ba.
Aka buƙaci amarya da ango su fito, nan fa Nadra ta noƙe ta ƙi fitowa, ganin take-taken ta ya saka ya riƙo hannunta, don idan ba haka ya yi ma ta ba ya san ba tashi za ta yi ba.
Janyo ta ya yi ya rike hannunsa cikin nata har suka fito cikin tsakiyar taron.
Ana ma su liƙin kuɗi ita da ƙokarin kare ƙirjinta take yi da hannayenta guda biyu.
Don abinda ya sa ta kara tsanar kayan saboda ƙirjinta da aka yi kamar na bra a tsuke kuma ga baby hannun arziki a jiki.
Ganin za ta rungume hannaye kamar mai jin sanyi ya saka ya yi saurin rike hannun nata yana rawa ana watsa ma su kuɗaɗe ƴan dubu-dubu har da ɗari biyar-biyar. Mama da su Aunty Rahama da sauran danginsa sai liƙi ake yi ma sa. Farin ciki ya lulluɓe Mama sai liƙi kawai take yi wa surikar tata. Don Nadra ta ji ta shiga ranta haka ma Aunty Rahama sai ɓarin kuɗi take yi, da sauran dangin Fahad.
Bayan dangin ango sun koma wajen zamansu sai ga dangin Amarya sun fito su ma. Su Gwaggo Laraba da Gwaggo Maimuna da saran dangin Abba da ƙawayen Umma.
Bayan sun ma sun yi ma su nasu liƙin sai abokan ango suka fito.
Nan fa Sidra ta kasa nutsuwa ganin samari matasa ne irin Fahad Ke ta yi ma su liƙi.
Ga Fahad ya ki sakin hannuwanta yadda yake rawa da ita ne ya saka ita ma idan ka kalle ta za ka yi zaton rawar take yi .
Ga takalmin ta gaji da shi kasancewar ita ba ma'abociya saka dogon takalmi ba ne, baya ta yi kamar za ta fadi sai ya yi saurin riƙo ƙugunta ya dawo da ita ta fado jikinsa.
Ba ta san san da ta kwantar da kai a ƙirjinsa ba saboda tsoron faɗuwar da za ta yi da dogon takalmin da ke ƙafarta.
Ta yi lamo a ƙirjinsa ta rintse idanunta tana jin yadda gaban ta ke faduwa.
Dariya ta ba shi yadda take da tsoro haka har ya yi murmushi yana kallon fuskanrta nan aka dinga tafi ana ɗaukarsu photo wanda hakan ya sa ta dawo cikin cikin nutsuwarta, da sauri ta raba jikinta da nasa.
Daga nan kuma aka fara daukar photo amarya da ango da sauran jama'a, dangi da abokan arziki.
Baga gama ba gajiya ya saka Nadra barin wajen ta nufi wajen zamanta ta zauna.
Daga nan kowa ya dinga zuwa yana dibar kalar abinci da abun sha da yake so.
*Abuja*
Satin Muryar Sidra ke tashi a cikin madaidaicin falon tana tsaye rike da kugu cike da masifa take kallon ƙawar tata Sady baby.
"Amma wannan ma su raunin hankali ne, wasa da hankalinmu ya yi ko me?"
"Ki hanyar da hankalinki ƙawata ba..."
"Dalla rufe ma ni baki wani kwantar da hankali zan yi, bayan na ga alamar mafarkina ba zai zama gaskiya ba, sanin kanki ne cewa burina na samu ɗaukaka na yi suna fiye da yadda waccen sakaryar da ta wulakanta ni saboda ta yi samu suna. Burina na rama wanda a dalilin haka na gudu ranar aurena da masoyina na bar kowa nawa don na samu cikar burina."
"Wallahi ya ce wai ai tun shekaran jiya aka yi ba mu zo akan lokaci ba bar an gama ta tacewa sun zaɓi wata, ya kuma tabbatar ma ni da cewa da a ce kin zo da ke za'a zaɓa saboda duk kin fi su haɗuwa kuma ya san za ki iya, lokaci daya za ka ki yi suna don babban kamfanin ne fa suke ɗaukar ƴan tallan."
