ta iya shaida ko su waye. Sakamakon fuskarsa sanye da mask sannan kuma sun sanya bakin glass a idanunsu.
"Ka ga wasu maza guda biyu ɗaukar mu photo fa suke yi."
"Da wani idanun zan kalle su na gane su ?"
"Ki rabu da su mu tafi kawai mu je mu dawo?"
"Amma kana ganin haka kawai za su dinga daukar mu photo ne, bayan ga mutane nan ba wanda suka ɗauka sai mu?"
Madadin ta ta tafi in da za su tafi sai ta nufi motar daidai lokacin da suka ja motar suka bar wajen.
Shiru ta yi ba tare da ta ce komai ba, amma zuciyarta na cike da tarin tambayoyi. Su waye waɗan nan kuma mene ne dalilin da ya saka suke ɗaukar su photo? Haka ranar da suka fito daga siyan waya aka dauke su photo ita ta shi .
Har suka ƙarasa wajan me dabino ta siya na ɗari biyu sai pure wayar mai sanyi ta siye na Naira ɗari.
Shi ya karba ya riƙe sannan suka kama hanyar gidan.
Suna shiga ana kiran sallar magrib. Tabarma ta shimfida ma sa a barandar kofar ɗakin sannan ta gabatar ma sa da kayan bude baki.
Sai da ya wanke baki sannan ya ci dabino da ruwa ya tafi masallaci.
Tashi ta yi ta gabatar da sallar magrib ita ma har lokacin hankalinta ya kasa kwanciya da waɗan nan mutane .
Sai da aka yi sallar isha'i ya dawo ita ma lokacin ta idar da sallar.
Suna zaune a ɗaki ta zuba ma sa abincin a plate, tuwon shinkafa ne da miyar kuɓewa .
Sai kunun tsamiya da ta dama ma sa bai sha ba ya tafi masallaci.
Sai yanzu ya sha kadan, tuwon na kadan ya ci ya ce ya ƙoshi.
Ta lura shi ba mai son cin abinci ba ne, haka ta dinga lallaɓa shi kamar ƙaranin yaro don ya ci tuwon da yawa.
Har ta samu ta ɗan kara kuma ta ji dadin hakan sosai.
"Sai lallaɓa ni kike yi kamar wani ƙaramin yaro ko?"
"Idan ban lallaɓa ka ba wa zan lallaɓa? Allah sarki ina ma zan ga karamin yaron da zan lallɓa?"
Ɗan jim ta yi kafin ta kuma cewa.
"Ina masifar son yara wallahi, idan na ga jariri hannun uwarsa sai na ƙi dama ni ce da babyn. Ka san Allah ina son na ga ranar da Allah zai azurta mu da babys ranar zan iya barci kuwa?"
Ta yi maganar cikin shauƙi sosai
Shiru ya yi bai ce komai ba, kafin ya ce.
"Ni a gani na a yadda muke cikin wannan halin bai kamata a ce mun tara zuri'a ba."
Ya yi maganar ya saka hannu a aljihu don ya ciro kudin da ya samu. Ya san daga haka zai kawar da zancen.
"Cinikin yau duka-duka Naira ɗari biyar ne."
Ko ɗaya fito kudin ya mikaa ta da hannu biyu ta karɓa. Sai dai tana dubawa ta ga Ɗari biyu ne madadin dari biyar da ya ce.
"Dari biyu na gani."
Cikin mamaki ya ce.
" Ɗari biyu da kika ce?"
"Ƙwarai kuwa haka na gani."
Shiru ya yi kafin ya ce.
"Wai me ya sa cuta ta yi yawa a wannan zamani da muke ciki ne, idan Allah ya ɗora wa mutane lalurar makanta sai hakan ya saka dogaro wajan cutar da shi?"
Cikin tausaya wa ta ce .
"Ka rabu da shi kansu suka cuta ba kai ba."
