tun da ya gane kece uwarsa ya canza ma ni yanzu da a baya ne ba zai iya kwana bai ji murya ta ba. Yanzu ya daina jin magana ta, da yana jin magana ta da ba zai saka ƙafa ya bar garin nan ba tare da an yi bikinsu ba, ga shi yanzu da an yi bukin tun last month tun da an gama shirin komai, ya tafi na tsawon watanni ya fifita aikinsa akan aure."
Ta karasa maganar ta na fice wa daga ɗakin.
Mom dafe goshi ta yi tana zama bakin gadon.
Ummee tana fita falo ta hadu da Dad yana saukowa. Dama Yaya kana ciki .
Kallon ƙanwar tasa ya yi yana murmushi
"Eh ina ciki Maryam,.lafiya dai ko?"
"Ba lafiya ba gaskiya."
"Subhanallah me ya faru?"
"Gabadaya Jalaluddeen ya canza, ka duba ana saura wata ɗaya aurensa ya bar garin nan ya ce nan da sati Uku zai dawo, sati Uku shiru wata wata uku shiru har yanzu ba ba wanda ya san me yake yi.A taƙaice ma tare da wata mace yake a can."
"Kin ga Maryam ki kwantar da hankalinki, har ya gama aikin da ya je yi ne sai kuma ya sa kansa wani aikin, idan ya kammala zai dawo. Duk satin da ya dawo a satin za'a ɗaura ma sa aure in sha Allah. Mace da kika ce kuma watakila tana taimaka masa ne wajen gudanar da aiki."
Za ta yi wata ƙorafin ya ɗaga ma ta hannu don ya san halin ƙanwar tasa ba ta raina abun magana, kafin ya ce.
"Ɗan ki yana jagorantan manyan jami'ai, tsara yadda za'a gudanar da bincike ko leƙen asiri, tattara da nazarin bayanan sirri. Bayar da rahoto ga manyan shugabanni, taimaka wa wajan tsara tsaron ƙasa. Shugabannin sa na son sa saboda kaifin basirarsa da hangen nesa, sirri da juriya, jarumtaka da riƙon amana. Ƙwarewar nazari da yanke shawara."
Ɗan ki ba gamagarin mutum ba ne, ba za ki samu lokacinsa a daidai wanann lokacin ba, ki yi ta yi ma sa addu'a Allah ya kare shi a duk in da yake."
"Amma har da matarka ba ta san halin da yake ciki ba take ɓoye ma ni?"
"Maryam kada ki kawo wanan a ranki, domin kuwa Dr ta yi ma ki kawaici da sadaukarwa, shin ta taɓa nuna ma ki wata alama da ke nuna ita ta haifa Jalaluddeen?"
Kai ta girgiza alamar a'a.
" Ko ta taɓa nuna tana da iko akan Jalaluddeen?"
Nan ma kai ta girgiza alamar a'a.
Gajeren murmushi ya yi kafin ya ce.
"Ko kin san cewa lokacin da Jalaluddeen ya haɗu da ƙanwar Dr a gidan nan ya nuna yana son ta ba karamin farin ciki Dr ta yi ba, ganin Ɗan ta zai auri ƴar ƙanwarta . Amma kika nuna iko da isa kika ce bai isa ya aure ta ba kin zaɓa ma sa ƴar ki. Haka ya hakura ya yi ma ki biyayya, Dr ba ta nuna damuwa ba. To me ya sa yanzu kike tuhumar ta a kan lamarin Jalaluddeen bayan ba wata shaƙuwa ce tsakanin su ba, in fact bai fi shekara da sanin cewa Dr ta haife shi ba, wanda bayan sanin bai zo gidan nan sama da sau uku ba."
Shiru Ummee ta yi sannan ta sauke ajiyar zuciya.
"To Yaya ni zan tafi sai anjima."
"Allah ya tsare ki gaida Mutanen gidan."
Daga haka ta fice daga falon in da ta sami Jimoh yana jiranta.
Dad ya nufi ɗakin Mom, da sallama ya shiga, yadda ya ga ta hada tagumi ya san zantukan ƙanwarsa ne suka taɓa ta.