"Aikin baza da wofi wallahi ni kin cuce ni kin sa na bar aurena na zo nan, da yanzu an ɗaura Mani aure da Fahad, dole na koma Kaduna a yammacin nan na roki iyayena gafara gobe a daura Mani aure da masoyina ba zan yi biyu babu ba."
"Biyu babu kam ai kin yi shi, ba ki ga tsunsu ba ki ga tarko kin ɓarar da damarki."
"Akan uban me kike magana ke kuma?"
Ta jiy maganar a fusace.
Mika ma ta wayar ta yi tana cewa
"Ga shi ki kalli yadda wannan bikin da Khadijah ta tura Mani."
A wulaƙance Sidra ke kallonta kafin ta karbi wayar ta fara dubawa. Photon farko shi ne in da ta ga Nadra kwance a kirjin Fahad ta rungume shi, yana kallon fuskarsa yana murmushi.
Sannan ta kalli in da suke tafiya yana rike da hannunta tana shigewa jikinsa sai na ukun in da suke rawa Ga mahaifiyar Fahad da Aunty Rahama na ma su liƙi tana dariya.
Sakin wayar ta yi tana dafe kanta da ta ji yana sara ma ta ga wani duhu da take gani. Tana girgiza kai tana cewa.
"No no no ba impossible ta ya Abba da Umma za su aiki ta haka, ko Fahad ba zai yarda da wannan abun ba, kawai editing ne aka haɗa amma Fahad nawa ne ni kaɗai ba babu macen da ta isa ta raɓe shi ban ga bayanta ba."
Wata budurwa ta karaso ta ajiye masu faranti da Fruits da wuƙa.
"Magana ta gaskiya dole ki hakura ya zama mijin ƙanwarki."
Wuƙar dake hannunta ta dauka tana nuna wacce ta yi maganar tana cewa
"Idan kika sake fadar haka sai na kashe ki."
Ganin ba ta da hankali ya saka ta ce.
"Allah huci zuciyarki na bar ki lafiya."
Wuƙar dake hannunsa ta fara yankar hannunta tana ta surutai cikin ficewar hayyaci.
Yadda jini ke zuba ya sa hankalin Sady baby tashi ta ce .
"Meye haka Sidra za ki illata kanki fa, ba ki ganin yadda jini ke fita daga jikinki?"
"Wallahi ba zan iya rayuwa ba Fahad ba ba wacce za ta raba ni da shi ki ce karya ne bai auri ƙanwa..."
Jiri ne ta ji yana ɗibarta ta zube wajen akan kujera.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce ✍️
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page0️⃣9️⃣
Jiri ta ji yana ɗibarta ta zube a wajen akan kujera.
Sady baby ta yo kanta tana kiran sunanta, sai a lokacin ta fahimci ashe suma ta yi.
Ganin ba kowa a falon ya duk sun watse ta nufa fridge da kanta. Ruwa ga ɗauko mai sanyi ta yayyafa ma ta.
Wani ajiyar zuciya ta ja kafin ta fashe da kuka. Idanunta a rufe take cewa.
"Sady ina fatan ba gaskiya ba ne ko? Na san yadda Fahad Majidaɗi ke so na ba zai iya auren wata ba, na taho nan da zumar idan ba na nan za su ɗaga bikin zuwa lokacin da zan dawo sai a ɗaura ma ni aure da shi ko?"
Cikin kwantar ma ta da hantdady ta ce.
"Ba komai wannan fa ƙsrya ne ba gaskiya ba ne, ki daina saka damuwa a ranki ke ma ki. San wannan zamani da muke ciki fuska kawai za'ayi amfani da shi aje a haɗa kamar a tare suka dauki photo. Ki cire s ranki ke fa da bakin ki kika ce Fahad na son ki zai hakura har sai kin dawo kafin ayi bikin auren naku."