Nan dai ta cigaba da kwantar ma sa da hankali har ya bar zancen, amma zuciyar sa na mamakin ha'inci na mutane. Kuma duk hakan ya faru ne sakamakon yau da ya fara zuwa kuma da safe ya yi cinikin kafin abokan zamansa su fito.
"Allah ya sa ma su albarka."
Ta fada tana jingina da bango ta lumshe idanunta.
"Na san kuɗaɗen da suke hannunki sun ƙare ko?"
“Ɗari biyu ya rage."
"To Ma'eesha Allah ya kara rufa ma na asiri."
"Ni ina ganin buhun gawayin da na siyo na ajiye a kitchen zan fara ɗaura shi a leda ina siyarwa, zan yi wa maƙota talla su dinga zuwa suna siye."
"Gawayi kuma ?"
"Eh mana ai ya fi a ce mun zauna haka nan, rayuwa ba za ta tafi ma na a haka ba, idan kayan abincin da muke da su suka ƙare waye zai ba mu ? Mutanen yanzu kansu kadai suka sani, wannan gyaran takalmin naka ba iya ɗaukar mu zai yi ba, amma idan na kulla ya kare sai na dinga siya ina ɗaurawa."
"To shi kanan Allah ya taimaka ya yi jagora."
"Amin ya rabbil izzati."
Ruwan wanka ta kai masa banɗaki ya yi kafin ya shirya ita ma ta shiga ta yi wankan. Ko da ta fito har ya gama shiri .
Karfe goma sha daya suka kwanta, ita tana kwance a katifa shi yana kwance a tabarma, kamar yadda ta yi wa kanta alkwari ba za ta sake ce ma sa ya kwanta a katifar ba kuwa ba ta sake ba, shi ma bai damu ba.
_Fahad_
Fitowarsa daga wanka kenan yana sanye da bathrobe a jikinsa.
Yana goge kansa dake jiƙe da ruwa, ya kalli gadon sai ya ga ta dunƙule ji jikinta wuri guda ta lulluɓe da bargo.
Jajayen idanuna ta kalle shi shi ma ita yake kallo kafin ta sunkuyar da kanta ƙasa.
"Tashi ki je ki yi wanka."
Banza ta yi masa ba ta motsa daga in da take ba.
"Ko na yi ma ki wankan ne?"
Nan ma shiru ba ta motsa ba
"Okay bari na yi ma ki to."
Jin haka ya saka ta kara rufe jikinta da bargon tana cewa.
"Ka daina kallo na zan tashi na yi da kaina."
Murmushin gefen baki ya yi kafin ya ce .
"Meye kuma ban gani ba yanzu? Ai duk wata kunya ta ƙare."
Takaici ya sa ta fara kukan shagwaɓa. Ya bar wajan ya nufi bathroom ɗin.
Ba jimawa ya fito sanye da farin towel sabo da ya cire daga ledarsa
Miƙa ma ta ya yi sai da ta shigar da shi cikin bargon sannan ta ɗaura ta fito daga cikin bargon.
Towel ɗin me girma ne Tana sauka ya cire sanin gadon da bargon da kayan da suka cire duka.
Jallabiya ya saka a jikinsa bayan ya shafa turare ya saka boxer .
Tana shiga banɗakin tsarkake jikinta ta yi sannan ta yi wanka ta dauki wani towel ta daura .
Tana fitowa ya shiga da kayan da ya kwashe kan gadon.
A warahing machine ya fara wanke kayansa da na ta sannan ya zuba sannan ya zuba su zanin gadon.
Bayan ta tashe ruwan kanta ta duba ba ta ga kayan da ya cire ba. Ba abayarta ba mayafin.
Tsaye ta yi tana jiran fitowarsa.
Yana fitowa ta ce
" kayana fa ban gan su ba."
Share ta ya yi kamar bai ji ta ba ya nufi hanyar fita. Da ido ta bi shi tana tura baki.
Downstairs ya sauka in da ya tarar da kowa a falon, Mama, Inna, Rumaisa, Farida, sai kuma Sidra.
