yi. Sanin irin son da Sidra ke yi wa Fahad, da yadda Fahad ke son ta. Ita Nadra da ba ce yana son ta ba ya za ta yi musamman da ta san halin Halin Nadra da dabi'arta ya sha banban da na Fahad.
Har suka gama gaisuwar suka tafi ta kasa magana tausayin Nadra kawai take yi .
Sallama suka yi ma su suka tafi .
A hanya ma kasa magana da juna su Fahad ya yi, domin su kadai suke ta firar su.
Suna isa gidan tun a harabar gidan ana ganinsa aka fara rangaɗa guɗa.
Abokan wasan sa na tsokanarsa bai bi ta kansu ba ya yi wucewarsa part ɗin sa.
Bai tsaya falo ba ya shiga bedroom ya mirza key ya rufe ya cire takalminsa da hularsa, sannan ya cire babban rigarsa ya cire rigar ciki.
Ya saura sai farin singileti a jikinsa. Agogon hannunsa ya kwance ya kwanta a saman tangamemen gadonsa.
.
Yana jin ana knocking amma ya share bai bude ba har suka gaji suka bar shi.
Abinci da aka ajiye masu da abun sha kowa ya fara ɗibar abinda ke ransa yana ci.
Suna nan sai ga wasu abokan na Fahad sun shigo cikin falon.
_Nadra_
Ta sha kyau iya kyau kamar ba ita ba, baƙar fatarta mai matukar kyau da ƙyalki sai shinning take yi.
Ga kayan ɗinkin riga da siket na less ta saka a jikinta, cikin kayan da Fahad ya siye wa Sidra ne wanda kudinsa zai kai kimanin dubu ɗari biyu. Sai arkar gold da ta saka kunne da wuya, har da warwaro da zobe.
Kasancewar ta ba mai son nuna jiki ba kuma less ɗin sun kama ma ta jiki ya saka ta saka babban gyale, duk da Hijabi ta so sakawa sai da Gwaggo Maimuna Yar Abba ta hana ta.
Shi ne fa ta saka babban Hijabin kasancewar ba kowa ya san cewa Sidra ba ta nan ba ya saka wasu da suka san ba Nadra ke aure ba ya saka suka tambayar ina Sidra take, ita kam sai sai ta ce ma su tana nan dawowa ta fita ne, wasu kuma sai ta sanar da su cewa ta tafi gyaran jiki ne.
Mamaki wasu ke yi ace yau ɗairin auren amma a ce ta je gyaran jiki, me ya saka ba ta yi da wuri ba
Ƙawar Nadra ɗaya ce wato A'isha Humaira, ta zo tana sanye da hijabi da niƙab a fuskarta.
Tana zaune kusa da Nadra suna firar yadda Sidra ya tafi wani wajen ta dade ba ta dawo ba.
Har lokacin sallah la'asar ta yi suka tashi Nadra ta shiga ta ɗauro alwala, sannan A'isha ta shiga.
Suna zaune suna azkar din yamma sai ga ƴar Gwaggo Laraba, wacce ba za ta wuce sa'ar Nadra ba ta shigo ta ce.
"Dama Mama ce ta ce na duba ko kin yi sallah mai kwalliya za ta zo ta yi ma ki kwalliyar zuwa Dinner party kafin ango ya ƙaraso tare za ku tafi da shi."
Zumbur ta mike tsaye tare da cewa.
"What?"
Wani kallo ta yi wa Salma kafin ta ce .
"Waye zai je Dinner party? Allah ya kiyaye, ni duk ire-iren waɗan nan wurare ban taɓa zuwa ba, duk wani taro in dai ba walima ba ce to ba zan tafi ba ballantana q ce na je a madadin Aunty Sidra, a jira idan ta dawo su je ta yi amma ba zan iya ba, I try my best but ba zan iya zuwa Dinner party ba."
Ta fada kamar za ta yi kuka.
Salma ta fit don ta sanar wa Mahaifiyar ta abinda ya faru.