Ba dai ta gamsu ba haka ta dai yi shiru don kanta na matsa wani irin ciwo ne mai tsanani.
"Bari na kira wata nurse dake kusa da mu, ta zo ta dubs wannan raunin da lima ji wa kanki da wuƙa.
Tana fadar haka ta fice daga falon zuwa kiran nurse.
Sidra ta dafe kanta dake ma ta ciwo sosai sannan ta kwantar da kai tana lumshe ido zuciyarta cike da tunanin Fahad, tana tuna ƙamshinsa mai saka ta nutsuwa da shauƙi.
_Nadra_
Tana zaune a mazauminta Fahad na gefenta yayin da mutane ke zagayowa su tsaya bayansu ana ɗaukarsu photo.
Yayin da mafi yawanci suna zuwa su ɗebi kalar abincin da suke son ci da kalar ruwan da suke so sha.
Ita dai Nadra ga ta nan ne kamar me jin sanyi .
Har aka gama ciye-xiye da lashe-lashe.
Sannan aka zo wajan yanka cake suka ta so don yanka xaket, a nan ne ya sake ganin aminiyar Sidra wato Khadijah. Ya yi mamakin yadda ta fito take fadar halayyar Nadra bayan ita kawa ce ga Sidra. To me ta zo yi? Wani makirin murmushi ya yi saboda ya san dole za ta tura wa Sidra abinda ke faruwa wajen wannan bikin, kuma yana da yakinin cewa yadda Sidra ke mahaukacin son sa dole za ta ji zafi a ranta idan ta ji ya aure ƙanwarta. Duk da ba ya da tabbacin zaman nasa da Nadra. Don haka ya kalli Khadijah dake ma su video tabbas Sidra za ta gani zai aikata abun da idan Sidra ta gani zata ɗanɗani ɓacin rai kwatankwacin yadda ta saka ya ji shi ma. Zai tabbatar ma ta kamar bai ji haushin abinda ta aikata ba
Hannunsa ya ɗaura saman na Nadra tana kokarin janye hannunsa bai ba ta damar hakan ba. Ya rike hannunta suka fara yanka cake.
Ƙasa-ƙasa da murya ta fara magana tana cewa .
"Yaya Fahad ka daina taɓa jikina ba na so ni ba Sidra ba ce, haramun ne Please ka daina."
Kamai bai ji ta ba bayan sun yanka cake ɗin aka dinga yi ma su tafi ana ɗaukarsu photo.
Sanin ba ba za ta yi abinda yake so a wajen ba, da kuma kokarin ɓata ran Sidra don ya san za ta gani..
Suna yankawa ya riƙo hannunta dake rike da cake, zuwa bakinsa ya kai ta ciyar da shi ana ma su photo, sauran na bakinsa sai ya tallabo gefen fuskarta da hannayensa biyu, sauran ba bakinsa ya haɗe bakinsa da nata wuri guda na cikin bakinsa ya tura ma ta a bakinta, take wajen ya ɗauki sowa da ihu ana tafi.
Nadra mutuwar tsaye ta yi saboda mamaki da al'ahabin Fahad Majidaɗi. Wai yau ita ce wani namiji da ba mijinta ba ya haɗe bakinsa da na ta waje ɗaya yana tura ma ta abinda ke cikin bakinsa a tsakiyar jama'a ko kunya baya ji a gaban kowa zai iya aikata hakan har iyayen sa na wajen. Lallai yau ta kara tabbatar Fahad mara kunya ne lamba ɗaya.
Barin wajen ta yi ta koma mazaunin ta. Kanta a sunkuye tana goge ƙwalla.
Ana kiran sallar magrib aka tashi daga taron, Amarya da ango suka nufi wajan motarsu.
Kunyar abinda Fahad ya ma ta ya saka ta kasa daga kai ta kalli kowa.
