi.
Kamar za ta yi kuka ta zo ta ɗauki akwatin kayan ta shiga da shi ciki.
Ko da ta shiga ta same su duka a falo.
Abba, Umma, Ammi, Gwaggo Laraba da Gwaggo Maimaina.
Ta yi sallama yayin da take shiga ciki, gabaɗaya suka amsa ma ta. Kallon fuskar Abba yake sakawa hanjin cikinta kaɗawa.
Ajiye akwatin kayan ta yi tare da zubewa akan gwuiwoyinta.
Tsawon lokacin ba wanda ya yi magana a falon sai shiru. Kafin Abba ya bude baki ya yi magana.
A baya na yanke hukuncin cire ki daga cikin zuri'a ta sakamakon abun da kika yi ma ni na kunyatawa da kuma tozarci. Ko sunan ki na hana a kira mun a cikin gidan nan, na zo kowa ya fita harkar ki. Amma abin takaici ashe kin koma gidan ƙanwarki da zama Nadra. Kuma na san zaman ki a gidan ta ba alkhairi ba ne. Sai kin haddasa ma ta masifa ita da mijinta, tabbas za ki addabi rayuwar su ne. Don haka na yanke hukuncin dawowar ki a cikin gidan nan. Kuma ko ƙofar gida ban yarda ki taka ki fita ba, sanan kuma nan da wata ɗaya zan aurar da ke sadaka ga duk wanda na ci karo da shi idan na tafi ƙauye a cikin satin nan."
Yana gama faɗar haka ta ɗora hannu biyu akai ta rushe da kuka tana fadin ta shiga uku ta lalace, don Allah Abba ya rufa ma ta asiri kada ya ma ta haka, amma bai saurare ta ba haka ya fice daga gidan.
Hararar ta Ammi ta yi tana cewa.
"Wannan hukunci da Abdullahi ya ɗauka ya yi ma ni daidai wallahi. Ya ma yi ma ki sassauci ne albarkacin mahaifiyarki da kullum take cikin damuwa akan ya yafe na ki ki dawo. Darajar ta kika ci hukuncin ya tsaya iya haka, amma hukuncin da ya so ɗauka a kanki ai sai kin tsani kanki da kanki."
Tana gama faɗar haka ta juya zuwa ɗakinta, ƴaƴanta Gwaggo Laraba da Gwaggo Maimuna suka mara ma ta bayan.
Aka bar Umma tsaye Sidra na durƙushe tana kuka tana roƙon Umma da ta ba Abba hakuri ya janye hukuncin da ya yi niyyar ɗauka kanta .
Umma ta kasa cewa komai ta yi tsaye kamar wacce aka dasa, amma da zaran ka kalli cikin idanun ta za ka hango tsantsar tashin hankali da take ciki.
_Daddy_
Yana zaune a bedroom ɗin sa ya saka hoton Mummy da Ma'eesha yana kallo yana zubar da hawaye.
"Kiyi haƙuri Hajiya na kasa rike amanar da Allah ya ba ni. Ƴa ɗaya tilo da Allah ya ba ni ina ji ina gani aka waufantar da rayuwar ta amma na kasa cewa komai. Yarinyar da muka haife ta mika rene ta cike da so da ƙauna, muka yi burin inganta rayuwar ta da bata farin ciki mai ɗorewa. Sai ga shi lokaci daya abubuwa suka dagule. Na san cewa kafin rasuwar ki ban yi ma ki adalci ba, na tauye ma ki hakkin ki ga ƴar da kika haifa ina ji ina gani aka mayar da rayuwar ta zuwa matakan rugujewa. Ban san a wani halin take ciki ba. Wasu abubuwan duk ba na iya tuna su tun bayar zuwan Mamy da yaranta gidan nan. Ki yafe ma ni don Allah, Allah ya yi ma ki rahama ya sa aljanna Firdausi ce makoma a gare ki. Ma'ee..."
"Alhaji!"
Ya ji Mamy ta kira sunan sa a tsawace. Da sauri ya juya yana goge hawaye.
Ƙarasowa ta yi cikin isa da taƙama ta ce.
"Me kake yi da wanan hoton, kuma kukan me kake yi ne? Wani sabon mutuwa aka yi ma ka ne, ko Ma'eesha ce ta muyiy. Da sauri ya girgiza kai ya na cewa .
"Ma'eesha na nan da ranta ba ta mutu ba in sha Allah."
Taɓe baki ta yi tana cewa.
"Ko ta mutu wa ya sa ni ko yunwa da wahala ta gama da ita, don wanan makahon mijinta ba wata sana'a da zai iya ba, sai sai idan bara za su dinga zuwa tare tana yi ma sa jagora. Ta yi maganar tana dariyar mugunta.
Wani tsabar Mamy ya ji a zuciyarsa amma ba zai iya yi ma ta komai ba.
"Alhaji."
Ta kara sunan sa tana ɗauke hoton Ma'eesha da mahaifiyarta akan cinyarsa. Ajiye su gefe ta yi tana tabe baki.
"Alhaji na ce ba wasu kuɗade ko dukiyar da suka rage a hannunka. Ka san yanzu girma ya kama ka ya kamata a
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 40 Chapter of 49