_Fahad_
Har karfe uku da rabi bai fito ba, da ya ga lokacin sallah ta yi na ya shiga bathroom ya ɗauro alwala ya fito
Nan suka cigaba da firarsu .Ganin karfe uku da da rabi ta yi ne ya saka suka je suna knocking.
Daidai lokacin shi ma zai fito don zuwa masallaci.
Shi ma sai a lokacin ya lura da abokinsa Sadik daje ƙasar Canada ya iso.
Rungume juna suka yi sanan suka fita tare don duk sun yi alwala a bathroom dake falon.
Gabɗaya suka je masallaci, suka bi jam'i aka yi sallah.
Bayan an idar a tare suka fito suka koma ciki.
Daidai lokacin ne Yar Fahad Aunty Rahama ta shigo.
Dukkanin su suka gaishe da ita don duk sun san ta don Fahad na zuwa da su gidanta .
"Se Aunty Babba."
Cewar Sadik yana dariya .
Kallon su ta yi tana cewa.
"Lokacin Dinner party ya kusa ku je ku saka shi ya shirya bana son Afrikan time."
"Wai ya ce b zai je Dinner party din nan ba an fasa yi ."
"Akan me wanna ai zandan banza ne, dole a yi shi kamar yadda ka tsara tun farko, idan zai cire wa kansa damuwa ya rungumi ƙaddararsa."
Tana fadar haka ta shiga bedroom, yana zaune a bakin gado ya yi shiru cikin tunani
Dafa kafaɗarsa t yi ya ɗago kai ya kalle ta.
"Tashi ka shirya ku je ka ɗauki Amaryarka ku je wajen Dinner party."
Kwaɓe fuska ya yi kamar zai yi kuka, kafin ya buɗe baki zai yi magana ta ce.
"Ba na son jin komai, kuma na fahimci matsalarka, ka yi abinda na ce maka kawai."
Dole ya tashi ba tare da ransa ya so ba ya nufi bathroom, sai da ta ji saukar ruwa alamar ya fara wanka sannan ta fice.
Don dama su matan sun shirya zuwa reception ɗin .
_Ma'eesha_
Tana zaune a ɗakin tun da ta idar da Sallah ta yi azkar ba ta tashi ba, tana tunanin hanyar da za ta samu dubu hamsin ta biya kudin hayar gidan nan.
Ga shi ta yi ma sa alkawarin yau za ta bashi kudin.
Sallamar makaho ta ji ya shigo, ta amsa ba tare da ta kalle shi ba.
Shigowa ya yi ya zauna kafin ya ce .
"Ina kwana?"
Sai a lokacin ita ma ta ce ma sa .
"Ina kwana?"
"Kin tashi lafiya?"
"Alhamdulillah."
"Ya zaman hakuri da rashin barci."
"Ai Ni na yi barci kai ne dai ka kwana a zaune kana ma ni fifita ."
"Ke ma ba barcin kika yi ba, na ji kina ta motsawa."
Tunani take yi 1k ya rage ma ta idan ta siyo abin da za su ci shi kenan ba ta da komai.
Wani tunani ta yi kafin ta ce.
"Zan fita na je na siyar da wayata ko zan samu na biya kudin hayar gidan nan, kuma sauran canjin mu samu na cin abinci da dan abun buƙata da ya dace.
Shiru ya yi kafin ya ce .
"Idan kika siyar haka za ki zauna ba waya?"
"Ai wayoyina biyu ne da ni, zan siyar da babbar na rike ƙaramar ina amfani da shi. Na san kudin zai yi yawa . Don wayar miliyan daya da dubu ɗari biyar aka siya mun, ko miliyan ɗaya idan na siyar zan samu abubuwa da yawa da zan siya ma su sauƙin kuɗi, kamar karamar katifa labule kayan aiki da kuma kayan abinci."
Shiru ya yi kafin ya ce .
"Allah ya tsare ya dawo dake lafiya ya sa ki samu abin da kike nema."