Ƙamshinsa ya bayyanar ma su da isowar sa wajen .
Inna da ta gama jin labarin da Mama ta ba ta na Sidra da Baba ya ce ta zauna sai ya dawo.
Fahad ya kalli Rumaisa ta ce .
"Ɗauko ma ni kayanki kala ɗaya ki kawo ma ni."
Gabaɗaya suka kalle shi cikin rashin fahimta musamman Ruamisa ta ce .
"Ban gane ba."
"Da wani Yaren na yi na ki magana, ki ɗauko kayanki cikin dogayen rigunan da na siyo ma ki a kasar Egypt last two weeks ."
"Okay."
Ta fada tana nufar ɗakinta. Inna ta kalli Fahad ta ce.
"Me za ka yi da kayan saka wa na mata kuma?"
"Nadra za ta saka?"
Kalmar da ya daki zuciyar Sidra kenan ta kalle shi ba shiri.
Inna ta ce .
"Me ya samu kayan da ta zo da shi?"
Share ta ya yi kamar bai ji me take cewa ba.
Jin ya yi banza da ita ne ta fara ma sa masifa wai ya kawo amarya don ta gaishe su amma bai bari ta gaishe su ba ta ƙunshe ta a ɗaki.
Ta in da take shiga ba ta nan take fita ba. Har Rumaisa ta ta kawo ma sa kayan ya karba ya haura sama.
Hankalin Sidra ya kasa kwanciya gabaɗaya ta rasa sukuni tana addu'a Allah ya sa ba abun da take tunani ba ne.
Yana shiga ya mika ma ta kayan riga ce doguwa tana da tsaga gefe da gefe da wando dogo dai mayafin madaidaici.
Banɗaki ta shige don ta sauya kayan, ya taɓe baki ya bar ɗakin.
Waya ya amsa yana magana yana kallon T.V dake aiki. A cikin wayar yana magana ne kan tafiyar da zai yi America zuwa gobe.
Bayan ya katse kiran wayar ne ya shiga bedroom ya same ta ta gama shiri, kayan sun karbe ta sosai sun yi ma ta kyau har ya kasa ɗauke idanunsa akan ta. Don dama kayan sun burge shi ne ya siya wa Rumaisa ita kuma ita kuma Sidra ya san ba ta san kaya ma su rufe jiki ne bai siyo ma ta ba.
"Mu je ki gaida Kakata tana can tana tambayar ki."
Ya yi gaba ta bi bayansa tana tafiya a hankali.
Takun takalmin Nadra ya jawo hankalin mutanen Falon, suka ga kayan da Fahad ya karba ne a jikinta.
Sai a lokacin kunya ya kama ta sakamakon kayan jikinta. Don kobdabya kawo ma ta kayan ba ta san daga ina ba ne amma ta san kowa dake Falon nan ya san cewa ba kayan da ta zo da shi ba kenan, yanzu sun san abinda suka aikata kenan.
Wani kunya ya lulluɓe ta kamar t ƙasa ta tsage ta shiga.
Jin ta tsaya cak ya saka ya ce .
"Lafiya ?"
"Yanzu idan suka kalle ni da wanann kayan ba wanda na zo da shi ba za su gane abun sa muka aikata ko?"
Sai da ya danne dariyarsa sannan ya ce .
"Eh sun san komai da na zo karɓar kaya sun tambaye ni na ce ke ce kika ce na ba ki hakkin ki na aure."
"Hawaye ya wanke fuskarta ta juya da sauri za ta koma sama. Cak ya dauko ta yaba saukowa downstairs.
Duk yadda ta so sauka haka bai ba ta wannan damar ba.
Sai da ya sauko ya dire ta a ɗaya daga cikin kujerun Falon.
Ganin za ta mike ne ya saka ya yi saurin zaunar da ita yana murmushi.
Mama ta ce .
"Lafiya ?"
Fahad ya ce .
"Wai ba za ta zo ta zauna tare da ku ba sai dai ta tsaya da mijinta."