Zama ya yi gefenta ya yana cewa.
"Dr har kin shirya?"
"Eh na shirya."
Ta fada tana kokarin saka farin gilashi a idanunta.
"Ki yi hakuri da abun da Maryam ta yi, kin san ba ta da fahimta ne, amma in sha Allah na san ba wata matsala."
Cikin damuwa ta ce.
"Ni ba ni ce na fitar da sirrin cewa ni ce mahaifiyar Jalaluddeen, ita ta fasa sirrin ta hanyar ba shi auren ƴar ta, ban taɓa saka baki a lamarin da ya shafi Jalaluddeen ba, ita ce take yanke hukunci kan al'amuran shi kame yadda uwa ke yi wa ɗanta. Iyaka ta da shi daga gaisuwa . Sai idan azumi ya zo yake jido ma na kayayyaki na abinci da na sakawa da kyautar kudade, daga nan kuma sai wata shekara. Na san cewa shi yake ɗauke da nauyin gidanta cin su sha da sutura duk a wuyansa yake ya dauke ma su Wannan. Duk shekara sai sun je Umara duka shi ke yi, hatta dangina mijinta da Jalaluddeen yake kallon dangin ubansa ya kai da yawan su Makkah sun sauke farali, dangin ja sun ci moriyar dukiyarsa ne? Duk kawaici da alkunya da nake nunwa ba ta gani har za ta zo tana tuhuma na akan Ɗan da na haifa?"
Dad ya san ranta ne ya ɓaci ɗin idan ba haka ba sama da shekara talatin da uku ba ta kiran Jalaluddeen da Ɗanta .
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce✍️
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page5️⃣6️⃣
Dad ya san ranta ne ya ɓaci dan idan ba haka ba sama da shekara talatin da uku ba ta kiran Jalaluddeen da Ɗanta .
"Ki yi haƙuri Dr "
"Ya wuce amma ka ja wa ƙanwarka kunne."
"In sha Allah hakan ba za ta sake faruwa ba."
A tare suka fito daga ɗakin in da ma'aikatan gidan suka jera breakfast a dinning table.
Ba ta ko kalli dinning area ba ta nufi hanyar fita.
"Dr ki tsaya ki yi breakfast ma na."
"Ba lokaci ana jira na, zan yi a can."
Daga haka ta fice ya raka ta har wurin motarta, da kanta take driving cikin nutsuwa ta bar gidan.
_Makaho_
Yana kammala abun da zai yi da misalin ƙarfe uku da rabi ne ya miƙe tsaye.
Kayan jikinsa ya cire ya saka kayan da ya zo da su a jikinsa. Duka wayoyinsa ya ajiye a nan, ya tafi da guda biyu ƙananu. Ɗaya na amfani domin aikinsa ne ɗaya kuma Wanda yake waya da Ma'eesha ne.
Baƙin gilashinsa ya saka sannan ya saka takalmin soso da zo da su. Ya kashe komai da ke ɗakin sannan ya fito daga ɗakin.
Har lokacin wanann mai nape na zaman jiransa, sai da ya fito ne ya shiga suka bar wajan.
Nesa kaɗan da wajan aikinsa ya ajiye shi, kafin ya fito ya ɗauko sandarsa ya cigaba da dogarawa yana irin tafiyar da yake saba yi.
Wajen sana'arsa ya ƙaraso da sallama, suka amsa ma sa, Bello me yalo yana yi ma sa sannu da dawowa kafin ya ce.
"Na ga ka daɗe lafiya dai ko?"
"Alhamdulillah wajen ne da nisa."
"Allah sarki sannu."
Gajeren murmushi kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba.
Yana nan zaune sai ya ga wata mota ta gifta kan titin.
Makaho ya cire tsohuwar wayrsa daga cikin aljihu, ba waya ce irin ta kowa ba, waya ce ta aikinsa.
Ya yi magana ƙasa-ƙasa a cikin wayar yake cewa.
"Target ya motsa."
