ta yi knocking ƙofar toilet ta tabbatar ba kowa kafin ta tura ƙofar. Ganin ba Sidra ya sa ta dauka ko ta fita zuwa wajen su Umma ne, don haka ta fita zuwa falon mutanen ɗazu ne a ciki, tana sanye har lokacin da hijabi ta nufi part ɗakin Umma. Da sallama a bakinta ta tarar da Umma tare da ƙanwar Abba wacce suke kira da Goggo Laraba da suka kwana ɗakin Umma."
Ta durƙusa ta gaishe su cikin girmamawa, suka amsa ma ta cike da kulawa. Gwaggo Laraba ta ce.
"Ina Amaryar take ne ko tana can tare da ƙawayenta?"
"Ai ƙawayenta tun jiya ta Kore su wai ta sallame su ba ta son kowa ta kwana a gidan."
Da mamaki Umma ke kallon Nadra, Gwaggo Laraba ta ce.
"Sidra ba ta da mutunci wallahi."
"Kira ma ni ita."
Cewar Umma tana budar drawar da take zuba magungunanta a ciki.
"To Umma bari na je na duba duk da ba ta cikin ɗakin."
Tana fita ta nufi part ɗin Abba ta gaishe she shi shi da wani wan Umma suna zaune .
Gaishe su ta yi cikin girmamawa sannan ta fita ta koma ɗakinsu. Ta nemi Sidra ba ta ciki.
Don haka sai ta yi tunanin bari ta zagaya duka gidan ko tana wanni wajen a cikin gidan.
Umma kuwa ta buɗe drawar da take saka magungunanta a ciki dan ta ɗauko man maganinta na sha'awa a ƙafa. Sai ta ga wata farar takarda, tana fitowa ta warware ta fara karantawa kamar haka.
*Assalamu alaikum*
*Iyayena ku gafarce ni zan yi wata tafiya domin cikar burina. Na san za ku shiga tashin hankali a yayin da kuka ga wannan wannan ya wasiƙar ta wa. Ku ba wa Fahad da iyayensa haƙiri na san yana so na zai jira har lokacin da na dawo mu yi aure.*
_Sidra Abdallah Maitama_
Wani jiri ne ya ɗebi Umma ta yi luu za ta faɗi, cikin zafin nama Gwaggo Laraba ta tare ta tare da zaunar da ita bakin gadon.
Takardar Gwaggo Laraba ta ɗauka tana karantawa.
"Innalillahi wa 'inna ilahir raji'un."
Shine kalmar da Gwaggo Laraba take furtawa.
Kafin ta ɗauki wayarta ta kira lambar wayar Yayanta wato Mahaifin Sidra.
Bugu ɗaya ya ɗaga, ta sanar da shi ya zo ɗakin Umma yanzu.
Sannan ta fita zuwa ɗakin da Mahaifiyarsu ta sauka, ta tarar da ita ita kaɗai, don ba wanda ya je wajenta saboda masifarta.
Ita ma Gwaggo Laraba ba ta sanar da ita abun da ya faru ba, ta dai ce ta zo ana neman ta a ɗakin Umma.
Carko-carko suka yi a ɗakin Umma, Daga Abba har mahaifiyar su da suke kira Ammi da Gwaggo Laraba.
Umma na kuka kamar ranta zai fita yayin da kowa ya kasa magana. Abba ransa ya kai matukar tashi, idanunsa sun yi jajir, Ammi sai alawadai da Sidra take yi yayin da Gwaggo Laraba ta kasa magana.
Nadra ce ta shigo da sallama, ganin mahaifinsu kwance tana hawaye ya saka ta ruga gabanta ta rike hannunta tana hawaye ta ce.
"Umma me ya same ki ?"
Ta ji tambayar tana hawaye. Ganin haka ya saka Gwaggo Laraba janyo Nadra tana cewa.
"Ba abinda ya same ta tana kukan rabuwa da Sidra ce, kin san daga Anjima za'a ɗaura aurenta shi ke nan fa ta zama yar wani Family."
Haka kawai Nadra ta ji ba ta gamsu ba tana son yin magana ta ki Umma na cewa.
"Kada ki damu Nadra kewa ne kawai da zan yi na Yayarki."