Kunya ya sake rufe ta ya fice daga gidan yana dariya.
"Kar ka damu Daughter na san halinsa tsokanarki yake yi na sani."
Ta yi maganar tana nuna wa Nadra kusa da ita , kamar tana jira ta mike ta koma jikin Mama ta kwantar da kanta kan cinyar Mama kamar yadda Umma ke yi ma ta idan sun yi faɗa da Sidra.
Fahad ne ya dawo ya kalli Mama ya ce.
"Gobe in sha Allah zan tafi America."
Mama ta ce.
"To ita kuma Nadra fa tare da ita za ka tafi?
"Idan za ta bi ni sai mu tafi tare da ita."
Sidra ta girgiza ma ta kai alamar ta ce a'a. Cikin sa'a kuka ta yi saurin cewa
"Ba zan bi shi ba zan zauna a nan gidan kafin ya dawo ko kuma ba koma wajen su Umma."
Mama ta ce
"A'a Daughter ba za ku je wajen Umma ba sai dai ki zauna nan kafin ya dawo sai ki koma gidanku."
Shi dai bai ce komai ba ya bar falon.
Bai dawo ba sai bayan magrib ya shigo da set na akwati. Kaya ne ya siyo wa Nadra wadanda ya fahimci za ta iya saka wa. Akasarin su dogayen rigunan Abaya ne da hijabai yadda ya san tana son kaya, sai flat shoes da handbag ɗin da underwears wanda ya san za su yi daidai size ɗin ta.
Part ɗin sa ya kai kayan bayan ya nuna wa Mama da Inna kayan kafin ya kai part ɗin sa.
Inna ta fara fadar cewa tsabar almubazzaranci ga kayan lefe ne zai je ya kifi wasu kayan.
Bai kula ta ba ya fita don yin sallar magrib.
Text message ya tura wa Nadra ganin ta tare a dakin mama.
*Ƙarfe goma na dare na yi ki yi ma su sallama ki koma part ɗina tare za mu kwana kafin gobe idan na tafi za ki iya kwana a dakin da kika ga dama.*
Tana kwance a gadon Mama bayan ta yi sallar isha'i ne ta ga message ɗin nasa.
Tura baki ta yi tana cewa.
"Ni ba ƴar iska ba ce da zan je kwana dakinka bayan abun da ka yi ma ni da safe."
Kamar ya san me take cewa sai ga wani message.
*Idan ba ki zo ba zan biyo ki ne ko a gaban Mama ne ba ruwana da kunya.*
Bayan ta karanta tana hawaye ta ce.
"Na shiga uku. Wallahi zai aikata bai da kunya."
Yana gama tura ma ta messages ɗin. Ya siye gasashshen kaza ya siye fresh milk ya bar wajen.
_Makaho_
Yana dawowa daga wajan da yake gyaran takalmin daidai kan kwanar da zai sada shi da hanyar unguwarsu wata baƙar motar ta tsaya a gabansa.
Wasu maza masu ƙirar samudawa ne suka fito su biyu, suka ɗauke shi suka saka shi a bayan motar bayan sun toshe ma sa baki da hannu kafin ya yi wani yunkuri, a guje motar ta bar layin .
Wata mota dake can gefe ta mara ma su baya a guje.
*Maman Ihsan ce*
09065327995
Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce ✍️
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page3️⃣8️⃣
Wasu maza ma su ƙirar samudawa suka fito su biyu. Suka ɗauke shi suka saka shi a bayan motar bayan sun toshe ma sa baki da hannu kafin ya yi wani yunkuri, a guje motar ta ta bar layin.
Wata mota dake can gefe ta mara ma su baya a guje.
Motar da ta fahimci ana binta ne sai Direban ya ce wa mutanen nan guda biyu da suke rike da Makaho cewa.
"Wancan me motar na fahimci bin mu yake yi fa?"
Ɗaya daga cikin mutane biyun ya ce.
"Ka san yadda za ka yi ka ɓace wa ganinsa."