Daga ɗaya bangaren aka amsa da .
"Kar ka bari ya ɓace."
Sai ya koma ya cigaba da gyaran takalmin da yake gyarawa kamar babu abun da ya faru.
Daga haka ya ɗan miƙe kasancewar yana da Ɗan tazara tsakanin sa da sauran mutane da suke Zaune kowa na sana'ar sa.
Kiran sallar la'asar ce ta saka ya ajiye komai ya tashi yana cewa.
"Bello don Allah taimaka ma ni da buta na yi alwala."
Kasancewar suna ajiye ruwan sallah a bokiti mai murfi.
Mai suyan awara dake kusa da su ta kalli Makaho ta ce.
"Wallahi shi ya sa Khalifa kake ƙara burge ni, ba ka wasa sa ibada."
Bai ce da ita Komai ba illa ya yi gajeren murmushi.
Bello ya kawo ma sa ruwan,.sai ya karkace hannu yana laluben gefen da ba nan butar take ba, sai da Bello ya rike hannunsa yana cewa .
"Ga ruwan nan."
Ya karba yana godiya. Gefe ya ma tsa ya yi alwala kafin ya ce .
"Jama'a ku tashi mu yi sallah lokaci na wuce wa yanzu za'a tayar."
Wasu sun tashi wasu kuma ko a jikinsu.
Bayan an idar da sallah ya fito daga masallacin gabaɗaya mai suyan awara ifanunta na kansa, tana ganin ikon Allah, cikkaken namiji mai cikar zati da haifa ya hadu ta ko ina sai dai jarabtarsa makanta da talauci.
"Bana son yawan kallo."
Ta ji maganar kamar daga sama, wanda sai da ganinta ya faɗi. Cike da mamaki ta ce.
"Khalifa waye ke kallo ka?"
"Ban san ko waye ba, amma ina ji a jikina ana kallona kuma kallo na ƙurilla."
Wanda yake faci daga can gefe ne ya bude baki ya ce.
"To meye abun kallo a jikin naka, nakasar za'a kalla ko me?"
Kafin ya yi magana mai suyan awara ta ce.
"Namiji ƙira da cikar zati , kyau da kwarjini."
"Dalla rufe wa mutane baki Mallama ina kwarjini ga makaho?"
Ya faɗa a fusace, dama yana jin haushi yana son me awara ba ta son sa, kuma ta yi ta yawan kallon makaho tana jan sa da fira duk da ba wani kula ta yake yi ba. Sai dai yana burge ta amma ba ta jin za ta iya soyayya da makaho talaka.
Mai Yalo da ya sa baki yana nuna wa Mai faci ya daina abun da yake yi , wanda shi kuma Makaho ya ya ɗauki kayan aikinsa ya tafi. Don idan ya tsaya tabbas zai iya illata wannan mutumin kuma za'a san shi waye.
_Ma'eesha_
Ta yi wanka tana jiran dawowar mijinta don tana ta damuwa tun karin safe bai ci komai ba, kamar ta sani kuwa dama bai ci komai ba, don ko ruwa bai sha a hotel ɗin ba.
Da sallama ya shigo cikin gidan, ta ɗago kai ta kalle shi tana amsawa da .
"Wa'alaika salam warahmatullah."
Ta mike fuskarta ɗauke da fara'a ta karbi kayan hannunsa tana yi ma sa sannu da zuwa.
"Yauwa ya gidan."
"Alhamdulillah."
Hannunsa ta riƙe ta taimaka ma sa ya zauna a tabarmar da ta shimfiɗa.
Zama ya yi ta kawo ma sa pure water mai sanyi da ta siyo a kanti ta zuba a jug.
Ya sha ruwan yana yi ma ta godiya.
Abinci ta kawo ma sa yana ci tana yi ma sa fifita har ya gama. A hankali ya furta
" Alhamdulillah."
Murmushi ta yi tana cewa .
"Ma sha Allah."
Kallonsa ta yi na wasu second kafin ta ce .
"Am na ce ba."
"Me kika ce ranki ya daɗe?"