Ya karasa maganar tana murmushin karfin hali.
"Umma na duba ko ina ban ga Sidra ba."
"Eh ta tafi wajen gyaran jiki ne Anjima za ta dawo. Ta shi ki tafi."
Haka kawai jikinta ya yi sanyi ta tashi ta tafi .
Cikin damuwa Ammi ta ce.
"Amma yarinyar nan ta gama tozarta mu, sai da ta bari mun tara jama'a gida ya cika da mutane sannan za ta ma na haka? Ga wasu mutane suna kan hanyar zuwa daga wasu garuruwa na nesa don halartar wannan ɗaurin auren ne za ta kunyata mu."
Sai da ta goge hawaye kafin ta ce.
"Abdullahi ka kira wadanda ke hanyar zuwa garin nan wajen daurin aure ka dakatar da su su juya su koma ba zancen auren kuma. Wadanda ke nan garin na dan dole su zo don Allah kaɗai ya san yawan su idan sun zo a basu hakuri su koma. Suma dangin angon a kira a ba su haƙuri su sallami baƙin da suka gayyata na nesa su koma garinsu na kusa kada su zo, wallahi Sidra ta gama kunyata mu ta tozarta mu."
"Ba za'a kira kowa ba ba wanda za mu dakatar daga zuwa kowa ya zo, kanta ta yi wa ba mu ba, wallahi ba ta isa ta tozarta mu ba. "
Da mamakin kowa ke kallonsa kafin ya ce.
"Za'a daura auren yau sai dai ba da Sidra ba tun da ta gudu, za'a ɗaura auren da ƙanwarta Nadra."
Da mamaki Gwaggo Laraba ke kallonsa kafin ta ce.
"Kar ka aikata abun da zai zo ya saka mu yi nadama, ka san irin soyayya da shaƙuwar da Fahad ya yi da Sidra, suna masifar son juna, ba wanda ya haɗa su sune suka ga juna suka hada kansu suke soyayya. Shin idan aka yi haka kana ganin Fahad zai yarda ya karbi ƙanwar Sidra a matsayin matarsa, ita ma Nadra za ta yarda ta zauna da saurayin Yayanta a matsayin mijin aurenta? Kuma shi Fahad irin mazan nan ne ƴan boko ma su son rayuwar wayewa, Shi ya sa ya nemi Sidra don ita ma haka rayuwarta take ba, amma ita Nadra da take da kunya da ustazanci ba ta damu da rayuwa ba shin ta ya ya zaman su zai yi daidaita tun da ra'ayinsu ba ɗaya ba?"
*To masoyana ga ni ɗauke da sabon labari, tafiya ne tsakanin duhu da haske, wata kila ya zo daidai da ra'ayinku🥰 watakila kuma akasin haka😒 Ni dai fatana a duk lokacin da kuka ci karo da abinda bai ma ku ba a cikin labrina to ku kasance ma su fahimtata da kuma yi ma ni uzuri. A cikin wannan labarin za mu fuskanci rayuwar waɗan nan jaruman guda biyar*
Khalifa (makaho)
Ma'eesha Ibrahim Khalil
Fahad Umar Majidaɗi
Sidra Abdullahi Maitama
Nadra Abdullahi Maitama
*Waɗan da suke da labari mabanbanta, ku dai ku kasance da ni a cikin wanan labarin don ganin wani dararasi ya zo da shi.*
*Maman Ihsan ce*✍️
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce ✍️
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page0️⃣2️⃣
"Kar ka aikata wani abin da zai zo ya saka mu yi nadama, ka san irin soyayya da shaƙuwar da Fahad ya yi da Sidra, suna masifar son juna, ba wanda ya haɗa su sune suka haɗa kansu suke soyayya. Shin idan aka haka kana ganin Fahad zai zai yarda ya karɓi kanwar Sidra a matsayin matarsa, ita ma Nadra za ta yarda ta zauna da saurayin Yar ta a matsayin mijin aurenta? Kuma shi Fahad ɗin irin mazan nan ne ƴan boko ma su son rayuwar wayewa, shi ya sa ya nemi Sidra don ita ma haka rayuwarta take . Amma ita Nadra da take da kunya da ustazanci ba ta damu da rayuwa ba shin ta ya ya zaman su zai daidaita tun da ra'ayinsu ba ɗaya ba?"