Ya yi maganar yana shaƙawa Khalifa hankaci a hancinsa. Wan da ya ya sa Khalifa ya a yi luu ya zube a kan kujerar."
Sai suka sake shi suna kallon motar da aka ce yana bin su. Daidai lokacin ne kuma wayar ɗaya daga cikinsu ya yi ringing.
Suna dubawa suka ga uban gidansu ne yake kiran wayar.
Amsawa ya yi yana cewa .
"Sai oga, aiki ya kammala muna hanya, sai dai mun fahimci wata baƙar mota tana nan tana bin mu, tun da muka dauke shi take bin mu ina kyautata zaton sun ga lokacin da muke dauke shi ne suka bi mu?"
Daga can ɓangaren ya ce .
"What's? Ta ya za ku yi sakaci haka bayan na faɗa ma ku yadda za ku gudanar da komai, to bari ku ji ku tabbatar kun tsere ma su domin idan har kuka yi sakaci aka kama ku to har da kanku kuka yi wa don ba zan taɓa bari miliyoyin da aka biyani akan aikin makahon nan ya tafi a kansa ba na rasa su."
Cikin tabbatarwa ya ce .
"Kafa ka damu boss ba mu taba ma ka matsala ba kuma ba za mu fara kan wannan ba."
Ogan na jin haka sai ya ce.
"Good job."
Ya katse kiran wayar.
Gudu suke ya kamar za su tashi dama don sun kama hanyar barin unguwannin da ke da mutane.
Yayin da su ma motar da take bayansu dai ƙara gudu suke yi don su ga sun tarar da su.
Su biyu ne a cikin motar wanda yake zaune mazaunin direba sai kuma ɗayan yana zaune gefen wajen me zaman banza.
Wanda ke zaune gefen wajen me zaman banza ya kira wata lamba, sannan ya kara a kunnensa.
Bayan an ɗaga ne ya ce .
"Hello sir"
Ta cikin wayar ya ji an ce .
"Hello ya ake ciki ne ina fatan ba wata matsala ko?"
"Akwai matsala yallaɓai."
Ɗan jim ya yi kafin ta ce .
"Meke faruwa?"
"Wallahi wasu ne suka ɗauke shi suka saka shi a motarsu suka bar wajen a guje."
Tsawa ya daka ma su yana cewa .
"Meye amfanin ku da har za ku yi sakaci da wasu za su samu damar ɗauke shi ba ku dakatar da su ba?"
"Wato abu ne da ba mu yi zato ba, ya dawo daga inda ya saba zuwa ya dauki hanyar gidan da yake zaune kenan sai suka ritsa shi suka tura shi a cikin motar da karfi wanda Kafin mu yi wani yunƙuri tuni sun bar wajen. Amma muna biye da su in sha Allah dai mun cin ma su"
"Ita yarinyar da kuka kuna ganinsu tare da ita fa?"
"Ita tana gida shi kaɗai ne suka kama."
"Okay me ya alaƙarsa da yarinyar ne?"
"Abun da har yanzu ba mu tabbatar ba kenan, amma bayan kuɓutar da shi za mu iya gano dangantakar da ke tsakaninsu da ita ."
Yana fadar haka sai ya ji an katse kiran wayar.
Daidai lokacin ne kuma suka nemi motar gabansu suka rasa. Sakamakon sun zo mararraba ce, hanayar ta rabu hudu suka rasa in za su bi , dan ba su san in da za su bi ba, mikewa ne ko kuma damar su za su bi ki hagu.
Gabaɗaya sun rasa in da za su tafi, ga shi mota daya suka fito da ita ballantana ace su rabu wani zai iya hangen su.
Sai dai kawai suka mike ba tare da sanin Ina motar gabansu ta yi ba
_Ma'eesha_
Ganin har na kira sallar magrib makaho bai dawo ba ne hankalin ta ya fara tashi.