Direbansa ya yi saurin bude ma ta murfin motar ta shiga ta zauna.
Daga nan ne ta fashe da kuka shi kuma yana can yana sallama da abokansa.
Har ya dawo ya shiga motar tana kuka. Kallonta ya yi cike da takaici ya ce.
"Ke me aka yi ma ki za ki saka mutane gaba kina kuka?"
"Kan me za ka aikata ma ni haka?"
Ƙyasta yatsunsa biyu ya yi ya ba da wani sauti wanda hakan ya saka diraban ya fita da sauri ya ba su waje, don ya gane uban gidan nasa na bukatar sirri ne."
"Kin ɗauka abun da na yi ma ki da son raina na yi ma ki ne, in ban da ƙaddara da ba ta riga fata ke kin isa ma na rike hannunki ne? Ba ki da wannan ajin da zan iya taɓa jikinki. Dole ne ta saka na aikata hakanna farko saboda biyayyar iyaye, na biyu don na ƙuntata. Amma ba don haka ba ko kallo ma kin ishe ni ne, ma ta masu class da waye wa ma ban kalle su b ballantana ke da kike..."
Kuka ta fashe da shi tana cewa.
"Ya isa ya ishe ni haka, ba sai ka ci mun mutunci ba, na ji ban ai matsayin..."
Tsawar da ya daka ma ta ne ya saka ta haɗiye sauran maganar, ke har kin isa ki dakatar da ni ina magana, last warning da zan Maki shi ne kada ki sake daga Mani hannu idan kina mun magana idan ba haka ba sai na ɓalla hannunki, don ma kin samu na taɓa jikinki har kike ma ni wani zancen banza dole ce ni ma ki sani ba don ƙaddara ba ba ki kai matsayin ba kuma ba za ki kai ba, dama wancan shashashan ustaz ɗin ya dace da ke ba ni ba "
Ya yi maganar yana saukd Glass ɗin motar ya yi dirban alama ya zo.
Zuciyarsa cike da takaici me ya saka ma ya sa wa iyayen yarinyar nan ya amince ne, sai yanzu take jin haushin kansa, ya dai san baya son ta to ta ta zai zauna da ita.
Har suka ƙarasa gidan ba wanda ya yi magana a cikinsu.
"Get out in my car."
Ya daka ma ta tsawa, da sauri ta fice tana kuka. Gajeren tsuki ya ja yayin da suke barin gidan.
*Ma'eesha.*
Suna ƙarasa wa ƙofar gidan hangi makaho na fitowa daga cikin gidan hannunsa rike da kayan aikinsa na gyaran takalma.
Tun daga nesa ta hango shi yana tafiya hannunsa ɗaya yana rike da kayan aikin gyaran takalminsa daya hannun rike da sandarsa ta jagora.
Yana jin mai nape ya tsaya a ƙofar gidan ya tsaya.
Fitowa ta yi daga cikin nape ɗin tana kallonsa da kayan aikinsa dake hannunsa.
Kafin ta dauke idanunta lokacin da mai keke nape ɗin ke ma ta magana.
"Hajiya sai kin samu wanda zai taimaka ma ki ya shigar ma ki da kayan cikin gidan."
"Ba damuwa ka ajiye kawai ka yi tafiyar ka zan nemo wanda zai taimaka ma ni."
"Idan ba damuwa zan shigar ma ki da shi ciki."
"A'a ka bar shi kawai ka yi tafiyar ka zan shigar da kayan."
Wani kallo mai nape ɗin ya yi ma sa kafin ya ce.
"Kai kuma daga ina, kana makaho har da sandar jagora ne za ka iya ɗaukar kayan nan da wani ido za ka ga in..."
Ma'eesha ta dakatar da shi ta hanyar cewa.
"Ya isa Mallam don yana makaho ba shi ke nufin kasashshe ba ne, to shi ne maigidan ya ce ba sai ka shiga ba don haka maganarsa ta zauna."