"Ka da ki damu Laraba in sha Allah babu nadamar da zai biyo baya in dai Nadra ya aura. Ni na haife su na san halin kowacce a cikinsu, sai ya fi jin daɗin zama da Nadra akan Sidra. Domin ita ce nake da yaƙinin zai iya sarrafa ta ta sarrafu ma sa yadda yake so, kuma ita ce zai iya daka ma ta tsawa ta saurare shi saɓanin Sidra. Da a ce tun farko Nadra ya gani yake kuma ta gudu, to ba zan taɓa cewa zan musanya ma sa ita da Sidra ba, don kada ya yi kuka da ni daga baya, amma Alhamdulillah tun da har Sidra ce ta gudu zan musanya ma sa madadinta da Nadra na tabbatar wata rana sai ya yi alfahari da wannan madadin, domin kuwa Nadra mace ɗaya ce har da ƙari."
Shiru dakin ya ɗauka ba wanda ya sake yin wata magana, domin kuwa sun san cewa Nadra ba ta da matsala.
"To yanzu ya kamata ka sanar da Fahad ɗin idan ya amince da Nadra."
Cewar Ammi tana kallonsa.
Wayarsa ya lalubo a cikin aljihun rigarsa yana dannawa lambar Fahad kira.
_Fahad_
Kwance yake a gadonsa ya lulluɓe da bargo yana barci.
Wayarsa dake saman side ta fara ruri.
Cikin barci ya ji kiran wayar, a tunaninsa Sidra ce, don da ita ya kwanta a ransa, bai same ta a waya ba. Kuma ya san ita ba ma'abiciyar kashe waya ba ne, kuma kullun asuba yakan kira wayarta ko ya turaa ta saƙon barka da safiya. Amma yau sai ya kira switch off.
A hankali ya bude idanunsa yana tashi zaune ya miƙa hannunsa ya ɗauki wayar.
Ganin sunan Mahaifin Sidra ne sai da gabansa ya faɗi.
Ya ɗauki wayar tana gab da tsinkewa.
"Assalamu alaikum."
Daga cikin wayar ya ji muryar Abba ya ce.
"Wa'alaika salam Fahad?"
"Na'am Abba."
"Idan ba damuwa ina son ganinka yanzu a gidana."
"To Abba."
Ya amsa sannan Abba ya kashe kiran wayar. Bargon da ya lulluɓe ya yaye ya sauko daga kan gadon. Farin wando ne Three-quarter ya sanya, babu riga a jikinsa ga wani zanen Tattoo a ƙirjinsa zuwa hannunsa.
Bathroom ya faɗa don yin wanka.
Tsawon mintuna talatin ya ɗauka yana wanka kafin ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa da wani ƙarami yana goge dogon gashinsa. Jikinsa sai kamshin shower gel da turaren wanka yake yi.
Tsadadden man shafawarsa ya shafa a jikisa, sannan ya fesa body spray. Closet ɗin sa ya shiga ya cikin tsadadden ɗanyar shaddar sky blue, sannan ya fesa turarensa mai suna Creed Aventus turare mai ƙarfi da jan hankali. Sannan ya ɗauki agogonsa Rolex date just ya ɗaura a tsitsiyar hannunsa. Ya duba bangaren takalmominsa ya ɗauki takalminsa Jimmy choo ya saka a ƙafarsa tsakanin nevy blue don haka ya saka hularsa nevy blue.
Ya fito ina da ya dauki wayoyinsa tare da key ɗin motarsa ya fara takunsa cikin izza wanda kallo ɗaya za ka yi ma sa ka san yana kan cin ganiyar samartakansa, kyau da cikar haibarsa suka sake bayyana.
Ƙamshin turarensa ya tabbatar wa da jama'ar dake falon yana gab da saukowa.
Idanu suka zuba wa upstairs ɗin yayin idanunsu ya sauka akansa.
A ƙalla mutanen da suke falon za su kai su goma kuma duk baƙi ne da suka zo bikin.
Gaishe su ya yi suka amsa suna ma sa ƴar tsokanar da ake yi wa ango.