Domin ta san baya taɓa kai wa magrib bai shigo ba. Don haka sai ta kira wayarsa. Tana jin yans riginging amma ba'a ɗaga ba. Sai ta dake kira a karo na biyu ta ji wata baƙuwar murya da ba ta taɓa jin sa baya ɗaga kiran wayar yana ka ta sallama. Gaban ta ne ya yi mummunan faduwa amma sai ta dake ta amsa sallamar.
"Wa'alaika Salam, ina mai wayar."
Hajiya tafiya nake yi akan hanya na ji ƙarar wayar, ko da na duba sau na ga kina kira,kafin na daga ta katse sai yanzu da kika sake kira."
Cikin tashin hankali ta ce.
"Ba ka ga wani makaho a wajan wayar ba?"
"Ba kowa sai kayan gyaran takalmin da suke watse a Wajen."
Hawaye ne ya wanke ma ta duka ta ce .
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un. Bawan Allah kana ina ne yanzu?"
Ya yi ma ta kwantancen farkon layin ta ce.
Ita matar me wayar da kayan gyaran takalmin ne ga ta nan fitowa .
Katse wayar ta yi ta daki hijabi ta saka sannan tana fita gudan sauri -sauri gudu-gudu. Har ya karasa wajan.
Tun daga nesa ta hango mutane za su kai biyar a waje ɗaya, ga kayan gyaran takalmin Khalifa nan na a waje ɗaya.
Tana ƙarasowa ta ce
"Don Allah ina kuka ga ya bi da ya zubar da kayansa a nan."
Ta yi tambayar tana kallonsu, wanda ya ba ta wayar ne yake cewa.
"Ga wayar da kayan ki tafi gida zai dawo."
Ta karaɓa tana kallonsa kamar wata sokuwa."
Ɗaya daga cikinsu ne ya ce.
"Kada ka ɓoye ma ta komai matasa ce fa. Hajiya ki yi addu'a Allah ya bayyanar ma ki mijinki, domin wasu ne suka zo da mota suka saka sa ciki da karfin tafiya
Kanta ta dafe tana cewa.
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, ina suka kai shi?"
"Allah masani sai dai duk yadda aka yi wadannan mutanen criminals ne dan ba su yi kama da jami'ai ba."
Goge hawayenta ta yi ta ce.
"Na gode Allah ya saka ma ku da alkhairi."
Tana gama fadar haka ta nufi gida rike da kayan aikinsa da wayarsa a hannunta.
Tana zuwa gidan ta ajiye kayan aikinsa ta fito dan zuwa police station ta kai report. Duk da ta san ba ta da kudin da zai kai ta ya dawo da ita, ɗari biyun da makaho ya ba ta ne wadanda aka cuce shi aka ba shi a matsayin ɗari biyar.
Jin kiran sallar isha'i ya sa ta dakata sai da ta gabatar da sallar isha'i kafin ta wuce bayan ta yi ma sa addu'o'i.
Sannan ta rufe gidan ta kama hanyar zuwa Ofishin ƴan sandan. Sai da ta kai bakin titi sannan ta tsaya.
Mai keke nape ta tare da sanar da shi ya ƙai ta police station ya sanar da ita kudin ta ɗari uku za ta biya, amma sai ta roke shi ya taimaka ɗari biyu take da shi. Ya ha kekensa ya tafi wai shi ba zai iya zuwa a dari biyu ba. Haka ta dinga tare ma su keke kusan su uku ba su dauke ta a ɗari biyu ba.
Hawaye ne ya dinga ambaliya a saman fuskarta kamar an bude famfo.
Bayan hannunta ta sa tana goge hawayenta kafin wani tunani ya fado ma ta a rai.
"A.S.P."
ASP Nasir Yusuf Wani tsohon saurayinta ne wanda ya taba nuna yana son ta a baya ita kuma ta nuna ba ta son sa. Saboda nacin son da yake yi ma ta ne har ta yi blocking nasa a waya, sakamakon yawan kira da messages. A gidan ma ta ce wa Maigadi idan ya zo ya ce ta bar ƙasar. Da haka ya hakura da ya fahimci ba ta son sa.