Wani kallo ya yi wa Ma'eesha na mamaki da al'ajabi kafin ya kalli makaho ya ce.
"Dama da kika ce ke matar aure ce daga gaske ne, kuma wannan ne mijin naki?"
"Eh shi ne mijin nawa sai aka yi ya ya?"
"Amma Hajiya a yadda kiken nan a ce makaho kike aure faƙiri ko dai asiri ya yi ma ki ko kuma auren manufa kika yi ne?"
Ba ta tanka ma sa ba ta buɗe jakarta ta ga 100k ya rage ma ta, ta ciro 10k ta mika wa mai nape ɗin ta ce.
"Na gode za ka iya tafiya ."
Washe baki ya yi sannan ya shiga ciki yana ma ta godiya ya bar wajen.
Makaho ne ya dauki karamin buhun shinkafar a hannu ɗaya, ɗayan hannun ya ɗauki katon ɗin taliya da na macaroni da cus-cus.
Da mamaki take kallonsa har ya shiga gidan ta bi bayansa tana kallon ikon Allah.
Ba ta yi mamakin ɗaukar kayan ba, saboda yana da ƙira irin na zaratan jaruman maza, don jikinsa ma a murɗe yake kamar irin mazan da suke yawan motsa jiki suna daga ƙarfe. Amma yadda ya ke tafiya haka nan ne ya ba ta mamaki.
Sai da ya gama ta kalle shi ta ce.
"Ta ya ka iya tafiya haka nan ba tare da ka yi karo da komai ba?"
Murmushi ya yi ya ce.
"Na riga na karanci yanayin gidan bayan fitar ki sai da na auna ta hanyar tafiya na san taku nawa zan yi da idan na kawo saitin ƙofar dakin na sani."
"Ina za ka je yanzu?"
"Zan je ne ko Allah zai sa na samu wani abun, gyaran tsakani nake zuwa?"
"Ta ya kake gane kalar takalmin da za ka san irin foolish ɗin takalmi fari ko baƙi?"
"Idan aka kawo ni kan tambaye wani kala ne, kafin na san irin kayan aikin da zan yi amfani da shi, duk countener dada nake amfani da su daban-daban ne na san na fari da na baki da kowane kala, iska tsinke wa ne idan na laluba ina gane wa sai na ɗinke."
"Ka hakura da fita don ina son mu yi gyaran dakin nan, za ka dinga ko mika Mani wani abun ne idan na ba ka ka rike za ka iya ko?"
"Zan iya in sha Allah."
Daga nan ya fita ya shigo da kayan aikinsa.
Ita kuma ta shiga ciki ta fara fito da trolly ɗin kayanta.
Har ya ajiye a barandar. Sai ya koma gefe ya tsaya.
Shara ta fara yi ta kwashe sannan ta shimfida leader carpet da ta siyo ya cika ɗakin ya yi kyau sosai.
Sannan ta shiga da ƴar madaidaiciyar katifarta ajiye a inda ya dace.
Sannan ta shimfida zanin godon ta sanya rigar pilow a pillow biyu da ta siyo ta jera.
Duk da kasancewar tana da mai yi ma ta gyaran ɗaki da wankin toilet amma hakan bai sa mahaifiyar ta ta bar ta haka ba ta koya ma ta ba, don ita ke gyara wa Mahaifinta ɗaki.
Labule ta ɗauko guda biyu na koda da window, a jikin bangon ɗakin ta samu ƙusa ta buga labulen na kofa da na window.
Sannan ta kalle shi ta ce.
"Ko za ka iya shigo ma ni da kayan nan duka?"
Kai ya jinjina ta ɗaga labulen ta sakala a jikin kofar.
Haka ya dinga shigo da kayan tana nuna ma sa in da zai ajiye, da zaran ya kai wajen za ta ce ma sa ya yi ya ajiye.
Har aka gama shigo da komai.
Kitchen ɗin fale-fale dake tsakar gidan ne ta ce ma sa ya dauki karamin buhun gawayin ya ajiye a ciki tare da murhun gawayi.