Bai saurare su ba ya nuf part ɗin Mama. A falo ya same ta ita da ƙanwarta ya gaishe su.
"Ina za ka je na gan ka da makullin motar ko breakfast ba ka yi ba."
"Ina sauri zan je na dawo kafin abokaina su iso don suna hanya."
"Ina za ka je ne wai?"
Cewar Aunty Nana ƙanwar mahaifiyarsa.
"Gidan surukaina ne suke nema na."
"Okay a dawo lafiya."
Daga nan ya fice, zuwa part ɗin Baba. Shi ma ya gaishe shi sannan ya sanar da shi fitar da zai yi.
Ta ƙofar falon Baba ya fita ba tare da ya koma main falon ba.
Wajen motar da zai fita da ita ya nufa, ya shiga motarsa ƙirar Mercedes Benz G63 AMG ya yi ma ta key, kafin ya horn har maigadi ya wangale ma sa gate ɗin gidan ya fice da motarsa. Wanda kallo ɗaya za ka yi wa motar ka san cewa an narka dukiya wajen siyen motar.
Kai tsaye ya dauki hanyar da za ta sada shi da unguwar su Sidra.
_Maeesha_
Tafiya kawai take yi tana hawaye hannunta rike da akwatina biyu, yayin da Makaho ke jan babbar akwatin da ɗaya hannunsa. Ɗayan hannu kuma yana rike da sandarsa yana dogarawa.
Bin bayansa kawai take yi ba tare da ta san in da za su tafi ba.
Tsawon lokaci suka ɗauka suna tafiya, kasancewar ba ta saba yin tafiyar kafa ba ga kaya duk ta bi ta gaji.
Don haka ta tsaya ba tare da ta yi magana ba, shi ma sai ya tsaya kamar ya san ta tsaya.
Sai dai bai yi magana ba ya yi shiru. Ganin ba ta da niyyar cigaba da tafiya ya saka ya ce.
"Ki yi hakuri mu tafi akwai sauran tafiya a gaban mu ga magrib ta kusa."
"Ba zan iya sake wani tafiya ba na gaji."
Kafin ya yi magana ta hangi mai keke nape ya fito layinsu tsaida shi ta yi ya tsaya a gabanta .
"Hajiya ina zuwa."
Kallon Makaho ta yi tare da cewa.
"Ka zo ka faɗa ma sa sunan unguwar."
Ya karasa yana lalube da sanda ya faɗa wa mai napep ɗin .
Mai nape ya saka akwatunan a baya ya ajiye daya a gefe, sannan ya ce su shiga .
Sai da ta shiga sannan ta ce wa makaho.
"Mallama ka shigo."
Kamar ba zai shiga ba sai kuma ya shiga baya bayan ya laluba ya zauna.
Shi ya sanar wa mai napep ɗin unguwar da zai kai su tare da ma sa kwatance.
Tun da suka shiga layin jikin Ma'eesha ya yi sanyi . Don kallo ɗaya za ka yi wa yankin ka san cewa unguwa ce ta talakawa. Don ba gini mai kyau a layin da zai tabbatar ma ka da akwai masu rufin asiri a layin.
Kamar yadda ya yi ma sa kwatance da masallacin kuwa haka aka yi, sai da ya kawo daidai masallacin da ya sanar da shi ya tsaya ya ce.
"Mun iso wajen."
"Mallam don Allah ka taya mu sauke kayan kasa."
"To Hajiya."
Ya fada yana saukowa bayan ya kashe keke nape ɗin nasa.
Sai dai ya sauke ma su kayan sannan ta tambaye shi kudinsa.
"Nawa ne mallam."
"Ki bada yadda kuke zuwa ."
"Mallam ka yi magana ban san ya ake biya ba, don ban taɓa hawa keke nape ba sai yau."
Wani kallo ya ma ta har zai yi wata magana sai ya lura da haƙorin Gold ɗin dake bakinta, hakan ya tabbatar ma sa da cewa Hajiya ce ita, kuma yanayin ta ma ya nuna ƴar hutu ce.
"Ki bayar da dubu ɗaya."
Ya fada yana shiga cikin napep ɗin nasa. Handbag ɗin ta ta zuge ta ciro 1k ta bashi.