"Na ce maganar sace ka da aka yi fa har yanzu hankalina bai kwanta ba, saboda rashin sanin manufar ma su satar naka, ga shi kai ba gani kake yi ba ballantana idan ka ga wani abu da bai ma ka ba ko makamancin abun da ya faru da kai ka nemi taimako a kowane waje kake. Idan ka fita gidan nan hankalina baya kwanciya sai na ga dwowar ka, ba na so na rasa ka a duniyata da ba na da kowa sai kai."
Ta karasa mgana tana zubar da hawaye.
"Kada ki damu in sha Allah ba abun da zai same ni."
Sallamar mace suka ji daga kofar gidan, suka amsa yayin da ya tashi ya shiga ɗaki kafin mai sallamar ya shigo cikin ɗakin.
Wata mata ce maƙociyarsu ta shigo gidan.
"Sannu da zuwa."
Ma'eesha ta faɗa cikin sakin fuska da walwala.
"Yauwa sannu baiwar Allah."
Matar ta faɗa tana zama a ranarma tare da ajiye madaidaiciyar jakar hannunta. Gaisawa suka yi kafin matar ta ce .
"Sunana Bilikisu maƙociyarki ce duk da ba ki shiga jama'a ballantana a saba da juna."
"Haka ne, in sha Allah zan shigo."
Duka maganar da suke yi yana jin su daga cikin ɗaki, ita matar ba ta san cewa mijin Ma'eesha na gidan ba, don haka ta ce .
"Talla na kawo ma ki ga su nan, kayan gyaran aure ne magungunan mata ma su kara ni'ima da Ɗanɗano "
Shiru Ma'eesha ta yi tana tunani, ita me za ta yi da waɗan nan kayan, ita da ba ta da ko sisi, ko tana da kuɗi ma ai ba za ta siye ba, meye amfanin su mijin da ko hannunta bai taɓa rike wa ba ballantana wata Mu'amalar aure ya shiga tsakanin su. Don sai dai ita ta rike hannunsa amma shi bai taɓa rike hannunta ba, ta lura ko jikinta bai so ya haɗu da nasa, take zai zame jikinsa ta rasa dalili.
Maganar matar ce ta dawo da ita cikin hayyacinta .
"Wanne kike so ga su nan na fito ma ki da su."
Ma'eesha ta kalli magunguna daga na kwali har na roba ga sunanyen su nan da yadda ake amfani da su.
Murmushi ta yi kafin ta ce.
"Allah ya kawo kasuwa."
"Haba baiwar Allah ai yanzu mata ba sa zama ba gyara, idan kina da kyawu sai ki kara da wanka, yadda oga zai samu gamsuwa yadda ya kamata"
Murmushi ta sake yi kafin ta ce .
"Ina da su da yawa ne idan na siye wasu yanzu za su yi ma ni yawa ne."
"Shi ke nan tun da haka kika ce, amma bari ba ba ki wasu kayan kyauta idan kika yi amfani da su da kanki za ki biyo ni."
Magunguna ta dauka kala uku sai wani turare ta ba ta su kyauta. Ba ta da wani zaɓi don haka ta karba tana yi ma ta godiya.
Fitar matar kenan sai ga Nasreen ta shigo da sallama.
"Assalamu alaikum Matar Khalifa na nan?"
Murmushi ta yi tana cewa .
"Ina zan je ƙawata."
Zama ta yi gefenta tana cewa.
"Daga unguwa nake na ce bari na biyo na duba ki."
"Allah sarki aiko na gode. Ya jikin Mama?"
"Mama ta ji sauƙi sosai."
"Ma sha Allah, Allah ya kara lafiya."
"Amin ya Allah."
Kallon magungunan ta yi kafin ta ce.
"Tofah, Ma'eesha kayan mata kike siya?"
Ba ta tanka ma ta ba ta dai yi murmushi.
"To a dai bi a hankali a san irin abun da za'a dinga sha."
"Ke ba fa sha nake yi ba, idan akwai macen auren da kika san tana sha kwashe ki kai ma ta."