Tana tsaka da tunanin sai wani mai nape ya tsaya yana cewa.
"Hajiya tafiya ne?"
Ta sanar da shi police station da zai kai ta ta kuka roke shi ya kai ta dari biyu take da shi.
Ganin tana cikin tashin hankali ya sa ya kai ta a haka nan.
Bayan ya sauke ta ne sai ta ba shi kudin ta ciri wayar ta ta yi unblock ɗin A.S.P
Sannan ma sa kira ta yin sai ta ji ringing ɗin wayar a bayanta. Ta waiga ta gan shi sanye da kakinsa na aiki yana kokarin shiga motarsa.
Wayar ya ciro ya duba yana kallon sunan da mamaki, a hankali ya furta.
"Ma'eesha."
Katse kiran ta yi ta karasa wajensa daidai lokacin da yake kokarin bin kiran nata.
_Fahad_
Bayan ya siye kaza da fresh milk park ya nufa in da suka saba zama su shaƙata su da abokansa.
Suna zaune su biyu Sadik da mukhatar suna ganin motarsa suka taso suka ƙarasa wajan , kasancewar ya sanar da su ba zai zauna ba.
Sadik ya shiga gaban motar yayin da Mukhatar ya shiga baya.
"Ya aka yi ne Ɗab America har an gama cin amarcin ne?"
Cewar Sadik yana kallon Fahad. Mukhtar dake baya ya ce .
"Wai kamshin me nake ji ne a cikin motar nan, har da tsaraba ka kawo ma na ne?"
Ya yi maganar yana kallon kazar.
"Ba sai ka ci ba tunda da kudinka na siya."
Mukhtar ya yi dariya yana cewa .
"Wai amarya ana siyo wa wannan kazar? Shegen sama ashe za ka sauko da wuri haka? Ai da cewa ka yi ba ka so har kana fushi da mutane shi ya sa yanzu na ga an..."
"Ya isa haka nan Mallamai, ba ruwanku, sallama na zo mu yi ba na da lokacin ɓatawa."
"Da Nadra za ka tafi ne?"
Cewar Sadik yana kallon fuskar Fahad."
"Why not ka je da ita ? Amma ka ce bayan kun yi aure can za ka zauna da matarka."
"Eh lokacin Ban san ita ba ce a lokacin Sidra ce zan aura kuma ita ta ce can za ta zauna ita da Nigeria sai ta zo ziyara. Ita kuma wannan da yake akwai duhun kai a tattare da ita cewa ta yi ba za ta je ba."
Nam suka ɗan taɓa fira Kafin suka yi sallama da juna suka fito ya bar wajen su ma kowa ya shiga motarsa suka bar wajen kowa ya kama hanyar gidansa.
_Nadra_
Tana zaune a dinning table suna cin abinci ita da iyalan gidan.
Duk wani motsi nata akan idanun Sidra take yin sa. Musamman ganin irin wayar da Nadra ke amfani da shi ya tashi. Musamman da ta ga lokaci lokaci tana duba wayarta.
Ita kuma Nadra sakon Fahad ne ke sake ba ta mamaki.
Bayan sun kammala cin abinci lokacin karfe tara ne sai Sidra ta ja hannun Nadra suka shiga ɗakinta.
Suna shiga ta tura ƙofar tana cewa.
"Ƙanwata wayarki sabuwa ce ko?"
Tana Murmushi take maganar yadda za ta bugu cikin Nadra ta faɗa ma ta.
"Eh sabuwa ce Yaya Fahad ya siya ma ni ita."
Sai da ta ji wani abu ya soki ƙrjinta kafin da daidaita kanta ta ce.
"Na ki ya ɓace ne?"
"A'a shi ya karba ya siyo ma ni wannan ."
"Okay amma dai ya kamata a ce kina kiran masoyinki a waya Ya Sayyadi kuna gaisawa, saboda ya san da cewa kuma jiransa shi ma ya jira ki."
Zaro idanunta waje
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 49