Bayan ta sallame shi ne Makaho ya ja akwatin kayanta babba ya yi gaba, ita dai bisa ta yi a baya har suka ƙarasa ƙofar wani gida. Gidan ƙofarsa ta ɓalle tun daga waje ma ana hangen wa su matan dake tsakar gidan.
'Na shiga uku ni Ma'eesha wane irin gida ne nan na faɗo.'
Sallama Makaho ya fara yi sai da aka ba shi izinin shiga sannan ya shiga tana bin sa a baya.
Ɗakunan gidan za su kai Ashirin. Don tsakar gidan ma cike yake da mata ga yara barkatai ta ko ina. A tsakar gidan.
Wasu yaran suna wasa, yayin da wasu na faɗa sai wasu yaran zaune sun jeru suna kashi a ta ko ina suke zaune ba tsari .
Wata dattijuwa ta kalli Makaho ta ce.
"Mallam Khalifa ka dawo ?"
"Eh Baba na dawo."
"To ma sha Allah, wannan ita ce Amaryar taka?"
"Eh ita ce."
Wata uwar ashar suka ji an danna, wanda ya saka hatta Makaho da Ma'eesha sai da suka tsaya cak daga tafiyar da suke yi.
Larai Dillaliya ce ta yi zargin tana kallon takalmar dake ƙafar Ma'eesha wanda a ƙalla kuɗinsa za su kai dubu ɗari 100k haka handbag ɗinda ke hannunta ma zai kai dubu ɗari.
Kafin a gama mamakin ashariyar da ta ɗura aka ci muryar Larai ta sake cewa.
"Wannan ita ce matar Khalifa makaho kenan?"
"Makaho ya cigaba da tafiya Ma'eesha kamar za ta faɗi sakamakon idanun da ta ji suna yawo a jikinta, sai dai kanta a ƙasa ba ta ba da damar ganin fuskarta sakamakon mayafin abyarta da ta rufe rabin fuskarta da shi hawaye ne kawai ke bin fuskarsta ba tare da kowa ya sani ba.
Hakan ya saka kanta a sunkuye tana kallon ƙasa yake tafiya ba ta yarda ta gaishe da mutanen gidan ba saboda kuka zai iya ƙwace ma ta matukar ta ce za ta buɗe baki ta yi magana.
Ɗakin karshen gidan wanda ke da ƙofar langa-langa ya tura ya shiga da sallama.
Ita ma shiga ta yi idanunsa na sauka kan buhun siminti da aka shimfiɗa a ɗakin
Ƙafarta ya harɗe cikin buhun da ake shimfiɗa madadin carpet. Nan ta lura ashe ɗakin ko flour babu, ba'ayi simintin ƙasar ɗakin ba ƙasa ne kawai sai aka shimfiɗa buhu a ƙasan ɗakin wanda ya rufe ƙasar ɗake ƙasan ɗakin. Hatta bangon ɗakin ana iya ƙirga bulo ɗin don shi na bangon ba'a shafa ma sa siminti ba. Ga bangon duk ya yi gantsa kuka alamar ya sha ruwa kafin aka yi rufin ɗakin.
Kanta ta ɗaga sama tana kallon rufin ɗakin, nan take hangen haske daga sama, wato zink ɗin ɗakin ya hude a wasu wuraren aka hangen hasken waje, langa-langa ba sabo ba ne aka saka.
Kuma idan ana ruwan sama da alama ba ƙaranin yoyon ruwa zai yi ba, don ba makawa dai ruwa ya cika ɗakin idan har mai ƙarfi ne.
Toshe bakinta ta yi tana kuka don kada sautin kukan ya fita, kafin ta ji tsayuwar ya gagare ta ta zube akan ƙafarta tana kuka mai tsuma zuciya.
Kamar ya san kuka take yi sai ta ji ya kira sunanta cikin kamilalliyar muryarsa mai cike da nutsuwa.
"Ma'eesha."
Ba ta amsa masa ba sai hawaye dake bin fuskarta.