A barandar ta ajiye ƙaramin Gas da ta siyo ta ce.
"Ka yi a hankali kar ka karaso ta nan gefen na ajiye Gas zan yi girki."
"To in sha Allah."
Shiga ciki ta yi ta buɗe kwalin tukwane da ta siyo, ta ciro ƙaramar ciki ta kunna gask ta zuba ruwa. Sannan ta ɗauko tabarma ta shimfida a gefe ta ce.
"Ka zauna ma na "
Sai da ya laluba ya ji inda tabarmar take sannan ya zauna a gefe.
Ita kuma ta dauko kujerar tsuguno na roba da ta siya ta zauna akai.
Sallama suka ji daga waje ana yi.
Makaho ya amsa sallamar yana mikewa tare da ɗaukar sandarsa.
"Wa'alaika salam warahmatullah."
Ya amsa yana nufar kofar gidan.
"Mallam Iro mijin Larai Dillaliya ne ya zo amsar kuɗin haya."
Jin haka ya saka Ma'eesha cewa.
"Ga kuɗinsa ka kai ma sa na san shi ya zo amsa."
Ta yi Maganar tana shiga ɗaki ta dauki handbag ɗin ta.
"Ana zuwa ."
Makaho ya yi maganar yana daga murya yadda Iro zai ji shi.
50k ta ƙirga ta ba shi yayin da kudin ya rage ma ta saura dubu arba'in.
Yana ganin makaho ya ce.
"Khalifa Barka da safiya."
"Barka dai Mallam Iro ya al'amura?"
"Alhamdulillah."
Kudin ya mika ma sa ya karɓa ya kirga ya ga sun cika.
"Ma sha Allah kudi sun cika, amma fa akwai dubu biyar da ya kamata Ku ba Ni da dillanci. Amma na yafe ma ku."
"To mun gode Allah ya saka da alkhairi ya sa la fi haka."
Da Amin ya amsa ya ma sa sallama ya bar gidan.
_Nadra_
Da kuka ta shiga ciki kai tsaye ta nufi ƙofar ɗakinsu ta shige, kan gado ta faɗa tana ci gaba da rusa kuka.
Gwaggo Laraba ta bi bayan ta da sauri.
Kan gadon ta nufa in da Nadra ke kwance ta kalle ta tana ɗaga ta .
"Nadra lafiya me ya faru?"
"Ba a gaban idanunku kuna kallonsa yana taɓa jikina duk da haka bai ma sa ba sai da ya tallabo fuskata ya haɗa bakinsa da nawa ya tura mun cake a cikin bakina, ba wanda ya yi ma sa magana ko ya hana sai sai tafa ma sa ake yi. Sannan kuma don na ma sa magana rashin dacewar abun da yake ma ni don na daga ma sa hannu wai idan na sake daga ma sa hannu sai ya karya hannun har yana zagin saurayi na wai wancan shashashan ustaz ɗin ne ya dace da ni, wallahi Ya Sayyadi ba shashasha ba ne mutum ne mai tsoron Allah da kiyaye dokokin Allah ba kamar shi da yake take dokokin Allah ba yana taɓa macen da ba matarsa ba. Wallahi Gwaggo ba namijin da ya taba rike ko da ƙumbata amma shi lokaci ɗaya ya zo ya..."
Dariyar da ta ji daga bakin kofar ne ya saka ta dakata tana kallonta fuska a murtuƙe.
Wata ƴar Gwaggo Laraba ce take dariya ta ce.
"Yanzu ma aka fara ba ki yi kuka ba tukuna."
Wani kukan ta saka saboda dariyar ya ƙular da ita, sai da Gwaggo Laraba ta Kore ta Sannan ta ce wa Nadra ta tashi ta yi wa wanka ta yi sallah.
Bayan kamar mintuna talatin ta shigo ta samu Nadra akan sallaya.