"Amin ya Allah, bari na je kafin mai karɓar kudin hayar ya zo ya yi Mani sallama."
Tana fadar haka ta tashi dama rigar Abaya ne a mijinta baƙa. Rolling kanta ta yi da mayafin abayar sannan ta dauki handbag ɗin ta da wayoyin ke ciki ta fice.
*Maman Ihsan ce.*
090 5327995
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce ✍️
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page0️⃣6️⃣
Tana fadar haka ta tashi dama rigar Abaya ne a jikinta baƙa. Rolling kanta ta yi da mayafin abayar sannan ta dauki handbag ɗin ta da wayoyin ta ke ciki ta fice ba tare da ta san in da ta dosa ba.
_Aunty Rahama_
Tana fita daga part ɗin Fahad ta nufi part ɗin Mama.
Tun kafin ta karasa jikin kofar bedroom ɗin take ta jin muryar kanwar mahaifiyar su wato Hajiya Jummai mahaifiyar Farida.
"Ai shi kenan ku shirya ku tafi wajen Dinner ni dai ba in da zan je a yanzu haka. Don Yaya na gama gane cewa ba ki ƙaunata ba ki ƙaunar ƴata. Saboda Fahad Farida ta bar garin ta ta bar iyayen ta da kowa na ta ta dawo nan gidan da zama, ba don komai ba sai don ta samu kusanci da Fahad. Amma yaron nan ya yi kamar bai gane tana son sa ba. Da ta gaji da bayyana ma sa irin son da take ma sa ya wulakanta ta, kuma kina cikin gidan nan kun san me ke faruwa. Yanzu yarinyar da ya ƙwallafa rai a kanta an ce ta gudu ta bar gidan iyayen ta. Madadin ya zo a bashi ƙanwarsa ya aura shi ne ya je aka ba shi kanwar yarinyar ya aura ko? Sanadin Haka ga Farida can kwance na kasa gane kanta, ba sunan da take kira sai na Yaya Fahad."
Murmushi Mama ta yi tare da cewa .
"In ban da abin ki Jummai ai ni abun farin ciki ne a wajena a ce ga ɗana zai auri ƴar ƙanwata. Amma ya ce baya son ta to ya za mu yi? Ba dole a bar shi ya auri wacce take so."
Hajiya Jummai za ta sake wata magana ta ga Mama ya tsuke ma ta fuska tana dauke kai alamar ba ta son zancen, ga hankulan mutane ya dawo kansu.
Mama fita ta yi daga cikin dakin tana tarbar baƙin da ke zuwa a lokacin.
Kasancewar Yamma ta yi lokacin da za'a je Dinner party ya yi mutane suka fara shirye-shiryen zuwa Dinner party. Ankon fari da baƙi suka yi . White an black.
Mata suka sanya ankon nasu material fari da baƙi ne sun yi kyau sosai.
Bangaren Fahad ma zuwa lokacin samari ne cike da falon nasa, su na sun yi ankon yadi na fari mai ratsin baƙi a jiki.
Gabɗaya kalar yadin suka sanya ba abinda ke tashi daga cikin falon sai waƙar bikin Fahad da aka yi da sunan Sidra.
_Aunty Rahama_
Ita ma ta shirya cikin ankon nata ɗinkin doguwar riga, tana rike da hannun ƙaramar ƴar ta mai suna Zahrah yar shekaru uku a duniya.
Part ɗin Fahad ta nufa don ta tabbatar ya shirya ganin karfe biyar ya kusa yi.
Da sallama ta shiga cikin falon, Sautin waƙar da bikin kawai ke tashi wasu na rawa yadda wakar ke ma su dad'i.
Hanyar bedroom ɗin Fahad ɗin ta nufa sai suka haɗu a corridor.
Shi ma angon ya yi dressing White and black. Yana sanye cikinsu tsadadden Suit ɗin sa baƙi, da farin shirt a ciki, ya sanya farin glass a idanunsa. Ƙafarsa sanye cikin cikin takaninsa cover shoe mai baƙi ƙirar Louis Vuitton mai ƙamshinsa mai dadi ke tashi daga jikinsa.