"Ki yi haƙuri na san wannan gidan bai dace da macen da ta taso cikin gata da hutu ba, kin taso cikin farin ciki na sani kina kwana a cikin A.c da katifa mai laushi ba'a dauke wuta ko an dauke ba iya sani saboda na'ura za ta fara aiki ki nan kuma ko fanka babu ballantana A.C ba na da halin da zan iya ciyar dake irin abincin da kike ci da ruwan da kike sha..."
Shiru ya yi sakamakon jin fitar ta daga ɗakin, tana fita ta yi tozali da fo da yarinya ta yi kashi ta tashi ba tare da an yi ma ya tsarki ba tana wasar ta. Wani na zaune kusa da fo ɗin yarinyar shi ma yana Kashin, Ma'eesha ta yamutse fuska, ta ji wata mata na cewa.
"Amarya hakuri za ki yi ɗakinki shi ne kuka da banɗaki dole ki dinga ganin haka.
"Ina ne banɗaki."
Ta tambaya tana kallon matar da idanunta da suka kumbura.
"Ga banɗaki nan jikin ɗakinki. Bari a kawo ma ki buta."
Kafin matar ta yi magana sai wata budurwa ta kawo wa Ma'eesha buta da ruwa a ciki.
Karɓa ta yi tana shiga ban dakin ta toshe hanci tare da fitowa a guje ta duƙa ƙofar ɗakinta tana kakarin amai, sakamakon wari da zaurin fitsari dake tashi a toilet ɗin.
Da kallo suka bi ta wasu na yi ma ta sannu. Bayan ta gama ne ta ga wannan buduwar da ta ba ta buta tana cewa .
"Tashi bari na gyara wajen."
Tana magana tana mika ma ta kasar pure water na ruwa, karba ta yi ta wanke baki sannan cikin kasalliyar murya ta ce.
"Thank you."
Cikin ɗakin ta koma ta ga makaho tsaye kamar yadda ta bar shi.
"Wallahi ba zan iya rayuwa a cikin wannan gidan ba."
Tana fadar haka ta janyo akwatin kayanta ta fito, shi ma ya janyo babban ya biyo ta suka fito suna tafiya."
Baba ta lalle su ta ce.
"Lafiya kuwa Khalifa?"
"Baba ina zuwa "
Abun da ya iya fada kenan saura. Matan kowa sai bin su yake da kallo. Suka ji muryar Larai Dillaliya tana cewa.
"Ni Ko da na kalli yarinyar nan na san ba kamar unguwar nan ba ne ballantana gidan nan, ko dai asiri Khalifa ya yi wa iyayen yarinyar nan ne da suka ɗauki ƴa suka ba shi aure?"
Ita dai Ma'eesaha ko kallo ba ta yi ma ta ba ballantana ta gane wa ke magana .
Tana zuwa ƙofar gidan ta ajiye akwatin hannunta, shi ma ya tsaya in da ya ji ta tsaya, ya ajiye akwatin amma sandarsa ta Manafi na hannunsa.
Handbag ɗin ta ta buɗe ta duba daga wayoyinta sai kuɗi 9k dama dubi goma ne ta ba mai napep dubu ɗaya ya rage dubu tara.
Ga shi matar Babanta ta amshe ATM card ɗin ta wanda a ƙalla tana da Naira sama da miliyan biyar a ciki. Pink lips din ta ta cije tana goge hawaye.
Kafin ta ce.
"Ina zan samu gidan haya kamar na zaman mutum ɗaya?"
"Gaskiya ban sani ba, amma dai idan aka tambaye Iro mijin Larai Dillaliya zai samo ma na, saboda dillancin gidajen haya yake yi a unguwar nan."
"Ina za'a same shi yanzu ?"
Kafin ya yi magana ne suka ji muryar wani mutum dake ƙoƙarin shiga cikin gidan yana cewa.
"Mallam Khalifa Amaryar ce nan?"
Yana tambayar amma idanunsa akan Ma'eesha wacce ta tsuke fuska, sakamakon kallon ƙurillar da yake yi ma ta.
"Yauwa Mallam Iro ka dawo?"
"Eh Allah ya yi."
"Dama yanzu muke maganar ka dai ga shi ka zo."
"Ikon Allah, ka san an ce ɗan halal ya ƙi ambato."
Kallon Ma'eesha ya yi yana cewa.
"Amarya ya garin ."