"Ban gane ba ke meye na siye to."
"Ba siya na yi ba, ba ni ta yi kuma ba zai ma ni amfani ba kamar yadda ke ma ba zai ma ki ba."
Cikin tashin fahimta Nasreen ta kalli Ma'eesha ta ce.
"Ni da ba matar aure ba ke kuma ai kina da miji."
"Hmmm sunan dai ina da miji ne kawai amma ba wani mu'amala ta aure ya taɓa haɗa ni da shi."
Da mamaki ta kalle Ma'eesha kafin ta ce
"Duk watannin da kuka yi ba wani abu da ya shiga tsakanin ki da shi kuna kwana daki ɗaya? Ko bai da lafiyar mazantaka ne?"
"Ban sani ba wallahi. Kuma kin san wani abu?"
"Sai kin faɗa."
"Ina matuƙar so na ga na samu ciki, saboda ina son yara a rayuwata , burina na ganni rungume da baby na."
"To ba ki tunanin a cikin wannan rayuwa da kike ciki za ku iya ɗaukar ɗawainiyar baby?"
"Za mu iya domin Allah baya ɗorawa bawa abun da ya fi ƙarfinsa. Kuma ba mu fatan dauwama cikin wanann halin da muke ciki."
"Okay yanzu kafin ki yi tunanin cikin da kike so ki fara tabbatar da lafiyar mijinki, idan kuna haɗa jiki wuri guda yanayinsa baya sauya wa?"
"Ai baya yarda mu hada jiki da juna, da zaran na hada jiki da shi zai zame da sauri, ke ko kwanciya baya yarda mu yi a shimfiɗa ɗaya."
Sai da Nasreen ta yi dariyar mai isarta kafin ta ce.
"Ina da tabbacin lafiyarsa ƙalau, kuma yana nisanta kansa daga ke ne saboda baya son wani abu ya shiga a tsakanin ki da shi. Don idan da bai da lafiya ne ba zai damu dan kun hada jiki ballantana ya nisanta kanki da shi, kin ga alamar yana tsoron abun da zai iya biyo baya ne, sai dai ban san dalilinsa na yin hakan ba."
Shiru Ma'eesha ta yi kafin ta ce .
"Ba damuwa sai mu tafi a yadda yake so, don duk yadda nake son haihuwa ba yadda za'ayi ina ƴa mace da aka sani da al-kunya na kai kaina wajan namiji ."
"Ba za ki kai kanki ba amma ai mace ce ke, akwai hanyoyi da yawa da za ki iya saka shi ya kawo kansa gare ki ba tare da ya shirya wa hakan ba."
Murmushi ta yi kafin ta ce.
"Bari na faɗa ma ki a kunne ."
Ta matso dab da Ma'eesha ta matso da fuskarta saitin kunnen Ma'eesha, ta fara yi ma ta magana cikin raɗa.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce✍️
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page5️⃣7️⃣
Ta matso dab da Ma'eesha ta matso da fuskarta saitin kunnen Ma'eesha, ta fara yi ma ta magana cikin raɗa.
Wani kallo Ma'eesha ta yi ma ta kafin ta ce.
,"Ke ni za ki kai ki baro? Wallahi ba zan yi ba sai dai mu yi ta zama a haka, matukar sai na bi wannan hanyar da kika zo ma ni da ita."
"To shi kenan tun da haka kika ce."
Fira suka ɗan taɓa kaɗan kafin ta miƙe bayan ta ciro kayan kwalama da ta zo ma ta da su. ice cream ne da au Chocolate ta ajiye ma ta, sallama suka yi ta fice daga gidan,.ita kuma ta ɗauki ledar kayan da kuma kayan matan da maƙociyarsu ta kawo ma ta su ta shiga ɗakin.
Da sallama a bakinta ta shiga ɗakin , ya amsa mata ta kalle shi ta ce.
"Lafiya ka zauna a ɗaki?"
"Na ga kin yi bakuwa ne shi ne na ba ki waje ku gaisa."
"Ayyah maƙociyarmu ce ita."
"Ayyah me ta zo yi ne?"