Hannunsa ɗaure da tsadadden agogonsa, ya yi masifar kyau wanda ya kara fito da ajinsa da kwarjininsa.
"Tabarakallah ma sha Allah, tsarki ya tabbata ga uban gijin da ya halicci wannan kyakkyawan angon."
Sai a lokacin ya lura da ita,kallonta ya yi fuska ba walwala .
"Na gaji da ganin wannan murtuƙewar taka haka, har yanzu kana tunanin Sidra ko?"
Bai ce komai ba ya kau da Kai gefe yana kallon wani wajen daban. Don haushin kowa ka yake ki a cikin Rayuwarsa
"Ka rungumi ƙaddararka a yadda ta zo maka Fahad. Don Allah ka yi kokarin cire Sidra daga cikin rayuwar ka, ka ɗauka ita ba matarka ba ce Nadra ce matarka. Dama can hakan Allah ya tsara, wata ba ta auren mijin wata, haka kuma wani baya auren matar wani. Ka rungumi Nadra ka yi irin rayuwar da ka tsara yi da Sidra da ita, ka ba ya kulawar da kake ba wa Sidra ka ƙunace ta kamar yadda ka ƙauna ci Sidra."
Girgiza kansa ya yi yana cewa.
"Ba na iya tunanin zan yi haka Sunyi Rahama."
Saboda ba ka son ta ko?"
Shiru ya yi ba tare da ya ce komai ba. Sai ya ji muryar ta tana sake cewa.
"Saboda ita ba fara ba ce iya ɓaka ce ya saka ba ka son ta masai Sidra baƙa ko?"
"Ba wannan ne kawai matsalar ba, ita wanann yarinyar sam ba ta waye ba, ta cika sanyi da yawa ga ta da zubin munafukai, ta dinga sunkuyar da kai wai ita mai kunya ni ba na son mace mai kunya, yadda kina san wata mutumiyar da can baya haka take sam ba ta waye ba. Wallahi ba na jin zan iya rayuwa da ita ba."
Murmushi Aunty Rahama ta yi tana cewa.
"Wannan ba matsala ba ne, kai za ka iya canz ta ta koma yadda kake so? Kai za ka koya ma ta son ka da irin rayuwar da kake so matukar bai sabawa addini ba. Don haka ka saki ranka don Allah ka daina wanann haɗe rai da kake yau rana ta musamman ce a wajanka ba ka ga yadda kowa ke farin ciki saboda kai ba, to kai me zai sa ka kasace cikin bakin ciki?"
Murmushi ya yi wanda iya fatar bakinsa ta tsaya sannan ya yi wa Zahrah Baby alamar ta zo.
Da sauri ta saki mahaifiyar tata ta nufi wajen uncle Fahad ɗin ta ta rungume shi.
Hannunta ya rike suka nufi falon Sunyi Rahama n jaddada ma sa wasu sun wuce ya je su dauki Amarya su tafi. Da to kawai ya amsa har ya karasa suke gaisawa da sauran wadanda suka zo ma sa .
Daga nan ne kuma aka fara fita don zuwa wajen Dinner party.
Shi ma fitowa ya yi suna tafiya yayin da Zahrah Baby ta nufi mahaifiyarta ganin za ta shiga wani motar.
Fahad kuwa wajen sabuwar motarsa wacce ya siya bai fara hawa ba sai yau, da burin yau ne zai fara hawanta shi da Sidra ashe ba haka ba ne shi da Nadra zai hau ta.
Wasu daga cikin abokan ango motarsu na cikin gidan suka shishshiga wasu kuma na su na waje ne suka dinga fita zuwa wajen motocin.
Wata galleliyar mota ƙirar Lamborghini urus ya nufa wanda yana ƙarasawa wajan motar sai ga diraba ya bude ma sa bayan motar, bayan ya shiga sannan ya rufe da hanzari direba ya nufi mazauninsa ya yi wa motar key suka bar gidan.