Wasu kaya ta ajiye ma ta wanda Nadra na ganin kayan ta mike tsaye tana cewa.
"Wannan ai kayan da Sunyi Sidra za ta saka ne idan za'a kai ta gidan mijinta, ko har ta dawo ne?"
"Ba na son yawan tambaya ki shirya cikin wannan kayan ki fito Falon Abbanki yana kiranki."
Haka kawai ta tsinci kanta da mummunan faduwar gaba wanda ba ta san dalili ba. Wayar Sidra ta gwada kira still switch off.
Zama ta yi bakin gadon taba kallon tsadadden leshin da kudinsa zai kai Naira dubu ɗari biyu. Da set na ɗan kunne da sarƙa siriri na Gold.
_Fahad_
Yana zaune a falo shi da iyayensa. Baba, Mama, Aunty Rahama sai mahaifiyar Baba wacce ake kira da Inna.
Mama ce take faɗa tana cewa
"Zancen banza waye za ka ajiye wa ita a nan? Wato saboda ba ka son ta ko? Ina ce a baya da muka ce a gyara ma ka part ɗin ka ka zauna da ita ka ce ba za ka zauna da matarka a family house ba. Saboda za'a saka ma ka idanu a takura ma ku. Wato saboda wacce kake so ta gudu ita wannan tun da ba son ta kake yi ba shi ne za ka ce wai kada a kai ta sabon gidan da ka yi niyyar zama da matarka ka fasa ko? Sannan za ka ce a kawo ta a ajiye a family house bayan a baya ka nuna ba ka so ko? To ba ka isa ba yadda ks hana gyara gidan aka kai ma ta kaya gidan iyayenta suka jera kaya tun shekaranjiya ba wanda zai je ya kwaso kayan nan, kuma dole ka zauna da ita a gidan, to uban waye za ka bar wa gidan ya zauna?"
Ina ta amsa da cewa .
"Kila har yanzu yana jiran ita waccen da ta gudu ta dawo ne ya saka ta a ciki, don alama ya nuna haka."
"
Baba ya yi saurin cewa.
"Haba sai ka ce ba Musulmai ba ta ya ya zai auri wa sannan ya auri ƙanwa kamar maguzawa? Ko maguzawa ai ba za su yi haka ba."
"Idan ma tana cikin zuvuyarka ka cire ta don ko saki Nadra saboda Sidra ba wanda zai yarda ka aure ta."
Cewar Aunty Rahama tana kallon Fahad da ta hade fuska kamar bai taɓa dariya ba.
Tashi ya yi ya bar ma su ɗakin suka bi shi da kallo, Mama ta raka shi da harara don har ga Allah tana ƙaunar Nadra.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce ✍️
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page1️⃣0️⃣
Tashi ya bar ma su ɗakin suka bi shi da kallo, Mama ta raka shi da harara don har ga Allah tana ƙaunar Nadra.
Baba ya kalli Mama ya ce.
Matuƙar yau iyayen yarinyar nan suka kai ta gidan mijinta to ki tabbatar bai kwana a gidan nan ba."
Jinjina kai Mama ta yi tare da cewa.
"In sha Allah."
_Makaho_
Yana zaune a tabarmar da Ma'eesha ta shimfiɗa ma sa ya ji muryarta tana cewa.
"Ba ri na je na siyo bread a shagon dake nan kusa da mu."
Bai tanka ma ta ba ita ma ba ta jira cewarsa ba ta yi ficewar ta.
Ba ya jima ba ta dawo da bread a leda da gwanhwanin milo da na madara.
Ta ajiye har ga Allah ta ji dadin siyayyar da ta yi, ba don ta yi tunanin siyar da wayar ba su da ba ta san yadda za ta yi ba. Duk da cewar a yanzu ma hankalin nata bai kwanta suka ba, saboda ta san yau da gobe duk abinda ta siyo za su ƙare ya za ta yi ne ina za ta samu wasu kuɗaɗen har ta sake siyo ma
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 49