Ba ta amsa ma sa ba ta ce.
"Gidan haya za ka nema ma ni a yanzu nake buƙata iya na zaman mutum ɗaya."
Shiru ya yi yana tunani kafin ya ce.
"Eh akwai guda ɗaya a unguwar nan, shi kadai ne iya na zaman mutum ɗaya, sauran dole sai kin samu makota."
"Ina so sannan ina son ya kasance gidan mai tsafta ne."
"Ba matsala in dai tsafta ce, sai dai ƙarami ne sosai gidan. In taƙaice ma ki iya ɗaki ɗaya ne tal a ciki wato single room ne, ba falo ɗaki ɗayan nan ne sai banɗaki da kitchen madaidaita."
Ba haka ta so ba ta so ko da mai falo ɗaya da ɗakin barci a samu, amma tun da ya ce wannan kadai ne za ta amshe shi, ya fi ma ta wanann gidan da ta fito yanzu na ƙazamai."
"Ina ne gidan?"
"Farkon layin nan ne?"
"Okay nawa ne kuɗin?"
"Ba tsada dubu hamsin ne a shekara ɗaya."
Tunanin ta ina za ta samu dubu hamsin ne, ga shi dama ba ta iya yin transfer money from account ɗin ta har tana tunanin zuwa bank sa saboda matsalar ga shi dubu tara take da shi yanzu haka, ga shi ana maganar gidan dubu hamsin.
*KADUNA*
_Fahad_
A ƙofar gate ɗin gidan su Sidra ya yi horn.
Maigadi ya wangale ma sa gate ya shiga da motarsa ciki .
Bayan ya yi parking bai fito daga cikin motar ba ya ɗauki wayarsa ya kira Abba. Ya sanar da shi ya iso, nan Abba ya ce ya shigo yana part ɗin sa.
Da sallama ya shiga ƙofar part ɗin Abba.
Suka amsa ma sa gabaɗaya suna zaune a falon. Abba, Umma, sai mahaifiyar Abba wato Ammi, da ƙanwar Abba Gwaggo Laraba sai Aminin Abba Alhaji Abubakar
Kallo ɗaya Gwaggon Laraba ta yi wa Fahad a zuciyarta ta ce.
"Sidra kin yi wa kanki, domin wannan yaron miji ne na kece raini ne da da gudun wuce sa'a. Allah ya sa ya amince da zaɓin Nadra kada ya ki amince."
Ƙamshinsa ya cika falon ya karasa ya durƙusa ya gaishe su. Suka amsa ma sa gabaɗaya.
Shiru ne ya biyo baya, kafin Abba ya ce.
"Fahad."
"Na'am Abba."
"Ka yi waya da Sidra ce?"
"A'a Abba ba mu yi waya da ita ba."
"Tun yaushe kenan kuma wani magana kuka yi?"
"Wannan karon sai da gabansa ya faɗi sakamakon tambayar da aka yi ma sa."
"Lokacin ta ce mani za'ayi ma ta zanen lalle zuwa dare za mu yi waya, to a daren na yi ta kira ba ta ɗauka ba har yau na ji wayar a kashe ."
Cikin fargaba ya ce.
"Ina fatan dai tana lafiya ba wani abun ne ya same ta ba ko?"
"Tana lafiya."
Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke yana jiran dalilin kiransa.
Abba ya mika ma sa wasikar da ta bari ya karba ya fara karantawa.
Sai da ya mike tsaye tsabar dirgici da tashin hankali. Kafin ya kalli gabɗaya jama'ar dake falon ɗaya bayan daya, sai a lokacin ya lura da dukkansu a kwai rashin hankali a tattare da su.
"Innalillahi wa 'inna ilahir raji'un."
Kalmar da ya furta kenan idanunsa sun rikiɗe zuwa ja.
Cikin sanyin jiki ya zauna yana cewa .
"Sidra why why do this to me me ya sa kika amince tun farko? Ina kika je kika bar ahalinki cikin tashin hankali ba tare da yin tunanin halin da za su shiga ba."
Tashi ya yi yana kallon su idanunsa sun yi ja hatta farar fuskarsa sai da ta ji ja.
"Ku sanar da mutane kawai an fasa daurin auren
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 49