Jingina bayansa ya yi da jikin motar sit ɗin motar ya lumshe idanunsa ƙamshinsa da sanyin ac ke ratsa kowane sashe na motar.
A ƙofar gidansu Nadra direban ya yi parking don ya san inda za su fara zuwa kafin su tafi Dinner party.
Yana ƙarasawa ya ga motoci na barin wajen.
_Nadra_
Bayan an gama yi ma ta wani kwalliyar ne aka fito da kayan da za ta saka.
Karɓa ta yi ta warware kayan ta juya gaba da baya ta kalle shi da kyau sannan ta ce.
"Yanzu Wai wannan kayan kuke tunanin ni Nadra zan saka?"
Gwaggo Laraba da mai kwalliyar sai wata ƙanwar Umma daje ɗakin suka kalle ta. Kafin su yi magana ta ce .
"Ku duba fa ku gani kayan ko hannun arziki bai da shi hannun ƙarani ne ga shi gaban rigar irin mai bayyanar da ƙirar halittar mace ne, wato shape ɗin ƙirjinta, don an yi ma sa gidan breast .
Yanzu dama ranar da Aunty Sidra suka fita da Yaya Fahad ta ce za su je siyan rigar da za su yi Dinner party da shi wannan kayan suka siyo? A yanzu a matsayin ta na matar aure ne za ta saka wannan kayan ta fita cikin jama'a ana kallonta? Shi ma Yaya Fahad da suka fita zaɓen kayan ya san wannan kayan suka zaɓo zai bar matarsa ta saka ta shiga cikin jama'a maza da mata?"
Ƙawar Umma mai suna Hajiyayye ta kalli Nadra ta ce.
"Daughter ki yi hakuri ki saka ku tafi ga angon can a mota yana zaman jira da?"
Kwaɓe fuska ta yi tare da cewa .
"Ba zan iya saka wannan kayan ba?"
Yar Abba Gwaggo Maimuna ce ta daka wa Nadra tsawa ta ce.
"Za ki saka ku tafi ana jiran ki ko sai na ɓata ma ki rai yanzu?"
Kasancewar Gwaggo Maimuna tana da zafi sosai ko Abba shakkarta yake yi, family ba wanda baya tsoron ta.
Gwaggo Laraba dai ba ya ce komai ba, don ita ma ta ga rashin dacewar kayan a wajen mace mai kunya wacce ta saba shigar mutunci da kamala ba za ta iya saka kayan nan. Kuma ta ga laifin Fahad wanda aka ce shi da Sidra suka zaɓo kayan, wani irin rashin sanin ya kamata ne ya bari matarsa ta shiga jama'a da wannan kayan, idan Sidra ba ta da hankali ai shi yana da wannan ai ba wayewa ba ne, tana tsaka da wannan tunanin ta ji muryar Gwaggo Maimuna na cewa.
"Nadra idan ba ki saka kayan nan kun tafi ba wallahi yanzu zan saka a danne mani ke na saka ma ki kayan nan ta karfin tsiya, ita Sidra da za ta saka me kika fi ta ne, ko ita ma ta san ciwon kanta ba sai ke ce mai sanin ya kamata, to sannu uztaziyya."
Gwaggo Laraba za ta yi magana kenan sai Gwaggo Maimuna ta ce .
"Ki yi Mani shiru Laraba idan aka biye ma ki yarinyar nan ba za ta saka kayan nan ba, don ba zan iya lallaɓa ta da kike yi ba, tun dazu sai bata wa mutane lokaci take yi ana ta jiranta."
Ba yadda Gwaggo Laraba ta iya saboda Gwaggo Maimuna yayarta ce, kuma ko mahaifun Nadra ne idan ta yi magana baya yi ma ta gardama don haka ta jinjina wa Nadra kai tana ma ta murmushi alamar ƙwarin guiwa.