Kallon magungunan ta yi wanda shi ma kallon magungunan yake yi, wanda kallo daya ya yi wa magungunan ya ɗauke kai, kuma ya san me magungunan ya ƙunsa amma kasancewar kallon makaho take yi ma sa ya sa ba ya san magungunan yake kallo ba, don duk firar su har da na Nasreen ya ji su.
Murmushi ta yi kafin ta ce.
"Kawai ta zo wai mu gaisa ne da ita kasancewar ban taɓa shiga maƙota mun gaisa, da na zo ya kamata na je na gaida su. Bayan matar ta fita ne Nasreen ta zo ita ma akan hanya yake har ya tafi."
"Ya jikin Maman nata?"
"Da sauki ta ce."
"Ma sha Allah, Allah ya kara ma ta lafiya."
"Amin ya Allah."
"Bari na je masallaci Magrib ta gabato."
"Okay bari na zuba ma ka ruwa a buga."
Daga nan ta fita daga dakin don zuba ma sa ruwa.
_Nadra_
Bayan ta yi wanka ne ta saka kayan barci riga da wando farare na su taushi da santsi , wandon dogo ne shi , ta tufke gashin kanta sannan ya saka hula.
Har za ta yi taurin akbar kwanta kuma sai ya tuna da gargadin da Fahad ya yi ma ta. Don haka sai ta ba nufi ƙofar fita daga ɗakin.
Yana zaune a falo hannunsa rike da waya yana sarrafa ta, tana fitowa ya tsaya yana kallonta sosai, domin kuwa ta yi ma sa kyau sosai fiye da yadda yake tunani, ga kayan barcin su.n zauna ma ta ɗagwas kamar saboda ita aka yi kayan.
Fuskarta a tsuke take, ganin ya tashi ya nufi dinning area ita ma ta tashi ta bi shi.
Ba ta zauna ba ya saka ma ta naman kaza a plate ya zuba ma ta yoghurt a glass cup.
"Zauna ki ci ki sha magani."
"Na ƙoshi."
Ta faɗa tana hade rai. Ɗaya kai ya yi ya kalle ta da kyau , kafin ya ce.
"Ba na son gardama kuma ba na maimaita magana dayay, kar ki bari na sake yi ma ki magana.
Zama ta yi tana tura ba ki , ga shi yunwar take ji amma kuma taurin kanta ya hana ta zauna ta ci. Ganin kallon da ya yi ma ta ne ya saka ta fara ci kamar za ta yi kuka .
Sai da ta ci kusan rabi ta ce ta ƙoshi. Kofin gabanta ya yi ma ta nuni da shi, ta ɗauki yoghurt din ta shanye.
Magani ya ba ta ta karba kamar za ta yi kuka, sai da ta shanye ta bar kasar Wajen. Da ido ya bi ta har ta shiga cikin ɗakinta.
Shi ma ya ci sauran wanda ya rage sannan ya kwashe kayan ya kai kitchen.
Ɗakinsa ya shiga ya yi wanka ya yi shirin barcina ya kwanta kan lafiyayyen gadonsa don yin barci.
Ita ma tana komawa ɗakinta ta wanke baki ta ɗauro alwala sannan ta kwanta barci. Ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita.
Amma shi kam Fahad a nasa ɓangaren ba haka ba ne, domin ya kasa barci sai tunanin Nadra ya saka shi gaba. Lokaci zuwa lokaci yake jan tsuki ya kasa gane dalilin da ya sa yarinyar nan ta yi kane-kane a cikin zuciyarsa. Yarinya sai ka ce Mayya. Sai cikin dare barci ya yi nasarar ɗauke shi.
_Ma'eesha_
Kamar yadda ya zame ma ta al'ada kullum sai Khalifa Makaho ya yi ma ta fifita take iya barci yau ma haka ne, yana tsaka da ma ta fifita barci ya yi awon gaba da ita.
Yana ganin ta yi barci ne ya yi sauri ya je ya ɗauko wata ƙatamar fanka a cikin kayansa, ya bude fankar ya ja ta ta ɗan yi tsayi sannan ya kunna ya ajiye ma ta.