Don haka Nadra ta saka kayan wanda ya yi masifar yi ma ta kyau, sai dai sun kama ta duk shape ɗin ƙirjinta ya fito da hips ɗin ta ma su ɗaukar hankali.
Dogowar rigar irin wanda bayansa je sharar ƙasa ne idan tana tafiya.
Kuka take son yi sai Gwaggo Maimuna ta ce.
"Ki haɗiye kukan nan kar ki kuskura ya fito waje."
Jin haka ya fasa kukan ta haɗiye shi mai kwalliya ta gyara ma ta in da hawayen ya zubo.
Ita ma kayan nata white and black ne, don rigar dari da baƙi ne sai mayafin kamar net da ka daura ma ta ne fari zalla.
Sarƙar gold ɗin ta aka saka mata a kunne da wuya sai hannu da yatsu wato warwaro da zobe. Da aka saka ma ta. Sai wani takalmi mai tsawo sosai da tsini ta saka. Wanda tsinin takalmin ya yi yawa. Kuma dama ita ba ma'abiciyar saka dogon takalmi ba ne duk, takalmi mai tsawo ba ne flat shoe take saka wa.
Haka ba yadda ta iya ta zira ƙafa tana kallon su yayin da mai kwalliyar ke yi ma ta hoto.
"To sai ki fita ki je ga angon nake can yana jiran ki."
"Ango na muka Gwaggo?".
Sai a lokacin Gwaggo Maimuna ta san cewa ta saki layi.
"Au angon Sidra nake son cewa fa."
"Ni wallahi da ta dawo na yanzu na huta da wannan masifar, ga shi wani gyaran jiki ne tun safe har yamma ba ta dawo ba?"
"Za ki wuce ko sai na ɓata ma ki rai?"
Tafiya take yi a hankali kasancewar ba ta iya tafiya da irin takalmimin nan ba.
Salma ƴar Gwaggo Laraba ke bin bayanta za ta taka ta wajan motar, don ƙawar ta A'isha Humaira ta wuce gida bayan ta yi sallar la'asar.
Yana zaune a bayan motar har lokacin idanunsa a lumshe suke.
Kamar an za ce ya biɗu lumtsatstsun idanunsa ya sauke su akan ta ta jikin mirror ya hago ta tana tafiya kamar wacce take tausayin ƙasa ta nufo motar .
_Makaho_
Bayan fitar Ma'eesha da ne ya samu ya kwanta a saman zanin da ta shimfida ma sa, sakamakon rashin rarcin da bai yi ba, don ko na mintuna biyar bai yi ba, ta sakamakon kwana da ya yi a zaune yana aiki. Yi wa Ma'eesha tare da kore ma ya sauro.
Yana kwance a saman zanin yana tunani sabuwar rayuwar da za su yi da Ma'eesha. Lallai dole ya tashi ya nemi abun yi saboda ya rike ta duk da ya san cewa ba zai iya ɗauka ɗawainiyar ta ba bisa la'akari da irin rayuwar da ta ta so ta saba da shi, da kuma abincin da ta saba ci da irin ruwar da ta saba sha da makwancinta da suturarta da mayyukan shafawarta da turarruka da ta saba amfani da su. Ta ya Ma'eesha za ta zauna da shi.
A tunaninsa ba za ta yarda ta zauna da shi ba, ya ɗauka za ta ci mutuncinsa ne ta wulakanta shi ta sa ya sake ta amma sai ya ga ba ta dauki rayuwar da zafi ba ta rungume kundin ƙaddararta, ta yarda tare za su yi karatun tare za su yi hadda sannan kuma tare zasu koka. Tabbas samun mace irin Ma'eesha a wanann zamanin sai an bincika.
Yana ta tufka da warwara har barci ya yi awon gaba da shi nan kwance akan zanin da ta shimfida ma sa .
_Ma'eesha_
Tana fita daga cikin gidan ta tari mai keke nape, bayan ya tsaya ya kalle ta ya ce
"Hajiya ina zuwa?"
"Mallam ka san in da ake siyen waya na hannu?"
"Eh na sani Hajiya, sai sai gaskiya ba su siye da daraja ba, yadda kika san ɓarayi haka suke, za ki siye waya da tsada amma su siye shi a wulaƙance. Amma idan kika je siye a wanensu tsada za su yi Maki."
"Mu je ka kai ni lalura ce ta saka zan siyar."
"To mu je amma ba lallai sun fito ba don sai karfe tara zuwa goma suke fitowa ."
"To mu je idan sun fito na siyar za ka kai ni kasuwa na yi soyayya sai mu kwashi kayan ka kai ni gida."
"To Bismillah."
Ta shiga suka ɗauki hanyar zuwa kasuwar.
Cikin ikon Allah suna ƙarasawa sai ga wani yana kokarin bude shago, da alama shi kadai ne ya fara fitowa .
Kashe kake nape ya yi ya yi ma ta jagora yana cewa.
"Mu je Hajiya."
Tana bin sa a baya suka shiga shagon da sallama.
Mai shagon ya amsa yana kallon su.
"Me kuke so?"
Ma'eesha ta ce
"Waya zan siyar Mallam?"
"Wace irin ce?"
"Iphone 15 ne."
Sai da ya tsaya ya kalle ta da kyau daga sama har ƙasa ya kare ma ta kallo ya tabbata ba ta yi kama da wacce za ta kawo ma sa wayar sata ba.
"Kawo mu gani."
Handbag ɗin ta ta buɗe ta ciro wayar ta ba shi sannan ya karba ya duba da kyau. Kafin ya kalle ta ya ce.
"Na gaji zan siye ta Naira dubu dari huɗu 400k."
Wani kallo ta yi ma sa ta ce.
"Mallam ka san nawa aka siya mun wayar nan kuwa? Ko wata biyu ba'a cika ba da mahaifina ya siya ma ni ita miliyan daya da dubu ɗari biyar na kawo ta yanzu za ka siye ta a wulaƙance?"
"To Hajiya ai ma na siye da daraja idan wasu na Naira dubu dari uku da hamsin za su siye ta, waya ko yau kika siye gobe kika kai kasuwa sai ta karye kin sani."
"Ban sani ba don ban taɓa siyar da waya ba sai sai na kyautar, wanan karon ma ƙaddara ce da ba za ka ganni a nan ba."
"To gaskiya zan siye ta dubu ɗari huɗu da hamsin."
"Don Allah ka kara Mallam wallahi matsala ce ta saka na siyar da wayar ba komai ba, lalura ce."
"Na sani don daga ganin ki kina cikin matsala, don haka zan tausaya ma ki na dutse dubu ɗari biyar 500k idan bai yi ma ki ba ki dauki wayarki ki tafi ."
Shiru ta yi tana mamakin wannan son zuciya a ce a cikin wata biyu ka yi asarar miliyan ɗaya ko rabin kudin ba za'a baka ba."
"Ka siye ko 700k ne mana."
"Ba wanda zai siye wayar nan a haka don sai a daɗe ba'a samu mai siye ba."
Sanin ba ta da wani zaɓi kuka tana bukatar kuɗi don ba ta da shi ya saka ta ce.
"Kawo kuɗin."
"Me nape ya yi saurin cewa.
"Hajjya kada ki siyar da wayar nan ki koma da abun ki gida ki yi hakuri."
Murmushin takaici ta yi tana cewa.
"Dole ne na siyar da wayar ba na da wani zaɓi ne."
"To ki jira wasu su zo sai ki yi ma su tallah."
"Ko sun zo farashi daya muke siyan kaya."
"Gaskiya ba ku da imani."
"Kar ka faɗa mani maganar banza akan sana'a ta, daga ganin ka ma kai karere ne.Hajiya iya dubu ɗari biyar idan ba ki siyar ba sai Anjima."
"Kawo kuɗin."
Ta fada kamar za ta yi kuka.
Ta cire sim da memory card, sannan ta sauke email ɗin ta dake kan wayar, ta goge komai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 49