Wani abu da ba ta sani ba, a duk lokacin da take yin barci Makaho kunna ma ta fanka yake yi ya fice daga gidan. Yakan je ne ya gudanar da bincikensa cikin dare. Saboda mutanen da yake yin aikin a kansu a dare suka fi yin harkokinsu. Don haka ne ma idan Ma'eeha ta yi barci yake ajiye ma ta fanka ya fice. Sai tsakiyar dare shiyoyin ƙarfe ƙarfe uku na dare yake dawowa, don a cikin awanni biyu yake kammala abun da ya fita da shi yake dawowa.
Kuma ita ba ta san da fankar a cikin gidan ba, don ba taɓa ma sa kaya take yi ba.
Bayan ya ajiye ma ta fankar ya cire kayansa ya sauya daga manyan kaya zuwa ƙananan kaya.
Na'urar ɗaukar sauti ya ɗauka ya maƙala a jikinsa sannan ya ɗauki ɓoyayyer wayarsa ta zuwa aiki ya bar gidan.
Nan Ma'eesha ta cigaba da barci ba tare da ta san baya gidan ba.
Sai zuwa can da misalin karfe uku da rabi ya dawo gidan.
Cikin sanɗa yake tafiya ya shigo cikin ɗakin.
Wasu takardu ya ɗauka a cikin kayansa ya yi rubutu a jiki, ya shigar da wasu bayanai, kafin ya tashi ya karasa in da take kwance tana barci .
Fankar ya dauke ya kashe sannan ya yi saurin zama a gabanta yana yi ma ta fifita .
Baya karfe huɗu ta cika ne ta farka daga barcin, ganinsa ta yi zaune yana yi ma ya fifita, karɓe mafecin ta yi tana cewa.
"Wai Yaya Khalifa me ya sa ba ka tausayin kanka ne?, Ta ya mutum ya zauna tun daga farkon dare har ƙarshen dare bai yi barci ba yana zaune, ko so kake yi ka samu wani ciwon mu shiga uku."
"Na saba babu abun da zai same ni."
"A'a barci ma lafiya ne ga jikin mu, yanzu ka kwanta na awa ɗaya idan ƙarfe biyar ta yi zan tayar da kai ka je masallaci ka yi sallah."
Ganin yadda ta dage har tana ɓata rai ne ya saka shi dole ya amice zai kwanta, ganin yana ƙoƙarin zuwa kan tabarmarsa ne ya saka ta rike hannunsa tana cewa .
"To ai yanzu ba kwanciya zan yi ba ballantana ka ce ba za ka kwanta tare da ni ba. Ka dawo kan katifar ka kwanta kai kaɗai ne za ka kwanta."
Murmushi kawai yayi sannan ya hau kan katifar ya kwanta.
Nan ta dinga yi ma sa fifita cikin mintuna goma barci ya yi awon gaba da shi.
Tana yi ma sa fifita na tsawon awa ɗaya sannan ta fara tunanin tayar da shi don lokacin sallah ya gabato.
Kyakkyawar fuskarsa ta zuba wa idanu tana kallonsa, sannan ta kira sunan sa a hankali.
"Yaya Khalifa, Yaya Khalifa, Yaya Khalifa."
A hankali ya amsa yana mai tashi zaune bakinsa da salati.
"Ka yi hakuri ka ji dadin barci , na ga lokacin sallah ta yi ne shi ya sa."
"Ba komai na gode Allah ya yi ma ki albarka."
Da Amin ta amsa sannan suka fito daga ɗakin don lokacin sallah ya yi .
_Sidra_
Tun da ta ga Fahad ya bar gidan da Nadra ranar ba ta iya barci ba, hankalinta ya kai ƙolololuwar tashi.
Duk ta firgice ta fita hayyacinta musamman da ta ga yadda Fahad ke ta rawar ƙafa akan Nadra yayin da ita ki kallo ba ta ishe shi ba.
Shirya wa ta yi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 33 Chapter of 49